40 Bible Verses About Hope in Hard Times
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
1 Saboda haka, da yake an same mu marasa laifi ta wurin bangaskiya, muna da salama tare da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi, 2 ta wurinsa ne muka sami shiga wannan alherin da muke tsaye yanzu, ta wurin bangaskiya. Muna kuma farin ciki a begen ɗaukakar Allah. 3 Ba haka kawai ba, amma muna kuma da farin ciki cikin shan wuyanmu, gama mun san cewa shan wuyan nan takan haifi jimiri; 4 jimiri kuma yakan kawo hali mai kyau; hali mai kyau kuma yakan sa bege. 5 Bege kuwa ba ya ba mu kunya, domin Allah ya zuba ƙaunarsa a zukatanmu ta wurin Ruhu Mai Tsarkin da ya ba mu.
-
18 A ganina, wuyar da muke sha a wannan lokaci ba su isa a kwatanta da ɗaukakar da za a bayyana a cikinmu ba.
-
28 Ba ku sani ba?
Ba ku ji ba?
Ubangiji madawwamin Allah ne,
Mahaliccin iyakokin duniya.
Ba zai taɓa gaji ko yă kasala ba,
kuma fahimtarsa ya wuce gaban ganewar mutum.
29 Yakan ba da ƙarfi ga waɗanda suka gaji
yă kuma ƙara ƙarfi ga marasa ƙarfi.
30 Ko matasa ma kan gaji su kuma kasala,
samari kuma kan yi tuntuɓe su fāɗi;
31 amma waɗanda suka dogara ga Ubangiji
za su sabunta ƙarfinsu.
Za su yi firiya da fikafikai kamar gaggafa;
za su kuma yi gudu ba kuwa za su gaji ba,
za su yi tafiya ba kuwa za su kasala ba.
-
13 Bari Allah na bege yă cika ku da matuƙar farin ciki da salama yayinda kuke dogara gare shi, domin ku yalwata cikin bege ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.
-
4 Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji kullum. Ina sāke gaya muku ku yi farin ciki! 5 Bari kowa yă kasance da sauƙinkai. Ubangiji ya yi kusan zuwa. 6 Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya. 7 Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za tă tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.
8 A ƙarshe, ’yan’uwa, duk abin da yake na gaskiya, duk abin da yake na girmamawa, duk abin da yake daidai, duk abin da yake da tsarki, duk abin da yake kyakkyawa, duk abin da yake na sha’awa, in ma wani abu mafifici ne, ko ya cancanci yabo, ku yi tunani a kan irin abubuwan nan. 9 Duk abin da kuka koya ko kuka karɓa ko kuka ji daga wurina, ko kuka gani a cikina, ku yi aiki da shi. Allah na salama kuma zai kasance tare da ku.
-
11 Gama na san shirye-shiryen da na yi muku,” in ji Ubangiji, “shirye-shiryen cin gaba ba na cutarwa ba, shirye-shiryen ba ku sa zuciya da kuma na nan gaba. 12 Sa’an nan za ku kira gare ni ku zo ku kuma yi addu’a gare ni, zan kuwa ji ku. 13 Za ku neme ni ku kuwa same ni sa’ad da kuka neme ni da dukan zuciyarku.
-
13 Babu wanda ya fi Allah, saboda haka sa’ad da ya yi alkawari ga Ibrahim, sai ya rantse da sunansa, 14 cewa, “Tabbatacce zan albarkace ka in kuma ba ka zuriya mai yawa.” 15 Haka kuwa bayan Ibrahim ya jira da haƙuri, sai ya karɓi abin da aka yi alkawari.
16 In mutane za su yi rantsuwa sukan yi haka da wanda ya fi su ne, rantsuwar kuwa takan tabbatar da abin da aka faɗa ta kuma kawo ƙarshen dukan gardama. 17 Saboda haka da Allah ya so yă bayyana nufinsa marar canjawa a sarari ga magādan abin da aka yi alkawari, sai ya tabbatar da shi da rantsuwa. 18 Allah ba ya karya! Haka ma alkawuransa da rantsuwarsa abubuwa biyu ne da ba a iya canjawa. Mun gudu zuwa wurin Allah domin kāriya. Ya kamata alkawuransa su ƙarfafawa sosai mu riƙe begen nan da yake gabanmu. 19 Muna da wannan bege kamar anka na rai, kafaffe da kuma tabbatacce. Yana shiga tsattsarkan wuri na can ciki a bayan labule, 20 inda Yesu, wanda ya sha gabanmu, ya shiga a madadinmu. Ya zama babban firist na har abada, bisa ga tsarin Melkizedek.
-
10 Saboda haka kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai;
kada ka karai, gama ni ne Allahnka.
Zan ƙarfafa ka in kuma taimake ka;
zan riƙe ka da hannun damana mai adalci.
11 “Duk wanda ya yi fushi da kai
tabbatacce zai sha kunya da ƙasƙanci;
waɗanda suka yi hamayya da kai
za su zama kamar ba kome ba su kuma hallaka.
12 Ko ka nemi abokan gābanka,
ba za ka same su ba.
Waɗanda suke yaƙi da kai
za su zama kamar ba kome ba.
13 Gama ni ne Ubangiji Allahnka,
wanda ya riƙe ka da hannun damana
ya kuma ce maka, Kada ka ji tsoro;
zan taimake ka.
-
6 Saboda haka, ku ƙasƙantar da kanku a ƙarƙashin hannun Allah mai ƙarfi, don yă ɗaukaka ku a lokacin da ya ga dama. 7 Ku danƙa masa dukan damuwarku, domin shi ne yake lura da ku.
8 Ku zama masu kamunkai, ku kuma zauna a faɗake. Abokin gābanku, Iblis yana kewayewa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai cinye. 9 Ku yi tsayayya da shi, kuna tsayawa daram cikin bangaskiya, domin kun san cewa ’yan’uwanku ko’ina a duniya suna shan irin wahalolin nan.
10 Allah mai dukan alheri, wanda ya kira ku ga madawwamiyar ɗaukaka cikin Kiristi, bayan kun sha wahala na ɗan lokaci, shi da kansa zai raya ku, yă kuma sa ku yi ƙarfi, ku kahu, ku kuma tsaya daram. 11 Gare shi bari iko yă tabbata har abada abadin. Amin.
-
2 Ku ɗauki wannan da farin ciki mai tsabta, ’yan’uwana, duk sa’ad da gwaje-gwaje na kowane iri suka zo muku, 3 domin kun san cewa gwajin bangaskiyarku yakan haifi daurewa. 4 Dole daurewa ta kammala aikinta don ku zama balagaggu da kuma cikakku, ba ku kuma rasa kome ba.
-
3 Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi! Cikin jinƙansa mai girma ya ba mu sabuwar haihuwa cikin bege mai rai ta wurin tashin Yesu Kiristi daga matattu, 4 da kuma cikin gādon da ba zai taɓa lalacewa, ɓacewa ko koɗewa ba, ajiyayye a sama dominku, 5 ku waɗanda ta wurin bangaskiya ake kiyayewa ta wurin ikon Allah har yă zuwa ceton da yake a shirye da za a bayyana a ƙarshen lokaci. 6 A kan wannan kuke cike da farin ciki ƙwarai, ko da yake yanzu na ɗan lokaci kuna fuskantar baƙin ciki daga gwaje-gwaje iri-iri. 7 Wannan kuwa domin a tabbatar da sahihancin bangaskiyarku ne, wadda ta fi zinariya daraja nesa, ita zinariya kuwa, ko da yake mai ƙarewa ce, akan gwada ta da wuta, domin bangaskiyan nan taku ta jawo muku yabo da girma da ɗaukaka a bayyanar Yesu Kiristi. 8 Ko da yake ba ku taɓa ganinsa ba, kuna ƙaunarsa; kuma ko da yake ba kwa ganinsa yanzu, kun gaskata shi, kun kuma cika da farin ciki ƙwarai, wanda ya fi gaban faɗi,
-
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta ’Ya’yan Kora maza. Bisa ga alamot Waƙa ce.
1 Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu,
kullum yana a shirye yă taimaka a lokacin wahala.
2 Saboda haka ba za mu ji tsoro ba, ko da ƙasa ta girgiza
duwatsu kuma suka fāɗi cikin zurfin teku,
3 ko da ruwansa suna ruri suna kumfa
duwatsu kuma suna girgiza da tumbatsansu. Sela
-
15 Duk wannan fa don amfaninku ne, domin alherin nan da yake bazuwa zuwa ga mutane masu yawa, yă zama dalilin godiya mai yawa ga ɗaukakar Allah.
16 Saboda haka, ba mu fid da zuciya ba. Ko da yake a waje, jikinmu mai mutuwa yana lalacewa, amma can ciki, ana sabunta mu kowace rana. 17 Don wannan ’yar wahalar tamu mai saurin wucewa, ita take tanadar mana madawwamiyar ɗaukaka mai yawa, fiye da kwatanci. 18 Domin ba abubuwan da ido yake gani ne muke dubawa ba, sai dai marasa ganuwa. Gama abubuwan da ake gani masu saurin wucewa ne, marasa ganuwa kuwa, madawwama ne.
-
1 To, ’yan’uwa, game da lokuta da ranaku, ba ma bukata mu rubuta muku, 2 gama kun sani sarai cewa ranar Ubangiji za tă zo kamar ɓarawo da dare. 3 Yayinda mutane suke cewa, “Akwai salama da zaman lafiya,” hallaka za tă auko musu farat ɗaya, kamar yadda naƙuda take kama mace mai ciki, ba za su kuwa tsira ba.
4 Amma ku, ’yan’uwa, ba kwa cikin duhu da wannan rana za tă zo muku ba zato kamar ɓarawo. 5 Dukanku ’ya’yan haske ne da kuma ’ya’yan rana. Mu ba mutanen dare ko na duhu ba ne. 6 Saboda haka fa, kada mu zama kamar saura, waɗanda suke barci, sai dai mu zama masu tsaro da masu kamunkai. 7 Gama masu barci, da dad dare suke barci, masu sha su bugu kuwa, da dad dare suke buguwa. 8 Amma da yake mu na rana ne, bari mu zama masu kamunkai, sanye da bangaskiya da ƙauna kamar sulke, begen cetonmu kuma kamar hular kwano. 9 Gama Allah bai naɗa mu don mu sha fushi ba, sai dai mu sami ceto ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi. 10 Ya mutu saboda mu domin, ko muna a faɗake ko muna barci, mu kasance tare da shi. 11 Saboda haka ku ƙarfafa juna ku kuma gina juna, kamar dai yadda kuke yi.
-
4 Ka cece ni, ya Allahna, daga hannun mugaye,
da kuma daga ikon mugaye da masu mugunta.
5 Gama kai ne abin sa zuciyata, ya Ubangiji Mai Iko Duka,
ƙarfin zuciyata tun ina yaro.
6 Daga haihuwa na dogara gare ka;
kai ka kawo ni daga cikin mahaifiyata.
Kullayaumi zan yabe ka.
7 Na zama kamar abin sa zuciya ga yawanci,
amma kai ne katangata mai ƙarfi.
8 Bakina ya cika da yabonka,
ina furta darajarka dukan yini.
-
5 Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka
kada kuma ka dangana ga ganewarka;
6 cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi,
zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.
-
26 Amma Mai Taimako, Ruhu Mai Tsarki, wanda Uba zai aiko cikin sunana, zai koya muku kome, zai kuma tuna muku duk abin da na faɗa muku. 27 Salama na bari tare da ku; salamata nake ba ku. Ba kamar yadda duniya take bayarwa nake ba ku ba. Kada zuciyarku ta ɓaci kada kuma ku ji tsoro.
-
6 Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tafe tare da ku, ba zai taɓa barinku ko yă yashe ku ba.”
-
Zabura ta Dawuda.
1 Ubangiji ne yake kiwona, ba zan rasa kome ba,
2 Yakan sa in kwanta a makiyaya mai ɗanyar ciyawa,
yakan bi da ni kusa da ruwaye marar hayaniya,
3 yakan maido da raina.
Yakan bi da ni a hanyoyin adalci
saboda sunansa.
4 Ko da na yi tafiya
ta kwari na inuwar mutuwa,
ba zan ji tsoron mugu ba,
gama kana tare da ni;
bulalarka na dūka da kuma sandanka na tafiya,
za su yi mini ta’aziyya.
5 Ka shirya mini tebur
a gaban abokan gābana.
Ka shafe kaina da mai;
kwaf nawa ya cika har yana zuba.
6 Tabbatacce alheri da ƙauna za su bi
dukan kwanakin raina,
zan kuwa zauna a gidan Ubangiji
har abada.
-
18 Amma idanun Ubangiji suna a kan wanda yake tsoronsa,
a kan waɗanda suke sa zuciya cikin ƙaunarsa marar ƙarewa,
-
22 Domin ƙaunar Ubangiji ba mu hallaka ba;
gama jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa.
23 Sababbi ne kowace safiya;
amincinka kuwa mai girma ne.
24 Na ce wa kaina, “Ubangiji shi ne nawa;
saboda haka zan jira shi.”
25 Ubangiji mai alheri ne ga waɗanda suke da bege a cikinsa,
ga kuma wanda yake neman shi;
26 yana da kyau ka jira shiru
domin samun ceton Ubangiji.
27 Yana da kyau mutum yă sha wuya
tun yana yaro.
-
20 Saboda wannan ne na nemi in gan ku in kuma yi magana da ku. Saboda begen Isra’ila ne, nake a daure da wannan sarƙa.”
-
28 Mun kuma san cewa a cikin dukan abubuwa Allah yana aikata alheri ga waɗanda suke ƙaunarsa, yana waɗanda aka kira bisa ga nufinsa.
-
3 Yabo ya tabbata ga Allah, da Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba mai tausayi, da kuma Allah na dukan ta’aziyya, 4 wanda yakan yi mana ta’aziyya a cikin dukan wahalolinmu, domin mu kuma mu iya ta’azantar da waɗanda suke cikin kowace irin wahala, da ta’aziyyar da mu kanmu muka samu daga Allah. 5 Gama kamar yadda wahalar Kiristi ta cika har tana zuba a cikin rayuwarmu, haka nan kuma ta wurin Kiristi ta’aziyyarmu ta cika har tana zuba.
-
5 Amma ta wurin bangaskiya muna marmarin jira adalcin da muke bege ta wurin Ruhu.
-
13 ’Yan’uwa, ba ma so ku kasance cikin jahilci game da waɗanda suka yi barci, ko kuwa ku yi baƙin ciki kamar sauran mutanen da ba su da bege. 14 Mun gaskata cewa Yesu ya mutu ya tashi kuma daga matattu, ta haka muka gaskata cewa Allah zai kawo waɗanda suka yi barci a cikinsa tare da Yesu. 15 Bisa ga maganar Ubangiji kansa, muna gaya muku cewa mu da muke raye har yanzu, waɗanda aka bari har dawowar Ubangiji, tabbatacce ba za mu riga waɗanda suka yi barci tashi ba. 16 Gama Ubangiji kansa zai sauko daga sama, da umarni mai ƙarfi, da muryar babban mala’ika da kuma busar ƙahon Allah, waɗanda suka mutu kuwa cikin Kiristi za su tashi da farko. 17 Bayan haka, mu da muke da rai da aka bari, za a ɗauke mu tare da su a cikin gizagizai don mu sadu da Ubangiji a sararin sama. Ta haka za mu kasance tare da Ubangiji har abada. 18 Saboda haka ku ƙarfafa juna da waɗannan kalmomi.
-
9 Abokaina, ko da yake muna irin maganan nan, mun tabbata kuna yi abubuwan nan masu kyau da waɗanda suka sami ceto suke yi. 10 Allah ba marar adalci ba ne. Ba zai manta da aikinku da kuma ƙaunar da kuka nuna masa wajen taimakon mutanensa da kuma ci gaba da taimakonsu da kuke yi ba.
-
32 Ku tuna da kwanakin nan da suka wuce bayan kun sami haske, sa’ad da kuka tsaya daram a tsananin shan wahala. 33 Wani lokaci a fili an tsananta muku aka kuma zage ku aka kuma tsananta muku; a wani lokaci kuma kuka tsaya tare da waɗanda aka yi musu haka. 34 Kuka ji tausayin waɗanda suke cikin kurkuku, da farin ciki kuma kuka yarda ku rabu da dukiyar da aka ƙwace muku, domin ku kanku kun san cewa kuna da madawwamiyar dukiya mafi kyau. 35 Saboda haka kada ku yar da tabbacinku; za a sāka muku a yalwace.
36 Kuna bukata ku jimre don sa’ad da kuka aikata nufin Allah, za ku karɓi abin da ya yi alkawari. 37 Gama,
“A cikin ɗan lokaci kaɗan,
mai zuwan nan zai zo
ba kuwa zai yi jinkiri ba.
38 Amma,
“Mai adalcina zai rayu ta wurin bangaskiya.
In kuwa ya ja da baya,
ba zan ji daɗinsa ba.”
39 Amma mu ba na waɗanda suke ja da baya, su kuma hallaka ba ne, amma na waɗanda suka gaskata, suka kuma sami ceto ne.
-
8 Ubangiji kansa yana tafe a gabanka, zai kuma kasance tare da kai, ba zai taɓa barinka ko yă yashe ka ba. Kada ka ji tsoro; kada kuma ka karai.”
-
9 Ubangiji shi ne mafakan waɗanda ake danniya,
mafaka a lokutan wahala.
10 Waɗanda suka san sunanka za su dogara da kai,
gama kai, Ubangiji, ba ka taɓa yashe waɗanda suke nemanka ba.
-
17 Adalai kan yi kuka, Ubangiji kuwa yakan ji su;
yakan cece su daga dukan wahalarsu.
18 Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai
ya kuma cece waɗanda aka ragargaza a ruhu.
19 Adali zai iya kasance da wahala da yawa,
amma Ubangiji yakan cece shi daga dukansu;
-
22 Ku kawo damuwoyinku ga Ubangiji
zai kuwa riƙe ku;
ba zai taɓa barin
mai adalci yă fāɗi ba.
-
7 Don kada in cika da girman kai saboda waɗannan mafifitan manyan wahayoyi, sai aka sa mini wata ƙaya a jikina wadda ta zama ɗan saƙon Shaiɗan, don ta wahalshe ni. 8 Sau uku na roƙi Ubangiji yă raba ni da wannan abu. 9 Amma ya ce mini, “Alherina ya ishe ka, domin a cikin rashin ƙarfi ne ake ganin cikar ikona.” Saboda haka, zan ƙara yin taƙama da farin ciki game da rashin ƙarfina, domin ikon Yesu Kiristi yă zauna tare da ni. 10 Shi ya sa nake murna cikin rashin ƙarfi, da zagi, da shan wahaloli, da tsanantawa, da matsaloli, saboda Kiristi. Don a sa’ad da nake marar ƙarfi a nan ne nake da ƙarfi.
-
10 Saboda wannan kuwa muke wahala da kuma fama, domin mun sa begenmu ga Allah mai rai, wanda yake Mai Ceton dukan mutane, musamman na waɗanda suka ba da gaskiya.
-
13 Saboda haka, ku shirya kanku don aiki; ku zama masu kamunkai; ku kafa begenku duka a kan alherin da za a ba ku sa’ad da aka bayyana Yesu Kiristi.
-
9 Ba ni na umarce ka ba? Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro. Kada ka ji tsoro; kada ka karaya, gama Ubangiji Allahnka zai kasance tare da kai duk inda za ka je.”
-
6 Saboda haka bari duk mai tsoron Allah yă yi addu’a gare ka
yayinda kake samuwa;
tabbatacce sa’ad da manyan ruwaye suka taso,
ba za su kai wurinsa ba.
7 Kai ne wurin ɓuyata;
za ka tsare ni daga wahala
ka kewaye ni da waƙoƙin ceto. Sela
8 Zan umarce ka in kuma koyar da kai a hanyar da za ka bi;
Zan ba ka shawara in kuma lura da kai.
-
28 “Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji kuke kuma fama da kaya, zan kuwa ba ku hutu. 29 Ku ɗauki karkiyata a kanku, ku kuma yi koyi da ni, gama ni mai tawali’u ne marar girman kai, za ku kuwa sami hutu don rayukanku. 30 Gama karkiyata mai sauƙi ce, kayana kuma marasa nauyi ne.”
-
33 “Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin a cikina ku sami salama. A duniyan nan za ku sha wahala. Amma ku yi ƙarfin hali! Na yi nasara a kan duniya.”
-
1 In ina iya yin magana da harsunan mutane, da na mala’iku, amma ba ni da ƙauna, na zama kamar kuge mai yawan ƙara, ko kuma ƙararrawa mai amo kawai. 2 In ina da baiwar annabci, ina kuma iya fahimtar dukan asirai da dukan ilimi, in kuma ina da bangaskiyar da zan iya kawar da manyan duwatsu, amma ba ni da ƙauna, ni ba kome ba ne. 3 In na ba wa matalauta dukan abin da nake da shi, na kuma miƙa jikina a ƙone, amma ba ni da ƙauna, ban yi riban kome ba.
4 Ƙauna tana da haƙuri, ƙauna tana da kirki. Ba ta kishi, ba ta burga, ba ta da girman kai. 5 Ba ta rashin ladabi, ba ta sonkai, ba ta da saurin fushi, ba ta riƙe mutum a zuciya. 6 Ƙauna ba ta jin daɗin mugunta, sai dai ta ji daɗin gaskiya. 7 Tana kāriya kullum, tana amincewa kullum, tana bege kullum, tana jimrewa kullum.
8 Ƙauna ba ta ƙarewa. Amma in akwai annabci zai shuɗe, harsuna su ɓace, ilimi kuma zai ƙare. 9 Gama saninmu ba cikakke ba ne, annabcinmu kuma ba cikakke ba ne. 10 Sai dai sa’ad da cikakken ya zo, sai wanda ba cikakke yă shuɗe. 11 Sa’ad da nake yaro, na yi magana kamar yaro, na yi tunani kamar yaro, na yanke shawara kamar yaro. Da na isa mutum kuwa, sai na bar halin yarantakata. 12 Yanzu kam muna ganin abubuwa kamar a madubi sai dai ba sosai ba, amma a ranan nan za mu gani fuska da fuska. Yanzu kam sanina ba cikakke ba ne, amma a ranan nan zan kasance da cikakken sani, kamar dai yadda Allah ya san ni a yanzu.
13 Yanzu kam abubuwan nan uku sun tabbata, bangaskiya, bege, da kuma ƙauna. Sai dai mafi girma a cikinsu ita ce ƙauna.
Shows Read in context, Share and Copy.