73 Bible Verses About Praise
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
Ta Dawuda.
1 Yabi Ubangiji, ya raina;
dukan abin da yake cikin cikina, yabi sunansa mai tsarki.
2 Yabi Ubangiji, ya raina,
kada kuma ka manta dukan alheransa,
3 wanda yake gafarta dukan zunubai
yake kuma warkar da dukan cututtuka,
4 wanda ya fanshi ranka daga rami
ya naɗa maka rawani da ƙauna da kuma tausayi,
5 Wanda ya ƙosar da kai da abubuwa masu kyau
domin a sabunta ƙuruciyarka kamar na gaggafa.
-
11 Sai na duba na kuma ji muryar mala’iku masu yawa, yawansu kuwa ya kai dubu dubbai, da kuma dubu goma sau dubu goma. Suka kewaye kursiyin da halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan nan. 12 Da babbar murya suka rera,
“Macancanci ne Ɗan Ragon nan da aka kashe,
don yă sami iko da wadata da hikima da ƙarfi
da girma da ɗaukaka da kuma yabo!”
13 Sa’an nan na ji kowace halitta a sama da ƙasa da ƙarƙashin ƙasa da kuma bisan teku, da kome da yake cikinsu yana rerawa,
“Gare shi mai zama a kan kursiyin da kuma ga Ɗan Ragon
yabo da girma da ɗaukaka da iko,
sun tabbata har abada abadin!”
14 Sai halittu huɗun nan masu rai suka ce, “Amin”, dattawan kuma suka fāɗi suka yi sujada.
-
15 Saboda haka, ta wurin Yesu, bari mu ci gaba da miƙa hadaya ta yabo ga Allah, yabon leɓuna da yake shaidar sunansa. 16 Kada kuma ku manta yin aikin nagari da kuma taimakon waɗansu, gama da irin waɗannan hadayu ne Allah yake jin daɗi.
-
Ta Dawuda. Sa’ad da ya yi kamar ya haukace a gaban Abimelek, Wanda ya kore shi, ya kuwa tafi.
1 Zan gode wa Ubangiji kullayaumi;
yabonsa kullum za su kasance a leɓunana.
2 Raina zai yi fariya a cikin Ubangiji;
bari waɗanda suke wahala su ji su kuma yi farin ciki.
3 Ku ɗaukaka Ubangiji tare da ni;
bari mu ɗaukaka sunansa tare.
4 Na nemi Ubangiji, ya kuwa amsa mini;
ya cece ni daga dukan tsoro.
-
22 Sai taron suka fāɗa wa Bulus da Sila gaba ɗaya, alƙalan kuwa suka yi umarni a tuɓe su a kuma yi musu dūka. 23 Bayan an yi musu bulala sosai, sai aka jefa su cikin kurkuku, aka umarci mai gadin kurkukun yă tsare su da kyau. 24 Da karɓan irin umarnan nan, sai ya sa su can cikin ɗakin kurkuku na ciki-ciki, kuma ya ɗaura ƙafafunsu a turu.
25 Wajen tsakar dare Bulus da Sila suna addu’a suna rera waƙoƙi ga Allah, sauran ’yan kurkuku kuwa suna sauraronsu.
-
Zabura ce ta yabo. Ta Dawuda.
1 Zan ɗaukaka ka, ya Allahna, Sarki;
zan yabi sunanka har abada abadin.
2 Kowace rana zan yabe ka
in kuma ɗaukaka sunanka har abada abadin.
3 Ubangiji da girma yake ya kuma cancanci yabo
girmansa ya fi ƙarfin ganewar mutum.
4 Tsara guda za tă yi maganar ayyukanka ga wata tsara;
za su yi magana game da manyan ayyukanka.
-
3 Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ya kawo mana kowace albarka ta ruhaniya daga sama. 4 Gama ya zaɓe mu a cikin Kiristi tun dā can, kafin ma a halicci duniya don mu zama masu tsarki da kuma marasa aibi a gabansa. 5 A cikin ƙauna, ya ƙaddara mu zama ’ya’yansa na riƙo ta wurin Kiristi Yesu, bisa ga nufinsa na alheri. 6 Ya yi haka don mu yabi Allah saboda alherin da ya yi mana saboda mu na ƙaunataccen Ɗansa ne.
-
18 Kada ku bugu da ruwan inabi, wanda yake kai ga lalaci. A maimako haka, ku cika da Ruhu. 19 Ku yi zance da juna cikin zabura, da waƙoƙi, da kuma waƙoƙin ruhaniya. Ku rera, ku kuma yi kiɗe-kiɗe a zuciyarku ga Ubangiji. 20 Kullum ku dinga yin amfani da sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, kuna gode wa Allah Uba a kome.
-
16 Ku bar maganar Kiristi ta zauna a cikinku a yalwace yayinda kuke koya, kuna kuma yi wa juna gargaɗi da dukan hikima, da kuma yayinda kuke waƙoƙin zabura, waƙoƙi da waƙoƙin ruhaniya tare da godiya a zukatanku ga Allah. 17 Kuma ko mene ne kuke yi, ko cikin magana ko cikin ayyuka, ku yi shi duka a cikin sunan Ubangiji Yesu, kuna yin godiya ga Allah Uba ta wurinsa.
-
4 Ku shiga ƙofofinsa da godiya
filayen gidansa kuma da yabo;
ku gode masa ku kuma yabi sunansa.
5 Gama Ubangiji yana da kyau kuma ƙaunarsa madawwamiya ce har abada;
amincinsa na cin gaba a dukan zamanai.
-
8 Kowace a cikin halittu huɗu masu rai ɗin nan tana da fikafikai guda shida, tana kuma cike da idanu a ko’ina, har ma ƙarƙashin fikafikanta. Dare da rana ba sa fasa cewa,
“ ‘Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki
shi ne Ubangiji Allah Maɗaukaki,’
wanda yake a dā, wanda yake a yanzu, wanda kuma yake nan gaba.”
9 Duk lokacin da halittu masu ran nan suka rera ɗaukaka, girma da kuma godiya ga wannan wanda yake zaune a kan kursiyin da kuma wanda yake mai rai har abada abadin, 10 sai dattawa ashirin da huɗun nan su fāɗi a ƙasa a gaban wannan wanda yake zaune a kursiyin, su yi sujada wa wannan wanda yake da rai har abada abadin. Sukan ajiye rawaninsu a gaban kursiyin suna cewa,
11 “Ya Ubangijinmu da Allahnmu,
ka cancanci ɗaukaka da girma da iko,
domin ka halicci dukan abubuwa,
kuma ta wurin nufinka aka halicce su
suka kuma kasance.”
-
5 Lawiyawan nan, Yeshuwa, Kadmiyel, Bani, Hashabnehiya, Sherebiya, Hodiya, Shebaniya da Fetahahiya, suka ce, “Ku miƙe tsaye ku yabi Ubangiji Allahnku, wanda yake har abada abadin.”
“Albarka ta tabbata ga sunanka mai ɗaukaka, bari kuma a ɗaukaka shi bisa dukan albarka da yabo. 6 Kai kaɗai ne Ubangiji. Kai ka yi sammai, har ma da sama sammai, da dukan rundunar taurari, da duniya da kuma dukan abin da yake cikinta, da tekuna da dukan abubuwan da suke cikinsu. Ka ba da rai ga kome, kuma rundunonin sama suna maka sujada.
-
3 Domin ƙaunarka ta fi rai kyau,
leɓunana za su ɗaukaka ka.
4 Zan yabe ka muddin raina,
kuma a cikin sunanka zai ɗaga hannuwana.
5 Raina zai ƙoshi kamar da abinci mafi kyau;
da leɓunan rerawa bakina zai yabe ka.
6 A gadona na tuna da kai;
ina tunaninka dukan dare.
7 Domin kai ne mai taimakona,
ina rera a cikin inuwar fikafikanka.
8 Raina ya manne maka;
hannunka na dama yana riƙe da ni.
-
1 Ya Ubangiji, kai ne Allahna; zan ɗaukaka ka in kuma yabi sunanka,
gama cikin cikakken aminci ka yi abubuwa masu banmamaki,
abubuwan da aka shirya tun da.
-
1 Ku zo, bari mu rera don farin ciki ga Ubangiji;
bari mu yi sowa da ƙarfi ga Dutsen cetonmu.
2 Bari mu zo gabansa da godiya
mu rera gare shi da kiɗi da waƙa.
3 Gama Ubangiji Allah mai girma ne,
babban Sarki a bisa dukan alloli.
4 A hannunsa ne zurfafan duniya suke,
ƙwanƙolin dutse kuma nasa ne.
5 Teku nasa ne, gama shi ne ya yi shi,
da hannuwansa kuma ya yi busasshiyar ƙasa.
6 Ku zo, bari mu rusuna mu yi sujada,
bari mu durƙusa a gaban Ubangiji Mahaliccinmu;
7 gama shi ne Allahnmu
mu mutanen makiyayansa ne,
garke kuwa a ƙarƙashin kulawarsa.
Yau, in kuka ji muryarsa,
-
4 Dattawan nan ashirin da huɗu da halittu huɗun nan masu rai suka fāɗi suka yi wa Allah sujada, wannan da yake zaune a kursiyi. Suka tā da murya suka ce,
“Amin, Halleluya!”
5 Sa’an nan wata murya ta fito daga kursiyin, tana cewa,
“Ku yabi Allahnmu,
dukanku da kuke bayinsa,
ku da kuke tsoronsa,
babba da yaro!”
6 Sai na ji wani abu mai ƙara kamar ƙasaitaccen taron mutane, kamar rurin ruwaye masu gudu da kuma kamar bugun tsawa mai ƙarfi, suna tā da murya suna cewa,
“Halleluya!
Gama Ubangiji Allahnmu Maɗaukaki ne yake mulki.
-
9 Amma ku zaɓaɓɓu ne, ƙungiyar firistocin babban Sarki, al’umma mai tsarki, jama’a mallakar Allah, domin ku shaida yabon shi wanda ya kira ku daga cikin duhu zuwa haskensa mai banmamaki.
-
6 Yabo ya tabbata ga Ubangiji,
gama ya ji kukata na neman jinƙai.
7 Ubangiji shi ne ƙarfina da garkuwata;
zuciyata ta amince da shi, kuma na sami taimako.
Zuciyata ta yi tsalle don farin ciki
zan kuwa yi godiya gare shi cikin waƙa.
-
21 Sai Yesu ya ce, “Uwargida, ina tabbatar miki, lokaci yana zuwa da ba za ku yi wa Uba sujada ko a dutsen nan, ko kuwa a Urushalima ba. 22 Ku Samariyawa ba ku san abin da kuke yi wa sujada ba; mu kuwa mun san abin da muke yi wa sujada, gama ceto daga Yahudawa yake. 23 Duk da haka, lokaci yana zuwa har ma ya riga ya yi, da masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada a Ruhu da kuma gaskiya, gama irin waɗannan masu sujada ne Uba yake nema. 24 Allah ruhu ne, masu yi masa sujada kuwa dole su yi masa sujada a ruhu, da gaskiya kuma.”
25 Macen ta ce, “Na san cewa Almasihu” (da ake ce da shi Kiristi) “yana zuwa. Sa’ad da ya zo kuwa, zai bayyana mana kome.”
26 Sai Yesu ya ce, “Ni mai maganan nan da ke, Ni ne shi.”
27 Suna gama magana ke nan sai almajiransa suka iso, suka yi mamakin ganin yana magana da mace. Amma ba wanda ya ce, “Me kake so?” Ko “Me ya sa kake magana da ita?”
28 Sai macen ta bar tulunta na ruwa, ta koma cikin gari ta ce wa mutane,
-
10 Amma mala’ikan ya ce musu, “Kada ku ji tsoro. Na kawo muku labari mai daɗi na farin ciki mai yawa ne wanda zai zama domin dukan mutane. 11 Yau a birnin Dawuda an haifa muku Mai Ceto; shi ne Kiristi Ubangiji. 12 Wannan zai zama alama a gare ku. Za ku tarar da jariri a nannaɗe a zane kwance a kwami.”
13 Ba labari sai ga taron rundunar sama suka bayyana tare da mala’ikan, suna yabon Allah suna cewa,
14 “Ɗaukaka ga Allah a can cikin sama,
a duniya kuma salama ga mutane waɗanda tagomashinsa yake bisansu.”
-
28 Harshena zai yi zancen adalcinka
da kuma yabonka dukan yini.
-
30 Zan yabe sunan Allah cikin waƙa
in kuma ɗaukaka shi tare wurin yin godiya.
31 Wannan zai gamshi Ubangiji fiye da saniya,
fiye da bijimi da ƙahoninsa da kuma kofatansa.
32 Matalauta za su gani su kuma yi murna,
ku da kuke neman Allah, bari zukatanku su rayu!
-
4 Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya,
ku ɓarke da waƙa ta murna tare da kiɗi;
5 ku yi kiɗi ga Ubangiji da garaya,
da garaya da ƙarar rerawa,
6 tare da bushe-bushe da karar ƙahon rago,
ku yi sowa don farin ciki a gaban Ubangiji, Sarki.
-
33 Zan rera ga Ubangiji dukan raina;
zan rera yabo ga Allahna muddin ina raye.
34 Bari tunanina yă gamshe shi,
yayinda nake farin ciki a cikin Ubangiji.
-
6 Bari kowane abu mai numfashi yă yabi Ubangiji.
Yabi Ubangiji.
-
33 Sa’an nan itatuwan jeji za su rera,
za su rera don farin ciki a gaban Ubangiji,
gama ya zo don yă hukunta duniya.
34 Ku yi godiya ga Ubangiji, gama shi nagari ne;
ƙaunarsa madawwamiya ce.
35 Ku yi kuka, ku ce, “Cece mu, ya Allah Mai Cetonmu;
tara mu ka kuma cece mu daga al’ummai,
don mu yi godiya ga sunanka mai tsarki,
don mu ɗaukaka a cikin yabonka.”
36 Yabi Ubangiji, Allah na Isra’ila,
daga madawwami zuwa madawwami.
Sai dukan mutane suka ce, “Amin.” Suka kuma “Yabi Ubangiji.”
-
68 “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila,
domin ya zo ya kuma fanshe mutanensa.
69 Ya tā mana ƙahon ceto
a gidan bawansa Dawuda
70 (yadda ya yi magana tun tuni ta wurin annabawansa masu tsarki),
-
19 A wannan dare sai aka bayyana wa Daniyel mafarkin cikin wahayi. Daniyel kuwa ya ɗaukaka Allah na sama. 20 Ya ce,
“Yabo ya tabbata ga sunan Allah har abada abadin;
hikima da iko nasa ne.
21 Yana sāke lokuta,
yana tuɓe sarakuna yana kuma naɗa waɗansu.
Yana ba da hikima ga masu hikima
kuma ilimi ga masu basira.
22 Yakan bayyana zurfafa da ɓoyayyun abubuwa;
ya san abin da yake cikin dare,
haske kuwa yana zaune tare da shi.
23 Na gode maka ina yabonka, Allah na kakannina.
Kai ka san hikima da iko,
ka sanar da ni abin da muka tambaye ka, ka kuma sanar da mu mafarkin sarki.”
-
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ga muryar “Mutuwar Ɗa.” Zabura ta Dawuda.
1 Zan yabe ka, ya Ubangiji, da dukan zuciyata;
zan faɗa dukan abubuwan banmamakinka.
-
13 Ka sami ɗaukaka, ya Ubangiji cikin ƙarfinka;
za mu rera mu kuma yabi ikonka.
-
1 Ku rera da farin ciki ga Ubangiji ku adalai;
daidai ne masu gaskiya su yabe shi.
2 Ku yabi Ubangiji da garaya;
ku yi kiɗi gare shi da molo mai tsirkiya goma.
3 Ku rera masa sabuwar waƙa;
ku yi kiɗi da gwaninta, ku kuma yi sowa don farin ciki.
-
7 Zuciyata tana nan daram, ya Allah,
zuciyata tana nan daram;
zan rera in kuma yi kaɗe-kaɗe.
8 Ka farka, raina!
Ku farka, garaya da molo!
Zan sa safe yă farka.
9 Zan yabe ka, ya Ubangiji, a cikin al’ummai;
zan rera game da kai a cikin mutane.
10 Gama ƙaunarka mai girma ce, tana kaiwa sammai;
amincinka na kaiwa sarari.
-
1 Yabi Ubangiji, ya raina.
Ya Ubangiji Allahna, kana da girma ƙwarai;
kana saye da daraja da ɗaukaka.
-
1 Yabi Ubangiji.
Yabi sunan Ubangiji;
yabe shi, ku bayin Ubangiji,
2 ku waɗanda kuke hidima a gidan Ubangiji,
cikin filayen gidan Allahnmu.
3 Yabi Ubangiji, gama Ubangiji nagari ne;
rera yabo ga sunansa, gama wannan yana da kyau.
4 Gama Ubangiji ya zaɓi Yaƙub ya zama nasa,
Isra’ila ya zama mallakarsa mai daraja.
-
1 Yabi Ubangiji.
Yabi Ubangiji, ya raina.
2 Zan yabi Ubangiji dukan kwanakina;
zan rera yabo ga Allahna muddin raina.
-
1 Yabi Ubangiji.
Yana da kyau a rera yabai ga Allahnmu,
abu mai daɗi ne daidai ne kuma a yabe shi!
-
10 Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji,
ku yi yabonsa daga iyakar duniya,
ku da kuka gangara zuwa teku, da kome da yake cikinsa,
ku tsibirai, da waɗanda suke zama a cikinsu.
11 Bari hamada da garuruwanta su tā da muryoyinsu;
bari wuraren zaman da Kedar ke zama su yi farin ciki.
Bari mutanen Sela su rera don farin ciki;
bari su yi sowa daga ƙwanƙolin duwatsu.
12 Bari su ɗaukaka Ubangiji
su kuma yi shelar yabonsa a tsibirai.
-
13 Akwai waninku da yake shan wahala? Ya kamata yă yi addu’a. Akwai wani mai murna? Sai yă rera waƙoƙin yabo.
-
11 Wane ne cikin alloli,
ya yi kamar ka, ya Ubangiji?
Wane ne kamar ka,
mai ɗaukaka cikin tsarki,
mai banrazana cikin ɗaukaka,
mai aikata al’ajabai?
-
3 Yabe shi da ƙarar kakaki,
yabe shi da garaya da molo,
4 yabe shi da ganga kuna taka rawa,
yabe shi da kayan kiɗi na tsirkiya kuna kuma busa,
5 yabe shi da kuge mai ƙara,
yabe shi da kuge masu ƙara sosai.
-
3 Suna kiran juna,
“Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki! Ubangiji Maɗaukaki ne;
duniya ta cika da ɗaukakarsa.”
-
4 “Na kira ga Ubangiji, wanda ya cancanci yabo,
na kuwa tsira daga abokan gābana.
-
Zabura ce. Wata waƙa. Don keɓewar haikali. Ta Dawuda.
1 Zan girmama ka Ya Ubangiji,
gama ka tsamo ni daga zurfafa
ba ka bar abokan gābana sun yi farin ciki a kaina ba.
2 Ya Ubangiji Allahna, na yi kira gare ka don taimako
ka kuwa warkar da ni.
3 Ya Ubangiji, ka dawo da ni daga kabari;
ka kiyaye ni daga gangarawa zuwa cikin rami.
4 Ku rera ga Ubangiji, ku tsarkakansa;
ku yabi sunansa mai tsarki.
-
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Tare da kayan kiɗi masu tsirkiya. Zabura. Waƙa.
1 Bari Allah yă yi mana alheri yă kuma albarkace mu
yă kuma sa fuskarsa ta haskaka a kanmu, Sela
2 don a san hanyoyinka a duniya,
cetonka kuma a cikin dukan al’ummai.
3 Bari mutane su yabe ka, ya Allah;
bari dukan mutane su yabe ka.
4 Bari al’ummai su yi murna su kuma rera don farin ciki,
gama kana mulkin mutanenka da adalci
kana kuma bi da al’umman duniya. Sela
-
14 Amma game da ni, kullayaumi zan kasance da sa zuciya;
zan yabe ka sau da sau.
15 Bakina zai ba da labarin adalcinka,
zai yi maganar cetonka dukan yini,
ko da yake ban san yawansa ba.
-
1 Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji;
ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka.
2 Ku rera ga Ubangiji, ku yabe sunansa;
ku yi shelar cetonsa kowace rana.
3 Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai,
manyan ayyukansa a cikin dukan mutane.
4 Gama da girma Ubangiji yake, ya kuma cancanci yabo;
tilas a ji tsoronsa fiye da dukan alloli.
-
1 Ku yi godiya ga Ubangiji, ku kira bisa sunansa;
ku sanar a cikin al’ummai abin da ya yi.
2 Ku rera gare shi, ku rera yabo gare shi;
ku faɗa dukan abubuwan mamakin da ya aikata.
3 Ku ɗaukaka a cikin sunansa mai tsarki;
bari zukatan waɗanda suke neman Ubangiji su yi farin ciki.
4 Ku sa rai ga Ubangiji da kuma ƙarfinsa;
ku nemi fuskarsa kullum.
5 Ku tuna da abubuwan mamakin da ya yi,
mu’ujizansa, da kuma hukunce-hukuncen da ya zartar,
-
Waƙa ce. Zabura ta Dawuda.
1 Zuciyata tsayayyiya ce, ya Allah;
zan rera in kuma yi kiɗi da dukan raina.
2 Ku farka, garaya da molo!
Zan farkar da rana.
3 Zan yabe ka, ya Ubangiji, a cikin al’ummai;
zan rera game da kai cikin mutane.
-
10 Ina jin daɗi ƙwarai a cikin Ubangiji;
raina yana farin ciki a cikin Allahna.
Gama ya suturce ni da rigunan ceto
ya yi mini ado da rigar adalci,
yadda ango yakan yi wa kansa ado kamar firist
kamar kuma yadda amarya takan sha ado da duwatsunta masu daraja.
11 Gama kamar yadda ƙasa takan sa tsire-tsire su tohu
lambu kuma ya sa iri ya yi girma,
haka Ubangiji Mai Iko Duka zai sa adalci da yabo
su tsiro a gaban dukan al’ummai.
-
11 sowa ta farin ciki da murna, muryoyin amarya da na ango, da muryoyin waɗanda suka kawo hadayun salama a gidan Ubangiji suna cewa,
“ ‘ “Ku yi godiya ga Ubangiji Maɗaukaki,
gama Ubangiji mai alheri ne;
ƙaunarsa za tă dawwama har abada.”
Gama zan mayar da wadatar ƙasar kamar yadda suke a dā,’ in ji Ubangiji.
-
37 Da ya yi kusa da wurin da hanyar ta gangara zuwa Dutsen Zaitun, sai dukan taron almajirai suka fara yabon Allah, da muryoyi masu ƙarfi, da murna, saboda dukan ayyukan banmamaki da suka gani. Suna cewa,
38 “Mai albarka ne sarki wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!”
“Salama ta kasance a sama, da ɗaukaka kuma a can cikin sama!”
-
9 Bayan wannan sai na duba, can a gabana kuwa ga wani taro mai girma, wanda ba mai iya ƙirgawa, daga kowace al’umma, kabila, mutane da kuma harshe, suna tsaye a gaban kursiyin da kuma gaban Ɗan Ragon nan. Suna saye da fararen tufafi suna kuma riƙe da rassan dabino a hannuwansu. 10 Suka tā da murya da ƙarfi suna cewa,
“Ceto na Allahnmu ne,
wanda yake zaune a bisan kursiyi,
da kuma na Ɗan Ragon.”
11 Dukan mala’iku suna tsaye kewaye da kursiyin da kuma kewaye da dattawan tare da halittu huɗun nan masu rai. Suka fāɗi da fuskokinsu ƙasa a gaban kursiyin suka kuma yi wa Allah sujada, 12 suna cewa,
“Amin!
Yabo da ɗaukaka,
da hikima da godiya da girma
da iko da ƙarfi
sun tabbata ga Allahnmu har abada abadin.
Amin!”
-
47 Ka cece mu, Ubangiji Allahnmu,
ka kuma tattara mu daga al’ummai,
don mu yi wa sunanka mai tsarki godiya
mu kuma ɗaukaka cikin yabonka.
48 Yabo ga Ubangiji, Allah na Isra’ila,
daga madawwami zuwa madawwami.
Bari dukan mutane su ce, “Amin!”
Yabo ga Ubangiji.
-
164 Sau bakwai a rana ina yabonka
saboda dokokinka masu adalci.
-
13 Bari su yabi sunan Ubangiji,
gama sunansa ne kaɗai mafi ɗaukaka;
darajarsa ta fi ƙarfin duniya da sammai.
14 Ya tayar wa mutanensa ƙaho,
yabon dukan tsarkakansa,
na Isra’ila, mutanen da suke kurkusa da zuciyarsa.
Yabi Ubangiji.
-
2 Yabe shi saboda ayyukansa masu iko;
yabe shi saboda mafificin girmansa.
-
10 Dawuda ya yabi Ubangiji a gaban dukan taron, yana cewa,
“Yabo gare ka, ya Ubangiji,
Allah na mahaifinmu Isra’ila,
har abada abadin.
11 Girma da iko
da ɗaukaka, da daraja da kuma nasara naka ne, ya Ubangiji,
gama kome a sama da ƙasa naka ne.
Mulki kuma naka ne, ya Ubangiji;
an kuma ɗaukaka ka a matsayin kai a bisa duka.
12 Wadata da girma daga gare ka suke;
kai ne mai mulkin dukan abubuwa.
A hannuwanka ne ƙarfi da iko suke
don ka ɗaukaka da kuma ba da ƙarfi ga duka.
13 Yanzu fa, Allahnmu, muna gode maka,
muna kuma yabon ɗaukakar sunanka.
-
6 Ku rera yabai ga Allah, ku rera yabai;
ku rera yabai ga Sarkinmu, ku rera yabai.
7 Gama Allah shi ne Sarkin dukan duniya;
ku rera zabura ta yabo gare shi.
-
8 Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa
da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane,
9 gama yana shayar da masu ƙishirwa
yana kuma ƙosar da mayunwata da abubuwa masu kyau.
-
46 Kowace rana suka ci gaba da taruwa a filin haikali. Suka gutsuttsura burodi a gidajensu suna cin abinci tare da farin ciki da zuciya ɗaya, 47 suna yabon Allah suna kuma samun tagomashin dukan mutane. Ubangiji kuwa ya ƙara yawansu kowace rana na waɗanda suke samun ceto.
-
15 To, me zan yi? Akwai lokutan da zan yi addu’a da ruhuna; akwai kuma lokutan da zan yi addu’a da hankalina. Wani lokaci ya kamata in yi waƙa da ruhuna, a wani lokacin kuma in yi waƙa da hankalina. 16 A cewa waɗansu baƙi suna cikin sujadarku, sa’ad da kuke yabon Allah da ruhunku, yaya waɗanda suke tare ku za su fahimta, har su ce, “Amin,” da yake ba su san abin da kuke faɗi ba? 17 Ko da yake kuna ba da godiya da kyau, amma wancan mutumin da yake tare da ku bai ginu ba.
-
1 Sa’an nan Musa da Isra’ilawa suka rera wannan waƙa ga Ubangiji suka ce,
“Zan rera waƙa ga Ubangiji
gama an ɗaukaka shi ƙwarai.
Doki da mahayinsa
ya jefa su cikin teku.
2 “Ubangiji ne ƙarfina da mafakata,
ya zama cetona.
Shi Allahna ne, zan yabe shi.
Allah na kakana, zan ɗaukaka shi.
-
10 Da masu ginin suka aza harsashin ginin haikalin Ubangiji, sai firistoci suka sa kayansu na firistoci suka riƙe ƙahonin busa, Lawiyawa (’ya’yan Asaf) kuwa suka riƙe kuge, suka yi shiri domin su rera yabo ga Ubangiji kamar yadda Dawuda Sarkin Isra’ila ya ba da umarni. 11 Suka rera waƙar yabo da godiya ga Ubangiji, suna cewa,
“Shi nagari ne;
ƙaunarsa kuwa ga Isra’ila har abada ce.”
Dukan jama’a kuwa suka yabi Ubangiji da murya mai ƙarfi, domin an aza harsashin ginin gidan Ubangiji.
-
32 Ku rera wa Allah, ya masarautan duniya,
ku rera yabo ga Ubangiji, Sela
33 gare shi wanda yake hawan daɗaɗɗen sararin sama,
wanda yake tsawa da babbar murya.
34 Ku yi shelar ikon Allah,
wanda ɗaukakarsa take a bisa Isra’ila,
wanda ikonsa yake a cikin sarari.
-
34 Bari sama da ƙasa su yabe shi,
tekuna da dukan abin da yake motsi a cikinsu,
-
21 Bakina zai yi magana cikin yabon Ubangiji.
Bari kowace halitta ta yabi sunansa mai tsarki
har abada abadin.
-
7 Rera wa Ubangiji waƙar godiya;
ku kada garaya ga Allahnmu.
8 Ya rufe sararin sama da gizagizai;
yana tanada wa duniya ruwan sama
yana kuma sa ciyawa tă yi girma a kan tuddai.
-
13 Ku rera ga Ubangiji!
Ku yabi Ubangiji!
Ya kuɓutar da ran mabukaci
daga hannuwan mugaye.
-
3 Yabo ya tabbata ga Allah, da Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba mai tausayi, da kuma Allah na dukan ta’aziyya, 4 wanda yakan yi mana ta’aziyya a cikin dukan wahalolinmu, domin mu kuma mu iya ta’azantar da waɗanda suke cikin kowace irin wahala, da ta’aziyyar da mu kanmu muka samu daga Allah.
-
2 Sai na ji ƙara daga sama kamar motsin ruwaye masu gudu, kamar kuma tsawa. Ƙarar da na ji ta yi kamar ta masu garaya da suke kiɗin garayarsu. 3 Suka kuwa rera sabuwar waƙa a gaban kursiyin da kuma a gaban halittu huɗun nan masu rai, da kuma a gaban dattawa. Ba wanda ya iya koyon waƙar sai mutanen nan 144,000 da aka fansa daga duniya.
-
46 Ubangiji mai rai ne! Yabo ya tabbata ga Dutsena!
Girma ya tabbata ga Allah Mai cetona!
47 Shi ne Allah mai sāka mini,
wanda yake sa al’ummai a ƙarƙashina,
48 wanda yakan cece ni daga abokan gābana.
Ana girmama ka bisa abokan gābana;
daga masu tā-da-na-zaune-tsaye ka kuɓutar da ni.
-
4 Rera wa Allah, rera yabo ga sunansa,
ku ɗaukaka wanda yake hawa a kan gizagizai;
sunansa Ubangiji ne, ku kuma yi farin ciki a gabansa.
5 Uba ga marayu, mai kāre gwauraye,
shi ne Allah a mazauninsa mai tsarki.
-
1 Yabi Ubangiji.
Ku yabe shi, ya ku bayin Ubangiji,
ku yabi sunan Ubangiji.
2 Bari a yabi sunan Ubangiji,
yanzu da har abada kuma.
Shows Read in context, Share and Copy.