68 Bible Verses About The Tongue

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About The Tongue
  1. 2 Dukanmu mukan yi tuntuɓe a hanyoyi dabam-dabam. In wani bai taɓa yin kuskure a cikin maganarsa ba, shi cikakke ne, yana kuma iya ƙame dukan jikinsa.

    3 Sa’ad da muka sa linzamai a bakunan dawakai don mu sa su yi mana biyayya, mukan iya bin da dabbar gaba ɗaya. 4 Ko kuwa misali, mu dubi jiragen ruwa, mana. Ko da yake suna da girma ƙwarai kuma iska mai ƙarfi ce take tura su, ana tuƙa su da ɗan ƙaramin sandan ƙarfe ne zuwa duk inda mai tuƙin jirgin yake so. 5 Haka ma harshe yake, ga shi ɗan ƙanƙanin gaɓar jiki ne, amma sai manyan fariya. Ku dubi yadda ɗan ƙaramin ƙyastu yake ƙuna wa babban jeji wuta mana. 6 Harshe ma wuta ne! A cikin duk gaɓoɓinmu, harshe shi ne tushen kowace irin mugunta, mai ɓata mutum gaba ɗaya, mai zuga zuciyar mutum ta tafasa, shi kuwa jahannama ce take zuga shi.

    7 Kowace irin dabba, tsuntsu, masu ja da ciki da kuma halittun da suke cikin teku an sarrafa su kuma mutum ne ya sarrafa, 8 amma ba mutumin da zai iya ya sarrafa harshe. Mugu ne marar hutu, cike da dafi mai kisa.

    9 Da harshe mukan yabi Ubangijinmu da kuma Ubanmu, da shi kuma muke la’antar mutane, waɗanda aka halitta a kamannin Allah. 10 Daga wannan baki guda yabo da la’ana suke fitowa. ’Yan’uwana, wannan bai kamata yă zama haka ba. 11 Ruwa mai kyau da kuma ruwan gishiri zai iya fito daga maɓulɓula ɗaya? 12 ’Yan’uwana, itacen ɓaure yana iya haifar ’ya’yan zaitun, ko kuma itacen inabi yă haifi ’ya’yan ɓaure? Haka ma, maɓulɓular ruwan gishiri ba zai iya ba da ruwa mai kyau ba.

    13 Wane ne mai hikima da fahimta a cikinku? Bari yă nuna ta ta wurin rayuwarsa mai kyau, ta wurin ayyukan da aka yi cikin tawali’un da suke fitowa daga hikima. 14 Amma in kuna cike da mugun kishi da kuma sonkai a cikin zukatanku, kada ku yi taƙama game da wannan, ko ku danne gaskiya. 15 Irin wannan “hikima” ba daga sama ta sauko ba, ta duniya ce, ta rashin ruhaniya, ta Iblis kuma. 16 Gama inda akwai kishi da sonkai, a can za a tarar da hargitsi da kowane irin mugun aiki.

    17 Amma hikimar da ta zo daga sama da fari tana da tsabta gaba ɗaya; sa’an nan mai ƙaunar salama ce, mai sanin ya kamata, mai biyayya, cike da jinƙai da aiki mai kyau, marar nuna bambanci, sahihiya kuma.

  2. 6 Bari maganarku kullum ta zama da ladabi da kuma daɗin ji, domin ku san amsar da ta dace ku ba wa kowa.

  3. 4 Harshen da ya kawo warkarwa shi ne itacen rai,

    amma harshe mai ƙarya kan ragargaza zuciya.

  4. 33 “Itace mai kyau, yakan ba da ’ya’ya masu kyau. Itace marar kyau kuma, yakan ba da ’ya’ya marasa kyau. Itace dai, da irin ’ya’yansa ne ake gane shi. 34 Ku macizai, ta yaya ku da kuke mugaye za ku iya magana kirki? Gama daga baki, mutum yakan faɗi abin da yake cikin zuciya. 35 Mutumin kirki yakan fito da abubuwa masu kyau daga ajiyar da aka a yi cikinsa, mugun mutum kuwa yakan fito da mugayen abubuwa daga cikin muguntar da aka yi ajiya a cikinsa. 36 Amma ina gaya muku cewa mutane za su ba da lissafi a ranar shari’a a kan kowace kalmar banza da suka faɗa. 37 Gama ta wurin kalmominka za a kuɓutar da kai, kuma ta wurin kalmominka za a hukunta ka.”

  5. 19 Sa’ad da magana ta yi yawa, ba a rasa zunubi a ciki,

    amma shi da ya ƙame harshensa mai hikima ne.

    20 Harshen adali azurfa ce zalla,

    amma zuciyar mugu ba ta da wani amfani.

    21 Leɓunan adalai kan amfane yawanci,

    amma wawa kan mutu saboda rashin azanci.

  6. 18 Maganganun rashin tunani sukan soki mutum kamar takobi,

    amma harshen mai hikima kan kawo warkarwa.

    19 Leɓunan gaskiya kan dawwama har abada,

    amma harshen ƙarya yakan dawwama na ɗan lokaci ne kawai.

  7. 26 In wani ya ɗauki kansa mai addini ne duk da haka bai ƙame harshensa ba, ruɗin kansa yake yi addininsa kuwa banza ne. 27 Addinin da Allah Ubanmu ya yarda da shi a matsayin mai tsabta da kuma marar aibi shi ne, a kula da marayu da gwauraye cikin damuwoyinsu, a kuma kiyaye kai daga lalacin da duniya take sa wa.

  8. 20 Daga abin da baki ya furta ne cikin mutum kan cika;

    girbi daga leɓunansa kuma yakan ƙoshi.

    21 Harshe yana da ikon rai da mutuwa,

    kuma waɗanda suke ƙaunarsa za su ci amfaninsa.

  9. 33 Bayan da ya jawo shi gefe, sai Yesu ya sa yatsotsinsa a kunnuwan mutumin, ya tofa miyau ya kuma taɓa harshen mutumin. 34 Ya ɗaga kai sama, ya ja numfashi mai zurfi, sa’an nan ya ce masa, “Effata!” (Wato, “Buɗe!”). 35 Bayan ya faɗa haka, sai kunnuwan mutumin suka buɗe, harshensa kuma ya kunce, sai ya fara magana sarai.

  10. 10 Gama,

    “Duk wanda yake so yă ji daɗin rayuwa,

    yă kuma ga kwanaki masu kyau

    dole yă ƙame harshensa daga mugunta

    leɓunansa kuma daga maganar yaudara.

    11 Dole yă juye daga mugunta, ya aikata nagarta;

    dole yă nemi salama yă kuma bi ta.

  11. 1 Amsa da tattausar harshe kan kwantar da fushi,

    amma magana da kakkausan harshe kan kuta fushi.

    2 Harshen mai hikima kan yi zance mai kyau a kan sani,

    amma bakin wawa kan fitar da wauta.

  12. 28 A cikin ikkilisiya, da farko dai Allah ya zaɓa waɗansu ya naɗa su su zama manzanni, na biyu annabawa, na uku malamai, sa’an nan masu yin ayyukan banmamaki, sai masu baiwar warkarwa, da masu taimakon waɗansu, da masu baiwar gudanarwa, sa’an nan kuma masu magana da harsuna iri-iri. 29 Shin, duka ne manzanni? Duka ne annabawa? Duka ne malamai? Duka ne suke da baiwar yin ayyukan banmamaki? 30 Duka ne suke da baiwar warkarwa? Duka ne suke magana da harsuna? Duka ne suke iya fassara? 31 Sai dai ku yi marmarin neman baye-baye mafi girma.

    Yanzu kuwa zan nuna muku mafificiyar hanya.

  13. 27 Mutum mai sani yakan yi la’akari da amfani da kalmomi,

    mutum mai basira kuma natsattse ne.

    28 Ko wawa in bai buɗe bakinsa ba, za a zaci shi mai hikima ne,

    da kuma mai basira inda ya ƙame bakinsa.

  14. 23 Duk wanda yake lura da bakinsa da kuma harshensa

    kan kiyaye kansa daga masifa.

  15. 29 Kada wata ƙazamar magana ta fita daga bakunanku, sai dai abin da yake da amfani don gina waɗansu bisa ga bukatunsu. Ta haka maganarku za tă zama da amfani ga masu jinta.

  16. 19 ’Yan’uwana ƙaunatattu, ku lura da wannan. Ya kamata kowa yă kasance mai saurin saurara, ba mai saurin magana ba, ba kuma mai saurin fushi ba, 20 gama fushin mutum ba ya kawo rayuwar adalcin da Allah yake so. 21 Saboda haka, ku rabu da ƙazamin hali da kuma kowace irin mugunta ku kuma yi na’am da maganar da aka shuka a cikinku da tawali’u, wadda za tă iya cetonku.

    22 Kada ku zama masu ji kawai, ku ruɗi kanku. A maimakon haka ku zama masu yin abin da ta ce.

  17. 3 Bari Ubangiji yă yanke dukan zaƙin bakinsu

    da kuma kowane harshe mai fariya,

    4 masu cewa,

    “Da harsunanmu za mu yi nasara;

    leɓunanmu za su kāre mu, wane ne maigidanmu?”

  18. 12 Duk waninku da yake ƙaunar rayuwa

    yana kuma so yă ga kwanaki masu kyau,

    13 ka kiyaye harshenka daga mugunta

    da kuma leɓunanku daga faɗar ƙarairayi.

  19. 3 Ka sa mai tsaro a bakina, ya Ubangiji;

    ka yi tsaron ƙofar leɓunana.

    4 Kada ka bar zuciyata ta juya ga yin abin da yake mugu,

    ta sa kai ga aikata mugayen ayyuka

    tare da mutane masu aikata mugunta;

    kada ka bari in ci abincinsu.

  20. 171 Bari leɓunana su cika da yabonka,

    gama ka koya mini ƙa’idodinka.

    172 Bari harshena yă rera game da maganarka,

    gama dukan umarnanka masu adalci ne.

  21. 16 Akwai abubuwa shida da Ubangiji ya ƙi,

    abubuwa bakwai da suke abin ƙyama gare shi,

    17 duban reni,

    harshe mai ƙarya,

    hannuwa masu zub da jinin marar laifi,

    18 zuciyar da take ƙulla mugayen dabaru,

    ƙafafun da suke sauri zuwa aikata mugunta,

    19 mai shaidar ƙarya wanda yake zuba ƙarairayi,

    da kuma mutumin da yake tā-da-na-zaune-tsaye a cikin ’yan’uwa.

  22. 13 Ta haka zan koyar wa masu laifi hanyoyinka,

    masu zunubi kuma za su komo gare ka.

    14 Ka cece ni daga laifin jini, ya Allah,

    Allahn da ya cece ni,

    harshena kuwa zai rera adalcinka.

    15 Ya Ubangiji, ka buɗe leɓunana,

    bakina kuwa zai furta yabonka.

  23. 24 Harshena zai ba da labarin ayyukanka masu adalci

    dukan yini,

    gama waɗanda suka so su cutar da ni

    sun sha kunya suka kuma rikice.

  24. 3 “Sun tanƙwasa harshensu

    kamar baka, don su harba ƙarya;

    ba da gaskiya ba ne

    suke nasara a cikin ƙasar.

    Sukan tashi daga wannan zunubi zuwa wancan;

    ba su san ni ba,”

    in ji Ubangiji.

  25. 8 Harshensu kibiya ce mai dafi;

    yana magana da ruɗu.

    Da bakinsa kowa yana maganar alheri da maƙwabcinsa,

    amma a zuciyarsa ya sa masa tarko.

  26. 10 Musa ya ce wa Ubangiji, “Ya Ubangiji, ni ban mai iya magana ba ne, ban taɓa iya ba, ko a yanzu ma, bayan ka yi magana da ni, gama ni mai nauyin baki ne, mai nauyin harshe kuma.”

    11 Ubangiji ya ce masa, “Wa ya ba mutum bakinsa? Wa yake maishe shi kurma ko bebe? Wa yake ba shi gani ko yă makanta shi? Ashe ba Ni Ubangiji ba ne? 12 Yanzu tafi, zan taimake ka ka yi magana, zan kuma koya maka abin da za ka faɗa.”

  27. 9 Babu ko kalma guda daga bakinsu da za a dogara da ita;

    marmarinsu kawai shi ne su hallakar da waɗansu.

    Maƙogwaronsu buɗaɗɗen kabari ne;

    da harshensu suna faɗin ƙarya.

  28. 7 Bakinsa ya cika da zage-zage da ƙarairayi da kuma barazana;

    wahala da mugunta suna a ƙarƙashin harshensa.

  29. 2 Harshenka kan shirya hallaka;

    yana nan kamar reza mai ci,

    kana ta ruɗu.

  30. 2 Ka cece ni, ya Ubangiji,

    daga leɓuna masu ƙarya

    da kuma daga harsuna masu yaudara.

    3 Me zai yi maka,

    me kuma ya fi,

    ya kai harshe mai yaudara?

  31. 12 Mutum da ba shi da azanci kan ki maƙwabci,

    amma mutum mai fahimi kan ƙame harshensa.

  32. 18 Kamar yadda mahaukaci yake harbin

    cukwimai ko kibiyoyi masu dafi

    19 haka yake da mutumin da ya ruɗe maƙwabci

    sa’an nan ya ce, “Wasa ne kawai nake yi!”

    20 In ba itace wuta takan mutu;

    haka kuma in ba mai gulma ba za a yi faɗa ba.

    21 Kamar yadda gawayi yake ga murhu, itace kuma ga wuta,

    haka mutum mai neman faɗa yake ga faɗa.

    22 Kalmomin mai gulma suna kama da burodi mai daɗi;

    sukan gangara can cikin cikin mutum.

    23 Kamar kaskon da aka dalaye da azurfar da ba a tace ba

    haka leɓuna masu mugun zuciya.

    24 Mai yin ƙiyayya yakan ɓoye kansa da maganar bakinsa,

    amma a cikin zuciyarsa yana cike da munafunci

    25 Ko da jawabinsa ya ɗauki hankali, kada ka gaskata shi,

    gama abubuwa ƙyama guda bakwai sun cika zuciyarsa.

  33. 62 Sai suka yi alamu wa mahaifinsa, don su san sunan da zai su a kira yaron. 63 Ya yi alama a kawo masa allo, a gaban kowa sai ya rubuta, “Sunansa Yohanna.” Dukan mutane kuwa suka yi mamaki. 64 Nan da nan bakinsa ya buɗe harshensa kuma ya saku, sai ya fara magana yana yabon Allah.

  34. 28 Harshena zai yi zancen adalcinka

    da kuma yabonka dukan yini.

  35. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don Yedutun. Zabura ta Dawuda.

    1 Na ce, “Zan lura da hanyoyina

    zan kuma kiyaye harshena daga zunubi;

    zan sa linzami a bakina

    muddin mugaye suna a gabana.”

  36. 1 Da ranar Fentekos ta yi, dukansu suna tare wuri ɗaya. 2 Ba zato ba tsammani sai aka ji motsi kamar ta babbar iska tana hurowa daga sama ta kuma cika dukan gidan da suke zaune. 3 Suka ga wani abin da ya yi kama da harsunan wuta, suka rarrabu suna kuma sassauka a kan kowannensu. 4 Dukansu kuwa suka cika da Ruhu Mai Tsarki suka kuma fara magana da waɗansu harsuna yadda Ruhu ya sa suka iya.

    5 To, a Urushalima akwai Yahudawa masu tsoron Allah, daga kowace ƙasa a duniya. 6 Da suka ji wannan motsi, taro ya haɗu wuri ɗaya a ruɗe, domin kowannensu ya ji suna magana da yarensa. 7 Cike da mamaki, suka yi tambaya suna cewa, “Ashe, duk waɗannan mutane masu magana ba Galiliyawa ba ne? 8 To, yaya kowannenmu yana ji suna yarensa? 9 Fartiyawa, Medes da Elamawa; mazaunan Mesofotamiya, Yahudiya da Kaffadokiya, Fontus da Asiya, 10 Firjiya da Famfiliya, Masar da sassa Libiya kusa da Sairin; baƙi daga Roma 11 (Yahudawa da kuma waɗanda suka tuba suka shiga Yahudanci); Kiretawa da Larabawa, mun ji su suna shelar abubuwan banmamaki na Allah da yarenmu!” 12 A ruɗe kuma cike da mamaki, suka tambayi junansu cewa, “Mene ne wannan yake nufi?”

  37. 13 “Maƙogwaronsu kamar buɗaɗɗun kaburbura ne,

    harsunansu suna yin ƙarya.”

    “Dafin mugun maciji yana a leɓunansu.”

    14 “Bakunansu sun cike da la’ana da ɗacin rai.”

  38. Zabura ta Dawuda.

    1 Ubangiji, wa zai zauna cikin wuri mai tsarkinka?

    Wa zai zauna a kan tudunka mai tsarki?

    2 Sai wanda ba shi da laifi

    kuma yana yin abin da yake daidai,

    wanda yake faɗin gaskiya daga zuciyarsa

    3 ba ya kuwa ɓata sunan wani da harshensa,

    wanda ba ya yi wa maƙwabcinsa mugunta

    ba ya kuwa baza jita-jita a kan ɗan’uwansa,

  39. 30 Bakin mutum mai adalci yakan yi magana da hikima,

    harshensa kuwa yakan yi maganar abin da yake daidai.

  40. 19 Kuna amfani da bakunanku don mugunta

    kuna kuma gyara harshenku don ruɗu.

  41. 23 Mutum yakan yi farin ciki a ba da amsar da take daidai,

    kuma ina misali a yi magana a lokacin da ya dace!

  42. 1 Ga mutum ne shirye-shiryen zuciya suke,

    amma daga Ubangiji ne amshin harshe kan zo.

  43. 23 Zuciyar mai hikima kan bi da bakinsa,

    kuma leɓunansa kan inganta umarni.

    24 Kalmomi masu daɗi suna kama da kakin zuma,

    mai zaƙi ga rai da kuma warkarwa ga ƙasusuwa.

  44. 4 Kana ƙaunar kowace kalmar cutarwa,

    Ya kai harshe mai ruɗu!

  45. 31 Bakin adalai kan fitar da hikima,

    amma za a dakatar da mugun harshe.

  46. 3 Duk mai lura da leɓunansa yakan lura da ransa,

    amma duk mai magana da haushi zai kai ga lalaci.

  47. 6 Dukiyar da aka samu ta wurin harshe mai yin ƙarya

    tarin tururi ne da kuma mugun tarko.

  48. 27 In mutum ya haƙa rami, shi zai fāɗi a ciki;

    in mutum ya mirgino dutse, dutsen zai mirgine a kansa.

    28 Harshe mai faɗin ƙarya yana ƙin waɗanda yake ɓata musu rai,

    daɗin baki kuma yakan aikata ɓarna.

  49. 20 Ka ga mutum mai yin magana da garaje?

    To, gara a sa zuciya ga wawa da a sa zuciya gare shi.

  50. 18 Amma abubuwan da suke fitowa ta baki suna fitowa ne daga zuciya, su ne kuma suke ƙazantar da mutum. 19 Gama daga zuciya ne mugayen tunani, kisankai, zina, fasikanci, sata, shaidar ƙarya, ɓatan suna, suka fitowa.

  51. 11 A rubuce yake cewa,

    “ ‘Muddin ina raye,’ in ji Ubangiji,

    ‘kowace gwiwa za tă durƙusa a gabana;

    kowane harshe kuma zai furta wa Allah.’ ”

  52. 16 “ ‘Kada ku yi ta yawo kuna yaɗa ƙarya a cikin mutanenku.

    “ ‘Kada ku yi wani abin da zai sa ran maƙwabcinku cikin hatsari. Ni ne Ubangiji.

    17 “ ‘Kada ka yi ƙiyayyar ɗan’uwanka a zuciya. Ka tsawata wa maƙwabcinka da gaske don kada ka sami rabo cikin laifinsa.

    18 “ ‘Kada ka nemi yin ramuwa, ko ka riƙe wani cikin mutanenka a zuciya, amma ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka. Ni ne Ubangiji.

  53. 2 Amma laifofinku sun raba

    ku da Allahnku;

    zunubanku sun ɓoye fuskarsa daga gare ku,

    saboda kada yă ji.

    3 Gama hannuwanku sun ƙazantu da jini,

    yatsotsinku kuma da alhaki.

    Leɓunanku suna faɗin ƙarairayi,

    harshenku kuma yana raɗar mugayen abubuwa.

  54. 4 Domin ƙishirwa

    harshen jarirai ya manne a rufin bakinsu;

    yaran suna roƙo a ba su burodi,

    amma ba wanda ya ba su.

  55. 12 Attajiranta masu fitina ne;

    mutanenta kuma maƙaryata ne

    harsunansu kuwa suna yaudara.

  56. 24 Sai ya yi masa kira ya ce, ‘Baba, Ibrahim, ka ji tausayina, ka aiki Lazarus ya sa ɗan yatsarsa a ruwa, ya ɗiga mini a harshe saboda in ji sanyi, domin ina shan azaba cikin wannan wuta.’

  57. 1 In ina iya yin magana da harsunan mutane, da na mala’iku, amma ba ni da ƙauna, na zama kamar kuge mai yawan ƙara, ko kuma ƙararrawa mai amo kawai. 2 In ina da baiwar annabci, ina kuma iya fahimtar dukan asirai da dukan ilimi, in kuma ina da bangaskiyar da zan iya kawar da manyan duwatsu, amma ba ni da ƙauna, ni ba kome ba ne. 3 In na ba wa matalauta dukan abin da nake da shi, na kuma miƙa jikina a ƙone, amma ba ni da ƙauna, ban yi riban kome ba.

  58. 14 Bari kalmomin bakina da tunanin zuciyata

    su zama abin gamsuwa a gabanka,

    Ya Ubangiji, Dutsena da Mai fansata.

  59. 2 gama mugaye da masu ruɗu

    sun buɗe bakunansu a kaina;

    sun yi magana a kaina da harsunan ƙarya.

  60. 4 Kafin in yi magana da harshena

    ka santa gaba ɗaya, ya Ubangiji.

  61. 11 Bakin adali maɓulɓulan rai ne,

    amma kalmar mugun takan ɓoye makircinsa.

  62. 25 Zuciya mai damuwa takan naƙasar da mutum,

    amma maganar alheri kan faranta masa rai.

  63. 28 Zuciyar mai adalci takan auna amsoshinta,

    amma bakin mugu yakan fitar da mugunta.

    29 Ubangiji yana nesa da mugaye

    amma yakan ji addu’ar adalai.

  64. 20 Mutum mai muguwar zuciya ba ya cin gaba;

    duk wanda yake da harshen ruɗu kan shiga wahala.

  65. 23 Da kaina na rantse,

    bakina ya furta cikin dukan mutunci

    kalmar da ba za a janye ba.

    A gabana kowace gwiwa za tă durƙusa;

    ta wurina kowane harshe zai rantse.

  66. 20 Yanzu za ka zama bebe, ba za ka ƙara iya magana ba sai ranar da wannan magana ta cika, saboda ba ka gaskata da kalmomina waɗanda za su zama gaskiya a daidai lokacinsu ba.”

    21 Ana cikin haka, mutane suna jiran Zakariya, suna kuma mamaki me ya sa ya daɗe haka a cikin haikali. 22 Da ya fito, bai iya yin musu magana ba. Sai suka gane, ya ga wahayi ne a haikali, domin ya dinga yin musu alamu, amma ya kāsa yin magana.

  67. 8 Ƙauna ba ta ƙarewa. Amma in akwai annabci zai shuɗe, harsuna su ɓace, ilimi kuma zai ƙare.

  68. 10 Mala’ika na biyar ya juye kwanonsa a bisan gadon sarautar dabbar, mulkinta kuwa ya zama duhu. Mutane suka yi ta cizon bakinsu saboda azaba 11 suka kuma la’anci Allah na sama saboda zafinsu, da kuma saboda gyambunansu, amma suka ƙi su tuba daga abin da suka riga suka yi.