50 Bible Verses About Health

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Health
  1. 22 Zuciya mai farin ciki magani ne mai kyau,

    amma bakin rai kan busar da ƙasusuwa.

    23 Mugun mutum yakan karɓa cin hanci a asirce

    don yă lalace yin adalci.

  2. 5 Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka

    kada kuma ka dangana ga ganewarka;

    6 cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi,

    zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.

    7 Kada ka zama mai hikima a ganinka;

    ka ji tsoron Ubangiji ka kuma guji mugunta.

    8 Wannan zai ba wa jikinka lafiya

    yă kuma adana ƙasusuwanka.

  3. 12 “Ina roƙonka ka gwada bayinka kwana goma. Kada ka ba mu kome sai kayan lambu mu ci da kuma baƙin ruwa mu sha. 13 Sa’an nan sai ka dubi fuskokinmu da na sauran samarin da suke ci daga abincin sarki; sa’an nan ka yi da bayinka bisa ga abin da ka gani.”

  4. 20 Ɗana, ka kula da abin da nake faɗa,

    ka saurara sosai ga kalmomina.

    21 Kada ka bari su rabu da kai,

    ka kiyaye su a cikin zuciyarka;

    22 gama rai ne ga waɗanda suke nemansu

    da kuma lafiya ga dukan jikin mutum.

    23 Fiye da kome duka, ka tsare zuciyarka,

    gama maɓulɓulan ruwan rijiyar rai ne.

    24 Ka kau da muguwar magana daga bakinka;

    ka yi nesa da magana marar kyau daga leɓunanka.

  5. 7 Ka kiyaye kanka daga tatsuniyoyi na rashin tsoron Allah da labaru banza na tsofaffin mata; a maimako, ka hori kanka ga zama mai tsoron Allah. 8 Gama horon jiki yana da amfani, amma tsoron Allah yana da amfani ga kowane abu, yana da albarka ga rai na yanzu da kuma rai mai zuwa.

  6. 26 Ya ce, “In kun kasa kunne ga muryar Ubangiji Allahnku kuka yi abin da yake daidai a idanunsa, in kun mai da hankali ga umarnansa, kuka kiyaye dukan farillansa, ba zan kawo muku wani ciwon da na kawo a kan Masarawa ba, gama ni ne Ubangiji da nake warkar da ku.”

  7. Ta Dawuda.

    1 Yabi Ubangiji, ya raina;

    dukan abin da yake cikin cikina, yabi sunansa mai tsarki.

    2 Yabi Ubangiji, ya raina,

    kada kuma ka manta dukan alheransa,

    3 wanda yake gafarta dukan zunubai

    yake kuma warkar da dukan cututtuka,

    4 wanda ya fanshi ranka daga rami

    ya naɗa maka rawani da ƙauna da kuma tausayi,

    5 Wanda ya ƙosar da kai da abubuwa masu kyau

    domin a sabunta ƙuruciyarka kamar na gaggafa.

    6 Ubangiji yana aikata adalci

    da kuma gaskiya ga duk waɗanda aka danne.

  8. 25 Ku bauta wa Ubangiji Allahnku, albarkansa kuwa za tă kasance a kan abincinku da ruwan shanku. Zan ɗauke cuta daga cikinku. 26 A ƙasarku, mace ba za tă yi ɓari ba, ba kuma za a sami marar haihuwa ba. Zan ba ku tsawon rai.

  9. 6 “ ‘Duk da haka, zan kawo lafiya da warkarwa gare ta; zan warkar da mutanena in kuma wadata su da salama da zama lafiya.

  10. 17 Amma zan mayar muku da lafiya

    in kuma warkar da mikinku,’ in ji Ubangiji,

    ‘domin ana ce da ku yasassu,

    Sihiyona wadda ba wanda ya kula da ita.’

  11. 8 Ka tuna da ranar Asabbaci domin ka kiyaye ta da tsarki. 9 Kwana shida za ka yi dukan aikinka, 10 amma rana ta bakwai Asabbaci ne ga Ubangiji, Allahnka. A ranar ba za ka yi wani aiki ba, ko kai, ko ɗanka, ko ’yarka, ko bawa, ko baiwa, ko dabbarka, ko baƙon da yake zama tare da kai. 11 Gama kwana shida Ubangiji ya halicci sama da ƙasa, da teku, da duk abin da yake cikinsu, amma ya huta a rana ta bakwai. Saboda haka Ubangiji ya albarkaci ranar Asabbaci, ya kuma mai da ita mai tsarki.

  12. 1 Saboda haka, ina roƙonku, ’yan’uwa, saboda yawan jinƙan Allah, ku miƙa jikunanku hadaya wadda take mai rai, mai tsarki abin karɓa kuma ga Allah, wannan ita ce hanyar hidimarku ta ruhaniya. 2 Kada ku ci gaba da yin abin da duniya take yi, sai dai ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so yake, abu mai kyau, mai daɗi da kuma cikakke.

  13. 23 Zuciyar mai hikima kan bi da bakinsa,

    kuma leɓunansa kan inganta umarni.

    24 Kalmomi masu daɗi suna kama da kakin zuma,

    mai zaƙi ga rai da kuma warkarwa ga ƙasusuwa.

  14. 29 Sa’an nan Allah ya ce, “Ga shi, na ba ku kowane tsiro mai ba da ’ya’ya masu kwaya da suke a fāɗin duniya, da dukan itatuwa masu ba da ’ya’ya, don su zama abinci a gare ku.

  15. 5 Amma na dogara a kan ƙaunarka marar ƙarewa;

    zuciyata tana farin ciki a cikin cetonka.

    6 Zan rera ga Ubangiji

    gama ya yi mini alheri.

  16. 2 Ya Ubangiji Allahna, na yi kira gare ka don taimako

    ka kuwa warkar da ni.

    3 Ya Ubangiji, ka dawo da ni daga kabari;

    ka kiyaye ni daga gangarawa zuwa cikin rami.

  17. 9 Sa’an nan za ku yi kira, Ubangiji kuma zai amsa;

    za ku yi kuka don neman taimako, zai kuwa ce ga ni nan.

    “In kuka kawar da karkiyar zalunci,

    kuka daina nuna wa juna yatsa da kuma faɗar mugayen maganganu,

    10 in kuma kuka ɗauki lokaci kuka ƙosar da mayunwata

    kuka kuma biya bukatun waɗanda suke shan tsanani,

    sa’an nan ne haskenku zai haskaka cikin duhu

    darenku kuma zai zama kamar tsakar rana.

    11 Ubangiji zai bishe ku kullum;

    zai biya muku bukatunku a ƙasa mai zafin rana

    ya kuma ƙarfafa ƙasusuwanku.

    Za ku zama kamar lambun da aka yi masa banruwa,

    kamar rafin da ruwansa ba ya ƙafewa.

  18. 34 Ina roƙonku yanzu ku ci abinci. Kuna bukatarsa don ku rayu. Ba ɗayanku da zai rasa ko gashin kansa guda ɗaya.”

  19. 16 Ashe, ba ku sani ba cewa ku kanku haikalin Allah ne, Ruhun Allah kuma yana zaune a cikinku? 17 Duk wanda ya ɓata haikalin Allah, Allah zai ɓata shi, don haikalin Allah mai tsarki ne, ku ne kuwa haikalin nan.

  20. 24 Ba ku sani ba cewa a gasar gudu, dukan masu gudu sukan yi gudu, amma guda ne kaɗai yakan sami lada? To, sai ku yi gudu yadda za ku sami lada. 25 Duk ’yan wasan gasa sukan hori kansu sosai. Sukan yi haka domin su sami rawanin da ba zai daɗe ba. Amma mu muna yi ne domin mu sami rawanin da zai dawwama. 26 To, ni fa ba gudu nake yi kamar mai gudu ba wurin zuwa ba. Dambena kuma ba naushin iska nake yi ba. 27 A’a, ina horon jikina in mai da shi bawana, saboda bayan na yi wa waɗansu wa’azi, ni kaina kada in kāsa cancantar samun lada.

  21. 1 Ruwan inabi mai yin ba’a ne, barasa kuma mai rikici ne;

    duk wanda suka sa ya kauce marar hikima ne.

  22. 14 Ka warkar da ni, ya Ubangiji, zan kuwa warke;

    ka cece ni zan kuwa cetu,

    gama kai ne nake yabo.

  23. 1 Dattijon nan,

    Zuwa ga ƙaunataccen abokina Gayus, wanda nake ƙauna ƙwarai da gaske.

    2 Abokina ƙaunatacce, ina addu’a ka sami zaman lafiya don kome yă yi maka daidai, kamar yadda ruhunka yake zaune lafiya.

  24. 3 Ya warkar da masu raunanar zuciya

    ya ɗaɗɗaura miyakunsu.

  25. 24 Shi kansa ya ɗauki zunubanmu a jikinsa a kan itace, domin mu mutu ga zunubai mu kuma rayu ga adalci; ta wurin raunukansa ne kuka sami warkarwa.

  26. 4 Zai share dukan hawaye daga idanunsu. Ba sauran mutuwa ko makoki ko kuka ko azaba, gama tsofaffin al’amura sun shuɗe.”

  27. 8 Amma Daniyel ya ƙudura a zuciyarsa ba zai ƙazantar da kansa da abinci da ruwan inabin sarki ba, sai ya tambayi sarkin fada don a ba shi izinin kada yă ƙazantar da kansa ta wannan hanya.

  28. 31 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ai, masu lafiya ba sa bukatar likita, sai dai marasa lafiya. 32 Ban zo don in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi zuwa ga tuba.”

  29. 12 In kuka mai da hankali ga waɗannan dokoki, kuka kuma yi hankali ga bin su, to, Ubangiji Allahnku zai kiyaye alkawarinsa na ƙauna gare ku, kamar yadda ya rantse wa kakanninku. 13 Zai ƙaunace ku, yă albarkace ku, yă kuma ƙara yawanku. Zai albarkaci ’ya’yanku, amfanin gonarku; hatsinku, sabon ruwan inabinku da kuma mai, ƙanana shanunku, da ’yan tumaki na tumakinku, a ƙasar da ya rantse wa kakanninku cewa zai ba ku. 14 Za a albarkace ku fiye da waɗansu mutane; babu wani cikin maza ko matanku da zai kasance babu haihuwa, ba kuwa wata dabbarku da za tă kasance babu haihuwa. 15 Ubangiji zai kiyaye ku daga kowace cuta. Ba zai wahalshe ku da mugayen cututtukan da kuka sani a Masar ba, amma zai aukar wa dukan maƙiyanku.

  30. 17 Waɗansu suka zama wawaye ta wurin hanyoyinsu na tayarwa

    suka kuwa sha wahala saboda laifofinsu.

    18 Ba su so su ga abinci ba

    suka kuwa kai bakin mutuwa.

    19 Sa’an nan suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu,

    ya kuwa cece su daga damuwarsu.

    20 Ya ba da umarninsa ya kuma warkar da su

    ya kuɓutar da su daga kabari.

    21 Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa

    da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane.

  31. 16 Ubangiji, ta waɗannan abubuwa ne mutane suke rayuwa;

    ruhuna kuma yana samun rai a cikinsu shi ma.

    Ka maido mini da lafiya

    ka kuma sa na rayu.

    17 Tabbatacce wannan kuwa saboda ribata ne

    cewa in sha irin wahalan nan.

    Cikin ƙaunarka ka kiyaye ni

    daga ramin hallaka;

    ka sa dukan zunubaina

    a bayanka.

  32. 31 amma waɗanda suka dogara ga Ubangiji

    za su sabunta ƙarfinsu.

    Za su yi firiya da fikafikai kamar gaggafa;

    za su kuma yi gudu ba kuwa za su gaji ba,

    za su yi tafiya ba kuwa za su kasala ba.

  33. 15 Mun sa zuciya ga salama

    amma ba lafiya,

    mun sa zuciya ga lokacin warkarwa

    amma sai ga razana.

  34. 28 Sa’an nan Yesu ya amsa ya ce, “Mace, kina da bangaskiya mai yawa! An biya miki bukatarki.” ’Yarta kuwa ta warke nan take.

    29 Yesu ya tashi daga nan ya bi ta gefen Tekun Galili. Sa’an nan ya haura gefen wani dutse ya zauna. 30 Taron mutane mai girma kuwa suka zo wurinsa, suna kawo masa guragu, makafi, shanyayyu, kurame da dai waɗansu da yawa, suka kuwa kwantar da su a gabansa; ya kuma warkar da su. 31 Mutanen kuwa suka yi mamaki sa’ad da suka ga kurame suna magana, shanyayyu suna samun lafiya, guragu suna takawa, makafi kuma suna ganin gari. Sai suka yabi Allah na Isra’ila.

  35. 3 Saboda hasalarka babu lafiya a jikina;

    ƙasusuwana ba lafiya saboda zunubina.

  36. 18 Maganganun rashin tunani sukan soki mutum kamar takobi,

    amma harshen mai hikima kan kawo warkarwa.

  37. 20 Kada ka haɗa kai da waɗanda suke shan ruwan inabi da yawa

    ko masu haɗama kansu da abinci,

    21 gama bugaggu da ruwan inabi da masu yawan ci sukan zama matalauta,

    gama jiri yakan yi musu sutura da tsummoki.

  38. 29 Yakan ba da ƙarfi ga waɗanda suka gaji

    yă kuma ƙara ƙarfi ga marasa ƙarfi.

  39. 22 Ba magani ne a Gileyad?

    Ba likita ne a can?

    To, me ya sa ba warkarwa

    wa raunin mutanena?

  40. 1 Da ya sauko daga dutsen, sai taron mutane mai yawan gaske suka bi shi. 2 Wani mutum mai kuturta ya zo ya durƙusa a gabansa ya ce, “Ubangiji, in kana so, kana iya tsabtacce ni.”

    3 Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin. Ya ce, “Ina so, ka tsabtacce!” Nan da nan aka warkar da shi daga kuturtarsa.

  41. 28 “Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji kuke kuma fama da kaya, zan kuwa ba ku hutu. 29 Ku ɗauki karkiyata a kanku, ku kuma yi koyi da ni, gama ni mai tawali’u ne marar girman kai, za ku kuwa sami hutu don rayukanku. 30 Gama karkiyata mai sauƙi ce, kayana kuma marasa nauyi ne.”

  42. 6 Ƙwallafa rai ga al’amuran halin mutuntaka ƙarshensa mutuwa ne, ƙwallafa rai ga al’amuran Ruhu kuwa rai ne da salama; 7 hankalin mai zunubi na gāba da Allah. Ba ya biyayya da dokar Allah, ba kuwa zai iya yin haka ba.

  43. 2 “Ubangiji ne ƙarfina da mafakata,

    ya zama cetona.

    Shi Allahna ne, zan yabe shi.

    Allah na kakana, zan ɗaukaka shi.

  44. 2 Ka yi mini jinƙai, Ubangiji, gama na suma;

    Ya Ubangiji, ka warkar da ni, gama ƙasusuwana suna zafin ciwo.

  45. 14 Ubangiji ne ƙarfina da waƙata;

    ya zama mai cetona.

  46. 17 Mugun ɗan saƙo kan shiga wahala,

    amma jakadan da mai aminci yakan kawo warkarwa.

  47. 8 Mahaifinsa kuwa yana kwanciya a gado yana fama da zazzaɓi da atuni. Bulus ya shiga ciki don yă gan shi, bayan ya yi masa addu’a, sai ya ɗibiya masa hannuwa ya warkar da shi. 9 Sa’ad da wannan ya faru, sauran marasa lafiya a tsibirin suka zo aka kuma warkar da su.

  48. 29 Gama ba wanda ya taɓa ƙin jikinsa, sai dai yă ciyar da shi, yă kuma kula da shi, kamar yadda Kiristi yake yi wa ikkilisiya,

  49. 19 Allahna kuma zai biya dukan bukatunku bisa ga ɗaukakar wadatarsa cikin Kiristi Yesu.

  50. 23 Ka daina shan ruwa kaɗai, yi amfani da ruwan inabi kaɗan saboda cikinka da kuma yawan rashin lafiyarka.