55 Bible Verses About Prosperity

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Prosperity
  1. 6 Ku tuna fa, duk wanda ya yi shuki kaɗan zai girbe kaɗan, kuma duk wanda ya yi shuki da yawa, zai girbe a yalwace. 7 Ya kamata kowa yă bayar bisa ga abin da ya yi shawara a zuciyarsa, ba tare da jin nauyi ko don dole ba, gama Allah yana son mai bayarwa da daɗin rai. 8 Allah kuwa yana da iko yă ba ku fiye da bukatarku, domin kullum ku wadata da kome ta kowace hanya, kuna ta bayarwa hannu sake, kowane irin kyakkyawan aiki. 9 Kamar yadda yake a rubuce cewa,

    “Ya ba gajiyayyu hannu sake,

    ayyukansa na alheri madawwama ne.”

    10 To, shi da yake ba mai shuka iri, yake kuma ba da abinci a ci, shi ne zai ba ku irin shukawa, yă riɓanya shi, yă kuma albarkaci ayyukanku na alheri da yawa. 11 Za a wadatar da ku ta kowace hanya, domin ku riƙa bayarwa hannu sake a kowane lokaci. Ta wurinmu kuma bayarwarku hannu sake za tă zama sanadin godiya ga Allah.

    12 Wannan hidimar da kuke yi, ba bukatun mutanen Allah kaɗai take biya ba, amma tana cike da hanyoyin nuna godiya masu yawa ga Allah.

  2. Zabura ta Dawuda.

    1 Ubangiji ne yake kiwona, ba zan rasa kome ba,

    2 Yakan sa in kwanta a makiyaya mai ɗanyar ciyawa,

    yakan bi da ni kusa da ruwaye marar hayaniya,

    3 yakan maido da raina.

    Yakan bi da ni a hanyoyin adalci

    saboda sunansa.

  3. 7 “Abu biyu ina roƙonka, ya Ubangiji;

    kada ka hana ni kafin in mutu.

    8 Ka kawar da ƙarya da kuma ƙarairayi nesa da ni;

    kada ka ba ni talauci ko arziki,

    amma ka ba ni abincina na yini kaɗai.

    9 In ba haka ba, zan wadace in ƙi ka

    har in ce, ‘Wane ne Ubangiji?’

    Ko kuwa in zama matalauci in yi sata

    ta haka in kunyata sunan Allahna.

  4. 11 Gama na san shirye-shiryen da na yi muku,” in ji Ubangiji, “shirye-shiryen cin gaba ba na cutarwa ba, shirye-shiryen ba ku sa zuciya da kuma na nan gaba. 12 Sa’an nan za ku kira gare ni ku zo ku kuma yi addu’a gare ni, zan kuwa ji ku. 13 Za ku neme ni ku kuwa same ni sa’ad da kuka neme ni da dukan zuciyarku. 14 Za ku same ni,” in ji Ubangiji, “zan kuma komo da ku daga bauta. Zan tattaro ku daga dukan al’ummai in sa ku inda na kore ku,” in ji Ubangiji, “zan kuma komo da ku zuwa wurin da na kwashe ku zuwa zaman bauta.”

  5. 6 Amma bin Allah da gamsuwa riba ce mai yawa. 7 Gama ba mu zo duniya da kome ba, ba kuwa za mu fita daga cikinta da kome ba. 8 In dai muna da abinci da sutura, ai, sai mu gamsu da su. 9 Mutanen da suke son yin arziki sukan fāɗi cikin jarraba, su fāɗa a tarko, suna mugayen sha’awace-sha’awace iri-iri na wauta da cutarwa, irin waɗanda suke dulmuyar da mutane, su kai ga lalacewa da hallaka. 10 Gama son kuɗi shi ne tushen kowane irin mugun abu. Waɗansu mutane, don tsananin son kuɗi, sun bauɗe daga bangaskiya suka kuma jawo wa kansu da baƙin ciki iri-iri.

    11 Amma kai, mutumin Allah, ka guji duk wannan, ka kuma nemi adalci, tsoron Allah, bangaskiya, ƙauna, jimrewa da kuma hankali.

  6. 17 Wataƙila ku ce wa kanku, “Ikona da ƙarfin hannuwana ne suka ba ni da wannan arziki.” 18 Amma ku tuna da Ubangiji Allahnku, gama shi ne wanda yake ba ku azanci na yin arziki, ta haka kuwa ya tabbatar da alkawarinsa, wanda ya rantse wa kakanninku, kamar yadda yake a yau.

    19 In kuka manta da Ubangiji Allahnku, kuka kuma bi waɗansu alloli, kuka yi musu sujada, kuka kuma rusuna musu, to, a yau ina gargaɗe ku cewa tabbatacce za a hallaka ku. 20 Kamar al’ummai da Ubangiji ya hallakar kafin ku, haka zai hallaka ku, domin ba ku yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnku ba.

  7. 2 Abokina ƙaunatacce, ina addu’a ka sami zaman lafiya don kome yă yi maka daidai, kamar yadda ruhunka yake zaune lafiya.

  8. 7 Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro, ka yi lura fa, ka yi biyayya da dokokin da bawana Musa ya ba ka; kada ka kauce ga bin dokokin ko hagu ko dama, domin ka yi nasara a duk, inda za ka je. 8 Kada ka bar Littafin Dokokin nan yă rabu da bakinka, sai dai ka yi ta tunani game da shi dare da rana, don ka lura, ka yi duk abin da aka rubuta a ciki, ta haka ne za ka yi nasara cikin duk abin da za ka yi. 9 Ba ni na umarce ka ba? Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro. Kada ka ji tsoro; kada ka karaya, gama Ubangiji Allahnka zai kasance tare da kai duk inda za ka je.”

  9. 8 “Mutum zai iya yi wa Allah fashi ne? Duk da haka kun yi mini fashi.

    “Amma sai kuka ce, ‘Yaya muka yi maka fashi?’

    “A wajen zakka da hadayu. 9 Kuna ƙarƙashin la’ana, dukan al’ummarku, domin kuna yin mini fashi. 10 Ku kawo dukan zakka cikin gidan ajiya, don a kasance da abinci a gidana. Ku gwada ni a wannan ku ga, ko ba zan buɗe taskokin sama in zubo muku albarka mai yawa, wadda har ba za ku rasa wurin sa ta ba, in ji Ubangiji Maɗaukaki. 11 Zan hana ƙwari su cinye hatsinku. Kuringar inabi a gonakinku kuma ba za su zubar da ’ya’yansu kafin su nuna ba,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. 12 “Sa’an nan dukan al’ummai za su ce da ku masu albarka, gama ƙasarku za tă yi daɗin zama,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.

  10. LITTAFI NA ƊAYA

    1 Mai farin ciki ne mutumin

    da ba ya aiki da shawarar mugaye

    ko yă yi abin da masu zunubi suke yi

    ko yă zauna tare da masu yin ba’a.

    2 Amma yana jin daɗin bin dokar Ubangiji,

    kuma yana ta nazarinta dare da rana.

    3 Yana kama da itacen da aka shuka kusa da maɓulɓulan ruwa,

    wanda yake ba da amfani a daidai lokaci

    wanda kuma ganyensa ba sa bushewa.

    Duk abin da yake yi, yakan yi nasara.

  11. 19 “Kada ku yi wa kanku ajiyar dukiya a duniya, inda asu da tsatsa suke ɓatawa, inda kuma ɓarayi sukan fasa, su yi sata. 20 Amma ku yi wa kanku ajiyar dukiya a sama, inda ba tsatsa da asu da za su ɓata su, inda kuma ba ɓarayin da za su fasa, su yi sata. 21 Gama inda dukiyarka take, a nan ne fa zuciyarka za tă kasance.

    22 “Ido shi ne fitilar jiki. In idanunka suna da kyau, dukan jikinka zai cika da haske. 23 Amma in idanunka suna da lahani, dukan jikinka ma zai cika da duhu. To, in hasken da yake a cikinka duhu ne, duhun ya wuce misali ke nan!

    24 “Ba mai iya bauta wa iyayengiji biyu. Ko dai yă ƙi ɗaya, yă ƙaunaci ɗaya, ko kuwa yă yi aminci ga ɗaya, sa’an nan yă rena ɗayan. Ba dama ku bauta wa Allah, ku kuma bauta wa kuɗi gaba ɗaya.”

  12. 9 Gama kun san alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi cewa ko da yake shi mawadaci ne, duk da haka, ya zama matalauci saboda ku, domin ta wurin talaucinsa, ku zama mawadata.

  13. 9 Ka girmama Ubangiji da dukan dukiyarka,

    ta wurin miƙa masa nunan fari na dukan amfanin gonarka;

    10 ta haka rumbunanka za su cika har su zuba,

    randunanka kuma su cika har baki da sabon ruwan inabi.

  14. 22 Albarkar Ubangiji kan kawo wadata,

    ba ya kuma ƙara wahala a kai.

  15. 31 Don haka, kada ku damu, kuna cewa, ‘Me za mu ci?’ Ko, ‘Me za mu sha?’ Ko kuma, ‘Me za mu sa?’ 32 Gama marasa sanin Allah suna fama neman dukan waɗannan abubuwa, Ubanku na sama kuwa ya san kuna bukatarsu. 33 Da farko dai, ku nemi mulkin Allah da kuma adalcinsa, za a kuwa ba ku dukan waɗannan abubuwa.

  16. 10 Sa’an nan dukan mutane a duniya za su ga cewa ana kiranku da sunan Ubangiji, za su kuwa ji tsoronku. 11 Ubangiji zai azurta ku sosai, a ’ya’yan cikinku, a ’ya’yan dabbobinku da kuma a hatsin gonarku, a cikin ƙasar da ya rantse wa kakanninku zai ba ku.

    12 Ubangiji zai buɗe sammai, wurin ajiyarsa mai yalwa, don yă aika da ruwan sama a gonarku a lokacinsa, yă kuma albarkaci dukan aikin hannuwanku. Za ku ba wa al’ummai masu yawa rance, amma ba za ku karɓa bashi daga wurin wani ba. 13 Ubangiji zai sa ku zama kai, ba wutsiya ba. In kun mai da hankali ga umarnan Ubangiji Allahnku da nake ba ku a wannan rana, kuka kuma lura, kuka bi su, kullum za ku kasance a bisa, ba a ƙasa ba. 14 Kada ku kauce zuwa dama ko zuwa hagu daga umarnan da na ba ku a yau, har ku bi waɗansu alloli kuna yin musu sujada.

  17. 11 Gama Ubangiji Allah rana ne da kuma garkuwa;

    Ubangiji yakan yi alheri da kuma daraja;

    ba ya hana kowane abu mai kyau

    wa waɗanda suke aikata abin da yake daidai.

    12 Ya Ubangiji Maɗaukaki,

    mai albarka ne mutumin da ya dogara gare ka.

  18. 15 Ban da haka, kamar yadda ku Filibbiyawa kuka sani, a farkon kwanakin da kuka ji bishara, sa’ad da na tashi daga Makidoniya, babu wata ikkilisiyar da tă yi tarayya da ni a fannin bayarwa da karɓa, sai ku kaɗai; 16 gama ko sa’ad da nake a Tessalonika ma, kun aiko mini da taimako sau da sau sa’ad da nake cikin bukata. 17 Ba cewa ina neman kyauta ba ne, sai dai ina neman abin da za a ƙara a kan ribarku. 18 An biya ni duka, biyan da ya wuce misali. Bukatata ta biya, da yake na karɓi kyautarku da kuka aiko ta hannun Afaforiditus. Baiwa mai ƙanshi, hadaya abar karɓa, mai faranta wa Allah rai. 19 Allahna kuma zai biya dukan bukatunku bisa ga ɗaukakar wadatarsa cikin Kiristi Yesu.

  19. 1 To, aka kai Yusuf Masar, Fotifar wani mutumin Masar wanda yake ɗaya daga cikin hafsoshin Fir’auna, shugaban masu tsaro, ya saye shi daga mutanen Ishmayel waɗanda suka kai shi can.

    2 Ubangiji kuwa yana tare da Yusuf, Yusuf kuwa yi nasara, ya zauna a gidan mutumin Masar maigidansa. 3 Sa’ad da maigidansa ya ga cewa Ubangiji yana tare da Yusuf, kuma cewa Ubangiji ya ba shi nasara a kome da ya yi, 4 sai Yusuf ya sami tagomashi a idanunsa, ya kuma zama mai hidimarsa. Fotifar ya sa shi yă zama shugaba a gidansa, ya kuma danƙa masa kome da yake da shi. 5 Daga lokacin da ya sa shi shugaban gidansa da kuma a kan dukan abin da yake da shi, sai Ubangiji ya albarkaci gidan mutumin Masar saboda Yusuf. Albarkar Ubangiji tana a kan kome da Fotifar yake da shi a gida da kuma a jeji. 6 Saboda haka sai ya bar kome a ƙarƙashin kulawar Yusuf, bai dame kansa a wani abu ba sai dai abincin da yake ci.

    To, fa, Yusuf ƙaƙƙarfa ne, kyakkyawa kuma,

  20. 27 Bari waɗanda suke murna saboda nasarata

    su yi sowa don farin ciki da murna;

    bari kullum su riƙa cewa, “A ɗaukaka Ubangiji,

    wanda yake farin ciki da zaman lafiyar bawansa.”

  21. 3 Ka dogara ga Ubangiji ka kuma aikata alheri;

    yi zama cikin ƙasar ka kuma more makiyaya mai lafiya.

    4 Ka ji daɗinka a cikin Ubangiji

    zai kuwa biya bukatun zuciyarka.

    5 Ka sa kanka a hanyar Ubangiji;

    ka kuma dogara gare shi zai kuwa yi wannan.

  22. 24 Wani mutum kan bayar hannu sake, duk da haka yakan sami fiye;

    wani yakan riƙe abin da ba nasa ba, amma sai ya ƙarasa cikin talauci.

    25 Mutum mai kyauta zai azurta;

    shi da yakan taimake waɗansu, za a taimake shi.

  23. 4 Rago ya ƙosa ya sami wani abu ainun amma ba ya samun kome,

    amma sha’awar mai aiki tuƙuru yakan ƙoshi sosai.

  24. 20 Abin da Hezekiya ya yi ke nan ko’ina a Yahuda, yana yin abin da yake da kyau, daidai da kuma mai aminci a gaban Ubangiji Allahnsa. 21 Cikin kome da ya yi cikin hidimar haikalin Allah, cikin biyayya kuma ga doka da umarnai, ya nemi Allahnsa, ya kuma yi aiki gabagadi. Ta haka kuwa ya yi nasara.

  25. Waƙar haurawa.

    1 Masu albarka ne dukan masu tsoron Ubangiji,

    waɗanda suke tafiya a hanyoyinsa.

    2 Za ka ci amfanin aikinka;

    albarku da wadata za su zama naka.

  26. 38 Ku bayar, ku ma sai a ba ku mudu a cike, a danƙare, har yă yi tozo, yana zuba, za a juye muku a hannun riga. Mudun da kuka auna da shi, da shi za a auna muku.”

  27. 1 Da lokacin mutuwar Dawuda ya yi kusa, sai ya gargaɗe Solomon ɗansa, ya ce, 2 “Ina gab da bin hanyar da kowa a duniya zai bi. Saboda haka ka yi ƙarfin hali, ka nuna kanka namiji, 3 ka kiyaye abin da Ubangiji Allahnka yake bukata. Yi tafiya a hanyoyinsa, ka kiyaye ƙa’idodi, da umarnai, da dokoki, da kuma farillansa, kamar yadda suke a rubuce a Dokar Musa, don ka yi nasara a cikin kome da za ka yi, da kuma inda za ka tafi. 4 Ubangiji kuwa zai kiyaye alkawarinsa gare ni da ya ce, ‘In zuriyarka suka lura da yadda suke rayuwa, in kuma suka yi tafiya da aminci a gabana da dukan zuciyarsu, da kuma dukan ransu, ba za ka kāsa samun mutum a kujerar sarautar Isra’ila ba.’

  28. 8 Ku gwada ku gani cewa Ubangiji yana da kyau;

    mai albarka ne mutumin da yake neman mafaka a gare shi.

    9 Ku ji tsoron Ubangiji, ku tsarkakansa,

    gama masu tsoronsa ba sa rasa kome.

    10 Zakoki za su iya rasa ƙarfi su kuma ji yunwa,

    amma waɗanda suke neman Ubangiji ba sa rasa abu mai kyau.

    11 Ku zo, ’ya’yana, ku saurare ni;

    zan koya muku tsoron Ubangiji.

  29. 25 Mai haɗama yakan jawo tā-da-na-zaune-tsaye,

    amma duk wanda ya dogara ga Ubangiji zai yi nasara.

  30. 13 Sai wani mutum daga cikin taron ya ce masa, “Malam, ka ce wa ɗan’uwana ya raba gādon da ni.”

    14 Yesu ya amsa masa ya ce, “Kai, wa ya naɗa ni alƙali, ko mai sulhu a tsakaninku?” 15 Sai ya ce musu, “Ku lura fa! Ku tsare kanku daga dukan kowane irin kwaɗayi. Ran mutum ba ya danganta a kan yawan dukiyarsa ba.”

    16 Sai ya gaya musu wannan misali ya ce, “Gonar wani mai arziki ta ba da amfani sosai. 17 Ya yi tunani a ransa ya ce, ‘Ba ni da inda zan ajiye amfanin gonana. Me zan yi ke nan?’

    18 “Sai ya ce, ‘Ga abin da zan yi. Zan rushe rumbunana, in gina manya, in zuba dukan hatsina da kayana a ciki. 19 Ni kuma zan ce wa raina, “Kana da kaya da yawa masu kyau, da aka yi ajiyarsu domin shekaru da dama masu zuwa. Yi hutunka, ka ci, ka sha, ka yi annashuwa.” ’

    20 “Amma Allah ya ce masa, ‘Kai wawa! A wannan dare za a nemi ranka. Bayan haka, wa zai gāji abin da ka tara wa kanka?’

    21 “Haka zai zama ga duk wanda ya tara wa kansa dukiya, amma ba shi da arziki a gaban Allah.”

  31. 7 Ku ba wa kowa hakkinsa. In kuna da bashin haraji, sai ku biya; in kuɗin shiga ne, ku biya kuɗin shiga; in ladabi ne, ku yi ladabi; in kuma girmamawa ne, ku ba da girma.

    8 Kada hakkin kowa yă zauna a kanku, sai dai na ƙaunar juna, don mai ƙaunar maƙwabcinsa ya cika Doka ke nan. 9 Umarnan nan, “Kada ka yi zina.” “Kada ka yi kisankai.” “Kada ka yi sata.” “Kada kuma ka yi ƙyashi.” Da dai duk sauran umarnai an ƙunshe su ne a wannan kalma “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”

  32. 6 Duk haka, wanda aka koya wa maganar Kiristi, bari yă raba abubuwan nan na alheri tare da wanda ya koyar da shi.

    7 Kada a ruɗe ku. Ba a yi wa Allah ba’a. Mutum yakan girbe abin da ya shuka ne. 8 Wanda ya yi shuki don yă gamshi mutuntakarsa, daga wannan mutuntaka zai girbi hallaka. Wanda ya yi shuki domin yă gamshi Ruhu, daga Ruhu zai girbi rai madawwami. 9 Kada mu gaji da yin nagarta, gama a daidai lokaci za mu girbe amfani, in ba mu fid da zuciya ba. 10 Saboda haka, in da hali, bari mu aikata nagarta ga dukan mutane, musamman ga waɗanda suke na iyalin masu bi.

  33. 2 Ku ɗauki wannan da farin ciki mai tsabta, ’yan’uwana, duk sa’ad da gwaje-gwaje na kowane iri suka zo muku, 3 domin kun san cewa gwajin bangaskiyarku yakan haifi daurewa. 4 Dole daurewa ta kammala aikinta don ku zama balagaggu da kuma cikakku, ba ku kuma rasa kome ba. 5 In waninku ya rasa hikima, ya kamata yă roƙi Allah, mai bayarwa hannu sake ga kowa ba tare da gori ba, za a kuwa ba shi. 6 Amma sa’ad da ya roƙa, dole yă gaskata, ba tare da shakka ba, domin shi mai shakka, yana kama da raƙumar ruwan tekun da iska take kori tana kuma ɓuɓɓugowa. 7 Kada irin wannan mutum yă yi tsammani zai sami wani abu daga Ubangiji;

  34. 14 “Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Lawodiseya, ka rubuta,

    Waɗannan su ne kalmomina Amin, amintaccen mashaidi mai gaskiya, da kuma mai mulkin halittar Allah.

    15 Na san ayyukanka, ba ka da sanyi ba ka kuma da zafi. Na so da kai ɗaya ne daga ciki, ko sanyi, ko zafi! 16 Amma domin kana tsaka-tsaka ba zafi ba, ba kuma sanyi ba, ina dab da tofar da kai daga bakina. 17 Ka ce, ‘Ina da arziki; na sami dukiya ba na kuma bukatar kome.’ Amma ba ka gane ba cewa kai matsiyaci ne, abin tausayi, matalauci, makaho kana kuma tsirara. 18 Na shawarce ka ka sayi zinariyar da aka tace cikin wuta daga gare ni, don ka yi arziki; da fararen tufafi ka sa, don ka rufe kunyar tsirancinka; da kuma maganin ido ka sa a idanunka, don ka gani.

    19 Waɗanda nake ƙauna su nake tsawata wa, nake kuma horo. Saboda haka ka yi himma ka tuba.

  35. 17 Ina ƙaunar waɗanda suke ƙaunata,

    kuma waɗanda suke nemana sukan same ni.

    18 Tare da ni akwai wadata da girmamawa,

    dukiya da wadata masu dawwama.

    19 ’Ya’yan itacena sun fi zinariya zalla;

    amfanin gonar da nake bayar ya fi azurfa mafi kyau.

    20 Ina tafiya a hanyar adalci,

    a kan hanyoyin gaskiya,

    21 ina ba da wadata ga waɗanda suke ƙaunata

    ina sa wuraren ajiyarsu su cika.

  36. 10 Ɓarawo yakan zo don yă yi sata ne kawai da kisa da kuma ɓarna. Ni kuwa na zo ne don su sami rai, su kuma same shi a yalwace.

  37. 12 Ishaku ya shuka hatsi a wannan ƙasa, a shekaran nan ya yi girbi ninki ɗari, domin Ubangiji ya albarkace shi. 13 Mutumin ya arzuta, arzikinsa ya yi ta haɓaka har ya zama attajiri. 14 Ya kasance da garkunan tumaki da na shanu da bayi masu yawa, har Filistiyawa suka yi ƙyashinsa.

  38. 7 Ubangiji ne yakan aika da talauci da kuma dukiya;

    yakan ƙasƙantar yă kuma ɗaukaka.

    8 Yakan tā da matalauci daga ƙura,

    yă kuma ɗaga mai bukata daga tarin toka;

    yă zaunar da su tare da ’ya’yan sarki;

    yă kuma sa su gāji mulki na ɗaukaka.

    “Harsashin duniya na Ubangiji ne;

    a bisansu ne ya kafa duniya.

    9 Zai kiyaye ƙafafun masu tsarki,

    amma mugaye za su lalace cikin duhu.

    “Ba bisa ga ƙarfi mutum ba ne mutum ke nasara;

  39. 23 In Ubangiji ya ji daɗin hanyar da mutum yake bi,

    zai sa sawu su kahu;

    24 ko ya yi tuntuɓe, ba zai fāɗi ba,

    gama Ubangiji yakan riƙe shi da hannunsa.

    25 Dā ni yaro ne amma yanzu na tsufa,

    duk da haka ban taɓa ganin an yashe masu adalci ba

    ko a ce ’ya’yansu suna roƙon burodi.

    26 Kullum suna bayar hannu sake suna kuma ba da bashi ba da wahala ba,

    za a yi wa ’ya’yansu albarka.

  40. 2 Dukiyar da aka samu a hanyar da ba tă dace ba, ba ta da albarka,

    amma adalci kan ceci mutum daga mutuwa.

    3 Ubangiji ba ya barin mai adalci da yunwa

    amma yakan lalace burin mugu.

    4 Ragwanci kan sa mutum yă zama matalauci,

    amma aiki tuƙuru kan ba da dukiya.

    5 Shi da ya tattara hatsi da rani ɗa ne mai hikima,

    amma shi da yakan yi barci a lokacin girbi ɗa ne wanda ya zama abin kunya.

    6 Albarka kan zauna a kan mai adalci kamar rawani,

    amma rikici kan sha bakin mugu.

  41. 3 “ ‘In kuka kiyaye farillaina, kuka yi biyayya da umarnaina, 4 zan aika da ruwan sama a lokacinsa, ƙasa kuma za tă ba da hatsi, itatuwa kuma za su haihu ’ya’yansu. 5 Masussukanku za su ci gaba har lokacin girbin inabi, girbin inabi kuma zai ci gaba har lokacin shuki, za ku kuma ci duk abincin da kuke so cikin salama a ƙasarku.

  42. 1 In kun yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku, kuka kuma lura, kuka bi dukan umarnan da na ba ku a yau, Ubangiji Allahnku zai sa ku bisa dukan al’ummai a duniya. 2 Dukan waɗannan albarku za su sauko muku, su zama naku, in kuka yi biyayya ga Ubangiji Allahnku.

  43. 15 Yeshurun ya yi ƙiba, ya yi kauri;

    cike da abinci, ya zama da nauyi, ya kuma zama sumul.

    Ya yashe Allahn da ya yi shi,

    ya ƙi Dutse Cetonsa.

  44. 11 Amma masu tawali’u za su gāji ƙasar

    su kuma zauna da cikakkiyar salama.

  45. 1 An fi son suna mai kyau fiye da wadata mai yawa;

    tagomashi kuma ya fi azurfa ko zinariya.

    2 Mawadaci da matalauci suna da abu guda.

    Ubangiji ne Mahaliccinsu duka.

  46. 11 Hikima, kamar gādo, abu mai kyau ne

    tana kuma da amfani ga waɗanda suka ga rana.

    12 Hikima mafaka ce

    takan kāre mutum kamar yadda kuɗi suke yi.

    Kiyayewar da hikima takan yi wa mai ita

    ita ce amfanin ilimi.

    13 Ku lura da abin da Allah ya yi.

    Wa zai iya miƙe

    abin da ya tanƙware?

    14 Sa’ad da al’amura suke tafiya daidai, ka yi farin ciki,

    amma sa’ad da suka lalace, ka tuna,

    Allah ne ya yi wancan

    shi ne kuma ya yi wannan.

    Saboda haka, mutum ba zai san

    wani abu game da nan gabansa ba.

  47. 5 Ga abin da Ubangiji yana cewa,

    “La’ananne ne mutumin da yake dogara ga mutum,

    wanda ya dogara ga jiki don ƙarfi

    wanda kuma zuciyarsa ta juya wa Ubangiji baya.

    6 Zai zama kamar ɗan kurmi a ƙasar da take kango;

    ba za su ga arziki sa’ad da ya zo ba.

    Za su zauna a busassun wuraren hamada,

    a cikin ƙasar gishiri inda ba kowa.

    7 “Amma mai albarka ne mutumin da yake dogara ga Ubangiji,

    wanda ƙarfin halinsa yana daga Ubangiji.

    8 Za su zama kamar itacen da aka dasa kusa da ruwa

    wanda ya miƙa saiwoyinsa zuwa cikin rafi.

    Ba ya jin tsoro sa’ad da zafi ya zo;

    ganyayensa kullum kore suke.

    Ba shi da damuwa a shekarar fări

    ba ya taɓa fasa ba da ’ya’ya.”

  48. 1 Isra’ila kuringa ce mai yaɗuwa;

    ya fitar da ’ya’ya wa kansa.

    Yayinda ’ya’yan suka ƙaru,

    ya gina ƙarin bagadai;

    da ƙasarsa ta wadata,

    ya yi wa keɓaɓɓun duwatsu ado.

    2 Zuciyarsu masu ruɗu ne,

    yanzu kuwa dole su ɗauki laifinsu.

    Ubangiji zai rushe bagadansu

    yă kuma hallaka keɓaɓɓun duwatsunsu.

  49. 11 Ba na faɗin haka domin ina cikin bukata, gama na koya yadda zan gamsu a cikin kowane hali. 12 Na san mene ne zaman rashi, na kuma san mene ne zaman samu. Zan iya zama cikin kowane hali, ko cikin ƙoshi ko cikin yunwa, ko cikin yalwa ko kuma cikin fatara. 13 Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi.

  50. 1 Me yake jawo faɗace-faɗace da gardandami a tsakaninku? Ashe, ba sha’awace-sha’awacenku da suke yaƙi a zukatanku ba ne? 2 Kukan nemi abu ku rasa, sai ku yi kisa da ƙyashi. In kuka rasa abin da kuke nema sai ku shiga yin gardama da faɗa. Kukan rasa ne, domin ba ku roƙi Allah ba. 3 Sa’ad da kuka roƙa, ba kwa samu, don kun roƙa da mugun nufi, don ku kashe abin da kuka samu a kan sha’awace-sha’awacenku.

    4 Ku mazinata, ba ku san cewa abokantaka da duniya gāba ce da Allah ba? Duk wanda ya zaɓa yă zama abokin duniya ya zama abokin gāban Allah ke nan.

  51. 27 Saboda haka Allah ya halicci mutum cikin siffarsa.

    Cikin kamannin Allah, Allah ya halicci mutum.

    Miji da mace ya halicce su.

    28 Allah ya albarkace su, ya kuma ce musu, “Ku yi ta haihuwa ku ƙaru da yawa, ku mamaye duniya, ku mallake ta. Ku yi mulki a bisa kifin teku, da tsuntsayen sararin sama, da kuma bisa kowace halitta mai rai wadda take rarrafe a ƙasa.”

    29 Sa’an nan Allah ya ce, “Ga shi, na ba ku kowane tsiro mai ba da ’ya’ya masu kwaya da suke a fāɗin duniya, da dukan itatuwa masu ba da ’ya’ya, don su zama abinci a gare ku. 30 Na kuma ba da dukan dabbobin ƙasa, da dukan tsuntsayen sama, da dukan abin da yake rarrafe a ƙasa, da dai iyakar abin da yake numfashi; haka kuma na ba da ganyaye su zama abinci.” Haka kuwa ya kasance.

  52. 1 Ubangiji ya ce wa Abram, “Tashi ka bar ƙasarka, da mutanenka, da iyalin mahaifinka, ka tafi ƙasar da zan nuna maka.

    2 “Zan mai da kai al’umma mai girma,

    zan kuma albarkace ka;

    zan sa sunanka yă zama mai girma,

    ka kuma zama sanadin albarka.

    3 Zan albarkaci duk wanda ya albarkace ka,

    in kuma la’anci duk wanda ya la’anta ka,

    dukan mutanen duniya

    za su sami albarka ta wurinka.”

  53. 23 In ka komo ga Maɗaukaki, za ka warke.

    In ka kawar da mugunta daga cikin gidanka.

    24 Ka jefar da zinariyarka a ƙasa,

    ka jefar da zinariyar Ofir da ka fi so a cikin duwatsu,

    25 sa’an nan ne Maɗaukaki zai zama zinariyarka,

    zai zama azurfa mafi kyau a wurinka.

    26 Ba shakka a lokacin ne za ka sami farin ciki

    daga wurin Maɗaukaki,

    ku kuma ɗaga idanunku ga Allah

    27 Za ka yi addu’a zuwa gare shi, zai kuwa ji ka,

    kuma za ka cika alkawuranka.

  54. 23 Duk aiki tuƙuru yakan kawo riba,

    amma zama kana surutu kan kai ga talauci kawai.

  55. 32 Shi da bai hana Ɗansa ba, sai ma ya ba da shi saboda mu duka, ashe, ba zai kuma ba mu, tare da shi, dukan abubuwa cikin alherinsa ba?