80 Bible Verses About Working Hard
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
22 Bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya cikin kome; kada ku yi aikin ganin ido kamar masu neman yabon mutane, sai dai ku yi aiki tsakaninku da Allah, kamar masu tsoron Ubangiji. 23 Kome kuke yi, ku yi shi da dukan zuciyarku, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba ga mutum ba. 24 Kun san cewa zai ba ku gādo a matsayin ladanku. Ubangiji Kiristi ne fa kuke bauta wa. 25 Duk wanda ya yi laifi, za a sāka masa don laifinsa, babu sonkai.
-
6 Ku tafi wurin kyashi, ku ragwaye;
ku lura da hanyoyinsa ku zama masu hikima!
7 Ba shi da jagora
ba shugaba ko mai mulki,
8 duk da haka yakan yi tanade-tanadensa da rani
ya kuma tattara abincinsa a lokacin girbi.
9 Har yaushe za ku kwanta a can, ku ragwaye?
Yaushe za ku farka daga barcinku?
10 Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi,
ɗan naɗin hannuwa don a huta,
11 talauci kuwa zai zo kamar ’yan hari
rashi kuma kamar ɗan fashi.
-
6 A cikin sunan Ubangiji Yesu Kiristi, muna muku umarni, ’yan’uwa, da ku kiyaye kanku daga kowane ɗan’uwa mai zaman banza da ba ya rayuwa bisa ga koyarwar da kuka karɓa daga wurinmu. 7 Gama ku kanku kun san yadda ya kamata ku bi gurbinmu. Ba mu yi zaman banza sa’ad da muke tare da ku ba, 8 ba mu kuwa ci abincin kowa ba tare da ba mu biya ba. A maimakon haka, mun yi aiki dare da rana, muna fama muna wahala kuma don kada mu nawaita wa waninku. 9 Mun yi wannan, ba don ba mu da ’yancin karɓar irin taimakon nan ba ne, sai dai domin mu zama gurbin da za ku bi. 10 Ko ma a sa’ad da muke tare da ku, mun ba ku wannan umarni cewa, “In mutum ya ƙi yin aiki, kada a ba shi abinci.”
11 Mun ji cewa waɗansunku suna zaman banza. Ba sa aikin kome; sai shisshigi kurum. 12 Irin waɗannan mutane muna ba da umarni muna kuma gargaɗe su cikin Ubangiji Yesu Kiristi su natsu su kuma nemi abincin da suke ci.
-
5 Gama rayayyu sun san za su mutu,
amma matattu ba su san kome ba;
ba su da wata lada nan gaba
an manta da su ke nan gaba ɗaya.
6 Ƙaunarsu, ƙiyayyarsu,
da kuma kishinsu tuni sun ɓace;
ba za su taɓa zama sashen
wani abin da yake faruwa a duniya ba.
7 Yi tafiyarka, ka ci abincinka da farin ciki, ka sha ruwan inabinka da farin zuciya, gama abin da ka yi duka daidai ne a wurin Allah. 8 Kullum ka kasance cikin farin riguna, ka kuma shafe kanka da mai kullum, 9 Ka more rayuwa da matarka, wadda kake ƙauna, dukan kwanakin nan marasa amfani da Allah ya ba ka a duniya. Gama wannan ne rabonka a rayuwa da kuma na faman aikinka a duniya. 10 Duk abin da hannunka yake yi, ka yi shi da dukan ƙarfinka, gama a cikin kabari in da za ka, babu aiki ko shirye-shirye, ko sani, ko hikima.
11 Na kuma ga wani abu a duniya.
Ba kullum maguji ne yake nasara a tsere ba,
ba kullum jarumi ne yake yin nasara ba,
ba kullum mai hikima ne da abinci ba
ba kullum mai basira ne yake da wadata ba
ba kullum gwani ne yake samun tagomashi ba;
amma sa’a, da tsautsayi, sukan sami kowannensu.
12 Ban da haka ma, ba wanda ya san sa’ad da lokacin mutuwarsa zai yi.
Kamar yadda akan kama kifi a muguwar raga,
ko a kama tsuntsu a tarko,
haka mugun lokaci yakan auko wa mutane, ba tsammani.
-
23 Duk aiki tuƙuru yakan kawo riba,
amma zama kana surutu kan kai ga talauci kawai.
24 Dukiyar masu hikima ita ce rawaninsu,
amma wautar wawaye kan haifar da wauta ne kawai.
-
15 Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka gabatar da kanka a gaban Allah a matsayin wanda aka amince da shi, ma’aikaci wanda ba shi da dalilin jin kunya wanda kuma yake fassara kalmar gaskiya daidai.
-
4 Rago ya ƙosa ya sami wani abu ainun amma ba ya samun kome,
amma sha’awar mai aiki tuƙuru yakan ƙoshi sosai.
-
5 Ku bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya. Ku nuna musu halin bangirma, kuna kuma yin musu biyayya cikin dukan abu, da zuciya ɗaya kamar ga Kiristi kuke yi. 6 Ku yi aiki sosai, ba don kawai ku gamshe su sa’ad da suke kallonku ba. Da yake ku bayin Kiristi ne, ku aikata nufin Allah da dukan zuciyarku. 7 Ku yi aikinku da kyakkyawar niyya, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba mutane ba. 8 Gama kun san cewa Ubangiji zai ba da lada ga kowa gwargwadon kowane aiki nagarin da ya yi, ko shi bawa ne, ko ’yantacce.
9 Ku kuma masu bayi, dole ku bi da bayinku da kyau. Ku daina ba su tsoro. Ku tuna, ku da su, Maigida ɗaya kuke da shi a sama, kuma ba ya nuna bambanci.
10 A ƙarshe, bari ƙarfin ikon Ubangiji yă ba ku ƙarfi. 11 Ku yafa dukan kayan yaƙin da Allah yake bayarwa, don ku iya kāre kanku daga dabarun Shaiɗan.
-
15 Ubangiji Allah ya ɗauko mutumin ya sa shi cikin Lambun Eden domin yă nome shi, yă kuma lura da shi.
-
10 Gaskiyar kuwa ita ce, kuna ƙaunar dukan ’yan’uwa ko’ina a Makidoniya. Duk da haka muna ƙara gargaɗe ku, ’yan’uwa, ku yi haka sau da sau. 11 Ku mai da wannan burinku na yi natsattsiyar rayuwa, kuna mai da hankali ga sha’anin da yake gabanku, kuna kuma yin aiki da hannuwanku, kamar dai yadda muka gaya muku, 12 don rayuwanku ta kullum ta zama da mutunci ga waɗanda suke na waje don kuma kada ku dogara a kan kowa.
-
24 Hannuwan masu aiki tuƙuru za su yi mulki,
amma ragwanci kan ƙarasa a aikin bauta.
-
31 Saboda haka, duk abin da kuke yi, ko ci ko sha, ku yi shi duka saboda ɗaukakar Allah.
-
11 Duk wanda ya nome gonarsa zai sami abinci a yalwace,
amma shi da yake naushin iska marar azanci ne.
-
6 Manomi mai aiki sosai ya kamata yă zama na fari wajen samun rabon amfanin gona. 7 Ka yi tunani a kan abin da nake faɗi, gama Ubangiji zai ba ka ganewa cikin dukan wannan.
8 Ka tuna da Yesu Kiristi, wanda aka tā da shi daga matattu, zuriyar Dawuda, wanda shi ne bisharata, 9 wadda nake shan wahala har ga daurin sarƙa kamar mai laifi. Amma Maganar Allah ba a daure take ba. 10 Saboda haka nake jure kome saboda zaɓaɓɓu, domin su ma su sami ceton da yake cikin Kiristi Yesu, tare da madawwamiyar ɗaukaka.
11 Ga wata magana tabbatacciya,
“In muka mutu tare da shi,
za mu rayu tare da shi;
12 in muka jimre,
za mu yi mulki tare da shi.
In muka yi mūsunsa,
shi ma zai yi mūsunmu;
13 in ba mu da aminci,
shi dai mai aminci ne,
domin shi ba zai iya mūsun kansa ba.”
-
4 Ragwanci kan sa mutum yă zama matalauci,
amma aiki tuƙuru kan ba da dukiya.
5 Shi da ya tattara hatsi da rani ɗa ne mai hikima,
amma shi da yakan yi barci a lokacin girbi ɗa ne wanda ya zama abin kunya.
-
10 Na yi farin ciki sosai ga Ubangiji don yanzu kun sāke nuna kun kula da ni. Ko da yake dā ma kun kula da ni sai dai ba ku sami dama ku nuna mini ba. 11 Ba na faɗin haka domin ina cikin bukata, gama na koya yadda zan gamsu a cikin kowane hali. 12 Na san mene ne zaman rashi, na kuma san mene ne zaman samu. Zan iya zama cikin kowane hali, ko cikin ƙoshi ko cikin yunwa, ko cikin yalwa ko kuma cikin fatara. 13 Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi.
-
3 Ka miƙa wa Ubangiji dukan abin da kake yi,
shirye-shiryenka kuwa za su yi nasara.
-
30 Na wuce cikin gonar rago,
na wuce cikin gonar inabin mutumin da ba shi da azanci;
31 ƙayayyuwa sun yi girma ko’ina,
ciyayi sun rufe ƙasar,
katangar duwatsu duk ta rushe.
32 Na yi tunani a zuciyata
na kuwa koyi darasi daga abin da na gani.
33 Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi,
ɗan naɗin hannuwa don a huta,
34 sai talauci ya shigo maka kamar ’yan fashi
rashi kuma ya zo maka kamar mai hari.
-
17 Kuma ko mene ne kuke yi, ko cikin magana ko cikin ayyuka, ku yi shi duka a cikin sunan Ubangiji Yesu, kuna yin godiya ga Allah Uba ta wurinsa.
-
28 Duk wanda yake sata, sai yă daina sata, dole kuma yă yi aiki, yă yi wani abu mai amfani da hannuwansa, don yă sami abin da zai iya raba da masu bukata.
-
12 Saboda haka, ya abokaina ƙaunatattu, kamar yadda kullum kuke biyayya ba kawai sa’ad da ina nan ba, amma yanzu da ba na nan tare da ku, ku ci gaba da yin ayyukan cetonku da tsoro da kuma rawan jiki, 13 gama Allah ne yake aiki a cikinku, don ku nufa ku kuma aikata bisa ga nufinsa mai kyau.
14 Ku yi kome ba tare da gunaguni ko gardama ba, 15 don ku zama marasa abin zargi, sahihai ’ya’yan Allah, waɗanda ba su da laifi, a zamanin mutane karkatattu, kangararru, waɗanda kuke haskakawa a cikinsu kamar fitilu a duniya 16 kuna kuwa cin gaba da riƙe maganar rai domin in yi taƙama a ranar Kiristi cewa ban yi gudu ko fama a banza ba. 17 Amma ko da ana tsiyaye jinina kamar hadaya ta sha a kan hadaya da kuma hidimar da take fitowa daga bangaskiyarku, ina murna ina kuma farin ciki da ku duka.
-
Waƙar haurawa. Ta Solomon.
1 In ba Ubangiji ne ya gina gida ba,
masu gininta suna wahala a banza ne.
In ba Ubangiji ne yake tsaron birni ba,
masu tsaro suna yin tsaro a banza.
2 Banza ne ka farka da wuri
ka koma da latti,
kana fama don abincin da za ka ci,
gama yakan ba da barci ga waɗanda yake ƙauna.
-
17 Bari alherin shugabanmu Allah yă kasance a kanmu;
ka albarkaci mana aikin hannuwanmu,
I, ka albarkaci aikin hannuwanmu.
-
8 In wani bai kula da danginsa ba, musamman iyalinsa na kurkusa, ya mūsunta bangaskiya ke nan, ya kuma fi marar ba da gaskiya muni.
-
24 Yanzu, ina farin ciki saboda wuyar da nake sha dominku, don ta wurin wuyan nan zan cika abin da ya rage na wuyar da Kiristi ya sha saboda jikinsa, wato, ikkilisiya. 25 Na zama mai hidimar ikkilisiya bisa ga aikin nan da Allah ya ba ni amana saboda ku, domin in sanar da maganar Allah sosai. 26 Wannan magana da nake gaya muku asiri ne da yake a ɓoye tun zamanai masu yawa, wanda yanzu aka bayyana ga tsarkaka. 27 Su ne Allah ya so yă sanar da yadda irin yalwar ɗaukakar asirin nan take a cikin al’ummai, asirin nan kuwa shi ne Kiristi a cikinku, begen ɗaukakar da za a bayyana.
28 Saboda haka ko’ina muka tafi, muna shela, muna gargaɗi, muna kuma koyar da kowa da dukan hikima, don mu miƙa kowa cikakke a cikin Kiristi. 29 Don haka ne ina fama, ina kuma ƙoƙari da duk ƙarfin nan da Kiristi ya ba ni.
-
7 Cikin kowane abu ka zama musu misali mai kyau ta wurin aikata abin da yake nagari. A cikin koyarwarka ka nuna mutunci da ƙwazo 8 da kuma sahihanci cikin maganar da ba za a iya kushewa ba, domin masu gāba da kai su ji kunya, su kuma rasa wani mugun abin da za su faɗa game da mu.
-
8 Ka tuna da ranar Asabbaci domin ka kiyaye ta da tsarki. 9 Kwana shida za ka yi dukan aikinka, 10 amma rana ta bakwai Asabbaci ne ga Ubangiji, Allahnka. A ranar ba za ka yi wani aiki ba, ko kai, ko ɗanka, ko ’yarka, ko bawa, ko baiwa, ko dabbarka, ko baƙon da yake zama tare da kai. 11 Gama kwana shida Ubangiji ya halicci sama da ƙasa, da teku, da duk abin da yake cikinsu, amma ya huta a rana ta bakwai. Saboda haka Ubangiji ya albarkaci ranar Asabbaci, ya kuma mai da ita mai tsarki.
-
33 Ban yi ƙyashin azurfa ko zinariya ko tufafin kowa ba. 34 Ku kanku kun san cewa hannuwan nan nawa sun biya mini bukatuna da kuma na abokan aikina. 35 Cikin kowane abin da na yi, na nuna muku cewa da irin wannan aiki tuƙuru don mu taimaki marasa ƙarfi, muna tunawa da kalmomin da Ubangiji Yesu kansa ya ce, ‘Bayarwa ta fi karɓa albarka.’ ”
-
17 Ga Adamu kuwa ya ce, “Saboda ka saurari matarka, ka kuma ci daga itacen da na ce, ‘Kada ka ci,’
“Za a la’anta ƙasa saboda kai.
Da wahala za ka ci daga cikinta dukan kwanakin rayuwarka.
18 Za tă ba ka ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya
za ka kuwa ci ganyayen gona.
19 Da zuffan goshinka za ka ci abincinka har ka koma ga ƙasa,
da yake daga cikinta aka yi ka.
Gama kai turɓaya ne,
kuma ga turɓaya za ka koma.”
-
1 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, 2 “Duba, na zaɓi Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, na kabilar Yahuda, 3 na kuma cika shi da Ruhun Allah, fasaha, azanci, da kuma sani cikin kowace irin sana’a, 4 don yin zāne-zāne na aikin zinariya, azurfa da tagulla, 5 don yanka da shirya duwatsu, yin aikin katako, da kuma yin kowane irin aikin sana’ar hannu. 6 Ban da haka, na zaɓi Oholiyab ɗan Ahisamak, na kabilar Dan, don yă taimake shi. Na kuma ba da fasaha ga dukan masu aikin sana’ar hannu, don yin duk abin da na umarce ka.
-
2 Za ka ci amfanin aikinka;
albarku da wadata za su zama naka.
-
58 Saboda haka, ƙaunatattu ’yan’uwana, ku tsaya da daram. Kada wani abu yă jijjiga ku. Ku ba da kanku kullum ga aikin Ubangiji, domin kun san cewa famar da kuke yi saboda Ubangiji ba a banza take ba.
-
1 Ta haka aka gama yin sammai da duniya da dukan abubuwan da suke cikinsu.
2 Kafin kwana ta bakwai, Allah ya gama aikin da yake yi, saboda haka a kwana ta bakwai, ya huta daga dukan aikinsa. 3 Allah kuwa ya albarkaci kwana ta bakwai, ya kuma mai da ita mai tsarki, saboda a kanta ne ya huta daga dukan aikin halittar da ya yi.
-
9 Wanda yake ragwanci a aikinsa
ɗan’uwa ne ga wanda yakan lalatar da abubuwa.
10 Sunan Ubangiji hasumiya ce mai ƙarfi;
masu adalci kan gudu zuwa wurinta don su zauna lafiya.
-
13 Kada ka so barci in ba haka ba za ka talauce;
ka zauna a faɗake za ka kuwa kasance da sauran abinci.
-
12 Muna aiki da gaske da hannuwanmu. In aka la’anta mu, mukan sa albarka. In aka tsananta mana, mukan jimre; 13 in aka ɓata mana suna, mukan mayar da alheri. Har yă zuwa wannan lokaci, mu ne kamar jujin duniya, abin ƙyamar kowa.
-
9 Kada mu gaji da yin nagarta, gama a daidai lokaci za mu girbe amfani, in ba mu fid da zuciya ba.
-
4 Amma saboda yawan ƙaunar da yake mana, Allah, wanda yake mai yawan jinƙai, 5 ya ba mu rai sa’ad da ya tashe Kiristi daga matattu. Ta wurin alherin Allah ne aka cece ku. 6 Allah ya tashe mu tare da Kiristi, ya kuma ba mu wurin zama tare da shi a cikin mulkin samaniya. 7 Allah ya yi haka domin a tsararraki masu zuwa yă nuna yalwar alherinsa da ya wuce misali, an bayyana alheransa da ya yi mana ta wurin Kiristi Yesu. 8 Allah ya cece ku ta wurin alheri sa’ad da kuka ba da gaskiya. Wannan kuwa ba yinku ba ne, kyauta ce daga Allah. 9 Ba kuwa saboda aikin lada ba, don kada wani yă ɗaga kai. 10 Ai, mu aikinsa ne, an sāke halittarmu a cikin Kiristi Yesu musamman domin mu yi kyawawan ayyuka, waɗanda Allah ya tanadar mana tun da fari, mu yi.
-
13 Rago yakan ce, “Akwai zaki a kan hanya,
zaki mai faɗa yana yawo a tituna!”
14 Kamar yadda ƙofa kan juya a ƙyaurensa,
haka rago yake jujjuya a gadonsa.
15 Rago kan sa hannunsa a kwano
ba ya ma iya ɗaga shi ya kai bakinsa.
16 Rago yana gani yana da hikima
fiye da mutane bakwai da suke ba da amsa da dalilai a kan ra’ayinsu.
-
24 Ba abin da mutum zai yi da ya fi yă ci, yă sha, yă ji wa ransa daɗi daga aikinsa. Na lura cewa wannan ma, ya fito daga hannun Allah ne,
-
18 Sa’an nan na gane cewa abu mai kyau ne, daidai ne kuma mutum yă ci, yă sha, yă kuma ji daɗin aikin da ya yi a ’yan kwanakin da Allah ya ba shi, gama wannan shi aka ƙaddara wa mutum daga faman wahalarsa a duniya a cikin ’yan kwanakin da Allah ya ba shi a duniya, gama wannan shi ne rabonsa. 19 Ban da haka ma, sa’ad da Allah ya ba wa mutum dukiya da wadata, ya kuma ba shi zarafi yă ji daɗinsu, ya kuma amince da rabonsa, sai yă ji daɗin aikinsa, wannan kyauta ce ta Allah. 20 Da ƙyar yake tunani a kan kwanakin rayuwarsa, domin Allah ya yarje masa, yă zauna da farin ciki.
-
37 Gama ba abin da zai gagari Allah.”
-
15 Ragwanci kan jawo zurfin barci,
mutum mai sanyin jiki kuma yana tare da yunwa.
-
5 Shirye-shiryen mai aiki tuƙuru kan kai ga riba
in kuwa ka cika gaggawa zai kai ga talauci.
-
5 “Ni ne kuringar inabin; ku ne kuma rassan. In mutum ya kasance a cikina ni kuma a cikinsa, zai ba da ’ya’ya da yawa; in ba tare da ni ba, ba za ku iya yin kome ba.
-
9 Dole ƙauna tă zama ta gaskiya. Ku ƙi duk abin da yake mugu; ku manne wa abin da yake nagari. 10 Ku ba da kanku ga juna cikin ƙauna irin ta ’yan’uwa. Kowa yă yi ƙoƙari wajen girmama wani fiye da kansa. 11 Kada ku zama marasa himma, sai dai masu himma a ruhaniyarku, kuna bauta wa Ubangiji. 12 Ku yi farin ciki cikin bege, haƙuri cikin shan wuya, aminci cikin addu’a. 13 Ku taimaki mutanen Allah masu bukata. Ku zama masu karɓan baƙi.
-
2 Na san ayyukanka, faman aikinka da daurewarka. Na san cewa ba ka iya haƙuri da mugayen mutane, ka gwada waɗanda suke cewa su manzanni ne, alhali kuwa ba haka ba ne, ka kuwa tarar cewa su na ƙarya ne. 3 Kai kam ka daure ka kuma jimre da wahala saboda sunana, ba ka kuwa gaji ba.
-
19 Wata ne ke ƙididdigar lokuta,
rana kuma ta san sa’ad da za tă fāɗi.
20 Ka yi duhu, sai ya zama dare,
sai dukan namun jeji a kurmi suka fito a maƙe.
21 Zakoki sun yi ruri sa’ad da suke farauta
suna kuma neman abincinsu daga Allah.
22 Rana ta fito, sai suka koma shiru;
suka koma suka kwanta a kogwanninsu.
23 Mutum yakan tafi aikinsa,
zuwa wurin aikinsa har yamma.
-
26 Kamar yadda ruwan tsami yake ga haƙora hayaƙi kuma ga idanu,
haka malalaci yake ga wanda ya aike shi.
-
4 Rago ba ya noma a lokacin noma;
saboda haka a lokacin girbi ba ya bukata samun kome.
-
13 Rago kan ce, “Akwai zaki a waje!”
Ko kuma “Za a kashe ni a tituna!”
-
16 Haka ma, bari haskenku yă haskaka a gaban mutane, domin su ga ayyukanku masu kyau, su kuwa yabi Ubanku da yake cikin sama.
-
16 To, domin Yesu yana yin waɗannan abubuwa a ranar Asabbaci, sai Yahudawa suka tsananta masa. 17 Yesu ya ce musu, “Ubana yana cikin aikinsa kullum har yă zuwa wannan rana, haka ni ma, ina kan aiki.”
-
5 Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka
kada kuma ka dangana ga ganewarka;
6 cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi,
zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.
-
25 Marmarin rago zai zama mutuwarsa,
domin hannuwansa sun ƙi su yi aiki.
-
14 Kada ku zalunci ɗan ƙodago matalauci da mabukaci, ko da shi ɗan’uwanku ne mutumin Isra’ila, ko baƙon da yake zama a cikin garuruwanku.
-
19 An tare hanyar rago da ƙayayyuwa,
amma hanyar mai aikata gaskiya buɗaɗɗiyar hanya ce.
-
15 Takan farka tun da sauran duhu;
ta tanada wa iyalinta abinci
ta kuma shirya wa ’yan matan gidanta ayyukan da za su yi.
-
10 Amma bisa ga alherin Allah, na zama abin da nake, alherinsa zuwa gare ni kuwa bai zama a banza ba. A’a, na yi aiki fiye da dukansu, duk da haka, ba ni ba ne, sai dai alherin Allah da yake tare da ni ne.
-
9 Ba shakka kuna iya tunawa, ’yan’uwa, famarmu da kuma wahalarmu; mun yi aiki dare da rana don kada mu zama nauyi wa wani yayinda muke muku wa’azin bisharar Allah.
-
30 Sa’an nan ya ce wa Isra’ilawa, “Duba Ubangiji ya zaɓi Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, daga kabilar Yahuda, 31 ya kuma cika shi da Ruhun Allah, da fasaha, azanci da kuma sani cikin dukan sana’ar hannu, 32 don yă ƙirƙiro zāne-zāne na gwaninta waɗanda za yi da zinariya, da azurfa da kuma tagulla. 33 Haka kuma wajen sassaƙar duwatsu na jerawa, da sassaƙar itace, da kowane irin aiki na gwaninta. 34 Ya kuma ba Bezalel da Oholiyab ɗan Ahisamak, daga kabilar Dan, iyawa don koya wa waɗansu. 35 Ya cika su da fasaha don yin kowane irin aikin sana’a, zāne-zāne, ɗinke-ɗinke shuɗi, shunayya da jan zare, da lallausan lilin, da kuma masu yin saƙa, sun gwaninta ƙwarai cikin kowane irin aikin hannu da kuma zāne-zāne.
-
11 Kuɗin da aka same su a rashin gaskiya yakan ɓace da sauri,
amma duk wanda ya tara kuɗi kaɗan-kaɗan za su yi ta ƙaruwa.
-
24 Rago kan sa hannunsa a kwano
ba ya ma iya ɗaga shi ya kai bakinsa!
-
27 Tana lura da sha’anin gidanta
kuma ba ta cin abincin ƙyuya.
-
4 Amma na ce, “Na yi aiki a banza;
na kashe duk ƙarfina a banza da wofi.
Duk da haka abin da yake nawa yana a hannun Ubangiji,
ladana kuma tana a wurin Allahna.”
-
38 Yayinda Yesu da almajiransa suna cikin tafiya, sai ya kai wani ƙauye inda wata mace mai suna Marta ta marabce shi a gidanta. 39 Tana da ’yar’uwa mai suna Maryamu, wadda ta zauna a gaban Ubangiji tana jin maganarsa. 40 Marta kuwa, aikin hidima da ya kamata a yi, ya ɗauke mata hankali, sai ta zo wurin Yesu, ta ce, “Ubangiji, ba ka damu da yadda ’yar’uwata ta bar mini aiki ni kaɗai ba? Gaya mata ta taimake ni!”
41 Amma Ubangiji ya amsa ya ce, “Marta, Marta, hankalinki ya tashi, kuma kina damuwa a kan abubuwa da yawa. 42 Amma abu ɗaya tak ake bukata, Maryamu ta zaɓi abin da ya fi kyau, kuma ba za a raba ta da shi ba.”
-
47 “Bawan da ya san nufin maigidansa, kuma bai yi shiri ba, ko kuma bai yi abin da maigidansa yake so ba, zai sha mummunan duka. 48 Amma wanda bai sani ba, ya kuwa yi abin da ya isa horo, za a dūke shi kaɗan. Duk wanda aka ba shi mai yawa, mai yawan ne za a bida daga gare shi. Duk wanda kuma aka ba shi riƙon amana mai yawa, fiye da haka kuma za a bida daga gare shi.
-
10 “Duk wanda ana amincewa da shi cikin ƙaramin abu, ana kuma amincewa da shi cikin babba. Kuma duk marar gaskiya cikin ƙaramin abu, zai zama marar gaskiya cikin babba.
-
38 Na aike ku girbin abin da ba ku yi aikinsa ba. Waɗansu sun yi aikin nan mai wahala, ku kuwa kun sami ladan aikinsu.”
-
20 Ya kamata kowa yă kasance a matsayin da yake ciki sa’ad da Allah ya kira shi.
21 Kai bawa ne sa’ad da aka kira ka? Kada wannan yă dame ka, sai dai in kana iya samun ’yanci, sai ka yi amfani da wannan dama. 22 Gama wanda yake bawa sa’ad da Ubangiji ya kira shi, ’yantacce ne na Ubangiji; haka ma, wanda yake ’yantacce sa’ad da aka kira shi, bawa ne na Kiristi. 23 Da tsada fa aka saye ku, kada ku zama bayin mutane. 24 ’Yan’uwa, a duk matsayin da mutum yake sa’ad da aka kira shi, sai yă kasance haka a sabuwar dangantakarsa da Allah.
-
11 Saboda haka Kiristi kansa ya ba wa waɗansu baiwa su zama manzanni, waɗansu su zama annabawa, waɗansu su zama masu wa’azi, waɗansu kuma su zama fastoci, da kuma malamai. 12 Ya yi haka don yă shirya mutanensa saboda ayyukan hidima, don a gina jikin Kiristi. 13 Wannan zai ci gaba har sai mun zama ɗaya a cikin bangaskiya da kuma ta wurin fahimtarmu na Ɗan Allah. Sa’an nan za mu zama balagaggu, kamar yadda Kiristi yake, mu kuma zama gaba ɗaya cikakku kamar sa.
14 An yi wannan kuwa don kada mu koma zama kamar yara, muna ta canja zukatanmu game da abin da muka gaskata don kawai wani ya faɗa mana wani abu dabam, ko domin wani ya yi wayo ya ruɗe mu, ya sa ƙarya ta zama kamar gaskiya. 15 Ya kamata kullum ƙauna tă sa mu faɗa gaskiya. Ta haka za mu yi girma a kowace hanya, mu kuma zama kamar Kiristi, wanda yake kan 16 dukan jiki. Shi ne ya haɗe jiki duka, ya kuma sa dukan gaɓoɓin jiki suna aiki daidai, yayinda kowace gaɓa take aikinta cikin ƙauna.
-
1 Bulus, Sila da Timoti,
Zuwa ga ikkilisiyar Tessalonikawa ta Allah Uba da Ubangiji Yesu Kiristi.
Alheri da salama su kasance tare da ku.
2 Kullum muna gode wa Allah dominku duka, muna ambatonku cikin addu’o’inmu. 3 Muna tunawa da aikinku ba fasawa a gaban Allah da Ubanmu ta wurin bangaskiya, da famar da kuke yi domin ƙauna, da kuma begenku marar gushewa ga Ubangijinmu Yesu Kiristi.
-
14 Muna kuma gargaɗe ku, ’yan’uwa, ku gargaɗe waɗanda suke zaman banza, ku ƙarfafa masu raunanar zuciya, ku taimaki marasa ƙarfi, ku yi haƙuri da kowa.
-
9 Kada a lasafta gwauruwa cikin jerin gwauraye sai ta wuce shekara sittin, ta kuma yi zaman aminci ga mijinta, 10 aka kuma santa sosai saboda ayyuka masu kyau, kamar renon ’ya’ya, da karɓan baƙi, tana yi wa tsarkaka hidima, tana taimakon waɗanda suke cikin wahala tana kuma ba da kanta ga yin kowane aikin mai kyau.
11 Game da gwauraye masu ƙuruciya kuwa, kada ka sa su cikin wannan lissafi. Gama sa’ad da sha’awar jikinsu ta kāsa daurewa game da wa’adin da suka yi da Kiristi, sai su so yin aure. 12 Ta haka suna jawo wa kansu hukunci, saboda sun karya alkawarinsu na farko. 13 Ban da haka, sukan koyi zaman banza, suna zirga-zirga gida-gida. Ba kawai sun zama masu zaman banza ba, har ma sun zama masu gulma da masu shisshigi, suna faɗin abubuwan da bai kamata su faɗa ba. 14 Saboda haka ina ba wa gwauraye masu ƙuruciya shawara su yi aure, su sami ’ya’ya, su lura da gidajensu kada kuwa su ba abokin gāba zarafin ɓata suna. 15 Waɗansu dai sun riga sun bauɗe sun bi Shaiɗan.
16 In mace mai bi tana da gwauraye a iyalinta, ya kamata tă taimake su, kada tă bar wa ikkilisiya wannan nauyi, domin ikkilisiya ta sami zarafin taimakon gwaurayen da suke da bukata ta ainihi.
-
3 Ka jure wa shan wahala tare da mu kamar soja mai kyau na Kiristi Yesu.
-
21 In mutum ya tsabtacce kansa daga na farkon zai zama kayan aikin hidima mai daraja, mai amfani ga Maigida, kuma shiryayye domin yin kowane aiki mai kyau.
-
14 Dole mutanenmu su koyi ba da kansu ga aikata abin da yake nagari, domin su iya biyan bukatunsu na yau da kullum kada kuma su yi rayuwar marar amfani.
-
4 Dole daurewa ta kammala aikinta don ku zama balagaggu da kuma cikakku, ba ku kuma rasa kome ba.
-
12 Mai albarka ne mutumin da yake daurewa cikin gwaji, gama bayan ya yi nasara da gwajin, zai sami rawanin rai wanda Allah ya yi alkawari ga waɗanda suke ƙaunarsa.
-
13 Sai na ji murya daga sama ta ce, “Rubuta, Masu albarka ne matattun da suka mutu cikin Ubangiji daga yanzu zuwa gaba.”
“I, za su huta daga faman aikinsu, gama ayyukansu za su bi su,” in ji Ruhu.
Shows Read in context, Share and Copy.