15 Bible Verses About Creativity

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Creativity
  1. 30 Sa’an nan ya ce wa Isra’ilawa, “Duba Ubangiji ya zaɓi Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, daga kabilar Yahuda, 31 ya kuma cika shi da Ruhun Allah, da fasaha, azanci da kuma sani cikin dukan sana’ar hannu, 32 don yă ƙirƙiro zāne-zāne na gwaninta waɗanda za yi da zinariya, da azurfa da kuma tagulla. 33 Haka kuma wajen sassaƙar duwatsu na jerawa, da sassaƙar itace, da kowane irin aiki na gwaninta. 34 Ya kuma ba Bezalel da Oholiyab ɗan Ahisamak, daga kabilar Dan, iyawa don koya wa waɗansu. 35 Ya cika su da fasaha don yin kowane irin aikin sana’a, zāne-zāne, ɗinke-ɗinke shuɗi, shunayya da jan zare, da lallausan lilin, da kuma masu yin saƙa, sun gwaninta ƙwarai cikin kowane irin aikin hannu da kuma zāne-zāne.

  2. 26 Sa’an nan Allah ya ce, “Bari mu yi mutum cikin siffarmu, cikin kamanninmu, bari kuma su yi mulki a bisa kifin teku, tsuntsayen sama, da kuma dabbobi, su yi mulki a bisa dukan duniya, da kuma a bisa dukan halittu, da masu rarrafe a ƙasa.”

    27 Saboda haka Allah ya halicci mutum cikin siffarsa.

    Cikin kamannin Allah, Allah ya halicci mutum.

    Miji da mace ya halicce su.

    28 Allah ya albarkace su, ya kuma ce musu, “Ku yi ta haihuwa ku ƙaru da yawa, ku mamaye duniya, ku mallake ta. Ku yi mulki a bisa kifin teku, da tsuntsayen sararin sama, da kuma bisa kowace halitta mai rai wadda take rarrafe a ƙasa.”

    29 Sa’an nan Allah ya ce, “Ga shi, na ba ku kowane tsiro mai ba da ’ya’ya masu kwaya da suke a fāɗin duniya, da dukan itatuwa masu ba da ’ya’ya, don su zama abinci a gare ku. 30 Na kuma ba da dukan dabbobin ƙasa, da dukan tsuntsayen sama, da dukan abin da yake rarrafe a ƙasa, da dai iyakar abin da yake numfashi; haka kuma na ba da ganyaye su zama abinci.” Haka kuwa ya kasance.

  3. 15 “Dubi dorina,

    wadda na halicce ku tare

    kuma ciyawa take ci kamar sa.

    16 Ga shi ƙarfinta yana a ƙugunta

    ikonta yana cikin tsokar cikinta.

    17 Wutsiyarta tana da ƙarfi kamar itacen al’ul;

    jijiyoyin cinyoyinta suna haɗe a wuri ɗaya.

    18 Ƙasusuwanta bututun tagulla ne,

    haƙarƙarinta kamar sandunan ƙarfe.

    19 Tana ta farko cikin ayyukan Allah,

    Mahaliccinta kaɗai yake iya tunkarar ta da takobi.

    20 Tuddai su suke tanada mata abinci

    a inda duk namun jeji suke wasa.

    21 Tana kwanciya a ƙarƙashin inuwar itacen lotus

    ta ɓuya cikin kyauro da fadama.

    22 Inuwa ta rufe ta da ƙaddaji,

    itatuwan wardi na rafi, sun kewaye ta.

    23 Sa’ad da kogi ya cika yana hauka, ba tă damu ba;

    ba abin da zai same ta ko da a gaban bakinta Urdun yake wucewa.

    24 Ko akwai wanda zai iya kama ta ba ta kallo,

    ko kuma a kama ta da tarko a huda hancinta?

  4. 1 A farko-farko, Allah ya halicci sama da ƙasa. 2 To, ƙasa dai ba ta da siffa, babu kuma kome a cikinta, duhu ne kawai ya rufe ko’ina, Ruhun Allah kuwa yana yawo a kan ruwan.

    3 Sai Allah ya ce, “Bari haske yă kasance,” sai kuwa ga haske. 4 Allah ya ga hasken yana da kyau, sai ya raba tsakanin hasken da duhu. 5 Allah ya kira hasken “yini,” ya kuma kira duhun “dare.” Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta fari ke nan.

    6 Allah ya ce, “Bari sarari yă kasance tsakanin ruwaye domin yă raba ruwa da ruwa.” 7 Saboda haka Allah ya yi sarari ya raba ruwan da yake ƙarƙashin sararin da ruwan da yake bisansa. Haka kuwa ya kasance.

  5. 13 Gama ka halicci ciki-cikina;

    ka gina ni gaba ɗaya a cikin mahaifar mahaifiyata.

    14 Ina yabonka domin yadda ka yi ni abin tsoro ne da kuma abin mamaki;

    ayyukanka suna da banmamaki,

    na san da haka sosai.

    15 Ƙasusuwana ba a ɓoye suke a gare ka ba

    sa’ad da aka yi ni asirce.

    Sa’ad da saƙa ni gaba ɗaya a zurfafan duniya.

    16 Idanunka sun ga jikina marar fasali;

    dukan kwanakin da aka tsara mini a rubuce suke a littafinka

    kafin ɗayansu yă kasance.

    17 Tunaninka suna da daraja gare ni, ya Allah!

    Yawansu ba su da iyaka!

    18 A ce zan iya ƙirgansu,

    za su fi yashin teku yawa.

    Sa’ad da na farka, ina nan tare da kai har yanzu.

  6. 10 Ai, mu aikinsa ne, an sāke halittarmu a cikin Kiristi Yesu musamman domin mu yi kyawawan ayyuka, waɗanda Allah ya tanadar mana tun da fari, mu yi.

  7. 7 Ni ne na siffanta haske na kuma halicci duhu,

    ni ne nake ba da nasara in kuma jawo bala’i;

    ni, Ubangiji ne ke aikata dukan waɗannan abubuwa.

    8 “Ku sammai, ku sauko da adalci kamar ruwan sama;

    bari gizagizai su zubar da yayyafi kamar adalci.

    Bari ƙasa ta buɗe,

    bari ceto ya tsiro,

    bari adalci ya yi girma tare da shi;

    ni, Ubangijine, na sa ya faru.

    9 “Kaitonka mai gardama da Wanda ya yi ka,

    da wanda yake kasko a cikin kasko a ƙasa.

    Yumɓu ya iya ce wa magini,

    ‘Me kake yi?’

    Aikinka na iya cewa,

    ‘Ba shi da hannuwa’?

    10 Kaiton wanda yake cewa mahaifinsa,

    ‘Me ka manta?’

    Ko kuwa ga mahaifiyarsa,

    ‘Me kin haifa?’

    11 “Ga abin da Ubangiji yana cewa,

    Mai Tsarkin nan na Isra’ila, da kuma Mahaliccinsa.

    Game da abubuwan da ke zuwa,

    kun tambaye ni game da ’ya’yana,

    ko kuwa kun ba ni umarni game da aikin hannuwana?

    12 Ai, ni ne wanda ya yi duniya

    na kuma halicci mutum a kanta.

    Hannuwana ne sun miƙe sammai;

    na umarci rundunar sararin sama.

  8. 29 Kana ganin mutumin da yake da gwaninta a cikin aikinsa?

    Zai yi wa sarakuna hidima;

    ba zai yi hidima wa mutanen da ba su iya ba.

  9. 15 Kana da ma’aikata masu yawa, masu fafarshe duwatsu, masu gini da masu aikin katako, da kuma gwanaye a kowane irin aikin 16 zinariya da azurfa, tagulla da ƙarfe, masu sana’a waɗanda suka wuce ƙirge. Yanzu ka fara aiki, Ubangiji kuma ya kasance tare da kai.”

  10. 7 Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mutum daga turɓayar ƙasa, ya kuma hura numfashin rai cikin hancinsa, mutumin kuwa ya zama rayayyen taliki.

  11. 1 Saboda haka, ina roƙonku, ’yan’uwa, saboda yawan jinƙan Allah, ku miƙa jikunanku hadaya wadda take mai rai, mai tsarki abin karɓa kuma ga Allah, wannan ita ce hanyar hidimarku ta ruhaniya. 2 Kada ku ci gaba da yin abin da duniya take yi, sai dai ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so yake, abu mai kyau, mai daɗi da kuma cikakke.

    3 Gama ta wurin alherin nan da aka yi mini ne ina ce wa kowannenku. Kada yă ɗauki kansa fiye da yadda ya kamata, a maimakon haka bari yă auna kansa cikin natsuwa, gwargwadon baiwar bangaskiyar da Allah yi masa. 4 Kamar dai yadda kowannenmu yake da jiki ɗaya da gaɓoɓi da yawa, gaɓoɓin nan kuwa ba aiki iri ɗaya suke yi ba, 5 haka ma a cikin Kiristi mu da muke da yawa mun zama jiki ɗaya, kuma kowace gaɓar ɗan’uwan sauran ne. 6 Muna da baye-baye dabam-dabam, gwargwadon alherin da aka yi mana. In baiwar mutum ta yin annabci ce, sai yă yi amfani da ita gwargwadon bangaskiyarsa. 7 In ta hidima ce; sai yă yi hidima. In kuma ta koyarwa ce, sai yă koyar; 8 in ta ƙarfafawa ce, sai yă ƙarfafa; in kuma ta ba da taimako ce don biyan bukatun waɗansu, sai yă yi haka hannu sake; in ta shugabanci ce, sai yă yi shugabanci da himma; in ta nuna jinƙai ce, sai yă yi haka da fara’a.

  12. 14 Kada ka yi sakaci da baiwarka, wadda aka ba ka ta wurin saƙon annabci sa’ad da ƙungiyar dattawa suka ɗibiya hannuwa a kanka.

    15 Ka yi ƙwazo cikin waɗannan batuttuwa; ka ba da kanka gaba ɗaya gare su, don kowa yă ga ci gabanka.

  13. 19 Gunki dai, maƙeri kan yi zubinsa,

    maƙerin zinariya kuma yă ƙera shi da zinariya

    yă kuma sarrafa masa sarƙoƙin azurfa.

    20 Mutumin da talauci ya sha kansa da ba zai iya miƙa irin hadayar nan ba

    kan zaɓi itacen da ba zai ruɓe ba.

    Yakan nemi gwanin sassaƙa

    don yă sassaƙa masa gunkin da ba zai fāɗi ba.

  14. 10 Waɗanda suke siffanta allah su kuma yi zubin gunki,

    waɗanda ba za su yi musu ribar kome ba?

    11 Shi da irinsa za su sha kunya;

    masu sassaƙa ba kome ba mutane ne kurum.

    Bari su tattaru su ɗauki matsayinsu;

    za su firgita su kuma sha mummunan kunya.

    12 Maƙeri yakan ɗauki kayan aiki

    ya yi aiki da shi a cikin garwashi;

    ya ƙera gunki da guduma,

    ya gyara shi da hannuwansa masu ƙarfi.

    Yakan ji yunwa ya kuma rasa ƙarfi;

    yakan sha ruwa ya kuma ji gajiya.

    13 Kafinta yakan gwada katako

    yă kuma zāna siffar da alli;

    yă goge shi da kayan aiki

    yă kuma zāna shi da alƙalami.

    Yă siffanta shi a kamannin mutum,

    mutum cikin dukan darajarsa,

    don yă ajiye shi a cikin masujada.

  15. 20 Gama tun halittar duniya halayen Allah marar ganuwa, madawwamin ikonsa da kuma allahntakarsa, ana iya ganinsu sarai, ana fahimtarsu ta wurin abubuwan da Allah ya halitta, domin kada mutane su sami wata hujja.