33 Bible Verses About Family

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Family
  1. 18 Mata, ku yi biyayya ga mazanku, yadda ya dace cikin Ubangiji.

    19 Maza, ku ƙaunaci matanku kada ku nuna musu hali marar tausayi.

    20 ’Ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku cikin kome, gama wannan yakan gamshi Ubangiji.

    21 Ubanni, kada ku matsa wa yaranku lamba, don kada su fid da zuciya.

    22 Bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya cikin kome; kada ku yi aikin ganin ido kamar masu neman yabon mutane, sai dai ku yi aiki tsakaninku da Allah, kamar masu tsoron Ubangiji. 23 Kome kuke yi, ku yi shi da dukan zuciyarku, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba ga mutum ba. 24 Kun san cewa zai ba ku gādo a matsayin ladanku. Ubangiji Kiristi ne fa kuke bauta wa. 25 Duk wanda ya yi laifi, za a sāka masa don laifinsa, babu sonkai.

  2. 1 Ku ’ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku, gama ku na Ubangiji, abin da ya dace ku yi ke nan. 2 Doka ta farko wadda aka haɗa da alkawari ita ce, “Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, 3 don ka zauna lafiya, ka kuma yi tsawon rai a duniya.”

    4 Ku kuma iyaye, kada ku tsokane ’ya’yanku. Ku yi musu reno mai kyau. Ku koyar da su, ku kuma gargaɗe su game da Ubangiji.

  3. 21 Saboda haka Ubangiji Allah ya sa mutumin ya yi barci mai nauyi; yayinda yake barci sai ya ɗauko ɗaya daga cikin haƙarƙarin mutumin, ya kuma rufe wurin da nama. 22 Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mace daga haƙarƙarin da ya ɗauko daga mutumin, ya kuwa kawo ta wurin mutumin.

    23 Sai mutumin ya ce,

    “Yanzu kam wannan ƙashi ne na ƙasusuwana

    nama kuma na namana.

    Za a ce da ita ‘mace,’

    gama an ciro ta daga namiji.”

    24 Wannan ne ya sa mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa, su kuma zama jiki ɗaya.

  4. 12 Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.

  5. 15 Amma in kuka ga ba za ku iya bauta wa Ubangiji ba, sai ku zaɓa yau wanda za ku bauta masa, ko allolin da kakanninku suka bauta musu a hayin Kogin Yuferites, ko kuma allolin Amoriyawa, waɗanda kuke zama a cikin ƙasarsu. Amma da ni da gidana, Ubangiji ne za mu bauta wa.”

  6. 6 Ka hori yaro a hanyar da ya kamata yă bi,

    kuma sa’ad da ya tsufa ba zai bar ta ba.

  7. 3 ’Ya’ya maza gādo ne daga Ubangiji,

    yara lada ne daga gare shi.

    4 Kamar kibiyoyi a hannun jarumi

    haka ’ya’ya mazan da aka haifa wa mutum a ƙuruciya.

    5 Mai albarka ne mutumin

    da korinsa sun cika da su.

    Ba za a kunyata su ba

    sa’ad da suke ƙarawa da abokan gābansu a ɗakin shari’a.

  8. 22 Matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, kamar ga Ubangiji ne kuke yi. 23 Gama miji shi ne kan mace, yadda Kiristi yake kai da kuma Mai Ceton ikkilisiya, wadda take jikinsa. 24 To, kamar yadda ikkilisiya take biyayya ga Kiristi, haka ma ya kamata mata su yi biyayya ga mazansu cikin kome.

    25 Maza, ku ƙaunaci matanku, kamar yadda Kiristi ya ƙaunaci ikkilisiya, ya kuma ba da kansa dominta. 26 Ya mai da ikkilisiya ta zama mai tsarki ta wurin ikon maganarsa, ya kuma tsabtacce ta ta wurin wanke ta da ruwa. 27 Kiristi ya yi haka don yă miƙa wa kansa ikkilisiya mai ɗaukaka da kuma mai tsarki, marar aibi, marar tabo, da kuma marar lahani. 28 Don haka, dole maza su ƙaunaci matansu kamar yadda suke ƙaunar jikunansu. Wanda yake ƙaunar matarsa, yana ƙaunar kansa ne.

  9. 26 Sa’an nan Allah ya ce, “Bari mu yi mutum cikin siffarmu, cikin kamanninmu, bari kuma su yi mulki a bisa kifin teku, tsuntsayen sama, da kuma dabbobi, su yi mulki a bisa dukan duniya, da kuma a bisa dukan halittu, da masu rarrafe a ƙasa.”

    27 Saboda haka Allah ya halicci mutum cikin siffarsa.

    Cikin kamannin Allah, Allah ya halicci mutum.

    Miji da mace ya halicce su.

    28 Allah ya albarkace su, ya kuma ce musu, “Ku yi ta haihuwa ku ƙaru da yawa, ku mamaye duniya, ku mallake ta. Ku yi mulki a bisa kifin teku, da tsuntsayen sararin sama, da kuma bisa kowace halitta mai rai wadda take rarrafe a ƙasa.”

  10. 4 Ku ji, ya Isra’ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne. 5 Ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku da dukan zuciyarku, da dukan ranku, da kuma dukan ƙarfinku. 6 Waɗannan umarnai da nake ba ku a yau, za su kasance a zukatanku. 7 Ku koya wa ’ya’yanku su da himma. Yi musu magana game da su sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya a hanya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi. 8 Ku ɗaura su su zama alamu a hannuwanku, ku kuma ɗaura su a goshinku. 9 Ku rubuta su a dogaran ƙofofin gidajenku, da ƙofofinku.

  11. 2 Waɗansu Farisiyawa suka zo suka gwada shi, ta wurin yin masa tambaya cewa, “Daidai ne bisa ga doka, mutum yă saki matarsa?”

    3 Ya amsa ya ce, “Me Musa ya umarce ku?”

    4 Suka ce, “Musa ya ba da izini mutum yă rubuta takardar saki, yă kuma kore ta.”

    5 Yesu ya ce, “Saboda taurin kanku ne, Musa ya rubuta muku wannan doka. 6 Amma a farkon halitta, Allah ya ‘halicce su miji da mace.’ 7 ‘Saboda wannan dalili, mutum zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa, 8 su biyun kuma za su zama jiki ɗaya.’ Saboda haka, su ba mutum biyu ba ne, amma mutum ɗaya. 9 Domin haka, abin da Allah ya haɗa, kada mutum yă raba.”

  12. 2 To, dole mai kula da Ikkilisiya yă kasance marar abin zargi, mijin mace guda, mai sauƙinkai, mai kamunkai, wanda ake girmama, mai karɓan baƙi, mai iya koyarwa, 3 ba mai buguwa ba, ba mai rikici ba sai dai mai hankali, ba mai yawan faɗa ba, ba kuma mai yawan son kuɗi ba. 4 Dole yă iya tafiyar da iyalinsa da kyau, yă kuma tabbata cewa ’ya’yansa suna yin masa biyayya da ladabin da ya dace. 5 (In mutum bai san yadda zai tafiyar da iyalinsa ba, yaya zai iya kula da ikkilisiyar Allah?)

  13. 8 In wani bai kula da danginsa ba, musamman iyalinsa na kurkusa, ya mūsunta bangaskiya ke nan, ya kuma fi marar ba da gaskiya muni.

  14. 4 Ƙauna tana da haƙuri, ƙauna tana da kirki. Ba ta kishi, ba ta burga, ba ta da girman kai. 5 Ba ta rashin ladabi, ba ta sonkai, ba ta da saurin fushi, ba ta riƙe mutum a zuciya. 6 Ƙauna ba ta jin daɗin mugunta, sai dai ta ji daɗin gaskiya. 7 Tana kāriya kullum, tana amincewa kullum, tana bege kullum, tana jimrewa kullum.

    8 Ƙauna ba ta ƙarewa. Amma in akwai annabci zai shuɗe, harsuna su ɓace, ilimi kuma zai ƙare.

  15. 26 Dukanku ’ya’yan Allah ne ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu. 27 Gama dukanku da aka yi muku baftisma cikin Kiristi, kuna sanye da Kiristi ke nan. 28 Babu bambanci tsakanin mutumin Yahuda da mutumin Al’ummai, bawa da ’yantacce, namiji da ta mace, gama dukanku ɗaya ne cikin Kiristi Yesu. 29 In kuwa ku na Kiristi ne, to, ku zuriyar Ibrahim ne, magāda kuma bisa ga alkawarin nan.

  16. Waƙar haurawa. Ta Dawuda.

    1 Abu mai kyau ne, mai daɗi kuma

    sa’ad da ’yan’uwa suna zaman lafiya!

  17. 10 Saboda haka, in da hali, bari mu aikata nagarta ga dukan mutane, musamman ga waɗanda suke na iyalin masu bi.

  18. 1 Haka ma, ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, domin in waɗansunsu ba su gaskata maganar ba, wataƙila a shawo kansu ba tare da magana ba 2 sa’ad da suka ga rayuwarku mai tsabta da kuma na ladabi. 3 Kyanku bai kamata yă zama na adon jiki ba, kamar kitso da sa kayan ado na zinariya da kuma sa kaya masu tsada. 4 Maimakon haka, kyanku ya kamata yă zama ainihi na halinku na ciki, kyan da ba ya koɗewa na tawali’u da kuma na natsattsen ruhu, wanda yake mai daraja a gaban Allah. 5 Gama haka matan masu tsarki na dā waɗanda suka sa begensu ga Allah suka yi wa kansu ado. Sun yi wa mazansu biyayya, 6 kamar Saratu, wadda ta yi biyayya ga Ibrahim, har ta kira shi maigidanta. Ku ’ya’yanta ne mata in kun aikata abin da yake daidai, ba ku kuma ba tsoro dama ba.

    7 Mazan aure, ku ma, ku yi zaman sanin ya kamata yayinda kuke zama da matanku, ku girmama su a matsayin abokan zama marasa ƙarfi da kuma a matsayin magādan kyautar rai na alheri tare da ku, don kada wani abu yă hana addu’o’inku.

  19. 3 Matarka za tă zama kamar kuringar inabi mai ’ya’ya

    a cikin gidanka;

    ’ya’yanka maza za su zama kamar tohon zaitun

    kewaye da teburinka.

    4 Ta haka mai albarka yake

    wanda yake tsoron Ubangiji.

    5 Bari Ubangiji ya albarkace ka daga Sihiyona

    dukan kwanakin ranka;

    bari ka ga wadatar Urushalima,

    6 bari kuma ka rayu ka ga ’ya’ya ’ya’yanka.

    Salama tă kasance tare da Isra’ila.

  20. 29 Duk wanda ya kawo wahala wa iyalinsa zai gāji iska kawai,

    kuma wawa zai zama bawan masu hikima.

  21. 20 Ɗa mai hikima kan kawo farin ciki wa mahaifinsa,

    amma wawa yakan rena mahaifiyarsa.

  22. 33 Duk da haka, dole kowannenku yă ƙaunaci matarsa kamar yadda yake ƙaunar kansa, kuma dole matar tă yi biyayya ga mijinta.

  23. 11 Wannan shi ne saƙon da kuka ji tun farko. Ya kamata mu ƙaunaci juna. 12 Kada ku zama kamar Kayinu, wanda ya zama na mugun nan, ya kuma kashe ɗan’uwansa. Me ya sa ya kashe shi? Domin ayyukansa mugaye ne, na ɗan’uwansa kuma na adalci ne. 13 Kada ku yi mamaki ’yan’uwana, in duniya ta ƙi ku. 14 Mun san cewa mun riga mun ratsa daga mutuwa zuwa rai, domin muna ƙaunar ’yan’uwanmu. Duk wanda ba ya ƙauna matacce ne har yanzu. 15 Duk mai ƙin ɗan’uwansa mai kisankai ne, kun kuma san cewa ba mai kisankan da yake da rai madawwami a cikinsa.

    16 Yadda muka san ƙauna ke nan, wato, Yesu Kiristi ya ba da ransa dominmu. Ya kamata mu ma mu ba da rayukanmu domin ’yan’uwanmu. 17 In wani yana da arziki, ya kuma ga ɗan’uwansa cikin rashi, bai kuwa taimake shi ba, anya, ƙaunar Allah tana a cikinsa kuwa? 18 ’Ya’yana ƙaunatattu, kada mu yi ƙauna da fatar baki kawai, sai dai mu nuna ta ta wurin aikatawa da kuma gaskiya.

  24. 5 Uba ga marayu, mai kāre gwauraye,

    shi ne Allah a mazauninsa mai tsarki.

    6 Allah ya shirya masu kaɗaici a cikin iyalai,

    ya jagorance ’yan kurkuku da waƙoƙi;

    amma ’yan tawaye suna zama a ƙasa mai zafin rana.

  25. 13 Yanzu kam abubuwan nan uku sun tabbata, bangaskiya, bege, da kuma ƙauna. Sai dai mafi girma a cikinsu ita ce ƙauna.

  26. 19 Muna ƙauna, domin ya ƙaunace mu da farko.

  27. 6 Jikoki rawanin tsofaffi ne,

    kuma iyaye su ne abin taƙamar ’ya’yansu.

  28. 15 Takan farka tun da sauran duhu;

    ta tanada wa iyalinta abinci

    ta kuma shirya wa ’yan matan gidanta ayyukan da za su yi.

    16 Takan lura da gona sosai ta kuma saye ta;

    daga abin da take samu na kuɗin shiga take shuka gonar inabi.

    17 Takan himmantu tă yi aikinta tuƙuru;

    hannuwanta suna da ƙarfi domin ayyukanta.

  29. 46 Yayinda Yesu yake cikin magana da taron, sai ga mahaifiyarsa da ’yan’uwansa tsaye a waje, suna so su yi magana da shi. 47 Wani ya ce masa, “Mahaifiyarka da ’yan’uwanka suna tsaye a waje, suna so su yi magana da kai.”

    48 Ya amsa masa ya ce, “Wace ce mahaifiyata, su wane ne kuma ’yan’uwana?” 49 Sai ya miƙa hannu wajen almajiransa ya ce, “Ga mahaifiyata da kuma ’yan’uwana. 50 Ai, duk wanda yake aikata nufin Ubana wanda yake cikin sama, shi ne ɗan’uwana da ’yar’uwata da kuma mahaifiyata.”

  30. 7 Tsoron Ubangiji shi ne masomin ilimi,

    amma wawaye sun rena hikima da horo.

    Gargaɗi don a rungumi hikima

    8 Ɗana, ka saurari umarnin mahaifinka

    kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.

    9 Za su zama kayan ado don su inganta ka

    da kuma sarƙar wuya don su yi wa wuyanka ado.

  31. 20 Ɗana, ka kiyaye umarnan mahaifinka

    kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.

  32. 3 To, ina so ku gane cewa shugaban kowane namiji Kiristi ne, shugaban mace namiji ne, shugaban Kiristi kuma Allah ne.

  33. 20 Duk wanda ya ce, “Ina ƙaunar Allah,” amma yana ƙin ɗan’uwansa, maƙaryaci ne. Gama duk wanda ba ya ƙaunar ɗan’uwansa da yake gani, ba zai iya ƙaunar Allah wanda ba ya gani ba.