54 Bible Verses About Mother's Day
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
Maganar ƙarshe. Mace Mai Halin Kirki
10 Wa yake iya samun mace mai halin kirki?
Darajarta ta fi ta lu’ulu’ai.
11 Mijinta yana da cikakken amincewa da ita
kuma ba ya rasa wani abu mai daraja.
12 Takan yi masa alheri ba mugunta ba,
dukan kwanakin ranta.
13 Takan zaɓi ulu da lilin
ta yi ta saƙa da hannuwanta da farin ciki.
14 Ita kamar jirgin ’yan kasuwa ne
tana kawo abincinta daga nesa.
15 Takan farka tun da sauran duhu;
ta tanada wa iyalinta abinci
ta kuma shirya wa ’yan matan gidanta ayyukan da za su yi.
16 Takan lura da gona sosai ta kuma saye ta;
daga abin da take samu na kuɗin shiga take shuka gonar inabi.
17 Takan himmantu tă yi aikinta tuƙuru;
hannuwanta suna da ƙarfi domin ayyukanta.
18 Takan tabbata akwai riba a kasuwancinta,
kuma fitilarta ba ya mutuwa da dare.
19 Da hannunta take riƙe abin kaɗi
ta kuma kama abin saƙa da yatsotsinta.
20 Takan marabci talakawa
takan kuma taimaki masu bukata.
21 Sa’ad da ƙanƙara ta fāɗi, ba ta jin tsoro saboda gidanta;
gama dukansu suna da tufafi masu kauri.
22 Takan yi wa gadonta kayan shimfiɗa;
tufafinta kuma na lilin ne mai laushi na shunayya.
23 Ana girmama mijinta a ƙofar shiga birni
inda yakan zauna a cikin dattawan gari.
24 Takan yi riguna na lilin ta sayar;
takan kuma sayar wa ’yan kasuwa da ɗamara.
25 Ƙarfi da mutunci su ne suturarta;
za tă iya yin dariyar kwanaki masu zuwa.
26 Tana magana da hikima,
kuma umarnai mai aminci yana a harshenta.
27 Tana lura da sha’anin gidanta
kuma ba ta cin abincin ƙyuya.
28 ’Ya’yanta sukan tashi su ce da ita mai albarka;
haka mijinta ma, yakan kuma yabe ta yana cewa,
29 “Mata da yawa suna yin abubuwan yabo,
amma ke kin fi su duka.”
30 Kayan tsari yana ruɗu, kyau kuma kan shuɗe;
amma mace mai tsoron Ubangiji abar yabo ce.
31 Ka ba ta ladar da ya dace tă samo wa kanta,
bari kuma ayyukanta su kawo mata yabo a ƙofar shiga birni.
-
25 To, tsaye kusa da gicciyen Yesu kuwa akwai mahaifiyarsa, tare da ’yar’uwar mahaifiyarsa, Maryamu matar Kilofas, da kuma Maryamu Magdalin. 26 Sa’ad da Yesu ya ga mahaifiyarsa a can, da kuma almajirin nan da yake ƙauna tsaye kusa, sai ya ce wa mahaifiyarsa, “Mace, ga ɗanki,” 27 ga almajirin kuwa ya ce, “Ga mahaifiyarka.” Tun daga wannan lokaci fa almajirin nan ya kai ta gidansa.
-
1 Ku ’ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku, gama ku na Ubangiji, abin da ya dace ku yi ke nan. 2 Doka ta farko wadda aka haɗa da alkawari ita ce, “Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, 3 don ka zauna lafiya, ka kuma yi tsawon rai a duniya.”
-
22 Ka kasa kunne ga mahaifinka, wanda ya ba ka rai,
kada kuwa ka rena mahaifiyarka sa’ad da ta tsufa.
23 Ka saye gaskiya kada kuwa ka sayar da ita;
ka nemi hikima, horo da fahimi.
24 Mahaifin adali yana da farin ciki sosai;
duk wanda yake da ɗa mai hikima yakan ji daɗinsa.
25 Bari mahaifinka da mahaifiyarka su yi murna;
bari wadda ta haife ka tă yi farin ciki!
-
12 Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.
-
Gargaɗi don a rungumi hikima
8 Ɗana, ka saurari umarnin mahaifinka
kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.
9 Za su zama kayan ado don su inganta ka
da kuma sarƙar wuya don su yi wa wuyanka ado.
-
6 Ka hori yaro a hanyar da ya kamata yă bi,
kuma sa’ad da ya tsufa ba zai bar ta ba.
-
3 Haka ma, ka koya wa tsofaffin mata su zama masu bangirma cikin rayuwarsu, ba masu ɓata suna ko masu jarrabar shan giya ba, sai dai su zama masu koyar da abin da yake nagari. 4 Sa’an nan za su iya su koya wa mata masu ƙuruciya su ƙaunaci mazansu da ’ya’yansu, 5 su kasance da kamunkai da kuma tsarki, masu aiki a gida, masu kirki da kuma masu biyayya ga mazansu, don kada wani yă rena maganar Allah.
-
1 Haka ma, ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, domin in waɗansunsu ba su gaskata maganar ba, wataƙila a shawo kansu ba tare da magana ba 2 sa’ad da suka ga rayuwarku mai tsabta da kuma na ladabi. 3 Kyanku bai kamata yă zama na adon jiki ba, kamar kitso da sa kayan ado na zinariya da kuma sa kaya masu tsada. 4 Maimakon haka, kyanku ya kamata yă zama ainihi na halinku na ciki, kyan da ba ya koɗewa na tawali’u da kuma na natsattsen ruhu, wanda yake mai daraja a gaban Allah.
-
13 Gama ka halicci ciki-cikina;
ka gina ni gaba ɗaya a cikin mahaifar mahaifiyata.
14 Ina yabonka domin yadda ka yi ni abin tsoro ne da kuma abin mamaki;
ayyukanka suna da banmamaki,
na san da haka sosai.
15 Ƙasusuwana ba a ɓoye suke a gare ka ba
sa’ad da aka yi ni asirce.
Sa’ad da saƙa ni gaba ɗaya a zurfafan duniya.
16 Idanunka sun ga jikina marar fasali;
dukan kwanakin da aka tsara mini a rubuce suke a littafinka
kafin ɗayansu yă kasance.
-
3 ’Ya’ya maza gādo ne daga Ubangiji,
yara lada ne daga gare shi.
4 Kamar kibiyoyi a hannun jarumi
haka ’ya’ya mazan da aka haifa wa mutum a ƙuruciya.
5 Mai albarka ne mutumin
da korinsa sun cika da su.
Ba za a kunyata su ba
sa’ad da suke ƙarawa da abokan gābansu a ɗakin shari’a.
-
41 Da Elizabet ta ji gaisuwar Maryamu, sai jaririn da yake a cikinta ya yi motsi. Elizabet kuma ta cika da Ruhu Mai Tsarki. 42 Sai ta ɗaga murya da ƙarfi ta ce, “Ke mai albarka ce a cikin mata. Mai albarka ne kuma ɗan da za ki haifa! 43 Me ya sa na sami wannan tagomashi har da mahaifiyar Ubangijina za tă zo wurina? 44 Da jin gaisuwarki, sai jaririn da yake cikina ya yi motsi don murna. 45 Mai albarka ce wadda ta gaskata cewa abin da Ubangiji ya faɗa mata zai cika!”
46 Sai Maryamu ta ce,
“Raina yana ɗaukaka Ubangiji
47 ruhuna kuma yana farin ciki da Allah Mai Cetona,
48 gama ya lura da ƙasƙancin baiwarsa.
Daga yanzu nan gaba dukan zamanai za su ce da ni mai albarka,
49 gama Mai Iko Duka ya yi mini manyan abubuwa,
sunansa labudda Mai Tsarki ne.
-
5 An tunashe ni da sahihiyar bangaskiyarka, wadda a farko ta kasance a cikin kakarka Loyis da kuma mahaifiyarka Yunis yanzu kuwa na tabbata tana cikinka.
-
20 Ɗana, ka kiyaye umarnan mahaifinka
kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.
21 Ka ɗaura su a zuciyarka har abada;
ka ɗaura su kewaye da wuyanka.
22 Sa’ad da kake tafiya, za su bishe ka;
sa’ad da kake barci, za su lura da kai;
sa’ad da ka farka, za su yi maka magana.
23 Gama waɗannan umarnai fitila ne,
wannan koyarwa haske ne,
kuma gyare-gyaren horo
hanyar rayuwa ce,
-
4 Ƙauna tana da haƙuri, ƙauna tana da kirki. Ba ta kishi, ba ta burga, ba ta da girman kai. 5 Ba ta rashin ladabi, ba ta sonkai, ba ta da saurin fushi, ba ta riƙe mutum a zuciya. 6 Ƙauna ba ta jin daɗin mugunta, sai dai ta ji daɗin gaskiya. 7 Tana kāriya kullum, tana amincewa kullum, tana bege kullum, tana jimrewa kullum.
-
1 Kada ka tsawata wa dattijo, sai dai ka gargaɗe shi a matsayinka. Ka ɗauki samari a matsayin ’yan’uwanka, 2 tsofaffin mata kuwa sai ka ce uwaye, ’yan mata kuma a matsayin ’yan’uwa da matuƙar tsarki.
-
26 Sai ta ce masa, “Ranka yă daɗe, ba ka gane ni ba? Ai, ni ce matar da ta taɓa tsayawa a gabanka, tana addu’a ga Ubangiji. 27 Wannan yaron ne na roƙa daga wurin Ubangiji, ya kuwa ba ni abin da na roƙa daga gare shi. 28 Saboda haka, na ba da shi ga Ubangiji muddin ransa, zai zama na Ubangiji.” A can kuwa ya yi wa Ubangiji sujada.
-
15 Sandar gyara kan ba da hikima,
amma yaron da aka bari ba horo kan jawo kunya ga mahaifiyarsa.
16 Sa’ad da mugaye suke cin nasara, haka zunubi zai yi ta ƙaruwa,
amma masu adalci za su ga fāɗuwar waɗannan mutane.
17 Ka hori ɗanka, zai kuwa ba ka salama;
zai ba ka farin cikin da kake so.
-
46 Yayinda Yesu yake cikin magana da taron, sai ga mahaifiyarsa da ’yan’uwansa tsaye a waje, suna so su yi magana da shi. 47 Wani ya ce masa, “Mahaifiyarka da ’yan’uwanka suna tsaye a waje, suna so su yi magana da kai.”
48 Ya amsa masa ya ce, “Wace ce mahaifiyata, su wane ne kuma ’yan’uwana?” 49 Sai ya miƙa hannu wajen almajiransa ya ce, “Ga mahaifiyata da kuma ’yan’uwana. 50 Ai, duk wanda yake aikata nufin Ubana wanda yake cikin sama, shi ne ɗan’uwana da ’yar’uwata da kuma mahaifiyata.”
-
35 Gama na zo ne in sa,
“ ‘gāba tsakanin mutum da mahaifinsa,
’ya da mahaifiyarta,
matar ɗa da surukarta,
36 abokan gāban mutum, za su zama mutanen gidansa ne.’
37 “Duk wanda ya fi ƙaunar mahaifinsa ko mahaifiyarsa fiye da ni, bai dace yă zama nawa ba; duk kuwa wanda yake ƙaunar ɗansa ko diyarsa fiye da ni, bai dace yă zama nawa ba; 38 duk wanda kuma bai ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, bai dace yă zama nawa ba.
-
48 Da iyayensa suka gan shi sai suka yi mamaki. Mahaifiyarsa ta ce masa, “Ɗana, don me ka yi mana haka? Ni da mahaifinka duk mun damu muna nemanka.”
49 Sai ya ce, “Don me kuke nemana? Ba ku san cewa, dole in kasance a gidan Ubana ba?” 50 Amma ba su fahimci abin da yake faɗin musu ba.
51 Sai ya koma Nazaret tare da su, yana yi musu biyayya. Mahaifiyarsa kuma ta riƙe dukan waɗannan abubuwa a zuciyarta.
-
57 Da yamma ta yi, sai ga wani mutum mai arziki daga Arimateya, sunansa Yusuf, wanda shi da kansa almajirin Yesu ne. 58 Ya je wurin Bilatus, ya roƙe shi yă ba shi jikin Yesu. Sai Bilatus ya umarta a ba shi. 59 Yusuf ya ɗauki jikin ya nannaɗe shi da zanen lilin mai tsabta. 60 Sa’an nan ya sa shi a sabon kabarinsa, wanda ya haƙa a dutse. Bayan ya gungura wani babban dutse ya rufe bakin kabarin, sai ya tafi abinsa. 61 Maryamu Magdalin da ɗayan Maryamun, suna zaune a wurin, ɗaura da kabarin.
-
16 Rut Amma Rut ta amsa, “Kada ki roƙe ni in bar ki ko in koma daga gare ki. Inda za ki, zan tafi, kuma inda za ki zauna, zan zauna. Mutanenki, za su zama mutanena kuma Allahnki, zai zama Allahna. 17 Inda za ki mutu zan mutu, zan mutu a can kuma za a binne ni. Bari Ubangiji ya hukunta ni da tsanani sosai, in wani abu in ba mutuwa ce ta raba ke da ni ba.”
-
38 Yayinda Yesu da almajiransa suna cikin tafiya, sai ya kai wani ƙauye inda wata mace mai suna Marta ta marabce shi a gidanta. 39 Tana da ’yar’uwa mai suna Maryamu, wadda ta zauna a gaban Ubangiji tana jin maganarsa. 40 Marta kuwa, aikin hidima da ya kamata a yi, ya ɗauke mata hankali, sai ta zo wurin Yesu, ta ce, “Ubangiji, ba ka damu da yadda ’yar’uwata ta bar mini aiki ni kaɗai ba? Gaya mata ta taimake ni!”
41 Amma Ubangiji ya amsa ya ce, “Marta, Marta, hankalinki ya tashi, kuma kina damuwa a kan abubuwa da yawa. 42 Amma abu ɗaya tak ake bukata, Maryamu ta zaɓi abin da ya fi kyau, kuma ba za a raba ta da shi ba.”
-
20 Ka san dokokin da suka ce, ‘Kada ka yi zina, kada ka yi kisankai, kada ka yi sata, kada ka ba da shaida ta ƙarya, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’ ”
-
14 Waɗannan duka suka duƙufa cikin addu’a, tare da waɗansu mata da Maryamu mahaifiyar Yesu, da kuma tare da ’yan’uwansa.
-
13 Yanzu kam abubuwan nan uku sun tabbata, bangaskiya, bege, da kuma ƙauna. Sai dai mafi girma a cikinsu ita ce ƙauna.
-
8 Fiye da kome, ku ƙaunaci juna sosai, domin ƙauna tana rufe zunubai masu ɗumbun yawa.
-
4 Ba abin da ya fi sa ni farin ciki fiye da in ji cewa ’ya’yana suna cikin gaskiyan nan.
-
5 Ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku da dukan zuciyarku, da dukan ranku, da kuma dukan ƙarfinku. 6 Waɗannan umarnai da nake ba ku a yau, za su kasance a zukatanku. 7 Ku koya wa ’ya’yanku su da himma. Yi musu magana game da su sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya a hanya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi. 8 Ku ɗaura su su zama alamu a hannuwanku, ku kuma ɗaura su a goshinku. 9 Ku rubuta su a dogaran ƙofofin gidajenku, da ƙofofinku.
-
18 In mutum yana da gagararren ɗa mai tawaye, wanda ba ya biyayya ga mahaifinsa da mahaifiyarsa, ba ya kuma jin su sa’ad da suke horonsa, 19 mahaifinsa da mahaifiyarsa za su kama shi su kawo shi ga dattawa a ƙofar garinsu. 20 Za su ce wa dattawan, “Wannan ɗanmu gagararre ne, mai tawaye. Ba ya mana biyayya. Mai zari ne, kuma mashayi.” 21 Sa’an nan dukan mazan garinsa za su jajjefe shi har yă mutu. Dole ku fid da mugu daga cikinku. Dukan Isra’ila kuwa za su ji wannan su kuma ji tsoro.
-
Karin maganar Solomon
1 Karin maganar Solomon.
Ɗa mai hikima yakan kawo wa mahaifinsa farin ciki,
amma wawan ɗa kan sa wa mahaifiyarsa baƙin ciki.
-
6 Jikoki rawanin tsofaffi ne,
kuma iyaye su ne abin taƙamar ’ya’yansu.
-
16 Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami. 17 Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yă yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin yă ceci duniya ta wurinsa.
-
22 Amma amfanin da Ruhu yake bayar shi ne ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci, 23 sauƙinkai, da kuma kamunkai. Ai, ba ruwan Doka da waɗannan abubuwa.
-
22 Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mace daga haƙarƙarin da ya ɗauko daga mutumin, ya kuwa kawo ta wurin mutumin.
23 Sai mutumin ya ce,
“Yanzu kam wannan ƙashi ne na ƙasusuwana
nama kuma na namana.
Za a ce da ita ‘mace,’
gama an ciro ta daga namiji.”
24 Wannan ne ya sa mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa, su kuma zama jiki ɗaya.
-
15 Zan kuma sa ƙiyayya
tsakaninka da macen,
tsakanin zuriyarka da zuriyarta.
Zai ragargaje kanka,
kai kuma za ka sari ɗiɗɗigensa.”
16 Sa’an nan ya ce wa macen,
“Zan tsananta naƙudarki ainun,
da azaba kuma za ki haifi ’ya’ya.
Za ki riƙa yin marmarin mijinki
zai kuwa yi mulki a kanki.”
-
20 Mutumin ya sa wa matarsa suna, Hawwa’u, gama za tă zama mahaifiyar masu rai duka.
-
16 Mace mai hankali na samu bangirma,
amma azzalumai za su sami dukiya.
-
22 Duk wanda ya sami mace ya sami abu mai kyau
ya kuma sami tagomashi daga Ubangiji.
-
20 In mutum ya zargi mahaifinsa ko mahaifiyarsa,
fitilarsa za tă mutu a tsakiyar duhu.
-
1 Bayan ranar Asabbaci, da sassafe, a ranar farko ta mako, Maryamu Magdalin tare da ɗaya Maryamun, suka je don su ga kabarin.
-
29 Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, babu wanda zai bar gida, ko ’yan’uwa maza da mata, ko mahaifiya, ko mahaifi, ko ’ya’ya, ko gonaki saboda ni, da kuma bishara, 30 sa’an nan yă kāsa samun ninkinsu ɗari a zamanin yanzu (na gidaje, da ’yan’uwa mata, da ’yan’uwa maza, da uwaye, da ’ya’ya, da gonaki amma tare da tsanani) a lahira kuma yă sami rai madawwami.
-
34 Maryamu ta tambayi mala’ikan ta ce, “Yaya wannan zai yiwu, da yake ni budurwa ce?”
35 Mala’ikan ya amsa ya ce, “Ruhu Mai Tsarki zai sauko miki, ikon Maɗaukaki kuma zai rufe ke. Saboda haka, Mai Tsarkin nan da za a haifa, za a kira shi Ɗan Allah. 36 ’Yar’uwarki Elizabet ma za tă haifi ɗa a tsufanta, ita da aka ce bakararriya, ga shi tana a watanta na shida. 37 Gama ba abin da zai gagari Allah.”
38 Maryamu ta amsa ta ce, “To, ni baiwar Allah ce, bari yă zama mini kamar yadda ka faɗa.” Sai mala’ikan ya tafi abinsa.
-
38 Gama na tabbata cewa ko mutuwa ko rai, ko mala’iku ko aljanu, ko abubuwa na yanzu ko abubuwa masu zuwa nan gaba, ko ikoki, 39 ko tsayi ko zurfi, ko wani abu dabam cikin dukan halitta da zai iya raba mu da ƙaunar Allah wadda take cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.
-
4 Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji kullum. Ina sāke gaya muku ku yi farin ciki! 5 Bari kowa yă kasance da sauƙinkai. Ubangiji ya yi kusan zuwa. 6 Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya. 7 Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za tă tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.
8 A ƙarshe, ’yan’uwa, duk abin da yake na gaskiya, duk abin da yake na girmamawa, duk abin da yake daidai, duk abin da yake da tsarki, duk abin da yake kyakkyawa, duk abin da yake na sha’awa, in ma wani abu mafifici ne, ko ya cancanci yabo, ku yi tunani a kan irin abubuwan nan.
-
11 kamar gaggafar da take yawo a kan sheƙarta
tana rufe ’ya’yanta,
ta buɗe fikafikanta don tă kwashe su
tă ɗauke su a kafaɗunta.
-
Waƙar haurawa. Ta Dawuda.
1 Zuciyata ba mai girman kai ba ce, ya Ubangiji,
idanuna ba sa fariya;
ban dami kaina da manyan al’amura ba
ko abubuwan da suka sha ƙarfina.
2 Amma na haƙura na kuma kwantar da raina;
kamar yaron da aka yaye tare da mahaifiyarsa,
kamar yaron da aka yaye haka raina yake a cikina.
-
14 Ana gādon dawakai da wadata daga iyaye ne,
amma mace mai basira daga Ubangiji ne.
-
20 Sai mahaifiyar ’ya’yan Zebedin nan ta zo wurin Yesu tare da ’ya’yanta, da ta durƙusa a ƙasa, sai ta roƙe shi yă yi mata wani abu.
21 Ya yi tambaya ya ce, “Mene ne kike so?”
Ta ce, “Ka sa daga cikin ’ya’yan nan nawa biyu, ɗaya yă zauna a damarka, ɗaya kuma a hagunka, a mulkinka.”
22 Yesu ya ce musu, “Ba ku san abin da kuke roƙo ba. Za ku iya sha daga kwaf da zan sha?”
Suka amsa, “Za mu iya.”
23 Yesu ya ce musu, “Tabbatacce za ku sha daga kwaf na, sai dai zama a damana, ko haguna, ba ni nake da izinin bayarwa ba. Waɗannan wurare na waɗanda Ubana ya shirya wa ne.”
-
29 Da suka bar majami’ar, sai suka tafi gidan su Siman da Andarawus, tare da Yaƙub da Yohanna. 30 Surukar Siman tana kwance da zazzaɓi, sai suka gaya wa Yesu game da ita. 31 Sai ya je wajenta, ya kama hannunta, ya ɗaga ta. Zazzaɓin kuwa ya sāke ta, ta kuma yi musu hidima.
-
27 Da Yesu yake cikin faɗin waɗannan abubuwa, sai wata mace daga cikin taron ta ɗaga murya ta ce masa, “Mai albarka ce uwar da ta haife ka, wadda ka sha mamanta.”
28 Yesu ya amsa ya ce, “A maimakon, masu albarka ne waɗanda suke jin maganar Allah, suna kuma biyayya da ita.”
-
34 “Urushalima, ayya Urushalima, ke da kika kashe annabawa, kuma kika jefa wa waɗanda aka aika gare ki da duwatsu. Sau da yawa na yi kewan in tattara ’ya’yanki wuri ɗaya, kamar yadda kaza takan tattara ’ya’yanta cikin fikafikanta, amma ba ki yarda ba!
-
2 A nan aka shirya abincin yamma don girmama Yesu. Marta ta ce yi hidima, Lazarus kuma yana ɗaya cikin waɗanda suke ci tare shi. 3 Sai Maryamu ta ɗauki wajen awo guda na nardi zalla, turare mai tsada; ta zuba a ƙafafun Yesu ta kuma goge ƙafafunsa da gashinta. Gidan duk ya cika da ƙanshin turaren.
Shows Read in context, Share and Copy.