97 Bible Verses About Deceit
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
23 Kamar kaskon da aka dalaye da azurfar da ba a tace ba
haka leɓuna masu mugun zuciya.
24 Mai yin ƙiyayya yakan ɓoye kansa da maganar bakinsa,
amma a cikin zuciyarsa yana cike da munafunci
25 Ko da jawabinsa ya ɗauki hankali, kada ka gaskata shi,
gama abubuwa ƙyama guda bakwai sun cika zuciyarsa.
26 Wataƙila ya ɓoye ƙiyayyarsa da ƙarya,
duk da haka za a tone muguntarsa a cikin taro.
27 In mutum ya haƙa rami, shi zai fāɗi a ciki;
in mutum ya mirgino dutse, dutsen zai mirgine a kansa.
28 Harshe mai faɗin ƙarya yana ƙin waɗanda yake ɓata musu rai,
daɗin baki kuma yakan aikata ɓarna.
-
4 “Ka yi hankali da abokanka;
kada ka amince da ’yan’uwanka.
Gama kowane ɗan’uwa munafuki ne,
kowane aboki kuma mai kushe ne.
5 Aboki kan ruɗi aboki,
ba mai faɗar gaskiya.
Sun koya wa harshensu faɗar ƙarya;
sun gajiyar da kansu da yin zunubi.
6 Kai kana zama a tsakiyar ruɗu;
cikin ruɗunsu sun ƙi su san ni,”
in ji Ubangiji.
7 Saboda haka ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa,
“Ga shi zan tace in kuma gwada su,
gama me kuwa zan yi
saboda zunubin mutanena?
8 Harshensu kibiya ce mai dafi;
yana magana da ruɗu.
Da bakinsa kowa yana maganar alheri da maƙwabcinsa,
amma a zuciyarsa ya sa masa tarko.
9 Bai kamata in hukunta su saboda wannan ba?”
In ji Ubangiji.
“Bai kamata in ɗau fansa
a kan irin al’umma kamar wannan ba?”
-
9 Zuciya ta fi kome ruɗu
ta fi ƙarfin warkewa.
Wa zai iya gane ta?
-
4 Kai ba Allahn da yake jin daɗin mugu ba ne;
gama kana gāba da dukan masu aikata mugunta.
5 Masu fariya ba za su iya tsaya
a gabanka ba.
Kana ƙin duk masu aikata abin da ba daidai ba.
6 Kakan hallaka masu yin ƙarya.
Masu kisankai da mutane masu ruɗu
Ubangiji yana ƙyama.
-
42 Yesu ya ce musu, “Da Allah ne Ubanku, da kun ƙaunace ni, gama daga Allah na fito yanzu kuma ga ni nan. Ban zo saboda kaina ba, amma shi ne ya aiko ni. 43 Me ya sa ba kwa gane da maganata? Don ba kwa iya jin abin da nake faɗi. 44 Ku na ubanku ne, Iblis, kuna kuwa so ku aikata abin da ubanku yake so. Shi mai kisankai ne tun farko. Ba ruwansa da gaskiya, gama gaskiya ba ta cikinsa. Yayinda yake ƙarya, yana yin halinsa ne, gama shi maƙaryaci ne, uban ƙarairayi kuma. 45 Amma domin ina faɗin gaskiya, ba kwa gaskata! 46 Akwai waninku da zai iya haƙaƙƙewa na taɓa yin zunubi? In kuwa gaskiya na faɗa, me ya sa ba kwa gaskata ni? 47 Wanda yake na Allah, yakan ji abin da Allah yake faɗi. Abin da ya sa ba kwa jin sa kuwa shi ne don ku ba na Allah ba ne.”
-
5 Saboda haka, sai ku fid da duk wani abin da yake kawo sha’awa a zukatanku, fasikanci, ƙazanta, sha’awa, muguwar sha’awa, da kuma kwaɗayi wanda shi ma bautar gumaka ne. 6 Gama fushin Allah zai sauko a kan masu aikata waɗannan. 7 Dā kun yi waɗannan abubuwa, sa’ad da rayuwar tana cikin duniya mai wannan hali. 8 Amma yanzu dole ku raba kanku da dukan ire-iren abubuwan nan. Ku daina fushi, ku daina ƙiyayya da ƙeta. Ku bar ɓatan suna da kuma ƙazamar magana daga leɓunanku. 9 Kada ku yi wa juna ƙarya, da yake kun tuɓe tsohon halinku tare da ayyukansa 10 kun ɗauki sabon halin nan da ake sabuntawa ga sani, bisa ga kamannin Mahaliccinsa.
-
1 To, maciji dai ya fi kowane a cikin namun jejin da Ubangiji Allah ya yi wayo. Ya ce wa macen, “Tabbatacce ne Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga kowane itace a lambu’?”
2 Macen ta ce wa macijin, “Za mu iya ci daga ’ya’ya itatuwa a lambun, 3 amma Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga ’ya’yan itacen da yake tsakiyar lambu, kada kuma ku taɓa shi, in ba haka ba kuwa za ku mutu.’ ”
4 Maciji ya ce wa macen, “Tabbatacce ba za ku mutu ba. 5 Gama Allah ya san cewa sa’ad da kuka ci daga itacen idanunku za su buɗe, za ku kuma zama kamar Allah, ku san abin da yake mai kyau da abin da yake mugu.”
-
10 Har yanzu zan manta, ya muguwar gida
da dukiyarki da kika samu a muguwar hanya
zan kuma manta da bugaggen mudun awo wanda ake zargi?
11 Zan kuɓutar da mutumin da yake da ma’auni na rashin gaskiya,
da kuma buhun ma’aunan ƙarya?
12 Attajiranta masu fitina ne;
mutanenta kuma maƙaryata ne
harsunansu kuwa suna yaudara.
13 Saboda haka, zan hallaka ku
in lalace ku saboda zunubanku.
-
22 sai ku tuɓe tsohon mutumin nan naku da kuma rayuwarku ta dā, wadda take lalacewa saboda sha’awace-sha’awacen da suke ruɗe ku. 23 A maimakon haka, bari Ruhu yă sabunta tunaninku da kuma halayenku. 24 Ku sanya sabon halin nan da aka halitta bisa ga kamannin Allah, halin nan kuwa, yă bayyana cikin adalci, da zaman tsarki.
25 Saboda haka dole kowannenku yă bar yin ƙarya, yă kuma riƙa faɗa wa maƙwabcinsa gaskiya, gama dukanmu gaɓoɓi jiki ɗaya ne.
-
12 Ku lura fa, ’yan’uwa, cewa kada waninku yă kasance da zuciya mai zunubi marar bangaskiya da takan juye daga bin Allah mai rai. 13 Sai dai ku ƙarfafa juna kullum, muddin akwai lokacin da ana ce da shi Yau, don kada waninku yă zama mai taurin zuciya ta wurin ruɗun zunubi.
-
20 Ya ci gaba, “Abin da yake fitowa daga mutum ne yake ƙazantar da shi. 21 Gama daga ciki, daga zuciyar mutane, mugayen tunani suke fitowa, fasikanci, sata, kisankai, zina, 22 kwaɗayi, ƙeta, ruɗu, ƙazantaccen sha’awa, kishi, ɓata suna, girman kai da kuma wauta. 23 Duk waɗannan mugayen abubuwa daga cikin suke fitowa, suna kuma ƙazantar da mutum.”
-
13 Kada ku kasance da ma’auni iri biyu a jakarku, ɗaya babba, ɗaya ƙarami. 14 Kada ku kasance da mudu iri biyu a jakarku, ɗaya babba, ɗaya ƙarami. 15 Dole ku kasance da ma’aunin da kuma mudun da yake daidai, kuma na gaskiya, saboda ku yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku. 16 Gama Ubangiji Allahnku yana ƙyamar duk mai yi waɗannan abubuwa, da kuma mai rashin gaskiya.
-
10 Gama,
“Duk wanda yake so yă ji daɗin rayuwa,
yă kuma ga kwanaki masu kyau
dole yă ƙame harshensa daga mugunta
leɓunansa kuma daga maganar yaudara.
11 Dole yă juye daga mugunta, ya aikata nagarta;
dole yă nemi salama yă kuma bi ta.
12 Gama idanun Ubangiji suna a kan masu adalci
kunnuwansa kuma suna jin addu’arsu,
amma fuskar Ubangiji tana gāba da masu mugunta.”
-
5 Wannan shi ne saƙon da muka ji daga wurinsa, muna kuma sanar da ku cewa Allah haske ne; a cikinsa kuwa babu duhu ko kaɗan. 6 In muka ce muna zumunci da shi amma muna tafiya cikin duhu, ƙarya muke yi, kuma ba ma rayuwa bisa ga gaskiya. 7 Amma in muna tafiya cikin haske, yadda yake cikin haske, muna da zumunci da juna ke nan, kuma jinin Yesu, Ɗansa, yana tsarkake mu daga dukan zunubi.
-
11 “ ‘Kada ku yi sata.
“ ‘Kada ku yi ƙarya.
“ ‘Kada ku ruɗe juna.
12 “ ‘Kada ku rantse bisa ƙarya da sunana, ta haka har ku ƙasƙantar da sunan Allahnku. Ni ne Ubangiji.
-
16 Akwai abubuwa shida da Ubangiji ya ƙi,
abubuwa bakwai da suke abin ƙyama gare shi,
17 duban reni,
harshe mai ƙarya,
hannuwa masu zub da jinin marar laifi,
18 zuciyar da take ƙulla mugayen dabaru,
ƙafafun da suke sauri zuwa aikata mugunta,
19 mai shaidar ƙarya wanda yake zuba ƙarairayi,
da kuma mutumin da yake tā-da-na-zaune-tsaye a cikin ’yan’uwa.
-
22 Ubangiji yana ƙyamar leɓunan masu ƙarya,
amma yana jin daɗin mutanen da suke masu gaskiya.
-
13 Gama irin waɗannan mutane manzannin ƙarya ne, ma’aikata ne masu ruɗi, sun ɓad da kamanni kamar su manzannin Kiristi ne. 14 Ba abin mamaki ba ne, gama Shaiɗan kansa ma yana ɓad da kamanni kamar shi mala’ikan haske ne. 15 Don haka, ba abin mamaki ba ne, in bayin Shaiɗan sun ɓad da kamanni kamar su bayin adalci ne. A ƙarshe, za a sāka musu gwargwadon ayyukansu.
-
16 Ba za ka ba da shaidar ƙarya a kan maƙwabcinka ba.
-
3 Ba zan kafa a gaban idanuna 1
wani abu marar kyau ba.
Na ƙi jinin ayyukan mutane marasa aminci;
ba za su manne mini ba.
4 Mutane masu mugun zuciya za su nesa da ni;
ba abin da zai haɗa ni da mugunta.
5 Duk wanda ya yi ɓatanci wa maƙwabcinsa a ɓoye
shi za a kashe;
duk mai renin wayo da mai girman kai,
ba zan jure masa ba.
6 Idanuna za su kasance a kan amintattu a cikin ƙasar,
don su zauna tare da ni;
tafiyarsa ba ta da zargi
zai yi mini hidima.
7 Babu mai ruɗun
da zai zauna a gidana;
babu mai ƙaryan
da zai tsaya a gabana.
8 Kowace safiya zan rufe bakunan
dukan mugaye a ƙasar;
zan yanke kowane mai aikata mugunta
daga birnin Ubangiji.
-
1 Saboda haka, ku rabu da kowace ƙeta da dukan ruɗu, munafunci, kishi, da kuma kowace irin ɓata suna. 2 Kamar sababbin jarirai, ku yi marmarin madara zalla ta ruhaniya, domin ta wurinta za ku yi girma cikin cetonku, 3 yanzu da kuka ɗanɗana alherin Ubangiji.
-
9 Mai shaidar ƙarya ba zai tafi babu hukunci ba,
kuma duk mai baza ƙarairayi zai hallaka.
-
8 Ku lura kada wani yă ruɗe ku da ilimin banza da wofi. Wannan koyarwa ta mutane ce kawai. Ta fito daga ikokin wannan duniya ne ba daga Kiristi ba.
-
8 Sa’an nan za a bayyana mai tawayen, Ubangiji Yesu kuwa zai hamɓare shi da numfashin bakinsa yă kuma hallaka shi da darajar dawowarsa. 9 Zuwan mai tawayen nan zai zama ta wurin aikin Shaiɗan da aka bayyana cikin kowane irin ayyukan banmamaki, alamu da abubuwan banmamaki na ƙarya, 10 da kuma cikin kowace irin muguntar da take ruɗin waɗanda suke hallaka. Sun hallaka ne domin sun ƙi su ƙaunaci gaskiya don su sami ceto. 11 Saboda haka Allah zai aiko musu da babban ruɗu don su gaskata ƙarya 12 don kuma a hukunta dukan waɗanda ba su gaskata gaskiyar ba sai dai suke jin daɗin mugunta.
-
2 “Na rantse da Allah mai rai, wanda ya danne mini gaskiyata,
Maɗaukaki, wanda ya sa nake cikin ɗacin rai.
3 Muddin ina da rai a cikina
kuma numfashin Allah yana cikin hancina,
4 bakina ba zai faɗi mugun abu ba,
harshena kuma ba zai yi ƙarya ba.
5 Ba zan taɓa yarda cewa kuna da gaskiya ba;
har in mutu, ba zan daina kāre mutuncina ba.
-
22 “Bai taɓa yin laifi ba sam,
ba a kuma sami ƙarya a bakinsa ba.”
-
8 Amma matsorata, da marasa bangaskiya, masu ƙazanta, masu kisankai, masu fasikanci, masu sihiri, masu bautar gumaka da dukan maƙaryata, wurinsu zai kasance a cikin tafkin wutar da yake farar wuta mai ci. Wannan fa ita ce mutuwa ta biyu.”
-
7 Bakinsa ya cika da zage-zage da ƙarairayi da kuma barazana;
wahala da mugunta suna a ƙarƙashin harshensa.
-
5 Shirye-shiryen masu adalci daidai ne,
amma shawarar mugaye ruɗu ne.
-
12 Labudda, duk masu niyyar zaman tsarkaka, suna na Kiristi Yesu, za su sha tsanani. 13 Mugayen mutane da masu ruɗi kuwa, ƙara muni za su riƙa yi, suna yaudara, ana kuma yaudararsu. 14 Amma kai kam, ka ci gaba da abin da ka koya ka kuma tabbatar, gama ka san waɗanda ka koye su daga gare su, 15 da kuma yadda tun kana ɗan jinjiri ka san Nassosi masu tsarki, waɗanda suke iya sa ka zama mai hikima zuwa ceto ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu.
-
14 Sai Ubangiji ya ce mini, “Annabawa suna ta annabcin ƙarya da sunana. Ban aike su ba, ban kuma naɗa su ba, ban yi musu magana ba. Suna muku annabci wahayin ƙarya, suna muku duba marar amfani, suna bautar gumaka suna kuma bayyana tunanin kansu ne. 15 Saboda haka, ga abin da Ubangiji ya ce game da annabawan da suke annabci da sunana. Ban aike su ba, duk da haka suna cewa, ‘Babu takobi ko yunwar da zai taɓa wannan ƙasa.’ Waɗannan annabawa takobi da yunwa za su hallaka su.
-
28 Da yake ba su yi tunani cewa ya dace su riƙe sanin Allah da suke da shi ba, sai ya yashe su ga tunanin banza da wofi, su aikata abin da bai kamata a yi ba. 29 Sun cika da kowace irin ƙeta, mugunta, kwaɗayi, da tunanin banza da wofi. Suka kuma cika da kishi, kisankai, faɗa, ruɗu, da kuma riƙo a zuci. Su masu gulma ne, 30 da masu ɓata suna, masu ƙin Allah, masu rashin kunya, masu girman kai, masu rigima; sukan ƙaga hanyoyin yin mugunta; suna rashin biyayya ga iyayensu; 31 su marasa hankali ne, marasa bangaskiya, marasa ƙauna, marasa tausayi. 32 Ko da yake sun san dokar adalcin Allah cewa masu aikata irin waɗannan abubuwa sun cancanci mutuwa, duk da haka ba cin gaba da aikata waɗannan abubuwa kaɗai suke yi ba, har ma suna goyon bayan masu yinsu.
-
2 Harshenka kan shirya hallaka;
yana nan kamar reza mai ci,
kana ta ruɗu.
3 Kana ƙaunar mugunta fiye da alheri,
ƙarya a maimakon faɗin gaskiya. Sela
4 Kana ƙaunar kowace kalmar cutarwa,
Ya kai harshe mai ruɗu!
5 Tabbatacce Allah zai kai ka ga madawwamiyar hallaka.
Zai fizge ka yă yayyage ka daga tentinka;
zai tumɓuke ka daga ƙasar masu rai. Sela
-
3 Sai dai ina tsoro kada yă zama, kamar yadda maciji ya yaudari Hawwa’u da makircinsa, ku ma a bauɗar da hankalinku daga sahihiyar biyayya amintacciya ga Kiristi.
-
20 Kada ka ba da shaidar ƙarya a kan maƙwabcinka.
-
35 Suna yin cikin rikici su kuma haifi mugunta;
cikinsu yana cike da ruɗami.”
-
3 Wa zai iya hawan tudun Ubangiji?
Wa zai iya tsaya a wurinsa mai tsarki?
4 Sai wanda yake da hannu mai tsabta da kuma tsabtar zuciya,
wanda ba ya ba da ransa ga bautar gunki
ko ya rantse bisa abin da yake ƙarya.
5 Zai sami albarka daga Ubangiji
da fiffitawa daga Allah Mai cetonsa.
-
12 Duk waninku da yake ƙaunar rayuwa
yana kuma so yă ga kwanaki masu kyau,
13 ka kiyaye harshenka daga mugunta
da kuma leɓunanku daga faɗar ƙarairayi.
-
3 Kalmomin bakinsa mugaye ne da kuma ruɗu;
ya daina zama mai hikima da yin alheri.
-
7 Ƙarar junanku ma da kuke yi, ai, kāsawa ce a gare ku. Ba gara ku haƙura a cuce ku ba? Ku kuma haƙura ko an zambace ku? 8 Amma ga shi ku da kanku kuna cuta, kuna kuma zamba, har ma ga ’yan’uwanku ne kuke yi wannan. 9 Ba ku sani ba cewa mugaye ba za su gāji mulkin Allah ba? Kada fa a ruɗe ku. Ba masu fasikanci ko masu bautar gumaka ko masu zina ko karuwan maza, ko ’yan daudu, 10 ko ɓarayi ko masu kwaɗayi ko mashaya ko masu ɓata suna ko masu zamba da za su gāji mulkin Allah. 11 Haka waɗansu a cikinku ma suke a dā. Amma an wanke ku, an tsarkake ku, aka kuma sa kuka zama marasa laifi cikin sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma ta wurin Ruhun Allahnmu.
-
11 Saboda haka Kiristi kansa ya ba wa waɗansu baiwa su zama manzanni, waɗansu su zama annabawa, waɗansu su zama masu wa’azi, waɗansu kuma su zama fastoci, da kuma malamai. 12 Ya yi haka don yă shirya mutanensa saboda ayyukan hidima, don a gina jikin Kiristi. 13 Wannan zai ci gaba har sai mun zama ɗaya a cikin bangaskiya da kuma ta wurin fahimtarmu na Ɗan Allah. Sa’an nan za mu zama balagaggu, kamar yadda Kiristi yake, mu kuma zama gaba ɗaya cikakku kamar sa.
14 An yi wannan kuwa don kada mu koma zama kamar yara, muna ta canja zukatanmu game da abin da muka gaskata don kawai wani ya faɗa mana wani abu dabam, ko domin wani ya yi wayo ya ruɗe mu, ya sa ƙarya ta zama kamar gaskiya.
-
2 Ka cece ni, ya Ubangiji,
daga leɓuna masu ƙarya
da kuma daga harsuna masu yaudara.
-
1 Ubangiji yana ƙyamar ma’aunan zamba,
amma ma’aunin da suke daidai ne abin farin cikinsa.
-
17 Mashaidin gaskiya kan ba da shaidar gaskiya,
amma mashaidin ƙarya yana baza ƙarairayi ne.
-
23 A lokacin in wani ya ce muku, ‘Duba, ga Kiristi nan!’ Ko, ‘Ga shi can!’ Kada ku gaskata. 24 Gama Kiristi masu yawa na ƙarya, da annabawan ƙarya za su firfito, su kuma aikata manyan alamu da ayyukan banmamaki don su ruɗi har da zaɓaɓɓu ma in zai yiwu. 25 Ga shi, na faɗa muku tun da wuri.
26 “Saboda haka in wani ya ce muku, ‘Ga shi can a hamada,’ kada ku fita; ko, ‘Ga shi nan a ɗakunan ciki,’ kada ku gaskata.
-
13 “Maƙogwaronsu kamar buɗaɗɗun kaburbura ne,
harsunansu suna yin ƙarya.”
“Dafin mugun maciji yana a leɓunansu.”
-
6 Kada wani yă ruɗe ku da kalmomin wofi, gama saboda waɗannan abubuwa ne fushin Allah yake zuwa a kan marasa biyayya. 7 Saboda haka kada ku haɗa kai da su.
-
14 amma akan jarrabce kowane mutum sa’ad da muguwar sha’awarsa ta janye shi ta kuma rinjaye shi. 15 Sa’an nan, bayan da sha’awar ta yi ciki, takan haifi zunubi; zunubi kuwa, sa’ad da ya balaga yakan haifi mutuwa.
16 Kada a ruɗe ku, ’yan’uwana ƙaunatattu. 17 Kowane abu mai kyau da kuma kowace cikakkiyar kyauta daga sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.
-
1 Amma a dā akwai annabawan ƙarya a cikin mutane, kamar yadda za a sami malaman ƙarya a cikinku. A ɓoye za su shigar da karkataccen koyarwa mai hallaka, har ma su yi mūsun Ubangiji mai iko duka wanda ya saye su suna kawo wa kansu hallaka farat ɗaya. 2 Da yawa za su bi hanyoyinsu na rashin kunya su kuma sa a rena hanyar gaskiya. 3 Cikin kwaɗayinsu waɗannan malaman ƙarya za su cuce ku da tatsuniyoyin da suka ƙaga. Hukuncinsu yana a rataye a kansu tun da daɗewa, hallakarsu kuma ba ta barci.
-
10 To, a lokacin, an yi yunwa a ƙasar, sai Abram ya gangara zuwa Masar don yă zauna a can na ɗan lokaci, domin yunwa ta yi tsanani. 11 Yayinda yana gab da shiga Masar, sai ya ce wa matarsa Saira, “Na sani ke kyakkyawar mace ce. 12 Sa’ad da Masarawa suka ganki, za su ce, ‘Wannan matarsa ce.’ Za su kuwa kashe ni, su bar ki da rai. 13 Saboda haka ki ce ke ’yar’uwata ce, domin ta dalilinki a mutunta ni, a kuma bar ni da rai.”
-
20 Ba sa maganar salama
sukan ƙirƙiro zage-zagen ƙarya
a kan waɗanda suka zama shiru a ƙasar.
-
1 Ka nuna ni marar laifi ne, ya Allah,
ka kuma nemi hakkina
a kan al’ummai marasa sanin Allah.
Ka kuɓutar da ni daga
masu ruɗu da mugayen mutane.
-
28 Kada ka ba da shaida a kan maƙwabcinka ba tare da isashen dalili ba,
ko ka yi amfani da leɓunanka ka yi ruɗu.
-
6 Wahayoyinsu ƙarya ne suna yin dubansu na ƙarya ne. Sukan ce, Ubangiji ya furta, alhali kuwa Ubangiji bai aike su ba; duk da haka sukan sa zuciya ga cikawar maganarsu. 7 Ba ku ga wahayin ƙarya kuka kuma faɗa yin duban ƙarya sa’ad da kuka ce, “Ubangiji ya furta,” ko da yake bai yi magana ba?
8 “ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa saboda maganganunku na ƙarya da wahayinku na ƙarya, ina gāba da ku, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. 9 Hannuna zai yi gāba da annabawan da suke ganin wahayin ƙarya suna kuma yin duban ƙarya. Ba za su kasance cikin taron mutanena ba, ba kuwa za a rubuta su a littafin gidan Isra’ila ba, ba za su shiga ƙasar Isra’ila ba. Ta haka za ku san cewa ni ne Ubangiji Mai Iko Duka.
-
2 Ba ruwanmu da ɓoye-ɓoye na munafuncin da suke abubuwan kunya. Ba ruwanmu da ruɗu, ko yin ƙarya da kalmar Allah. Sai dai muna faɗin gaskiya a fili. Ta haka ne kowa zai yi shaidar gaskiyarmu a gaban Allah cikin zuciyarsa.
-
11 Ya kamata mace ta riƙa koyo cikin natsuwa da cikakkiyar biyayya. 12 Ban ba mace izini ta koyar ko tă yi mulki a kan namiji ba; sai dai ta zauna shiru. 13 Gama Adamu ne aka fara halitta, sa’an nan Hawwa’u. 14 Ba kuma Adamu ne aka yaudara ba; macen ce aka yaudara ta kuma zama mai zunubi.
-
10 In muka ce ba mu yi zunubi ba, mun mai da shi maƙaryaci ke nan, maganarsa kuwa ba ta da wuri a cikinmu.
-
11 Sai na ga wata dabba tana fitowa daga ƙasa. Tana da ƙahoni biyu kamar ɗan rago, amma ta yi magana kamar maciji. 12 Ta mori dukan ikon dabban nan ta fari a madadinta, ta sa duniya da mazaunanta su yi wa dabba ta farin nan sujada, wadda aka warkar mata da raunin nan da zai iya kashe ta. 13 Ta kuma yi manyan ayyuka da kuma alamu masu banmamaki, har ta sa wuta ta sauko daga sama zuwa ƙasa a gaban idon mutane. 14 Saboda alamun nan da aka ba ta iko tă yi a madadin dabban nan ta fari, sai ta ruɗi mazaunan duniya. Ta umarce su su kafa siffa don girmama dabbar da aka ji mata rauni da takobi duk da haka ta rayu. 15 Aka ba ta iko tă ba da numfashi ga siffar dabban nan ta fari, don tă yi magana tă kuma sa a kashe duk waɗanda suka ƙi yi wa siffar sujada.
-
27 Babu wani abu marar tsarkin da zai taɓa shiga cikin birnin, babu kuma wani mai aikata abin kunya ko ruɗi da zai shiga, sai dai waɗanda aka rubuta sunayensu a cikin littafin rai na Ɗan Ragon.
-
14 “Masu albarka ne waɗanda suka wanke tufafinsu, don su sami izinin ci daga itacen rai su kuma shiga birnin ta ƙofofi. 15 Waɗanda suke waje kuwa karnuka ne, masu sihiri, masu fasikanci, masu kisankai, masu bautar gumaka, da duk wanda yake ƙaunar ƙarya yake kuma aikata ta.
-
6 Kun san cewa na yi aiki wa mahaifinku da dukan ƙarfina, 7 duk da haka mahaifinku ya cuce ni ta wurin sauya albashina sau goma. Amma dai, Allah bai yardar masa yă yi mini lahani ba. 8 In ya ce, ‘Dabbare-dabbare ne za su zama ladanka,’ sai dukan garkunan su haifi dabbare-dabbare, in kuma ya ce, ‘Masu zāne-zāne ne za su zama ladanka,’ sai dukan garkunan su haifi ƙananan masu zāne-zāne. 9 Ta haka Allah ya kwashe dabbobin mahaifinku ya ba ni.
-
35 “ ‘Kada ku yi amfani da mudun ƙarya sa’ad da kuke awon tsawo, nauyi, ko yawan abu. 36 Ku yi amfani da ma’auni na gaskiya da mudu na gaskiya, da kuma magwaji na gaskiya. Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar.
-
22 Gehazi ya amsa ya ce, “Lafiya ƙalau. Maigidana ne ya aiko ni cewa, ‘Samari biyu daga ƙungiyar annabawa sun ziyarce ni daga ƙasa mai duwatsu na yankin Efraim. Ina roƙonka ka ba su talenti na azurfa da tufafi kashi biyu.’ ”
23 Na’aman ya ce, “Ba damuwa, karɓi talenti biyu.” Ya roƙi Gehazi yă karɓa, sa’an nan ya ƙunsa masa talentin biyu na azurfa ya sa masa a kan jakankuna biyu, ya haɗa da tufafi kashi biyu, ya ba bayinsa biyu suka ɗauka, ya ce su sha gaban Gehazi. 24 Da Gehazi ya isa wani tudu, sai ya karɓi kayan daga wurin bayin ya shiga da su a ɓoye a cikin gida. Sa’an nan ya sallami mutanen suka tafi. 25 Sa’an nan ya shiga ya tsaya a gaban maigidansa Elisha.
Sai Elisha ya tambaye shi ya ce, “Ina ka je, Gehazi?”
Sai Gehazi ya amsa ya ce, “Bawanka bai je ko’ina ba.”
26 Amma Elisha ya ce masa, “Ashe, ba ina tare da kai a ruhu ba sa’ad da mutumin ya sauko daga keken yaƙinsa ya tarye ka. Kana gani wannan lokaci ne da za a karɓi kuɗi, da riguna, da gonar inabi, da tumaki, da bijimai, da bayi maza da mata? 27 Kuturtar Na’aman zai manne maka da zuriyarka har abada.” Sai Gehazi ya fita daga gaban Elisha a kuturce, fari fat kamar dusar ƙanƙara.
-
2 Mai farin ciki ne mutumin
da Ubangiji ba ya lissafin zunubinsa a kansa
wanda kuma babu ruɗu a ruhunsa.
-
5 Mashaidi na gaskiya ba ya ruɗu,
amma mashaidin ƙarya kan baza ƙarairayi.
-
25 Mashaidin gaskiya kan ceci rayuka,
amma mashaidin ƙarya mai ruɗu ne.
-
9 Aka yi jana’izarsa tare da mugaye,
aka binne shi tare da masu arziki,
ko da yake bai taɓa yin wani tashin hankali ba,
ko a sami ƙarya a bakinsa.
-
13 “Kaiton wanda ya gina gidansa ta hanyar rashin adalci,
ɗakunansa na sama kuma ta hanyar rashin gaskiya,
yana sa mutanen ƙasarsa suna aiki a banza
ba ya biyansu wahalarsu.
-
12 Mutanen Efraim sun kewaye ni da ƙarairayi,
gidan Isra’ila da ruɗu.
Mutanen Yahuda kuma suna yi wa Allah ƙin ji,
har ma a kan Mai Tsarkin nan mai aminci.
-
7 Ɗan kasuwa yana amfani da mudu marar gaskiya;
yana jin daɗin cuta.
8 Efraim yana fariya yana cewa,
“Ni mai arziki ne ƙwarai; na azurta.
Da dukan wadatata ba za a sami
wani laifi ko zunubi a gare ni ba.”
-
1 Kaiton birni mai zub da jini,
wadda take cike da ƙarairayi,
cike da ganima,
wadda ba a rasa masu fāɗawa cikin wahala!
-
18 Kada ku ruɗi kanku. In waninku yana tsammani cewa yana da hikima, yadda duniya ta ɗauki hikima, to, sai ya mai da kansa “wawa” don yă zama mai hikima. 19 Gama hikimar duniyan nan, wauta ce a gaban Allah, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yakan kama masu hikima a cikin makircinsu”;
-
4 Ga shi! Zaluncin da kuka yi na hakkin ma’aikatan gonakinku yana ta ƙara. Kukan masu girbi ya kai kunnuwan Ubangiji Maɗaukaki.
-
13 Sai Ubangiji Allah ya ce wa matar, “Me ke nan kika yi?”
Matar ta ce, “Macijin ne ya ruɗe ni, na kuwa ci.”
-
6 Sai Ishaku ya zauna a Gerar.
7 Sa’ad da mutanen wurin suka tambaye shi game da matarsa, sai ya ce, “’Yar’uwata ce,” gama yana tsoro yă ce, “Ita matata ce.” Ya yi tunani, “Mutane wannan wuri za su kashe ni ta dalili Rebeka, domin kyakkyawa ce.”
-
18 Shi kuwa ya tafi wurin mahaifinsa ya ce, “Babana.”
Shi kuma ya amsa “I, ɗana, wane ne?”
19 Yaƙub ya ce wa mahaifinsa, “Ni ne Isuwa ɗan farinka. Na yi yadda ka faɗa mini. Ina roƙonka tashi ka zauna ka ci naman, domin ka sa mini albarkarka.”
-
1 Ubangiji ya ce wa Musa, 2 “In wani ya yi zunubi bai kuma yi aminci ga Ubangiji ba, wato, ta wurin yin wa abokin zamansa karya game da ajiyar da abokin ya ba shi amana, ko a kan wani alkawarin da suka yi wa juna, ko kuwa a kan yă cuci abokin, 3 ko kuma idan ya sami abin da ya ɓace amma ya yi ƙarya cewa bai samu ba. Ko ya yi rantsuwar ƙarya a kan duk irin abubuwan da akan aikata na laifi, 4 sa’ad da mutum ya yi irin laifin nan, ya kuwa tabbata mai laifi ne, to, sai yă komar da abin da ya ƙwace, ko abin da ya samu ta hanyar zalunci, ko abin da aka ba shi ajiya, ko abin da ya tsinta. 5 Zai mai da abin da ya yi rantsuwar ƙarya a kai. Zai mayar wa mai abin da abinsa a yadda yake, har yă ƙara kashi ashirin bisa ɗari na abin. A ranar da zai yi hadaya don laifinsa, a ranar ce zai mayar wa mai abin da abinsa.
-
19 Allah ba mutum ba ne, da zai yi ƙarya,
shi ba ɗan mutum ba ne, da zai canja tunaninsa.
Yana maganar abin da ba zai iya aikata ba ne?
Yakan kuma yi alkawarin da ba zai iya cikawa ba?
-
12 Waɗanda suke neman raina sun sa tarkonsu,
waɗanda suke so su cuce ni suna zance lalatar da ni;
yini sukutum suna ƙulla mini maƙarƙashiya.
-
118 Ka ki dukan waɗanda suka kauce daga ƙa’idodinka,
gama yaudararsu banza ne.
-
8 Hikima masu la’akari shi ne su yi tunani a kan hanyoyinsu,
amma wautar wawaye ruɗu ne.
-
6 Dukiyar da aka samu ta wurin harshe mai yin ƙarya
tarin tururi ne da kuma mugun tarko.
-
18 Amma abubuwan da suke fitowa ta baki suna fitowa ne daga zuciya, su ne kuma suke ƙazantar da mutum. 19 Gama daga zuciya ne mugayen tunani, kisankai, zina, fasikanci, sata, shaidar ƙarya, ɓatan suna, suka fitowa.
-
20 Ka san dokokin da suka ce, ‘Kada ka yi zina, kada ka yi kisankai, kada ka yi sata, kada ka ba da shaida ta ƙarya, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’ ”
-
8 Amma Zakka ya tashi a tsaye, ya ce wa Ubangiji, “Duba, Ubangiji! Nan take, rabin dukiyar da nake da shi, na ba wa matalauta. In kuma na taɓa cutan wani, a kan wani abu, zan mayar da shi ninki huɗu.”
-
12 Ta haka suka tā da hankalin mutane da dattawa da kuma malaman dokoki. Suka kama Istifanus suka kawo shi a gaban Majalisa. 13 Suka kawo masu ba da shaidar ƙarya, waɗanda suka ba da shaida cewa, “Wannan mutum ba ya rabuwa da maganar banza a kan wurin nan mai tsarki da kuma doka. 14 Gama mun ji shi yana cewa wannan Yesu Banazare zai rushe wurin nan ya kuma canja al’adun da Musa ya ba mu.”
-
7 Kada a ruɗe ku. Ba a yi wa Allah ba’a. Mutum yakan girbe abin da ya shuka ne. 8 Wanda ya yi shuki don yă gamshi mutuntakarsa, daga wannan mutuntaka zai girbi hallaka. Wanda ya yi shuki domin yă gamshi Ruhu, daga Ruhu zai girbi rai madawwami.
-
8 In muka ce ba mu da zunubi, muna ruɗin kanmu ne, gaskiya kuwa ba ta cikinmu.
-
7 Masu ruɗi da yawa, waɗanda ba su yarda da zuwan Yesu Kiristi cikin jiki ba, sun riga sun fito a duniya. Duk irin mutumin nan mai ruɗi ne kuma magabcin Kiristi.
-
31 Sai suka ɗauki rigar Yusuf, suka yanka akuya suka tsoma rigar a cikin jinin. 32 Suka ɗauki rigan nan mai gwanin kyau, suka kawo wa mahaifinsu suka ce, “Mun sami wannan. Ka bincika shi ka gani ko rigar ɗanka ne.”
33 Ya gane shi, sai ya ce, “Rigar ɗana ne! Waɗansu mugayen namun jeji sun cinye shi. Tabbatacce an yayyaga Yusuf.”
34 Sa’an nan Yaƙub ya kyakkece tufafinsa, ya sa tufafin makoki, ya kuma yi makoki domin ɗansa kwanaki masu yawa. 35 Dukan ’ya’yansa maza da mata, suka zo don su ta’azantar da shi, amma ya ƙi yă ta’azantu. Ya ce, “A’a, cikin makoki zan gangara zuwa kabari wurin ɗana.” Saboda haka, mahaifin Yusuf ya yi kuka saboda shi.
-
20 A ƙarshe, wani ruhu ya zo gaba, ya tsaya a gaban Ubangiji ya ce, ‘Zan ruɗe shi.’
“Ubangiji ya yi tambaya, ‘Ta wace hanya?’
21 “Ya ce, ‘Zan tafi in zama ruhun ƙarya a bakunan dukan annabawansa.’
“Ubangiji ya ce, ‘Za ka yi nasara a ruɗinsa. Ka tafi, ka yi haka.’
22 “To yanzu, Ubangiji ya sa ruhun ruɗu a bakunan waɗannan annabawanka. Ubangiji ya ƙayyade masifa dominka.”
-
18 Mugun mutum kan sami albashin ƙarya
amma shi da ya shuka adalci zai girbe lada tabbatacce.
-
19 Leɓunan gaskiya kan dawwama har abada,
amma harshen ƙarya yakan dawwama na ɗan lokaci ne kawai.
20 Akwai ruɗu a zukatan waɗanda suke ƙulla mugunta,
amma waɗanda suke aikata alheri za su yi farin ciki.
-
27 Kamar keji cike da tsuntsaye,
gidajensu sun cika da ruɗu;
sun yi arziki suka kuma zama masu iko
28 suka kuma yi ƙiba, suka yi bul-bul.
Mugayen ayyukansu ba su da iyaka;
ba sa wa marayu shari’ar adalci,
ba sa kāre ’yancin matalauta.
-
1 To wani mutum mai suna Ananiyas tare da matarsa Saffiratu, shi ma ya sayar da wata mallakarsa. 2 Da cikakken sanin matarsa ya ajiye sashi daga cikin kuɗin don kansa, ya kuma kawo sauran ya ajiye a sawun manzanni.
3 Sai Bitrus ya ce, “Ananiyas, ta yaya Shaiɗan ya cika zuciyarka haka da ka yi wa Ruhu Mai Tsarki ƙarya ka kuma ajiye wa kanka sauran kuɗin da ka karɓa na filin? 4 Ba naka ba ne kafin ka sayar da shi? Bayan da ka sayar da shi kuma, kuɗin ba naka ba ne? Me ya sa ka yi tunanin yin irin wannan abu? Ba mutum ne ka yi wa ƙarya ba, Allah ne ka yi masa.”
-
9 Aka jefar da ƙaton jan macijin ƙasa, tsohon maciji nan da ake kira Iblis, ko Shaiɗan, wanda ya ɓad da dukan duniya. Aka jefar da shi ƙasa, tare da mala’ikunsa a duniya.
-
7 Sa’ad da shekaru dubun nan suka cika, za a saki Shaiɗan daga kurkukun da yake, 8 zai kuma fito don yă ruɗi al’ummai da suke a kursuyoyi huɗu na duniya, Gog da Magog, yă tattara su don yaƙi. Yawansu kuwa ya yi kamar yashi a bakin teku. 9 Suka mamaye duk fāɗin duniya suka kuma kewaye sansanin mutanen Allah, birnin da yake ƙauna. Amma wuta ta fito daga sama ta cinye su. 10 Aka jefa Iblis da ya ruɗe su cikin tafkin farar wuta, inda aka jefa dabban nan da annabin ƙaryan nan. Za a ba su azaba dare da rana har abada abadin.
Shows Read in context, Share and Copy.