62 Bible Verses About Suffering
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
21 Tun daga wannan lokaci Yesu ya fara bayyana wa almajiransa cewa dole yă tafi Urushalima yă sha wahaloli da yawa a hannun dattawa, manyan firistoci da kuma malaman dokoki, dole a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.
22 Bitrus ya ja shi gefe ya fara tsawata masa yana cewa, “Sam, Ubangiji! Wannan ba zai taɓa faruwa da kai ba!”
23 Yesu ya juya ya ce wa Bitrus, “Rabu da ni, Shaiɗan! Kai abin sa tuntuɓe ne a gare ni; ba ka tunanin al’amuran Allah, sai dai al’amuran mutane.”
24 Sa’an nan Yesu ya ce wa almajiransa, “Duk mai son bina, dole yă ƙi kansa, yă ɗauki gicciyensa, yă bi ni. 25 Gama duk mai son ceton ransa zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni, zai same shi.
-
18 “In duniya ta ƙi ku, ku san cewa ta fara ƙin na ne. 19 Da ku na duniya ne, da ta ƙaunaci abinta. Kamar yadda yake, ku ba na duniya ba ne, na zaɓe ku daga duniya, shi ya sa duniya take ƙinku. 20 Ku tuna da kalmomin da na yi muku cewa, ‘Ba bawan da ya fi maigidansa,’ In sun tsananta mini, ku ma za su tsananta muku. Da sun yi biyayya da koyarwata, da za su yi biyayya da taku ma.
-
13 Wata rana lokacin da ’ya’yan Ayuba suke cikin biki a gidan babban ɗansa, 14 sai ɗan aika ya zo wurin Ayuba ya ce masa, “Shanu suna huɗa, jakuna kuma suna kiwo nan kusa, 15 sai Sabenawa suka auka musu suka kwashe su suka tafi, suka karkashe masu yi maka aiki duka, ni kaɗai na tsira na zo in gaya maka!”
16 Yana cikin magana sai ga wani ɗan aika ya zo ya ce, “Wutar Allah ta sauko daga sama ta ƙona dukan tumaki da masu lura da su, wato, bayinka, ni kaɗai na tsira na zo in gaya maka!”
17 Yana cikin magana sai ga wani ɗan aika ya zo ya ce, “Ƙungiyoyin mahara uku na Kaldiyawa sun auka wa raƙumanka sun kwashe su duka, suka kuma karkashe masu yi maka aiki, ni kaɗai ne na tsira na zo in gaya maka!”
18 Yana cikin magana, sai ga wani ɗan aika ya zo ya ce, “’Ya’yanka maza da mata suna biki, suna ci suna sha a gidan babban ɗanka, 19 sai wata iska mai ƙarfi daga hamada ta auka ta rushe gidan, gidan kuwa ya fāɗi a kan ’ya’yanka ya kashe su, ni kaɗai na tsira na zo in gaya maka!”
20 Da jin haka sai Ayuba ya tashi ya yayyaga tufafin jikinsa, ya aske kansa. Ya fāɗi a ƙasa ya yi sujada 21 ya ce,
“Tsirara na fito daga cikin mahaifiyata,
tsirara kuma zan koma.
Ubangiji ya bayar, Ubangiji kuma ya karɓa;
yabo ya tabbata ga Ubangiji.”
22 Cikin wannan duka Ayuba bai yi wa Allah zunubi ta wurin ba shi laifi ba.
-
16 Ruhu kansa yana ba da shaida tare da ruhunmu cewa mu ’ya’yan Allah ne. 17 In kuwa mu ’ya’ya ne, to, mu magāda ne, magādan Allah da kuma abokan gādo tare da Kiristi, in kuwa muna tarayya a cikin shan wuyarsa to, za mu yi tarayya a cikin ɗaukakarsa.
18 A ganina, wuyar da muke sha a wannan lokaci ba su isa a kwatanta da ɗaukakar da za a bayyana a cikinmu ba. 19 Halitta tana jira da marmari ta ƙosa ta ga bayyanuwar ’ya’yan Allah. 20 Gama an sa halitta a cikin wulaƙanci, ba da son ta ba, sai dai ta wurin nufin wannan da ya mai da ita haka, da bege 21 cewa za a ’yantar da halitta kanta daga bautarta ga ruɓewa a kuma kawo ta cikin ’yancin ɗaukakar ’ya’yan Allah.
22 Mun san cewa dukan halitta tana nishi sai ka ce mace mai naƙuda har yă zuwa wannan lokaci. 23 Ba haka kaɗai ba ma, mu kanmu da muke da nunan fari na Ruhu, muna nishi a ciki-cikinmu yayinda muke jira da marmari a maishe mu ’ya’yan riƙo na Allah, fansar jikunanmu.
-
3 Yabo ya tabbata ga Allah, da Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba mai tausayi, da kuma Allah na dukan ta’aziyya, 4 wanda yakan yi mana ta’aziyya a cikin dukan wahalolinmu, domin mu kuma mu iya ta’azantar da waɗanda suke cikin kowace irin wahala, da ta’aziyyar da mu kanmu muka samu daga Allah. 5 Gama kamar yadda wahalar Kiristi ta cika har tana zuba a cikin rayuwarmu, haka nan kuma ta wurin Kiristi ta’aziyyarmu ta cika har tana zuba. 6 In muna shan wahala, ai, muna shanta domin ta’aziyyarku, da cetonku ne, in mun sami ta’aziyya, ai, mun same ta domin ta’aziyyarku ce, wadda take sa ku jure wa irin wahalan nan, da muke sha. 7 Begen da muke da shi dominku kuwa, tabbatacce ne, domin mun san cewa kamar yadda kuke tarayya da mu a cikin wahalolinmu, haka kuma kuke tarayya da mu a cikin ta’aziyyarmu.
8 ’Yan’uwa, ba ma so ku zama da rashin sani, a kan wahalolin da muka sha a lardin Asiya. Mun sha wahaloli sosai, har abin ya fi ƙarfinmu, ya sa muka fid da tsammanin rayuwa. 9 Ba shakka, a zuciyarmu mun ji kamar hukuncin kisa ne aka yi mana. Wannan kuwa ya faru ne domin kada mu dogara da kanmu, sai dai ga Allah, wanda yake tā da matattu. 10 Shi ya cece mu daga irin wannan hatsari na mutuwa, zai kuwa cece mu. A kansa muka kafa bege cewa zai ci gaba da cetonmu, 11 yayinda kuke taimakonmu ta wurin addu’o’inku. Mutane da yawa kuwa za su yi godiya ta dalilinmu, saboda albarkar da aka yi mana, ta amsa addu’o’i masu yawa.
-
3 Ba haka kawai ba, amma muna kuma da farin ciki cikin shan wuyanmu, gama mun san cewa shan wuyan nan takan haifi jimiri; 4 jimiri kuma yakan kawo hali mai kyau; hali mai kyau kuma yakan sa bege. 5 Bege kuwa ba ya ba mu kunya, domin Allah ya zuba ƙaunarsa a zukatanmu ta wurin Ruhu Mai Tsarkin da ya ba mu.
6 Kun ga, a daidai lokaci, yayinda muke marasa ƙarfi, Kiristi ya mutu saboda waɗanda ba su san Allah ba. 7 Da ƙyar wani yă mutu saboda mai adalci, ko da yake saboda mutumin kirki wani zai iya ƙarfin hali yă mutu. 8 Amma Allah ya nuna mana ƙaunarsa a wannan. Tun muna masu zunubi tukuna, Kiristi ya mutu dominmu.
-
18 Bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku da matuƙar ladabi, ba kawai ga waɗanda suke da kirki da masu sauƙinkai ba, amma har ga masu zafin rai ma. 19 Gama abin yabo ne in mutum ya yi haƙuri cikin zafin wahalar rashin adalci saboda yana sane da Allah. 20 Amma ina abin taƙama in kuka sha duka saboda kun yi laifi kuka kuma jimre? Sai dai in kuka sha wahala saboda yin nagari kuka kuma jimre, abin yabo ne a gaban Allah. 21 Ga wannan ne aka kira ku, domin Kiristi ya sha wahala dominku, ya bar muku gurbin da ya kamata ku bi.
22 “Bai taɓa yin laifi ba sam,
ba a kuma sami ƙarya a bakinsa ba.”
23 Sa’ad da suka zazzage shi, bai rama ba; sa’ad da ya sha wahala, bai yi barazana ba. A maimakon haka, ya miƙa kansa ga wanda yake shari’ar adalci.
-
12 Abokaina ƙaunatattu, kada ku yi mamakin gwaji mai tsananin da kuke sha, sai ka ce wani baƙon abu ne yake faruwa da ku. 13 Sai dai ku yi murna cewa kuna tarayya cikin shan wahalolin Kiristi, domin ku kai ga farin ciki mai yawa sa’ad da aka bayyana ɗaukakarsa. 14 In an zage ku saboda sunan Kiristi, ku masu albarka ne, gama Ruhun ɗaukaka da kuma na Allah yana bisanku. 15 In kuna shan wahala, kada yă zama don ku masu kisankai ne ko ɓarayi ko masu wani irin laifi ko kuma masu shisshigi. 16 Amma fa, in kuka sha wahala a matsayin ku Kirista ne, kada ku ji kunya, sai dai ku yabi Allah cewa kuna amsa wannan suna.
-
3 Mutane suka rena shi suka ƙi shi,
mutum ne cike da baƙin ciki, ya kuma saba da wahala.
Kamar wanda mutane suna ɓuya fuskokinsu daga gare shi
aka rena shi aka yi banza da shi.
4 Tabbatacce ya ɗauki cututtukanmu
ya kuma daure da baƙin cikinmu
duk da haka muka ɗauka Allah ya hukunta shi ne,
ya buge shi ya kuma sa ya sha azaba.
5 Amma aka yi masa rauni saboda laifofinmu,
aka ƙuje shi saboda kurakuranmu;
hukuncin da ya kawo mana salama ya kasance a kansa,
kuma ta wurin mikinsa ya sa muka warke.
6 Dukanmu, muna kama da tumakin da suka ɓata,
kowannenmu ya kama hanyarsa;
Ubangiji kuwa ya sa hukunci ya auko a kansa
hukuncin da ya wajaba a kanmu.
-
2 Ku ɗauki wannan da farin ciki mai tsabta, ’yan’uwana, duk sa’ad da gwaje-gwaje na kowane iri suka zo muku, 3 domin kun san cewa gwajin bangaskiyarku yakan haifi daurewa. 4 Dole daurewa ta kammala aikinta don ku zama balagaggu da kuma cikakku, ba ku kuma rasa kome ba.
-
7 Amma abin da dā ya zama mini riba yanzu, na ɗauka hasara ce saboda Kiristi. 8 Me kuma ya fi, na ɗauki dukan abubuwa hasara ne in aka kwatanta da mafificiyar girman sanin Kiristi Yesu Ubangijina, wanda saboda shi ne na yi hasarar kome. Na mai da su kayan wofi, domin in sami Kiristi 9 a kuma same ni a cikinsa, ba da wani adalcin kaina wanda yake zuwa daga bin doka ba, sai dai adalcin da yake samuwa ta wurin bangaskiya a cikin Kiristi, adalcin da yake fitowa daga Allah da kuma yake zuwa ta wurin bangaskiya. 10 Ina so in san Kiristi da ikon tashinsa daga matattu da kuma zumuncin tarayya cikin shan wahalarsa, in kuma zama kamar sa a cikin mutuwarsa, 11 yadda kuma ko ta yaya, in kai ga tashin nan daga matattu.
-
8 Ku zama masu kamunkai, ku kuma zauna a faɗake. Abokin gābanku, Iblis yana kewayewa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai cinye. 9 Ku yi tsayayya da shi, kuna tsayawa daram cikin bangaskiya, domin kun san cewa ’yan’uwanku ko’ina a duniya suna shan irin wahalolin nan.
10 Allah mai dukan alheri, wanda ya kira ku ga madawwamiyar ɗaukaka cikin Kiristi, bayan kun sha wahala na ɗan lokaci, shi da kansa zai raya ku, yă kuma sa ku yi ƙarfi, ku kahu, ku kuma tsaya daram. 11 Gare shi bari iko yă tabbata har abada abadin. Amin.
12 Da taimakon Sila, wanda na ɗauka a matsayin ɗan’uwa mai aminci, na rubuta muku a taƙaice, ina ƙarfafa ku ina kuma shaida muku cewa wannan shi ne alherin Allah na gaske. Ku tsaya daram a cikinsa.
-
1 Saboda haka, da yake muna kewaye da irin wannan taron shaidu mai girma, sai mu yar da duk abin da yake hana mu da kuma zunubin da yake saurin daure mu, mu kuma yi tseren da aka sa a gabanmu da nacewa. 2 Bari mu kafa idanunmu a kan Yesu, tushe da kuma kammalar bangaskiyarmu, wanda ya jure kunyar gicciye da aka yi masa, domin ya san cewa daga baya zai yi farin ciki ya yi haka. Yanzu kuma yana zaune a hannun dama na kursiyin Allah. 3 Ku lura da wannan wanda ya jure da irin hamayyan nan daga masu zunubi, don kada ku gaji, har ku fid da zuciya.
4 Cikin famanku da zunubi, ba ku yi tsayayya har ga zub da jininku ba tukuna.
-
1 Sa’an nan na ga sabon sama da sabuwar duniya, gama sama na farko da duniya ta farko sun shuɗe, babu kuma wani teku. 2 Na ga Birni Mai Tsarki, sabuwar Urushalima tana saukowa daga sama, daga Allah, a shirye kamar amaryar da aka yi mata ado mai kyau saboda mijinta. 3 Na kuma ji wata babbar murya daga kursiyin tana cewa, “Yanzu mazaunin Allah yana tare da mutane, zai kuma zauna tare da su. Za su zama mutanensa, Allah kansa kuwa zai kasance tare da su yă kuma zama Allahnsu. 4 Zai share dukan hawaye daga idanunsu. Ba sauran mutuwa ko makoki ko kuka ko azaba, gama tsofaffin al’amura sun shuɗe.”
-
1 Da Yesu yana tafiya, sai ya ga wani mutum wanda aka haifa makaho. 2 Sai almajiransa suka tambaye shi suka ce, “Rabbi, wane ne ya yi zunubi, mutumin ne, ko iyayensa, da ya sa aka haife shi makaho?”
3 Sai Yesu ya ce, “Ba don mutumin ko iyayensa sun yi zunubi ne ba, sai dai don a bayyana aikin Allah ne a rayuwarsa.
-
27 Kome ya faru, ku yi zaman da ya cancanci bisharar Kiristi. Ta haka, ko na zo na gan ku, ko ban zo ba, in ji labari cewa kun tsaya da ƙarfi a cikin ruhu ɗaya, kuna fama kamar mutum ɗaya saboda bangaskiyar bishara 28 ba tare da kun ji tsoron waɗanda suke gāba da ku ta kowace hanya ba. Wannan alama ce a gare su cewa za a hallaka su, amma a gare ku za a cece ku, wannan tabbacin kuwa daga wurin Allah ne. 29 Gama an ba ku zarafi a madadin Kiristi cewa ba gaskatawa da shi kaɗai ba kuka yi ba, har ma ku sha wahala dominsa, 30 da yake kuna shan faman da kuka gan na sha, kuna kuma jin cewa har yanzu ina sha.
-
12 Gama idanun Ubangiji suna a kan masu adalci
kunnuwansa kuma suna jin addu’arsu,
amma fuskar Ubangiji tana gāba da masu mugunta.”
13 Wa zai yi muku lahani in kun himmantu ga yin nagarta? 14 Amma ko da za ku sha wahala saboda abin da yake daidai, ku masu albarka ne. “Kada ku ji tsoron abin da suke tsoro; kada kuma ku firgita.” 15 Sai dai a cikin zukatanku ku keɓe Kiristi a matsayin Ubangiji. A kullum, ku kasance a shirye ku ba da amsa ga duk wanda yake neman ku ba da dalilin wannan begen da kuke da shi. Amma ku yi wannan cikin tawali’u da ladabi, 16 tare da lamiri mai kyau, saboda waɗanda suke maganganun banza a kan kyawawan ayyukanku cikin Kiristi su ji kunya da irin ɓata suna da suke yi. 17 Ya fi kyau, in nufin Allah ne, a sha wahala don yin nagarta fiye da yin mugunta.
-
16 Sa’an nan ya ce wa macen,
“Zan tsananta naƙudarki ainun,
da azaba kuma za ki haifi ’ya’ya.
Za ki riƙa yin marmarin mijinki
zai kuwa yi mulki a kanki.”
17 Ga Adamu kuwa ya ce, “Saboda ka saurari matarka, ka kuma ci daga itacen da na ce, ‘Kada ka ci,’
“Za a la’anta ƙasa saboda kai.
Da wahala za ka ci daga cikinta dukan kwanakin rayuwarka.
18 Za tă ba ka ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya
za ka kuwa ci ganyayen gona.
19 Da zuffan goshinka za ka ci abincinka har ka koma ga ƙasa,
da yake daga cikinta aka yi ka.
Gama kai turɓaya ne,
kuma ga turɓaya za ka koma.”
-
33 “Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin a cikina ku sami salama. A duniyan nan za ku sha wahala. Amma ku yi ƙarfin hali! Na yi nasara a kan duniya.”
-
7 Don kada in cika da girman kai saboda waɗannan mafifitan manyan wahayoyi, sai aka sa mini wata ƙaya a jikina wadda ta zama ɗan saƙon Shaiɗan, don ta wahalshe ni. 8 Sau uku na roƙi Ubangiji yă raba ni da wannan abu. 9 Amma ya ce mini, “Alherina ya ishe ka, domin a cikin rashin ƙarfi ne ake ganin cikar ikona.” Saboda haka, zan ƙara yin taƙama da farin ciki game da rashin ƙarfina, domin ikon Yesu Kiristi yă zauna tare da ni. 10 Shi ya sa nake murna cikin rashin ƙarfi, da zagi, da shan wahaloli, da tsanantawa, da matsaloli, saboda Kiristi. Don a sa’ad da nake marar ƙarfi a nan ne nake da ƙarfi.
-
6 A kan wannan kuke cike da farin ciki ƙwarai, ko da yake yanzu na ɗan lokaci kuna fuskantar baƙin ciki daga gwaje-gwaje iri-iri. 7 Wannan kuwa domin a tabbatar da sahihancin bangaskiyarku ne, wadda ta fi zinariya daraja nesa, ita zinariya kuwa, ko da yake mai ƙarewa ce, akan gwada ta da wuta, domin bangaskiyan nan taku ta jawo muku yabo da girma da ɗaukaka a bayyanar Yesu Kiristi. 8 Ko da yake ba ku taɓa ganinsa ba, kuna ƙaunarsa; kuma ko da yake ba kwa ganinsa yanzu, kun gaskata shi, kun kuma cika da farin ciki ƙwarai, wanda ya fi gaban faɗi, 9 gama kuna samun sakamakon bangaskiyarku, ceton rayukanku ke nan.
-
16 Zan nuna masa wahalar da dole zai sha saboda sunana.”
-
23 In su bayin Kiristi ne, ni na fi su ma, ina magana kamar ruɗaɗɗe ne fa! Ai, na fi su shan fama ƙwarai da gaske, da shan dauri, na sha dūka marar iyaka, na sha hatsarin mutuwa iri-iri. 24 Sau biyar Yahudawa suka yi mini bulala arba’in ɗaya babu. 25 Sau uku aka bulale ni da bulalar ƙarfe, sau ɗaya aka jajjefe ni da duwatsu, sau uku jirgin ruwa ya ragargaje ina ciki, na kwana na kuma yini ruwan teku yana tafiya da ni. 26 Na yi tafiye-tafiye da yawa, na sha hatsari a koguna, na sha hatsarin ’yan fashi, na sha hatsari a hannun kabilarmu, na sha hatsari a hannun al’ummai, na sha hatsari a birane, na sha hatsari a jeji, na sha hatsari a teku, na kuma sha hatsarin ’yan’uwa na ƙarya. 27 Na yi fama, na shan wuya, ga kuma rashin barci sau da yawa. Na san abin da ake nufin da jin yunwa da ƙishirwa, sau da yawa kuwa na kasance da rashin abinci, na sha sanyi da zaman tsirara. 28 Ban da waɗannan abubuwa, kowace rana ina ɗauke da nauyin kula da dukan ikkilisiyoyi. 29 Wane ne ya rasa ƙarfi, da ban ji shi a jikina ba? Wane ne ya fāɗi cikin zunubi, da ban ji zafin wannan ba?
-
35 Wane ne zai raba mu da ƙaunar Kiristi? Masifa ce ko wahala ko tsanani ko yunwa ko tsiraici ko hatsari ko takobi? 36 Kamar yadda yake a rubuce cewa,
“Saboda kai ne muke fuskantar mutuwa dukan yini;
an ɗauke mu kamar tumakin da za a yanka.”
37 A’a, cikin dukan waɗannan abubuwa mun ma fi masu nasara ta wurin shi wanda ya ƙaunace mu. 38 Gama na tabbata cewa ko mutuwa ko rai, ko mala’iku ko aljanu, ko abubuwa na yanzu ko abubuwa masu zuwa nan gaba, ko ikoki, 39 ko tsayi ko zurfi, ko wani abu dabam cikin dukan halitta da zai iya raba mu da ƙaunar Allah wadda take cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.
-
8 A matse muke a kowane gefe, sai dai ba a gurgunta mu ba. An rikitar da mu, amma ba mu fid da zuciya ba. 9 An tsananta mana, amma ba a yashe mu ba, an fyaɗe mu da ƙasa, amma ba a hallaka mu ba. 10 Kullum muna ɗauke da mutuwar Yesu a jikinmu, domin ran Yesu yă bayyana a jikinmu. 11 Muddin muna a raye, kullum zaman mutuwa muke yi saboda Yesu, don a bayyana ran Yesu ta wurin jikin nan namu mai mutuwa.
-
16 Saboda haka, ba mu fid da zuciya ba. Ko da yake a waje, jikinmu mai mutuwa yana lalacewa, amma can ciki, ana sabunta mu kowace rana. 17 Don wannan ’yar wahalar tamu mai saurin wucewa, ita take tanadar mana madawwamiyar ɗaukaka mai yawa, fiye da kwatanci. 18 Domin ba abubuwan da ido yake gani ne muke dubawa ba, sai dai marasa ganuwa. Gama abubuwan da ake gani masu saurin wucewa ne, marasa ganuwa kuwa, madawwama ne.
-
8 Ka tuna da Yesu Kiristi, wanda aka tā da shi daga matattu, zuriyar Dawuda, wanda shi ne bisharata, 9 wadda nake shan wahala har ga daurin sarƙa kamar mai laifi. Amma Maganar Allah ba a daure take ba. 10 Saboda haka nake jure kome saboda zaɓaɓɓu, domin su ma su sami ceton da yake cikin Kiristi Yesu, tare da madawwamiyar ɗaukaka.
11 Ga wata magana tabbatacciya,
“In muka mutu tare da shi,
za mu rayu tare da shi;
12 in muka jimre,
za mu yi mulki tare da shi.
In muka yi mūsunsa,
shi ma zai yi mūsunmu;
-
12 Labudda, duk masu niyyar zaman tsarkaka, suna na Kiristi Yesu, za su sha tsanani.
-
14 Saboda haka, da yake muna da babban firist mai girma wanda ya ratsa sama, Yesu Ɗan Allah, bari mu riƙe bangaskiyan nan wadda muke shaidawa da ƙarfi. 15 Gama babban firist da muke da shi ba marar juyayin kāsawarmu ba ne, amma muna da wanda aka gwada ta kowace hanya, kamar dai yadda akan yi mana, duk da haka bai yi zunubi ba. 16 Saboda haka sai mu matso kusa da kursiyin alheri da ƙarfi zuciya, don mu sami jinƙai mu kuma sami alherin da zai taimake mu a lokacin bukata.
-
3 Dole kullum mu gode wa Allah saboda ku, ’yan’uwa, haka kuwa ya dace, domin bangaskiyarku tana girma gaba-gaba, ƙaunar da kowannenku yake yi wa juna kuwa tana ƙaruwa. 4 Saboda haka, a cikin ikkilisiyoyin Allah muna taƙama game da daurewarku da kuma bangaskiyarku cikin dukan tsanani da gwaje-gwajen da kuke sha.
5 Dukan wannan yana tabbatar cewa hukuncin Allah daidai ne, saboda haka kuma za a lissafta ku a kan kun cancanci mulkin Allah, wanda dominsa ne kuke shan wahala.
-
9 Sai dai muna ganin Yesu, wanda aka mai da shi ƙasa kaɗan da darajar mala’iku, yanzu kuwa an naɗa shi da ɗaukaka da girma domin yă sha wahalar mutuwa, domin ta wurin alherin Allah yă ɗanɗana mutuwa saboda kowa.
10 Ta wurin kawo ’ya’ya masu yawa zuwa ga ɗaukaka, ya dace cewa Allah, wanda dominsa da kuma ta wurinsa ne kome yake kasancewa, ya sa tushen cetonsu yă zama cikakke ta wurin shan wahala.
-
7 Saboda haka ’yan’uwa, sai ku yi haƙuri har dawowar Ubangiji. Ku dubi yadda manomi yakan jira gona ta ba da amfaninta mai kyau, da kuma yadda yake haƙurin jiran ruwan sama na damina da na kaka. 8 Haka ku ma, ku yi haƙuri, ku tsaya da ƙarfi, gama dawowar Ubangiji ya yi kusa. 9 ’Yan’uwa, kada ku yi gunaguni da juna, don kada a hukunta ku. Alƙalin yana tsaye a bakin ƙofa!
10 ’Yan’uwa, ku ɗauki annabawa da suka yi magana a cikin sunan Ubangiji, a matsayin gurbi na haƙuri a cikin shan wahala. 11 Kamar yadda kuka sani, mukan ce da waɗanda suka jure, masu albarka ne. Kun ji daurewar Ayuba, kuka kuma ga abin da Ubangiji ya yi a ƙarshe. Ubangiji yana cike da tausayi da jinƙai.
-
1 Saboda haka, da yake Kiristi ya sha wahala a jikinsa, sai ku ma ku yi wa kanku ɗamara da irin wannan hali, gama wanda ya sha wahala a jikinsa ya gama da zunubi ke nan. 2 Ta haka, ba ya sauran rayuwarsa a kan mugayen sha’awace-sha’awacen jiki, sai dai nufin Allah.
-
71 Ya yi kyau da na sha wahala
don in koyi ƙa’idodinka.
-
10 Masu albarka ne waɗanda ake tsananta musu don gani an yi adalci,
gama mulkin sama nasu ne.
11 “Masu albarka ne ku, sa’ad da mutane suke zaginku, suna tsananta muku, suna kuma faɗin kowace irin muguwar magana a kanku saboda ni. 12 Ku yi murna ku kuma yi farin ciki, domin ladarku mai yawa ne a sama, gama haka suka tsananta wa annabawan da suka riga ku.
-
40 Jawabinsa ya rinjaye su. Suka kira manzannin suka sa aka yi musu bulala. Sa’an nan suka kwaɓe su kada su ƙara magana a cikin sunan Yesu, suka kuma bar su suka tafi.
41 Manzannin suka bar Majalisar, suna farin ciki domin an ga sun cancanta a kunyata su saboda Sunan nan. 42 Kowace rana, a filin haikali da kuma gida-gida, ba su fasa koyarwa da kuma shelar labari mai daɗi cewa Yesu shi ne Kiristi ba.
-
50 Ta’aziyyata cikin wahalata ita ce
alkawarinka yana kiyaye raina.
-
13 Ba jarrabar da ta taɓa samunku, wadda ba a saba yi wa mutum ba. Allah mai aminci ne; ba zai bari a jarrabce ku fiye da ƙarfinku ba. Amma in aka jarrabce ku, zai nuna muku mafita, domin ku iya cin nasara.
-
8 “Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Simirna, ka rubuta,
Waɗannan su ne kalmomin wannan da yake na Farko da na Ƙarshe, wanda ya mutu ya kuma sāke tashi da rai.
9 Na san wahalarka da kuma talaucinka, duk da haka kai mai arziki ne! Na san ɓata suna da waɗannan suke yi maka waɗannan da suke cewa su Yahudawa ne alhali kuwa ba haka ba ne, su dai majami’ar Shaiɗan ne. 10 Kada ka ji tsoron wahalar da kake gab da sha. Ina gaya maka, Iblis zai sa waɗansunku a kurkuku don yă gwada ku. Za ku sha tsanani na kwana goma. Ka yi aminci ko da za a kashe ka, ni kuwa zan ba ka rawanin rai.
-
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da salon “Matar Zomon Safiya.” Zabura ta Dawuda.
1 Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?
Me ya sa ka yi nisa da cetona,
ka yi nesa daga kalmomin nishina?
2 Ya Allahna, na yi kuka da rana, amma ba ka amsa ba,
da dare kuma ban yi shiru ba.
-
21 Suka yi wa’azin Labari mai daɗi a wannan birni, suka kuma sami almajirai da yawa. Sai suka koma Listira, Ikoniyum da kuma Antiyok, 22 suna gina almajirai suna kuma ƙarfafa su su tsaya da gaske cikin bangaskiya. Suka ce, “Sai da shan wahaloli masu yawa za mu shiga mulkin Allah.”
-
2 Ku ɗauki nawayar juna, a haka kuwa za ku cika dokar Kiristi.
-
11 Ba na faɗin haka domin ina cikin bukata, gama na koya yadda zan gamsu a cikin kowane hali. 12 Na san mene ne zaman rashi, na kuma san mene ne zaman samu. Zan iya zama cikin kowane hali, ko cikin ƙoshi ko cikin yunwa, ko cikin yalwa ko kuma cikin fatara. 13 Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi.
14 Duk da haka kun kyauta da kuka yi tarayya da ni cikin wahalolina.
-
24 Yanzu, ina farin ciki saboda wuyar da nake sha dominku, don ta wurin wuyan nan zan cika abin da ya rage na wuyar da Kiristi ya sha saboda jikinsa, wato, ikkilisiya. 25 Na zama mai hidimar ikkilisiya bisa ga aikin nan da Allah ya ba ni amana saboda ku, domin in sanar da maganar Allah sosai. 26 Wannan magana da nake gaya muku asiri ne da yake a ɓoye tun zamanai masu yawa, wanda yanzu aka bayyana ga tsarkaka.
-
8 Saboda haka kada ka ji kunyar ba da shaida game da Ubangijinmu, ko kuwa ka ji kunyata, ni da nake ɗan sarƙa saboda shi. Sai dai ka haɗa kai tare da ni cikin shan wahala saboda bishara ta wurin ikon Allah, 9 wanda ya cece mu ya kuma kira mu ga rayuwar tsarki ba saboda wani abin da muka yi ba sai dai saboda nufinsa da kuma alherinsa. An ba mu wannan alheri cikin Kiristi Yesu tun fil azal, 10 amma yanzu an bayyana ta ta wurin bayyanuwar Mai Cetonmu, Kiristi Yesu, wanda ya hallaka mutuwa ya kuma kawo rai da rashin mutuwa a sarari ta wurin bishara. 11 A wannan bishara ce, aka naɗa ni mai shela da manzo da kuma malami. 12 Shi ya sa nake shan wahalar da nake sha. Duk da haka ba na jin kunya, domin na san wanda na gaskata da shi, na kuma tabbata cewa yana iya kiyaye abin da na danƙa masa amana don wancan rana.
-
10 Mun zama masu wauta saboda Kiristi, ku kuwa kuna da hikima sosai a cikin Kiristi! Ba mu da ƙarfi, amma ku kuna da ƙarfi! Ana girmama ku, mu kuwa ana ƙasƙantar da mu! 11 Har yă zuwa wannan sa’a, yunwa da ƙishirwa muke ciki, muna sanye da tsummoki, ana wulaƙanta mu, ba mu kuma da gida. 12 Muna aiki da gaske da hannuwanmu. In aka la’anta mu, mukan sa albarka. In aka tsananta mana, mukan jimre; 13 in aka ɓata mana suna, mukan mayar da alheri. Har yă zuwa wannan lokaci, mu ne kamar jujin duniya, abin ƙyamar kowa.
-
1 Ya ku Galatiyawa marasa azanci! Wa ya ruɗe ku? A idanunku aka bayyana Yesu Kiristi gicciyeyye a sarari. 2 Zan so in san abu guda tak daga gare ku. Kun karɓi Ruhu ta wurin kiyaye Doka ne, ko kuwa ta wurin gaskata abin da kuka ji? 3 Ashe, rashin azancinku har ya kai ga haka? Bayan kun fara da Ruhu, a yanzu kuma da halin mutuntaka za ku ƙarasa? 4 Ashe, wahaloli dabam-dabam da kuka sha sun zama a banza ke nan? Haka zai yiwu kuwa? 5 Allah ya ba ku Ruhunsa yana kuma aikata ayyukan banmamaki a cikinku saboda kuna kiyaye Doka ne, ko kuwa domin kuna gaskatawa abin da kuka ji ne? 6 Ku dubi Ibrahim mana, “Ya gaskata Allah, aka kuwa lissafta wannan adalci ne a gare shi.”
-
3 Ka jure wa shan wahala tare da mu kamar soja mai kyau na Kiristi Yesu.
-
9 Matarsa ta ce masa, “Har yanzu kana nan da amincinka? Ka la’anta Allah ka mutu!”
10 Ya amsa ya ce, “Kina magana kamar wawiya. Alheri kaɗai za mu dinga samu daga Allah ban da wahala?”
A cikin wannan duka Ayuba bai yi zunubi ba cikin maganarsa.
-
10 Duk da haka nufin Ubangiji ne a ƙuje shi yă kuma sa yă sha wahala,
kuma ko da yake Ubangiji ya sa ransa ya zama hadaya don zunubi,
zai ga zuriyarsa zai kuma kawo masa tsawon rai,
nufin Ubangiji kuma zai yi nasara a hannunsa.
-
41 “Sa’an nan zai ce wa waɗanda suke a hagunsa, ‘Ku rabu da ni, la’anannu, zuwa cikin madawwamiyar wutar da aka shirya don Iblis da mala’ikunsa. 42 Gama da nake jin yunwa, ba ku ba ni abinci ba, da nake jin ƙishirwa, ba ku ba ni abin sha ba, 43 da na yi baƙunci, ba ku karɓe ni ba, da nake bukatar tufafi, ba ku yi mini sutura ba, da na yi rashin lafiya kuma ina a kurkuku, ba ku lura da ni ba.’
44 “Su ma za su amsa, su ce, ‘Ubangiji, yaushe muka gan ka cikin yunwa ko ƙishirwa ko baƙo ko cikin bukatar tufafi ko cikin rashin lafiya ko cikin kurkuku, ba mu taimake ka ba?’
45 “Zai amsa, yă ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, duk abin da ba ku yi wa ɗaya daga cikin waɗannan mafi ƙanƙanta ba, ba ku yi mini ba ke nan.’
46 “Sa’an nan za su tafi cikin madawwamiyar hukunci, amma masu adalci kuwa za su shiga rai madawwami.”
-
9 “Dole ku yi zaman tsaro. Za a ba da ku ga hukuma, a kuma bulale ku a majami’u. Saboda ni kuma, za ku tsaya a gaban gwamnoni da sarakuna, domin ku ba da shaida a gabansu. 10 Dole sai an fara yin wa’azin bishara ga dukan al’ummai. 11 Sa’ad da aka kama ku, aka kuma kai ku don a yi muku shari’a, kada ku damu da abin da za ku faɗa. Sai dai ku faɗi abin da aka ba ku a lokacin. Gama ba ku kuke magana ba, Ruhu Mai Tsarki ne.
12 “Ɗan’uwa zai ba da ɗan’uwa a kashe. Mahaifi zai ba da ɗansa. ’Ya’ya za su tayar wa iyayensu, su kuma sa a kashe su. 13 Dukan mutane za su ƙi ku saboda ni, amma wanda ya tsaya da ƙarfi har ƙarshe, zai sami ceto.
-
42 “Uba, in ka yarda, ka ɗauke mini wannan kwaf, amma ba nufina ba, sai dai naka.”
-
13 Babu ƙaunar da ta fi wannan, a ce mutum ya ba da ransa saboda abokansa.
-
5 Ubangiji kuwa ya lura cewa muguntar mutum ta yi yawa a duniya, kuma kowane abin da yake tunani a zuciyarsa mugu ne kawai a kowanne lokaci. 6 Ubangiji ya damu da ya yi mutum a duniya, abin ya zafe shi ƙwarai. 7 Saboda haka Ubangiji ya ce, “Zan kawar da mutum, da dabbobi, da halittu masu rarrafe a ƙasa da kuma tsuntsayen sama waɗanda na halitta, daga doron ƙasa, saboda na damu da na yi su.”
-
2 Ku tuna yadda Ubangiji Allahnku ya bishe ku a dukan hanya, a cikin hamada waɗannan shekaru arba’in, don yă ƙasƙantar da ku, yă kuma gwada ku don yă san abin da yake a zuciyarku, ko za ku kiyaye umarnansa, ko babu. 3 Ya ƙasƙantar da ku, ya bar ku da yunwa, sa’an nan ya ciyar da ku da Manna, wadda ku, ko kakanninku, ba su sani ba, ta haka ne ya sa kuka sani cewa, ba da abinci kaɗai mutum zai rayu ba, amma ta wurin kowace kalmar da ta fito daga bakin Ubangiji.
-
25 Zuciya mai damuwa takan naƙasar da mutum,
amma maganar alheri kan faranta masa rai.
-
1 Sa’an nan Ruhu ya kai Yesu cikin hamada don Iblis yă gwada shi. 2 Bayan ya yi azumi yini arba’in da kuma dare arba’in, sai ya ji yunwa. 3 Sai mai gwajin ya zo wurinsa ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, ka ce wa duwatsun nan su zama burodi.”
4 Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake cewa, ‘Ba da abinci kaɗai mutum yake rayuwa ba, sai dai da kowace kalmar da take fitowa daga bakin Allah.’”
-
46 Wajen sa’a ta tara, Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktani?” (Wato, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?”).
47 Sa’ad da waɗanda suke tsattsaye a wurin suka ji haka, sai suka ce, “Yana kiran Iliya.”
48 Nan da nan, ɗaya daga cikinsu ya ruga, ya sami soso, ya jiƙa shi da ruwan tsami, ya sa a sanda, ya miƙa wa Yesu, yă sha. 49 Sauran kuwa suka ce, “Ƙyale shi mu ga, ko Iliya zai zo yă cece shi.”
50 Da Yesu ya sāke ɗaga murya da ƙarfi, sai ya saki ruhunsa.
-
15 Sai ya ce musu, “Na yi marmari ƙwarai don in ci wannan Bikin Ƙetarewa tare da ku, kafin in sha wahala. 16 Ina dai gaya muku, ba zan ƙara cinsa ba, sai ya sami cika a mulkin Allah.”
17 Bayan ya ɗauki kwaf ruwan inabi, ya yi godiya, sai ya ce, “Ku karɓa, ku rarraba wa junanku. 18 Ina dai gaya muku, ba zan ƙara sha daga ’ya’yan inabi ba, sai mulkin Allah ya zo.”
19 Sai ya ɗauki burodi ya yi godiya, ya kakkarya ya ba su, da cewa, “Wannan jikina ne, da aka bayar dominku. Ku riƙa yin haka don tunawa da ni.”
20 Haka kuma, bayan abincin, ya ɗauki kwaf ruwan inabi ya ce, “Wannan kwaf ruwan inabi shi ne, na sabon alkawari cikin jinina, da aka zubar dominku.
-
26 In wata gaɓa tana a damuwa, duk sai su damu tare. In kuma an ɗaukaka wata gaɓa, sai duk su yi farin ciki tare.
-
12 Mai albarka ne mutumin da yake daurewa cikin gwaji, gama bayan ya yi nasara da gwajin, zai sami rawanin rai wanda Allah ya yi alkawari ga waɗanda suke ƙaunarsa.
Shows Read in context, Share and Copy.