60 Bible Verses About Grief

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Grief
  1. 13 ’Yan’uwa, ba ma so ku kasance cikin jahilci game da waɗanda suka yi barci, ko kuwa ku yi baƙin ciki kamar sauran mutanen da ba su da bege. 14 Mun gaskata cewa Yesu ya mutu ya tashi kuma daga matattu, ta haka muka gaskata cewa Allah zai kawo waɗanda suka yi barci a cikinsa tare da Yesu. 15 Bisa ga maganar Ubangiji kansa, muna gaya muku cewa mu da muke raye har yanzu, waɗanda aka bari har dawowar Ubangiji, tabbatacce ba za mu riga waɗanda suka yi barci tashi ba. 16 Gama Ubangiji kansa zai sauko daga sama, da umarni mai ƙarfi, da muryar babban mala’ika da kuma busar ƙahon Allah, waɗanda suka mutu kuwa cikin Kiristi za su tashi da farko. 17 Bayan haka, mu da muke da rai da aka bari, za a ɗauke mu tare da su a cikin gizagizai don mu sadu da Ubangiji a sararin sama. Ta haka za mu kasance tare da Ubangiji har abada. 18 Saboda haka ku ƙarfafa juna da waɗannan kalmomi.

  2. 1 Ganin taron mutane, sai ya hau kan gefen dutse ya zauna.

    Almajiransa kuwa suka zo wurinsa, 2 sai ya fara koya musu.

    Yana cewa,

    3 “Masu albarka ne waɗanda suke matalauta a ruhu,

    gama mulkin sama nasu ne.

    4 Masu albarka ne waɗanda suke makoki,

    gama za a yi musu ta’aziyya.

  3. 1 Sa’an nan na ga sabon sama da sabuwar duniya, gama sama na farko da duniya ta farko sun shuɗe, babu kuma wani teku. 2 Na ga Birni Mai Tsarki, sabuwar Urushalima tana saukowa daga sama, daga Allah, a shirye kamar amaryar da aka yi mata ado mai kyau saboda mijinta. 3 Na kuma ji wata babbar murya daga kursiyin tana cewa, “Yanzu mazaunin Allah yana tare da mutane, zai kuma zauna tare da su. Za su zama mutanensa, Allah kansa kuwa zai kasance tare da su yă kuma zama Allahnsu. 4 Zai share dukan hawaye daga idanunsu. Ba sauran mutuwa ko makoki ko kuka ko azaba, gama tsofaffin al’amura sun shuɗe.”

    5 Wannan da yake zaune a kursiyin ya ce. “Ina yin kome sabo!” Sai ya ce, “Rubuta wannan, domin waɗannan kalmomi amintattu ne gaskiya ne kuma.”

  4. 3 Yabo ya tabbata ga Allah, da Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba mai tausayi, da kuma Allah na dukan ta’aziyya, 4 wanda yakan yi mana ta’aziyya a cikin dukan wahalolinmu, domin mu kuma mu iya ta’azantar da waɗanda suke cikin kowace irin wahala, da ta’aziyyar da mu kanmu muka samu daga Allah. 5 Gama kamar yadda wahalar Kiristi ta cika har tana zuba a cikin rayuwarmu, haka nan kuma ta wurin Kiristi ta’aziyyarmu ta cika har tana zuba.

  5. 18 Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai

    ya kuma cece waɗanda aka ragargaza a ruhu.

  6. 31 Sa’an nan Dawuda ya ce wa Yowab da dukan mutanen da suke tare da shi, “Ku yayyage rigunarku, ku sa tsummoki, ku yi tafiya kuna kuka a gaban Abner.” Sarki Dawuda kansa ya bi masu ɗauke da gawar daga baya. 32 Suka binne Abner a Hebron, sarki kuwa ya ɗaga murya ya yi kuka a kabarin Abner.

    33 Sarki ya kuma yi wannan waƙar makoki domin Abner ya ce,

    “Daidai ne Abner yă mutu, kamar yadda marasa bin doka suke mutuwa?

    34 Hannuwanka ba a daure suke ba,

    ƙafafunka ba a tabaibaye suke ba.

    Ka mutu kamar waɗanda suke mutuwa a hannun mugaye.”

    Sai dukan mutane suka sāke fashe da kuka saboda shi.

    35 Sa’an nan duk suka zo suka roƙi Dawuda yă ci wani abu tun rana ba tă fāɗi ba; amma Dawuda ya rantse ya ce, “Bari Allah yă hukunta ni, in na ɗanɗana abinci ko wani abu kafin rana ta fāɗi!”

  7. 3 Ya warkar da masu raunanar zuciya

    ya ɗaɗɗaura miyakunsu.

  8. 26 Haka nan ma, Ruhu yana taimakonmu cikin rashin ƙarfinmu. Ba mu san abin da ya kamata mu roƙa cikin addu’a ba, amma Ruhu kansa yana roƙo a madadinmu da nishe-nishen da kalmomi ba sa iya bayyanawa. 27 Shi kuma wanda yake binciken zukatanmu ya san halin Ruhu, domin Ruhu yana roƙo a madadin tsarkaka bisa ga nufin Allah.

    28 Mun kuma san cewa a cikin dukan abubuwa Allah yana aikata alheri ga waɗanda suke ƙaunarsa, yana waɗanda aka kira bisa ga nufinsa.

  9. 52 farat ɗaya, cikin ƙyaftawar ido, da busan ƙaho na ƙarshe. Gama za a busa ƙaho, za a tā da matattu da jiki irin da ba ya ruɓewa, za a kuma sauya kamanninmu. 53 Gama dole mai ruɓa yă maye wa mai ruɓan nan, marar mutuwa kuma yă maye wa mai mutuwan nan. 54 Sa’ad da mai ruɓan nan ya maye marar ruɓan nan, mai mutuwa kuma ya maye marar mutuwan nan, sa’an nan ne karin maganar da yake a rubuce zai zama gaskiya cewa, “An haɗiye mutuwa cikin nasara.”

    55 “Ya ke mutuwa, ina nasararki?

    Ya ke mutuwa, ina dafinki?”

    56 Zunubi ne yake ba wa mutuwa dafi, Doka kuma take ba wa zunubi iko. 57 Amma godiya ga Allah! Shi ne ya ba mu nasara ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi.

    58 Saboda haka, ƙaunatattu ’yan’uwana, ku tsaya da daram. Kada wani abu yă jijjiga ku. Ku ba da kanku kullum ga aikin Ubangiji, domin kun san cewa famar da kuke yi saboda Ubangiji ba a banza take ba.

  10. 9 Ka yi mini jinƙai, ya Ubangiji, gama ina cikin damuwa;

    idanuna sun gaji da baƙin ciki,

    raina da jikina sun tafke tilis.

    10 Baƙin ciki ya rufe raina

    shekaruna sun cika da nishi;

    ƙarfina ya karai saboda azaba,

    ƙasusuwana kuma sun gaji tiƙis.

  11. 1 Akwai lokaci domin kowane abu,

    da kuma lokaci domin kowane aiki a duniya.

    2 Lokacin haihuwa da lokacin mutuwa,

    lokacin shuki da lokacin tumɓukewa.

    3 Lokacin kisa da lokacin warkarwa,

    lokacin rushewa da lokacin ginawa.

    4 Lokacin kuka da lokacin dariya,

    lokacin makoki da lokacin rawa.

  12. 28 “Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji kuke kuma fama da kaya, zan kuwa ba ku hutu. 29 Ku ɗauki karkiyata a kanku, ku kuma yi koyi da ni, gama ni mai tawali’u ne marar girman kai, za ku kuwa sami hutu don rayukanku. 30 Gama karkiyata mai sauƙi ce, kayana kuma marasa nauyi ne.”

  13. 10 Shekara arba’in na yi fushi da wancan tsara;

    na ce, ‘Su mutane ne waɗanda zukatansu suka kauce,

    kuma ba su san hanyoyina ba.’

  14. 6 Saboda haka, ku ƙasƙantar da kanku a ƙarƙashin hannun Allah mai ƙarfi, don yă ɗaukaka ku a lokacin da ya ga dama. 7 Ku danƙa masa dukan damuwarku, domin shi ne yake lura da ku.

  15. 5 Ubangiji kuwa ya lura cewa muguntar mutum ta yi yawa a duniya, kuma kowane abin da yake tunani a zuciyarsa mugu ne kawai a kowanne lokaci. 6 Ubangiji ya damu da ya yi mutum a duniya, abin ya zafe shi ƙwarai. 7 Saboda haka Ubangiji ya ce, “Zan kawar da mutum, da dabbobi, da halittu masu rarrafe a ƙasa da kuma tsuntsayen sama waɗanda na halitta, daga doron ƙasa, saboda na damu da na yi su.” 8 Amma Nuhu ya sami tagomashi a gaban Ubangiji.

  16. 34 Sa’an nan Yaƙub ya kyakkece tufafinsa, ya sa tufafin makoki, ya kuma yi makoki domin ɗansa kwanaki masu yawa. 35 Dukan ’ya’yansa maza da mata, suka zo don su ta’azantar da shi, amma ya ƙi yă ta’azantu. Ya ce, “A’a, cikin makoki zan gangara zuwa kabari wurin ɗana.” Saboda haka, mahaifin Yusuf ya yi kuka saboda shi.

    36 Ana cikin haka, Midiyawa suka sayar da Yusuf a Masar wa Fotifar, ɗaya daga cikin shugabannin ’yan gadin fadar Fir’auna.

  17. 8 Ka lissafta makokina;

    ka jera hawayena a littafinka,

    ba a rubuce suke a cikin littafinka ba?

  18. 1 “Kada zuciyarku ta ɓaci. Ku gaskata da Allah, ku kuma gaskata da ni. 2 A cikin gidan Ubana akwai wurin zama da yawa; da a ce ba haka ba ne, da na gaya muku. Za ni can don in shirya muku wuri. 3 In kuwa na tafi na shirya muku wuri, sai in dawo in ɗauke ku ku kasance tare da ni don ku kasance inda nake. 4 Ai, kun san hanyar zuwa inda za ni.”

    5 Sai Toma ya ce masa, “Ubangiji, ba mu san inda za ka ba, to, ta yaya za mu san hanyar?”

    6 Yesu ya amsa ya ce, “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai dai ta wurina.

  19. 4 Ko da na yi tafiya

    ta kwari na inuwar mutuwa,

    ba zan ji tsoron mugu ba,

    gama kana tare da ni;

    bulalarka na dūka da kuma sandanka na tafiya,

    za su yi mini ta’aziyya.

  20. 35 Yesu ya yi kuka.

  21. 10 Shi ya sa na yi fushi da wancan zamani,

    na kuma ce, ‘Kullum zukatansu a karkace suke,

    ba su kuma san hanyoyina ba.’

  22. 19 Gama abin yabo ne in mutum ya yi haƙuri cikin zafin wahalar rashin adalci saboda yana sane da Allah.

  23. 2 Ta rasu a Kiriyat Arba (wato, Hebron) a ƙasar Kan’ana, Ibrahim kuwa ya tafi ya yi makokin Saratu, yana kuka saboda ita.

  24. 5 Yanzu dai, kada ku damu, kada kuma ku yi fushi da kanku saboda kun sayar da ni a nan, gama Allah ya aiko ni gabanku ne don in ceci rayuka.

  25. 26 Jikina da zuciyata za su iya raunana,

    amma Allah ne ƙarfin zuciyata

    da kuma rabona har abada.

  26. 10 Saboda haka kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai;

    kada ka karai, gama ni ne Allahnka.

    Zan ƙarfafa ka in kuma taimake ka;

    zan riƙe ka da hannun damana mai adalci.

  27. 15 Ku yi murna da masu murna, ku yi kuka da masu kuka.

  28. 17 Da su wane ne kuwa ya yi fushi har shekaru arba’in? Ba da waɗanda suka yi zunubi, waɗanda suka mutu a hamada ba?

  29. 10 Ku bayar hannu sake gare shi, ku kuma yi haka ba tare da gunaguni ba; saboda wannan fa Ubangiji Allahnku zai albarkace ku a cikin dukan aikinku, da kuma kome da kuka sa hannunku a kai.

  30. 20 Da jin haka sai Ayuba ya tashi ya yayyaga tufafin jikinsa, ya aske kansa. Ya fāɗi a ƙasa ya yi sujada 21 ya ce,

    “Tsirara na fito daga cikin mahaifiyata,

    tsirara kuma zan koma.

    Ubangiji ya bayar, Ubangiji kuma ya karɓa;

    yabo ya tabbata ga Ubangiji.”

    22 Cikin wannan duka Ayuba bai yi wa Allah zunubi ta wurin ba shi laifi ba.

  31. 13 sai suka zauna da shi a ƙasa har kwana bakwai. Ba wanda ya ce masa kome, don sun ga tsananin wahalar da yake ciki.

  32. 7 Idanuna sun rasa ƙarfi da baƙin ciki;

    sun rasa ƙarfi saboda dukan abokan gābana.

  33. 5 Gama fushinsa na ɗan lokaci ne

    amma alherinsa har matuƙa ne;

    mai yiwuwa a yi kuka da dare

    amma farin ciki kan zo da safe.

  34. 4 Tabbatacce ya ɗauki cututtukanmu

    ya kuma daure da baƙin cikinmu

    duk da haka muka ɗauka Allah ya hukunta shi ne,

    ya buge shi ya kuma sa ya sha azaba.

    5 Amma aka yi masa rauni saboda laifofinmu,

    aka ƙuje shi saboda kurakuranmu;

    hukuncin da ya kawo mana salama ya kasance a kansa,

    kuma ta wurin mikinsa ya sa muka warke.

    6 Dukanmu, muna kama da tumakin da suka ɓata,

    kowannenmu ya kama hanyarsa;

    Ubangiji kuwa ya sa hukunci ya auko a kansa

    hukuncin da ya wajaba a kanmu.

  35. 17 Sau na uku ya ce masa, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata?”

    Sai Bitrus ya ɓata rai saboda Yesu ya tambaye shi sau na uku, “Kana ƙaunata?” Ya ce, “Ubangiji ka san kome duka; ka san cewa, ina ƙaunarka.”

    Yesu ya ce, “Ciyar da tumakina.

  36. 7 Da ’ya’yan Yaƙub maza suka dawo daga jeji sai suka ji labarin. Abin kuwa ya zafe su ƙwarai, don Shekem ya jawo abin kunya wa jama’ar Isra’ila ta wurin kwana da ’yar Yaƙub, don bai kamata wannan abu yă faru ba.

  37. 29 Sa’ad da Ruben ya dawo wurin rijiyar, sai ya tarar cewa Yusuf ba ya can, sai ya kyakkece tufafinsa.

  38. 6 Sa’an nan Musa ya ce wa Haruna da Eleyazar da Itamar ’ya’yansa maza, “Kada ku bar gashin kanku barkatai, kada kuma ku yage tufafinku, don kada ku mutu. Yin haka zai jawo fushin Ubangiji a kan dukan jama’a. Amma dangoginku, wato, dukan Isra’ilawa, suna iya kuka saboda waɗanda Ubangiji ya hallaka da wuta.

  39. 19 Sai Tamar ta zuba toka a kanta, ta kuma yayyage doguwar riga mai kayan adon da take sanye da shi. Ta sa hannunta a kai, ta tafi tana kuka da ƙarfi.

  40. 40 Sau da yawa sun tayar masa a cikin hamada

    suka kuma ɓata masa rai a jeji!

  41. 25 Da yake wawa yakan kawo baƙin ciki ga mahaifinsa

    da ɓacin rai ga wanda ya haife shi.

  42. 1 Suna mai kyau ya fi turare mai ƙanshi,

    kuma ranar mutuwa ta fi ranar haihuwa.

    2 Gara a tafi gidan makoki

    da a je gidan biki,

    gama mutuwa ce ƙaddarar kowane mutum;

    ya kamata masu rai su lura da haka.

    3 Baƙin ciki ya fi dariya,

    gama baƙin ciki yakan kawo gyara.

    4 Zuciyar masu hikima tana a gidan makoki,

    amma zuciya wawaye tana a gidan shagali.

  43. 22 Da jin wannan, sai mutumin ya ɓata fuskarsa, ya tafi da baƙin ciki, gama yana da arziki sosai.

  44. 22 Haka ku ma, yanzu ne lokacin baƙin cikinku, amma zan sāke ganinku za ku kuma yi farin ciki, ba kuwa wanda zai ɗauke muku farin cikinku.

  45. 15 In kana ɓata wa ɗan’uwanka zuciya saboda abincin da kake ci, ba halin ƙauna kake nunawa ba ke nan. Kada abincin da kake ci yă zama hanyar lalatar da ɗan’uwanka wanda Kiristi ya mutu dominsa.

  46. 4 Gama na rubuta muku ne cikin baƙin ciki mai yawa da ɓacin zuciya har ma da hawaye mai yawa, ba don in sa ku baƙin ciki ba ne, a’a, sai dai domin in nuna muku zurfin ƙaunar da nake yi muku.

  47. 1 Yusuf kuwa ya fāɗa a kan mahaifinsa, ya yi kuka a kansa, ya kuma sumbace shi. 2 Sa’an nan Yusuf ya umarci masu maganin da suke yin masa hidima, su shafe mahaifinsa Isra’ila da maganin hana ruɓa. Saboda haka masu maganin suka shafe shi da maganin hana ruɓa. 3 Suka ɗauki kwana arba’in cif suna yin wannan, gama kwanakin da ake bukata ke nan don shafewa da maganin hana ruɓa. Masarawa kuwa suka yi makoki dominsa kwana saba’in.

  48. 29 sa’ad da dukan jama’a kuwa suka ji cewa Haruna ya mutu, sai dukan gidan Isra’ila suka yi makoki dominsa har kwana talatin.

  49. 8 Isra’ilawa suka yi makoki domin Musa a filayen Mowab kwana talatin, sai da lokacin kuka, da na makoki suka ƙare.

  50. 26 Sa’an nan Isra’ilawa, dukan mutane, suka haura zuwa Betel, a can suka zauna suna kuka a gaban Ubangiji. Suka yi azumi a wannan rana har yamma suka miƙa hadayun ƙonawa da hadayun salama ga Ubangiji.

  51. 8 Elkana mijinta kuwa yakan ce mata, “Hannatu don me kike kuka? Me ya sa ba za ki ci abinci ba? Don me kika karaya? Ashe, ban fi ’ya’ya goma a gare ki ba?”

  52. 11 “Na damu da na naɗa Shawulu sarki, domin ya juya mini baya, bai kuma bi umarnina ba.” Sama’ila ya damu ƙwarai, ya yi kuka ga Ubangiji dukan dare.

  53. 6 Dawuda kuwa ya damu ƙwarai domin mutanensa suna niyyar su jajjefe shi da duwatsu, kowannensu ransa ya ɓace saboda ’ya’yansa maza da mata, amma Dawuda ya sami ƙarfafawa a cikin Ubangiji Allahnsa.

  54. 2 “Da kawai za a iya auna wahalata

    a kuma sa ɓacin raina a ma’auni!

  55. 21 Sa’ad da zuciyata ta ɓaci

    hankalina kuma ya tashi,

  56. 3 Ka ce, ‘Kaitona! Ubangiji ya ƙara baƙin ciki da wahalata; na gaji da nishe-nishe ban kuma huta ba.’ ”

  57. 13 Saboda haka, zan hallaka ku

    in lalace ku saboda zunubanku.

  58. 20 Gaskiya nake gaya muku, za ku yi kuka da kuma gunji, yayinda duniya take murna. Za ku yi baƙin ciki, amma baƙin cikinku zai koma farin ciki.

  59. 18 A ganina, wuyar da muke sha a wannan lokaci ba su isa a kwatanta da ɗaukakar da za a bayyana a cikinmu ba.

  60. 14 Saboda haka, da yake muna da babban firist mai girma wanda ya ratsa sama, Yesu Ɗan Allah, bari mu riƙe bangaskiyan nan wadda muke shaidawa da ƙarfi. 15 Gama babban firist da muke da shi ba marar juyayin kāsawarmu ba ne, amma muna da wanda aka gwada ta kowace hanya, kamar dai yadda akan yi mana, duk da haka bai yi zunubi ba. 16 Saboda haka sai mu matso kusa da kursiyin alheri da ƙarfi zuciya, don mu sami jinƙai mu kuma sami alherin da zai taimake mu a lokacin bukata.