85 Bible Verses About Worship

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Worship
  1. 19 Sai macen ta ce, “Ranka yă daɗe, ina gani kai annabi ne. 20 Kakanninmu sun yi sujada a dutsen nan, amma ku Yahudawa kun ce a Urushalima ne ya kamata a yi sujada.”

    21 Sai Yesu ya ce, “Uwargida, ina tabbatar miki, lokaci yana zuwa da ba za ku yi wa Uba sujada ko a dutsen nan, ko kuwa a Urushalima ba. 22 Ku Samariyawa ba ku san abin da kuke yi wa sujada ba; mu kuwa mun san abin da muke yi wa sujada, gama ceto daga Yahudawa yake. 23 Duk da haka, lokaci yana zuwa har ma ya riga ya yi, da masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada a Ruhu da kuma gaskiya, gama irin waɗannan masu sujada ne Uba yake nema. 24 Allah ruhu ne, masu yi masa sujada kuwa dole su yi masa sujada a ruhu, da gaskiya kuma.”

  2. 1 Ku zo, bari mu rera don farin ciki ga Ubangiji;

    bari mu yi sowa da ƙarfi ga Dutsen cetonmu.

    2 Bari mu zo gabansa da godiya

    mu rera gare shi da kiɗi da waƙa.

    3 Gama Ubangiji Allah mai girma ne,

    babban Sarki a bisa dukan alloli.

    4 A hannunsa ne zurfafan duniya suke,

    ƙwanƙolin dutse kuma nasa ne.

    5 Teku nasa ne, gama shi ne ya yi shi,

    da hannuwansa kuma ya yi busasshiyar ƙasa.

    6 Ku zo, bari mu rusuna mu yi sujada,

    bari mu durƙusa a gaban Ubangiji Mahaliccinmu;

    7 gama shi ne Allahnmu

    mu mutanen makiyayansa ne,

    garke kuwa a ƙarƙashin kulawarsa.

    Yau, in kuka ji muryarsa,

  3. Zabura ta Dawuda.

    1 Ku ba da girma ga Ubangiji, ya ku manya,

    ku ba da girma ga Ubangiji saboda ɗaukaka da kuma ƙarfinsa.

    2 Ku ba da girma ga Ubangiji, ɗaukakar da ta dace da sunansa;

    ku bauta wa Ubangiji cikin ɗaukakar tsarkinsa.

  4. 8 Bayan ya karɓa, sai halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan nan ashirin da huɗu suka fāɗi ƙasa a gaban Ɗan Ragon. Kowannensu yana da garaya kuma suna riƙe da kaskon zinariya cike da turare, waɗanda suke addu’o’in tsarkaka. 9 Suka rera sabuwar waƙa,

    “Ka cancanci ka karɓi naɗaɗɗen littafin

    ka kuma buɗe hatimansa,

    domin an kashe ka,

    da jininka kuma ka sayi mutane wa Allah,

    daga kowace kabila da harshe da mutane da kuma al’umma.

    10 Ka mai da su masarauta da kuma firistoci, don su yi wa Allahnmu hidima,

    kuma za su yi mulki a duniya.”

    11 Sai na duba na kuma ji muryar mala’iku masu yawa, yawansu kuwa ya kai dubu dubbai, da kuma dubu goma sau dubu goma. Suka kewaye kursiyin da halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan nan. 12 Da babbar murya suka rera,

    “Macancanci ne Ɗan Ragon nan da aka kashe,

    don yă sami iko da wadata da hikima da ƙarfi

    da girma da ɗaukaka da kuma yabo!”

    13 Sa’an nan na ji kowace halitta a sama da ƙasa da ƙarƙashin ƙasa da kuma bisan teku, da kome da yake cikinsu yana rerawa,

    “Gare shi mai zama a kan kursiyin da kuma ga Ɗan Ragon

    yabo da girma da ɗaukaka da iko,

    sun tabbata har abada abadin!”

    14 Sai halittu huɗun nan masu rai suka ce, “Amin”, dattawan kuma suka fāɗi suka yi sujada.

  5. 1 Saboda haka, ina roƙonku, ’yan’uwa, saboda yawan jinƙan Allah, ku miƙa jikunanku hadaya wadda take mai rai, mai tsarki abin karɓa kuma ga Allah, wannan ita ce hanyar hidimarku ta ruhaniya. 2 Kada ku ci gaba da yin abin da duniya take yi, sai dai ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so yake, abu mai kyau, mai daɗi da kuma cikakke.

  6. 8 Kowace a cikin halittu huɗu masu rai ɗin nan tana da fikafikai guda shida, tana kuma cike da idanu a ko’ina, har ma ƙarƙashin fikafikanta. Dare da rana ba sa fasa cewa,

    “ ‘Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki

    shi ne Ubangiji Allah Maɗaukaki,’

    wanda yake a dā, wanda yake a yanzu, wanda kuma yake nan gaba.”

    9 Duk lokacin da halittu masu ran nan suka rera ɗaukaka, girma da kuma godiya ga wannan wanda yake zaune a kan kursiyin da kuma wanda yake mai rai har abada abadin, 10 sai dattawa ashirin da huɗun nan su fāɗi a ƙasa a gaban wannan wanda yake zaune a kursiyin, su yi sujada wa wannan wanda yake da rai har abada abadin. Sukan ajiye rawaninsu a gaban kursiyin suna cewa,

    11 “Ya Ubangijinmu da Allahnmu,

    ka cancanci ɗaukaka da girma da iko,

    domin ka halicci dukan abubuwa,

    kuma ta wurin nufinka aka halicce su

    suka kuma kasance.”

  7. 1 Sa’ad da Solomon ya gama yin addu’a, sai wuta ya sauko daga sama ya cinye hadaya ta ƙonawa da kuma sadakokin, ɗaukakar Ubangiji kuwa ta cika haikalin. 2 Firistoci ba su iya shiga haikalin Ubangiji ba domin ɗaukakar Ubangiji ta cika shi. 3 Sa’ad da dukan Isra’ilawa suka ga wutar na saukowa, ɗaukakar Ubangiji kuma tana a bisa haikalin, sai suka durƙusa a dakali da fuskokinsu a ƙasa, suka yi sujada suka kuma yi godiya ga Ubangiji suna cewa,

    “Ubangiji mai alheri ne,

    ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.”

    4 Sai sarki da dukan mutanen suka miƙa hadayu a gaban Ubangiji. 5 Sarki Solomon kuwa ya miƙa hadayar bijimai dubu ashirin da biyu da kuma tumaki da awaki dubu ɗari da dubu ashirin. Ta haka sarki da dukan mutane suka keɓe haikalin Allah. 6 Firistoci suka ɗauki matsayinsu, haka kuma Lawiyawa suka tsaya a matsayinsu riƙe da kayansu na bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe na Ubangiji, waɗanda Sarki Dawuda ya yi domin yabon Ubangiji. An yi amfani da su sa’ad da ake godiya, ana kuma cewa, “Ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.” Kurkusa da Lawiyawa, firistoci suka busa ƙahoninsu, dukan Isra’ila kuwa suna a tsaye.

  8. Zabura ce. Don yin godiya.

    1 Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya.

    2 Yi wa Ubangiji sujada da murna;

    ku zo gabansa da waƙoƙin farin ciki.

    3 Ku san cewa Ubangiji shi ne Allah.

    Shi ne ya yi mu, mu kuwa nasa ne;

    mu mutanensa ne, tumakin makiyayarsa.

    4 Ku shiga ƙofofinsa da godiya

    filayen gidansa kuma da yabo;

    ku gode masa ku kuma yabi sunansa.

  9. 52 Sai suka yi masa sujada, suka koma Urushalima cike da murna sosai. 53 Sai suka ci gaba da zama a cikin haikalin, suna yabon Allah.

  10. 9 Bayan wannan sai na duba, can a gabana kuwa ga wani taro mai girma, wanda ba mai iya ƙirgawa, daga kowace al’umma, kabila, mutane da kuma harshe, suna tsaye a gaban kursiyin da kuma gaban Ɗan Ragon nan. Suna saye da fararen tufafi suna kuma riƙe da rassan dabino a hannuwansu. 10 Suka tā da murya da ƙarfi suna cewa,

    “Ceto na Allahnmu ne,

    wanda yake zaune a bisan kursiyi,

    da kuma na Ɗan Ragon.”

    11 Dukan mala’iku suna tsaye kewaye da kursiyin da kuma kewaye da dattawan tare da halittu huɗun nan masu rai. Suka fāɗi da fuskokinsu ƙasa a gaban kursiyin suka kuma yi wa Allah sujada, 12 suna cewa,

    “Amin!

    Yabo da ɗaukaka,

    da hikima da godiya da girma

    da iko da ƙarfi

    sun tabbata ga Allahnmu har abada abadin.

    Amin!”

  11. 7 Sai Hiridus ya kira Masanan nan a ɓoye, yă gano daga wurinsu daidai lokacin da tauraron ya bayyana. 8 Sai ya aike su Betlehem ya ce, “Ku je ku binciko a hankali game da yaron nan. Da kun same shi, sai ku kawo mini labari nan da nan, domin ni ma in je in yi masa sujada.”

    9 Bayan sun saurari sarki, sai suka kama hanyarsu, tauraron da suka gani a gabas kuwa yana tafe a gabansu, sai da ya kai inda yaron yake. 10 Da suka ga tauraron, sai suka yi farin ciki ƙwarai. 11 Suka shiga gidan, suka kuwa ga yaron tare da mahaifiyarsa Maryamu. Suka durƙusa har ƙasa, suka yi masa sujada. Sa’an nan suka kunce dukiyarsu, suka miƙa masa kyautai na zinariya da na turare da na mur.

  12. 9 Saboda haka Allah ya ɗaukaka shi zuwa mafificin wuri

    ya kuma ba shi sunan da ya fi dukan sunaye,

    10 don a sunan Yesu kowace gwiwa za tă durƙusa,

    a sama da a ƙasa da kuma a ƙarƙashin ƙasa,

    11 kowane harshe kuma yă furta cewa Yesu Kiristi Ubangiji ne,

    don ɗaukakar Allah Uba.

  13. 3 suka rera waƙar Musa bawan Allah da kuma waƙar Ɗan Ragon suna cewa,

    “Ayyukanka suna da girma da kuma banmamaki,

    ya Ubangiji Maɗaukaki.

    Al’amuranka suna da aminci da kuma gaskiya,

    ya Sarkin zamanai.

    4 Wane ne ba zai ji tsoronka,

    yă kuma kawo ɗaukaka ga sunanka ba, ya Ubangiji?

    Gama kai kaɗai ne mai tsarki.

    Dukan al’ummai za su zo

    su yi sujada a gabanka,

    gama an bayyana ayyukan adalcinka.”

  14. 1 ’Ya’yan Haruna maza, Nadab da Abihu suka ɗauki farantansu, suka sa wuta a ciki, suka zuba turare a kai; suka kuma miƙa haramtacciyar wuta a gaban Ubangiji, ba irin wadda Ubangiji ya umarta ba. 2 Sai wuta ta fito daga Ubangiji ta cinye su, suka kuma mutu a gaban Ubangiji. 3 Sai Musa ya ce Haruna, “Ga abin da Ubangiji yake nufi sa’ad da ya ce,

    “ ‘A cikin waɗanda suka kusace ni

    za a tabbata ni mai tsarki ne;

    a fuskar dukan mutane

    za a kuwa girmama ni.’ ”

    Haruna ya yi shiru.

  15. 27 Hezekiya ya ba da umarni a miƙa hadaya ta ƙonawa a kan bagade. Yayinda aka fara miƙawa, ana rerawa ga Ubangiji, tare da bushe-bushe da kiɗe-kiɗen kayan waƙa na Dawuda sarkin Isra’ila. 28 Dukan taron suka durƙusa suka yi sujada, yayinda mawaƙa suke rerawa, ana kuma busa ƙahoni, dukan wannan ya ci gaba sai da aka gama miƙa hadaya ta ƙonawa.

    29 Sa’ad da aka gama miƙawa, sai sarki da mutanen da suke tare da shi suka durƙusa suka yi sujada. 30 Sarki Hezekiya da fadawansa suka umarci Lawiyawa su yabi Ubangiji da kalmomin Dawuda da na Asaf mai duba. Saboda haka suka rera yabai da murna, suka sunkuyar da kawunansu suka yi sujada.

  16. 31 Nan da nan Yesu ya miƙa hannu ya kamo shi ya ce, “Kai mai ƙarancin bangaskiya, don me ka yi shakka?”

    32 Da suka hau jirgin ruwan, sai iskar ta kwanta. 33 Waɗanda suke cikin jirgin ruwan kuwa suka yi masa sujada, suna cewa, “Gaskiya kai Ɗan Allah ne.”

  17. 15 Saboda haka, ta wurin Yesu, bari mu ci gaba da miƙa hadaya ta yabo ga Allah, yabon leɓuna da yake shaidar sunansa.

  18. 20 Sai Nuhu ya gina bagaden hadaya ga Ubangiji, ya ɗiba waɗansu dabbobi da tsuntsaye masu tsabta, ya yi hadaya ta ƙonawa da su a kan bagaden. 21 Da Ubangiji ya ji ƙanshi mai daɗi, sai ya ce a zuciyarsa, “Ba zan ƙara la’anta ƙasa saboda mutum ba, ko da yake dukan tunanin zuciyar mutum mugu ne tun yana ƙarami. Ba kuwa zan ƙara hallaka dukan halittu masu rai, kamar yadda na yi ba.

  19. 1 Sai Allah ya faɗi waɗannan kalmomi ya ce,

    2 “Ni ne Ubangiji Allahnka, wanda ya fitar da ku daga Masar, daga ƙasar bauta.

    3 “Ba za ka yi wa kanka waɗansu alloli ba sai ni.

    4 Ba za ka yi wa kanka waɗansu alloli a siffar wani abu a sama a bisa, ko a ƙarƙashin ƙasa, ko a ƙarƙashin ruwa ba. 5 Ba za ka durƙusa gare su, ko ka yi musu sujada ba. Gama ni, Ubangiji Allahnka mai kishi ne, nakan hukunta ’ya’ya har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suke ƙina, 6 amma ina nuna ƙauna ga tsara dubbai na waɗanda suke ƙaunata, suke kuma kiyaye umarnaina.

  20. 13 Ubangiji ya ce,

    “Waɗannan mutane sun zo kusa da ni da bakinsu

    suka kuma girmama ni da leɓunansu,

    amma zukatansu suna nesa daga gare ni.

    Sujadar da suke mini

    cike take da dokokin da mutane suka koyar.

    14 Saboda haka zan firgita waɗannan mutane sau ɗaya

    da abubuwan banmamaki a kan abubuwan banmamaki;

    hikimar masu hikima za tă lalace,

    azancin masu azanci zai ɓace.”

  21. 24 Da karɓan irin umarnan nan, sai ya sa su can cikin ɗakin kurkuku na ciki-ciki, kuma ya ɗaura ƙafafunsu a turu.

    25 Wajen tsakar dare Bulus da Sila suna addu’a suna rera waƙoƙi ga Allah, sauran ’yan kurkuku kuwa suna sauraronsu. 26 Ba zato ba tsammani sai aka yi wata babbar girgizar ƙasa har tushen ginin kurkukun ya jijjiga. Nan da nan sai duk ƙofofin kurkukun suka bubbuɗe, sarƙoƙin kowa kuma suka ɓaɓɓalle.

  22. 14 Fiye da waɗannan duka, ku yi ƙaunar juna, gama ƙauna ce take haɗa kome gaba ɗaya.

    15 Ku bar salamar Kiristi tă yi mulki a zukatanku, da yake a matsayin gaɓoɓin jiki ɗaya an kira ku ga salama. Ku zama masu godiya. 16 Ku bar maganar Kiristi ta zauna a cikinku a yalwace yayinda kuke koya, kuna kuma yi wa juna gargaɗi da dukan hikima, da kuma yayinda kuke waƙoƙin zabura, waƙoƙi da waƙoƙin ruhaniya tare da godiya a zukatanku ga Allah. 17 Kuma ko mene ne kuke yi, ko cikin magana ko cikin ayyuka, ku yi shi duka a cikin sunan Ubangiji Yesu, kuna yin godiya ga Allah Uba ta wurinsa.

  23. 6 Haka kuma, sa’ad da Allah ya kawo ɗan farinsa a duniya ya ce,

    “Bari dukan mala’ikun Allah su yi masa sujada.”

  24. 7 Ya ce da babbar murya, “Ku ji tsoron Allah ku kuma ɗaukaka shi, domin sa’ar hukuncinsa ya yi. Ku yi wa wannan da ya halicci sammai, ƙasa, teku, da maɓulɓulan ruwa sujada.”

  25. 13 Ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku bauta masa shi kaɗai, ku kuma yi alkawaranku da sunansa. 14 Kada ku bi waɗansu alloli, allolin mutanen da suke kewaye da ku;

  26. 22 Amma Sama’ila ya ce,

    “Ubangiji yana murna da sadaka da hadaya

    fiye da biyayya ga maganar Ubangiji?

    Yin biyayya ta fi hadaya

    a kula kuma ta fi ƙibabbun raguna.

  27. 35 Da Ubangiji ya ƙulla alkawari da Isra’ilawa, ya dokace su cewa, “Kada ku yi wa waɗansu alloli sujada ko ku durƙusa a gabansu ku bauta musu, ko ku miƙa musu hadaya. 36 Amma Ubangiji wanda ya fito da ku daga Masar da iko mai girma da hannu mai ƙarfi, shi ne za ku yi masa sujada. Gare shi za ku durƙusa ku kuma miƙa masa hadayu.

  28. 10 Da masu ginin suka aza harsashin ginin haikalin Ubangiji, sai firistoci suka sa kayansu na firistoci suka riƙe ƙahonin busa, Lawiyawa (’ya’yan Asaf) kuwa suka riƙe kuge, suka yi shiri domin su rera yabo ga Ubangiji kamar yadda Dawuda Sarkin Isra’ila ya ba da umarni. 11 Suka rera waƙar yabo da godiya ga Ubangiji, suna cewa,

    “Shi nagari ne;

    ƙaunarsa kuwa ga Isra’ila har abada ce.”

    Dukan jama’a kuwa suka yabi Ubangiji da murya mai ƙarfi, domin an aza harsashin ginin gidan Ubangiji.

  29. 5 Lawiyawan nan, Yeshuwa, Kadmiyel, Bani, Hashabnehiya, Sherebiya, Hodiya, Shebaniya da Fetahahiya, suka ce, “Ku miƙe tsaye ku yabi Ubangiji Allahnku, wanda yake har abada abadin.”

    “Albarka ta tabbata ga sunanka mai ɗaukaka, bari kuma a ɗaukaka shi bisa dukan albarka da yabo. 6 Kai kaɗai ne Ubangiji. Kai ka yi sammai, har ma da sama sammai, da dukan rundunar taurari, da duniya da kuma dukan abin da yake cikinta, da tekuna da dukan abubuwan da suke cikinsu. Ka ba da rai ga kome, kuma rundunonin sama suna maka sujada.

  30. 5 Bayan lokacin bikin ya wuce, sai Ayuba yă aika su zo don yă tsarkake su. Tun da sassafe zai miƙa hadaya ta ƙonawa domin kowannensu, don yana tunani cewa, “Mai yiwuwa ’ya’yana sun yi wa Allah zunubi, ko sun la’anta shi a cikin zuciyarsu.” Haka Ayuba ya saba yi.

  31. 20 Da jin haka sai Ayuba ya tashi ya yayyaga tufafin jikinsa, ya aske kansa. Ya fāɗi a ƙasa ya yi sujada 21 ya ce,

    “Tsirara na fito daga cikin mahaifiyata,

    tsirara kuma zan koma.

    Ubangiji ya bayar, Ubangiji kuma ya karɓa;

    yabo ya tabbata ga Ubangiji.”

  32. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Waƙa. Zabura.

    1 Ku yi sowa ta farin ciki ga Allah, dukan duniya!

    2 Ku rera ɗaukaka ga sunansa;

    ku sa yabonsa yă zama da ɗaukaka!

    3 Ku ce wa Allah, “Ayyukanka da banmamaki suke!

    Ikonka da girma yake

    har abokan gābanka suna durƙusa a gabanka.

    4 Dukan duniya sun rusuna a gabanka

    suna rera yabo gare ka,

    suna rera yabo ga sunanka.” Sela

  33. 1 A shekarar da Sarki Uzziya ya mutu, na ga Ubangiji zaune a kan kujerar sarauta a sama cike da ɗaukaka, zatinsa ya cika haikali. 2 A bisansa akwai serafofi, kowanne yana da fikafikai shida. Fikafikai biyu sun rufe fuskokinsu, da biyu suka rufe ƙafafunsu, biyu kuma da su suke tashi. 3 Suna kiran juna,

    “Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki! Ubangiji Maɗaukaki ne;

    duniya ta cika da ɗaukakarsa.”

    4 Da jin ƙarar muryoyinsu madogarai da madogaran ƙofa suka girgiza, haikali kuma ya cika da hayaƙi.

    5 Sai na tā da murya na ce, “Kaitona! Na shiga uku! Gama ni mutum ne mai leɓuna marar tsarki, kuma ina raye a cikin mutane masu leɓuna marasa tsarki, idanuna kuma sun ga Sarki, Ubangiji Maɗaukaki.”

    6 Sai ɗaya daga cikin serafofin ya yi firiya zuwa wurina tare da garwashi mai wuta a hannunsa, wanda ya ɗiba da arautaki daga bagade. 7 Da shi ne ya taɓa bakina ya ce, “Duba, wannan ya taɓa leɓunanka, yanzu fa an kawar da laifofinka, an kuma gafarta maka zunubanka.”

    8 Sa’an nan na ji muryar Ubangiji tana cewa, “Wa zan aika? Wa zai tafi mana?”

    Sai na ce, “Ga ni! Ka aike ni!”

  34. 10 To, da Daniyel ya ji labarin cewa an fitar da doka, sai ya tafi gidansa a ɗakinsa na sama inda tagogin ɗakin suke duban wajen Urushalima. Sau uku yakan durƙusa yă yi addu’a yana yin godiya ga Allahnsa, kamar yadda ya saba yi.

  35. 10 Sai Yesu ya ce masa, “Rabu da ni, Shaiɗan! Gama a rubuce yake, ‘Yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kaɗai kuma za ka bauta wa.’”

  36. 5 Iblis ya kai shi can kan wani wuri mai tsawo, ya nunnuna masa a ƙyiftawar ido dukan mulkokin duniya. 6 Ya ce masa, “Zan ba ka dukan ikonsu da darajarsu, gama ni aka danƙa wa, kuma zan bai wa duk wanda na ga dama. 7 Saboda haka in ka yi mini sujada, dukan wannan zai zama naka.”

    8 Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake, ‘Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, kuma shi kaɗai za ka bauta wa.’”

  37. 22 bari mu matso kusa da Allah da zuciya mai gaskiya da kuma cikakken tabbaci mai zuwa ta wurin bangaskiya. Bari mu bar zukatan da tsabta, lamirinmu babu mugunta, da kuma jikunanmu a wanke da ruwa. 23 Bari mu tsaya da ƙarfi a kan ga begen da muka ce namu ne, gama shi da ya yi alkawarin, mai aminci ne. 24 Bari kuma mu yi tunani a kan yadda za mu gargaɗe juna ga ƙauna da kuma ayyuka nagari. 25 Kada mu daina taruwa kamar yadda waɗansu suka saba, sai dai mu ƙarfafa juna, tun ba ma da kuka ga Ranan nan tana kusatowa ba.

  38. 4 Dattawan nan ashirin da huɗu da halittu huɗun nan masu rai suka fāɗi suka yi wa Allah sujada, wannan da yake zaune a kursiyi. Suka tā da murya suka ce,

    “Amin, Halleluya!”

    5 Sa’an nan wata murya ta fito daga kursiyin, tana cewa,

    “Ku yabi Allahnmu,

    dukanku da kuke bayinsa,

    ku da kuke tsoronsa,

    babba da yaro!”

    6 Sai na ji wani abu mai ƙara kamar ƙasaitaccen taron mutane, kamar rurin ruwaye masu gudu da kuma kamar bugun tsawa mai ƙarfi, suna tā da murya suna cewa,

    “Halleluya!

    Gama Ubangiji Allahnmu Maɗaukaki ne yake mulki.

    7 Bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna

    mu kuma ɗaukaka shi!

    Domin lokacin auren Ɗan Ragon ya yi,

    amaryarsa kuwa ta shirya kanta.

  39. 14 Kada ku bauta wa wani allah, gama Ubangiji, wanda sunansa Kishi, Allah ne mai kishi.

  40. 4 Ku ji, ya Isra’ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne. 5 Ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku da dukan zuciyarku, da dukan ranku, da kuma dukan ƙarfinku. 6 Waɗannan umarnai da nake ba ku a yau, za su kasance a zukatanku. 7 Ku koya wa ’ya’yanku su da himma. Yi musu magana game da su sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya a hanya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi. 8 Ku ɗaura su su zama alamu a hannuwanku, ku kuma ɗaura su a goshinku. 9 Ku rubuta su a dogaran ƙofofin gidajenku, da ƙofofinku.

  41. 6 Ezra ya yabi Ubangiji, Allah mai girma; dukan mutane kuwa suka tā da hannuwansu suka amsa, “Amin! Amin!” Sa’an nan suka sunkuya suka yi wa Ubangiji sujada da fuskokinsu har ƙasa.

  42. 1 A rana ta ashirin da huɗu ga watan nan, Isra’ilawa suka taru, suna yin azumi, suna sa rigunan makoki, suna kuma zuba toka a kansu. 2 Waɗanda suke zuriyar Isra’ilawa suka ware kansu daga dukan baƙi. Suka tsaya, suka kuma furta zunubansu da muguntar kakanninsu. 3 Sa’ad da suke nan a tsaye, aka ɗauki awa uku ana karanta Littafin Dokar Ubangiji Allahnsu. Aka kuma ɗauki awa uku ana sujada ga Ubangiji Allahnsu.

  43. 7 Amma ni, ta wurin jinƙanka mai girma,

    zan shiga gidanka;

    da bangirma zan durƙusa

    ga haikalinka.

  44. 4 Abu guda na roƙi Ubangiji,

    wannan shi ne na nema,

    cewa in zauna a gidan Ubangiji

    dukan kwanakin raina,

    in dubi kyan Ubangiji

    in kuma neme shi a cikin haikalinsa.

  45. 8 A cikin alloli babu kamar ka, ya Ubangiji;

    babu ayyukan da za a kwatanta da naka.

    9 Dukan al’umman da ka yi

    za su zo su yi sujada a gabanka, ya Ubangiji;

    za su kawo ɗaukaka ga sunanka.

    10 Gama kai mai girma ne kana kuma aikata ayyuka masu banmamaki;

    kai kaɗai ne Allah.

  46. 1 Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji;

    ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka.

    2 Ku rera ga Ubangiji, ku yabe sunansa;

    ku yi shelar cetonsa kowace rana.

    3 Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai,

    manyan ayyukansa a cikin dukan mutane.

    4 Gama da girma Ubangiji yake, ya kuma cancanci yabo;

    tilas a ji tsoronsa fiye da dukan alloli.

    5 Gama dukan allolin al’ummai gumaka ne,

    amma Ubangiji ne ya yi sammai.

    6 Daraja da ɗaukaka suna a gabansa;

    ƙarfi da ɗaukaka suna a cikin tsarkakar wurinsa.

  47. 5 Ku ɗaukaka Ubangiji Allahnmu

    ku kuma yi masa sujada a wurin sa ƙafafunsa;

    shi mai tsarki ne.

  48. 3 Bari su yabi sunansa tare da rawa

    suna kuma yin kiɗi gare shi da ganga da garaya.

  49. 6 Bari kowane abu mai numfashi yă yabi Ubangiji.

    Yabi Ubangiji.

  50. 1 Ya Ubangiji, kai ne Allahna; zan ɗaukaka ka in kuma yabi sunanka,

    gama cikin cikakken aminci ka yi abubuwa masu banmamaki,

    abubuwan da aka shirya tun da.

  51. 13 Ba labari sai ga taron rundunar sama suka bayyana tare da mala’ikan, suna yabon Allah suna cewa,

    14 “Ɗaukaka ga Allah a can cikin sama,

    a duniya kuma salama ga mutane waɗanda tagomashinsa yake bisansu.”

  52. 15 Sai ku yi hankali sosai da yadda kuke rayuwa, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai kamar masu hikima. 16 Ku kuma yi matuƙar amfani da kowane zarafi, don kwanakin nan mugaye ne. 17 Saboda haka kada ku zama wawaye, sai dai ku fahimci ko mene ne nufin Ubangiji. 18 Kada ku bugu da ruwan inabi, wanda yake kai ga lalaci. A maimako haka, ku cika da Ruhu. 19 Ku yi zance da juna cikin zabura, da waƙoƙi, da kuma waƙoƙin ruhaniya. Ku rera, ku kuma yi kiɗe-kiɗe a zuciyarku ga Ubangiji. 20 Kullum ku dinga yin amfani da sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, kuna gode wa Allah Uba a kome.

    21 Ku yi biyayya da juna saboda bangirmar da kuke nuna wa Kiristi.

  53. 9 Amma ku zaɓaɓɓu ne, ƙungiyar firistocin babban Sarki, al’umma mai tsarki, jama’a mallakar Allah, domin ku shaida yabon shi wanda ya kira ku daga cikin duhu zuwa haskensa mai banmamaki.

  54. 8 Ni, Yohanna, na ji, na kuma ga abubuwan nan. Kuma sa’ad da na ji, na kuma gan su, sai na fāɗi a ƙasa a gaban mala’ikan da yake nuna mini su, don in yi sujada. 9 Amma ya ce mini, “Kada ka yi haka! Ni abokin bautarku ne, kai da ’yan’uwanka annabawa, da kuma waɗanda suke kiyaye kalmomin wannan littafi. Allah za ka yi wa sujada!”

  55. 2 Sai Allah ya ce, “Ka ɗauki ɗanka, makaɗaicin ɗanka Ishaku, wanda kake ƙauna, ka tafi yankin Moriya, ka miƙa shi hadaya ta ƙonawa a can a kan ɗaya daga cikin duwatsun da zan nuna maka.”

  56. 8 “Sa’an nan ka sa su yi mini wuri mai tsarki, domin in zauna a cikinsu. 9 Ka ƙera wannan tabanakul da duk kayan da suke ciki da waje, daidai yadda zan nuna maka.

  57. 10 Lokacin da mutane suka ga al’amudin girgije a tsaye a ƙofar tentin, sai duk su miƙe tsaye su yi sujada, kowa a ƙofar tentinsa.

  58. 12 Yanzu fa, ya Isra’ila, mene ne Ubangiji Allahnku yake so a gare ku, in ba ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin hanyoyinsa, ku ƙaunace shi, ku bauta wa Ubangiji Allahnku da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku, 13 ku kuma kiyaye umarnan Ubangiji da kuma ƙa’idodinsa da nake ba ku a yau don amfaninku ba?

  59. 10 yanzu kuwa na kawo ’ya’yan fari na gonar da kai, ya Ubangiji ka ba ni.” Sai ku sa kwandon a gaban Ubangiji Allahnku, sa’an nan ku rusuna a gabansa. 11 Ku da Lawiyawa da baƙin da suke a cikinku, za ku yi murna cikin dukan abubuwa masu kyau da Ubangiji Allahnku ya ba ku tare da gidanku.

  60. 5 Dawuda da dukan gidan Isra’ila suka yi biki sosai da dukan ƙarfinsu a gaban Ubangiji, da waƙoƙi, da molaye, da garayu, da ganguna, da kacau-kacau da kuma kuge.

  61. 11 Sa’an nan firistoci suka janye daga Wuri Mai Tsarki. Dukan firistocin da suke can sun tsarkake kansu, ko daga wace ɓangarori suka fito. 12 Dukan Lawiyawa waɗanda suke mawaƙa, Asaf, Heman, Yedutun da ’ya’yansu maza da dangoginsu, suka tsaya a gefen gabas na bagaden, saye da lilin mai kyau suna kuma kaɗa ganguna, garayu da molaye. Tare da su akwai firistoci 120 masu busan ƙahoni. 13 Masu busan ƙahonin da mawaƙa suka haɗu da baki ɗaya sai ka ce murya guda ce, don su yabi su kuma yi godiya ga Ubangiji. Haɗe da busan ƙahoni, ganguna da sauran kayayyaki, suka tā da muryoyinsu cikin yabo ga Ubangiji suka rera,

    “Yana da kyau;

    ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.”

    Sai haikalin Ubangiji ya cika da girgije, 14 Firistoci ba su iya yin hidimarsu ba saboda girgijen, gama ɗaukakar Ubangiji ta cika haikalin Allah.

  62. 27 Dukan iyakokin duniya

    za su tuna su kuma juya ga Ubangiji,

    kuma dukan iyalan al’ummai

    za su rusuna a gabansa,

    28 gama mulki na Ubangiji ne

    kuma yana mulki a bisa al’ummai.

  63. 4 Sa’an nan zan tafi bagaden Allah,

    ga Allah, farin cikina da murnata.

    Zan yabe ka da garaya,

    Ya Allah, Allahna.

  64. 14 “Ku miƙa hadayar godiya ga Allah,

    ku cika alkawuranku ga Mafi Ɗaukaka,

    15 ku kira gare ni a ranar wahala;

    zan cece ku, za ku kuwa girmama ni.”

  65. 3 Domin ƙaunarka ta fi rai kyau,

    leɓunana za su ɗaukaka ka.

    4 Zan yabe ka muddin raina,

    kuma a cikin sunanka zai ɗaga hannuwana.

  66. 1 Ku yi godiya ga Ubangiji, ku kira bisa sunansa;

    ku sanar a cikin al’ummai abin da ya yi.

    2 Ku rera gare shi, ku rera yabo gare shi;

    ku faɗa dukan abubuwan mamakin da ya aikata.

    3 Ku ɗaukaka a cikin sunansa mai tsarki;

    bari zukatan waɗanda suke neman Ubangiji su yi farin ciki.

    4 Ku sa rai ga Ubangiji da kuma ƙarfinsa;

    ku nemi fuskarsa kullum.

    5 Ku tuna da abubuwan mamakin da ya yi,

    mu’ujizansa, da kuma hukunce-hukuncen da ya zartar,

    6 Ya ku zuriyar Ibrahim bawansa,

    Ya ku ’ya’yan Yaƙub, zaɓaɓɓensa.

  67. 1 Yabi Ubangiji.

    Yabi Ubangiji daga sammai,

    yabe shi a bisa sammai.

    2 Yabe shi, dukanku mala’ikunsa,

    yabe shi, dukanku rundunarsa na sama.

  68. 11 Ubangiji ya ce, “Yawan hadayunku,

    mene ne suke a gare ni?”

    Ina da isashen hadayun ƙonawa,

    na raguna da na kitsen dabbobi masu ƙiba;

    ba na jin daɗin

    jinin bijimai da na tumaki da kuma na awaki.

    12 Sa’ad da kuka zo don ku bayyana a gabana,

    wa ya nemi wannan daga gare ku,

    da kuke kai da kawowa a filayen gidana?

    13 Ku daina kawo hadayu marasa amfani!

    Turarenku abin ƙyama ne gare ni.

    Ina ƙin bukukkuwanku na Sabon Wata, da na ranakun Asabbaci, da taronku na addini,

    ba zan iya jure wa mugun taronku ba.

    14 Bukukkuwanku na Sabon Wata da na tsarkakan ranaku

    na ƙi su.

    Sun zama mini kaya;

    na gaji da ɗaukansu.

    15 Sa’ad da kuka ɗaga hannuwanku wajen yin addu’a,

    zan ɓoye fuskata daga gare ku;

    ko da kun miƙa addu’o’i masu yawa,

    ba zan kasa kunne ba.

    Hannuwanku sun cika da jini!

    16 Ku yi wanka ku kuma tsabtacce kanku.

    Ku kawar da mugayen ayyukanku daga gabana;

    Ku daina aikata mugunta.

    17 Ku koyi yin nagarta; ku nemi adalci.

    Ku ƙarfafa waɗanda aka zalunta.

    Ku ba wa marayu hakkinsu,

    ku taimaki gwauruwa.

  69. 13 Kuma a wannan rana zai busa ƙaho mai kāra sosai. Waɗanda suke mutuwa a Assuriya da kuma waɗanda aka kai zaman bauta a Masar za su zo su kuma yi wa Ubangiji sujada a dutse mai tsarki a Urushalima.

  70. 7 Ku munafukai! Daidai ne Ishaya ya yi annabci a kanku da ya ce,

    8 “ ‘Waɗannan mutane da baki kawai suke girmama ni,

    amma zukatansu suna nesa da ni.

    9 A banza suke mini sujada,

    koyarwarsu, dokoki ne kawai da mutane suke koyarwa.’ ”

  71. 6 Ya amsa ya ce, “Daidai ne Ishaya ya yi annabci game da ku munafukai; kamar yadda yake a rubuce cewa,

    “ ‘Waɗannan mutane da baki suke girmama ni,

    amma zukatansu sun yi nesa da ni.

    7 A banza suke mini sujada,

    koyarwarsu, dokokin mutane ne kawai.’

  72. 1 Wata rana, Bitrus da Yohanna suna haurawa zuwa haikali a lokacin addu’a da ƙarfe uku na rana.

  73. 2 Yayinda suna cikin sujada da azumi ga Ubangiji, Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Ku keɓe mini Barnabas da Shawulu domin aikin da na kira su.” 3 Saboda haka bayan suka yi azumi da addu’a, sai suka ɗibiya musu hannuwansu a kansu suka sallame su.

  74. 16 Sai dattawan nan ashirin da huɗu da suke zaune a kursiyoyinsu a gaban Allah, suka fāɗi da fuskokinsu a ƙasa suka kuma yi wa Allah sujada, 17 suna cewa,

    “Muna maka godiya ya Ubangiji Allah, Maɗaukaki,

    wanda yake a yanzu, shi ne kuma a dā,

    domin ka karɓi ikonka mai girma

    ka kuma fara mulki.

  75. 16 Suka wofinta dukan umarnan Ubangiji Allahnsu, suka yi wa kansu gumakan zubi na siffar ’yan maruƙa biyu, da kuma ginshiƙin Ashera. Suka rusuna wa rundunan taurari, suka kuma yi wa Ba’al sujada. 17 Suka miƙa ’ya’yansu maza da mata hadaya ta wuta. Suka yi duba, suka yi sihiri suka kuma ba da kansu ga mugunta a gaban Ubangiji; suka sa ya yi fushi.

    18 Saboda haka Ubangiji ya yi fushi ƙwarai da Isra’ila, ya kuma kawar da su daga gabansa. Kabilar Yahuda kaɗai aka bari, 19 ko Yahuda ma ba su kiyaye umarnan Ubangiji Allahnsu ba. Sun bi gurbin da Isra’ila ta kawo. 20 Saboda haka Ubangiji ya wofinta mutanen Isra’ila; ya azabtar da su, ya kuma ba da su a hannun masu kwasar ganima, sai da ya shafe su ƙaƙaf daga gabansa.

  76. 31 Bari sammai su yi farin ciki, bari duniya tă yi murna;

    bari su ce a cikin al’ummai, “Ubangiji yana mulki!”

    32 Bari teku da kome da yake cikinsa su yi ruri;

    bari gonaki da kome a cikinsu su yi farin ciki!

    33 Sa’an nan itatuwan jeji za su rera,

    za su rera don farin ciki a gaban Ubangiji,

    gama ya zo don yă hukunta duniya.

    34 Ku yi godiya ga Ubangiji, gama shi nagari ne;

    ƙaunarsa madawwamiya ce.

  77. 9 Zan yabe ka, ya Ubangiji, a cikin al’ummai;

    zan rera game da kai a cikin mutane.

  78. Zabura ta Dawuda. Sa’ad da yake a hamadar Yahuda.

    1 Ya Allah, kai ne Allahna,

    da nacewa na neme ka;

    raina yana ƙishinka,

    jikina yana marmarinka,

    cikin busasshiyar ƙasar da ta zozaye

    inda babu ruwa.

  79. 8 Bakina ya cika da yabonka,

    ina furta darajarka dukan yini.

  80. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit. Na ’Ya’yan Kora maza. Zabura ce.

    1 Ina misalin kyan wurin zamanka,

    Ya Ubangiji Maɗaukaki!

    2 Raina yana marmari, har yana suma,

    don filayen gidan Ubangiji;

    zuciyata da namana na tā da murya

    domin Allah mai rai.

    3 Har tsada ma ta sami gida,

    tsatsewa kuma ta yi wa kanta sheƙa,

    inda za tă ƙyanƙyashe ’ya’yanta,

    wuri kusa da bagadenka,

    Ya Ubangiji Maɗaukaki, Sarkina da kuma Allahna.

  81. 10 Rana guda a filayen gidan sun fi

    dubu a wani wuri dabam;

    zan gwammaci in zama mai tsaron ƙofa a gidan Allahna

    da in zauna a tentunan mugaye.

  82. Ta Dawuda.

    1 Yabi Ubangiji, ya raina;

    dukan abin da yake cikin cikina, yabi sunansa mai tsarki.

  83. 20 Yabi Ubangiji, ku mala’ikunsa,

    ku jarumawa masu yi masa aiki,

    waɗanda suke yin biyayya da maganarsa.

    21 Yabi Ubangiji, dukanku rundunarsa ta sama,

    ku bayinsa waɗanda kuke aikata nufinsa.

    22 Yabi Ubangiji, dukanku ayyukansa

    ko’ina a mulkinsa.

    Yabi Ubangiji, ya raina.

  84. 3 Ubangiji da girma yake ya kuma cancanci yabo

    girmansa ya fi ƙarfin ganewar mutum.

  85. 16 Ku riƙa farin ciki kullum; 17 ku ci gaba da yin addu’a; 18 ku yi godiya cikin kowane hali, gama wannan shi ne nufin Allah dominku cikin Kiristi Yesu.