90 Bible Verses About Worshiping God

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Worshiping God
  1. 21 Sai Yesu ya ce, “Uwargida, ina tabbatar miki, lokaci yana zuwa da ba za ku yi wa Uba sujada ko a dutsen nan, ko kuwa a Urushalima ba. 22 Ku Samariyawa ba ku san abin da kuke yi wa sujada ba; mu kuwa mun san abin da muke yi wa sujada, gama ceto daga Yahudawa yake. 23 Duk da haka, lokaci yana zuwa har ma ya riga ya yi, da masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada a Ruhu da kuma gaskiya, gama irin waɗannan masu sujada ne Uba yake nema. 24 Allah ruhu ne, masu yi masa sujada kuwa dole su yi masa sujada a ruhu, da gaskiya kuma.”

  2. 1 Ku zo, bari mu rera don farin ciki ga Ubangiji;

    bari mu yi sowa da ƙarfi ga Dutsen cetonmu.

    2 Bari mu zo gabansa da godiya

    mu rera gare shi da kiɗi da waƙa.

    3 Gama Ubangiji Allah mai girma ne,

    babban Sarki a bisa dukan alloli.

    4 A hannunsa ne zurfafan duniya suke,

    ƙwanƙolin dutse kuma nasa ne.

    5 Teku nasa ne, gama shi ne ya yi shi,

    da hannuwansa kuma ya yi busasshiyar ƙasa.

    6 Ku zo, bari mu rusuna mu yi sujada,

    bari mu durƙusa a gaban Ubangiji Mahaliccinmu;

    7 gama shi ne Allahnmu

    mu mutanen makiyayansa ne,

    garke kuwa a ƙarƙashin kulawarsa.

    Yau, in kuka ji muryarsa,

  3. 1 Saboda haka, ina roƙonku, ’yan’uwa, saboda yawan jinƙan Allah, ku miƙa jikunanku hadaya wadda take mai rai, mai tsarki abin karɓa kuma ga Allah, wannan ita ce hanyar hidimarku ta ruhaniya.

  4. Zabura ce. Don yin godiya.

    1 Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya.

    2 Yi wa Ubangiji sujada da murna;

    ku zo gabansa da waƙoƙin farin ciki.

    3 Ku san cewa Ubangiji shi ne Allah.

    Shi ne ya yi mu, mu kuwa nasa ne;

    mu mutanensa ne, tumakin makiyayarsa.

    4 Ku shiga ƙofofinsa da godiya

    filayen gidansa kuma da yabo;

    ku gode masa ku kuma yabi sunansa.

  5. Zabura ta Dawuda.

    1 Ku ba da girma ga Ubangiji, ya ku manya,

    ku ba da girma ga Ubangiji saboda ɗaukaka da kuma ƙarfinsa.

    2 Ku ba da girma ga Ubangiji, ɗaukakar da ta dace da sunansa;

    ku bauta wa Ubangiji cikin ɗaukakar tsarkinsa.

  6. 8 Ku ba wa Ubangiji ɗaukakar da ta dace da sunansa;

    ku kawo sadaka ku kuma zo cikin filayen gidansa.

    9 Ku bauta wa Ubangiji da darajar tsarkinsa;

    ku yi rawar jiki a gabansa, dukan duniya.

  7. 8 Kowace a cikin halittu huɗu masu rai ɗin nan tana da fikafikai guda shida, tana kuma cike da idanu a ko’ina, har ma ƙarƙashin fikafikanta. Dare da rana ba sa fasa cewa,

    “ ‘Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki

    shi ne Ubangiji Allah Maɗaukaki,’

    wanda yake a dā, wanda yake a yanzu, wanda kuma yake nan gaba.”

    9 Duk lokacin da halittu masu ran nan suka rera ɗaukaka, girma da kuma godiya ga wannan wanda yake zaune a kan kursiyin da kuma wanda yake mai rai har abada abadin, 10 sai dattawa ashirin da huɗun nan su fāɗi a ƙasa a gaban wannan wanda yake zaune a kursiyin, su yi sujada wa wannan wanda yake da rai har abada abadin. Sukan ajiye rawaninsu a gaban kursiyin suna cewa,

    11 “Ya Ubangijinmu da Allahnmu,

    ka cancanci ɗaukaka da girma da iko,

    domin ka halicci dukan abubuwa,

    kuma ta wurin nufinka aka halicce su

    suka kuma kasance.”

  8. 14 Fiye da waɗannan duka, ku yi ƙaunar juna, gama ƙauna ce take haɗa kome gaba ɗaya.

    15 Ku bar salamar Kiristi tă yi mulki a zukatanku, da yake a matsayin gaɓoɓin jiki ɗaya an kira ku ga salama. Ku zama masu godiya. 16 Ku bar maganar Kiristi ta zauna a cikinku a yalwace yayinda kuke koya, kuna kuma yi wa juna gargaɗi da dukan hikima, da kuma yayinda kuke waƙoƙin zabura, waƙoƙi da waƙoƙin ruhaniya tare da godiya a zukatanku ga Allah. 17 Kuma ko mene ne kuke yi, ko cikin magana ko cikin ayyuka, ku yi shi duka a cikin sunan Ubangiji Yesu, kuna yin godiya ga Allah Uba ta wurinsa.

  9. 28 Saboda haka, da yake muna karɓar mulkin da ba ya jijjiguwa, sai mu yi godiya, ta haka kuwa mu yi wa Allah sujada yadda ya kamata, tare da bangirma da kuma tsoro, 29 gama “Allahnmu wuta ne mai cinyewa.”

  10. 15 Saboda haka, ta wurin Yesu, bari mu ci gaba da miƙa hadaya ta yabo ga Allah, yabon leɓuna da yake shaidar sunansa. 16 Kada kuma ku manta yin aikin nagari da kuma taimakon waɗansu, gama da irin waɗannan hadayu ne Allah yake jin daɗi.

  11. 5 Lawiyawan nan, Yeshuwa, Kadmiyel, Bani, Hashabnehiya, Sherebiya, Hodiya, Shebaniya da Fetahahiya, suka ce, “Ku miƙe tsaye ku yabi Ubangiji Allahnku, wanda yake har abada abadin.”

    “Albarka ta tabbata ga sunanka mai ɗaukaka, bari kuma a ɗaukaka shi bisa dukan albarka da yabo. 6 Kai kaɗai ne Ubangiji. Kai ka yi sammai, har ma da sama sammai, da dukan rundunar taurari, da duniya da kuma dukan abin da yake cikinta, da tekuna da dukan abubuwan da suke cikinsu. Ka ba da rai ga kome, kuma rundunonin sama suna maka sujada.

  12. 29 ku ba wa Ubangiji ɗaukakar da ta dace da sunansa.

    Ku kawo hadaya ku kuma zo gabansa;

    ku yi wa Ubangiji sujada cikin darajar tsarkinsa.

  13. 17 Saboda haka kada ku zama wawaye, sai dai ku fahimci ko mene ne nufin Ubangiji. 18 Kada ku bugu da ruwan inabi, wanda yake kai ga lalaci. A maimako haka, ku cika da Ruhu. 19 Ku yi zance da juna cikin zabura, da waƙoƙi, da kuma waƙoƙin ruhaniya. Ku rera, ku kuma yi kiɗe-kiɗe a zuciyarku ga Ubangiji. 20 Kullum ku dinga yin amfani da sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, kuna gode wa Allah Uba a kome.

    21 Ku yi biyayya da juna saboda bangirmar da kuke nuna wa Kiristi.

  14. 9 Saboda haka Allah ya ɗaukaka shi zuwa mafificin wuri

    ya kuma ba shi sunan da ya fi dukan sunaye,

    10 don a sunan Yesu kowace gwiwa za tă durƙusa,

    a sama da a ƙasa da kuma a ƙarƙashin ƙasa,

    11 kowane harshe kuma yă furta cewa Yesu Kiristi Ubangiji ne,

    don ɗaukakar Allah Uba.

  15. 3 Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ya kawo mana kowace albarka ta ruhaniya daga sama. 4 Gama ya zaɓe mu a cikin Kiristi tun dā can, kafin ma a halicci duniya don mu zama masu tsarki da kuma marasa aibi a gabansa. 5 A cikin ƙauna, ya ƙaddara mu zama ’ya’yansa na riƙo ta wurin Kiristi Yesu, bisa ga nufinsa na alheri. 6 Ya yi haka don mu yabi Allah saboda alherin da ya yi mana saboda mu na ƙaunataccen Ɗansa ne.

  16. 9 Bayan wannan sai na duba, can a gabana kuwa ga wani taro mai girma, wanda ba mai iya ƙirgawa, daga kowace al’umma, kabila, mutane da kuma harshe, suna tsaye a gaban kursiyin da kuma gaban Ɗan Ragon nan. Suna saye da fararen tufafi suna kuma riƙe da rassan dabino a hannuwansu. 10 Suka tā da murya da ƙarfi suna cewa,

    “Ceto na Allahnmu ne,

    wanda yake zaune a bisan kursiyi,

    da kuma na Ɗan Ragon.”

    11 Dukan mala’iku suna tsaye kewaye da kursiyin da kuma kewaye da dattawan tare da halittu huɗun nan masu rai. Suka fāɗi da fuskokinsu ƙasa a gaban kursiyin suka kuma yi wa Allah sujada, 12 suna cewa,

    “Amin!

    Yabo da ɗaukaka,

    da hikima da godiya da girma

    da iko da ƙarfi

    sun tabbata ga Allahnmu har abada abadin.

    Amin!”

  17. 8 Ni, Yohanna, na ji, na kuma ga abubuwan nan. Kuma sa’ad da na ji, na kuma gan su, sai na fāɗi a ƙasa a gaban mala’ikan da yake nuna mini su, don in yi sujada. 9 Amma ya ce mini, “Kada ka yi haka! Ni abokin bautarku ne, kai da ’yan’uwanka annabawa, da kuma waɗanda suke kiyaye kalmomin wannan littafi. Allah za ka yi wa sujada!”

  18. 9 Suka rera sabuwar waƙa,

    “Ka cancanci ka karɓi naɗaɗɗen littafin

    ka kuma buɗe hatimansa,

    domin an kashe ka,

    da jininka kuma ka sayi mutane wa Allah,

    daga kowace kabila da harshe da mutane da kuma al’umma.

    10 Ka mai da su masarauta da kuma firistoci, don su yi wa Allahnmu hidima,

    kuma za su yi mulki a duniya.”

    11 Sai na duba na kuma ji muryar mala’iku masu yawa, yawansu kuwa ya kai dubu dubbai, da kuma dubu goma sau dubu goma. Suka kewaye kursiyin da halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan nan. 12 Da babbar murya suka rera,

    “Macancanci ne Ɗan Ragon nan da aka kashe,

    don yă sami iko da wadata da hikima da ƙarfi

    da girma da ɗaukaka da kuma yabo!”

    13 Sa’an nan na ji kowace halitta a sama da ƙasa da ƙarƙashin ƙasa da kuma bisan teku, da kome da yake cikinsu yana rerawa,

    “Gare shi mai zama a kan kursiyin da kuma ga Ɗan Ragon

    yabo da girma da ɗaukaka da iko,

    sun tabbata har abada abadin!”

    14 Sai halittu huɗun nan masu rai suka ce, “Amin”, dattawan kuma suka fāɗi suka yi sujada.

  19. 7 Ubangiji ya bayyana ga Abram ya ce, “Ga zuriyarka ne zan ba da wannan ƙasa.” Saboda haka Abram ya gina bagade a can ga Ubangiji, wanda ya bayyana gare shi.

    8 Daga can, ya ci gaba zuwa wajen tuddai a gabashin Betel ya kafa tentinsa, Betel yana yamma, Ai, kuma a gabas. A can ya gina bagade ga Ubangiji ya kuma kira bisa sunan Ubangiji.

  20. 1 Sai Allah ya faɗi waɗannan kalmomi ya ce,

    2 “Ni ne Ubangiji Allahnka, wanda ya fitar da ku daga Masar, daga ƙasar bauta.

    3 “Ba za ka yi wa kanka waɗansu alloli ba sai ni.

    4 Ba za ka yi wa kanka waɗansu alloli a siffar wani abu a sama a bisa, ko a ƙarƙashin ƙasa, ko a ƙarƙashin ruwa ba. 5 Ba za ka durƙusa gare su, ko ka yi musu sujada ba. Gama ni, Ubangiji Allahnka mai kishi ne, nakan hukunta ’ya’ya har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suke ƙina, 6 amma ina nuna ƙauna ga tsara dubbai na waɗanda suke ƙaunata, suke kuma kiyaye umarnaina.

  21. 1 ’Ya’yan Haruna maza, Nadab da Abihu suka ɗauki farantansu, suka sa wuta a ciki, suka zuba turare a kai; suka kuma miƙa haramtacciyar wuta a gaban Ubangiji, ba irin wadda Ubangiji ya umarta ba. 2 Sai wuta ta fito daga Ubangiji ta cinye su, suka kuma mutu a gaban Ubangiji. 3 Sai Musa ya ce Haruna, “Ga abin da Ubangiji yake nufi sa’ad da ya ce,

    “ ‘A cikin waɗanda suka kusace ni

    za a tabbata ni mai tsarki ne;

    a fuskar dukan mutane

    za a kuwa girmama ni.’ ”

    Haruna ya yi shiru.

  22. 1 A rana ta ashirin da huɗu ga watan nan, Isra’ilawa suka taru, suna yin azumi, suna sa rigunan makoki, suna kuma zuba toka a kansu. 2 Waɗanda suke zuriyar Isra’ilawa suka ware kansu daga dukan baƙi. Suka tsaya, suka kuma furta zunubansu da muguntar kakanninsu. 3 Sa’ad da suke nan a tsaye, aka ɗauki awa uku ana karanta Littafin Dokar Ubangiji Allahnsu. Aka kuma ɗauki awa uku ana sujada ga Ubangiji Allahnsu.

  23. Zabura ta Dawuda. Sa’ad da yake a hamadar Yahuda.

    1 Ya Allah, kai ne Allahna,

    da nacewa na neme ka;

    raina yana ƙishinka,

    jikina yana marmarinka,

    cikin busasshiyar ƙasar da ta zozaye

    inda babu ruwa.

    2 Na gan ka a wuri mai tsarki

    na kuma dubi ikonka da ɗaukakarka.

    3 Domin ƙaunarka ta fi rai kyau,

    leɓunana za su ɗaukaka ka.

    4 Zan yabe ka muddin raina,

    kuma a cikin sunanka zai ɗaga hannuwana.

  24. 13 Ubangiji ya ce,

    “Waɗannan mutane sun zo kusa da ni da bakinsu

    suka kuma girmama ni da leɓunansu,

    amma zukatansu suna nesa daga gare ni.

    Sujadar da suke mini

    cike take da dokokin da mutane suka koyar.

    14 Saboda haka zan firgita waɗannan mutane sau ɗaya

    da abubuwan banmamaki a kan abubuwan banmamaki;

    hikimar masu hikima za tă lalace,

    azancin masu azanci zai ɓace.”

  25. 42 Suka ba da kansu ga koyarwar manzanni da kuma ga zumunci, ga gutsuttsura burodin da kuma ga addu’a. 43 Kowa ya cika da tsoro, manzannin kuwa suka aikata abubuwan banmamaki da alamu masu yawa. 44 Dukan masu bi suna tare, suna kuma mallakar kome tare. 45 Suka dinga sayar da ƙaddarorinsu da kayayyakinsu, suka ba wa kowa gwargwadon bukatarsa. 46 Kowace rana suka ci gaba da taruwa a filin haikali. Suka gutsuttsura burodi a gidajensu suna cin abinci tare da farin ciki da zuciya ɗaya, 47 suna yabon Allah suna kuma samun tagomashin dukan mutane. Ubangiji kuwa ya ƙara yawansu kowace rana na waɗanda suke samun ceto.

  26. 7 Ku munafukai! Daidai ne Ishaya ya yi annabci a kanku da ya ce,

    8 “ ‘Waɗannan mutane da baki kawai suke girmama ni,

    amma zukatansu suna nesa da ni.

    9 A banza suke mini sujada,

    koyarwarsu, dokoki ne kawai da mutane suke koyarwa.’ ”

  27. 8 Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake, ‘Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, kuma shi kaɗai za ka bauta wa.’”

  28. 29 Musa da Haruna suka tattara dukan dattawan Isra’ilawa, 30 sai Haruna ya gaya musu dukan abin da Ubangiji ya ce wa Musa. Ya kuma aikata mu’ujizan a gaban mutanen, 31 sai suka gaskata. Sa’ad da suka ji cewa Ubangiji ya damu da su, ya kuma ga azabarsu, sai suka durƙusa suka yi sujada.

  29. 31 Bari sammai su yi farin ciki, bari duniya tă yi murna;

    bari su ce a cikin al’ummai, “Ubangiji yana mulki!”

    32 Bari teku da kome da yake cikinsa su yi ruri;

    bari gonaki da kome a cikinsu su yi farin ciki!

    33 Sa’an nan itatuwan jeji za su rera,

    za su rera don farin ciki a gaban Ubangiji,

    gama ya zo don yă hukunta duniya.

    34 Ku yi godiya ga Ubangiji, gama shi nagari ne;

    ƙaunarsa madawwamiya ce.

    35 Ku yi kuka, ku ce, “Cece mu, ya Allah Mai Cetonmu;

    tara mu ka kuma cece mu daga al’ummai,

    don mu yi godiya ga sunanka mai tsarki,

    don mu ɗaukaka a cikin yabonka.”

    36 Yabi Ubangiji, Allah na Isra’ila,

    daga madawwami zuwa madawwami.

    Sai dukan mutane suka ce, “Amin.” Suka kuma “Yabi Ubangiji.”

  30. 3 Sa’ad da dukan Isra’ilawa suka ga wutar na saukowa, ɗaukakar Ubangiji kuma tana a bisa haikalin, sai suka durƙusa a dakali da fuskokinsu a ƙasa, suka yi sujada suka kuma yi godiya ga Ubangiji suna cewa,

    “Ubangiji mai alheri ne,

    ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.”

  31. 22 Zan furta sunanka ga ’yan’uwana;

    cikin taron masu sujada zan yabe ka.

    23 Ku da kuke tsoron Ubangiji, ku yabe shi!

    Dukanku zuriyar Yaƙub, ku girmama shi!

    Ku girmama shi, dukanku zuriyar Isra’ila!

  32. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Waƙa. Zabura.

    1 Ku yi sowa ta farin ciki ga Allah, dukan duniya!

    2 Ku rera ɗaukaka ga sunansa;

    ku sa yabonsa yă zama da ɗaukaka!

    3 Ku ce wa Allah, “Ayyukanka da banmamaki suke!

    Ikonka da girma yake

    har abokan gābanka suna durƙusa a gabanka.

    4 Dukan duniya sun rusuna a gabanka

    suna rera yabo gare ka,

    suna rera yabo ga sunanka.” Sela

  33. 24 Da karɓan irin umarnan nan, sai ya sa su can cikin ɗakin kurkuku na ciki-ciki, kuma ya ɗaura ƙafafunsu a turu.

    25 Wajen tsakar dare Bulus da Sila suna addu’a suna rera waƙoƙi ga Allah, sauran ’yan kurkuku kuwa suna sauraronsu. 26 Ba zato ba tsammani sai aka yi wata babbar girgizar ƙasa har tushen ginin kurkukun ya jijjiga. Nan da nan sai duk ƙofofin kurkukun suka bubbuɗe, sarƙoƙin kowa kuma suka ɓaɓɓalle.

  34. 14 Kada ku bauta wa wani allah, gama Ubangiji, wanda sunansa Kishi, Allah ne mai kishi.

  35. Zabura ce ta yabo. Ta Dawuda.

    1 Zan ɗaukaka ka, ya Allahna, Sarki;

    zan yabi sunanka har abada abadin.

    2 Kowace rana zan yabe ka

    in kuma ɗaukaka sunanka har abada abadin.

    3 Ubangiji da girma yake ya kuma cancanci yabo

    girmansa ya fi ƙarfin ganewar mutum.

    4 Tsara guda za tă yi maganar ayyukanka ga wata tsara;

    za su yi magana game da manyan ayyukanka.

  36. 3 Yabe shi da ƙarar kakaki,

    yabe shi da garaya da molo,

    4 yabe shi da ganga kuna taka rawa,

    yabe shi da kayan kiɗi na tsirkiya kuna kuma busa,

    5 yabe shi da kuge mai ƙara,

    yabe shi da kuge masu ƙara sosai.

    6 Bari kowane abu mai numfashi yă yabi Ubangiji.

    Yabi Ubangiji.

  37. 8 Har wa yau, Iblis ya kai shi bisa wani dutse mai tsawo sosai, ya nunnuna masa dukan mulkokin duniya da darajarsu. 9 Ya ce, “Zan ba ka dukan wannan, in za ka durƙusa ka yi mini sujada.”

    10 Sai Yesu ya ce masa, “Rabu da ni, Shaiɗan! Gama a rubuce yake, ‘Yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kaɗai kuma za ka bauta wa.’”

  38. 52 Sai suka yi masa sujada, suka koma Urushalima cike da murna sosai. 53 Sai suka ci gaba da zama a cikin haikalin, suna yabon Allah.

  39. 1 Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji;

    ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka.

    2 Ku rera ga Ubangiji, ku yabe sunansa;

    ku yi shelar cetonsa kowace rana.

    3 Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai,

    manyan ayyukansa a cikin dukan mutane.

    4 Gama da girma Ubangiji yake, ya kuma cancanci yabo;

    tilas a ji tsoronsa fiye da dukan alloli.

    5 Gama dukan allolin al’ummai gumaka ne,

    amma Ubangiji ne ya yi sammai.

    6 Daraja da ɗaukaka suna a gabansa;

    ƙarfi da ɗaukaka suna a cikin tsarkakar wurinsa.

  40. 10 To, da Daniyel ya ji labarin cewa an fitar da doka, sai ya tafi gidansa a ɗakinsa na sama inda tagogin ɗakin suke duban wajen Urushalima. Sau uku yakan durƙusa yă yi addu’a yana yin godiya ga Allahnsa, kamar yadda ya saba yi.

  41. 3 Gama mu ne masu kaciya, mu da muke yi sujada ta wurin Ruhun Allah, mu da muke taƙama a cikin Kiristi Yesu, mu da ba mu dogara da ayyukan da ake gani ba,

  42. 3 suka rera waƙar Musa bawan Allah da kuma waƙar Ɗan Ragon suna cewa,

    “Ayyukanka suna da girma da kuma banmamaki,

    ya Ubangiji Maɗaukaki.

    Al’amuranka suna da aminci da kuma gaskiya,

    ya Sarkin zamanai.

    4 Wane ne ba zai ji tsoronka,

    yă kuma kawo ɗaukaka ga sunanka ba, ya Ubangiji?

    Gama kai kaɗai ne mai tsarki.

    Dukan al’ummai za su zo

    su yi sujada a gabanka,

    gama an bayyana ayyukan adalcinka.”

  43. 20 Da jin haka sai Ayuba ya tashi ya yayyaga tufafin jikinsa, ya aske kansa. Ya fāɗi a ƙasa ya yi sujada 21 ya ce,

    “Tsirara na fito daga cikin mahaifiyata,

    tsirara kuma zan koma.

    Ubangiji ya bayar, Ubangiji kuma ya karɓa;

    yabo ya tabbata ga Ubangiji.”

  44. 8 A cikin alloli babu kamar ka, ya Ubangiji;

    babu ayyukan da za a kwatanta da naka.

    9 Dukan al’umman da ka yi

    za su zo su yi sujada a gabanka, ya Ubangiji;

    za su kawo ɗaukaka ga sunanka.

    10 Gama kai mai girma ne kana kuma aikata ayyuka masu banmamaki;

    kai kaɗai ne Allah.

  45. 5 Ku ɗaukaka Ubangiji Allahnmu

    ku kuma yi masa sujada a wurin sa ƙafafunsa;

    shi mai tsarki ne.

  46. 6 Ya amsa ya ce, “Daidai ne Ishaya ya yi annabci game da ku munafukai; kamar yadda yake a rubuce cewa,

    “ ‘Waɗannan mutane da baki suke girmama ni,

    amma zukatansu sun yi nesa da ni.

    7 A banza suke mini sujada,

    koyarwarsu, dokokin mutane ne kawai.’

  47. 9 Amma ku zaɓaɓɓu ne, ƙungiyar firistocin babban Sarki, al’umma mai tsarki, jama’a mallakar Allah, domin ku shaida yabon shi wanda ya kira ku daga cikin duhu zuwa haskensa mai banmamaki.

  48. 4 Dattawan nan ashirin da huɗu da halittu huɗun nan masu rai suka fāɗi suka yi wa Allah sujada, wannan da yake zaune a kursiyi. Suka tā da murya suka ce,

    “Amin, Halleluya!”

    5 Sa’an nan wata murya ta fito daga kursiyin, tana cewa,

    “Ku yabi Allahnmu,

    dukanku da kuke bayinsa,

    ku da kuke tsoronsa,

    babba da yaro!”

    6 Sai na ji wani abu mai ƙara kamar ƙasaitaccen taron mutane, kamar rurin ruwaye masu gudu da kuma kamar bugun tsawa mai ƙarfi, suna tā da murya suna cewa,

    “Halleluya!

    Gama Ubangiji Allahnmu Maɗaukaki ne yake mulki.

    7 Bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna

    mu kuma ɗaukaka shi!

    Domin lokacin auren Ɗan Ragon ya yi,

    amaryarsa kuwa ta shirya kanta.

  49. 20 Sa’an nan Miriyam annabiya, ’yar’uwar Haruna ta ɗauki ganga a hannunta, dukan mata kuwa suka bi ta, da ganguna suna rawa. 21 Miriyam ta yi musu waƙa.

    “Ku rera ga Ubangiji

    gama ya ci gawurtacciyar nasara.

    Doki da mahayi,

    ya jefa cikin teku.”

  50. 27 Hezekiya ya ba da umarni a miƙa hadaya ta ƙonawa a kan bagade. Yayinda aka fara miƙawa, ana rerawa ga Ubangiji, tare da bushe-bushe da kiɗe-kiɗen kayan waƙa na Dawuda sarkin Isra’ila. 28 Dukan taron suka durƙusa suka yi sujada, yayinda mawaƙa suke rerawa, ana kuma busa ƙahoni, dukan wannan ya ci gaba sai da aka gama miƙa hadaya ta ƙonawa.

    29 Sa’ad da aka gama miƙawa, sai sarki da mutanen da suke tare da shi suka durƙusa suka yi sujada. 30 Sarki Hezekiya da fadawansa suka umarci Lawiyawa su yabi Ubangiji da kalmomin Dawuda da na Asaf mai duba. Saboda haka suka rera yabai da murna, suka sunkuyar da kawunansu suka yi sujada.

  51. Ta Dawuda. Sa’ad da ya yi kamar ya haukace a gaban Abimelek, Wanda ya kore shi, ya kuwa tafi.

    1 Zan gode wa Ubangiji kullayaumi;

    yabonsa kullum za su kasance a leɓunana.

    2 Raina zai yi fariya a cikin Ubangiji;

    bari waɗanda suke wahala su ji su kuma yi farin ciki.

    3 Ku ɗaukaka Ubangiji tare da ni;

    bari mu ɗaukaka sunansa tare.

  52. 3 Bari su yabi sunansa tare da rawa

    suna kuma yin kiɗi gare shi da ganga da garaya.

  53. 20 Sa’ad da kuka taru, ba Cimar Ubangiji kuke ci ba, 21 gama yayinda kuke ci, kowa yakan ci gaba ba tare da jiran wani ba. Wani yă zauna da yunwa, wani kuma yă bugu. 22 Kai, ba ku da gidajen da za ku ci ku sha ne? Ko dai kun rena ikkilisiyar Allah ne, kuna kuma wulaƙanta waɗanda ba su da kome? Me zan ce muku? In yabe ku ne game da wannan? A’a, ko kaɗan!

    23 Gama abin da na karɓa daga wurin Ubangiji shi ne nake ba ku. Ubangiji Yesu, a daren da aka bashe shi, ya ɗauki burodi, 24 bayan ya yi godiya, sai ya kakkarya ya ce, “Wannan jikina ne, wanda yake dominku, ku yi wannan don tunawa da ni.” 25 Haka kuma bayan cimar, ya ɗauki kwaf, yana cewa, “Wannan kwaf ne sabon alkawari a jinina; ku yi wannan, a duk sa’ad da kuke sha, don tunawa da ni.” 26 Gama a duk sa’ad da kuke cin wannan burodi, kuke kuma sha daga wannan kwaf, kuna shelar mutuwar Ubangiji ne har yă dawo.

    27 Saboda haka, duk wanda ya ci burodin ko ya sha daga kwaf na Ubangiji da rashin cancanta, ya yi laifin wulaƙanta jiki da jinin Ubangiji ke nan. 28 Dole kowa yă bincike kansa kafin yă ci burodin yă kuma sha daga kwaf ɗin.

  54. 6 Sai na ga wani mala’ika yana tashi sama a tsakiyar sararin sama, yana kuma da madawwamiyar bishara wadda zai yi shela ga waɗanda suke zama a duniya, ga kowace al’umma, kabila, harshe, da kuma jama’a. 7 Ya ce da babbar murya, “Ku ji tsoron Allah ku kuma ɗaukaka shi, domin sa’ar hukuncinsa ya yi. Ku yi wa wannan da ya halicci sammai, ƙasa, teku, da maɓulɓulan ruwa sujada.”

  55. 9 Sai mala’ikan ya ce mini, “Rubuta, ‘Masu albarka ne waɗanda aka gayyace su zuwa bikin auren Ɗan Ragon!’ ” Sai ya ƙara da cewa, “Waɗannan su ne kalmomin Allah da gaske.”

    10 Da wannan sai na fāɗi a gabansa, don in yi masa sujada. Amma ya ce mini, “Kada ka yi haka! Ni ma abokin bauta ne da kai da kuma ’yan’uwanka waɗanda suke riƙe da shaidar Yesu. Ka yi wa Allah sujada! Domin shaidar Yesu ita ce ruhun annabci.”

  56. 9 Yayinda Musa ya shiga cikin tentin, sai al’amudin girgije yă sauko, yă tsaya a ƙofar yayinda Ubangiji yana magana da Musa. 10 Lokacin da mutane suka ga al’amudin girgije a tsaye a ƙofar tentin, sai duk su miƙe tsaye su yi sujada, kowa a ƙofar tentinsa.

  57. 4 Ku ji, ya Isra’ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne. 5 Ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku da dukan zuciyarku, da dukan ranku, da kuma dukan ƙarfinku. 6 Waɗannan umarnai da nake ba ku a yau, za su kasance a zukatanku. 7 Ku koya wa ’ya’yanku su da himma. Yi musu magana game da su sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya a hanya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi. 8 Ku ɗaura su su zama alamu a hannuwanku, ku kuma ɗaura su a goshinku. 9 Ku rubuta su a dogaran ƙofofin gidajenku, da ƙofofinku.

  58. 22 Amma Sama’ila ya ce,

    “Ubangiji yana murna da sadaka da hadaya

    fiye da biyayya ga maganar Ubangiji?

    Yin biyayya ta fi hadaya

    a kula kuma ta fi ƙibabbun raguna.

  59. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ga muryar “Mutuwar Ɗa.” Zabura ta Dawuda.

    1 Zan yabe ka, ya Ubangiji, da dukan zuciyata;

    zan faɗa dukan abubuwan banmamakinka.

    2 Zan yi murna in kuma yi farin ciki a cikinka;

    zan rera yabo ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka.

  60. 11 Ka mai da kukata ta zama rawa;

    ka tuɓe rigar makokina ka sa mini na farin ciki,

    12 don zuciyata za tă iya rera gare ka ba kuwa za tă yi shiru ba.

    Ya Ubangiji Allahna, zan yi maka godiya har abada.

  61. 4 Sa’an nan zan tafi bagaden Allah,

    ga Allah, farin cikina da murnata.

    Zan yabe ka da garaya,

    Ya Allah, Allahna.

  62. Ta Dawuda.

    1 Yabi Ubangiji, ya raina;

    dukan abin da yake cikin cikina, yabi sunansa mai tsarki.

  63. 16 Ku riƙa farin ciki kullum; 17 ku ci gaba da yin addu’a; 18 ku yi godiya cikin kowane hali, gama wannan shi ne nufin Allah dominku cikin Kiristi Yesu.

  64. 12 Yanzu fa, ya Isra’ila, mene ne Ubangiji Allahnku yake so a gare ku, in ba ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin hanyoyinsa, ku ƙaunace shi, ku bauta wa Ubangiji Allahnku da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku, 13 ku kuma kiyaye umarnan Ubangiji da kuma ƙa’idodinsa da nake ba ku a yau don amfaninku ba?

  65. 15 Da Gideyon ya ji mafarkin da fassararsa, sai ya yi wa Allah sujada. Ya koma sansanin Isra’ila ya yi kira da ƙarfi ya ce, “Ku tashi! Ubangiji ya ba da sansanin Midiyawa a hannuwanku.”

  66. 11 Sa’an nan firistoci suka janye daga Wuri Mai Tsarki. Dukan firistocin da suke can sun tsarkake kansu, ko daga wace ɓangarori suka fito. 12 Dukan Lawiyawa waɗanda suke mawaƙa, Asaf, Heman, Yedutun da ’ya’yansu maza da dangoginsu, suka tsaya a gefen gabas na bagaden, saye da lilin mai kyau suna kuma kaɗa ganguna, garayu da molaye. Tare da su akwai firistoci 120 masu busan ƙahoni. 13 Masu busan ƙahonin da mawaƙa suka haɗu da baki ɗaya sai ka ce murya guda ce, don su yabi su kuma yi godiya ga Ubangiji. Haɗe da busan ƙahoni, ganguna da sauran kayayyaki, suka tā da muryoyinsu cikin yabo ga Ubangiji suka rera,

    “Yana da kyau;

    ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.”

    Sai haikalin Ubangiji ya cika da girgije, 14 Firistoci ba su iya yin hidimarsu ba saboda girgijen, gama ɗaukakar Ubangiji ta cika haikalin Allah.

  67. 15 Yanzu, idanuna za su buɗu, kunnuwata kuma za su saurara ga addu’o’in da aka miƙa a wannan wuri. 16 Na zaɓi na kuma tsarkake wannan haikali saboda Sunana yă kasance a can har abada. Idanuna da kuma zuciyata kullum za su kasance a can.

  68. 5 Sai Ezra ya buɗe littafin. Dukan mutane kuwa suka gan shi domin yana tsaye a bisa fiye da inda mutane suke tsaye; yayinda ya buɗe littafin kuwa, dukan mutane suka miƙe tsaye. 6 Ezra ya yabi Ubangiji, Allah mai girma; dukan mutane kuwa suka tā da hannuwansu suka amsa, “Amin! Amin!” Sa’an nan suka sunkuya suka yi wa Ubangiji sujada da fuskokinsu har ƙasa.

  69. 25 Daga gare ka yabona yake zuwa cikin babban taro;

    a gaban waɗanda suke tsoronka zan cika alkawarina.

    26 Matalauta za su ci su ƙoshi;

    su da suke neman Ubangiji za su yabe shi,

    bari zukatanku su rayu har abada!

    27 Dukan iyakokin duniya

    za su tuna su kuma juya ga Ubangiji,

    kuma dukan iyalan al’ummai

    za su rusuna a gabansa,

    28 gama mulki na Ubangiji ne

    kuma yana mulki a bisa al’ummai.

  70. 3 Wa zai iya hawan tudun Ubangiji?

    Wa zai iya tsaya a wurinsa mai tsarki?

    4 Sai wanda yake da hannu mai tsabta da kuma tsabtar zuciya,

    wanda ba ya ba da ransa ga bautar gunki

    ko ya rantse bisa abin da yake ƙarya.

    5 Zai sami albarka daga Ubangiji

    da fiffitawa daga Allah Mai cetonsa.

    6 Irin tsaran waɗanda suke nemansa ke nan,

    waɗanda suke neman fuskarka, ya Allah na Yaƙub. Sela

  71. 1 Ku yi godiya ga Ubangiji, ku kira bisa sunansa;

    ku sanar a cikin al’ummai abin da ya yi.

    2 Ku rera gare shi, ku rera yabo gare shi;

    ku faɗa dukan abubuwan mamakin da ya aikata.

    3 Ku ɗaukaka a cikin sunansa mai tsarki;

    bari zukatan waɗanda suke neman Ubangiji su yi farin ciki.

    4 Ku sa rai ga Ubangiji da kuma ƙarfinsa;

    ku nemi fuskarsa kullum.

    5 Ku tuna da abubuwan mamakin da ya yi,

    mu’ujizansa, da kuma hukunce-hukuncen da ya zartar,

    6 Ya ku zuriyar Ibrahim bawansa,

    Ya ku ’ya’yan Yaƙub, zaɓaɓɓensa.

  72. 1 Ya Ubangiji, kai ne Allahna; zan ɗaukaka ka in kuma yabi sunanka,

    gama cikin cikakken aminci ka yi abubuwa masu banmamaki,

    abubuwan da aka shirya tun da.

  73. 6 Baƙin da suka miƙa kansu ga Ubangiji

    don su bauta masa,

    su kuma ƙaunaci sunan Ubangiji,

    waɗanda kuma suke yin masa sujada,

    duk waɗanda suka kiyaye Asabbaci ba tare da ƙazantar da shi ba

    suka kuma riƙe alkawarina kankan,

    7 waɗannan ne zan kai tsattsarkan dutsena

    in sa su yi farin ciki a gidana na addu’a.

    Hadayunsu na ƙonawa da sadakokinsu

    za su zama abin karɓa a bagadena;

    gama za a ce da gidana

    gidan addu’a domin dukan al’ummai.”

  74. 28 Sa’an nan Nebukadnezzar ya ce, “Yabo ya tabbata ga Allahn Shadrak, Meshak da Abednego wanda ya aiko da mala’ikansa ya ceci bayinsa da suka dogara matuƙa a gare shi, suka ki bin umarnin sarki kuma su na a shirye domin su ba da ransu da suka ƙi bauta ko su yi sujada ga wani allah sai dai Allahnsu.

  75. 5 ku ma, a matsayinku na duwatsu masu rai, ana gina ku ga zama gidan ruhaniya don ku zama tsattsarkar ƙungiyar firistoci, kuna miƙa hadayun ruhaniya, abin karɓa ga Allah ta wurin Yesu Kiristi.

  76. 10 Da masu ginin suka aza harsashin ginin haikalin Ubangiji, sai firistoci suka sa kayansu na firistoci suka riƙe ƙahonin busa, Lawiyawa (’ya’yan Asaf) kuwa suka riƙe kuge, suka yi shiri domin su rera yabo ga Ubangiji kamar yadda Dawuda Sarkin Isra’ila ya ba da umarni. 11 Suka rera waƙar yabo da godiya ga Ubangiji, suna cewa,

    “Shi nagari ne;

    ƙaunarsa kuwa ga Isra’ila har abada ce.”

    Dukan jama’a kuwa suka yabi Ubangiji da murya mai ƙarfi, domin an aza harsashin ginin gidan Ubangiji. 12 Amma tsofaffin firistoci, da Lawiyawa, da shugabannin iyalai da yawa, waɗanda dā suka ga yadda haikali na farko yake, suka fashe da kuka mai ƙarfi sa’ad da suka ga an aza harsashin ginin wannan haikali, yayinda waɗansu kuma suka yi ihu da farin ciki. 13 Ba wanda zai iya rabe tsakanin ihun farin ciki da na kuka, domin mutanen sun tā da murya sosai har aka ji su daga nesa.

  77. 2 Zan rusuna ta wajen haikalinka mai tsarki

    zan kuma yabi sunanka

    saboda ƙaunarka da amincinka,

    saboda ka ɗaukaka a bisa kome

    sunanka da kuma maganarka.

  78. 21 “Na ƙi, ina kuma ƙyamar bukukkuwanku na addini;

    ba na son ganin tarurrukanku.

    22 Ko da kun kawo mini hadayu na ƙonawa da kuma hadayu na hatsi,

    ba zan karɓa ba.

    Ko da kun kawo zaɓaɓɓun hadayu na zumunta,

    ba zan ɗauke su a bakin kome ba.

    23 Ku tashi daga nan da surutan waƙoƙinku!

    Ba zan saurari kaɗe-kaɗe da bushe bushenku ba.

    24 Amma bari gaskiya ta kwararo kamar kogi,

    adalci kuma kamar rafin da ba ya taɓa bushewa!

  79. 6 Da me zan zo a gaban Ubangiji

    in rusuna a gaban Maɗaukaki Allah?

    Shin, zan zo ne a gabansa da hadaya ta ƙonawa,

    da ɗan maraƙi bana ɗaya?

    7 Ubangiji zai ji daɗin hadayar raguna dubbai

    da kuma rafuffukan mai dubbai goma?

    Zan ba da ɗan farina ne don laifina,

    ko ’ya’yan jikina domin zunubin raina?

    8 Ya nuna maka, ya mutum, abin da yake mai kyau.

    Me Ubangiji yake bukata daga gare ka kuwa

    shi ne ka yi gaskiya ka so aikata jinƙai

    ka kuma yi tafiya da tawali’u a gaban Allah.

  80. 16 Na ji sai zuciyata ta buga,

    leɓunana sun yi rawa da jin murya;

    ƙasusuwana suka ruɓe,

    ƙafafuna kuma sun yi rawa.

    Duk da haka zan jira da haƙuri ga ranar bala’i

    ta zo a kan al’umman nan mai kawo mana hari.

    17 Ko da yake itace ɓaure bai tohu ba,

    ba kuma ’ya’ya a kuringar inabi,

    ko da yake zaitun bai ba da amfani ba,

    gonaki kuma ba su ba da abinci ba,

    ko da yake babu tumaki a garke,

    ba kuma shanu a turaku,

    18 duk da haka zan yi farin ciki da Ubangiji,

    zan yi murna da Allah Mai Cetona.

  81. 18 Ana bayyana fushin Allah daga sama a kan dukan rashin sanin Allah da kuma muguntar mutanen da suke danne gaskiya ta wurin muguntarsu, 19 gama abin da ana iya sani game da Allah a bayyane yake a gare su, domin Allah ya bayyana musu shi. 20 Gama tun halittar duniya halayen Allah marar ganuwa, madawwamin ikonsa da kuma allahntakarsa, ana iya ganinsu sarai, ana fahimtarsu ta wurin abubuwan da Allah ya halitta, domin kada mutane su sami wata hujja.

    21 Gama ko da yake sun san Allah, ba su ɗaukaka shi a matsayin Allah ko su gode masa ba, sai dai tunaninsu ya zama banza, zukatansu masu wauta kuma suka duhunta. 22 Ko da yake sun ɗauka su masu hikima ne, sai suka zama wawaye, 23 suka kuma yi musayar ɗaukakar Allah marar mutuwa da siffofin da aka ƙera su yi kama da mutum mai mutuwa da tsuntsaye da dabbobi da kuma halittu masu ja da ciki.

    24 Saboda haka Allah ya yashe su ga mugayen sha’awace-sha’awacen zukatansu ga fasikanci don a ƙasƙantar da jikunansu ga yin abin kunya. 25 Sun sauya gaskiyar Allah da ƙarya, suka kuma yi wa abubuwan da aka halitta sujada suna bauta musu a maimakon Mahalicci, wanda ake yabo har abada. Amin.

  82. 26 Me za mu ce ke nan ’yan’uwa? Sa’ad da kuka taru, wani yakan yi waƙa, wani koyarwa, wani wahayi, wani yin magana da wani harshe, wani kuma fassara. Dole ne a yi duka don gina ikkilisiya. 27 In kuwa waɗansu za su yi magana a wani harshe, to, kada su fi mutum biyu ko uku, kuma a yi bi da bi, wani kuma yă fassara. 28 In babu mai fassara, sai mai magana yă yi shiru a cikin ikkilisiya, yă yi wa kansa magana da kuma Allah.

    29 Annabawa biyu ko uku za su iya yin magana, sauran kuma sai su auna a hankali abin da aka faɗa. 30 In kuma wahayi ya zo wa wani da yake zaune, sai mai magana na farko yă yi shiru. 31 Dukanku kuna iya yin annabci bi da bi, domin kowa yă sami koyarwa da ƙarfafawa. 32 Ruhohin annabawa kuwa suna ƙarƙashin sarrafawar annabawa. 33 Gama Allah, ba Allah mai sa rikicewa ba ne, sai dai mai salama. Kamar yadda yake a dukan ikkilisiyoyi na tsarkaka.

    34 Ya kamata mata su zauna shiru a cikin ikkilisiyoyi. Ba su da izinin yin magana, sai dai su yi biyayya yadda Doka ta faɗi. 35 In suna so su yi tambaya game da wani abu, ya kamata su tambayi mazansu a gida, domin abin kunya ne mace tă yi magana a cikin ikkilisiya.

    36 Shin, a kanku ne maganar Allah ta fara? Ko kuma a gare ku ne kaɗai ta iso? 37 In wani yana tsammani shi annabi ne, ko yana da baiwar ruhaniya, bari yă gane cewa abin da nake rubuta muku umarnin Ubangiji ne. 38 In ya ƙi kula da wannan, shi ma sai a ƙi kula da shi.

    39 Saboda haka ’yan’uwana, ku yi marmarin yin annabci, kada kuma ku hana magana da harsuna. 40 Sai dai a yi kome daidai da kuma cikin tsari.

  83. 25 Gama Ubangiji mai girma ne ya kuma cancanci yabo;

    dole a ji tsoronsa fiye da dukan alloli.

  84. 3 Duk da haka kana a kursiyi a matsayin Mai Tsarkin nan;

    kai ne yabon Isra’ila.

  85. Waƙa ce. Zabura ta ’ya’yan Kora maza.

    1 Ubangiji mai girma ne, kuma mafificin yabo,

    a birnin Allahnmu, dutsensa mai tsarki.

  86. 9 Zan yabe ka, ya Ubangiji, a cikin al’ummai;

    zan rera game da kai a cikin mutane.

  87. 4 Rera wa Allah, rera yabo ga sunansa,

    ku ɗaukaka wanda yake hawa a kan gizagizai;

    sunansa Ubangiji ne, ku kuma yi farin ciki a gabansa.

    5 Uba ga marayu, mai kāre gwauraye,

    shi ne Allah a mazauninsa mai tsarki.

  88. 8 Bakina ya cika da yabonka,

    ina furta darajarka dukan yini.

  89. 1 Yabi Ubangiji.

    Yabi Ubangiji daga sammai,

    yabe shi a bisa sammai.

    2 Yabe shi, dukanku mala’ikunsa,

    yabe shi, dukanku rundunarsa na sama.

    3 Yabe shi, rana da wata,

    yabe shi, dukanku taurari masu haskakawa.

    4 Yabe shi, ku bisa sammai

    da kuma ku ruwan bisa sarari.

    5 Bari su yabi sunan Ubangiji,

    gama ya umarta aka kuwa halicce su.

  90. 37 Yesu ya amsa ya ce, “ ‘Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka da dukan ranka da kuma dukan hankalinka.’ 38 Wannan, ita ce doka ta fari da kuma mafi girma. 39 Ta biye kuma kamar ta farkon take. ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’