65 Bible Verses About Music
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
15 Ku bar salamar Kiristi tă yi mulki a zukatanku, da yake a matsayin gaɓoɓin jiki ɗaya an kira ku ga salama. Ku zama masu godiya. 16 Ku bar maganar Kiristi ta zauna a cikinku a yalwace yayinda kuke koya, kuna kuma yi wa juna gargaɗi da dukan hikima, da kuma yayinda kuke waƙoƙin zabura, waƙoƙi da waƙoƙin ruhaniya tare da godiya a zukatanku ga Allah. 17 Kuma ko mene ne kuke yi, ko cikin magana ko cikin ayyuka, ku yi shi duka a cikin sunan Ubangiji Yesu, kuna yin godiya ga Allah Uba ta wurinsa.
-
18 Kada ku bugu da ruwan inabi, wanda yake kai ga lalaci. A maimako haka, ku cika da Ruhu. 19 Ku yi zance da juna cikin zabura, da waƙoƙi, da kuma waƙoƙin ruhaniya. Ku rera, ku kuma yi kiɗe-kiɗe a zuciyarku ga Ubangiji. 20 Kullum ku dinga yin amfani da sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, kuna gode wa Allah Uba a kome.
21 Ku yi biyayya da juna saboda bangirmar da kuke nuna wa Kiristi.
-
6 Yayinda mutane suke dawowa gida bayan da Dawuda ya kashe Bafilistin, mata suka fito daga dukan biranen Isra’ila don su sadu da Sarki Shawulu, suna waƙoƙi da raye-raye masu farin ciki, da ganguna da sarewa. 7 Suna rawa suna cewa,
“Shawulu ya kashe dubbansa,
Dawuda kuwa ya kashe dubun dubbai.”
-
1 Yabi Ubangiji.
Yabi Allah a cikin wurinsa mai tsarki;
yabe shi a cikin sammai na ikonsa.
2 Yabe shi saboda ayyukansa masu iko;
yabe shi saboda mafificin girmansa.
3 Yabe shi da ƙarar kakaki,
yabe shi da garaya da molo,
4 yabe shi da ganga kuna taka rawa,
yabe shi da kayan kiɗi na tsirkiya kuna kuma busa,
5 yabe shi da kuge mai ƙara,
yabe shi da kuge masu ƙara sosai.
6 Bari kowane abu mai numfashi yă yabi Ubangiji.
Yabi Ubangiji.
-
4 da akwatin alkawarin Allah yake ciki. Ahiyo kuwa yana tafiya a gaban Abinadab. 5 Dawuda da dukan gidan Isra’ila suka yi biki sosai da dukan ƙarfinsu a gaban Ubangiji, da waƙoƙi, da molaye, da garayu, da ganguna, da kacau-kacau da kuma kuge.
-
8 Na tara wa kaina azurfa da zinariya, ina da ma’ajin sarakuna da yankuna. Na samo wa kaina mawaƙa mata da maza, da dukan irin matan da kowane namiji zai so.
-
14 To, fa, Ruhun Ubangiji ya riga ya rabu da Shawulu, sai mugun ruhu daga Ubangiji ya soma ba shi wahala.
15 Ma’aikatan Shawulu suka ce masa, “Duba, ga mugun ruhu daga Allah yana ba ka wahala. 16 Ranka yă daɗe, muna so ka ba mu izini mu tafi, mu nemo wanda ya iya kiɗan molo, domin duk sa’ad da mugun ruhun nan daga Allah ya tashi, sai yă kaɗa molon don hankalinka yă kwanta.”
17 Saboda haka Shawulu ya ce wa ma’aikatansa, “Ku nemo wanda ya iya kiɗan molo sosai ku kawo mini.”
18 Ɗaya daga cikin bayin ya ce, “Na san wani yaro, ɗan Yesse na Betlehem, ya iya kiɗan molo, yana da hikima, shi kuma ya iya yaƙi. Ya iya magana, ga shi kuma kyakkyawa, Ubangiji kuwa yana tare da shi.”
19 Sai Shawulu ya aiki manzanni zuwa wurin Yesse ya ce, “Ka aiko mini da ɗanka Dawuda wanda yake kiwon tumaki.” 20 Saboda haka Yesse ya ɗauki jaki tare da burodi da ruwan inabi da ɗan ƙarami bunsuru ya ba wa ɗansa Dawuda yă kai wa Shawulu.
21 Dawuda ya isa wurin Shawulu ya shiga hidimarsa. Shawulu kuwa ya so shi ƙwarai da gaske. Dawuda ya zama ɗaya daga cikin masu sanya sulke. 22 Sa’an nan Shawulu ya aika saƙo wurin Yesse cewa, “Ka bar Dawuda yă yi mini hidima domin ina jin daɗinsa ƙwarai.”
23 Duk lokacin da ruhun nan daga Allah ya sauko a kan Shawulu, sai Dawuda yă ɗauki molonsa yă kaɗa. Sa’an nan sauƙi yă zo wa Shawulu, mugun ruhu kuma yă rabu da shi.
-
11 Kaiton waɗanda suke tashi da sassafe
don su nufi wurin shaye-shaye,
waɗanda suke raba dare
har sai sun bugu da ruwan inabi.
12 Suna kaɗa garaya, da molaye a bukukkuwansu,
ganguna da busa da ruwan inabi,
amma ba su kula da ayyukan Ubangiji ba,
ba sa biyayya ga aikin hannuwansa.
-
4 Kuna kwanciya a kan gadajen da aka yi musu shimfiɗar hauren giwa
kuna mimmiƙe a kan kujerunku.
Kuna cin naman ƙibabbun raguna
da na ƙosassun ’yan maruƙa.
5 Kuna kaɗa molayenku yadda Dawuda ya yi
kuna ƙirƙiro waƙoƙi a kan kayan kaɗe-kaɗe.
6 Da manyan kwanoni kuke shan ruwan inabi
kuna kuma shafa mai mafi kyau,
amma ba kwa baƙin ciki game da kangon da Yusuf ya zama.
-
25 Sarki Hezekiya ya ajiye Lawiyawa a cikin haikalin Ubangiji tare da ganguna, garayu da molaye, yadda Dawuda da Gad mai duba na sarki da kuma annabi Natan suka tsara. Ubangiji ne ya umarta wannan ta wurin annabawansa. 26 Saboda haka Lawiyawa suka tsaya a shirye tare da kayan kiɗin Dawuda, firistoci kuma tare da ƙahoninsu.
27 Hezekiya ya ba da umarni a miƙa hadaya ta ƙonawa a kan bagade. Yayinda aka fara miƙawa, ana rerawa ga Ubangiji, tare da bushe-bushe da kiɗe-kiɗen kayan waƙa na Dawuda sarkin Isra’ila. 28 Dukan taron suka durƙusa suka yi sujada, yayinda mawaƙa suke rerawa, ana kuma busa ƙahoni, dukan wannan ya ci gaba sai da aka gama miƙa hadaya ta ƙonawa.
29 Sa’ad da aka gama miƙawa, sai sarki da mutanen da suke tare da shi suka durƙusa suka yi sujada. 30 Sarki Hezekiya da fadawansa suka umarci Lawiyawa su yabi Ubangiji da kalmomin Dawuda da na Asaf mai duba. Saboda haka suka rera yabai da murna, suka sunkuyar da kawunansu suka yi sujada.
-
5 “Bayan wannan, za ka tafi Gebiya ta Allah, inda sansanin Filistiyawa yake. Kana shiga garin, za ka sadu da jerin gwanon annabawa suna gangarowa daga tudu, ana kaɗa garaya, ana bugan ganguna, ana hura sarewa, ana kuma bugan molo, a gabansu, su kuma za su yi ta annabci.
-
8 Bayan ya karɓa, sai halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan nan ashirin da huɗu suka fāɗi ƙasa a gaban Ɗan Ragon. Kowannensu yana da garaya kuma suna riƙe da kaskon zinariya cike da turare, waɗanda suke addu’o’in tsarkaka. 9 Suka rera sabuwar waƙa,
“Ka cancanci ka karɓi naɗaɗɗen littafin
ka kuma buɗe hatimansa,
domin an kashe ka,
da jininka kuma ka sayi mutane wa Allah,
daga kowace kabila da harshe da mutane da kuma al’umma.
10 Ka mai da su masarauta da kuma firistoci, don su yi wa Allahnmu hidima,
kuma za su yi mulki a duniya.”
11 Sai na duba na kuma ji muryar mala’iku masu yawa, yawansu kuwa ya kai dubu dubbai, da kuma dubu goma sau dubu goma. Suka kewaye kursiyin da halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan nan. 12 Da babbar murya suka rera,
“Macancanci ne Ɗan Ragon nan da aka kashe,
don yă sami iko da wadata da hikima da ƙarfi
da girma da ɗaukaka da kuma yabo!”
13 Sa’an nan na ji kowace halitta a sama da ƙasa da ƙarƙashin ƙasa da kuma bisan teku, da kome da yake cikinsu yana rerawa,
“Gare shi mai zama a kan kursiyin da kuma ga Ɗan Ragon
yabo da girma da ɗaukaka da iko,
sun tabbata har abada abadin!”
14 Sai halittu huɗun nan masu rai suka ce, “Amin”, dattawan kuma suka fāɗi suka yi sujada.
-
3 Aka ƙidaya Lawiyawan da suke ’yan shekaru talatin da haihuwa ko fiye, suka kai wajen mutum dubu talatin da takwas. 4 Dawuda ya ce, “Cikin waɗannan, dubu ashirin da huɗu za su lura da aikin haikalin Ubangiji, dubu shida su zama manyan na ma’aikata da alƙalai. 5 Dubu huɗu su zama matsaran ƙofofi, dubu huɗu kuma su yabi Ubangiji da kayayyakin bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe waɗanda na tanada saboda wannan manufa.”
-
1 Ku rera da farin ciki ga Ubangiji ku adalai;
daidai ne masu gaskiya su yabe shi.
2 Ku yabi Ubangiji da garaya;
ku yi kiɗi gare shi da molo mai tsirkiya goma.
3 Ku rera masa sabuwar waƙa;
ku yi kiɗi da gwaninta, ku kuma yi sowa don farin ciki.
4 Gama maganar Ubangiji daidai ne da kuma gaskiya;
yana da aminci cikin kome da yake yi.
-
4 Sai mai shela ya daga murya da ƙarfi ya ce, “Wannan shi ne abin da aka umarce ku ku yi, ya ku mutane da al’umma da kowane yare. 5 Da zarar kuka ji karar ƙaho, da sarewa, da garaya da goge da molo da algaita da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe ku rusuna ku yi sujada ga wannan gunkin da sarki Nebukadnezzar ya kafa. 6 Duk wanda bai rusuna ya yi sujada ba, nan take za a jefa shi a cikin tendarun wuta.”
7 Saboda haka, da zarar suka ji karar ƙaho, da sarewa, garaya da goge da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe da kowane irin kaɗe-kaɗe kowane mutum da ko wace al’umma da kowane irin yare suka sunkuya suka yi sujada ga wannan siffa ta zinariya da sarki Nebukadnezzar ya kafa.
-
19 Sa’ad da dawakai, kekunan yaƙi da mahayan dawakan Fir’auna suka shiga cikin teku, Ubangiji ya mayar da ruwan teku a kansu, amma Isra’ilawa suka wuce a cikin teku a busasshiyar ƙasa. 20 Sa’an nan Miriyam annabiya, ’yar’uwar Haruna ta ɗauki ganga a hannunta, dukan mata kuwa suka bi ta, da ganguna suna rawa. 21 Miriyam ta yi musu waƙa.
“Ku rera ga Ubangiji
gama ya ci gawurtacciyar nasara.
Doki da mahayi,
ya jefa cikin teku.”
-
4 Ya sa Lawiyawa su yi hidima a gaban akwatin alkawarin Ubangiji, su ɗaukaka, su gode, su kuma yabi Ubangiji, Allah na Isra’ila. 5 Asaf shi ne babba, sai Zakariya na biye, sa’an nan Ya’aziyel, Shemiramot, Yehiyel, Mattitiya, Eliyab, Benahiya, Obed-Edom da Yehiyel. Su ne za su kaɗa molaye, da garayu, Asaf kuwa zai buga ganguna, 6 Benahiya da Yahaziyel firistoci za su busa ƙahoni kullum a gaban akwatin alkawarin Allah.
7 A wannan rana, da farko, Dawuda ya sa Asaf da ’yan’uwansa su rera wannan zabura ta yabo ga Ubangiji.
8 Ku yi godiya ga Ubangiji, ku yi shelar sunansa;
ku sanar a cikin al’ummai abin da ya yi.
9 Ku rera gare shi, ku rera yabo gare shi;
ku faɗa dukan ayyukan banmamakinsa.
-
4 Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya,
ku ɓarke da waƙa ta murna tare da kiɗi;
5 ku yi kiɗi ga Ubangiji da garaya,
da garaya da ƙarar rerawa,
6 tare da bushe-bushe da karar ƙahon rago,
ku yi sowa don farin ciki a gaban Ubangiji, Sarki.
7 Bari teku su yi ruri, da kuma kome da yake cikinsa,
duniya da kuma kome da yake cikinta.
8 Bari koguna su tafa hannuwansu,
bari duwatsu su rera tare don farin ciki;
9 bari su rera a gaban Ubangiji,
gama yana zuwa domin yă hukunta duniya.
Zai hukunta duniya da adalci
mutane kuma cikin gaskiya.
-
25 Wajen tsakar dare Bulus da Sila suna addu’a suna rera waƙoƙi ga Allah, sauran ’yan kurkuku kuwa suna sauraronsu. 26 Ba zato ba tsammani sai aka yi wata babbar girgizar ƙasa har tushen ginin kurkukun ya jijjiga. Nan da nan sai duk ƙofofin kurkukun suka bubbuɗe, sarƙoƙin kowa kuma suka ɓaɓɓalle.
-
21 “Na ƙi, ina kuma ƙyamar bukukkuwanku na addini;
ba na son ganin tarurrukanku.
22 Ko da kun kawo mini hadayu na ƙonawa da kuma hadayu na hatsi,
ba zan karɓa ba.
Ko da kun kawo zaɓaɓɓun hadayu na zumunta,
ba zan ɗauke su a bakin kome ba.
23 Ku tashi daga nan da surutan waƙoƙinku!
Ba zan saurari kaɗe-kaɗe da bushe bushenku ba.
24 Amma bari gaskiya ta kwararo kamar kogi,
adalci kuma kamar rafin da ba ya taɓa bushewa!
-
1 Sai na duba, can a gabana kuwa ga Ɗan Rago, tsaye a kan Dutsen Sihiyona, tare da shi akwai kuma mutane 144,000 waɗanda suke da sunansa da sunan Ubansa a rubuce a goshinsu. 2 Sai na ji ƙara daga sama kamar motsin ruwaye masu gudu, kamar kuma tsawa. Ƙarar da na ji ta yi kamar ta masu garaya da suke kiɗin garayarsu. 3 Suka kuwa rera sabuwar waƙa a gaban kursiyin da kuma a gaban halittu huɗun nan masu rai, da kuma a gaban dattawa. Ba wanda ya iya koyon waƙar sai mutanen nan 144,000 da aka fansa daga duniya.
-
1 A bakin kogunan Babilon muka zauna muka yi kuka
sa’ad da muka tuna da Sihiyona.
2 A can a kan rassan itatuwa
muka rataye garayunmu,
3 gama a can masu kamunmu suka sa mu yi waƙoƙi,
masu ba mu azaba suka nema waƙoƙin farin ciki;
suka ce, “Ku rera mana ɗaya daga cikin waƙoƙin Sihiyona!”
4 Yaya za mu rera waƙoƙin Ubangiji
a baƙuwar ƙasa?
5 In na manta da ke, ya Urushalima,
bari hannuna na dama manta da iyawarsa.
6 Bari harshena yă manne wa rufin bakina
in ban tuna da ke ba,
in ban so Urushalima
farin cikin mafi girma ba.
-
8 Kaɗe-kaɗen garayu sun yi shiru,
surutun masu murna ya daina,
garayan farin ciki ya yi shiru.
9 Babu sauran shan ruwan inabi suna rera waƙa;
barasa ya zama da ɗaci ga masu shanta.
-
1 Sa’an nan Musa da Isra’ilawa suka rera wannan waƙa ga Ubangiji suka ce,
“Zan rera waƙa ga Ubangiji
gama an ɗaukaka shi ƙwarai.
Doki da mahayinsa
ya jefa su cikin teku.
2 “Ubangiji ne ƙarfina da mafakata,
ya zama cetona.
Shi Allahna ne, zan yabe shi.
Allah na kakana, zan ɗaukaka shi.
-
13 Akwai waninku da yake shan wahala? Ya kamata yă yi addu’a. Akwai wani mai murna? Sai yă rera waƙoƙin yabo.
-
1 Ku zo, bari mu rera don farin ciki ga Ubangiji;
bari mu yi sowa da ƙarfi ga Dutsen cetonmu.
2 Bari mu zo gabansa da godiya
mu rera gare shi da kiɗi da waƙa.
-
30 Yefta kuwa ya yi wa’adi da Ubangiji ya ce, “In ka ba da Ammonawa a hannuwana, 31 duk abin da ya fara fitowa daga ƙofar gidana don yă tarye ni, sa’ad da na komo daga yaƙi da Ammonawa, zai zama na Ubangiji, zan miƙa shi hadaya ta ƙonawa.”
32 Sa’an nan Yefta ya haye zuwa wajen Ammonawa don yaƙi da su. Ubangiji kuwa ya ba da su a hannuwansa. 33 Ya hallaka birane ashirin tun daga Arower zuwa yankin Minnit, har zuwa Abel-Keramim. Haka Isra’ila ta cinye Ammonawa ƙaf.
34 Sa’ad da Yefta ya komo gida a Mizfa, wa ya fito yă tarye shi, ’yarsa tilo, tana rawa kiɗin ganguna! Ita ce kaɗai ’yarsa. Ban da ita ba shi da ɗa ko ’ya. 35 Da ya gan ta, sai ya yayyage tufafinsa ya yi kuka ya ce, “Kaito! ’Yata! Kin karya mini gwiwa, kuma na lalace, domin na yi wa’adi ga Ubangiji da ba zan iya in karya ba.”
-
6 Dawuda da dukan Isra’ilawa tare da shi suka tafi Ba’ala na Yahuda (Kiriyat Yeyarim) don su haura daga can su kawo akwatin alkawarin Allah Ubangiji, wanda yake zama tsakanin kerubobi, akwatin alkawarin da ake kira da Sunan.
7 Suka ɗauki akwatin alkawarin Allah daga gidan Abinadab a kan sabon keken shanu, Uzza da Ahiyo ne suke lura da shi. 8 Dawuda da dukan Isra’ilawa suka yi shagali da dukan ƙarfinsu a gaban Allah, tare da waƙoƙi da garayu, molaye, ganguna, kuge da ƙahoni.
-
43 A rana ta uku kuma suka miƙa manyan hadayu, suna farin ciki domin Allah ya ba su farin ciki mai girma. Mata da yara suka yi farin ciki su ma. An ji ƙarar farin ciki da ake yi a Urushalima daga nesa.
-
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit. Ta Asaf.
1 Ku rera don farin ciki ga Allah ƙarfinmu;
ku yi sowa ga Allah na Yaƙub!
2 Ku fara kaɗe-kaɗe, ku buga ganga,
ku kaɗa garaya da molo masu daɗi.
3 Ku busa ƙahon rago a Sabon Wata,
da kuma sa’ad da wata ya kai tsakiya, a ranar Bikinmu;
4 wannan ƙa’ida ce domin Isra’ila,
farilla ta Allah na Yaƙub.
-
12 Sarki ya yi amfani da almug don yă yi kayan ado wa haikalin Ubangiji da kuma don fadan sarki, don kuma yă yi molaye, da garayu saboda mawaƙa. Ba a taɓa yin jigilar katakon almug ko a gani irin yawan katakai haka ba har wa yau.)
-
2 Sai na ga abin da ya yi kamar tekun gilashi gauraye da wuta kuma tsaye kusa da teku, waɗanda suka ci nasara bisan dabbar da siffarta da bisan lambar sunanta. Suna riƙe da garayu waɗanda Allah ya ba su 3 suka rera waƙar Musa bawan Allah da kuma waƙar Ɗan Ragon suna cewa,
“Ayyukanka suna da girma da kuma banmamaki,
ya Ubangiji Maɗaukaki.
Al’amuranka suna da aminci da kuma gaskiya,
ya Sarkin zamanai.
4 Wane ne ba zai ji tsoronka,
yă kuma kawo ɗaukaka ga sunanka ba, ya Ubangiji?
Gama kai kaɗai ne mai tsarki.
Dukan al’ummai za su zo
su yi sujada a gabanka,
gama an bayyana ayyukan adalcinka.”
-
27 To, fa, Dawuda yana saye da kyakkyawar rigar lilin, kamar yadda dukan Lawiyawa waɗanda suke ɗaukar akwatin alkawarin suka sa, da kuma yadda mawaƙa, da Kenaniya, wanda yake bi da waƙar mawaƙan ya sa. Dawuda kuma ya sa efod lilin. 28 Sai dukan Isra’ila suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji da sowa, da ƙarar ƙahonin raguna da busan ƙahoni, da na ganguna, suna kuma kaɗa molaye da garayu.
-
12 Sa’ad da Ataliya ta ji surutun mutane suna gudu suna yabon sarki, sai ta tafi wurinsu a haikalin Ubangiji. 13 Ta duba, a can kuwa ga sarki, tsaye kusa da ginshiƙinsa a mashigi. Manyan sojoji da masu bushe-bushe suna kusa da sarki, dukan mutanen ƙasar kuwa suna farin ciki suna busa ƙahoni, mawaƙa kuma da kayan kiɗi suna bi da yabo. Sai Ataliya ta yage rigunanta ta yi ihu tana cewa, “Cin amanar ƙasa! Cin amanar ƙasa!”
-
31 Garayata ta zama ta makoki,
sarewata kuma ta zama ta kuka.
-
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da salon “Lili.” Na ’ya’yan Kora maza. Maskil Waƙar Aure.
1 Zuciyata ta cika da kyakkyawan kan magana
yayinda nake rera ayoyina wa sarki;
harshena ne alƙalamin ƙwararren marubuci.
-
22 Zan yabe ka da garaya
saboda amincinka, ya Allah;
zan rera yabo gare ka da molo,
Ya Mai Tsarki na Isra’ila.
23 Leɓunana za su yi sowa don farin ciki
sa’ad da na rera yabo gare ka,
ni, wanda ka fansa.
-
18 Sa’an nan sarki ya koma fadarsa ya kwana bai ci ba, kuma babu wata liyafar da aka kawo masa. Ya kuma kāsa barci.
-
30 Da suka rera waƙa, sai suka fita, suka tafi Dutsen Zaitun.
-
7 Zuciyata tana nan daram, ya Allah,
zuciyata tana nan daram;
zan rera in kuma yi kaɗe-kaɗe.
8 Ka farka, raina!
Ku farka, garaya da molo!
Zan sa safe yă farka.
9 Zan yabe ka, ya Ubangiji, a cikin al’ummai;
zan rera game da kai a cikin mutane.
10 Gama ƙaunarka mai girma ce, tana kaiwa sammai;
amincinka na kaiwa sarari.
11 Bari a ɗaukaka ka, ya Allah, bisa sammai;
bari ɗaukakarka ta kasance a dukan duniya.
-
Zabura ce. Waƙa ce. Domin ranar Asabbaci.
1 Yana da kyau a yabi Ubangiji
a kuma yi kiɗi ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka,
2 don a yi shelar ƙaunarka da safe
amincinka kuma da dare,
3 da kiɗin molo mai tsirkiya goma
da kuma ƙarar garaya.
-
1 Yabi Ubangiji.
Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji,
yabonsa a cikin taron tsarkaka.
2 Bari Isra’ila su yi farin ciki da Mahaliccinsu;
bari mutanen Sihiyona su yi murna da Sarkinsu.
3 Bari su yabi sunansa tare da rawa
suna kuma yin kiɗi gare shi da ganga da garaya.
-
23 Da Yesu ya shiga gidan mai mulkin ya ga masu busan sarewa da taro mai hayaniya, 24 sai ya ce, “Ku ba da wuri. Ai, yarinyar ba tă mutu ba, tana barci ne.” Amma suka yi masa dariya.
-
8 Da Yoshuwa ya gama yin wa mutane magana, sai firistoci guda bakwai waɗanda suke riƙe da ƙahoni guda bakwai a gaban Ubangiji suka sha gaba suna busa ƙahoninsu, akwatin alkawari kuwa yana biye da su.
-
6 Firistoci suka ɗauki matsayinsu, haka kuma Lawiyawa suka tsaya a matsayinsu riƙe da kayansu na bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe na Ubangiji, waɗanda Sarki Dawuda ya yi domin yabon Ubangiji. An yi amfani da su sa’ad da ake godiya, ana kuma cewa, “Ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.” Kurkusa da Lawiyawa, firistoci suka busa ƙahoninsu, dukan Isra’ila kuwa suna a tsaye.
-
7 Rera wa Ubangiji waƙar godiya;
ku kada garaya ga Allahnmu.
-
12 “Ɗan mutum, ka yi makoki domin sarkin Taya ka kuma ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
“ ‘Ka kasance hatimin cikakke,
cike da hikima da cikakke a kyau.
13 Ka kasance a Eden,
a lambun Allah;
aka yi maka ado da kowane dutse mai daraja,
yakutu, tofaz, da zumurrudu,
kirisolit, onis da yasfa,
saffaya, turkuwoyis da beril.
Tsare-tsare da shirye-shiryenka an yi su da zinariya ne;
a ranar da aka halicce ka an shirya su.
14 An shafe ka kamar kerub mai tsaro,
gama haka na naɗa ka.
Kana a tsattsarkan dutsen Allah;
ka yi tafiya a tsakiyar duwatsun wuta.
15 Ka kasance marar laifi cikin dukan hanyoyinka
daga ranar da aka halicce ka
sai da aka sami mugunta a cikinka.
-
11 An yi ƙasa da dukan alfarmarka zuwa kabari,
tare da surutan garayunka;
tsutsotsi sun bazu a ƙarƙashinka
tsutsotsi kuma suka rufe ka.
-
13 Zan kawo ƙarshen waƙoƙinki masu surutu, ba kuwa za a ƙara jin kaɗe-kaɗen garayunki ba.
-
26 Da suka rera waƙa, sai suka fita, suka tafi Dutsen Zaitun.
-
15 To, me zan yi? Akwai lokutan da zan yi addu’a da ruhuna; akwai kuma lokutan da zan yi addu’a da hankalina. Wani lokaci ya kamata in yi waƙa da ruhuna, a wani lokacin kuma in yi waƙa da hankalina.
-
1 A wannan rana ce Debora da Barak ɗan Abinowam suka rera wannan waƙa.
2 “Sa’ad da ’ya’yan sarki a Isra’ila suka yi jagora,
sa’ad da mutane suka niyya su ba da kansu,
suna yabon Ubangiji!
3 “Ya sarakuna, ku ji! Ku saurara, ku masu mulki!
Zan yi waƙa ga Ubangiji, zan yi waƙa;
zan yi kaɗe-kaɗe ga Ubangiji, Allah na Isra’ila.
-
22 Kenaniya, shugaban Lawiyawa, shi ne mai bi da waƙoƙi. Wannan hakkinsa ne, gama shi gwani ne a wannan fanni.
-
64 Yawan jama’ar duka ya kai mutum 42,360, 65 ban da bayinsu maza da mata 7,337; suna kuma da mawaƙa maza da mata 200.
-
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ga muryar “Mutuwar Ɗa.” Zabura ta Dawuda.
1 Zan yabe ka, ya Ubangiji, da dukan zuciyata;
zan faɗa dukan abubuwan banmamakinka.
2 Zan yi murna in kuma yi farin ciki a cikinka;
zan rera yabo ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka.
-
Waƙa ce. Zabura ta Dawuda.
1 Zuciyata tsayayyiya ce, ya Allah;
zan rera in kuma yi kiɗi da dukan raina.
2 Ku farka, garaya da molo!
Zan farkar da rana.
3 Zan yabe ka, ya Ubangiji, a cikin al’ummai;
zan rera game da kai cikin mutane.
4 Gama ƙaunarka da girma take, bisa fiye da sammai;
amincinka ya kai sarari.
-
9 Zan rera sabuwar waƙa gare ka, ya Allah;
a kan molo mai tsirkiya goma zan yi maka kiɗi,
-
15 A wannan lokaci za a manta da Taya har shekaru saba’in, tsawon rayuwar sarki. Amma a ƙarshen waɗannan shekaru saba’in, zai zama wa Taya kamar yadda yake a waƙar karuwa cewa,
16 “Ɗauki garaya, ki ratsa birni,
Ya ke karuwar da aka manta da ita;
kaɗa garaya da kyau, ki rera waƙoƙi masu yawa,
saboda a tuna da ke.”
-
33 Zan rera ga Ubangiji dukan raina;
zan rera yabo ga Allahna muddin ina raye.
34 Bari tunanina yă gamshe shi,
yayinda nake farin ciki a cikin Ubangiji.
-
10 An ɗauke farin ciki da murna daga gonakin itatuwa masu ’ya’ya;
babu wanda yake rerawa ko yake sowa a cikin gonakin inabi;
babu wanda yake matsin ruwan inabi a wuraren matsi,
gama na kawo ƙarshen yin sowa.
-
1 In ina iya yin magana da harsunan mutane, da na mala’iku, amma ba ni da ƙauna, na zama kamar kuge mai yawan ƙara, ko kuma ƙararrawa mai amo kawai.
-
4 Ka sa firistoci guda bakwai su riƙe ƙahoni raguna su kasance a gaban akwatin alkawari. A rana ta bakwai sai ku zaga birnin sau bakwai, firistocin suna busa ƙahoni. 5 Sa’ad da kuka ji sun ɗauki dogon lokaci suna busa ƙaho, sai mutane gaba ɗaya su tā da murya su yi ihu da ƙarfi; katangar birnin kuwa za tă rushe, sai sojoji su haura, ko wanne yă nufi inda ya fuskanta kai tsaye.”
-
29 Allah ya ba Solomon hikima da hangen nesa mai girma, da kuma fāɗin fahimta marar iyaka, kamar yashi a bakin teku. 30 Hikimar Solomon ta fi hikimar mutanen Gabas, ta kuma fi dukan hikimar Masar girma. 31 Ya fi kowane mutum hikima, har da Etan dangin Ezra ma. Yana da hikima fiye da Heman, Kalkol da Darda, ’ya’yan Mahol maza. Sunansa ya bazu ko’ina a ƙasashen da suke kewaye. 32 Ya yi karin magana dubu uku. Waƙoƙinsa kuwa sun kai dubu ɗaya da biyar.
-
6 To, ’yan’uwa, a ce na zo wurinku ina kuma yin magana da waɗansu harsuna, amfanin me zan yi muku in ban zo muku da wani bayani ko sani ko annabci, ko kuma kalmar koyarwa ba? 7 Abubuwan nan marasa rai ma da sukan yi ƙara, kamar su algaita ko molo, in muryarsu ba tă fita sosai ba, yaya wani zai san abin da ake busawa ko kaɗawa? 8 Haka ma in ba a busa ƙaho sosai ba, wa zai yi shirin yaƙi?
-
22 Ba za a ƙara jin
ƙarar kiɗin masu garaya da muryar mawaƙa, da na masu bushe-bushe, da na masu busan ƙaho
a cikinki ba.
Ba za a ƙara samun ma’aikaci na kowace irin sana’a
a cikinki kuma ba.
Ba za a ƙara jin ƙarar dutsen niƙa
a cikinki kuma ba.
Shows Read in context, Share and Copy.