55 Bible Verses About Drunkenness

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Drunkenness
  1. 15 Sai ku yi hankali sosai da yadda kuke rayuwa, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai kamar masu hikima. 16 Ku kuma yi matuƙar amfani da kowane zarafi, don kwanakin nan mugaye ne. 17 Saboda haka kada ku zama wawaye, sai dai ku fahimci ko mene ne nufin Ubangiji. 18 Kada ku bugu da ruwan inabi, wanda yake kai ga lalaci. A maimako haka, ku cika da Ruhu. 19 Ku yi zance da juna cikin zabura, da waƙoƙi, da kuma waƙoƙin ruhaniya. Ku rera, ku kuma yi kiɗe-kiɗe a zuciyarku ga Ubangiji. 20 Kullum ku dinga yin amfani da sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, kuna gode wa Allah Uba a kome.

    21 Ku yi biyayya da juna saboda bangirmar da kuke nuna wa Kiristi.

  2. 1 Ruwan inabi mai yin ba’a ne, barasa kuma mai rikici ne;

    duk wanda suka sa ya kauce marar hikima ne.

  3. 29 Wa yake wayyo? Wa yake baƙin ciki?

    Wa yake neman fada? Wa yake gunaguni?

    Wa yake da raunuka ba dalili? Wa yake da jan idanu?

    30 Waɗanda suke daɗe suna shan ruwan inabi,

    waɗanda suke neman ƙoƙon damammen ruwan inabi.

    31 Kada ka ƙyifce ido a ruwan inabi sa’ad da ya yi ja,

    sa’ad da yana da kyan gani a cikin ƙwarya,

    sa’ad da yana gangarawa sumul a maƙogwaro!

    32 A ƙarshe yana sara kamar maciji

    da kuma dafi kamar gamsheƙa.

    33 Idanunka za su riƙa gane-gane,

    zuciyarka kuma za su riƙa tunani abubuwa masu rikitarwa.

  4. 19 Ayyukan mutuntaka kuwa a fili suke. Wato, fasikanci, ƙazanta da kuma lalata; 20 bautar gumaka da sihiri; ƙiyayya, faɗa, kishi, fushi mai zafi, sonkai, tsattsaguwa, hamayya, 21 da ƙyashi; buguwa, shashanci, da ire-irensu. Na gargaɗe ku, yadda na yi a dā, cewa masu irin wannan rayuwa ba za su gāji mulkin Allah ba.

    22 Amma amfanin da Ruhu yake bayar shi ne ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci, 23 sauƙinkai, da kuma kamunkai. Ai, ba ruwan Doka da waɗannan abubuwa.

  5. 11 Kaiton waɗanda suke tashi da sassafe

    don su nufi wurin shaye-shaye,

    waɗanda suke raba dare

    har sai sun bugu da ruwan inabi.

    12 Suna kaɗa garaya, da molaye a bukukkuwansu,

    ganguna da busa da ruwan inabi,

    amma ba su kula da ayyukan Ubangiji ba,

    ba sa biyayya ga aikin hannuwansa.

  6. 4 “Ba na sarakuna ba ne, ya Lemuwel,

    ba na sarakuna ba ne su sha ruwan inabi,

    ba na masu mulki ba ne su yi marmarin barasa,

    5 don kada su sha su manta da abin da doka ta umarta,

    su hana wa waɗanda aka danne hakkinsu.

    6 A ba da barasa ga waɗanda suke cikin halin ƙaƙa naka yi,

    ruwan inabi ga waɗanda suke cikin wahala;

    7 bari su sha su manta da talaucinsu

    kada kuma su ƙara tunawa da ɓacin ransu.

    8 “Yi magana domin bebaye,

    domin hakkin dukan waɗanda suke naƙasassu.

    9 Yi magana a kuma yi shari’ar adalci;

    a tsare hakkin talakawa da masu bukata.”

  7. 19 Ka saurara, ɗana, ka zama mai hikima,

    ka kafa zuciyarka a hanyar da take daidai.

    20 Kada ka haɗa kai da waɗanda suke shan ruwan inabi da yawa

    ko masu haɗama kansu da abinci,

    21 gama bugaggu da ruwan inabi da masu yawan ci sukan zama matalauta,

    gama jiri yakan yi musu sutura da tsummoki.

  8. 7 Da waɗannan kuma masu tangaɗi saboda sun sha ruwan inabi

    suke jiri don sun sha barasa

    Firistoci da annabawa suna tangaɗi saboda sun sha barasa

    sun kuma yi tatur da ruwan inabi;

    suna jiri saboda sun sha barasa,

    suna tangaɗi sa’ad da suke ganin wahayi,

    suna tuntuɓe sa’ad da suke ba da shawara.

    8 Duk amai ya rufe teburori

    kuma babu wani wurin da ba a ɓata ba.

  9. 34 “Ku lura fa don kada son jin daɗi na banza, da shaye-shaye, da damuwa na rayuwa su rinjayi zuciyarku, har ranar ta auko muku ba tsammani kamar tarko.

  10. 11 Ku yi wannan domin kun san irin zamanin da kuke ciki. Lokaci ya yi da za ku farka daga barcinku, don cetonmu ya yi kusa yanzu fiye da lokacin da muka fara ba da gaskiya. 12 Dare fa ya kusan ƙarewa; gari kuma yana gab da wayewa. Saboda haka bari mu kawar da ayyukan duhu mu kuma yafa kayan yaƙi na haske. 13 Bari mu tafiyar da al’amuranmu yadda ya dace a yi da rana, ba a cikin shashanci da buguwa ba, ba cikin fasikanci da rashin kunya ba, ba kuma cikin faɗa da kishi ba. 14 A maimakon haka, ku ɗauki halin Ubangiji Yesu Kiristi, kada kuma ku yi tunani game da yadda za ku gamsar da sha’awace-sha’awacen mutuntaka.

  11. 20 Nuhu, mutumin ƙasa, shi ne farko da ya fara yin gonar inabi. 21 Sa’ad da ya sha ruwan inabin ya kuwa bugu, sai ya kwanta tsirara cikin tentinsa. 22 Ham, mahaifin Kan’ana ya ga tsiraici mahaifinsa, ya kuma faɗa wa ’yan’uwansa biyu a waje.

  12. 23 Ka daina shan ruwa kaɗai, yi amfani da ruwan inabi kaɗan saboda cikinka da kuma yawan rashin lafiyarka.

    24 Zunuban waɗansu mutane a fili suke, suna shan gabansu zuwa hukunci; zunuban waɗansu kuwa sukan bi su a baya. 25 Haka ma ayyuka nagari a fili suke, ko ba ma a fili suke ba, ba a iya ɓoye su.

  13. 8 Sa’an nan Ubangiji ya yi magana da Haruna ya ce, 9 “Kai da ’ya’yanka maza, ba za ku sha ruwan inabi ko wani abu mai sa jiri ba a duk sa’ad da za ku shiga cikin Tentin Sujada, in ba haka ba za ku mutu. Wannan dawwammamiyar farilla ce wa tsararraki masu zuwa. 10 Dole ku bambanta tsakanin mai tsarki da marar tsarki, tsakanin marar tsabta da mai tsabta, 11 za ku kuma koyar da Isra’ilawa dukan farillan da Ubangiji ya ba su ta wurin Musa.”

  14. 1 Saboda haka, da yake Kiristi ya sha wahala a jikinsa, sai ku ma ku yi wa kanku ɗamara da irin wannan hali, gama wanda ya sha wahala a jikinsa ya gama da zunubi ke nan. 2 Ta haka, ba ya sauran rayuwarsa a kan mugayen sha’awace-sha’awacen jiki, sai dai nufin Allah. 3 Gama kun ɓata lokaci sosai a dā kuna yin abubuwan da masu bauta gumaka suka zaɓa su yi, kuna rayuwa cikin lalata, sha’awace-sha’awace, buguwa, shashanci, shaye-shaye da kuma bautar gumaka masu banƙyama. 4 Sun yi mamaki da ba kwa haɗa kai da su a yanzu, da ba kwa kutsa kai tare da su cikin irin rayuwar banzan nan, har suna zaginku. 5 Amma dole su ba da lissafi gare shi wanda yake a shirye yă shari’anta masu rai da matattu. 6 Dalilin ke nan da ya sa aka yi wa’azin bishara har ga waɗanda yanzu suke mutattu, don ko da yake an hukunta su a matsayin mutane a batun jiki, amma su rayu ga Allah a batun ruhu.

  15. 9 Ba ku sani ba cewa mugaye ba za su gāji mulkin Allah ba? Kada fa a ruɗe ku. Ba masu fasikanci ko masu bautar gumaka ko masu zina ko karuwan maza, ko ’yan daudu, 10 ko ɓarayi ko masu kwaɗayi ko mashaya ko masu ɓata suna ko masu zamba da za su gāji mulkin Allah. 11 Haka waɗansu a cikinku ma suke a dā. Amma an wanke ku, an tsarkake ku, aka kuma sa kuka zama marasa laifi cikin sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma ta wurin Ruhun Allahnmu.

  16. 14 Yana sa ciyawa tă yi girma saboda shanu,

    tsire-tsire domin mutum ya nome,

    suna fid da abinci daga ƙasa,

    15 ruwan inabi yakan sa zuciyar mutum tă yi murna,

    mai kuwa yakan sa fuska tă yi haske,

    abinci kuma da yake riƙe zuciyarsa.

  17. 17 Duk mai son jin daɗi zai zama matalauci;

    duk mai son ruwan inabi da mai ba zai taɓa zama mai arziki ba.

  18. 1 Kaito ga wannan rawani, girman kai na mashayan Efraim,

    ga fure mai yanƙwanewa, darajar kyansa,

    da aka sa a kan kwari mai ba da amfani,

    ga birnin nan, wadda take girman kan waɗanda aka ƙasƙantar da ruwan inabinsu!

    2 Duba, Ubangiji yana da wanda yake da iko da kuma ƙarfi.

    Kamar dutsen ƙanƙara da kuma iska mai ɓarna,

    kamar kwararowar ruwa da rigyawa mai kirmewa,

    zai jefa shi har ƙasa da ƙarfi.

    3 Za a tattaka wannan rawani,

    girman kai na mashayan Efraim da ƙafa.

  19. 15 “Kaito wanda ya ba wa maƙwabtansa abin sha,

    yana ta zubawa daga salkan ruwan inabi har sai sun bugu,

    don dai yă ga tsiraicinsu.

    16 Za ka cika da kunya a maimakon ɗaukaka.

    Yanzu lokacinka ne! Kai ma ka sha, a kuma tone asirinka!

    Gama kwaf na hannun daman Ubangiji yana zuwa kewaye da kai,

    abin kunya kuma zai rufe darajarka.

    17 Ɓarnar da ka yi wa Lebanon zai komo kanka,

    kuma hallakar dabbobin da ka yi zai sa dabbobi su tsorata ka.

    Gama ka zub da jinin mutum;

    ka hallaka ƙasashe, da birane, da kuma kowa da yake cikinsu.

  20. 22 Kaiton waɗanda suke jarumawa a shan ruwan inabi

    da gwanaye a haɗin abubuwan sha,

    23 waɗanda suke ƙyale masu laifi don sun ba da cin hanci,

    amma su hana a yi gaskiya wa marasa laifi.

  21. 11 ga karuwanci,

    ga tsoho da kuma sabon ruwan inabi,

    waɗanda suka ɗauke ganewar mutanena.

    12 Sun nemi shawarar gunkin da aka yi da itace

    suka kuwa sami amsa daga sanda.

    Halin karuwanci yakan ɓad da su;

    sun yi rashin aminci ga Allahnsu.

  22. 11 Yanzu dai ina rubuta muku cewa kada ku haɗa kai da duk mai kiran kansa ɗan’uwa, amma yana fasikanci, ko kwaɗayi, ko bautar gumaka, ko ɓata suna, ko mashayi, ko mazambaci. Kada ku ko ci abinci da irin wannan mutum.

  23. 1 To, ’yan’uwa, game da lokuta da ranaku, ba ma bukata mu rubuta muku, 2 gama kun sani sarai cewa ranar Ubangiji za tă zo kamar ɓarawo da dare. 3 Yayinda mutane suke cewa, “Akwai salama da zaman lafiya,” hallaka za tă auko musu farat ɗaya, kamar yadda naƙuda take kama mace mai ciki, ba za su kuwa tsira ba.

    4 Amma ku, ’yan’uwa, ba kwa cikin duhu da wannan rana za tă zo muku ba zato kamar ɓarawo. 5 Dukanku ’ya’yan haske ne da kuma ’ya’yan rana. Mu ba mutanen dare ko na duhu ba ne. 6 Saboda haka fa, kada mu zama kamar saura, waɗanda suke barci, sai dai mu zama masu tsaro da masu kamunkai. 7 Gama masu barci, da dad dare suke barci, masu sha su bugu kuwa, da dad dare suke buguwa. 8 Amma da yake mu na rana ne, bari mu zama masu kamunkai, sanye da bangaskiya da ƙauna kamar sulke, begen cetonmu kuma kamar hular kwano. 9 Gama Allah bai naɗa mu don mu sha fushi ba, sai dai mu sami ceto ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi. 10 Ya mutu saboda mu domin, ko muna a faɗake ko muna barci, mu kasance tare da shi. 11 Saboda haka ku ƙarfafa juna ku kuma gina juna, kamar dai yadda kuke yi.

  24. 36 Da Abigiyel ta kai gida sai ta sami Nabal cikin gida yana ta fama biki iri na sarakuna. Yana ji wa ransa daɗi, ya kuma bugu tilis, saboda haka ba tă ce masa kome ba sai da gari ya waye. 37 Da safe sa’ad da Nabal ya natsu, sai matarsa ta gaya masa dukan abin da ya faru. Sai zuciyarsa ta tsinke, ya zama kamar dutse.

  25. 13 Dawuda ya gayyace shi, ya kuwa ci ya sha tare da shi, Dawuda ya sa ya bugu tilis. Amma da yamma Uriya ya koma ya kwanta a tabarmarsa cikin bayin maigidan sarki; bai je gida ba.

  26. 9 Zimri, ɗaya daga cikin shugabanni, wanda ya shugabanci rabin kekunan yaƙin Ela, ya yi maƙarƙashiya a kansa. Ela yana a Tirza a lokacin, ya bugu a gidan Arza, sarkin fada a Tirza. 10 Zimri ya shiga, ya buge shi ya kashe a shekara ta ashirin da bakwai na Asa sarkin Yahuda. Sa’an nan ya gāje shi a matsayin sarki.

  27. 1 Sarki Belshazar ya yi babban biki domin dubban hakimansa ya kuma sha ruwan inabi tare da su. 2 Yayinda Belshazar yake shan ruwan inabi, sai ya umarta a kawo zinariya da azurfan da Nebukadnezzar mahaifinsa ya kwaso daga haikali a Urushalima, saboda sarki da hakimansa, da matansa da ƙwarƙwaransa su sha da su. 3 Sai suka kawo kayan zinariyan nan da aka kwaso daga haikalin Allah a Urushalima, sarki kuwa da hakimansa, da matansa, da ƙwarƙwaransa suka yi ta sha da su. 4 Yayinda suke shan ruwan inabin, sai suka yabi allolin zinariya da azurfa, da na tagulla, da na ƙarfe, da na itace da kuma na dutse.

    5 Nan da nan sai ga yatsotsin hannun mutum sun bayyana, suna yin rubutu a kan shafen bangon, kusa da wurin da ake ajiye fitilar fadar sarki. Sarki kuwa yana ganin hannun yayinda yake rubutu. 6 Sai fuskarsa ta ruɗe, ya kuma ji tsoro ƙwarai har gwiwoyinsa suka yi ta bugun juna, ƙafafunsa kuma suka rasa ƙarfi.

  28. 2 To, dole mai kula da Ikkilisiya yă kasance marar abin zargi, mijin mace guda, mai sauƙinkai, mai kamunkai, wanda ake girmama, mai karɓan baƙi, mai iya koyarwa, 3 ba mai buguwa ba, ba mai rikici ba sai dai mai hankali, ba mai yawan faɗa ba, ba kuma mai yawan son kuɗi ba.

  29. 1 Dole ka koyar da abin da yake bisa sahihiyar koyarwa. 2 Ka koya wa tsofaffin maza su kasance masu sauƙinkai, waɗanda suka cancanci girmamawa, masu kamunkai, sahihai wajen bangaskiya, da ƙauna da kuma jimiri.

    3 Haka ma, ka koya wa tsofaffin mata su zama masu bangirma cikin rayuwarsu, ba masu ɓata suna ko masu jarrabar shan giya ba, sai dai su zama masu koyar da abin da yake nagari. 4 Sa’an nan za su iya su koya wa mata masu ƙuruciya su ƙaunaci mazansu da ’ya’yansu, 5 su kasance da kamunkai da kuma tsarki, masu aiki a gida, masu kirki da kuma masu biyayya ga mazansu, don kada wani yă rena maganar Allah.

  30. 12 Yayinda take addu’a ga Ubangiji, Eli ya lura da bakinta. 13 Hannatu tana addu’a a zuci, ba a jin muryarta, sai leɓunanta ne kawai suna motsi. Eli kuwa ya yi tsammani ta bugu ne. 14 Sai ya ce mata, “Har yaushe za ki ci gaba da maye? Ki daina shan ruwan inabi.”

    15 Hannatu ta ce, “Ba haka ba ne, ranka yă daɗe, ni mace ce da take cikin matsala ƙwarai da gaske. Ban sha ruwan inabi ba, ko wani abu mai sa maye, ina dai faɗa wa Ubangiji abin da yake damuna ne. 16 Kada ka yi zato baiwarka ’yar iska ce. Ina addu’a a nan saboda yawan azaba da baƙin cikin da nake ciki.”

  31. 13 Duk da haka waɗansu suka yi musu ba’a suka ce, “Sun yi tatil da ruwan inabi ne.”

    14 Sai Bitrus ya miƙe tsaye tare da Sha Ɗayan nan, ya ɗaga muryarsa ya yi wa taron jawabi ya ce, “’Yan’uwana Yahudawa da dukanku da kuke zama cikin Urushalima, bari in bayyana muku wannan, ku saurara da kyau ga abin da zan faɗa. 15 Waɗannan mutane ba su bugu ba, kamar yadda kuka ɗauka. Yanzu ƙarfe tara na safe ne kawai!

  32. 20 Kada ku lalatar da aikin Allah saboda abinci. Dukan abinci mai tsabta ne, sai dai ba daidai ba ne mutum yă ci abin da zai sa wani yă yi tuntuɓe. 21 Ya fi kyau kada ka ci nama ko ka sha ruwan inabi ko kuma ka yi wani abin da zai sa ɗan’uwanka yă fāɗi.

    22 Bari duk ra’ayin da kake da shi game da wannan sha’ani yă kasance tsakaninka da Allah. Mai albarka ne wanda zuciyarsa ba tă ba shi laifi game da abin da shi da kansa ya ɗauka cewa daidai ne ba. 23 Amma wanda yake da shakka yakan jawo wa kansa hukunci ne in ya ci, domin yana ci ne ba bisa ga bangaskiya ba; kuma duk abin da bai zo daga bangaskiya ba zunubi ne.

  33. 31 Saboda haka, duk abin da kuke yi, ko ci ko sha, ku yi shi duka saboda ɗaukakar Allah. 32 Kada ku sa wani yă yi tuntuɓe, ko mutumin Yahuda ne, ko mutumin Al’ummai ko kuma ikkilisiyar Allah 33 kamar dai yadda nake ƙoƙarin faranta wa kowa rai, ta kowace hanya. Gama ba don kaina kaɗai nake yi ba, sai dai don amfanin mutane da yawa, don su sami ceto.

  34. 20 Sa’ad da kuka taru, ba Cimar Ubangiji kuke ci ba, 21 gama yayinda kuke ci, kowa yakan ci gaba ba tare da jiran wani ba. Wani yă zauna da yunwa, wani kuma yă bugu. 22 Kai, ba ku da gidajen da za ku ci ku sha ne? Ko dai kun rena ikkilisiyar Allah ne, kuna kuma wulaƙanta waɗanda ba su da kome? Me zan ce muku? In yabe ku ne game da wannan? A’a, ko kaɗan!

  35. 1 Ubangiji ya ce wa Musa, 2 “Yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘In mace, ko namiji yana so yă yi alkawari na musamman, alkawarin zaman keɓaɓɓe ga Ubangiji, a matsayin Banazare, 3 dole yă keɓe kansa daga ruwan inabi, ko daga waɗansu abubuwa sha masu sa maye, kada kuma yă sha ruwan tsamin da aka yi daga ruwan inabi, ko daga waɗansu abubuwa sha masu sa maye. Ba zai sha ruwan ’ya’yan inabi, ko yă ci ’ya’yan inabi ɗanye ko busasshe ba.

  36. 48 Amma in wannan bawa mugu ne, ya kuma ce a ransa, ‘Maigidana ba zai dawo da wuri ba.’ 49 Sa’an nan yă fara dūkan ’yan’uwansa bayi, yana ci yana kuma sha tare da mashaya. 50 Maigidan wannan bawa zai dawo a ranar da bai yi tsammani ba, a sa’ar kuma da bai sani ba. 51 Maigidan zai farfasa masa jiki da bulala, yă kuma ba shi wuri tare da munafukai, inda za a yi kuka da cizon haƙora.

  37. 18 In mutum yana da gagararren ɗa mai tawaye, wanda ba ya biyayya ga mahaifinsa da mahaifiyarsa, ba ya kuma jin su sa’ad da suke horonsa, 19 mahaifinsa da mahaifiyarsa za su kama shi su kawo shi ga dattawa a ƙofar garinsu. 20 Za su ce wa dattawan, “Wannan ɗanmu gagararre ne, mai tawaye. Ba ya mana biyayya. Mai zari ne, kuma mashayi.” 21 Sa’an nan dukan mazan garinsa za su jajjefe shi har yă mutu. Dole ku fid da mugu daga cikinku. Dukan Isra’ila kuwa za su ji wannan su kuma ji tsoro.

  38. 4 To, sai ki lura kada ki sha ruwan inabi ko wani abu mai sa maye, kada kuma ki ci wani abu marar tsarki, 5 gama za ki yi ciki, ki haifi ɗa. Aska ba za tă taɓa kansa ba, domin yaron zai zama Banazare, keɓaɓɓe ga Allah tun daga haihuwa, shi ne kuwa zai soma ceton Isra’ilawa daga hannuwan Filistiyawa.”

    6 Sa’an nan matar ta tafi wajen mijinta ta faɗa masa cewa, “Wani mutumin Allah ya zo wurina. Ya yi kama da mala’ikan Allah, yana da bantsoro ƙwarai. Ban tambaye shi inda ya fito ba, kuma bai gaya mini sunansa ba. 7 Sai dai ya ce mini, ‘Za ki yi ciki, ki kuma haifi ɗa. To, fa, kada ki sha ruwan inabi ko abu mai sa maye kada kuma ki ci abin da yake marar tsarki, gama ɗan zai zama Banazare na Allah tun daga haihuwa har ranar mutuwarsa.’ ”

  39. 19 Ba ku san cewa jikin nan naku haikalin Ruhu Mai Tsarki ba ne wanda yake cikinku yake kuma daga Allah? Ku ba na kanku ba ne; 20 saye ku fa aka yi da tsada, saboda haka, sai ku girmama Allah da jikinku.

  40. 8 Gaskiya ne cewa ba ma samun yardar Allah ta wurin abin da muke ci. Ba ma rasa wani abu idan ba mu ci ba, kuma ba ma ƙaru da wani abu in muka ci.

    9 Sai dai ku yi hankali, kada yin amfani da ’yancinku yă zama abin sa tuntuɓe ga marasa ƙarfi. 10 Gama in wani wanda lamirinsa ba shi da ƙarfi ya gan ka, kai da kake da wannan sani, kana ci a haikalin gumaka, ashe, ba zai sami ƙarfin halin cin abin da aka miƙa wa gumaka ba? 11 Saboda haka ta wurin sanin nan naka sai ka sa wannan ɗan’uwa marar ƙarfi wanda Kiristi ya mutu dominsa yă hallaka. 12 Sa’ad da ka rushe lamiri mai bi marar ƙarfi, ka yi wa Kiristi zunubi ke nan. 13 Saboda haka, in abin da nake ci zai sa ɗan’uwana yă yi zunubi, ba zan ƙara cin nama ba, don kada in sa shi yă yi tuntuɓe.

  41. 14 Ubangiji ya sa zuba musu

    ruhun jiri;

    suka sa Masar ta yi tangaɗi cikin kome da take yi,

    kamar yadda mutumin da ya bugu yake tangaɗi cikin amansa.

  42. 27 “Sa’an nan na faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ku sha, ku bugu ku kuma yi amai, ku fāɗi, kada kuma ku ƙara tashi saboda takobin da zan aiko muku.’ 28 Amma in suka ki su karɓi kwaf ɗin daga hannunka su sha, ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa dole ku sha!

  43. 31 Kin bi hanyar ’yar’uwarki; saboda haka zan sa kwaf nata a hannunki.

    32 “Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,

    “Za ki sha kwaf na ’yar’uwarki,

    kwaf wanda yake da girma da kuma zurfi;

    zai jawo dariya da kuma reni

    gama yana ɗauke da abubuwa da yawa.

    33 Za ki cika da buguwa da baƙin ciki,

    kwaf lalaci da kaɗaici,

    kwaf na ’yar’uwarki Samariya.

    34 Za ki sha shi ki kuma lashe shi ƙaf;

    za ki buga shi da ƙasa ya yi rugu-rugu

    ki tsattsage nononki.

    Ni Ubangiji Mai Iko Duka na faɗa.

  44. 16 “Da me zan kwatanta wannan zamani? Suna kama da yara da suke zaune a kasuwa, suna kiran juna, suna cewa,

    17 “ ‘Mun yi muku busa,

    ba ku kuwa yi rawa ba,

    mun rera waƙar makoki,

    ba ku kuwa yi makoki ba.’

    18 Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo ba ya ciye-ciye, ba ya shaye-shaye, sai suka ce, ‘Ai, yana da aljani.’ 19 Ɗan Mutum ya zo yana ciye-ciye, yana shaye-shaye, sai suka ce, ‘Ga mai haɗama da kuma mashayi, abokin masu karɓar haraji da masu zunubi.’ Amma akan tabbatar da hikima ta wurin ayyukanta.”

  45. 9 Uban bikin kuwa ya ɗanɗana ruwan da aka juya ya zama ruwan inabi. Bai san daga ina ya fito ba, ko da yake bayin da suka ɗiba ruwan sun sani. Sai ya kira angon waje ɗaya 10 ya ce, “Kowa yakan kawo ruwan inabi mafi kyau da fari, sa’an nan marar kyan bayan baƙin sun sha da yawa; amma ka ajiye ruwan inabi mafi kyau sai yanzu.”

    11 Wannan shi ne na fari cikin abubuwan banmamakin da Yesu ya yi a Kana ta Galili. Ta haka ya bayyana ɗaukakarsa, almajiransa kuwa suka ba da gaskiya gare shi.

  46. 7 Da yake an danƙa wa mai kula da ikkilisiya riƙon amana saboda Allah, dole yă zama marar aibi ba mai girman kai ba, ba mai saurin fushi ba, ba mai buguwa ba, ba mai rikici ba, ba kuma mai son ƙazamar riba ba. 8 A maimakon haka dole yă zama mai karɓan baƙi, mai son abu nagari, mai kamunkai, mai adalci, mai tsarki da kuma natsattse. 9 Dole yă riƙe tabbataccen saƙon nan kam-kam yadda aka koyar, don yă iya ƙarfafa waɗansu da sahihiyar koyarwa yă kuma ƙaryata waɗanda suke gāba da shi.

  47. 8 Ku zama masu kamunkai, ku kuma zauna a faɗake. Abokin gābanku, Iblis yana kewayewa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai cinye.

  48. 1 Ɗaya daga cikin mala’iku bakwai masu ɗauke da kwanoni bakwai nan, ya zo ya ce mini, “Zo, zan nuna maka hukuncin babbar karuwan nan da take zaune a bisan ruwaye masu yawa. 2 Da ita ce sarakunan duniya suka yi zina mazaunan duniya kuma suka bugu da ruwan inabin zinace zinacenta.”

  49. 9 Ku firgita ku kuma yi mamaki,

    ku makance kanku ku kuma zama a makance;

    ku bugu, amma ba da ruwan inabi ba,

    ku yi tangaɗi, amma ba daga barasa ba.

    10 Ubangiji ya kawo muku barci mai nauyi,

    Ya rufe idanunku (annabawa);

    ya rufe kawunanku (masu duba).

  50. 6 Na tattake al’ummai cikin fushina;

    cikin hasalata kuma na sa sun bugu

    na kuma zub da jininsu a ƙasa.”

  51. 42 Zan sa kibiyoyina su bugu da jini,

    yayinda takobina yana cin nama,

    jinin kisassu da na kamammu,

    kawunan shugabannin abokan gāba.”

  52. 17 Ki farka, ki farka!

    Ki tashi, ya Urushalima,

    ke da kika sha daga hannun Ubangiji

    kwaf na fushinsa,

    ke da kika shanye har ƙasar kwaf

    kwaf da ya sa mutane suna tangaɗi.

  53. 21 Saboda haka ki ji wannan, ke mai wahala,

    wadda ta bugu, amma ba da ruwan inabi.

    22 Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,

    Allahnki, wanda ya kāre mutanensa,

    “Duba, na ƙwace daga hannunki

    kwaf da ya sa ki tangaɗi;

    daga wannan kwaf, kwaf na fushina,

    ba za ki ƙara sha ba.

    23 Zan sa shi a hannuwan masu gwada miki azaba,

    waɗanda suke ce miki,

    ‘Fāɗi rubda ciki don mu iya taka a kanki.’

    Kika kuma mai da bayanki kamar ƙasa,

    kamar titin da ake takawa a kai.”

  54. 7 Babilon ta zama ƙoƙon zinariya a hannun Ubangiji,

    ta sa dukan duniya ta yi maye.

    Ƙasashe sun sha ruwan inabinta,

    saboda haka yanzu sun haukace.

    8 Farat ɗaya Babilon za tă fāɗi ta farfashe.

    Ku yi kuka dominta!

    Ku samo mata magani saboda azabarta;

    wataƙila za a iya warkar da ita.

    9 “ ‘Da mun warkar da Babilon,

    amma ba za tă warke ba;

    mu ƙyale ta kowane yă koma garinsu,

    gama hukuncinta ya kai sammai,

    ya yi tsawo kamar gizagizai.’

  55. 10 Ɓarawo yakan zo don yă yi sata ne kawai da kisa da kuma ɓarna. Ni kuwa na zo ne don su sami rai, su kuma same shi a yalwace.