90 Bible Verses About Drinking

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Drinking
  1. 1 Ruwan inabi mai yin ba’a ne, barasa kuma mai rikici ne;

    duk wanda suka sa ya kauce marar hikima ne.

  2. 15 Sai ku yi hankali sosai da yadda kuke rayuwa, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai kamar masu hikima. 16 Ku kuma yi matuƙar amfani da kowane zarafi, don kwanakin nan mugaye ne. 17 Saboda haka kada ku zama wawaye, sai dai ku fahimci ko mene ne nufin Ubangiji. 18 Kada ku bugu da ruwan inabi, wanda yake kai ga lalaci. A maimako haka, ku cika da Ruhu. 19 Ku yi zance da juna cikin zabura, da waƙoƙi, da kuma waƙoƙin ruhaniya. Ku rera, ku kuma yi kiɗe-kiɗe a zuciyarku ga Ubangiji. 20 Kullum ku dinga yin amfani da sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, kuna gode wa Allah Uba a kome.

  3. 19 Ayyukan mutuntaka kuwa a fili suke. Wato, fasikanci, ƙazanta da kuma lalata; 20 bautar gumaka da sihiri; ƙiyayya, faɗa, kishi, fushi mai zafi, sonkai, tsattsaguwa, hamayya, 21 da ƙyashi; buguwa, shashanci, da ire-irensu. Na gargaɗe ku, yadda na yi a dā, cewa masu irin wannan rayuwa ba za su gāji mulkin Allah ba.

    22 Amma amfanin da Ruhu yake bayar shi ne ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci, 23 sauƙinkai, da kuma kamunkai. Ai, ba ruwan Doka da waɗannan abubuwa. 24 Waɗanda suke na Kiristi Yesu, sun gicciye mutuntaka tare da abubuwan da mutum yake marmari da kuma sha’awace-sha’awacensa. 25 Da yake muna rayuwa ta Ruhu ne, bari mu ci gaba da al’amuranmu ta wurin Ruhu.

  4. 4 “Ba na sarakuna ba ne, ya Lemuwel,

    ba na sarakuna ba ne su sha ruwan inabi,

    ba na masu mulki ba ne su yi marmarin barasa,

    5 don kada su sha su manta da abin da doka ta umarta,

    su hana wa waɗanda aka danne hakkinsu.

    6 A ba da barasa ga waɗanda suke cikin halin ƙaƙa naka yi,

    ruwan inabi ga waɗanda suke cikin wahala;

    7 bari su sha su manta da talaucinsu

    kada kuma su ƙara tunawa da ɓacin ransu.

    8 “Yi magana domin bebaye,

    domin hakkin dukan waɗanda suke naƙasassu.

    9 Yi magana a kuma yi shari’ar adalci;

    a tsare hakkin talakawa da masu bukata.”

  5. 29 Wa yake wayyo? Wa yake baƙin ciki?

    Wa yake neman fada? Wa yake gunaguni?

    Wa yake da raunuka ba dalili? Wa yake da jan idanu?

    30 Waɗanda suke daɗe suna shan ruwan inabi,

    waɗanda suke neman ƙoƙon damammen ruwan inabi.

    31 Kada ka ƙyifce ido a ruwan inabi sa’ad da ya yi ja,

    sa’ad da yana da kyan gani a cikin ƙwarya,

    sa’ad da yana gangarawa sumul a maƙogwaro!

    32 A ƙarshe yana sara kamar maciji

    da kuma dafi kamar gamsheƙa.

    33 Idanunka za su riƙa gane-gane,

    zuciyarka kuma za su riƙa tunani abubuwa masu rikitarwa.

    34 Za ka zama kamar wanda yake barci a tsakiyar tekuna,

    kwance a sama itacen jirgin ruwa.

    35 Za ka ce “Sun buge ni, amma ban ji ciwo ba!

    Sun daddoke ni, amma ba na jin zafinsa!

    Yaushe zan farka

    don in ƙara shan wani?”

  6. 11 Kaiton waɗanda suke tashi da sassafe

    don su nufi wurin shaye-shaye,

    waɗanda suke raba dare

    har sai sun bugu da ruwan inabi.

    12 Suna kaɗa garaya, da molaye a bukukkuwansu,

    ganguna da busa da ruwan inabi,

    amma ba su kula da ayyukan Ubangiji ba,

    ba sa biyayya ga aikin hannuwansa.

    13 Saboda haka mutanena za su yi zaman bauta

    domin rashin fahimi;

    manyan mutanensu za su mutu da yunwa

    talakawansu kuma su mutu da ƙishirwa.

    14 Saboda haka kabari ya fadada marmarinsa

    ya kuma buɗe bakinsa babu iyaka;

    cikinsa manyan mutanensu da talakawansu za su gangara

    tare da dukan masu hayaniyarsu da masu murnansu.

  7. 23 Ka daina shan ruwa kaɗai, yi amfani da ruwan inabi kaɗan saboda cikinka da kuma yawan rashin lafiyarka.

  8. 8 Sa’an nan Ubangiji ya yi magana da Haruna ya ce, 9 “Kai da ’ya’yanka maza, ba za ku sha ruwan inabi ko wani abu mai sa jiri ba a duk sa’ad da za ku shiga cikin Tentin Sujada, in ba haka ba za ku mutu. Wannan dawwammamiyar farilla ce wa tsararraki masu zuwa. 10 Dole ku bambanta tsakanin mai tsarki da marar tsarki, tsakanin marar tsabta da mai tsabta, 11 za ku kuma koyar da Isra’ilawa dukan farillan da Ubangiji ya ba su ta wurin Musa.”

  9. 19 Ka saurara, ɗana, ka zama mai hikima,

    ka kafa zuciyarka a hanyar da take daidai.

    20 Kada ka haɗa kai da waɗanda suke shan ruwan inabi da yawa

    ko masu haɗama kansu da abinci,

    21 gama bugaggu da ruwan inabi da masu yawan ci sukan zama matalauta,

    gama jiri yakan yi musu sutura da tsummoki.

  10. 9 Ba ku sani ba cewa mugaye ba za su gāji mulkin Allah ba? Kada fa a ruɗe ku. Ba masu fasikanci ko masu bautar gumaka ko masu zina ko karuwan maza, ko ’yan daudu, 10 ko ɓarayi ko masu kwaɗayi ko mashaya ko masu ɓata suna ko masu zamba da za su gāji mulkin Allah. 11 Haka waɗansu a cikinku ma suke a dā. Amma an wanke ku, an tsarkake ku, aka kuma sa kuka zama marasa laifi cikin sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma ta wurin Ruhun Allahnmu.

  11. 11 Ku yi wannan domin kun san irin zamanin da kuke ciki. Lokaci ya yi da za ku farka daga barcinku, don cetonmu ya yi kusa yanzu fiye da lokacin da muka fara ba da gaskiya. 12 Dare fa ya kusan ƙarewa; gari kuma yana gab da wayewa. Saboda haka bari mu kawar da ayyukan duhu mu kuma yafa kayan yaƙi na haske. 13 Bari mu tafiyar da al’amuranmu yadda ya dace a yi da rana, ba a cikin shashanci da buguwa ba, ba cikin fasikanci da rashin kunya ba, ba kuma cikin faɗa da kishi ba. 14 A maimakon haka, ku ɗauki halin Ubangiji Yesu Kiristi, kada kuma ku yi tunani game da yadda za ku gamsar da sha’awace-sha’awacen mutuntaka.

  12. 14 Yana sa ciyawa tă yi girma saboda shanu,

    tsire-tsire domin mutum ya nome,

    suna fid da abinci daga ƙasa,

    15 ruwan inabi yakan sa zuciyar mutum tă yi murna,

    mai kuwa yakan sa fuska tă yi haske,

    abinci kuma da yake riƙe zuciyarsa.

  13. 8 Haka masu hidima a cikin ikkilisiya; su ma, su zama maza da sun cancanci girmamawa, masu gaskiya, ba masu yawan shan ruwan inabi ba, ba masu kwaɗayin ƙazamar riba ba. 9 Dole su riƙe asirin bangaskiya su kuma kasance da lamiri mai tsabta. 10 Dole a fara gwada su tukuna; sa’an nan in ba a sami wani abin zargi game da su ba, sai su shiga aikin masu hidima.

    11 A haka kuma, dole matansu su zama matan da suka cancanci girmamawa, ba masu gulma ba, sai dai masu sauƙinkai da kuma masu aminci a cikin kome.

    12 Dole mai hidimar ikkilisiya yă zama mijin mace guda dole kuma yă iya tafiyar da ’ya’yansa da kuma iyalinsa da kyau. 13 Waɗanda suke hidima da kyau suna samar wa kansu kyakkyawan suna da kuma cikakken tabbatarwa a cikin bangaskiyarsu cikin Kiristi Yesu.

  14. 34 “Ku lura fa don kada son jin daɗi na banza, da shaye-shaye, da damuwa na rayuwa su rinjayi zuciyarku, har ranar ta auko muku ba tsammani kamar tarko.

  15. 19 Saboda haka sai mu yi iya ƙoƙari mu aikata abin da zai kawo salama da kuma ingantawa ga juna. 20 Kada ku lalatar da aikin Allah saboda abinci. Dukan abinci mai tsabta ne, sai dai ba daidai ba ne mutum yă ci abin da zai sa wani yă yi tuntuɓe. 21 Ya fi kyau kada ka ci nama ko ka sha ruwan inabi ko kuma ka yi wani abin da zai sa ɗan’uwanka yă fāɗi.

    22 Bari duk ra’ayin da kake da shi game da wannan sha’ani yă kasance tsakaninka da Allah. Mai albarka ne wanda zuciyarsa ba tă ba shi laifi game da abin da shi da kansa ya ɗauka cewa daidai ne ba. 23 Amma wanda yake da shakka yakan jawo wa kansa hukunci ne in ya ci, domin yana ci ne ba bisa ga bangaskiya ba; kuma duk abin da bai zo daga bangaskiya ba zunubi ne.

  16. 2 Akwai wani mutumin Zora, mai suna Manowa, daga kabilar Dan, matarsa kuwa bakararriya ce, ba ta haihuwa. 3 Mala’ikan Ubangiji ya bayyana gare ta ya ce, “Ga shi ke bakararriya ce ba kya haihuwa, amma za ki yi ciki ki kuma haifi ɗa. 4 To, sai ki lura kada ki sha ruwan inabi ko wani abu mai sa maye, kada kuma ki ci wani abu marar tsarki, 5 gama za ki yi ciki, ki haifi ɗa. Aska ba za tă taɓa kansa ba, domin yaron zai zama Banazare, keɓaɓɓe ga Allah tun daga haihuwa, shi ne kuwa zai soma ceton Isra’ilawa daga hannuwan Filistiyawa.”

    6 Sa’an nan matar ta tafi wajen mijinta ta faɗa masa cewa, “Wani mutumin Allah ya zo wurina. Ya yi kama da mala’ikan Allah, yana da bantsoro ƙwarai. Ban tambaye shi inda ya fito ba, kuma bai gaya mini sunansa ba. 7 Sai dai ya ce mini, ‘Za ki yi ciki, ki kuma haifi ɗa. To, fa, kada ki sha ruwan inabi ko abu mai sa maye kada kuma ki ci abin da yake marar tsarki, gama ɗan zai zama Banazare na Allah tun daga haihuwa har ranar mutuwarsa.’ ”

  17. 7 Da waɗannan kuma masu tangaɗi saboda sun sha ruwan inabi

    suke jiri don sun sha barasa

    Firistoci da annabawa suna tangaɗi saboda sun sha barasa

    sun kuma yi tatur da ruwan inabi;

    suna jiri saboda sun sha barasa,

    suna tangaɗi sa’ad da suke ganin wahayi,

    suna tuntuɓe sa’ad da suke ba da shawara.

    8 Duk amai ya rufe teburori

    kuma babu wani wurin da ba a ɓata ba.

  18. 1 Dole ka koyar da abin da yake bisa sahihiyar koyarwa. 2 Ka koya wa tsofaffin maza su kasance masu sauƙinkai, waɗanda suka cancanci girmamawa, masu kamunkai, sahihai wajen bangaskiya, da ƙauna da kuma jimiri.

    3 Haka ma, ka koya wa tsofaffin mata su zama masu bangirma cikin rayuwarsu, ba masu ɓata suna ko masu jarrabar shan giya ba, sai dai su zama masu koyar da abin da yake nagari. 4 Sa’an nan za su iya su koya wa mata masu ƙuruciya su ƙaunaci mazansu da ’ya’yansu, 5 su kasance da kamunkai da kuma tsarki, masu aiki a gida, masu kirki da kuma masu biyayya ga mazansu, don kada wani yă rena maganar Allah.

  19. 1 Saboda haka, da yake Kiristi ya sha wahala a jikinsa, sai ku ma ku yi wa kanku ɗamara da irin wannan hali, gama wanda ya sha wahala a jikinsa ya gama da zunubi ke nan. 2 Ta haka, ba ya sauran rayuwarsa a kan mugayen sha’awace-sha’awacen jiki, sai dai nufin Allah. 3 Gama kun ɓata lokaci sosai a dā kuna yin abubuwan da masu bauta gumaka suka zaɓa su yi, kuna rayuwa cikin lalata, sha’awace-sha’awace, buguwa, shashanci, shaye-shaye da kuma bautar gumaka masu banƙyama. 4 Sun yi mamaki da ba kwa haɗa kai da su a yanzu, da ba kwa kutsa kai tare da su cikin irin rayuwar banzan nan, har suna zaginku.

  20. 16 “Da me zan kwatanta wannan zamani? Suna kama da yara da suke zaune a kasuwa, suna kiran juna, suna cewa,

    17 “ ‘Mun yi muku busa,

    ba ku kuwa yi rawa ba,

    mun rera waƙar makoki,

    ba ku kuwa yi makoki ba.’

    18 Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo ba ya ciye-ciye, ba ya shaye-shaye, sai suka ce, ‘Ai, yana da aljani.’ 19 Ɗan Mutum ya zo yana ciye-ciye, yana shaye-shaye, sai suka ce, ‘Ga mai haɗama da kuma mashayi, abokin masu karɓar haraji da masu zunubi.’ Amma akan tabbatar da hikima ta wurin ayyukanta.”

  21. 22 Kaiton waɗanda suke jarumawa a shan ruwan inabi

    da gwanaye a haɗin abubuwan sha,

    23 waɗanda suke ƙyale masu laifi don sun ba da cin hanci,

    amma su hana a yi gaskiya wa marasa laifi.

  22. 1 Ubangiji ya ce wa Musa, 2 “Yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘In mace, ko namiji yana so yă yi alkawari na musamman, alkawarin zaman keɓaɓɓe ga Ubangiji, a matsayin Banazare, 3 dole yă keɓe kansa daga ruwan inabi, ko daga waɗansu abubuwa sha masu sa maye, kada kuma yă sha ruwan tsamin da aka yi daga ruwan inabi, ko daga waɗansu abubuwa sha masu sa maye. Ba zai sha ruwan ’ya’yan inabi, ko yă ci ’ya’yan inabi ɗanye ko busasshe ba. 4 Muddin yana Banazare, ba zai ci wani abin da ya fito daga ’ya’yan inabi ba, ko ƙwayar inabi, ko ɓawonsa ma.

  23. 20 Nuhu, mutumin ƙasa, shi ne farko da ya fara yin gonar inabi. 21 Sa’ad da ya sha ruwan inabin ya kuwa bugu, sai ya kwanta tsirara cikin tentinsa. 22 Ham, mahaifin Kan’ana ya ga tsiraici mahaifinsa, ya kuma faɗa wa ’yan’uwansa biyu a waje. 23 Amma Shem da Yafet suka ɗauki mayafi, suka shimfiɗa a kafaɗarsu, sa’an nan suka shiga suna tafiya da baya har zuwa inda mahaifinsu yake kwance, suka rufe tsiraicinsa. Suka kau da fuskokinsu domin kada su ga tsiraicin mahaifinsu.

  24. 1 Ga wata tabbatacciyar magana. In wani ya sa zuciyarsa a kan zama mai kula da ikkilisiya, yana marmarin yin aiki mai daraja ne. 2 To, dole mai kula da Ikkilisiya yă kasance marar abin zargi, mijin mace guda, mai sauƙinkai, mai kamunkai, wanda ake girmama, mai karɓan baƙi, mai iya koyarwa, 3 ba mai buguwa ba, ba mai rikici ba sai dai mai hankali, ba mai yawan faɗa ba, ba kuma mai yawan son kuɗi ba. 4 Dole yă iya tafiyar da iyalinsa da kyau, yă kuma tabbata cewa ’ya’yansa suna yin masa biyayya da ladabin da ya dace. 5 (In mutum bai san yadda zai tafiyar da iyalinsa ba, yaya zai iya kula da ikkilisiyar Allah?) 6 Kada yă zama sabon tuba, in ba haka zai zama mai girman kai yă kuma fāɗa cikin irin hukuncin da ya fāɗo wa Iblis. 7 Dole kuma yă kasance da shaida mai kyau ga waɗanda suke na waje, don kada yă zama abin kunya yă kuma fāɗa cikin tarkon Iblis.

  25. 15 “Kaito wanda ya ba wa maƙwabtansa abin sha,

    yana ta zubawa daga salkan ruwan inabi har sai sun bugu,

    don dai yă ga tsiraicinsu.

    16 Za ka cika da kunya a maimakon ɗaukaka.

    Yanzu lokacinka ne! Kai ma ka sha, a kuma tone asirinka!

    Gama kwaf na hannun daman Ubangiji yana zuwa kewaye da kai,

    abin kunya kuma zai rufe darajarka.

  26. 13 Amma mala’ikan ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, Zakariya; an ji addu’arka. Matarka Elizabet za tă haifa maka ɗa, za ka kuma ba shi suna Yohanna. 14 Zai zama abin murna da farin ciki a gare ka, mutane da yawa kuwa za su yi murna don haihuwarsa, 15 gama zai zama mai girma a gaban Ubangiji. Ba kuwa zai taɓa shan ruwan inabi ko wani abu mai sa maye ba. Zai cika da Ruhu Mai Tsarki tun haihuwa.

  27. 4 Amma ku, ’yan’uwa, ba kwa cikin duhu da wannan rana za tă zo muku ba zato kamar ɓarawo. 5 Dukanku ’ya’yan haske ne da kuma ’ya’yan rana. Mu ba mutanen dare ko na duhu ba ne. 6 Saboda haka fa, kada mu zama kamar saura, waɗanda suke barci, sai dai mu zama masu tsaro da masu kamunkai. 7 Gama masu barci, da dad dare suke barci, masu sha su bugu kuwa, da dad dare suke buguwa. 8 Amma da yake mu na rana ne, bari mu zama masu kamunkai, sanye da bangaskiya da ƙauna kamar sulke, begen cetonmu kuma kamar hular kwano. 9 Gama Allah bai naɗa mu don mu sha fushi ba, sai dai mu sami ceto ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi. 10 Ya mutu saboda mu domin, ko muna a faɗake ko muna barci, mu kasance tare da shi.

  28. 17 Duk mai son jin daɗi zai zama matalauci;

    duk mai son ruwan inabi da mai ba zai taɓa zama mai arziki ba.

  29. 11 Yanzu dai ina rubuta muku cewa kada ku haɗa kai da duk mai kiran kansa ɗan’uwa, amma yana fasikanci, ko kwaɗayi, ko bautar gumaka, ko ɓata suna, ko mashayi, ko mazambaci. Kada ku ko ci abinci da irin wannan mutum.

  30. 7 Yi tafiyarka, ka ci abincinka da farin ciki, ka sha ruwan inabinka da farin zuciya, gama abin da ka yi duka daidai ne a wurin Allah.

  31. 26 Yayinda suke cikin cin abinci, Yesu ya ɗauki burodi, ya yi godiya ya kuma kakkarya, ya ba wa almajiransa yana cewa, “Ku karɓa ku ci; wannan jikina ne.”

    27 Sa’an nan ya ɗauki kwaf, ya yi godiya, ya kuma ba su, yana cewa, “Ku shassha daga cikinsa, dukanku. 28 Wannan jinina ne na sabon alkawari, wanda aka zubar saboda mutane da yawa, don gafarar zunubai. 29 Ina gaya muku, ba zan ƙara shan ruwan inabin nan ba har sai ranar da zan sha shi sabo tare da ku a mulkin Ubana.”

    30 Da suka rera waƙa, sai suka fita, suka tafi Dutsen Zaitun.

  32. 12 “Ina da dama in yi kome,” sai dai ba kome ba ne yake da amfani. “Ina da dama in yi kome” sai dai ba abin da zai mallake ni.

  33. 31 Saboda haka, duk abin da kuke yi, ko ci ko sha, ku yi shi duka saboda ɗaukakar Allah.

  34. 12 Sai Dawuda ya ce masa, “Ka ƙara dakata a nan kwana ɗaya, gobe kuwa in sallame ka.” Saboda haka Uriya ya dakata a Urushalima a ranar, da kuma ta biye. 13 Dawuda ya gayyace shi, ya kuwa ci ya sha tare da shi, Dawuda ya sa ya bugu tilis. Amma da yamma Uriya ya koma ya kwanta a tabarmarsa cikin bayin maigidan sarki; bai je gida ba.

  35. 48 Amma in wannan bawa mugu ne, ya kuma ce a ransa, ‘Maigidana ba zai dawo da wuri ba.’ 49 Sa’an nan yă fara dūkan ’yan’uwansa bayi, yana ci yana kuma sha tare da mashaya. 50 Maigidan wannan bawa zai dawo a ranar da bai yi tsammani ba, a sa’ar kuma da bai sani ba. 51 Maigidan zai farfasa masa jiki da bulala, yă kuma ba shi wuri tare da munafukai, inda za a yi kuka da cizon haƙora.

  36. 19 Ba ku san cewa jikin nan naku haikalin Ruhu Mai Tsarki ba ne wanda yake cikinku yake kuma daga Allah? Ku ba na kanku ba ne; 20 saye ku fa aka yi da tsada, saboda haka, sai ku girmama Allah da jikinku.

  37. 9 Ku firgita ku kuma yi mamaki,

    ku makance kanku ku kuma zama a makance;

    ku bugu, amma ba da ruwan inabi ba,

    ku yi tangaɗi, amma ba daga barasa ba.

  38. 9 Ku zo, dukanku namun jeji,

    ku zo ku ci, dukanku namun jeji!

    10 Matsaran Isra’ila makafi ne,

    dukansu jahilai ne;

    dukansu bebayen karnuka ne

    ba za su iya haushi ba;

    suna kwance ne kawai suna mafarki,

    suna son barci ba dama.

    11 Su karnuka ne masu kwaɗayi;

    ba su taɓa ƙoshi.

    Su makiyaya ne marasa ganewa;

    duk sun nufi inda suka ga dama,

    kowa yana nemar wa kansa riba.

    12 Kowanne yakan ce, “Zo, bari in samo ruwan inabi!

    Bari mu cika cikinmu da barasa!

    Gobe ma zai zama kamar yau,

    ko ma fiye da haka.”

  39. 7 Sai Yesu ya ce wa bayin, “Ku ciccika tulunan da ruwa.” Suka kuwa ciccika su fal.

    8 Sa’an nan ya ce musu, “Yanzu ku ɗiba ku kai wa uban bikin.”

    Suka yi haka. 9 Uban bikin kuwa ya ɗanɗana ruwan da aka juya ya zama ruwan inabi. Bai san daga ina ya fito ba, ko da yake bayin da suka ɗiba ruwan sun sani. Sai ya kira angon waje ɗaya 10 ya ce, “Kowa yakan kawo ruwan inabi mafi kyau da fari, sa’an nan marar kyan bayan baƙin sun sha da yawa; amma ka ajiye ruwan inabi mafi kyau sai yanzu.”

  40. 8 Gaskiya ne cewa ba ma samun yardar Allah ta wurin abin da muke ci. Ba ma rasa wani abu idan ba mu ci ba, kuma ba ma ƙaru da wani abu in muka ci.

    9 Sai dai ku yi hankali, kada yin amfani da ’yancinku yă zama abin sa tuntuɓe ga marasa ƙarfi. 10 Gama in wani wanda lamirinsa ba shi da ƙarfi ya gan ka, kai da kake da wannan sani, kana ci a haikalin gumaka, ashe, ba zai sami ƙarfin halin cin abin da aka miƙa wa gumaka ba? 11 Saboda haka ta wurin sanin nan naka sai ka sa wannan ɗan’uwa marar ƙarfi wanda Kiristi ya mutu dominsa yă hallaka. 12 Sa’ad da ka rushe lamiri mai bi marar ƙarfi, ka yi wa Kiristi zunubi ke nan. 13 Saboda haka, in abin da nake ci zai sa ɗan’uwana yă yi zunubi, ba zan ƙara cin nama ba, don kada in sa shi yă yi tuntuɓe.

  41. 7 Da yake an danƙa wa mai kula da ikkilisiya riƙon amana saboda Allah, dole yă zama marar aibi ba mai girman kai ba, ba mai saurin fushi ba, ba mai buguwa ba, ba mai rikici ba, ba kuma mai son ƙazamar riba ba. 8 A maimakon haka dole yă zama mai karɓan baƙi, mai son abu nagari, mai kamunkai, mai adalci, mai tsarki da kuma natsattse. 9 Dole yă riƙe tabbataccen saƙon nan kam-kam yadda aka koyar, don yă iya ƙarfafa waɗansu da sahihiyar koyarwa yă kuma ƙaryata waɗanda suke gāba da shi.

  42. 13 Zai ƙaunace ku, yă albarkace ku, yă kuma ƙara yawanku. Zai albarkaci ’ya’yanku, amfanin gonarku; hatsinku, sabon ruwan inabinku da kuma mai, ƙanana shanunku, da ’yan tumaki na tumakinku, a ƙasar da ya rantse wa kakanninku cewa zai ba ku.

  43. 5 Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka

    kada kuma ka dangana ga ganewarka;

    6 cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi,

    zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.

    7 Kada ka zama mai hikima a ganinka;

    ka ji tsoron Ubangiji ka kuma guji mugunta.

    8 Wannan zai ba wa jikinka lafiya

    yă kuma adana ƙasusuwanka.

    9 Ka girmama Ubangiji da dukan dukiyarka,

    ta wurin miƙa masa nunan fari na dukan amfanin gonarka;

    10 ta haka rumbunanka za su cika har su zuba,

    randunanka kuma su cika har baki da sabon ruwan inabi.

  44. 11 ga karuwanci,

    ga tsoho da kuma sabon ruwan inabi,

    waɗanda suka ɗauke ganewar mutanena.

  45. 1 Saboda haka, ina roƙonku, ’yan’uwa, saboda yawan jinƙan Allah, ku miƙa jikunanku hadaya wadda take mai rai, mai tsarki abin karɓa kuma ga Allah, wannan ita ce hanyar hidimarku ta ruhaniya. 2 Kada ku ci gaba da yin abin da duniya take yi, sai dai ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so yake, abu mai kyau, mai daɗi da kuma cikakke.

    3 Gama ta wurin alherin nan da aka yi mini ne ina ce wa kowannenku. Kada yă ɗauki kansa fiye da yadda ya kamata, a maimakon haka bari yă auna kansa cikin natsuwa, gwargwadon baiwar bangaskiyar da Allah yi masa.

  46. 13 Hannatu tana addu’a a zuci, ba a jin muryarta, sai leɓunanta ne kawai suna motsi. Eli kuwa ya yi tsammani ta bugu ne. 14 Sai ya ce mata, “Har yaushe za ki ci gaba da maye? Ki daina shan ruwan inabi.”

    15 Hannatu ta ce, “Ba haka ba ne, ranka yă daɗe, ni mace ce da take cikin matsala ƙwarai da gaske. Ban sha ruwan inabi ba, ko wani abu mai sa maye, ina dai faɗa wa Ubangiji abin da yake damuna ne.

  47. 13 Duk da haka waɗansu suka yi musu ba’a suka ce, “Sun yi tatil da ruwan inabi ne.”

    14 Sai Bitrus ya miƙe tsaye tare da Sha Ɗayan nan, ya ɗaga muryarsa ya yi wa taron jawabi ya ce, “’Yan’uwana Yahudawa da dukanku da kuke zama cikin Urushalima, bari in bayyana muku wannan, ku saurara da kyau ga abin da zan faɗa. 15 Waɗannan mutane ba su bugu ba, kamar yadda kuka ɗauka. Yanzu ƙarfe tara na safe ne kawai!

  48. 8 Ku zama masu kamunkai, ku kuma zauna a faɗake. Abokin gābanku, Iblis yana kewayewa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai cinye.

  49. 30 Lot da ’ya’yansa biyu mata suka bar Zowar suka kuma zauna a cikin duwatsu, gama ya ji tsoro yă zauna a Zowar. Shi da ’ya’yansa biyu mata suka zauna a ciki wani kogo. 31 Wata rana ’yarsa babba ta ce wa ƙanuwarta, “Mahaifinmu ya tsufa, kuma babu wani mutum kusa a nan da zai yi mana ciki mu haifi ’ya’ya; yadda al’ada take a ko’ina a duniya. 32 Bari mu sa mahaifinmu yă sha ruwan inabi, sa’an nan sai mu kwana da shi, don kada zuriyar mahaifinmu ta ƙare.”

    33 A wannan dare, suka sa mahaifinsu ya sha ruwan inabi, ’yar farin ta shiga ta kwana da shi. Shi kuwa bai san sa’ad da ta kwanta ko sa’ad da ta tashi ba.

    34 Kashegari, ’yar farin ta ce wa ƙanuwar, “Jiya da dare na kwana da mahaifina. Bari mu sa yă sha ruwan inabi kuma yau da dare, ke ma ki shiga ki kwana da shi, domin kada zuriyar mahaifinmu ta ƙare.” 35 Sai suka sa mahaifinsu ya sha ruwan inabi, a wannan dare ma, ƙanuwar ta shiga ta kwana da shi. Bai kuwa san sa’ad da ta kwanta ko sa’ad da ta tashi ba.

    36 Ta haka ’ya’yan Lot biyu mata duk suka yi ciki daga mahaifinsu. 37 ’Yar farin ta haifi ɗa, ta kuma ba shi suna Mowab, shi ne mahaifin Mowabawa a yau. 38 ’Yar ƙaramar ma ta haifi ɗa, ta kuwa ba shi suna Ben-Ammi, shi ne mahaifin Ammonawa a yau.

  50. 1 Sarki Belshazar ya yi babban biki domin dubban hakimansa ya kuma sha ruwan inabi tare da su. 2 Yayinda Belshazar yake shan ruwan inabi, sai ya umarta a kawo zinariya da azurfan da Nebukadnezzar mahaifinsa ya kwaso daga haikali a Urushalima, saboda sarki da hakimansa, da matansa da ƙwarƙwaransa su sha da su. 3 Sai suka kawo kayan zinariyan nan da aka kwaso daga haikalin Allah a Urushalima, sarki kuwa da hakimansa, da matansa, da ƙwarƙwaransa suka yi ta sha da su. 4 Yayinda suke shan ruwan inabin, sai suka yabi allolin zinariya da azurfa, da na tagulla, da na ƙarfe, da na itace da kuma na dutse.

  51. 17 Game da umarnan nan dai, ban yaba muku ba, domin taruwarku ba ta kirki ba ce, ɓarna ce. 18 Da farko dai, na ji cewa sa’ad da kuka taru a matsayin ikkilisiya, akwai tsattsaguwa a tsakaninku, har na fara yarda da zancen. 19 Ba shakka dole a sami bambanci a tsakaninku don a nuna wa Allah ya amince da shi a cikinku. 20 Sa’ad da kuka taru, ba Cimar Ubangiji kuke ci ba, 21 gama yayinda kuke ci, kowa yakan ci gaba ba tare da jiran wani ba. Wani yă zauna da yunwa, wani kuma yă bugu. 22 Kai, ba ku da gidajen da za ku ci ku sha ne? Ko dai kun rena ikkilisiyar Allah ne, kuna kuma wulaƙanta waɗanda ba su da kome? Me zan ce muku? In yabe ku ne game da wannan? A’a, ko kaɗan!

  52. 8 A hannun Ubangiji akwai kwaf

    cike da ruwan inabi mai kumfa gauraye da kayan yaji;

    yakan zuba shi, dukan mugayen duniya kuwa

    su sha shi tas.

  53. 6 A kan wannan dutse Ubangiji Maɗaukaki zai shirya bikin abinci mai kyau don dukan mutane,

    liyafar ajiyayyen ruwan inabi da nama mafi kyau da ruwan inabi mafi kyau.

    7 A wannan dutse zai kawar da

    baƙin cikin da ya lulluɓe dukan mutane,

    ƙyallen da ya rufe dukan al’ummai;

    8 zai haɗiye mutuwa har abada.

    Ubangiji Mai Iko Duka zai share hawaye

    daga dukan fuskoki;

    zai kawar da kunyar mutanensa

    daga dukan duniya.

    Ubangiji ne ya faɗa.

    9 A wannan rana za su ce,

    “Tabbatacce wannan shi ne Allah;

    mun dogara a gare shi, ya kuma cece mu.

    Wannan shi ne Ubangiji, mun dogara a gare shi;

    bari mu yi murna mu kuma yi farin ciki a cikin cetonsa.”

  54. 5 Ku farka, ku bugaggu, ku yi kuka!

    Ku yi kuka da ƙarfi, ku dukan mashayan ruwan inabi;

    ku yi kuka mai ƙarfi saboda sabon ruwan inabi,

    gama an riga an ƙwace ta daga leɓunanku.

    6 Wata al’umma ta mamaye ƙasata,

    tana da ƙarfi ba ta kuma ƙidayuwa;

    tana da haƙoran zaki,

    da zagar zakanya.

  55. 9 Babu sauran shan ruwan inabi suna rera waƙa;

    barasa ya zama da ɗaci ga masu shanta.

  56. 14 ‘Yehonadab ɗan Rekab ya umarci ’ya’yansa maza kada su sha ruwan inabi sun kuma kiyaye wannan umarni. Har yă zuwa yau ba sa shan ruwan inabi, domin sun yi biyayya da umarnin kakansu. Amma na yi muku magana sau da sau, duk da haka ba ku yi biyayya ba.

  57. 31 Kin bi hanyar ’yar’uwarki; saboda haka zan sa kwaf nata a hannunki.

    32 “Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,

    “Za ki sha kwaf na ’yar’uwarki,

    kwaf wanda yake da girma da kuma zurfi;

    zai jawo dariya da kuma reni

    gama yana ɗauke da abubuwa da yawa.

    33 Za ki cika da buguwa da baƙin ciki,

    kwaf lalaci da kaɗaici,

    kwaf na ’yar’uwarki Samariya.

    34 Za ki sha shi ki kuma lashe shi ƙaf;

    za ki buga shi da ƙasa ya yi rugu-rugu

    ki tsattsage nononki.

    Ni Ubangiji Mai Iko Duka na faɗa.

  58. 22 Yesu ya ce musu, “Ba ku san abin da kuke roƙo ba. Za ku iya sha daga kwaf da zan sha?”

    Suka amsa, “Za mu iya.”

    23 Yesu ya ce musu, “Tabbatacce za ku sha daga kwaf na, sai dai zama a damana, ko haguna, ba ni nake da izinin bayarwa ba. Waɗannan wurare na waɗanda Ubana ya shirya wa ne.”

  59. 23 Sai kuma ya ɗauki kwaf ruwan inabi, ya yi godiya, ya kuma miƙa musu, dukansu suka sha daga ciki.

    24 Sai ya ce musu, “Wannan jinina ne na alkawari, wanda aka zubar da shi saboda mutane da yawa. 25 Gaskiya nake gaya muku, ‘Ba zan ƙara sha daga ’ya’yan inabi ba, sai ranan nan, da zan sha shi sabo a mulkin Allah.’ ”

  60. 17 Bayan ya ɗauki kwaf ruwan inabi, ya yi godiya, sai ya ce, “Ku karɓa, ku rarraba wa junanku. 18 Ina dai gaya muku, ba zan ƙara sha daga ’ya’yan inabi ba, sai mulkin Allah ya zo.”

  61. 9 Mala’ika na uku ya biyo su ya ce da babbar murya, “Duk wanda ya yi wa dabban nan da siffarta sujada ya kuma sami alamarta a goshi ko a hannu, 10 shi ma zai sha ruwan inabin fushin Allah, wanda aka zuba da duk ƙarfinsa a kwaf fushinsa. Za a ba shi azaba da farar wuta mai ci a gaban tsarkakan mala’iku da na Ɗan Ragon. 11 Hayaƙin azabarsu kuwa zai dinga tashi har abada abadin. Kuma babu hutu dare ko rana wa waɗanda suke wa dabbar da siffarta sujada, ko kuwa ga duk wanda ya sami alamar sunanta.”

  62. 18 In mutum yana da gagararren ɗa mai tawaye, wanda ba ya biyayya ga mahaifinsa da mahaifiyarsa, ba ya kuma jin su sa’ad da suke horonsa, 19 mahaifinsa da mahaifiyarsa za su kama shi su kawo shi ga dattawa a ƙofar garinsu. 20 Za su ce wa dattawan, “Wannan ɗanmu gagararre ne, mai tawaye. Ba ya mana biyayya. Mai zari ne, kuma mashayi.” 21 Sa’an nan dukan mazan garinsa za su jajjefe shi har yă mutu. Dole ku fid da mugu daga cikinku. Dukan Isra’ila kuwa za su ji wannan su kuma ji tsoro.

  63. 28 Absalom ya umarci mutanensa ya ce, “Ku saurara! Sa’ad da Amnon ya bugu sosai da giya na kuma ce muku, ‘Ku bugi Amnon,’ sai ku kashe shi. Kada ku ji tsoro. Ashe, ba ni ne na ba ku wannan umarni ba? Ku yi ƙarfin hali, ku kuma yi jaruntaka.” 29 Saboda haka mutanen Absalom suka yi wa Amnon abin da Absalom ya umarta. Sai dukan sauran ’ya’yan sarki maza suka hau dawakansu suka gudu.

  64. 8 Ubangiji ya rantse da hannunsa na dama

    ta hannunsa kuma mai iko cewa,

    “Ba zan ƙara ba da hatsinki

    ya zama abinci ga abokan gābanki ba,

    baƙi kuma ba za su ƙara shan ruwan inabin

    wanda kika sha wahala samu ba;

    9 amma waɗanda suka girbe shi za su ci shi

    su kuma yabi Ubangiji,

    waɗanda kuma suka tattara ’ya’yan inabi za su sha shi

    a filayen wurina mai tsarki.”

  65. 15 Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya faɗa mini, “Ka karɓi kwaf ruwan inabin nan na fushina a wurina, ka sa dukan al’umman da na aike ka gare su, su sha. 16 Sa’ad da suka sha, za su yi ta tangaɗi su kuma yi hauka saboda takobin da zan aika a cikinsu.” 17 Saboda haka na karɓi kwaf daga hannun Ubangiji na sa dukan al’ummai waɗanda ya aiko ni wurinsu su sha.

  66. 18 Ta haka Ubangiji zai yi kishin ƙasarsa

    yă kuma ji tausayin mutanensa.

    19 Ubangiji zai amsa musu ya ce,

    “Ina aika da hatsi, sabon ruwan inabi, da mai,

    isashe da zai ƙosar da ku sosai;

    ba kuma zan ƙara maishe ku

    abin dariya ga al’ummai ba.

  67. 18 “A wannan rana duwatsu za su ɗiga da sabon ruwan inabi,

    tuddai kuma za su malmalo madara;

    dukan rafuffukan Yahuda za su yi ta gudano da ruwa.

    Maɓulɓula kuma za tă fito daga gidan Ubangiji

    haka ma ruwa a kwarin itatuwan ƙirya.

  68. 1 Hikima ta gina gidanta;

    ta yi ginshiƙansa bakwai.

    2 Ta shirya abincinta gauraye da ruwan inabinta;

    ta kuma shirya teburinta.

    3 Ta aiki bayinta mata, tana kuma kira

    daga wurare masu tsayi na birnin.

    4 “Bari dukan waɗanda suke marasa azanci su zo nan ciki!”

    Tana faɗa wa marasa hankali.

    5 “Ku zo, ku ci abincina

    da ruwan inabin da na gauraye.

  69. 27 “Sa’an nan na faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ku sha, ku bugu ku kuma yi amai, ku fāɗi, kada kuma ku ƙara tashi saboda takobin da zan aiko muku.’ 28 Amma in suka ki su karɓi kwaf ɗin daga hannunka su sha, ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa dole ku sha! 29 Ga shi, na sa masifa tă yi aiki cikin birnin da ake kira da sunana, kuna gani za ku tafi ba hukunci? Ba za ku tafi ba hukunci ba, gama ina kawo wa dukan mazaunan duniya takobi, in ji Ubangiji Maɗaukaki.’

  70. 8 Amma Daniyel ya ƙudura a zuciyarsa ba zai ƙazantar da kansa da abinci da ruwan inabin sarki ba, sai ya tambayi sarkin fada don a ba shi izinin kada yă ƙazantar da kansa ta wannan hanya.

  71. 3 Ban ci abinci mai kyau ba; ba nama ko ruwa inabin da ya shiga bakina; kuma ba na amfani da man shafawa gaba ɗaya har sai da sati nan uku suka wuce.

  72. 22 Kada ku ji tsoro, ya ku namun jeji,

    gama wuraren kiwo sun yi kore shar.

    Itatuwa suna ba da ’ya’yansu;

    itacen ɓaure da na inabi suna ba da amfaninsu.

    23 Ku yi murna, ya ku mutanen Sihiyona,

    ku yi farin ciki cikin Ubangiji Allahnku,

    gama ya ba ku

    ruwan bazara cikin adalci.

    Yakan aika muku yayyafi a yalwace,

    na bazara da na kaka, kamar dā.

    24 Masussukai za su cika da hatsi;

    randuna za su cika da sabon ruwan inabi da mai suna zuba.

  73. 42 Ya sāke tafiya sau na biyu, ya yi addu’a ya ce, “Ubana, in ba zai yiwu a ɗauke wannan kwaf ba sai na sha shi, to, bari a aikata nufinka.”

  74. 34 A can, suka ba shi ruwan inabi gauraye da wani abu mai ɗaci yă sha. Amma da ya ɗanɗana, sai ya ƙi sha.

  75. 13 Yesu ya amsa ya ce, “Kowa ya sha wannan ruwa, zai sāke jin ƙishirwa, 14 amma duk wanda ya sha ruwan da zan ba shi, ba zai ƙara jin ƙishirwa ba. Tabbatacce, ruwan da zan ba shi, zai zama masa maɓuɓɓugan ruwa da yake ɓuɓɓugowa har yă zuwa rai madawwami.”

  76. 53 Sai Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, sai kun ci naman jikin Ɗan Mutum kuka kuma sha jininsa, ba za ku kasance da rai a cikinku ba. 54 Duk wanda ya ci naman jikina ya kuma sha jinina, yana da rai madawwami. Ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe. 55 Gama naman jikina abinci ne na gaskiya jinina kuma abin sha ne na gaskiya. 56 Duk wanda ya ci naman jikina ya kuma sha jinina, yana cikina, ni kuma ina cikinsa.

  77. 11 Sai Yesu ya umarce Bitrus ya ce, “Mai da takobinka kube! Ba zan sha kwaf da Uba ya ba ni ba?”

  78. 19 Ko da yake ina da ’yanci ba na kuma ƙarƙashin kowa, na mai da kaina bawa ga kowa, domin in rinjayi mutane da yawa. 20 Ga Yahudawa na zama kamar mutumin Yahuda, domin in rinjayi Yahudawa. Ga waɗanda suke ƙarƙashin doka kuma, na zama kamar wanda yake ƙarƙashin Dokar (ko da yake ni kaina ba na ƙarƙashin Doka), domin in rinjayi waɗanda suke ƙarƙashin Doka. 21 Ga waɗanda ba su da Dokar kuwa, na zama kamar wanda ba shi da Dokar (ko da yake ba ni da ’yanci daga dokar Allah, amma ina ƙarƙashin dokar Kiristi), domin in rinjayi waɗanda ba su da dokar. 22 Ga waɗanda ba su da ƙarfi, na zama marar ƙarfi, domin in rinjayi waɗanda ba su da ƙarfi. Na zama dukan abu ga dukan mutane, domin ko ta yaya in zai yiwu, in ceci waɗansu. 23 Ina yin dukan waɗannan ne saboda bishara, domin in sami rabo a cikin albarkarta.

  79. 23 “Ana da dama a yi kome” sai dai ba kome ba ne yake da amfani. “Ana da dama a yi kome” sai dai ba kome ba ne mai ginawa. 24 Kada wani yă kula da kansa kawai, sai dai yă kula da waɗansu kuma.

  80. 28 Allah yă ba ka daga raɓar sama da kuma yalwar ƙasa,

    yalwar hatsi da sabon ruwan inabi.

  81. 13 Mala’ikan Ubangiji ya ce, “Dole matarka ta kiyaye duk abin da na riga na gaya mata. 14 Kada tă ci kowane iri abin da ya fito daga inabi, ba kuwa za tă sha ruwan inabi, ko abu mai sa maye ko ta ci abu marar tsarki ba. Dole tă kiyaye duk abin da na umarce mata.”

  82. 8 A shekara ta ashirin da shida ta Asa sarkin Yahuda, Ela ɗan Ba’asha ya zama sarkin Isra’ila, ya kuma yi mulki a Tirza shekaru biyu.

    9 Zimri, ɗaya daga cikin shugabanni, wanda ya shugabanci rabin kekunan yaƙin Ela, ya yi maƙarƙashiya a kansa. Ela yana a Tirza a lokacin, ya bugu a gidan Arza, sarkin fada a Tirza. 10 Zimri ya shiga, ya buge shi ya kashe a shekara ta ashirin da bakwai na Asa sarkin Yahuda. Sa’an nan ya gāje shi a matsayin sarki.

  83. 20 Bari idanunsa su ga yadda zai hallaka;

    bari yă sha daga fushin Maɗaukaki.

  84. 1 Kaito ga wannan rawani, girman kai na mashayan Efraim,

    ga fure mai yanƙwanewa, darajar kyansa,

    da aka sa a kan kwari mai ba da amfani,

    ga birnin nan, wadda take girman kan waɗanda aka ƙasƙantar da ruwan inabinsu!

    2 Duba, Ubangiji yana da wanda yake da iko da kuma ƙarfi.

    Kamar dutsen ƙanƙara da kuma iska mai ɓarna,

    kamar kwararowar ruwa da rigyawa mai kirmewa,

    zai jefa shi har ƙasa da ƙarfi.

    3 Za a tattaka wannan rawani,

    girman kai na mashayan Efraim da ƙafa.

  85. 17 “Ɗan mutum, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ka gayyato kowane irin tsuntsu da dukan namun jeji, ‘Ku taru ku kuma zo wuri ɗaya daga ko’ina don hadayar da nake shirya muku, babbar hadaya a kan duwatsun Isra’ila. A can za ku ci nama ku kuma sha jini. 18 Za ku ci naman manyan mutane ku kuma sha jinin sarakunan duniya sai ka ce an yanka raguna da ’yan tumaki, awaki da bijimai, dukansu turkakkun dabbobi daga Bashan. 19 A hadayar da nake shirya muku, za ku ci kitse sai kun ƙoshi ku kuma sha jini sai kun bugu. 20 A teburina za ku ci iya ƙoshiyarku da naman jama’a da kuma mahaya, manyan mutane da sojoji na kowane iri,’ in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

  86. 4 Kuna kwanciya a kan gadajen da aka yi musu shimfiɗar hauren giwa

    kuna mimmiƙe a kan kujerunku.

    Kuna cin naman ƙibabbun raguna

    da na ƙosassun ’yan maruƙa.

    5 Kuna kaɗa molayenku yadda Dawuda ya yi

    kuna ƙirƙiro waƙoƙi a kan kayan kaɗe-kaɗe.

    6 Da manyan kwanoni kuke shan ruwan inabi

    kuna kuma shafa mai mafi kyau,

    amma ba kwa baƙin ciki game da kangon da Yusuf ya zama.

    7 Saboda haka za ku zama na farkon da za su tafi zaman bauta;

    bukukkuwanku da shagulgulanku za su ƙare.

  87. 37 A rana ta ƙarshe kuma mafi girma ta Bikin, Yesu ya tsaya ya yi magana da babbar murya ya ce, “Duk mai jin ƙishirwa, yă zo wurina yă sha.

  88. 13 Saboda haka, ku shirya kanku don aiki; ku zama masu kamunkai; ku kafa begenku duka a kan alherin da za a ba ku sa’ad da aka bayyana Yesu Kiristi. 14 Kamar ’ya’ya masu biyayya, kada ku bi mugayen sha’awace-sha’awacen da dā kuke da su sa’ad da kuke rayuwa a cikin jahilci. 15 Amma kamar yadda wanda ya kira ku yake mai tsarki, haka ku ma sai ku kasance masu tsarki cikin dukan abubuwan da kuke yi;

  89. 17 Waɗannan mutane maɓulɓulai ne babu ruwa da kuma hazon da guguwar iska take kora. An shirya matsanancin duhu dominsu. 18 Gama suna surutai banza na girman kai, ta wurin son bin fasikanci na mutuntaka, sukan jan hankulan mutanen da suke kuɓucewa daga waɗancan masu zama cikin kuskure. 19 Suna yin musu alkawarin ’yanci, yayinda su kansu bayi ne ga aikin lalata gama mutum bawa ne ga duk abin da ya mallake shi. 20 In har sun kuɓuta daga lalacin duniya ta wurin sanin Ubangijinmu da kuma Mai Cetonmu Yesu Kiristi sai suka sāke koma a cikin lalacin, har ya rinjaye su, za su fi muni a ƙarshe fiye da farko. 21 Zai fi musu kyau da ba su taɓa sanin hanyar adalci ba, fiye da a ce sun sani sa’an nan su juya bayansu ga umarni mai tsarkin nan da aka ba su. 22 A kansu karin maganan nan gaskiya ce, “Kare ya koma kan amansa,” da kuma, “Alade da aka yi wa wanka, ya koma birgimarsa cikin laka.”

  90. 3 Gama dukan al’ummai sun sha ruwan inabin

    haukan zinace zinacenta.

    Sarakunan duniya sun yi zina tare da ita,

    attajiran duniya kuma sun arzuta da almubazzarancinta.”