22 Bible Verses About Spring
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
10 Ƙaunataccena ya yi magana ya ce mini,
“Tashi, ƙaunatacciyata,
kyakkyawata, ki zo tare da ni.
11 Duba! Damina ta wuce;
ruwan sama ya ɗauke ya kuma ƙare.
12 Furanni sun hudo a duniya;
lokaci yin waƙa ya zo,
ana jin kukan kurciyoyi
ko’ina a ƙasarmu.
13 Itacen ɓaure ya fid da ’ya’yansa da sauri;
tohon inabi suna ba da ƙanshinsu.
Tashi, zo, ƙaunatacciyata;
kyakkyawata, zo tare da ni.”
-
23 Sukan jira ni kamar yadda ake jiran ruwan sama.
Sukan sha daga cikin maganganuna kamar mai shan ruwan bazara.
-
3 Bari mu yarda da Ubangiji;
bari mu nace gaba don mu yarda da shi.
Muddin rana tana fitowa,
zai bayyana;
zai zo mana kamar ruwan bazara,
kamar ruwan saman farko da yake jiƙe ƙasa.”
-
1 Ku roƙi Ubangiji yă ba ku ruwa a lokacin bazara;
Ubangiji ne yake yin gizagizan hadari.
Shi ne yake ba wa mutane yayyafin ruwan sama
yana kuma ba da tsire-tsire na fili ga kowa.
-
22 Kada ku ji tsoro, ya ku namun jeji,
gama wuraren kiwo sun yi kore shar.
Itatuwa suna ba da ’ya’yansu;
itacen ɓaure da na inabi suna ba da amfaninsu.
23 Ku yi murna, ya ku mutanen Sihiyona,
ku yi farin ciki cikin Ubangiji Allahnku,
gama ya ba ku
ruwan bazara cikin adalci.
Yakan aika muku yayyafi a yalwace,
na bazara da na kaka, kamar dā.
-
7 Saboda haka ’yan’uwa, sai ku yi haƙuri har dawowar Ubangiji. Ku dubi yadda manomi yakan jira gona ta ba da amfaninta mai kyau, da kuma yadda yake haƙurin jiran ruwan sama na damina da na kaka.
-
1 Akwai lokaci domin kowane abu,
da kuma lokaci domin kowane aiki a duniya.
2 Lokacin haihuwa da lokacin mutuwa,
lokacin shuki da lokacin tumɓukewa.
3 Lokacin kisa da lokacin warkarwa,
lokacin rushewa da lokacin ginawa.
4 Lokacin kuka da lokacin dariya,
lokacin makoki da lokacin rawa.
5 Lokacin warwatsa duwatsu da lokacin tara su,
lokacin runguma da lokacin dainawa.
6 Lokacin nema, da lokacin fid da zuciya,
lokacin ajiyewa da lokacin zubarwa.
7 Lokacin yagewa da lokacin ɗinkewa,
lokacin yin shiru da lokacin magana.
8 Lokacin ƙauna da lokacin ƙiyayya,
lokacin yaƙi da lokacin salama.
-
7 Gama Ubangiji Allahnku yana fitar da ku zuwa cikin ƙasa mai kyau, ƙasa mai rafuffuka da tafkunan ruwa, tare da maɓulɓulai masu gudu a kwari da tuddai; 8 ƙasa mai alkama da sha’ir, inabi da ɓaure, rumman, man zaitun da zuma; 9 ƙasa inda abinci ba zai yi ƙaranci ba, ba kuma za ku rasa kome ba; ƙasa ce inda ƙarfe ne duwatsunta, ana kuma haƙar tagulla a tuddanta.
-
13 Saboda haka in kun yi biyayya ga umarnan da nake ba ku a yau cikin aminci, kuna ƙaunaci Ubangiji Allahnku, kuna kuma bauta masa da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku, 14 sai in aika da ruwan sama a ƙasarku a lokacinsa, ruwan saman bazara da kuma na kaka, don ku tattara hatsinku, sabon inabinku da kuma manku.
-
LITTAFI NA ƊAYA
1 Mai farin ciki ne mutumin
da ba ya aiki da shawarar mugaye
ko yă yi abin da masu zunubi suke yi
ko yă zauna tare da masu yin ba’a.
2 Amma yana jin daɗin bin dokar Ubangiji,
kuma yana ta nazarinta dare da rana.
3 Yana kama da itacen da aka shuka kusa da maɓulɓulan ruwa,
wanda yake ba da amfani a daidai lokaci
wanda kuma ganyensa ba sa bushewa.
Duk abin da yake yi, yakan yi nasara.
-
15 Sa’ad da fuskar sarki ta haska, yana nufin rai ke nan;
tagomashinsa yana kamar girgijen ruwa a bazara.
-
2 Bari koyarwata tă zubo kamar ruwan sama
kalmomina kuma su sauko kamar raɓa,
kamar yayyafi a kan sabuwar ciyawa,
kamar ruwan sama mai yawa a kan tsirai marasa ƙarfi.
-
11 Gama kamar yadda ƙasa takan sa tsire-tsire su tohu
lambu kuma ya sa iri ya yi girma,
haka Ubangiji Mai Iko Duka zai sa adalci da yabo
su tsiro a gaban dukan al’ummai.
-
26 Kamar rafi mai laka ko rijiyar da ta gurɓace
haka yake da mai adalci wanda ya miƙa wuya ga mugaye.
-
28 “Me ya sa kuke damuwa a kan riguna? Ku dubi yadda furannin jeji suke girma mana. Ba sa aiki ko saƙa. 29 Duk da haka ina gaya muku ko Solomon cikin dukan darajarsa bai sa kayan adon da ya kai na ko ɗaya a cikinsu ba. 30 In haka Allah yake yi wa ciyawar jeji sutura, wadda yau tana nan, gobe kuwa a jefa a cikin wuta, ba zai ma fi yi muku sutura ba, ya ku masu ƙarancin bangaskiya?
-
14 Allah kuma ya ce, “Bari haskoki su kasance a sararin sama domin su raba yini da dare, bari su zama alamu domin su nuna yanayi, da ranaku, da kuma shekaru, 15 bari kuma haskokin su kasance a sararin sama domin su ba da haske a duniya.” Haka kuwa ya kasance.
-
9 Gama a gare ka akwai maɓulɓular rai
cikin haskenka mukan ga haske.
-
10 Ya sa maɓulɓulai suka zuba ruwa cikin kwaruruka;
yana gudu tsakanin duwatsu.
11 Suna ba da ruwa ga dukan namun jeji;
jakunan jeji suna kashe ƙishirwansu.
12 Tsuntsaye sarari suna sheƙunansu kusa da ruwan;
suna rera cikin rassa.
13 Yana wa duwatsu banruwa daga ɗakinsa na sama;
ƙasa tana ƙoshiya da amfanin aikinsa.
-
14 Koyarwar mai hikima maɓulɓulan rai ne,
mai juyar da mutum daga tarkon mutuwa.
-
27 Tsoron Ubangiji shi ne maɓulɓular rai
yakan juye mutum daga tarkon mutuwa.
-
13 “Mutanena sun aikata zunubai guda biyu.
Sun rabu da ni,
ni da nake maɓulɓular ruwan rai,
sun kuma haƙa tankunan ruwansu,
tankuna ruwan da suka fashe da ba za su iya riƙe ruwa ba.
-
23 Amma mutanen nan suna da tauraren zukata, kuma ’yan tawaye ne;
sun kauce suka kuma rabu da ni.
24 Ba sa faɗa wa kansu, ‘Bari mu ji tsoron Ubangiji Allahnmu,
wanda yake ba mu ruwan sama a kan kari na kaka da na bazara,
wanda kullum yake tabbatar mana da girbi.’
25 Laifofinku sun raba ku da waɗannan abubuwa;
zunubanku sun hana ku samun alheri.
Shows Read in context, Share and Copy.