25 Bible Verses About Fall

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Fall
  1. 12 Waɗannan mutane sun zama kamar ƙazanta a taronku na soyayya, suna ta ciye-ciye a cikinku, ba kunya ba tsoro. Su masu kiwo ne da suke ciyar da kansu kawai. Su kamar hadari ne da babu ruwa da iska take kori. Su kamar itatuwa ne, marasa ’ya’ya da rani, waɗanda aka tumɓuke, ko kamar itatuwan da aka tumɓuke suka kuma mutu ƙurmus. 13 Su kamar raƙuman ruwan teku ne masu hauka, suna taƙama da tumbatsan kumfar kunyarsu. Su kamar taurari ne masu yawo barkatai, waɗanda aka ajiye mugun duhu saboda su har abada.

  2. 24 Ba sa faɗa wa kansu, ‘Bari mu ji tsoron Ubangiji Allahnmu,

    wanda yake ba mu ruwan sama a kan kari na kaka da na bazara,

    wanda kullum yake tabbatar mana da girbi.’

    25 Laifofinku sun raba ku da waɗannan abubuwa;

    zunubanku sun hana ku samun alheri.

  3. 1 Akwai lokaci domin kowane abu,

    da kuma lokaci domin kowane aiki a duniya.

    2 Lokacin haihuwa da lokacin mutuwa,

    lokacin shuki da lokacin tumɓukewa.

  4. 5 Masu albarka ne waɗanda ƙarfinsu yana daga gare ka,

    waɗanda suka kafa zukatansu a yin tafiya zuwa wuri mai tsarki ne.

    6 Yayinda suke wuce ta Kwarin Baka,

    sukan mai da shi wurin maɓulɓulai;

    ruwan sama na farko kuma kan rufe shi da tafkuna.

  5. 13 Saboda haka in kun yi biyayya ga umarnan da nake ba ku a yau cikin aminci, kuna ƙaunaci Ubangiji Allahnku, kuna kuma bauta masa da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku, 14 sai in aika da ruwan sama a ƙasarku a lokacinsa, ruwan saman bazara da kuma na kaka, don ku tattara hatsinku, sabon inabinku da kuma manku. 15 Zan tanadar da ciyawa a filaye don shanunku, za ku ci, ku kuma ƙoshi.

  6. 22 “Muddin duniya tana nan,

    lokacin shuki da na girbi,

    lokacin sanyi da na zafi,

    lokacin damina da na rani,

    dare da rana

    ba za su daina ba.”

  7. 1 “ ‘A rana ta farko ga wata na bakwai, a yi tsattsarkan taro, kada kuma a yi aikin da aka saba na kullum. Rana ce don busa ƙahoni.

  8. 19 Wata ne ke ƙididdigar lokuta,

    rana kuma ta san sa’ad da za tă fāɗi.

  9. 4 Rago ba ya noma a lokacin noma;

    saboda haka a lokacin girbi ba ya bukata samun kome.

  10. 27 “Rana ta goma ta wata bakwai, za tă zama Ranar Kafara. Sai ku yi taro mai tsarki don ku yi mūsun kanku ku kuma miƙa hadayar da aka yi da wuta ga Ubangiji.

  11. 34 “Faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘A ranar goma sha biyar ga wata na bakwai, za a fara Bikin Tabanakul na Ubangiji, zai kuma ɗauki kwana bakwai.

  12. 7 “ ‘A rana ta goma ga wannan watan bakwai, za a yi tsattsarkan taro. Ba za ku ci abinci ba, ba kuma za ku yi aiki ba.

  13. 12 “ ‘A rana ta goma sha biyar ga wata na bakwai, za a yi tsattsarkan taro, ba kuwa za a yi aikin da aka saba yi ba. Ku yi biki ga Ubangiji har kwana bakwai.

  14. 7 Saboda haka ’yan’uwa, sai ku yi haƙuri har dawowar Ubangiji. Ku dubi yadda manomi yakan jira gona ta ba da amfaninta mai kyau, da kuma yadda yake haƙurin jiran ruwan sama na damina da na kaka. 8 Haka ku ma, ku yi haƙuri, ku tsaya da ƙarfi, gama dawowar Ubangiji ya yi kusa.

  15. 23 Ku yi murna, ya ku mutanen Sihiyona,

    ku yi farin ciki cikin Ubangiji Allahnku,

    gama ya ba ku

    ruwan bazara cikin adalci.

    Yakan aika muku yayyafi a yalwace,

    na bazara da na kaka, kamar dā.

  16. 37 Sai ya ce wa almajiransa, “Girbi yana da yawa, amma ma’aikata kaɗan ne. 38 Saboda haka ku roƙi Ubangijin girbi, yă aiko da ma’aikata cikin gonarsa na girbi.”

  17. 9 Kada mu gaji da yin nagarta, gama a daidai lokaci za mu girbe amfani, in ba mu fid da zuciya ba.

  18. 14 Allah kuma ya ce, “Bari haskoki su kasance a sararin sama domin su raba yini da dare, bari su zama alamu domin su nuna yanayi, da ranaku, da kuma shekaru,

  19. 26 Zan albarkace su in kuma sa tuduna kewaye da su. Zan zubo yayyafi a lokacinsa; za a kasance da yayyafin albarka.

  20. 21 “Kwana shida za ku yi aiki, amma a rana ta bakwai za ku huta; ko da lokacin noma ne, ko lokacin girbi, sai ku huta.

  21. 37 An kafa tushen haikalin Ubangiji a shekara ta huɗu, a watan Zif. 38 A shekara ta goma sha ɗaya, a watan Bul, wata na takwas ke nan, aka gama haikalin daidai yadda aka tsara shi bisa ga fasalinsa. Solomon ya ɗauki shekara bakwai yana ginin haikalin.

  22. 9 Guguwa tana fitowa daga inda take,

    sanyi kuma daga iska mai sanyi.

  23. 17 Duk da haka bai bar kansa babu shaida ba. Ya nuna alheri ta wurin ba ku ruwan sama da kuma amfanin gona a lokutansu; ya ba ku abinci mai yawa ya kuma cika zukatanku da farin ciki.”

  24. 6 Bari kowane abu mai numfashi yă yabi Ubangiji.

    Yabi Ubangiji.

  25. 5 Shi da ya tattara hatsi da rani ɗa ne mai hikima,

    amma shi da yakan yi barci a lokacin girbi ɗa ne wanda ya zama abin kunya.