51 Bible Verses About Rest

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Rest
  1. 28 “Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji kuke kuma fama da kaya, zan kuwa ba ku hutu. 29 Ku ɗauki karkiyata a kanku, ku kuma yi koyi da ni, gama ni mai tawali’u ne marar girman kai, za ku kuwa sami hutu don rayukanku. 30 Gama karkiyata mai sauƙi ce, kayana kuma marasa nauyi ne.”

  2. 1 Saboda haka, da yake alkawarin shiga hutunsa yana nan har yanzu, sai mu yi hankali kada waninku yă kāsa shiga. 2 Gama mu ma mun ji an yi mana wa’azin bishara, kamar yadda su ma suka ji; sai dai saƙon da suka ji ba tă amfane su ba, domin waɗanda suka ji ba su karɓe shi da bangaskiya ba. 3 Mu kam da muka gaskata mu ne muka shiga wannan hutu, kamar yadda Allah ya ce,

    “Saboda haka na yi rantsuwa cikin fushina,

    ‘Ba za su taɓa shiga hutuna ba.’ ”

    Allah ya faɗa haka ko da yake ya riga ya kammala aikinsa tun halittar duniya. 4 Gama a wani wuri ya yi magana a kan rana ta bakwai cikin waɗannan kalmomi, “A rana ta bakwai kuwa Allah ya huta daga dukan aikinsa.” 5 Haka kuma a nassin nan ya ce, “Ba za su taɓa shiga hutuna ba.”

    6 Har yanzu dai da sauran dama domin waɗansu su shiga, su kuwa waɗanda aka fara yi wa albishirin nan sun kāsa shiga saboda rashin biyayya. 7 Saboda haka Allah ya sāke sa wata rana, yana kiranta Yau, bayan wani dogon lokaci Allah ya yi magana ta bakin Dawuda, yadda aka riga aka faɗa,

    “Yau, in kuka ji muryarsa,

    kada ku taurare zukatanku.”

    8 Gama da a ce Yoshuwa ya ba su hutu, da Allah bai yi magana daga baya a kan wata rana dabam ba. 9 Har yanzu, akwai wani hutun Asabbacin da ya rage domin mutanen Allah; 10 gama duk wanda ya shiga hutun Allah, shi ma yakan huta daga nasa aiki, kamar yadda Allah ya huta daga nasa. 11 Saboda haka, bari mu yi iyakacin ƙoƙarinmu mu shiga wannan hutu, don kada wani yă kāsa ta wurin bin gurbinsu na rashin biyayya.

    12 Maganar Allah tana da rai, tana kuma da ƙarfin aiki. Ta fi kowane takobi mai baki biyu kaifi. Maganarsa takan ratsa har ciki-ciki, tana raba rai da ruhu, gaɓoɓi da kuma ɓargon ƙashi; har sai ta tone ainihi wane ne muke. 13 Babu wani abu cikin dukan halittar da yake ɓoye daga fuskar Allah. Kowane abu a buɗe yake yana kuma a shimfiɗe a idanun wanda dole mu ba da lissafi a gare shi.

    14 Saboda haka, da yake muna da babban firist mai girma wanda ya ratsa sama, Yesu Ɗan Allah, bari mu riƙe bangaskiyan nan wadda muke shaidawa da ƙarfi. 15 Gama babban firist da muke da shi ba marar juyayin kāsawarmu ba ne, amma muna da wanda aka gwada ta kowace hanya, kamar dai yadda akan yi mana, duk da haka bai yi zunubi ba. 16 Saboda haka sai mu matso kusa da kursiyin alheri da ƙarfi zuciya, don mu sami jinƙai mu kuma sami alherin da zai taimake mu a lokacin bukata.

  3. 1 Ta haka aka gama yin sammai da duniya da dukan abubuwan da suke cikinsu.

    2 Kafin kwana ta bakwai, Allah ya gama aikin da yake yi, saboda haka a kwana ta bakwai, ya huta daga dukan aikinsa. 3 Allah kuwa ya albarkaci kwana ta bakwai, ya kuma mai da ita mai tsarki, saboda a kanta ne ya huta daga dukan aikin halittar da ya yi.

  4. 30 Manzannin suka taru kewaye da Yesu, suka ba shi rahoton duk abin da suka yi, da kuma suka koyar. 31 To, saboda mutane da yawa suna kai da kawowa, har ma ba su sami damar cin abinci ba, sai ya ce musu, “Ku zo mu kaɗaita inda ba kowa don ku ɗan huta.”

    32 Sai suka tafi a jirgin ruwa su kaɗai, inda ba kowa.

  5. 8 Ka tuna da ranar Asabbaci domin ka kiyaye ta da tsarki. 9 Kwana shida za ka yi dukan aikinka, 10 amma rana ta bakwai Asabbaci ne ga Ubangiji, Allahnka. A ranar ba za ka yi wani aiki ba, ko kai, ko ɗanka, ko ’yarka, ko bawa, ko baiwa, ko dabbarka, ko baƙon da yake zama tare da kai. 11 Gama kwana shida Ubangiji ya halicci sama da ƙasa, da teku, da duk abin da yake cikinsu, amma ya huta a rana ta bakwai. Saboda haka Ubangiji ya albarkaci ranar Asabbaci, ya kuma mai da ita mai tsarki.

  6. Zabura ta Dawuda.

    1 Ubangiji ne yake kiwona, ba zan rasa kome ba,

    2 Yakan sa in kwanta a makiyaya mai ɗanyar ciyawa,

    yakan bi da ni kusa da ruwaye marar hayaniya,

    3 yakan maido da raina.

    Yakan bi da ni a hanyoyin adalci

    saboda sunansa.

  7. 6 Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya. 7 Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za tă tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.

    8 A ƙarshe, ’yan’uwa, duk abin da yake na gaskiya, duk abin da yake na girmamawa, duk abin da yake daidai, duk abin da yake da tsarki, duk abin da yake kyakkyawa, duk abin da yake na sha’awa, in ma wani abu mafifici ne, ko ya cancanci yabo, ku yi tunani a kan irin abubuwan nan. 9 Duk abin da kuka koya ko kuka karɓa ko kuka ji daga wurina, ko kuka gani a cikina, ku yi aiki da shi. Allah na salama kuma zai kasance tare da ku.

  8. 13 Sai na ji murya daga sama ta ce, “Rubuta, Masu albarka ne matattun da suka mutu cikin Ubangiji daga yanzu zuwa gaba.”

    “I, za su huta daga faman aikinsu, gama ayyukansu za su bi su,” in ji Ruhu.

    14 Na duba, can gabana kuwa ga farin girgije, zaune kuma a kan girgijen kuwa ga wani da ya yi kamar “ɗan mutum” tare da rawanin zinariya a kansa da kuma lauje mai kaifi a hannunsa.

  9. 11 “Me ya sa ban mutu ba da za a haife ni,

    ko kuma in mutu sa’ad da ana haihuwata ba?

    12 Me ya sa aka haife ni,

    aka tanada nono na sha na rayu?

    13 Da yanzu ina kwance cikin salama;

    da ina barcina cikin salama

    14 tare da sarakuna da mashawarta a cikin ƙasa,

    waɗanda suka gina wa kansu wuraren da yanzu duk sun rushe,

    15 da shugabanni waɗanda suke da zinariya,

    waɗanda suka cika gidajensu da azurfa.

    16 Ko kuma don me ba a ɓoye ni a cikin ƙasa kamar jaririn da aka haifa ba rai ba,

    kamar jaririn da bai taɓa ganin hasken rana ba.

    17 A wurin mugaye za su daina yin mugunta,

    gajiyayyu kuma za su huta.

    18 Waɗanda aka daure za su sami jin daɗin;

    an sake su ba za su sāke jin ana tsawata masu ba.

    19 Manyan da ƙanana suna a can,

    bawa kuma ya sami ’yanci daga wurin maigidansa.

  10. 12 Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, 13 “Ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘Dole ku kiyaye Asabbataina. Wannan zai zama alama tsakanina da ku daga tsara zuwa tsara, saboda ku sani ni ne Ubangiji, wanda ya mai da ku masu tsarki.

    14 “ ‘Ku kiyaye Asabbaci, domin yă zama mai tsarki a gare ku. Duk wanda ya ƙazantar da shi, za a kashe shi; duk wanda ya yi wani aiki a ranar, za a ware shi daga mutane. 15 Kwana shida, za a yi aiki, amma a rana ta bakwai, Asabbaci ne na hutu, mai tsarki ga Ubangiji. Duk wanda ya yi wani aiki a Asabbaci, za a kashe shi. 16 Isra’ilawa za su kiyaye Asabbaci, suna bikinsa daga tsara zuwa tsara a matsayin madawwamin alkawari. 17 Zai zama alama tsakanina da Isra’ilawa har abada, gama cikin kwana shida Ubangiji ya yi sama da ƙasa, a rana ta bakwai kuma ya daina aiki, ya kuma huta.’ ”

  11. 14 Ubangiji ya amsa ya ce, “Zan tafi tare da kai, zan kuma rage maka nauyin kaya.”

  12. 9 Ya sa yaƙoƙi suka yi tsit

    ko’ina a duniya.

    Ya kakkarya bakkuna ya kuma ragargaza māsu,

    ya ƙone garkuwoyi da wuta.

    10 “Ku natsu ku kuma san cewa ni ne Allah;

    za a ɗaukaka ni a cikin al’ummai,

    za a ɗaukaka ni cikin duniya.”

    11 Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu;

    Allah na Yaƙub ne kagararmu. Sela

  13. 3 Ka dogara ga Ubangiji ka kuma aikata alheri;

    yi zama cikin ƙasar ka kuma more makiyaya mai lafiya.

    4 Ka ji daɗinka a cikin Ubangiji

    zai kuwa biya bukatun zuciyarka.

    5 Ka sa kanka a hanyar Ubangiji;

    ka kuma dogara gare shi zai kuwa yi wannan.

    6 Zai sa adalcinka yă haskaka kamar hasken safiya,

    gaskiyarka kuma kamar rana a tsaka.

    7 Ka natsu a gaban Ubangiji

    ka kuma jira da haƙuri gare shi;

    kada ka tsorata sa’ad da mutane ke nasara a hanyoyinsu,

    sa’ad da suke aikata mugayen shirye-shiryensu.

    8 Kada ka yi fushi kada kuma ka yi hasala;

    kada ka tsorata, wannan yakan kai ga mugunta ne kawai.

  14. 6 Ku tafi wurin kyashi, ku ragwaye;

    ku lura da hanyoyinsa ku zama masu hikima!

    7 Ba shi da jagora

    ba shugaba ko mai mulki,

    8 duk da haka yakan yi tanade-tanadensa da rani

    ya kuma tattara abincinsa a lokacin girbi.

    9 Har yaushe za ku kwanta a can, ku ragwaye?

    Yaushe za ku farka daga barcinku?

    10 Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi,

    ɗan naɗin hannuwa don a huta,

    11 talauci kuwa zai zo kamar ’yan hari

    rashi kuma kamar ɗan fashi.

  15. 12 “Kwana shida za ku yi aikinku, amma a rana ta bakwai, kada ku yi aiki, saboda saniyarku da jakinku su huta, haka kuma bawan da aka haifa a gidanku, da kuma baƙon da yake a cikinku yă wartsake.

  16. 7 gama shi ne Allahnmu

    mu mutanen makiyayansa ne,

    garke kuwa a ƙarƙashin kulawarsa.

    Yau, in kuka ji muryarsa,

    8 “Kada ku taurare zukatanku kamar yadda kuka yi a Meriba,

    kamar yadda kuka yi a wancan rana a Massa a hamada,

    9 inda kakanninku suka gwada suka kuma jarraba ni,

    ko da yake sun ga abin da na yi.

    10 Shekara arba’in na yi fushi da wancan tsara;

    na ce, ‘Su mutane ne waɗanda zukatansu suka kauce,

    kuma ba su san hanyoyina ba.’

    11 Saboda haka na yi rantsuwa cikin fushina,

    ‘Ba za su taɓa shiga hutuna ba.’ ”

  17. 1 Ubangiji ya yi magana da Musa a kan Dutsen Sinai ya ce, 2 “Yi wa Isra’ilawa magana, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka shiga ƙasar da zan ba ku, dole ƙasar kanta ta kiyaye Asabbaci ga Ubangiji. 3 Shekara shida, za ku yi shuki, shekara shida kuma za ku aske gonakin inabinku, ku kuma tattara hatsinsu. 4 Amma a shekara ta bakwai, ƙasar za tă sami hutun Asabbaci, Asabbaci ga Ubangiji. Kada ku yi shuki a gonakinku, ko kuwa ku aske gonakinku na inabi.

  18. 12 Ka kiyaye ranar Asabbaci ta wurin kiyaye ta da tsarki, yadda Ubangiji Allahnka ya umarce ka. 13 Kwanaki shida za ka yi aiki, ka kuma yi dukan aikinka, 14 amma rana ta bakwai, Asabbaci ne ga Ubangiji Allahnka. A kanta ba za ka yi wani aiki ba, ko kai, ko ɗanka, ko ’yarka, ko bawanka, ko baiwarka, ko saniyarka, ko jakinka, ko wani daga dabbobinka, ko baƙo a ƙofofinka, don bayinka maza da mata su ma su huta, kamar ka. 15 Ka tuna fa, dā kai bawa ne a ƙasar Masar amma Ubangiji Allahnka ya fitar da kai daga can da iko da kuma ƙarfi. Saboda haka Ubangiji Allahnka ya umarce ka ka kiyaye ranar Asabbaci.

  19. 8 Zan kwanta in kuma yi barci lafiya,

    gama kai kaɗai, ya Ubangiji,

    kake sa mazaunina yă kasance lafiya lau.

  20. 1 Shi wanda yake zama a wurin Mafi Ɗaukaka

    zai huta a cikin inuwar Maɗaukaki.

    2 Zan ce game da Ubangiji, “Shi ne mafakata da kagarata,

    Allahna, wanda nake dogara.”

  21. 5 Ubangiji mai alheri ne da kuma mai adalci;

    Allahnmu yana cike da tausayi.

    6 Ubangiji yana tsare masu tawali’u;

    sa’ad da nake cikin tsananin bukata, ya cece ni.

    7 Ka kwantar da hankali, ya raina,

    gama Ubangiji mai alheri ne a gare ka.

    8 Gama kai, ya Ubangiji, ka ceci raina daga mutuwa,

    idanuna daga hawaye,

    ƙafafuna daga tuntuɓe,

  22. 13 Rago yakan ce, “Akwai zaki a kan hanya,

    zaki mai faɗa yana yawo a tituna!”

    14 Kamar yadda ƙofa kan juya a ƙyaurensa,

    haka rago yake jujjuya a gadonsa.

    15 Rago kan sa hannunsa a kwano

    ba ya ma iya ɗaga shi ya kai bakinsa.

    16 Rago yana gani yana da hikima

    fiye da mutane bakwai da suke ba da amsa da dalilai a kan ra’ayinsu.

  23. 3 A ranar da Ubangiji ya hutashe ku daga wahala da azaba da muguwar bauta, 4 za ku yi wa sarkin Babilon wannan ba’a.

    Mai danniya ya zo ga ƙarshe!

    Dubi yadda fushinsa ya ƙare!

  24. 28 Ba ku sani ba?

    Ba ku ji ba?

    Ubangiji madawwamin Allah ne,

    Mahaliccin iyakokin duniya.

    Ba zai taɓa gaji ko yă kasala ba,

    kuma fahimtarsa ya wuce gaban ganewar mutum.

    29 Yakan ba da ƙarfi ga waɗanda suka gaji

    yă kuma ƙara ƙarfi ga marasa ƙarfi.

    30 Ko matasa ma kan gaji su kuma kasala,

    samari kuma kan yi tuntuɓe su fāɗi;

    31 amma waɗanda suka dogara ga Ubangiji

    za su sabunta ƙarfinsu.

    Za su yi firiya da fikafikai kamar gaggafa;

    za su kuma yi gudu ba kuwa za su gaji ba,

    za su yi tafiya ba kuwa za su kasala ba.

  25. 21 “Kwana shida za ku yi aiki, amma a rana ta bakwai za ku huta; ko da lokacin noma ne, ko lokacin girbi, sai ku huta.

  26. 22 Me mutum zai samu daga aikin da ya yi duka, da irin ɗawainiyar da ya sha a kan yin aikin a duniya? 23 Dukan kwanakinsa aikinsa damuwa ce da ɓacin zuciya; ko da dare ma hankalinsa ba a kwance yake ba. Wannan ma ba shi da amfani.

    24 Ba abin da mutum zai yi da ya fi yă ci, yă sha, yă ji wa ransa daɗi daga aikinsa. Na lura cewa wannan ma, ya fito daga hannun Allah ne, 25 gama in ba tare da shi ba, wa zai iya ci yă sha yă kuma ji daɗi?

  27. 24 Ba zato ba tsammani, sai wani babban hadari ya taso a tafkin, har raƙuman ruwan suka sha kan jirgin. Amma Yesu yana barci. 25 Almajiran suka je suka tashe shi, suna cewa, “Ubangiji, ka cece mu! Za mu nutse!”

  28. 23 Wata ranar Asabbaci, Yesu yana ratsa gonakin hatsi, sai almajiransa da suke tafiya tare da shi, suka fara kakkarya waɗansu kan hatsi. 24 Farisiyawa suka ce masa, “Duba, me ya sa suke yin abin da doka ta hana a yi, a ranar Asabbaci?”

    25 Ya amsa ya ce, “Ashe, ba ku taɓa karanta abin da Dawuda ya yi ba, sa’ad da shi da abokan tafiyarsa suka ji yunwa, suna kuma cikin bukata? 26 Ya shiga gidan Allah a zamanin Abiyatar babban firist, ya ci keɓaɓɓen burodin nan, ya kuma ba wa abokan tafiyarsa abin da firistoci kaɗai sukan ci bisa ga doka?”

    27 Sai ya ce musu, “An yi Asabbaci saboda mutum ne, ba mutum saboda Asabbaci ba. 28 Don haka, Ɗan Mutum Ubangiji ne, har ma da na Asabbaci.”

  29. 30 Na wuce cikin gonar rago,

    na wuce cikin gonar inabin mutumin da ba shi da azanci;

    31 ƙayayyuwa sun yi girma ko’ina,

    ciyayi sun rufe ƙasar,

    katangar duwatsu duk ta rushe.

    32 Na yi tunani a zuciyata

    na kuwa koyi darasi daga abin da na gani.

    33 Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi,

    ɗan naɗin hannuwa don a huta,

    34 sai talauci ya shigo maka kamar ’yan fashi

    rashi kuma ya zo maka kamar mai hari.

  30. 22 “Babu salama ga mugaye” in ji Ubangiji.

  31. 10 Suka yi kira da babbar murya suka ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, Mai Tsarki da kuma Mai Gaskiya, sai yaushe za ka shari’anta mazaunan duniya ka kuma ɗauki mana fansar jininmu?” 11 Sai aka ba wa kowannensu farin riga, aka kuma faɗa musu su ɗan jira kaɗan sai an cika adadin abokansu masu hidima da kuma ’yan’uwansu waɗanda za a kashe kamar yadda su ma aka kashe su.

  32. 11 Hayaƙin azabarsu kuwa zai dinga tashi har abada abadin. Kuma babu hutu dare ko rana wa waɗanda suke wa dabbar da siffarta sujada, ko kuwa ga duk wanda ya sami alamar sunanta.”

  33. 5 Gama sa’ad da muka zo Makidoniya, jikin nan namu bai sami hutu ba, sai ma aka matsa mana a ta kowane gefe, a waje ga rikici, a zukatanmu kuma ga tsoro. 6 Amma Allah, wanda yakan yi wa masu ɓacin rai ta’aziyya ya yi mana ta’aziyya da zuwan Titus, 7 ba ma don zuwansa kaɗai ba, har ma a game da ƙarfafa zuciyan nan da ya samu a wurinku. Ya gaya mana yadda kuke so ku gan ni sosai, da kuma yadda kuka yi baƙin ciki game da abin da ya faru, da niyyar da kuka yi na goyon bayana. Wannan ne ya sa na ji daɗi ƙwarai.

  34. 8 ka tashi, ya Ubangiji, ka kuma zo wurin hutunka,

    kai da akwatin alkawarin ƙarfinka.

  35. 15 Ragwanci kan jawo zurfin barci,

    mutum mai sanyin jiki kuma yana tare da yunwa.

  36. 17 Aikin adalci zai zama salama;

    tasirin adalci zai zama natsuwa da tabbaci har abada.

    18 Mutanena za su zauna lafiya a wuraren salama,

    a gidaje masu kāriya,

    a wuraren hutun da babu fitina.

  37. 25 Zan wartsake waɗanda suka gaji in kuma ƙosar da waɗanda ransu ya yi yaushi.”

  38. 4 To, ya zama dole yă bi ta Samariya. 5 Sai ya zo wani gari a Samariya da ake ce da shi Saikar, kurkusa da filin da Yaƙub ya ba wa ɗansa Yusuf. 6 Rijiyar Yaƙub kuwa tana can, Yesu kuwa, saboda gajiyar tafiya, sai ya zauna a bakin rijiyar. Wajen sa’a ta shida ne.

  39. 27 Salama na bari tare da ku; salamata nake ba ku. Ba kamar yadda duniya take bayarwa nake ba ku ba. Kada zuciyarku ta ɓaci kada kuma ku ji tsoro.

  40. 9 Amma ya ce mini, “Alherina ya ishe ka, domin a cikin rashin ƙarfi ne ake ganin cikar ikona.” Saboda haka, zan ƙara yin taƙama da farin ciki game da rashin ƙarfina, domin ikon Yesu Kiristi yă zauna tare da ni.

  41. 1 Sa’an nan na ga sabon sama da sabuwar duniya, gama sama na farko da duniya ta farko sun shuɗe, babu kuma wani teku. 2 Na ga Birni Mai Tsarki, sabuwar Urushalima tana saukowa daga sama, daga Allah, a shirye kamar amaryar da aka yi mata ado mai kyau saboda mijinta. 3 Na kuma ji wata babbar murya daga kursiyin tana cewa, “Yanzu mazaunin Allah yana tare da mutane, zai kuma zauna tare da su. Za su zama mutanensa, Allah kansa kuwa zai kasance tare da su yă kuma zama Allahnsu. 4 Zai share dukan hawaye daga idanunsu. Ba sauran mutuwa ko makoki ko kuka ko azaba, gama tsofaffin al’amura sun shuɗe.”

    5 Wannan da yake zaune a kursiyin ya ce. “Ina yin kome sabo!” Sai ya ce, “Rubuta wannan, domin waɗannan kalmomi amintattu ne gaskiya ne kuma.”

  42. 9 Gama ba ku kai wurin hutawa wanda Ubangiji Allahnku zai ba ku gādo ba tukuna.

  43. 21 Ɗana, ka riƙe sahihiyar shari’a da kuma basira,

    kada ka bar su su rabu da kai;

    22 za su zama rai a gare ka,

    abin adon da zai gyara wuyanka.

    23 Sa’an nan za ka bi hanyarka lafiya,

    ƙafarka kuwa ba zai yi tuntuɓe ba;

    24 sa’ad da ka kwanta, ba za ka ji tsoro ba;

    sa’ad da ka kwanta, barci zai yi maka daɗi.

  44. 24 Hannuwan masu aiki tuƙuru za su yi mulki,

    amma ragwanci kan ƙarasa a aikin bauta.

  45. 4 Rago ya ƙosa ya sami wani abu ainun amma ba ya samun kome,

    amma sha’awar mai aiki tuƙuru yakan ƙoshi sosai.

  46. 4 Rago ba ya noma a lokacin noma;

    saboda haka a lokacin girbi ba ya bukata samun kome.

  47. 12 Barcin ma’aikaci daɗi gare shi,

    ko yă ci kaɗan ko da yawa,

    amma yalwar mai arziki

    ba ta barinsa yă iya yin barci.

  48. 18 In mutum rago ne, sai tsaiko yă lotsa,

    in hannuwansa ba masa yin kome, ɗaki yakan yi yoyo.

  49. 11 Muna so kowannenku yă nuna ƙwazon nan har zuwa ƙarshe, domin ku tabbatar da begenku. 12 Ba ma so ku zama masu ƙyuya, sai dai ku yi koyi da waɗanda ta wurin bangaskiya da haƙuri suka gāji abin da aka yi alkawari.

  50. 38 Yayinda Yesu da almajiransa suna cikin tafiya, sai ya kai wani ƙauye inda wata mace mai suna Marta ta marabce shi a gidanta. 39 Tana da ’yar’uwa mai suna Maryamu, wadda ta zauna a gaban Ubangiji tana jin maganarsa. 40 Marta kuwa, aikin hidima da ya kamata a yi, ya ɗauke mata hankali, sai ta zo wurin Yesu, ta ce, “Ubangiji, ba ka damu da yadda ’yar’uwata ta bar mini aiki ni kaɗai ba? Gaya mata ta taimake ni!”

    41 Amma Ubangiji ya amsa ya ce, “Marta, Marta, hankalinki ya tashi, kuma kina damuwa a kan abubuwa da yawa. 42 Amma abu ɗaya tak ake bukata, Maryamu ta zaɓi abin da ya fi kyau, kuma ba za a raba ta da shi ba.”

  51. 18 Kuma ga su wane ne Allah ya rantse cewa ba za su taɓa shiga hutunsa ba, in ba ga marasa biyayyan nan ba? 19 Saboda haka mun ga cewa ba su iya shiga ba, saboda rashin bangaskiyarsu ne.