38 Bible Verses About Safe Travels
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
Waƙar haurawa.
1 Na tā da idanuna zuwa wajen tuddai,
ta ina ne taimakona zai zo?
2 Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji,
wanda ya kafa sama da ƙasa.
3 Ba zai bari ƙafarka tă yi santsi ba,
shi da yake tsaronka ba zai yi gyangyaɗi ba;
4 tabbatacce, shi da yake tsaron Isra’ila
ba ya gyangyaɗi ko barci.
5 Ubangiji yana tsaronka,
Ubangiji ne inuwa a hannun damanka;
6 rana ba za tă buge ka cikin yini ba
balle wata da dare.
7 Ubangiji zai kiyaye ka daga dukan masifa,
zai tsare ranka;
8 Ubangiji zai kiyaye shigarka da fitarka
yanzu da har abada kuma.
-
2 Zan ce game da Ubangiji, “Shi ne mafakata da kagarata,
Allahna, wanda nake dogara.”
3 Tabbatacce zai cece ka
daga tarkon mai farauta
da kuma daga cututtuka masu kisa.
4 Zai rufe ka da fikafikansa,
a ƙarƙashin fikafikansa kuwa za ka sami mafaka;
amincinsa zai zama maka garkuwa da katanga.
5 Ba za ka ji tsoron razanar dare,
ko kibiyoyi da suke firiya da rana ba,
6 ko bala’in da yake aukowa cikin duhu,
ko annobar da take hallakarwa da tsakar rana.
7 Dubu za su iya fāɗuwa a gefenka,
dubu goma a hannun damanka,
amma ba abin da zai zo kusa da kai.
-
21 Ɗana, ka riƙe sahihiyar shari’a da kuma basira,
kada ka bar su su rabu da kai;
22 za su zama rai a gare ka,
abin adon da zai gyara wuyanka.
23 Sa’an nan za ka bi hanyarka lafiya,
ƙafarka kuwa ba zai yi tuntuɓe ba;
24 sa’ad da ka kwanta, ba za ka ji tsoro ba;
sa’ad da ka kwanta, barci zai yi maka daɗi.
-
9 In ka mai da Mafi Ɗaukaka wurin zamanka,
har ma Ubangiji wanda yake mafakata,
10 to, babu wani mugun abin da zai same ka,
ba masifar da za tă zo kusa da tentinka.
11 Gama zai umarci mala’ikunsa game da kai
don su tsare ka a dukan hanyoyinka;
12 za su tallafe ka da hannuwansu,
don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.
-
6 Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya. 7 Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za tă tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.
8 A ƙarshe, ’yan’uwa, duk abin da yake na gaskiya, duk abin da yake na girmamawa, duk abin da yake daidai, duk abin da yake da tsarki, duk abin da yake kyakkyawa, duk abin da yake na sha’awa, in ma wani abu mafifici ne, ko ya cancanci yabo, ku yi tunani a kan irin abubuwan nan. 9 Duk abin da kuka koya ko kuka karɓa ko kuka ji daga wurina, ko kuka gani a cikina, ku yi aiki da shi. Allah na salama kuma zai kasance tare da ku.
-
8 Ubangiji kansa yana tafe a gabanka, zai kuma kasance tare da kai, ba zai taɓa barinka ko yă yashe ka ba. Kada ka ji tsoro; kada kuma ka karai.”
-
1 To, fa, ga abin da Ubangiji yana cewa,
shi da ya halicce ka, ya Yaƙub,
shi da ya siffanta ka, ya Isra’ila,
“Kada ka ji tsoro, gama na fanshe ka;
na kira ka da suna; kai nawa ne.
2 Sa’ad da kuka bi ta ruwaye,
zan kasance tare da ku;
sa’ad da kuka bi ta koguna,
ba za su kwashe ku ba.
Sa’ad da kuke tafiyata cikin wuta,
ba za tă ƙone ku ba;
harsunan wutar ba za su ƙone ku ba.
3 Gama ni ne Ubangiji, Allahnku,
Mai Tsarkin nan na Isra’ila, Mai Cetonku;
na bayar da Masar don fansa,
Kush da Seba a maimakonku.
4 Da yake ku masu daraja da kuma girma ne a idona,
saboda kuma ina ƙaunarku,
zan ba da mutane a maimakonku,
al’umma kuma domin ranku.
5 Kada ku ji tsoro, gama ina tare da ku;
zan kawo yaranku daga gabas
in kuma tattara ku daga yamma.
6 Zan ce wa arewa, ‘Ku miƙa su!’
Ga kudu kuma, ‘Kada ku riƙe su.’
Kawo ’ya’yana maza daga nesa
’ya’yana mata kuma daga iyakar duniya,
7 kowa da ake kira da sunana,
wanda aka halitta saboda ɗaukakata,
wanda na siffanta na kuma yi.”
-
7 Ina zan tafi daga Ruhunka?
Ina zan gudu in tafi daga gabanka?
8 In na haura zuwa sammai, kana a can;
in na yi gado a zurfafa, kana a can.
9 In na tashi a fikafikan safiya,
in na sauka a gefe mai nisa na teku,
10 can ma hannunka zai bishe ni,
hannunka na dama zai riƙe ni gam.
-
9 ’Yan Adam sukan yi shirye-shiryensu a zukatansu,
amma Ubangiji ne yake da ikon cika matakansa.
-
7 Kai ne wurin ɓuyata;
za ka tsare ni daga wahala
ka kewaye ni da waƙoƙin ceto. Sela
8 Zan umarce ka in kuma koyar da kai a hanyar da za ka bi;
Zan ba ka shawara in kuma lura da kai.
-
23 In Ubangiji ya ji daɗin hanyar da mutum yake bi,
zai sa sawu su kahu;
24 ko ya yi tuntuɓe, ba zai fāɗi ba,
gama Ubangiji yakan riƙe shi da hannunsa.
-
Zabura ta Dawuda.
1 Ubangiji ne yake kiwona, ba zan rasa kome ba,
2 Yakan sa in kwanta a makiyaya mai ɗanyar ciyawa,
yakan bi da ni kusa da ruwaye marar hayaniya,
3 yakan maido da raina.
Yakan bi da ni a hanyoyin adalci
saboda sunansa.
4 Ko da na yi tafiya
ta kwari na inuwar mutuwa,
ba zan ji tsoron mugu ba,
gama kana tare da ni;
bulalarka na dūka da kuma sandanka na tafiya,
za su yi mini ta’aziyya.
5 Ka shirya mini tebur
a gaban abokan gābana.
Ka shafe kaina da mai;
kwaf nawa ya cika har yana zuba.
6 Tabbatacce alheri da ƙauna za su bi
dukan kwanakin raina,
zan kuwa zauna a gidan Ubangiji
har abada.
-
28 Mun kuma san cewa a cikin dukan abubuwa Allah yana aikata alheri ga waɗanda suke ƙaunarsa, yana waɗanda aka kira bisa ga nufinsa.
-
7 Mala’ikan Ubangiji ya kafa sansani kewaye da waɗanda suke tsoronsa,
ya kuwa cece su.
-
3 Za ka kiyaye shi da cikakken salama
shi wanda ya kafa zuciyarsa gare ka,
domin ya dogara a gare ka.
4 Ku dogara ga Ubangiji,
gama shi Ubangiji, ne madawwamin Dutse.
-
1 Ga abin da yake cikin wasiƙar annabi Irmiya da ya aika daga Urushalima zuwa ga sauran dattawan da suka ragu a cikin masu zaman bauta da kuma zuwa ga firistoci, annabawa da kuma dukan sauran mutanen da Nebukadnezzar ya kwashe zuwa zaman bauta daga Urushalima zuwa Babilon. 2 (Wannan ya faru bayan Sarki Yekoniya da mahaifiyar sarauniya, shugabannin fada da kuma dukan shugabannin Yahuda da Urushalima, gwanayen sana’a da masu sassaƙa suka tafi zaman bauta daga Urushalima.) 3 Ya ba da wasiƙar ta hannun Eleyasa ɗan Shafan da Gemariya ɗan Hilkiya, waɗanda Zedekiya sarkin Yahuda ya aika wurin Sarki Nebukadnezzar a Babilon. Wasiƙar ta ce,
4 Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ga dukan waɗanda aka kwashe zuwa zaman bauta daga Urushalima zuwa Babilon. 5 “Ku gina gidaje ku zauna; ku dasa gonaki ku kuma ci abin da suka haifar. 6 Ku yi aure ku kuma haifi ’ya’ya maza da mata; ku nemi mata wa ’ya’yanku maza, ku kuma ba da ’ya’yanku mata ga aure, saboda su ma za su haifi ’ya’ya maza da mata. Ku riɓaɓɓanya a can, kada ku ragu. 7 Haka kuma, ku nemi zaman salama da cin gaba a birnin da aka kai ku zaman bauta. Ku yi addu’a ga Ubangiji saboda birnin, domin in ya ci gaba, ku ma za ku ci gaba.” 8 I, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa, “Kada ku bar annabawa da masu sihiri a cikinku su ruɗe ku. Kada ku saurari mafarkan da dā kuke ƙarfafa su su yi. 9 Suna muku annabcin ƙarya da sunana. Ban aike su ba,” in ji Ubangiji.
10 Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Sa’ad da shekaru saba’in suka cika a Babilon, zan zo muku in cika alkawarin alherina don in komo da ku zuwa wannan wuri. 11 Gama na san shirye-shiryen da na yi muku,” in ji Ubangiji, “shirye-shiryen cin gaba ba na cutarwa ba, shirye-shiryen ba ku sa zuciya da kuma na nan gaba. 12 Sa’an nan za ku kira gare ni ku zo ku kuma yi addu’a gare ni, zan kuwa ji ku. 13 Za ku neme ni ku kuwa same ni sa’ad da kuka neme ni da dukan zuciyarku. 14 Za ku same ni,” in ji Ubangiji, “zan kuma komo da ku daga bauta. Zan tattaro ku daga dukan al’ummai in sa ku inda na kore ku,” in ji Ubangiji, “zan kuma komo da ku zuwa wurin da na kwashe ku zuwa zaman bauta.”
15 Za ku iya ce, “Ubangiji ya tā da annabawa saboda mu a Babilon.”
-
15 Ya ce, musu, “Ku tafi cikin dukan duniya, ku yi wa’azin bishara ga dukan halitta. 16 Duk wanda ya gaskata, aka kuma yi masa baftisma, zai sami ceto. Amma duk wanda bai gaskata ba kuwa, zai hallaka.
-
6 Za ku zama masu albarka sa’ad da kuka shiga, za ku kuma zama masu albarka sa’ad da kuka fita.
-
14 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Yanzu ranar mutuwarka ta yi kusa. Ka kira Yoshuwa, ku shigo Tentin Sujada, inda zan ba shi ragamar aiki.” Saboda haka Musa da Yoshuwa suka zo, suka kuma shiga Tentin Sujada.
15 Ubangiji kuwa ya bayyana a Tentin Sujada a cikin ginshiƙin girgije, sai girgijen ya tsaya a ƙofar Tentin Sujada. 16 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Za ka huta tare da kakanninka, waɗannan mutane kuwa ba da daɗewa ba za su yi karuwanci ga baƙin alloli na ƙasar da za su shiga. Za su yashe ni su kuma karya alkawarin da na yi da su. 17 A wannan rana zan yi fushi da su, in kuma yashe su; zan ɓoye fuskata daga gare su, za a kuwa hallaka su. Masifu masu yawa da wahaloli masu yawa za su auka musu, a wannan rana kuwa za su ce, ‘Masifun nan sun same mu domin Allahnmu ba ya tare da mu’ 18 Tabbatacce kuwa, zan ɓoye musu fuskata saboda muguntar da suka aikata, suka kuma bi gumaka.
19 “To, sai ka rubuta wannan waƙa domin kanka, ka koya wa Isra’ilawa, ka kuma sa su rera ta, don tă zama shaida a kansu. 20 Sa’ad da na kawo su cikin ƙasa mai zub da madara da zuma, ƙasar da na yi alkawari da rantsuwa ga kakanninsu, sa’ad da kuma suka ci suka ƙoshi, suka kuma yi ƙiba, za su juya ga waɗansu alloli su bauta musu, su ƙi ni, su kuma karya alkawarina. 21 Sa’ad da kuma masifu masu yawa da wahaloli masu yawa suka auko musu, wannan waƙa za tă zama shaida a kansu, domin zuriyarsu ba za tă manta da ita ba. Na san abin da za su iya yi, kafin ma in kawo su cikin ƙasar da na yi musu alkawari da rantsuwa.” 22 Sai Musa ya rubuta wannan waƙa a wannan rana, ya kuma koya wa Isra’ilawa.
23 Ubangiji ya ba wa Yoshuwa ɗan Nun wannan umarni, “Ka ƙarfafa, ka kuma yi ƙarfin hali, gama za ka kawo Isra’ilawa cikin ƙasar da na yi musu alkawari da rantsuwa, ni kaina kuwa zan kasance tare da kai.”
-
8 Ubangiji mai alheri da kuma tausayi,
mai jinkirin fushi cike kuma da ƙauna.
9 Ubangiji nagari ne ga duka;
yana tausayin dukan abubuwan da ya yi.
-
5 Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka
kada kuma ka dangana ga ganewarka;
6 cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi,
zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.
-
25 Kada ka ji tsoron masifar da za tă faru farat ɗaya
ko lalacin da yakan auka wa mugaye,
26 gama Ubangiji zai zama ƙarfin halinka
zai kuwa kiyaye ƙafarka daga fāɗawa a tarko.
-
19 Saboda haka ku tafi, ku mai da dukan al’umman duniya su zama almajiraina, kuna yi musu baftisma a cikin sunan Uba, da na Ɗa, da na Ruhu Mai Tsarki, 20 kuna kuma koya musu, su yi biyayya da duk abin da na umarce ku, kuma tabbatacce, ina tare da ku kullum, har ƙarshen zamani.”
-
5 Waɗansu daga cikin almajiransa, suka fara magana a kan yadda aka yi wa haikalin ado da duwatsu masu kyau, da kuma kyautai da aka keɓe wa Allah. Amma Yesu ya ce, 6 “Wannan abin da kuke kallo a nan, lokaci yana zuwa da ba za a bar wani dutse a kan wani dutse ba. Kowannensu, za a rushe shi.”
7 Suka tambaye shi suka ce, “Malam, yaushe waɗannan za su faru? Kuma wace alama za tă nuna cewa suna dab da faruwa?”
8 Ya amsa ya ce, “Ku lura, kada ku kuma a ruɗe ku. Gama da yawa za su zo a cikin sunana, suna cewa, ‘Ai, ni ne shi,’ da kuma, ‘Lokaci ya yi kusa.’ Kada ku bi su. 9 Sa’ad da kuka ji labarin yaƙe-yaƙe, da juye juyen mulki, kada ku tsorota. Dole ne waɗannan abubuwa su fara faruwa, amma ƙarshen ba zai zo nan da nan ba.”
10 Sai ya ce musu, “Al’umma za tă tasar wa al’umma, mulki zai tasar wa mulki. 11 Za a yi manyan girgizar ƙasa, da yunwa, da annoba a wurare dabam-dabam, da kuma abubuwa masu bantsoro, da manyan alamu daga sama.
12 “Amma kafin duk abubuwa nan, za a kama ku a tsananta muku. Za a kai ku majami’u, da kurkuku. Za a kuma kai ku gaban sarakuna da gwamnoni, kuma dukan waɗannan saboda sunana. 13 Wannan zai sa ku zama shaidu a gare su. 14 Amma ku yi ƙuduri, wato, ku shirya zuciyarku, a kan ba za ku damu ba kafin lokacin, game da yadda za ku kāre kanku. 15 Gama zan ba ku kalmomi, da hikima waɗanda ba ko ɗaya daga cikin maƙiyanku, za su iya tsayayya da ku, ko su ƙaryata. 16 Har iyayenku, da ’yan’uwanku maza, da danginku, da abokanku ma, duk za su bashe ku, su kuma kashe waɗansunku. 17 Duk mutane za su ƙi ku saboda ni. 18 Amma ko gashi ɗaya na kanku, ba zai hallaka ba. 19 Ta wurin tsayawa da ƙarfi, za ku sami rai.
20 “In kuka ga mayaƙa sun kewaye Urushalima, za ku sani rushewarta ya yi kusa. 21 A lokacin nan, bari waɗanda suke Yahudiya, su gudu zuwa cikin duwatsu. Bari waɗanda suke cikin birnin kuma su fita, bari kuma waɗanda suke ƙauye kada su shiga birnin. 22 Gama wannan shi ne lokacin hukunci, saboda a cika duk abin da aka rubuta. 23 Zai zama abin kaito ga mata masu ciki, da mata masu renon ’ya’ya, a waɗancan kwanakin! Za a yi baƙin ciki mai tsanani a ƙasar, da kuma fushi mai tsanani a kan mutanen nan. 24 Za a kashe su da takobi, a kuma ɗauke su ’yan kurkuku, zuwa dukan al’ummai. Al’ummai za su tattaka Urushalima, har sai lokacin Al’ummai ya cika.
-
13 Amma dole kullum mu gode wa Allah dominku, ’yan’uwa waɗanda Ubangiji ya ƙaunace, domin daga farko Allah ya zaɓe ku don a cece ku ta wurin aikin tsarkakewar Ruhu da kuma ta wurin gaskatawa da gaskiya. 14 Ya kira ku ga wannan ta wurin bishararmu, don ku sami rabo a cikin ɗaukakar Ubangijinmu Yesu Kiristi.
15 Saboda haka fa, ’yan’uwa, sai ku tsaya daram ku riƙe koyarwar da muka miƙa muku, ko ta wurin maganar baki ko kuma ta wurin wasiƙa.
16 Ubangijinmu Yesu Kiristi kansa da kuma Allah Ubanmu, wanda ya ƙaunace mu kuma ta wurin alherinsa yă ba mu madawwamiyar ƙarfafawa da kyakkyawar bege, 17 yă ƙarfafa zukatanku yă kuma gina ku cikin kowane aikin nagari da kuma magana.
-
17 Sa’ad da Fir’auna ya bar mutane su tafi, Allah bai bi da su a hanyar da ta bi ta iyakar Filistiyawa ba, ko da yake wannan hanya ce ta fi kusa. Gama Allah ya ce, “In suka fuskanci yaƙi, wataƙila su canja ra’ayinsu su koma Masar.” 18 Saboda haka Allah ya kewaye da mutanen ta hamada zuwa Jan Teku. Isra’ilawa kuwa suka fita daga Masar da shirin yaƙi.
19 Musa ya ɗauki ƙasusuwan Yusuf tare da shi, gama Yusuf ya sa Isra’ilawa su rantse masa. Ya ce, “Tabbatacce Allah zai taimake ku, sai ku ɗibi ƙasusuwana tare da ku daga wannan wuri.”
20 Bayan sun bar Sukkot sai suka kafa sansani a Etam a bakin hamada. 21 Da rana Ubangiji yakan ja gabansu a cikin al’amudin girgije domin yă bishe su a kan hanyarsu, da dare kuma a cikin al’amudin wuta domin yă ba su haske, domin su iya tafiya dare da rana. 22 Al’amudan nan biyu, na girgije da na wuta, ba su daina yi wa jama’a jagora ba.
-
3 Allahna shi ne dutsena. A gare shi nake samun kāriya
shi ne garkuwata da kuma ƙahon cetona.
Shi ne mafakata, maɓuyata, da mai cetona.
Daga mutane masu fitina, ka cece ni.
-
11 Amma bari dukan waɗanda suke neman mafaka gare ka su yi murna;
bari kullum su yi ta rerawa saboda farin ciki.
Ka buɗe kāriyarka a bisansu,
domin waɗanda suke ƙaunar sunanka su yi farin ciki a cikinka.
12 Gama tabbatacce, ya Ubangiji, kakan albarkaci adalai;
kakan kewaye su da tagomashinka kamar garkuwa.
-
36 Ka fadada hanyar da yake a ƙarƙashina,
don kada ɗiɗɗigena yă juya.
-
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta ’Ya’yan Kora maza. Bisa ga alamot Waƙa ce.
1 Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu,
kullum yana a shirye yă taimaka a lokacin wahala.
-
6 Ubangiji yana tare da ni; ba zan ji tsoro ba.
Me mutum zai yi mini?
-
1 Ɗana, in ka yarda da kalmomina
ka kuma ajiye umarnaina a cikinka,
2 kana kasa kunne ga abin da yake na hikima,
kana kuma yin ƙoƙari ka fahimce shi,
3 in kuma ka kira ga tsinkaya
ka kuma kira da ƙarfi don ganewa,
4 in ka neme shi yadda ake neman azurfa
ka kuma neme shi kamar yadda ake neman ɓoyayyiyar dukiya,
5 to, za ka gane tsoron Ubangiji
ka kuma sami sanin Allah.
6 Gama Ubangiji yana ba da hikima,
daga bakinsa kuma, sani da ganewa sukan fito.
7 Yana riƙe da nasara a ma’aji don masu yin gaskiya,
shi ne mafaka ga waɗanda tafiyarsu ba ta da laifi,
8 gama yana tsare abin da masu adalci suke bukata
yana kuma tsare hanyar amintattunsa.
9 Sa’an nan za ku fahimci abin da yake daidai da abin da yake na adalci
da abin da yake gaskiya, da kowace hanya mai kyau.
10 Gama hikima za tă shiga cikin zuciyarka,
sani kuma zai faranta maka rai.
11 Tsinkaya za tă tsare ka,
ganewa kuma za tă yi maka jagora.
12 Hikima za tă cece ka daga hanyoyin mugayen mutane,
daga kalmomin mutane masu ɓatanci,
13 waɗanda suke barin miƙaƙƙun hanyoyi
don su yi tafiya a hanyoyi masu duhu,
14 waɗanda suke jin daɗin yin abin da ba shi da kyau
suna kuma farin ciki a mugayen ɓatanci,
15 waɗanda hanyoyinsu karkatattu ne
waɗanda kuma suke cuku-cuku a hanyoyinsu.
16 Zai kiyaye ku kuma daga mazinaciya,
daga mace mai lalata, mai ƙoƙarin kama ka da daɗin bakinta,
17 wadda ta bar mijin ƙuruciyarta
ta kuma ƙyale alkawarin da ta yi a gaban Allah.
18 Gama gidanta yana kai ga mutuwa
hanyarta kuma ga ruhohin matattu.
19 Duk wanda ya ziyarce ta ba ya ƙara komowa
ba zai ƙara komowa ga hanyar rai.
20 Don haka dole ku yi tafiya a hanyoyin mutanen kirki
ku kuma yi ta bi hanyoyin adalai.
21 Gama masu aikata gaskiya za su zauna a cikin ƙasar,
marasa laifi kuma za su kasance a cikinta;
22 amma za a fid da mugaye daga ƙasar,
za a tumɓuke marasa aminci kuma daga gare ta.
-
10 Saboda haka kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai;
kada ka karai, gama ni ne Allahnka.
Zan ƙarfafa ka in kuma taimake ka;
zan riƙe ka da hannun damana mai adalci.
-
17 ba makamin da aka ƙera don yă cuce ki da zai yi nasara,
za ki kuma mayar da magana ga duk wanda ya zarge ki.
Wannan ne gādon bayin Ubangiji,
kuma wannan ita ce nasararsu daga gare ni,”
in ji Ubangiji.
-
1 Bayan haka, Ubangiji ya naɗa waɗansu mutum saba’in da biyu, ya aike su biyu-biyu, su riga shi yin gaba zuwa kowane gari da kowane wuri da zai shiga. 2 Ya ce musu, “Girbi na da yawa, amma ma’aikata kaɗan ne. Saboda haka, ku roƙi Ubangijin girbi ya aikar da ma’aikata zuwa gonarsa. 3 Ku tafi! Ina aikan ku kamar tumaki cikin kyarketai. 4 Kada ku ɗauki jakar kuɗi, ko jaka, ko takalma. Kada ma ku gai da kowa a kan hanya.
5 “Sa’ad da kuka shiga wani gida, ku fara da cewa, ‘Salama a gare ku mutanen gida.’ 6 In akwai mutum mai salama a gidan, salamarku za tă kasance tare da shi, in kuwa babu, salamarku za tă koma muku. 7 Ku zauna a wannan gidan, kuna ci kuna shan duk abin da suka ba ku, gama ma’aikaci ya cancanci albashinsa. Kada ku yi yawan sāke masauƙi, daga gida zuwa gida.
8 “Sa’ad da kuka shiga garin, kuma aka karɓe ku, ku ci ko mene ne da aka ajiye a gabanku. 9 Ku warkar da marasa lafiya da suke wurin. Ku kuma faɗa musu cewa, ‘Mulkin Allah yana kusa da ku.’ 10 Amma sa’ad da kuka shiga garin, kuma ba a karɓe ku ba, ku bi titi-titi ku ce, 11 ‘Ko ƙurar garinku da kuke manne a ƙafafunmu, mun karkaɗe muku. Duk da haka, ku tabbatar da wannan, “Mulkin Allah yana kusa.” ’ 12 Ina dai faɗa muku, a ranan nan, za a fi jin tausayin Sodom fiye da wannan garin.
-
27 Salama na bari tare da ku; salamata nake ba ku. Ba kamar yadda duniya take bayarwa nake ba ku ba. Kada zuciyarku ta ɓaci kada kuma ku ji tsoro.
-
37 A’a, cikin dukan waɗannan abubuwa mun ma fi masu nasara ta wurin shi wanda ya ƙaunace mu. 38 Gama na tabbata cewa ko mutuwa ko rai, ko mala’iku ko aljanu, ko abubuwa na yanzu ko abubuwa masu zuwa nan gaba, ko ikoki, 39 ko tsayi ko zurfi, ko wani abu dabam cikin dukan halitta da zai iya raba mu da ƙaunar Allah wadda take cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.
-
3 Ubangiji mai aminci ne, zai ƙarfafa ku, yă kuma tsare ku daga mugun nan. 4 Muna da tabbaci cikin Ubangiji cewa kuna bin umarnai da muka yi muku, za ku kuma ci gaba da yin abubuwan da muka umarta. 5 Bari Ubangiji yă bi da zukatanku ga ƙaunan nan ta Allah da kuma jimirin nan na Kiristi.
Shows Read in context, Share and Copy.