106 Bible Verses About Love and Compassion
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
29 Kada wata ƙazamar magana ta fita daga bakunanku, sai dai abin da yake da amfani don gina waɗansu bisa ga bukatunsu. Ta haka maganarku za tă zama da amfani ga masu jinta. 30 Kada kuma ku ɓata wa Ruhu Mai Tsarki na Allah rai, wanda da shi aka hatimce ku da shi don ranar fansa. 31 Ku rabu da kowane irin ɗacin rai, haushi da hasala, faɗa da ɓata suna, ku rabu da kowace irin ƙeta. 32 Ku yi alheri, ku kuma ji tausayin juna, kuna gafarta wa juna, kamar yadda a cikin Kiristi, Allah ya gafarta muku.
-
12 Da yake Allah ya mai da ku zaɓaɓɓu, tsarkaka, ƙaunatattu, sai ku dinga jin tausayin juna, kuna yin alheri, kuna nuna tawali’u da sauƙinkai da jimrewa. 13 Ku riƙa yin haƙuri da juna kuna kuma gafarta wa juna duk wani laifin da wani ya yi muku. Ku gafarta kamar yadda Ubangiji ya gafarce ku. 14 Fiye da waɗannan duka, ku yi ƙaunar juna, gama ƙauna ce take haɗa kome gaba ɗaya.
15 Ku bar salamar Kiristi tă yi mulki a zukatanku, da yake a matsayin gaɓoɓin jiki ɗaya an kira ku ga salama. Ku zama masu godiya.
-
35 Yesu ya zazzaga dukan garuruwa da ƙauyuka, yana koyarwa a majami’unsu, yana wa’azin labari mai daɗi na mulkin yana kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya. 36 Da ya ga taron mutane, sai ya ji tausayinsu, domin an wulaƙanta su ba su kuma da mai taimako, kamar tumaki marasa makiyayi. 37 Sai ya ce wa almajiransa, “Girbi yana da yawa, amma ma’aikata kaɗan ne. 38 Saboda haka ku roƙi Ubangijin girbi, yă aiko da ma’aikata cikin gonarsa na girbi.”
-
8 A ƙarshe, dukanku ku zauna lafiya da juna; ku zama masu juyayi, kuna ƙaunar juna kamar ’yan’uwa, ku zama masu tausayi da kuma tawali’u. 9 Kada ku rama mugunta da mugunta ko zagi da zagi, sai dai ku sa albarka, gama ga wannan ne aka kira ku, ku kuma gāji albarka.
-
8 Sai maganar Ubangiji ta sāke zuwa wa Zakariya cewa, 9 “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ku yi shari’ar gaskiya; ku nuna jinƙai da tausayi ga juna. 10 Kada ku danne gwauruwa ko maraya, baƙo ko talaka. A cikin zuciyarku kada ku yi mugun tunani game da juna.’
-
22 Domin ƙaunar Ubangiji ba mu hallaka ba;
gama jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa.
23 Sababbi ne kowace safiya;
amincinka kuwa mai girma ne.
-
29 Sa’ad da Yesu da almajiransa suke barin Yeriko, sai wani babban taro ya bi shi. 30 Makafi biyu kuwa suna zaune a bakin hanya, da suka ji cewa Yesu yana wucewa, sai suka ɗaga murya suka ce, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayinmu!”
31 Mutane suka tsawata musu, suka ce musu su yi shiru. Sai suka ƙara ɗaga murya suna cewa, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayinmu!”
32 Yesu ya tsaya ya kira su. Ya tambaye su, “Me kuke so in yi muku?”
33 Suka amsa suka ce, “Ubangiji, muna so mu sami ganin gari.”
34 Sai Yesu ya ji tausayinsu, ya taɓa idanunsu. Nan da nan kuwa suka sami ganin gari, suka kuma bi shi.
-
13 Sa’ad da Yesu ya ji abin da ya faru, sai ya shiga jirgin ruwa ya janye shi kaɗai zuwa wani wuri inda ba kowa. Da jin haka, taron mutane suka bi shi da ƙafa daga garuruwa. 14 Da Yesu ya sauka ya kuma ga taro mai yawa, sai ya ji tausayinsu ya kuma warkar da marasa lafiyarsu.
-
16 Yadda muka san ƙauna ke nan, wato, Yesu Kiristi ya ba da ransa dominmu. Ya kamata mu ma mu ba da rayukanmu domin ’yan’uwanmu. 17 In wani yana da arziki, ya kuma ga ɗan’uwansa cikin rashi, bai kuwa taimake shi ba, anya, ƙaunar Allah tana a cikinsa kuwa? 18 ’Ya’yana ƙaunatattu, kada mu yi ƙauna da fatar baki kawai, sai dai mu nuna ta ta wurin aikatawa da kuma gaskiya.
-
18 Musa kuwa ya ce, “To, ka nuna mini ɗaukakarka.”
19 Sai Ubangiji ya ce, “Zan wuce a gabanka, Ni Ubangiji zan yi shelar sunana a gabanka. Zan yi alheri ga duk wanda na so in yi masa alheri, zan nuna jinƙai ga duk wanda na so in yi masa jinƙai. 20 Amma ya ce, ba za ka ga fuskata ba, don ba mutumin da zai gan ni yă rayu.”
21 Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Ga wani wuri kusa da ni inda za ka tsaya bisa dutsen. 22 A sa’ad da ɗaukakata tana wucewa, zan sa ka a cikin tsaguwar dutsen, in rufe ka da hannuna har sai na wuce. 23 Sa’an nan zan ɗauke hannuna, ka kuwa ga bayana; amma fuskata, ba za ka gani ba.”
-
16 “Amma su kakanninmu, suka yi fariya da taurinkai, ba su kuwa yi biyayya ga umarnanka ba. 17 Suka ƙi su saurare ka, suka kāsa tuna da mu’ujizan da ka aikata a cikinsu. Suka yi taurinkai, cikin tawayensu kuma suka naɗa shugaba don su koma bautarsu. Amma kai Allah ne mai gafartawa, mai alheri da jinƙai, mai jinkirin fushi, mai yalwar ƙauna. Saboda haka ba ka yashe su ba, 18 ko ma sa’ad da suka yi wa kansu siffar ɗan maraƙi, suka ce, ‘Wannan shi ne allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar,’ ko sa’ad da suka yi saɓo mai bantsoro.
-
9 “A gare ni wannan ya yi kamar kwanakin Nuhu,
sa’ad da na rantse cewa ruwan Nuhu ba za su ƙara rufe duniya ba.
Yanzu fa na rantse ba zan yi fushi da ke ba,
ba zan ƙara tsawata miki kuma ba.
10 Ko da duwatsu za su girgiza
a kuma tumɓuke tuddai,
duk da haka madawwamiyar ƙaunata da nake yi miki ba za tă jijjigu ba
ba kuwa za a kawar da alkawarin salamata ba,”
in ji Ubangiji, wanda ya ji tausayinki.
-
15 Amma kai, ya Ubangiji, kai Allah mai tausayi ne da kuma mai alheri,
mai jinkirin fushi, mai yawan ƙauna da aminci.
16 Ka juyo gare ni ka yi mini jinƙai;
ka ba wa bawanka ƙarfi;
ka ceci ni gama na bauta maka
yadda mahaifiyata ta yi.
-
Ta Dawuda.
1 Yabi Ubangiji, ya raina;
dukan abin da yake cikin cikina, yabi sunansa mai tsarki.
2 Yabi Ubangiji, ya raina,
kada kuma ka manta dukan alheransa,
3 wanda yake gafarta dukan zunubai
yake kuma warkar da dukan cututtuka,
4 wanda ya fanshi ranka daga rami
ya naɗa maka rawani da ƙauna da kuma tausayi,
5 Wanda ya ƙosar da kai da abubuwa masu kyau
domin a sabunta ƙuruciyarka kamar na gaggafa.
-
8 Cikin fushi mai zafi
na ɓoye fuskata daga gare ki na ɗan lokaci,
amma da madawwamin alheri
zan ji tausayinki,”
in ji Ubangiji Mai Fansarki.
-
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Sa’ad da annabi Natan ya zo wurinsa bayan Dawuda ya yi zina da Batsheba.
1 Ka yi mini jinƙai, ya Allah,
bisa ga ƙaunarka marar ƙarewa;
bisa ga tausayinka mai girma
ka shafe laifofina.
2 Ka wanke dukan kurakuraina
ka tsarkake ni daga zunubina.
-
31 Gama Ubangiji ba ya
yashe mutane har abada.
32 Ko da ya kawo ɓacin rai, zai nuna tausayi sosai,
ƙaunarsa tana da yawa.
33 Gama ba haka kawai yake kawo wahala
ko ɓacin rai ga ’yan adam ba.
34 Bai yarda a tattake
’yan kurkuku a ƙasa ba,
35 ko kuma a danne wa mutum hakkinsa
a gaban Maɗaukaki,
36 ko kuma a danne wa mutum shari’ar gaskiya
ashe Ubangiji ba zai ga irin waɗannan abubuwa ba?
-
4 Ƙauna tana da haƙuri, ƙauna tana da kirki. Ba ta kishi, ba ta burga, ba ta da girman kai. 5 Ba ta rashin ladabi, ba ta sonkai, ba ta da saurin fushi, ba ta riƙe mutum a zuciya. 6 Ƙauna ba ta jin daɗin mugunta, sai dai ta ji daɗin gaskiya. 7 Tana kāriya kullum, tana amincewa kullum, tana bege kullum, tana jimrewa kullum.
8 Ƙauna ba ta ƙarewa. Amma in akwai annabci zai shuɗe, harsuna su ɓace, ilimi kuma zai ƙare.
-
1 In kuna da wata ƙarfafawa daga tarayya da Kiristi, in da wata ta’aziyya daga ƙaunarsa, in da wani zumunci da Ruhu, in da juyayi da tausayi, 2 to, sai ku sa farin cikina yă zama cikakke ta wurin kasance da hali ɗaya, kuna ƙauna ɗaya, kuna zama ɗaya cikin ruhu da kuma manufa. 3 Kada ku yi kome da sonkai ko girman kai, sai dai cikin tawali’u, ku ɗauki waɗansu sun fi ku.
-
6 Sai Ubangiji ya wuce a gaban Musa, ya yi shela ya ce, “Ni ne Ubangiji Allah mai tausayi, mai alheri, mai jinkirin fushi, cike da ƙauna da aminci, 7 nakan nuna ƙauna wa dubbai, nakan kuma gafarta mugunta, tawaye da zunubi. Amma ba na barin mai laifi, ba tare da na hore shi ba; nakan hukunta ’ya’ya da jikoki har tsara ta uku da ta huɗu saboda laifin iyaye.”
-
13 Kamar yadda mahaifi yake jin tausayin ’ya’yansa,
haka Ubangiji yake jin tausayin waɗanda suke tsoronsa;
-
8 Ubangiji mai alheri da kuma tausayi,
mai jinkirin fushi cike kuma da ƙauna.
9 Ubangiji nagari ne ga duka;
yana tausayin dukan abubuwan da ya yi.
-
18 Wane ne Allah kamar ka,
wanda yake yafe zunubi yă kuma gafarta laifofin mutanensa da suka ragu?
Ba ka zama mai fushi har abada
amma kana marmari ka nuna jinƙai.
19 Za ka sāke jin tausayinmu;
za ka tattake zunubanmu a ƙarƙashin sawunka
ka kuma tura dukan kurakuranmu zuwa cikin zurfafan teku.
20 Za ka yi wa Yaƙub aminci,
ka kuma nuna jinƙai ga Ibrahim,
kamar yadda ka yi alkawari da rantsuwa ga kakanninmu
tun a kwanankin dā.
-
34 Da Yesu ya sauka, ya ga taro mai yawa, sai ya ji tausayinsu, gama kamar tumaki suke waɗanda ba su da makiyayi. Sai ya fara koya musu abubuwa da yawa.
-
1 Sa’ad da dukan albarku da la’anonin nan da na sa a gabanku suka zo muku, kuka kuma sa su a zuciya, a duk inda Ubangiji Allahnku ya watsar da ku a cikin al’ummai, 2 sa’ad da kuma ku da ’ya’yanku kuka komo ga Ubangiji Allahnku, kuka kuma yi biyayya da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku, bisa ga kome da na umarce ku a yau, 3 a sa’an nan ne Ubangiji Allahnku zai yi muku jinƙai, yă ji tausayinku, yă kuma sāke tattara ku daga dukan al’ummai inda ya warwatsa ku. 4 Ko da ma an kore ku zuwa ƙasa mafi nisa a ƙarƙashin sammai, daga can Ubangiji Allahnku zai tattara ku, yă dawo da ku. 5 Zai dawo da ku zuwa ƙasar da take ta kakanninku, za ku kuwa mallake ta. Zai sa ku yi arziki, ku kuma yi yawa fiye da kakanninku.
-
7 Ka nuna mini girmar ƙaunarka mai banmamaki,
kai da kake ceton waɗanda suke neman mafaka daga abokan gābansu
da hannunka na dama.
-
8 Ubangiji mai tausayi ne da kuma alheri,
mai jinkirin fushi, cike da ƙauna.
-
7 Zan ba da labarin alherin Ubangiji,
ayyukan da suka sa a yabe shi,
bisa ga dukan abubuwan da Ubangiji ya yi mana,
I, ayyuka masu kyan da ya yi
domin gidan Isra’ila,
bisa ga jinƙansa da yawan alheransa.
-
8 Ya nuna maka, ya mutum, abin da yake mai kyau.
Me Ubangiji yake bukata daga gare ka kuwa
shi ne ka yi gaskiya ka so aikata jinƙai
ka kuma yi tafiya da tawali’u a gaban Allah.
-
40 Wani mutum mai kuturta ya zo wurinsa, ya durƙusa ya roƙe shi ya ce, “In kana so, za ka iya tsabtacce ni.”
41 Cike da tausayi, sai Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin ya ce, “Na yarda, ka tsabtacce!” 42 Nan da nan, sai kuturtar ta rabu da shi, ya kuma warke.
43 Yesu ya sallame shi nan take, da gargaɗi mai ƙarfi cewa, 44 “Ka lura kada ka gaya wa kowa wannan. Amma ka tafi ka nuna kanka ga firist, ka kuma miƙa hadayun da Musa ya umarta saboda tsarkakewarka, don yă zama shaida gare su.” 45 A maimakon haka, sai ya fita, ya fara magana a sake, yana baza labarin. Saboda haka, Yesu bai ƙara iya shiga cikin gari a fili ba, sai dai ya kasance a wuraren da ba kowa. Duk da haka, mutane suka yi ta zuwa wurinsa daga ko’ina.
-
12 Da ya yi kusa da ƙofar garin, sai ga wata gawa ana fitowa da ita. Shi ne ɗa kaɗai ga mahaifiyarsa, ita kuma gwauruwa ce. Taro mai yawa daga garin yana tare da ita. 13 Da Ubangiji ya gan ta, sai ya ji tausayinta ya ce, “Kada ki yi kuka.”
14 Yesu ya je ya taɓa akwatin gawar, sai masu ɗaukarsa suka tsaya cik. Sai ya ce, “Saurayi, na ce maka, tashi!” 15 Sai mamacin ya tashi zaune, ya fara magana. Yesu kuma ya ba da shi ga mahaifiyarsa.
-
3 Yabo ya tabbata ga Allah, da Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba mai tausayi, da kuma Allah na dukan ta’aziyya, 4 wanda yakan yi mana ta’aziyya a cikin dukan wahalolinmu, domin mu kuma mu iya ta’azantar da waɗanda suke cikin kowace irin wahala, da ta’aziyyar da mu kanmu muka samu daga Allah.
-
6 Da ta buɗe kwandon, sai ta ga yaro yana kuka, ta kuwa ji tausayinsa. Ta ce, “Wannan ɗaya daga cikin jariran Ibraniyawa ne.”
-
1 Ubangiji zai yi wa Yaƙub jinƙai;
zai sāke zaɓi Isra’ila
yă kuma zaunar da su a ƙasarsu.
Baƙi ma za su zo su zauna tare da su
su haɗa kai da gidan Yaƙub.
2 Al’ummai za su ɗauke su
su kuma kawo wurin da yake nasu.
Gidan Isra’ila kuwa za tă mallaki al’ummai
a matsayin bayi maza da mata a ƙasar Ubangiji.
Za su mai da waɗanda suka kama su su zama kamammu
su kuma yi mulki a kan waɗanda suka taɓa danne su.
3 A ranar da Ubangiji ya hutashe ku daga wahala da azaba da muguwar bauta,
-
15 “Yana yiwuwa mahaifiya ta manta da jariri a ƙirjinta
ta kuma kāsa nuna tausayi ga yaron da ta haifa?
Mai yiwuwa ta manta,
amma ba zan taɓa manta da ke ba!
16 Duba, na zāna ki a tafin hannuwana;
katangarki kullum suna a gabana.
-
33 Amma wani mutumin Samariya da yake kan tafiya, da ya kai inda mutumin yake, ya gan shi, sai ya ji tausayinsa. 34 Ya je wurinsa, ya daddaure masa raunukansa, sa’an nan ya zuba mai, da ruwan inabi. Ya ɗauki mutumin ya sa a kan jakinsa, ya kai shi wani masauƙi, ya yi jinyarsa. 35 Kashegari, sai ya ɗauki dinari biyu, ya ba wa mai masauƙin ya ce, ‘Ka lura da shi, bayan na dawo, zan biya ka duk abin da ka ƙara kashewa a kansa.’
36 “A ganinka, a cikin waɗannan mutane uku, wane ne maƙwabcin mutumin da ya fāɗi a hannun mafasa?”
37 Masanin dokoki ya amsa ya ce, “Wanda ya nuna masa jinƙai.”
Yesu ya ce masa, “Je ka, ka yi haka nan.”
-
15 Gama babban firist da muke da shi ba marar juyayin kāsawarmu ba ne, amma muna da wanda aka gwada ta kowace hanya, kamar dai yadda akan yi mana, duk da haka bai yi zunubi ba. 16 Saboda haka sai mu matso kusa da kursiyin alheri da ƙarfi zuciya, don mu sami jinƙai mu kuma sami alherin da zai taimake mu a lokacin bukata.
-
3 Igiyoyin mutuwa sun shaƙe ni,
wahalar kabari sun zo a kaina;
na cika da wahala da ɓacin rai.
4 Sai na kira ga sunan Ubangiji na ce,
“Ya Ubangiji, ka cece ni!”
5 Ubangiji mai alheri ne da kuma mai adalci;
Allahnmu yana cike da tausayi.
-
12 In kuka ji an yi magana a kan wani daga cikin biranen da Ubangiji Allahnku yake ba ku ku zauna a ciki 13 cewa mugaye sun taso a cikinku, suna rikitar da mutane a birni, suna cewa, “Mu je mu yi wa waɗansu alloli sujada” (allolin da ba ku sani ba), 14 to, sai ku bincike labarin sosai a hankali. In kuwa gaskiya ne, an kuma tabbatar wannan abin ƙyama ya faru a cikinku, 15 dole a karkashe dukan waɗanda suke zama a wannan birni da takobi. Ku hallaka su ƙaƙaf, ku karkashe mutanen birnin da kuma dabbobinsa. 16 Ku tattara dukan ganimar birnin a tsakiyar gari, ku ƙone birnin da kuma ganimar ƙurmus a matsayin hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji Allahnku. Birnin zai kasance kufai har abada, kada a sāke gina shi. 17 Ba za a iske wani daga cikin abubuwan nan da aka haramta a hannuwanku ba, saboda Ubangiji yă juya daga fushinsa mai ƙuna, yă nuna jinƙai, yă ji tausayinku, yă kuma ƙara yawanku, kamar yadda ya alkawarta da rantsuwa ga kakanninku,
-
22 Hazayel sarkin Aram ya musguna wa Isra’ila a duk tsawon mulkin Yehoyahaz. 23 Amma Ubangiji ya nuna musu alheri, ya ji tausayinsu, ya kuma damu da su saboda alkawarinsa da Ibrahim, Ishaku da Yaƙub. Har yă zuwa yau bai yarda yă hallaka su ko yă shafe su daga gabansa ba.
-
38 Duk da haka ya kasance mai jinƙai;
ya gafarta laifofinsu
bai kuwa hallaka su ba.
Sau da sau ya janye fushinsa
bai kuwa sa fushinsa yă ƙuna ba.
-
18 Duk da haka Ubangiji yana marmari ya yi muku alheri;
ya tashi don yă nuna muku jinƙai.
Gama Ubangiji Allah ne mai aikata gaskiya.
Masu albarka ne dukanku waɗanda suke dogara gare shi!
-
6 “Zan ƙarfafa gidan Yahuda
in kuma ceci gidan Yusuf.
Zan maido da su
domin ina jin tausayinsu.
Za su zama kamar
ban taɓa ƙinsu ba,
gama ni ne Ubangiji Allahnsu
zan kuma amsa musu.
-
32 Yesu ya kira almajiransa wurinsa ya ce, “Ina jin tausayin mutanen nan; gama kwana uku ke nan suke tare da ni ba abin da za su ci. Ba na so in sallame su da yunwa, don kada su kāsa a hanya.”
33 Sai almajiransa suka amsa suka ce, “Ina za mu sami isashen burodi a wannan wurin da babu kowa mu ciyar da irin taron nan?”
34 Yesu ya tambaye su, “Burodi guda nawa kuke da shi?”
Suka amsa suka ce, “Guda bakwai da ’yan ƙananan kifaye.”
35 Ya sa taron su zazzauna a ƙasa. 36 Sa’an nan ya ɗauki burodi guda bakwai da kuma kifayen nan, da ya yi godiya, sai ya kakkarya su ya ba wa almajiran, su kuma suka ba wa mutane. 37 Duk kuwa suka ci, suka ƙoshi. Daga baya almajiran suka kwashe ragowar gutsattsarin cike da kwanduna bakwai.
-
16 Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami. 17 Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yă yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin yă ceci duniya ta wurinsa.
-
34 “Sabon umarni nake ba ku. Ku ƙaunaci juna. Kamar yadda na ƙaunace ku, ku ma ku ƙaunaci juna. 35 Ta haka kowa zai san cewa ku almajiraina ne, in kuna ƙaunar juna.”
-
15 Gama ya ce wa Musa,
“Zan nuna jinƙai ga wanda zan nuna jinƙai,
zan kuma ji tausayin wanda zan ji tausayi.”
-
2 Kullum ku kasance masu sauƙinkai da kuma hankali; ku zama masu haƙuri, kuna jimrewa da juna cikin ƙauna. 3 Ku yi ƙoƙari sosai ku kiyaye zaman ɗayan nan da Ruhu ya ba ku, ku yi haka ta wurin zaman lafiya da juna.
-
11 Kamar yadda kuka sani, mukan ce da waɗanda suka jure, masu albarka ne. Kun ji daurewar Ayuba, kuka kuma ga abin da Ubangiji ya yi a ƙarshe. Ubangiji yana cike da tausayi da jinƙai.
-
20 Amma ku, abokaina ƙaunatattu, ku gina kanku cikin bangaskiyarku mafi tsarki, ku kuma yi addu’a cikin Ruhu Mai Tsarki. 21 Ku zauna cikin ƙaunar Allah yayinda kuke jira jinƙan Ubangijinmu Yesu Kiristi don yă kawo ku ga rai madawwami.
22 Ku ji tausayin waɗanda suke shakka; 23 ku cece waɗansu ta wurin fizge su daga wuta. Ga waɗansu kuma ku ji tausayinsu, amma tare da tsoro, har ma ku yi ƙyamar tufafin da suka ɓata da ayyukansu na jiki.
-
8 Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“A lokacin tagomashina zan amsa muku,
kuma a ranar ceto zan taimake ku;
zan kiyaye ku zan kuma sa
ku zama alkawari ga mutane,
don ku maido da ƙasa
ku kuma sāke raba gādon kufai,
9 don ku ce wa waɗanda suke cikin kurkuku, ‘Ku fito,’
ga waɗanda suke cikin duhu kuma, ‘Ku ’yantu!’
“Za su yi kiwo kusa da hanyoyi
su kuma sami wurin kiwo a kowane tudu.
10 Ba za su taɓa jin yunwa ko ƙishi ba,
ba kuwa zafin hamada ko rana ta buge su ba.
Shi da ya yi musu jinƙai zai jagorance su
ya kuma bishe su kusa da maɓulɓulan ruwa.
11 Zan mayar da dukan duwatsu su zama hanyoyi,
a kuma gyara manyan hanyoyina.
12 Duba, za su zo daga nesa
waɗansu daga arewa, waɗansu daga yamma,
waɗansu daga yankin Aswan.”
-
13 Ku yi sowa don farin ciki, ya ku sammai;
ki yi farin ciki, ya ke duniya;
ku ɓarke da waƙa, ya ku duwatsu!
Gama Ubangiji ya ta’azantar da mutanensa
zai kuma ji tausayin mutanensa da suke shan wahala.
-
18 A waccan rana zan yi alkawari dominsu
da namun jeji da kuma tsuntsayen sararin sama
da dukan halittu masu rarrafe a ƙasa.
Baka da takobi da yaƙi
zan sa su ƙare a ƙasar,
domin duk su zauna lafiya.
19 Zan ɗaura aure da ke har abada;
zan ɗaura aure da yake cikin adalci da gaskiya,
cikin ƙauna da jinƙai.
20 Zan ɗaura aure da yake cikin aminci
za ki kuwa yarda cewa ni ne Ubangiji.
-
2 Sai ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji, ba irin abin da na faɗa ke nan ba tun ina gida? Wannan ne ya sa na yi ƙoƙarin tserewa zuwa Tarshish. Ai, na sani kai Allah ne mai alheri da tausayi, mai jinkirin fushi da cikakkiyar ƙauna, kai Allah ne mai dakatar da nufinka na yin hukunci.
-
4 Amma da alheri da kuma ƙaunar Allah Mai Cetonmu suka bayyana, 5 sai ya cece mu, ba saboda abubuwan adalcin da muka aikata ba, sai dai saboda jinƙansa. Ya cece mu ta wurin wankan nan na sāke haihuwa da kuma sabuntawan nan ta Ruhu Mai Tsarki, 6 wanda ya zubo mana a yalwace ta wurin Yesu Kiristi Mai Cetonmu,
-
1 Wata rana Dawuda ya yi tambaya ya ce, “Akwai wani har yanzu da ya rage a gidan Shawulu wanda zan nuna masa alheri saboda Yonatan?”
2 To, akwai wani bawa na gidan Shawulu mai suna Ziba. Sai aka kira shi yă bayyana a gaban Dawuda, sarki ya ce masa, “Kai ne Ziba?”
Sai ya ce, “I, ni ne, ranka yă daɗe.”
3 Sa’an nan sarki ya yi tambaya ya ce, “Babu wani har yanzu da ya rage a gidan Shawulu don in nuna masa alherin Allah?”
Ziba ya ce wa sarki, “Har yanzu akwai ɗan Yonatan da ya rage, sai dai shi gurgu ne a dukan ƙafafu.”
4 Sarki ya ce, “Ina yake?”
Ziba ya ce, “Yana a gidan Makir ɗan Ammiyel a Lo Debar.”
-
50 Ka gafarta wa mutanenka, waɗanda suka yi maka zunubi; ka gafarta dukan laifofin da suka yi maka, ka kuma sa waɗanda suka ci su a yaƙi su ji tausayinsu.
-
6 Ka tuna, ya Ubangiji da jinƙai da kuma ƙaunarka mai girma,
gama suna nan tun dā.
7 Kada ka tuna da zunuban ƙuruciyata
da kuma hanyoyin tawayena;
bisa ga ƙaunarka ka tuna da ni,
gama kai nagari ne, ya Ubangiji.
-
3 Wadata da arziki suna a cikin gidansa,
adalcinsa zai dawwama har abada.
4 Ko a cikin duhu haske kan haskaka wa mai aikata gaskiya,
mai alheri mai tausayi da kuma mai adalci.
5 Abu mai kyau zai zo masa shi da yake kyauta yake kuma ba da bashi hannu sake,
shi da yake yin al’amuransa cikin gaskiya.
-
7 Bayan kwana goma sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya. 8 Saboda haka ya kira Yohanan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji waɗanda suke tare da shi da dukan jama’a daga ƙarami zuwa babba. 9 Ya ce musu, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda kuka aike ni gare shi don in gabatar da kukanku, yana cewa, 10 ‘In kuka zauna a wannan ƙasa, zan gina ku ba zan kuwa rushe ku ba; zan dasa ku ba kuwa zan tumɓuke ku ba, gama ina baƙin ciki a kan masifar da na aukar a kanku. 11 Kada ku ji tsoron sarkin Babilon, wanda kuke tsoro a yanzu. Kada ku ji tsoronsa, in ji Ubangiji, gama ina tare da ku zan kuma cece ku daga hannuwansa. 12 Zan nuna muku jinƙai don yă nuna muku jinƙai ya kuma maido da ku ƙasarku.’
-
8 “Yaya zan ba da kai, Efraim?
Yaya zan miƙa ka, Isra’ila?
Yaya zan yi da kai kamar Adma?
Yaya zan yi da kai kamar Zeboyim?
Zuciyata ta canja a cikina;
dukan tausayina ya huru.
9 Ba zan zartar da fushina mai zafi ba,
ba kuwa zan juya in ragargaza Efraim ba.
Gama ni Allah ne, ba mutum ba,
Mai Tsarki a cikinku.
Ba zan zo cikin fushi ba.
-
13 Ku kyakkece zuciyarku
ba rigunanku ba.
Ku juyo ga Ubangiji Allahnku,
gama shi mai alheri ne mai tausayi kuma
mai jinkirin fushi da yawan ƙauna,
yakan kuma janye daga aika da bala’i.
14 Wa ya sani? Ko zai juya yă kuma ji tausayi
yă sa mana albarka
ta wurin hadaya ta gari da hadaya ta sha
wa Ubangiji Allahnku.
-
15 Ku yi murna da masu murna, ku yi kuka da masu kuka.
-
22 Amma amfanin da Ruhu yake bayar shi ne ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci, 23 sauƙinkai, da kuma kamunkai. Ai, ba ruwan Doka da waɗannan abubuwa.
-
33 Wani lokaci a fili an tsananta muku aka kuma zage ku aka kuma tsananta muku; a wani lokaci kuma kuka tsaya tare da waɗanda aka yi musu haka. 34 Kuka ji tausayin waɗanda suke cikin kurkuku, da farin ciki kuma kuka yarda ku rabu da dukiyar da aka ƙwace muku, domin ku kanku kun san cewa kuna da madawwamiyar dukiya mafi kyau.
-
11 yadda suka yi tun lokacin da na naɗa shugabanni bisan mutanena Isra’ila, zan kuma hutashe ka daga hannun abokan gābanka.
“ ‘Ubangiji ya furta maka cewa Ubangiji kansa zai kafa maka gida. 12 Sa’ad da kwanakinka suka ƙare, za ka huta tare da kakanninka, zan tā da zuriyarka, na cikinka, zan kuma sa mulkinsa ya kahu. 13 Shi zai gina gida domin Sunana, zan kuwa kafa gadon sarautarsa har abada. 14 Zan zama Ubansa, shi kuma yă zama ɗana. Idan ya yi laifi, zan yi amfani da mutane in hukunta shi. Mutane ne za su zama bulalata. 15 Amma ba za a taɓa ɗauke ƙaunata daga gare shi yadda na ɗauke ta daga wurin Shawulu ba, shi wannan wanda na kawar daga gabanka. 16 Gidanka da kuma masarautarka za su dawwama har abada a gabana; gadon sarautarka kuma zai kahu har abada.’ ”
-
6 Sa’ad da Mefiboshet ɗan Yonatan, ɗan Shawulu, ya zo wurin Dawuda, sai ya rusuna har ƙasa ya yi gaisuwar bangirma.
Dawuda ya ce, “Mefiboshet!”
Shi kuwa ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, ga ni, bawanka.”
7 Dawuda ya ce, “Kada ka ji tsoro, gama tabbatacce zan nuna maka alheri saboda mahaifinka Yonatan. Zan mayar maka da dukan ƙasar da take ta kakanka Shawulu, kullum kuma za ka ci a teburina.”
-
10 Ba na ɓoye adalcinka cikin zuciyata;
ina maganar amincinka da cetonka.
Ban ɓoye ƙaunarka da gaskiyarka
a gaban taron jama’arka mai girma ba.
11 Kada ka hana mini jinƙanka, ya Ubangiji;
bari ƙaunarka da gaskiyarka kullum su kāre ni.
-
16 Ka amsa mini, ya Ubangiji cikin alherin ƙaunarka;
cikin jinƙanka mai girma ka juyo gare ni.
-
4 Ya sa a tuna da abubuwa masu banmamaki nasa;
Ubangiji mai alheri ne mai tausayi kuma.
-
17 Duk wanda yake kirki ga matalauta yana ba wa Ubangiji bashi ne,
zai kuwa sami lada game da abin da ya yi.
-
22 Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“Duba, sojoji suna zuwa
daga ƙasar arewa;
babbar al’umma ce ta yunƙuro
daga iyakokin duniya.
23 Suna riƙe da baka da māshi;
mugaye ne kuma marasa tausayi.
Motsinsu kamar ƙugin teku ne
yayinda suke hawan dawakansu;
suna zuwa a jere kamar wanda ya yi shirin yaƙi
don su fāɗa miki, ya Diyar Sihiyona.”
-
31 “Lokaci yana zuwa,” in ji Ubangiji,
“sa’ad da zan yi sabon alkawari
da gidan Isra’ila
da kuma gidan Yahuda.
32 Ba zai zama kamar alkawarin
da na yi da kakanni kakanninsu ba
sa’ad da na kama su da hannu
na bishe su daga Masar,
domin sun take alkawarina,
ko da yake na zama miji a gare su,”
in ji Ubangiji.
33 “Ga alkawarin da zan yi da gidan Isra’ila
bayan wannan lokaci,” in ji Ubangiji.
“Zan sa dokata a tunaninsu
in kuma rubuta ta a zukatansu.
Zan zama Allahnsu,
za su kuma zama mutanena.
34 Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabci ba,
ko ya koya wa ɗan’uwansa cewa, ‘Ka san Ubangiji,’
domin duk za su san ni,
daga ƙaraminsu har zuwa babba,”
in ji Ubangiji.
“Gama zan gafarta muguntarsu
ba zan kuwa ƙara tuna da zunubansu ba.”
-
6 Gama jinƙai nake bukata, ba hadaya ba,
ku kuma san Allah a maimakon hadayun ƙonawa.
-
43 “Kun dai ji an faɗa, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka, ka kuma ƙi abokin gābanka.’ 44 Amma ina gaya muku, ku ƙaunaci abokan gābanku kuma ku yi wa waɗanda suke tsananta muku addu’a, 45 don ku zama ’ya’yan Ubanku na sama. Shi yakan sa ranarsa ta haskaka a kan mugaye da masu kirki; yakan kuma sako ruwan sama a bisa masu adalci da marasa adalci. 46 In masoyarku kawai kuke ƙauna, wace lada ce gare ku? Ko masu karɓar haraji ma ba haka suke yi ba? 47 In kuwa kuna gai da ’yan’uwanku ne kaɗai, me kuke yi fiye da waɗansu? Marasa bin Allah ma ba haka suke yi ba? 48 Saboda haka sai ku zama cikakku, yadda Ubanku na sama yake cikakke.
-
13 Amma ku je ku koyi abin da wannan yake nufi, ‘Jinƙai nake bukata, ba hadaya ba.’ Gama ban zo domin in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi.”
14 Sai almajiran Yohanna suka zo suka tambaye shi suka ce, “Me ya sa mu da Farisiyawa muke azumi, amma almajiranka ba sa yi?”
15 Yesu ya amsa ya ce, “Yaya baƙin ango za su yi makoki yayinda yake tare da su? Lokaci yana zuwa da za a ɗauke ango daga gare su, sa’an nan za su yi azumi.
16 “Ba mai yin faci da sabon ƙyalle a kan tsohuwar riga, gama facin zai kece rigar yă sa kecewar ma ta fi ta dā muni.
-
20 Sai ya tashi ya kama hanya ya koma wurin mahaifinsa.
“Amma tun yana nesa, mahaifinsa ya hange shi. Tausayi kuma ya kama shi, sai ya tashi ya ruga da gudu wurinsa, ya rungume shi, ya yi masa sumba.
-
7 Allah ya yi haka domin a tsararraki masu zuwa yă nuna yalwar alherinsa da ya wuce misali, an bayyana alheransa da ya yi mana ta wurin Kiristi Yesu.
-
10 Kowa yă yi amfani da kowace baiwar da ya samu don kyautata wa waɗansu, cikin aminci yana aikata alherin Allah a hanyoyi dabam-dabam.
-
6 amma ina nuna ƙauna ga tsara dubbai na waɗanda suke ƙaunata, suke kuma kiyaye umarnaina.
-
21 Shawulu ya ce, “Ubangiji ya yi muku albarka, gama kun damu da ni.
-
34 Ku yi godiya ga Ubangiji, gama shi nagari ne;
ƙaunarsa madawwamiya ce.
-
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda bawan Ubangiji. Ya rera ta ga Ubangiji kalmomin wannan waƙa sa’ad da Ubangiji ya cece shi daga hannun dukan abokan gābansa da kuma daga hannun Shawulu, ya ce,
1 Ina ƙaunarka, ya Ubangiji, ƙarfina.
-
21 Yabo ya tabbata ga Ubangiji,
gama ya nuna ƙaunarsa mai banmamaki gare ni
sa’ad da aka yi mini kwanto kewaye da birni.
-
3 Domin ƙaunarka ta fi rai kyau,
leɓunana za su ɗaukaka ka.
-
77 Bari tausayinka yă zo mini don in rayu,
gama dokarka ce farin cikina.
-
2 Zan rusuna ta wajen haikalinka mai tsarki
zan kuma yabi sunanka
saboda ƙaunarka da amincinka,
saboda ka ɗaukaka a bisa kome
sunanka da kuma maganarka.
-
18 Bakkunansu za su kashe samari;
ba za su ji tausayin jarirai ba
ba za su kuwa nuna jinƙai ga ’yan yara ba.
-
11 Sa’ad da rassanta suka bushe, sai su kakkarye su
mata kuma su zo su yi itacen wuta da su.
Gama mutane ne marar azanci;
saboda haka Mahaliccinsu bai ji tausayinsu ba,
Mahaliccinsu bai nuna musu jinƙai ba.
-
14 Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Game da dukan mugayen maƙwabtana waɗanda suka ƙwace gādon da na ba wa mutanena Isra’ila kuwa, zan tumɓuke su daga ƙasashensu zan kuma tumɓuke gidan Yahuda daga cikinsu. 15 Amma bayan na tumɓuke su, zan sāke jin tausayi in komo da kowannensu zuwa gādonsa da kuma ƙasarsa.
-
14 Zan fyaɗe su a kan juna, iyaye da ’ya’yansu maza, in ji Ubangiji. Tausayi ko jinƙai, ko juyayi ba zai hana ni hallaka su ba.’ ”
-
7 Bayan wannan, in ji Ubangiji, zan ba da Zedekiya sarkin Yahuda, fadawansa da kuma mutanen wannan birni waɗanda suka tsira daga annoba, takobi da kuma yunwa, ga Nebukadnezzar sarkin Babilon da kuma ga abokan gābansu waɗanda suke neman ransu. Zai kashe su da takobi; ba zai ji tausayinsu ko ya yi musu jinƙai ko ya yi juyayinsu ba.’
-
26 to zan ƙi zuriyar Yaƙub da na Dawuda bawana ba zan kuma zaɓi ɗaya daga cikin ’ya’yansa maza ya yi mulki a kan zuriyar Ibrahim, Ishaku da Yaƙub ba. Gama zan mayar da wadatarsu in kuma yi musu jinƙai.’ ”
-
42 Suna riƙe da baka da māshi;
mugaye ne marasa tausayi.
Amonsu ya yi kamar rurin teku
yayinda suke hawan dawakansu;
suna zuwa kamar mutane a dāgār yaƙi
don su fāɗa miki, ya Diyar Babilon.
-
1 Ku ji maganar Ubangiji, ku Isra’ilawa,
gama Ubangiji yana da tuhumar da zai kawo
a kan ku waɗanda suke zama a ƙasar.
“Babu aminci, babu ƙauna,
babu yarda da Allah a cikin ƙasar.
-
7 Masu albarka ne waɗanda suke masu jinƙai,
gama za a nuna musu jinƙai.
-
33 Ashe, bai kamata kai ma ka ji tausayin abokin bautarka yadda na yi maka ba?’
-
19 Yesu bai yardar masa ba, amma ya ce, “Ka tafi gida wurin iyalinka, ka gaya musu babban alherin da Ubangiji ya yi maka, da yadda ya yi maka jinƙai.”
-
27 “Amma ina faɗa muku, ku da kuke ji na, ku ƙaunaci abokan gābanku, ku yi wa masu ƙinku alheri. 28 Ku albarkaci waɗanda suke la’anta ku, ku kuma yi wa waɗanda suke wulaƙanta ku addu’a. 29 In wani ya mare ka a wannan kumatu, juya masa ɗayan ma, in wani ya ƙwace maka babban riga, kada ma ka hana masa ’yar cikin ma. 30 Duk wanda ya roƙe ka abu, ka ba shi. In kuma wani ya yi maka ƙwace, kada ka nema yă mayar maka. 31 Ka yi wa waɗansu abin da kai kake so su yi maka.
-
8 Kada hakkin kowa yă zauna a kanku, sai dai na ƙaunar juna, don mai ƙaunar maƙwabcinsa ya cika Doka ke nan. 9 Umarnan nan, “Kada ka yi zina.” “Kada ka yi kisankai.” “Kada ka yi sata.” “Kada kuma ka yi ƙyashi.” Da dai duk sauran umarnai an ƙunshe su ne a wannan kalma “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.” 10 Ƙauna ba ta cutar da maƙwabci. Saboda haka ƙauna cika Doka ce.
-
2 Ku ɗauki nawayar juna, a haka kuwa za ku cika dokar Kiristi.
-
1 Ku zama masu koyi da Allah, kamar ƙaunatattun ’ya’ya, 2 ku kuma yi rayuwar ƙauna, kamar yadda Kiristi ya ƙaunace mu, har ya ba da kansa dominmu a matsayin sadaka mai ƙanshi da kuma hadaya ga Allah.
-
2 Da yake babban firist ɗin mai kāsawa ne, yana iya bin da jahilai da kuma waɗanda suka kauce hanya, a hankali.
-
27 Addinin da Allah Ubanmu ya yarda da shi a matsayin mai tsabta da kuma marar aibi shi ne, a kula da marayu da gwauraye cikin damuwoyinsu, a kuma kiyaye kai daga lalacin da duniya take sa wa.
-
1 Dubi irin ƙaunar da Uba ya ƙaunace mu da ita mana, har ana ce da mu ’ya’yan Allah! Haka kuwa muke! Dalilin da ya sa duniya ba tă san mu ba shi ne, don ba tă san shi ba. 2 Abokaina ƙaunatattu, yanzu, mu ’ya’yan Allah ne, kuma abin da za mu zama nan gaba ba a riga an bayyana ba. Sai dai mun san cewa sa’ad da Kiristi ya bayyana, za mu zama kamar sa, domin za mu gan shi kamar yadda yake.
-
7 Abokaina ƙaunatattu, mu ƙaunaci juna, domin ƙauna tana zuwa daga Allah ne. Duk mai ƙauna, haifaffe ne na Allah, ya kuma san Allah. 8 Duk wanda ba ya ƙauna, bai san Allah ba, domin Allah ƙauna ne.
Shows Read in context, Share and Copy.