53 Bible Verses About Kids

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Kids
  1. 1 Ku ’ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku, gama ku na Ubangiji, abin da ya dace ku yi ke nan. 2 Doka ta farko wadda aka haɗa da alkawari ita ce, “Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, 3 don ka zauna lafiya, ka kuma yi tsawon rai a duniya.”

    4 Ku kuma iyaye, kada ku tsokane ’ya’yanku. Ku yi musu reno mai kyau. Ku koyar da su, ku kuma gargaɗe su game da Ubangiji.

  2. 3 ’Ya’ya maza gādo ne daga Ubangiji,

    yara lada ne daga gare shi.

    4 Kamar kibiyoyi a hannun jarumi

    haka ’ya’ya mazan da aka haifa wa mutum a ƙuruciya.

    5 Mai albarka ne mutumin

    da korinsa sun cika da su.

    Ba za a kunyata su ba

    sa’ad da suke ƙarawa da abokan gābansu a ɗakin shari’a.

  3. 1 A lokacin nan sai almajirai suka zo wurin Yesu suka yi tambaya suka ce, “Wane ne mafi girma a mulkin sama?”

    2 Sai ya kira ƙaramin yaro ya sa shi yă tsaya a tsakiyarsu. 3 Sai ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, in ba kun canja kuka zama kamar ƙananan yara ba, labudda, ba za ku shiga mulkin sama ba. 4 Saboda haka, duk wanda ya ƙasƙantar da kansa kamar wannan yaro, shi ne mafi girma a mulkin sama. 5 Duk kuma wanda ya karɓi ƙaramin yaro kamar wannan a cikin sunana ya karɓe ni ne.

    6 “Amma duk wanda ya sa ɗaya daga cikin ƙananan nan da suka gaskata da ni ya yi zunubi, zai fiye masa a rataya babban dutsen niƙa a wuyarsa, a kuma nutsar da shi a zurfin teku.

  4. 13 Mutane suka kawo ƙananan yara wurin Yesu don yă taɓa su, amma almajiran suka kwaɓe su. 14 Da Yesu ya ga haka, sai ya yi fushi, ya ce musu, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su, gama mulkin Allah na irin waɗannan ne. 15 Gaskiya nake gaya muku, duk wanda bai karɓi mulkin Allah kamar ƙaramin yaro ba, ba zai taɓa shiga mulkin ba.” 16 Sai ya ɗauki yaran a hannuwansa, ya ɗibiya musu hannuwansa, ya kuma albarkace su.

  5. 13 Sa’an nan aka kawo yara ƙanana wurin Yesu don yă ɗibiya musu hannuwansa, yă kuma yi musu addu’a. Amma almajirai suka tsawata wa waɗanda suka kawo su.

    14 Yesu ya ce, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su, gama mulkin sama na irin waɗannan ne.” 15 Sa’ad da ya ɗibiya musu hannuwansa, sai ya tafi abinsa.

  6. 6 Ka hori yaro a hanyar da ya kamata yă bi,

    kuma sa’ad da ya tsufa ba zai bar ta ba.

  7. 20 ’Ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku cikin kome, gama wannan yakan gamshi Ubangiji.

    21 Ubanni, kada ku matsa wa yaranku lamba, don kada su fid da zuciya.

  8. 33 Suka iso Kafarnahum. Da yana cikin gida, sai ya tambaye su ya ce, “Gardamar me kuke yi a hanya?” 34 Amma suka yi shiru, don a hanya suna gardama ne, a kan ko wane ne a cikinsu ya fi girma?

    35 Da Yesu ya zauna, sai ya kira Sha Biyun ya ce, “In wani yana so yă zama na fari, dole yă zama na ƙarshe duka, da kuma bawan kowa.”

    36 Ya ɗauki wani ƙaramin yaro ya sa yă tsaya a tsakiyarsu. Ya ɗauke shi a hannunsa, ya ce musu, 37 “Duk wanda ya karɓi ɗaya daga cikin waɗannan ƙananan yara a cikin sunana, ni ya karɓa. Duk wanda kuma ya karɓe ni, ba ni ya karɓa ba, amma wanda ya aiko ni ne ya karɓa.”

  9. Gargaɗi don a rungumi hikima

    8 Ɗana, ka saurari umarnin mahaifinka

    kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.

    9 Za su zama kayan ado don su inganta ka

    da kuma sarƙar wuya don su yi wa wuyanka ado.

  10. 5 Ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku da dukan zuciyarku, da dukan ranku, da kuma dukan ƙarfinku. 6 Waɗannan umarnai da nake ba ku a yau, za su kasance a zukatanku. 7 Ku koya wa ’ya’yanku su da himma. Yi musu magana game da su sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya a hanya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi. 8 Ku ɗaura su su zama alamu a hannuwanku, ku kuma ɗaura su a goshinku. 9 Ku rubuta su a dogaran ƙofofin gidajenku, da ƙofofinku.

  11. 14 Makafi da guragu suka zo wurinsa a haikali, ya kuwa warkar da su. 15 Amma da manyan firistoci da malaman dokoki suka ga abubuwan banmamakin da ya yi, yara kuma suna ihu a filin haikali suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda,” sai fushi ya kama su.

    16 Suka tambaye shi suka ce, “Kana jin abin da waɗannan suke faɗa?”

    Yesu ya amsa ya ce, “I, ba ku taɓa karanta ba cewa,

    “ ‘Daga leɓunan yara da jarirai

    kai, Ubangiji, ka shirya wa kanka yabo’?”

  12. 12 Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.

  13. 7 Ku jimre shan wahala a matsayin horo; Allah yana yi da ku kamar ’ya’ya. Gama wane ɗa ne mahaifinsa ba ya horonsa? 8 In ba a hore ku ba (kowa kuwa yakan sami horo), to, ku shegu ne ba ’ya’yan gida ba. 9 Ban da haka ma, dukanmu mun kasance da ubannin jiki waɗanda suka hore mu muka kuma yi musu ladabi. Ashe, bai kamata mu yi wa Uban ruhohinmu biyayya mu kuwa rayu ba! 10 Ubanninmu sun hore mu na ɗan lokaci yadda suka ga ya fi kyau; amma Allah yakan hore mu don amfaninmu, domin mu sami rabo cikin tsarkinsa. 11 Babu horon da yake da daɗi a lokacin da ake yinsa, sai dai zafi. Amma daga baya waɗanda suka horu ta haka sukan sami kwanciyar rai wadda aikin adalci yake bayarwa.

  14. 11 In na ce, “Tabbatacce duhu zai ɓoye ni

    haske kuma zai zama dare kewaye da ni,”

    12 duhu ma ba zai zama duhu gare ka ba;

    dare zai haskaka kamar rana,

    gama duhu ya yi kamar haske gare ka.

    13 Gama ka halicci ciki-cikina;

    ka gina ni gaba ɗaya a cikin mahaifar mahaifiyata.

    14 Ina yabonka domin yadda ka yi ni abin tsoro ne da kuma abin mamaki;

    ayyukanka suna da banmamaki,

    na san da haka sosai.

    15 Ƙasusuwana ba a ɓoye suke a gare ka ba

    sa’ad da aka yi ni asirce.

    Sa’ad da saƙa ni gaba ɗaya a zurfafan duniya.

    16 Idanunka sun ga jikina marar fasali;

    dukan kwanakin da aka tsara mini a rubuce suke a littafinka

    kafin ɗayansu yă kasance.

  15. 15 Mutane suna kawo jarirai wurin Yesu don yă taɓa su. Da almajiransa suka ga haka, sai suka kwaɓe su. 16 Amma Yesu ya kira yaran a wurinsa ya ce, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina. Kada ku hana su, gama mulkin Allah na irin waɗannan ne. 17 Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ba zai karɓi mulkin Allah kamar ƙaramin yaro ba, ba zai taɓa shiga mulkin ba.”

  16. 15 Wauta tana da yawa a zuciyar yara,

    amma sandar horo zai kore ta nesa da su.

  17. 17 Ka hori ɗanka, zai kuwa ba ka salama;

    zai ba ka farin cikin da kake so.

  18. 46 Wata gardama ta tashi a tsakanin almajiran, a kan ko wane ne a cikinsu zai zama mafi girma 47 Da yake Yesu ya san tunaninsu, sai ya ɗauki wani ƙaramin yaro, ya sa ya tsaya kusa da shi. 48 Sai ya ce musu, “Duk wanda ya karɓi wannan ƙaramin yaron a cikin sunana, ni ya karɓa, kuma duk wanda ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ne. Gama mafi ƙanƙanta duka a cikinku, shi ne kuma mafi girma.”

  19. 15 Sandar gyara kan ba da hikima,

    amma yaron da aka bari ba horo kan jawo kunya ga mahaifiyarsa.

  20. 24 Duk wanda ba ya horon ɗansa ba ƙaunarsa yake yi ba,

    amma duk mai ƙaunarsa yakan kula ya hore shi.

  21. 15 “Duk wanda ya bugi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole a kashe shi.

    16 “Duk wanda ya saci mutum ya sayar da shi, ko kuwa aka iske shi a hannunsa, lalle kashe shi za a yi.

    17 “Duk wanda ya la’anta mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole a kashe shi.

  22. 6 Jikoki rawanin tsofaffi ne,

    kuma iyaye su ne abin taƙamar ’ya’yansu.

  23. 11 Ku zo, ’ya’yana, ku saurare ni;

    zan koya muku tsoron Ubangiji.

  24. 5 Wawa yakan ƙi kulawa da horon da mahaifinsa yake masa,

    amma duk wanda ya yarda da gyara kan nuna azanci.

  25. 32 “Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni;

    masu albarka ne waɗanda suke kiyaye hanyoyina.

    33 Ku saurari umarnina ku kuma zama masu hikima;

    kada ku ƙyale ta.

  26. 11 Akan san ƙananan yara ta ayyukansu,

    ana iya sani ko rayuwarsu amintattu ne, mai nagarta.

    12 Kunnuwan da suke ji da kuma idanun da suke gani,

    Ubangiji ne ya yi su duka.

  27. 16 Ka ba da girma ga mahaifinka da mahaifiyarka, yadda Ubangiji Allahnka ya umarce ka, don ka yi tsawon rai, ka kuma sami zaman lafiya a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.

  28. 1 Ku saurara ’ya’yana ga koyarwar mahaifinku;

    ku mai da hankali, ku sami fahimi.

    2 Ina ba ku sahihiyar koyarwa,

    saboda haka kada ku ƙyale koyarwata.

    3 Sa’ad da nake yaro a gidan mahaifina,

    yaro kaɗai kuma na mahaifiyata,

    4 ya koya mini ya ce,

    “Ka riƙe kalmomina da dukan zuciyarka;

    ka kiyaye umarnaina za ka kuwa rayu.

    5 Ka nemi hikima, ka nemi fahimi;

    kada ka manta da kalmomina ko ka kauce daga gare su.

    6 Kada ka ƙyale hikima, za tă kuwa tsare ka;

    ka ƙaunace ta, za tă kuwa lura da kai.

    7 Hikima ce mafi girma duka; saboda haka ka nemi hikima.

    Ko da za tă ci duk abin da kake da shi, ka dai nemi fahimi.

  29. 1 Saboda haka, ku rabu da kowace ƙeta da dukan ruɗu, munafunci, kishi, da kuma kowace irin ɓata suna. 2 Kamar sababbin jarirai, ku yi marmarin madara zalla ta ruhaniya, domin ta wurinta za ku yi girma cikin cetonku, 3 yanzu da kuka ɗanɗana alherin Ubangiji.

  30. 5 Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka

    kada kuma ka dangana ga ganewarka;

    6 cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi,

    zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.

  31. 13 Kada ka bar yaro ba horo;

    in ka yi masa horo da sanda, ba zai mutu ba.

    14 Ka hukunta shi da sanda

    ka ceci ransa daga mutuwa.

  32. 5 Samari, ku ma, ku yi biyayya ga waɗanda suka girme ku. Dukanku, ku yafa sauƙinkai ga juna, domin,

    “Allah yana gāba da mai girman kai,

    amma yakan yi alheri ga mai sauƙinkai.”

  33. 3 Na yi farin ciki ƙwarai sa’ad da waɗansu ’yan’uwa suka zo suka yi zance game da yadda kake da aminci ga gaskiyan nan da kuma yadda kake cin gaba cikin gaskiyan nan. 4 Ba abin da ya fi sa ni farin ciki fiye da in ji cewa ’ya’yana suna cikin gaskiyan nan.

  34. 14 Bari Ubangiji yă sa ku ƙaru,

    da ku da ’ya’yanku.

  35. 3 Matarka za tă zama kamar kuringar inabi mai ’ya’ya

    a cikin gidanka;

    ’ya’yanka maza za su zama kamar tohon zaitun

    kewaye da teburinka.

  36. 7 “Ku roƙa za a ba ku; ku nema za ku samu; ku ƙwanƙwasa za a kuwa buɗe muku ƙofa. 8 Gama duk wanda ya roƙa, akan ba shi; wanda ya nema kuwa, yakan samu, wanda kuma ya ƙwanƙwasa, za a buɗe masa ƙofa.

    9 “Wane ne a cikinku in ɗansa ya roƙe shi burodi, sai yă ba shi dutse? 10 Ko kuwa in ya roƙe shi kifi, sai yă ba shi maciji? 11 In ku da kuke mugaye kun san yadda za ku ba da kyautai masu kyau ga ’ya’yanku, balle Ubanku na sama, ba zai fi ku iya ba da abubuwa masu kyau, ga su waɗanda suka roƙe shi ba!

  37. 30 Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan hankalinka, da kuma dukan ƙarfinka.’

  38. 11 “Wane mahaifi ne a cikinku, in ɗansa ya roƙe shi kifi, zai ba shi maciji a maimakon, 12 ko kuma in ya roƙi ƙwai, ya ba shi kunama? 13 In fa haka ne, ko da yake ku mugaye ne, kun san ba ’ya’yanku kyautai masu kyau, balle fa Ubanku na sama, zai yi fiye da haka, ta wurin ba da Ruhu Mai Tsarki, ga masu roƙonsa!”

  39. 1 Ku zama masu koyi da Allah, kamar ƙaunatattun ’ya’ya, 2 ku kuma yi rayuwar ƙauna, kamar yadda Kiristi ya ƙaunace mu, har ya ba da kansa dominmu a matsayin sadaka mai ƙanshi da kuma hadaya ga Allah.

  40. 1 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Je wurin Fir’auna, gama na riga na taurare zuciyarsa da kuma zukatan fadawansa domin in aikata waɗannan mu’ujizai nawa a tsakiyarsu, 2 don kuma ku gaya wa ’ya’yanku da jikokinku yadda na tsananta wa Masarawa, da kuma yadda na aikata mu’ujizai a cikinsu, don ku sani ni ne Ubangiji.”

  41. 9 “ ‘In wani ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole a kashe shi. Domin ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, alhakin jininsa zai zauna a kansa.

  42. 20 Ɗana, ka kiyaye umarnan mahaifinka

    kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.

  43. Karin maganar Solomon

    1 Karin maganar Solomon.

    Ɗa mai hikima yakan kawo wa mahaifinsa farin ciki,

    amma wawan ɗa kan sa wa mahaifiyarsa baƙin ciki.

  44. 20 Ɗa mai hikima kan kawo farin ciki wa mahaifinsa,

    amma wawa yakan rena mahaifiyarsa.

  45. 18 Ka hori ɗanka, gama yin haka akwai sa zuciya;

    kada ka goyi baya lalacewarsa.

  46. 24 Mahaifin adali yana da farin ciki sosai;

    duk wanda yake da ɗa mai hikima yakan ji daɗinsa.

  47. 1 Ka tuna da Mahaliccinka

    a kwanakin ƙuruciyarka,

    kafin lokacin wahala ta zo

    shekaru kuma su ƙarato sa’ad da za ka ce,

    “Ba na jin daɗinsu,”

  48. 42 “Idan kuma wani yă sa ɗaya daga cikin waɗannan ’yan yara masu gaskatawa da ni yă yi laifi, zai fiye masa a rataya wani babban dutsen niƙa a wuyarsa, a jefa shi cikin teku.

  49. 21 Macen da za tă haihu takan yi naƙuda domin lokacinta ya yi; amma sa’ad da ta haihu, sai ta manta da wahalar domin farin ciki an haifi jariri a duniya.

  50. 11 Sa’ad da nake yaro, na yi magana kamar yaro, na yi tunani kamar yaro, na yanke shawara kamar yaro. Da na isa mutum kuwa, sai na bar halin yarantakata.

  51. 20 ’Yan’uwa, ku daina tunani kamar yara. Wajen mugunta ku zama jarirai, sai dai wajen tunaninku, ku zama manya.

  52. 26 Dukanku ’ya’yan Allah ne ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu. 27 Gama dukanku da aka yi muku baftisma cikin Kiristi, kuna sanye da Kiristi ke nan.

  53. 4 Amma in gwauruwa tana da ’ya’ya ko jikoki, to, sai su fara koyon yin ayyukan addininsu ga danginsu, ta haka za su sāka wa iyayensu da kakanninsu, gama wannan yakan gamshi Allah.