80 Bible Verses About Listening

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Listening
  1. 19 ’Yan’uwana ƙaunatattu, ku lura da wannan. Ya kamata kowa yă kasance mai saurin saurara, ba mai saurin magana ba, ba kuma mai saurin fushi ba, 20 gama fushin mutum ba ya kawo rayuwar adalcin da Allah yake so.

  2. 22 Kada ku zama masu ji kawai, ku ruɗi kanku. A maimakon haka ku zama masu yin abin da ta ce. 23 Duk wanda yake ji magana ne kawai, bai kuwa aikata abin da ta ce ba, yana kama da mutumin da ya kalli fuskarsa a madubi 24 bayan ya kalli kansa, sa’ad da ya tashi daga wurin, nan da nan sai yă manta da kamanninsa. 25 Amma duk mai duba cikakkiyar ƙa’idan nan ta ’yanci, ya kuma nace a kanta, ya zama ba mai ji ne kawai yă mance ba, sai dai mai yi ne yă zartar, to wannan shi za a yi wa albarka a cikin abin da yake yi.

    26 In wani ya ɗauki kansa mai addini ne duk da haka bai ƙame harshensa ba, ruɗin kansa yake yi addininsa kuwa banza ne. 27 Addinin da Allah Ubanmu ya yarda da shi a matsayin mai tsabta da kuma marar aibi shi ne, a kula da marayu da gwauraye cikin damuwoyinsu, a kuma kiyaye kai daga lalacin da duniya take sa wa.

  3. 9 Almajiransa suka tambaye shi ma’anar wannan misali. 10 Sai ya ce, “Ku ne aka ba sanin asirin mulkin Allah, amma ga sauran mutane kam, ina magana da misalai, saboda,

    “ ‘ko da yake suna kallo, ba za su gani ba,

    ko da yake suna ji, ba za su gane ba.’

    11 “Ga ma’anar misalin, irin, shi ne maganar Allah. 12 Waɗanda suka fāɗi a kan hanya su ne mutanen da suka ji, amma Iblis, yakan zo ya ɗauke maganar daga zuciyarsu, don kada su gaskata, su sami ceto. 13 Na kan dutse kuwa, su ne da jin maganar, sukan karɓa da murna, amma ba su da saiwa. Sukan gaskata na ɗan lokaci, amma lokacin gwaji, sai su ja da baya. 14 Irin da suka fāɗi a cikin ƙaya kuwa, su ne mutanen da suka ji, amma a kwana a tashi, tunanin kayan duniya, da neman arziki, da son jin daɗi, sukan hana su ba da ’ya’ya. 15 Amma irin da suka fāɗi a ƙasa mai kyau kuwa, su ne mutane masu kyakkyawar zuciya, mai kyau, da suka ji, suka riƙe, suka kuma jimre har suka ba da ’ya’ya.”

  4. 1 Ɗana, in ka yarda da kalmomina

    ka kuma ajiye umarnaina a cikinka,

    2 kana kasa kunne ga abin da yake na hikima,

    kana kuma yin ƙoƙari ka fahimce shi,

    3 in kuma ka kira ga tsinkaya

    ka kuma kira da ƙarfi don ganewa,

    4 in ka neme shi yadda ake neman azurfa

    ka kuma neme shi kamar yadda ake neman ɓoyayyiyar dukiya,

    5 to, za ka gane tsoron Ubangiji

    ka kuma sami sanin Allah.

  5. 15 “In ɗan’uwanka ya yi maka laifi, ka je ka nuna masa laifinsa, tsakaninku biyu kaɗai. In ya saurare ka, ka maido da ɗan’uwanka ke nan. 16 Amma in bai saurare ka ba, ka je tare da mutum ɗaya ko biyu, domin ‘a tabbatar da kowace magana a bakin shaidu biyu ko uku.’ 17 In kuwa ya ƙi yă saurare su, sai ka gaya wa ikkilisiya; in kuma ya ƙi yă saurari ikkilisiya ma, ka yi da shi kamar marar sanin Allah ko mai karɓar haraji.

    18 “Gaskiya nake gaya muku, duk abin da kuka daure a duniya, za a daure a sama, duk kuma abin da kuka kunce a duniya, za a kunce shi a sama.

  6. 9 Saboda haka, Eli ya gaya wa Sama’ila cewa, “Je ka kwanta, in kuma ya kira ka, ka ce masa, ‘Ya Ubangiji ka yi magana gama bawanka yana saurara.’ ” Sama’ila ya koma ya kwanta a wurin kwanciyarsa.

    10 Ubangiji kuma ya zo ya tsaya a wurin, yana kira ya ce, “Sama’ila, Sama’ila!” Kamar yadda ya kira a lokutan baya.

    Sai Sama’ila ya ce, “Yi magana gama bawanka yana saurara.”

  7. 24 “Saboda haka duk wanda yake jin kalmomin nan nawa yake kuma aikata su, yana kama da mutum mai hikima wanda ya gina gidansa a kan dutse. 25 Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuma ta hura ta bugi gidan; duk da haka bai fāɗi ba, gama yana da harsashinsa a kan dutse. 26 Amma duk wanda yake jin kalmomin nan nawa bai kuwa aikata su ba, yana kama da wani wawa wanda ya gina gidansa a kan yashi. 27 Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuwa ta hura ta bugi gidan, sai ya fāɗi da mummunar ragargajewa kuwa.”

    28 Sa’ad da Yesu ya gama faɗin waɗannan abubuwa, sai taron mutanen suka yi mamakin koyarwarsa, 29 domin ya koyar kamar wani wanda yake da iko, ba kamar malamansu na dokoki ba.

  8. 23 Duk mai kunnen ji, bari yă ji.”

    24 Ya ci gaba da cewa, “Ku lura da abin da kuke ji da kyau. Mudun da ka auna da shi, da shi za a auna maka, har ma a ƙara. 25 Duk wanda yake da shi, za a ƙara masa, duk wanda kuma ba shi da shi, ko abin da yake da shi ma, za a karɓe daga gare shi.”

  9. 9 Da dare Bulus ya ga wahayin wani mutumin Makidoniya yana tsaye yana roƙonsa cewa, “Ka zo Makidoniya ka taimake mu.” 10 Bayan Bulus ya ga wahayin, muka shirya nan take mu tashi zuwa Makidoniya, mun tabbata cewa, Allah ya kira mu mu yi musu wa’azin bishara.

    11 Daga Toruwas muka tashi zuwa teku muka kuma shiga jirgin ruwa muka miƙe kai tsaye zuwa Samotiras, kashegari kuma muka nufi Neyafolis. 12 Daga can muka tafi Filibbi, wata babbar alkaryar Roma wadda kuma take babban birni a gundumar Makidoniya. Muka zauna a can kwanaki masu yawa.

    13 A Asabbaci, muka fita ƙofar birnin zuwa bakin kogi, inda muke tsammani za mu sami wurin yin addu’a. Muka zauna muka fara yin wa matan da suka taru a can magana. 14 Ɗaya daga cikin waɗanda suka saurare mu mace ce mai suna Lidiya, mai sayar da yadunan jan garura masu tsada daga birnin Tiyatira, mai yi wa Allah sujada. Ubangiji ya buɗe zuciyarta har ta karɓi saƙon Bulus. 15 Da aka yi mata baftisma tare da iyalin gidanta, sai ta gayyace mu zuwa gidanta. Ta ce, “In kun amince ni mai bi ce cikin Ubangiji, sai ku zo ku sauka a gidana.” Sai ta kuwa rinjaye mu.

  10. 14 Wannan shi ne ƙarfin halin da muke da shi sa’ad da muke zuwa a gaban Allah, gama mun san cewa kome muka roƙa bisa ga nufinsa, yakan saurare mu. 15 In kuwa muka san cewa yana sauraranmu, ko mene ne muka roƙa, mun sani, mun riga mun sami abin da muka roƙa daga gare shi ke nan.

  11. 13 Duk wanda yakan ba da amsa kafin ya saurara,

    wannan wauta ce da kuma abin kunya.

  12. 17 Saboda haka, bangaskiya takan zo ne ta wurin jin saƙo, akan ji saƙon kuma ta wurin maganar Kiristi.

  13. 20 Ka kasa kunne ga shawara ka kuma yarda da umarni,

    a ƙarshe kuwa za ka yi hikima.

    21 Da yawa ne shirye-shiryen zuciyar mutum,

    amma manufar Ubangiji ce takan cika.

  14. 13 Gama dukan Annabawa da kuma Doka sun yi ta annabci har yă zuwa kan Yohanna. 14 In kuna niyya ku yarda da wannan, to, shi ne Iliya da dā ma zai zo. 15 Duk mai kunnen ji, yă ji.

    16 “Da me zan kwatanta wannan zamani? Suna kama da yara da suke zaune a kasuwa, suna kiran juna, suna cewa,

    17 “ ‘Mun yi muku busa,

    ba ku kuwa yi rawa ba,

    mun rera waƙar makoki,

    ba ku kuwa yi makoki ba.’

  15. 28 Yesu ya amsa ya ce, “A maimakon, masu albarka ne waɗanda suke jin maganar Allah, suna kuma biyayya da ita.”

  16. 1 Ina ƙaunar Ubangiji, gama ya ji muryata;

    ya ji kukata ta neman jinƙai.

    2 Domin ya juye kunnensa gare ni,

    zan kira gare shi muddin ina da rai.

  17. 19 Sai Yesu ya ba su wannan amsa cewa, “Gaskiya nake gaya muku, Ɗan ba ya iya yin kome da kansa; yana yin abin da ya ga Ubansa yake yi ne kawai, gama duk abin da Uban yake yi shi ne Ɗan ma yake yi.

  18. 20 Ga ni! Ina tsaye a bakin ƙofa, ina ƙwanƙwasawa. Duk wanda ya ji muryata ya kuma buɗe ƙofar, zan shiga in kuma ci tare da shi, shi kuma tare da ni.

    21 Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ikon zama tare da ni a kursiyina, kamar yadda na ci nasara, kuma ina zaune tare da Ubana a kursiyinsa. 22 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi.”

  19. 3 Wataƙila su saurara kowanne kuma ya juyo daga mugun hanyarsa. Sa’an nan in yi juyayi in kuma janye masifar da nake shirin kawo a kansu saboda muguntar da suka aikata. 4 Ka faɗa musu, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, in ba ku saurare ni, ku kuma bi dokata, wadda na sa a gabanku ba, 5 in kuma ba ku saurari maganganun bayina annabawa, waɗanda na aika muku sau da sau ba (ko da yake ba ku saurara ba), 6 to, sai in mai da gidan nan kamar Shilo, birnin nan kuma abin la’ana a cikin al’umman duniya.’ ”

  20. 5 Yayinda yake cikin magana, sai wani girgije mai haske ya rufe su, sai wata murya daga cikin girgijen ta ce, “Wannan Ɗana ne, wanda nake ƙauna; wanda kuma nake jin daɗinsa ƙwarai. Ku saurare shi!”

  21. 30 “Game da kai kuma, ɗan mutum, mutanen ƙasarka suna magana da juna game da kai a katanga da kuma ƙofofin gidaje, suna ce wa juna, ‘Ku zo mu tafi mu ji maganar da ta zo daga wurin Ubangiji.’ 31 Mutanena sukan zo wurinka, yadda suka saba su zauna a gabanka don su saurari maganarka, amma ba sa aiki da abin da suka ji. Da bakunansu suna nuna ƙauna, amma zukatansu cike da haɗama suke don ƙazamar riba. 32 Tabbatacce, gare su ba ka fi mai waƙar ƙauna da murya mai daɗi kana kuma yin kiɗa sosai ba, gama sukan ji maganarka amma ba sa amfani da ita.

    33 “Sa’ad da dukan wannan ya cika kuma zai cika ɗin, sa’an nan za su sani akwai annabi a tsakiyarsu.”

  22. 10 Almajiran suka zo wurinsa suka tambaye shi, “Me ya sa kake wa mutane magana da misalai?”

    11 Ya amsa ya ce, “Sanin asirin mulkin sama kam, ku aka ba wa, amma su ba a ba su ba. 12 Duk wanda yake da shi, za a ƙara masa, zai kuwa samu a yalwace. Duk wanda kuma ba shi da shi, ko ɗan abin da yake da shi ma, za a karɓe. 13 Abin da ya sa nake musu magana da misalai ke nan.

    “Ko da yake suna kallo, ba sa gani;

    ko da yake suna saurara, ba sa ji ko su gane.

    14 A kansu ne aka cika annabcin Ishaya cewa,

    “ ‘Za ku yi ta ji amma ba za ku taɓa ganewa ba;

    za ku yi ta kallo amma ba za ku taɓa gani ba.

    15 Gama zuciyar mutanen nan ta taurare;

    da ƙyar suke ji da kunnuwansu,

    sun kuma rufe idanunsu.

    Da ba haka ba, mai yiwuwa su gani da idanunsu,

    su kuma ji da kunnuwansu,

    su gane a zuciyarsu,

    su kuwa juya, in kuma warkar da su.’

    16 Amma idanunku masu albarka ne domin suna gani, haka ma kunnuwanku domin suna ji. 17 Gama gaskiya nake gaya muku, annabawa da mutane masu adalci da yawa sun yi marmarin ganin abin da kuke gani amma ba su gani ba, su kuma ji abin da kuke ji amma ba su ji ba.

  23. 9 Sai Yesu ya ce, “Duk mai kunnen ji, yă ji.”

    10 Lokacin da yake shi kaɗai, Sha Biyun, da kuma waɗanda suke kewaye da shi, suka tambaye shi game da misalan. 11 Sai ya ce musu, “An ba ku sanin asirin mulkin Allah. Amma ga waɗanda suke waje kuwa, kome sai da misalai. 12 Saboda,

    “ ‘ko sun dinga duba, ba za su taɓa gane ba,

    kuma ko su dinga ji, ba za su taɓa fahimta ba,

    in ba haka ba, mai yiwuwa, su tuba, a gafarta musu!’ ”

  24. 14 Sai Yesu ya sāke kiran taron wurinsa ya ce, “Ku saurare ni dukanku, ku kuma fahimci wannan.

  25. 27 Tumakina sukan saurari muryata; na sansu, suna kuma bi na. 28 Ina ba su rai madawwami, ba za su taɓa hallaka ba; ba kuma mai ƙwace su daga hannuna.

  26. 7 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ikon ci daga itacen rai, da yake cikin aljannar Allah.

  27. 15 Idanun Ubangiji suna a kan masu adalci

    kuma kunnuwansa suna sauraran kukansu;

  28. 32 “Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni;

    masu albarka ne waɗanda suke kiyaye hanyoyina.

    33 Ku saurari umarnina ku kuma zama masu hikima;

    kada ku ƙyale ta.

    34 Mai albarka ne wanda ya saurare ni;

    yana tsaro kullum a ƙofofina,

    yana jira a ƙofar shigata.

  29. 12 Sa’an nan za ku kira gare ni ku zo ku kuma yi addu’a gare ni, zan kuwa ji ku. 13 Za ku neme ni ku kuwa same ni sa’ad da kuka neme ni da dukan zuciyarku.

  30. 2 In ba ku saurara ba, in kuma ba ku sa zuciyarku ga girmama sunana ba, zan aukar muku da la’ana, zan kuma la’antar da albarkunku. I, na riga na la’anta su, domin ba ku sa zuciyarku ga girmama ni ba, in ji Ubangiji Maɗaukaki.

  31. 1 Akwai wani Bafarisiye mai suna Nikodimus, wani ɗan majalisar Yahudawa. 2 Ya zo wurin Yesu da dad dare ya ce, “Rabbi, mun sani kai malami ne daga Allah. Gama ba wanda zai iya yin waɗannan abubuwan banmamaki da kake yi in Allah ba ya tare da shi.”

    3 Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an sāke haihuwarsa.”

    4 Nikodimus ya yi tambaya ya ce, “Yaya za a haifi mutum sa’ad da ya tsufa? Tabbatacce ba zai sāke koma sau na biyu a cikin mahaifiyarsa don a haife shi kuma ba!”

    5 Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an haife shi ta wurin ruwa da kuma Ruhu.

  32. 5 Allah ya ba ku Ruhunsa yana kuma aikata ayyukan banmamaki a cikinku saboda kuna kiyaye Doka ne, ko kuwa domin kuna gaskatawa abin da kuka ji ne?

  33. 6 Cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji;

    Na yi kuka ga Allahna don taimako.

    A Haikalinsa ya ji muryata,

    Kukana na neman taimako ya kai kunnensa.

  34. 2 Wawa ba ya sha’awa ya sami fahimta

    amma abin da yake so ya yi kaɗai, shi ne ya ba da ra’ayinsa.

  35. 27 In ka daina jin umarni, ɗana,

    za ka kuwa kauce daga kalmomin sani.

  36. 47 Wanda yake na Allah, yakan ji abin da Allah yake faɗi. Abin da ya sa ba kwa jin sa kuwa shi ne don ku ba na Allah ba ne.”

  37. 25 Wajen tsakar dare Bulus da Sila suna addu’a suna rera waƙoƙi ga Allah, sauran ’yan kurkuku kuwa suna sauraronsu.

  38. 13 Muna kuma gode wa Allah ba fasawa domin, sa’ad da kuka karɓi maganar Allah, wadda kuka ji daga gare mu, kun karɓe ta ba kamar maganar mutane ba, sai dai kamar yadda take, maganar Allah wadda take aiki a cikinku ku da kuka ba da gaskiya.

  39. 1 A gaban Allah da kuma Kiristi Yesu, wanda zai yi wa masu rai da matattu shari’a, saboda kuma bayyanuwarsa da mulkinsa, ina ba ka umarni. 2 Ka yi wa’azin Maganar Allah, ka zama a shirye a kullum, ko da zarafi, ko babu zarafi, ka yi gyara, ka kwaɓe, ka kuma ƙarfafa, da matuƙar haƙuri da koyarwa cikin natsuwa. 3 Gama lokaci yana zuwa da mutane ba za su jure da sahihiyar koyarwa ba. A maimako, don cimma burinsu, za su taro wa kansu malamai masu yawa, domin su faɗi abin da kunnuwansu masu ƙaiƙayi suke so su ji. 4 Za su juye kunnuwansu daga gaskiya zuwa ga jin tatsuniyoyi.

  40. 1 In wani annabi ko mai mafarkai, ya bayyana a cikinku, ya kuma yi muku shelar wata alama mai banmamaki ko al’ajabi, 2 in kuwa alamar, ko al’ajabin da annabin ya yi faɗin ya faru, ya kuma ce, “Bari mu bi waɗansu alloli (allolin da ba ku sani ba) mu kuma yi musu sujada,” 3 kada ku saurari kalmomin wannan annabi ko mai mafarki. Ubangiji Allahnku yana gwada ku ne don yă sani ko kuna ƙaunarsa da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku.

  41. 15 Hanyar wawa daidai take a gare shi,

    amma mai hikima kan saurari shawara.

  42. 2 Ku ji, ya ku mutane duka,

    ki saurara, ya ke duniya da dukan mazauna cikinki,

    bari Ubangiji Mai Iko Duka yă zama shaida a kanku,

    daga haikalinsa mai tsarki.

  43. 7 Sai wani girgije ya bayyana, ya rufe su, wata murya kuma ta fito daga girgijen, ta ce, “Wannan Ɗana ne, wanda nake ƙauna, ku saurare shi!”

  44. 29 “Ibrahim ya amsa ya ce, ‘Suna da Musa da Annabawa, ai, sai su saurare su.’

    30 “Sai ya ce, ‘A’a, ya uba, Ibrahim, in dai wani ya tashi daga matattu ya je wurinsu, za su tuba.’

    31 “Amma ya ce masa, ‘In ba su saurari Musa da Annabawa ba, kai, ko da wani ya tashi daga matattu ma, ba za su saurare shi ba.’ ”

  45. 4 Ku ji, ya Isra’ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne. 5 Ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku da dukan zuciyarku, da dukan ranku, da kuma dukan ƙarfinku. 6 Waɗannan umarnai da nake ba ku a yau, za su kasance a zukatanku. 7 Ku koya wa ’ya’yanku su da himma. Yi musu magana game da su sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya a hanya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi. 8 Ku ɗaura su su zama alamu a hannuwanku, ku kuma ɗaura su a goshinku. 9 Ku rubuta su a dogaran ƙofofin gidajenku, da ƙofofinku.

  46. 8 “Ku ji, ya mutanena, zan kuwa gargaɗe ku,

    in ba za ku saurare ni ba, ya Isra’ila!

  47. 5 Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka

    kada kuma ka dangana ga ganewarka;

    6 cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi,

    zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.

  48. 18 “Ka ji, kai kurma;

    duba, kai makaho, ka kuma gani!

    19 Wane ne makaho in ba bawana ba,

    da kuma kurma in ba ɗan aikan da na aika ba?

    Wane ne makaho kamar wanda ya miƙa kai gare ni,

    makaho kamar bawan Ubangiji?

    20 Kun ga abubuwa masu yawa, amma ba ku kula ba;

    kunnuwanku suna a buɗe, amma ba kwa jin wani abu.”

  49. 3 ‘Kira gare ni zan kuwa amsa maka in kuma faɗa maka manyan abubuwan da ba a iya kaiwa, da ba ka sani ba.’

  50. 4 Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake cewa, ‘Ba da abinci kaɗai mutum yake rayuwa ba, sai dai da kowace kalmar da take fitowa daga bakin Allah.’”

  51. 47 Zan nuna muku kwatancin mutumin da yakan zo wurina, yă ji kalmomina, yă kuma aikata. 48 Yana kama da mutumin da ya gina gida, wanda ya haƙa ƙasa da zurfi, sa’an nan ya kafa tushen ginin a kan dutse. Da ambaliyar ruwa ta taso, ƙarfin ruwa kuwa ya buga gidan, wannan bai jijjiga shi ba, domin an yi masa tushen gini na ainihi. 49 Amma wanda yakan ji kalmomina, ba ya kuma aikata su, yana kama da mutumin da ya gina gida a ƙasa, ba tare da ya kafa tushen gini ba. A sa’ad da ƙarfin ruwa ya buga gidan, sai gidan yă rushe, mummunar rushewa kuwa.”

  52. 38 Yayinda Yesu da almajiransa suna cikin tafiya, sai ya kai wani ƙauye inda wata mace mai suna Marta ta marabce shi a gidanta. 39 Tana da ’yar’uwa mai suna Maryamu, wadda ta zauna a gaban Ubangiji tana jin maganarsa. 40 Marta kuwa, aikin hidima da ya kamata a yi, ya ɗauke mata hankali, sai ta zo wurin Yesu, ta ce, “Ubangiji, ba ka damu da yadda ’yar’uwata ta bar mini aiki ni kaɗai ba? Gaya mata ta taimake ni!”

    41 Amma Ubangiji ya amsa ya ce, “Marta, Marta, hankalinki ya tashi, kuma kina damuwa a kan abubuwa da yawa. 42 Amma abu ɗaya tak ake bukata, Maryamu ta zaɓi abin da ya fi kyau, kuma ba za a raba ta da shi ba.”

  53. 16 Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami. 17 Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yă yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin yă ceci duniya ta wurinsa.

  54. 25 Gaskiya nake gaya muku, lokaci yana zuwa har ma ya riga ya zo sa’ad da matattu za su ji muryar Ɗan Allah waɗanda kuwa suka ji za su rayu.

  55. 27 Gama zuciyar mutanen nan ta yi tauri;

    da ƙyar suke ji da kunnuwansu,

    sun kuma rufe idanunsu.

    In ba haka ba za su iya gani da idanunsu,

    su ji da kunnuwansu,

    su fahimta a zukatansu,

    su kuma juyo, in kuwa warkar da su.’

  56. 4 Ubangiji Allahnku ne za ku bi, shi ne kuma za ku girmama. Ku kiyaye umarnansa, ku kuma yi masa biyayya; ku bauta masa, ku kuma manne masa.

  57. 11 Ku zo, ’ya’yana, ku saurare ni;

    zan koya muku tsoron Ubangiji.

  58. 17 Duk wanda ya mai da hankali ga horo kan nuna hanyar rai,

    amma duk wanda ya ƙyale gyara kan sa waɗansu su kauce.

  59. 14 Saboda rashin jagora al’umma takan fāɗi,

    amma masu ba da shawara da yawa kan tabbatar da nasara.

  60. 1 Ɗa mai hikima yakan mai da hankali ga umarnin mahaifinsa,

    amma mai ba’a ba ya sauraran kwaɓi.

  61. 12 Kamar ’yan kunnen zinariya ko kuwa kayan ado na zinariya zalla

    haka yake da tsawatawar mai hikima ga kunne mai saurarawa.

  62. 9 Ya ce, “Je ka ka faɗa wa wannan mutane,

    “ ‘Kome yawan kasa kunne da za ku yi, ba za ku fahimta ba;

    Kome yawan dubar da za ku yi, ba za ku san abin da yake faruwa ba.’

    10 Ka sa zuciyar mutanen nan ta dushe;

    kunnuwansu su kurunce,

    idanunsu kuma su makance.

    In ba haka ba za su iya gani da idanunsu,

    su ji da kunnuwansu,

    su fahimta da zuciyarsu,

    su kuma juyo a kuma warkar da su.”

  63. 11 “Amma suka ƙi su saurara; da taurinkai suka juya bayansu suka kuma toshe kunnuwansu. 12 Suka taurare zukatansu kamar dutse, suka ƙi jin abin da doka ko kuma maganar Ubangiji Maɗaukaki take faɗi wadda ya aika ta wurin Ruhunsa ta wurin annabawan farko. Saboda haka Ubangiji Maɗaukaki ya ji fushi ƙwarai.

  64. 30 Ni kaɗai dai ba na iya yin kome, ina shari’a ne bisa ga abin da na ji. Shari’ata kuwa mai adalci ce. Gama ba na neman gamsar da kaina, sai dai in gamshi shi wanda ya aiko ni.

  65. 13 Amma sa’ad da shi, Ruhun gaskiya ya zo, zai bi da ku zuwa ga dukan gaskiya. Ba zai yi magana don kansa ba; zai faɗi abin da ya ji ne kaɗai, zai kuma faɗa muku abin da bai faru ba tukuna.

  66. 13 Gama ba masu jin dokar ne suke da adalci a gaban Allah ba, amma waɗanda suke yin biyayya da dokar, su za a ce da su masu adalci.

  67. 9 Duk abin da kuka koya ko kuka karɓa ko kuka ji daga wurina, ko kuka gani a cikina, ku yi aiki da shi. Allah na salama kuma zai kasance tare da ku.

  68. 8 A ƙarshe, dukanku ku zauna lafiya da juna; ku zama masu juyayi, kuna ƙaunar juna kamar ’yan’uwa, ku zama masu tausayi da kuma tawali’u. 9 Kada ku rama mugunta da mugunta ko zagi da zagi, sai dai ku sa albarka, gama ga wannan ne aka kira ku, ku kuma gāji albarka. 10 Gama,

    “Duk wanda yake so yă ji daɗin rayuwa,

    yă kuma ga kwanaki masu kyau

    dole yă ƙame harshensa daga mugunta

    leɓunansa kuma daga maganar yaudara.

    11 Dole yă juye daga mugunta, ya aikata nagarta;

    dole yă nemi salama yă kuma bi ta.

    12 Gama idanun Ubangiji suna a kan masu adalci

    kunnuwansa kuma suna jin addu’arsu,

    amma fuskar Ubangiji tana gāba da masu mugunta.”

  69. 8 Zan umarce ka in kuma koyar da kai a hanyar da za ka bi;

    Zan ba ka shawara in kuma lura da kai.

    9 Kada ka zama kamar doki ko doki,

    wanda ba su da azanci

    wanda dole sai an bi da su da linzami da ragama

    in ba haka ba, ba za su zo wurinka ba.

  70. 10 Ka halitta zuciya mai tsabta a cikina, ya Allah,

    ka kuma sabunta tsayayyen ruhu a cikina.

    11 Kada ka fid da ni daga gabanka

    ko ka ɗauke Ruhunka Mai Tsarki daga gare ni.

    12 Ka mayar mini farin cikin cetonka

    ka kuma ba ni ruhun biyayya, yă riƙe ni.

    13 Ta haka zan koyar wa masu laifi hanyoyinka,

    masu zunubi kuma za su komo gare ka.

    14 Ka cece ni daga laifin jini, ya Allah,

    Allahn da ya cece ni,

    harshena kuwa zai rera adalcinka.

  71. 20 Ɗana, ka kiyaye umarnan mahaifinka

    kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.

    21 Ka ɗaura su a zuciyarka har abada;

    ka ɗaura su kewaye da wuyanka.

  72. 31 Duk wanda ya mai da hankali sa’ad da ake tsawata masa

    ba zai kasance dabam a cikin masu hikima ba.

  73. 20 Duk wanda ya mai da hankali ga umarni yakan yi nasara,

    kuma mai albarka ne wanda yake dogara ga Ubangiji.

    21 Akan ce da masu hikima a zuciya hazikai,

    kuma kalmomi masu daɗi kan inganta umarni.

    22 Fahimi shi ne maɓulɓular rai ga waɗanda suke da shi,

    amma wauta kan kawo hukunci ga wawaye.

  74. 12 Kunnuwan da suke ji da kuma idanun da suke gani,

    Ubangiji ne ya yi su duka.

  75. 35 Wata murya ta fito daga cikin girgijen, tana cewa, “Wannan Ɗana ne, zaɓaɓɓena, ku saurare shi.”

  76. 16 “Wanda ya saurare ku, ni yake saurara. Wanda ya ƙi ku, ni yake ƙi. Amma wanda ya ƙi ni kuwa, ya ƙi wanda ya aiko ni ne.”

  77. 1 “Gaskiya nake gaya muku, mutumin da bai shiga inda ake ajiye garken tumaki ta ƙofa ba, amma ya hau ta katanga, ɓarawo ne, ɗan fashi kuma. 2 Mutumin da ya shiga ta ƙofa makiyayin tumakinsa ne. 3 Mai gadin yakan buɗe wa makiyayin ƙofa, tumakin kuma sukan saurari muryarsa. Yakan kira tumakinsa da suna, yă kuma fid da su waje. 4 Sa’ad da ya fitar da dukan nasa waje, sai ya ja gabansu, tumakinsa kuma sukan bi shi domin sun san muryarsa. 5 Amma ba za su taɓa bin baƙo ba; sai dai ma su guje masa don ba su san muryar baƙo ba.”

  78. 16 Yana miƙewa tsaye, sai Bulus ya yi musu alama da hannu ya ce, “Mutanen Isra’ila da kuma ku Al’ummai da kuke wa Allah sujada, ku saurare ni!

  79. 2 Zan so in san abu guda tak daga gare ku. Kun karɓi Ruhu ta wurin kiyaye Doka ne, ko kuwa ta wurin gaskata abin da kuka ji?

  80. 8 A ƙarshe, ’yan’uwa, duk abin da yake na gaskiya, duk abin da yake na girmamawa, duk abin da yake daidai, duk abin da yake da tsarki, duk abin da yake kyakkyawa, duk abin da yake na sha’awa, in ma wani abu mafifici ne, ko ya cancanci yabo, ku yi tunani a kan irin abubuwan nan.