107 Bible Verses About Liars

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Liars
  1. 43 Me ya sa ba kwa gane da maganata? Don ba kwa iya jin abin da nake faɗi. 44 Ku na ubanku ne, Iblis, kuna kuwa so ku aikata abin da ubanku yake so. Shi mai kisankai ne tun farko. Ba ruwansa da gaskiya, gama gaskiya ba ta cikinsa. Yayinda yake ƙarya, yana yin halinsa ne, gama shi maƙaryaci ne, uban ƙarairayi kuma. 45 Amma domin ina faɗin gaskiya, ba kwa gaskata! 46 Akwai waninku da zai iya haƙaƙƙewa na taɓa yin zunubi? In kuwa gaskiya na faɗa, me ya sa ba kwa gaskata ni? 47 Wanda yake na Allah, yakan ji abin da Allah yake faɗi. Abin da ya sa ba kwa jin sa kuwa shi ne don ku ba na Allah ba ne.”

  2. 9 Kada ku yi wa juna ƙarya, da yake kun tuɓe tsohon halinku tare da ayyukansa 10 kun ɗauki sabon halin nan da ake sabuntawa ga sani, bisa ga kamannin Mahaliccinsa.

  3. 1 ’Ya’yana ƙaunatattu, ina rubuta muku wannan ne don kada ku yi zunubi. Amma in wani ya yi zunubi, muna da wani wanda yake magana da Uba don taimakonmu, wato, Yesu Kiristi, Mai Adalci. 2 Shi ne hadayar kafara saboda zunubanmu, kuma ba don namu kaɗai ba amma har ma da zunuban duniya duka.

    3 Ta haka za mu tabbata cewa mun san shi in muna yin biyayya da umarnansa. 4 Mutumin da ya ce, “Na san shi,” amma ba ya yin abin da ya umarta, maƙaryaci ne, gaskiya kuwa ba ta cikinsa. 5 Amma in wani ya yi biyayya da maganarsa, ƙaunar Allah ta zama cikakkiya ke nan a cikinsa. Ta haka muka san cewa muna cikinsa. 6 Duk wanda ya ce yana rayuwa a cikinsa dole yă yi tafiya kamar yadda Yesu ya yi.

  4. 16 Akwai abubuwa shida da Ubangiji ya ƙi,

    abubuwa bakwai da suke abin ƙyama gare shi,

    17 duban reni,

    harshe mai ƙarya,

    hannuwa masu zub da jinin marar laifi,

    18 zuciyar da take ƙulla mugayen dabaru,

    ƙafafun da suke sauri zuwa aikata mugunta,

    19 mai shaidar ƙarya wanda yake zuba ƙarairayi,

    da kuma mutumin da yake tā-da-na-zaune-tsaye a cikin ’yan’uwa.

    20 Ɗana, ka kiyaye umarnan mahaifinka

    kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.

  5. 17 To, ina dai faɗa muku, ina kuma nace faɗa muku a cikin Ubangiji, cewa kada ku ci gaba da yin rayuwa kamar yadda Al’ummai suke yi, masu banzan tunani. 18 Suna a cikin duhu a fahimtarsu, kuma a rabe suke daga ran Allah saboda jahilcin da yake cikinsu ta dalilin taurarewar zukatansu. 19 Ba sa damu da wani abu ko mai kyau ko marar kyau. Rayukansu sun cika da kowace irin ƙazanta da haɗama.

    20 Amma ba abin da aka koya muku ke nan ba sa’ad da kuka zo ga sanin Kiristi. 21 Da yake kun ji duka game da shi, kuka kuma koyi gaskiyar da take cikin Yesu, 22 sai ku tuɓe tsohon mutumin nan naku da kuma rayuwarku ta dā, wadda take lalacewa saboda sha’awace-sha’awacen da suke ruɗe ku. 23 A maimakon haka, bari Ruhu yă sabunta tunaninku da kuma halayenku. 24 Ku sanya sabon halin nan da aka halitta bisa ga kamannin Allah, halin nan kuwa, yă bayyana cikin adalci, da zaman tsarki.

    25 Saboda haka dole kowannenku yă bar yin ƙarya, yă kuma riƙa faɗa wa maƙwabcinsa gaskiya, gama dukanmu gaɓoɓi jiki ɗaya ne. 26 “Cikin fushinku kada ku yi zunubi.” Kada ku bar rana ta fāɗi kuna fushi, 27 kada kuma ku ba wa Iblis dama.

  6. 7 Da yake an danƙa wa mai kula da ikkilisiya riƙon amana saboda Allah, dole yă zama marar aibi ba mai girman kai ba, ba mai saurin fushi ba, ba mai buguwa ba, ba mai rikici ba, ba kuma mai son ƙazamar riba ba. 8 A maimakon haka dole yă zama mai karɓan baƙi, mai son abu nagari, mai kamunkai, mai adalci, mai tsarki da kuma natsattse. 9 Dole yă riƙe tabbataccen saƙon nan kam-kam yadda aka koyar, don yă iya ƙarfafa waɗansu da sahihiyar koyarwa yă kuma ƙaryata waɗanda suke gāba da shi.

    10 Gama akwai ’yan tawaye da yawa, masu surutun banza da masu ruɗi, musamman ƙungiyar masu kaciya. 11 Dole a hana su yin magana, domin suna kawo rushewar iyalai ta wurin koyar da abubuwan da bai kamata su koyar ba don neman ƙazamar riba. 12 Wani daga cikin annabawansu ma ya ce, “Kiretawa a kullum maƙaryata ne, mugayen dabbobi, ragwaye haɗamammu.” 13 Wannan shaida gaskiya ce. Saboda haka, sai ka tsawata musu sosai, don su zama sahihai a wajen bangaskiya, 14 ba za su kuma mai da hankalinsu ga tatsuniyoyin Yahudawa ko ga umarnan waɗanda suke ƙin gaskiya ba. 15 Ga tsarkaka kuwa, kome mai tsarki ne, amma ga waɗanda suke marasa tsarki da kuma marasa ba da gaskiya, ba abin da yake da tsarki. Gaskiya dai, hankulansu da lamirinsu duk marasa tsarki ne. 16 Sun ɗauka cewa sun san Allah, amma ta wurin ayyukansu suna mūsunsa. Sun zama abin ƙyama, marasa biyayya, ba su ma isa su yi aiki nagari ba.

  7. 22 Ubangiji yana ƙyamar leɓunan masu ƙarya,

    amma yana jin daɗin mutanen da suke masu gaskiya.

  8. 7 Duk wanda ya ci nasara zai gāji dukan wannan, zan kuma zama Allahnsa, shi kuma zai zama ɗana. 8 Amma matsorata, da marasa bangaskiya, masu ƙazanta, masu kisankai, masu fasikanci, masu sihiri, masu bautar gumaka da dukan maƙaryata, wurinsu zai kasance a cikin tafkin wutar da yake farar wuta mai ci. Wannan fa ita ce mutuwa ta biyu.”

  9. 1 To wani mutum mai suna Ananiyas tare da matarsa Saffiratu, shi ma ya sayar da wata mallakarsa. 2 Da cikakken sanin matarsa ya ajiye sashi daga cikin kuɗin don kansa, ya kuma kawo sauran ya ajiye a sawun manzanni.

    3 Sai Bitrus ya ce, “Ananiyas, ta yaya Shaiɗan ya cika zuciyarka haka da ka yi wa Ruhu Mai Tsarki ƙarya ka kuma ajiye wa kanka sauran kuɗin da ka karɓa na filin? 4 Ba naka ba ne kafin ka sayar da shi? Bayan da ka sayar da shi kuma, kuɗin ba naka ba ne? Me ya sa ka yi tunanin yin irin wannan abu? Ba mutum ne ka yi wa ƙarya ba, Allah ne ka yi masa.”

    5 Da Ananiyas ya ji wannan, sai ya fāɗi ya mutu. Sai babban tsoro kuwa ya kama duk waɗanda suka ji abin da ya faru.

  10. 16 Ba za ka ba da shaidar ƙarya a kan maƙwabcinka ba.

  11. 1 To, maciji dai ya fi kowane a cikin namun jejin da Ubangiji Allah ya yi wayo. Ya ce wa macen, “Tabbatacce ne Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga kowane itace a lambu’?”

    2 Macen ta ce wa macijin, “Za mu iya ci daga ’ya’ya itatuwa a lambun, 3 amma Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga ’ya’yan itacen da yake tsakiyar lambu, kada kuma ku taɓa shi, in ba haka ba kuwa za ku mutu.’ ”

    4 Maciji ya ce wa macen, “Tabbatacce ba za ku mutu ba. 5 Gama Allah ya san cewa sa’ad da kuka ci daga itacen idanunku za su buɗe, za ku kuma zama kamar Allah, ku san abin da yake mai kyau da abin da yake mugu.”

  12. 5 Duk wanda ya yi ɓatanci wa maƙwabcinsa a ɓoye

    shi za a kashe;

    duk mai renin wayo da mai girman kai,

    ba zan jure masa ba.

    6 Idanuna za su kasance a kan amintattu a cikin ƙasar,

    don su zauna tare da ni;

    tafiyarsa ba ta da zargi

    zai yi mini hidima.

    7 Babu mai ruɗun

    da zai zauna a gidana;

    babu mai ƙaryan

    da zai tsaya a gabana.

    8 Kowace safiya zan rufe bakunan

    dukan mugaye a ƙasar;

    zan yanke kowane mai aikata mugunta

    daga birnin Ubangiji.

  13. 23 Kamar kaskon da aka dalaye da azurfar da ba a tace ba

    haka leɓuna masu mugun zuciya.

    24 Mai yin ƙiyayya yakan ɓoye kansa da maganar bakinsa,

    amma a cikin zuciyarsa yana cike da munafunci

    25 Ko da jawabinsa ya ɗauki hankali, kada ka gaskata shi,

    gama abubuwa ƙyama guda bakwai sun cika zuciyarsa.

    26 Wataƙila ya ɓoye ƙiyayyarsa da ƙarya,

    duk da haka za a tone muguntarsa a cikin taro.

    27 In mutum ya haƙa rami, shi zai fāɗi a ciki;

    in mutum ya mirgino dutse, dutsen zai mirgine a kansa.

    28 Harshe mai faɗin ƙarya yana ƙin waɗanda yake ɓata musu rai,

    daɗin baki kuma yakan aikata ɓarna.

  14. 11 “ ‘Kada ku yi sata.

    “ ‘Kada ku yi ƙarya.

    “ ‘Kada ku ruɗe juna.

    12 “ ‘Kada ku rantse bisa ƙarya da sunana, ta haka har ku ƙasƙantar da sunan Allahnku. Ni ne Ubangiji.

  15. 13 Ni ne Alfa da kuma Omega, na Fari da kuma na Baya, Farko da kuma Ƙarshe.

    14 “Masu albarka ne waɗanda suka wanke tufafinsu, don su sami izinin ci daga itacen rai su kuma shiga birnin ta ƙofofi. 15 Waɗanda suke waje kuwa karnuka ne, masu sihiri, masu fasikanci, masu kisankai, masu bautar gumaka, da duk wanda yake ƙaunar ƙarya yake kuma aikata ta.

  16. 4 Kai ba Allahn da yake jin daɗin mugu ba ne;

    gama kana gāba da dukan masu aikata mugunta.

    5 Masu fariya ba za su iya tsaya

    a gabanka ba.

    Kana ƙin duk masu aikata abin da ba daidai ba.

    6 Kakan hallaka masu yin ƙarya.

    Masu kisankai da mutane masu ruɗu

    Ubangiji yana ƙyama.

  17. 9 Mai shaidar ƙarya ba zai tafi babu hukunci ba,

    kuma duk mai baza ƙarairayi zai hallaka.

  18. 1 Ruhu a sarari ya faɗa cewa a kwanakin ƙarshe waɗansu za su watsar da bangaskiya su bi ruhohi masu ruɗu da kuma abubuwan da aljanu suke koyarwa. 2 Irin koyarwan nan tana zuwa ne daga waɗansu munafukai maƙaryata, waɗanda aka yi wa lamirinsu kaca-kaca.

  19. 8 Mun san cewa doka tana da kyau in an yi amfani da ita yadda ya kamata. 9 Mun kuma san cewa an yi doka ba domin masu adalci ba sai dai masu tawaye, da marasa biyayya, da marasa bin Allah, da masu zunubi, da marasa tsarkaka, da masu saɓon Allah, da masu kashe iyaye maza da mata, da masu kisankai, 10 da masu zina da kuma da maza masu kwana da maza, ko mata masu kwana da mata, da masu cinikin bayi da masu ƙarya da kuma masu shaidar ƙarya, da kuma duk wani abin da ya saɓa wa sahihiyar koyarwa, 11 da take bisa ga bishara mai ɗaukaka ta Allah mai albarka, wadda ya danƙa mini.

  20. 27 Babu wani abu marar tsarkin da zai taɓa shiga cikin birnin, babu kuma wani mai aikata abin kunya ko ruɗi da zai shiga, sai dai waɗanda aka rubuta sunayensu a cikin littafin rai na Ɗan Ragon.

  21. 1 Da ma kaina maɓulɓulan ruwa ne

    idanuna kuma maɓulɓulan hawaye!

    Da sai in yi kuka dare da rana

    saboda mutanena da aka kashe.

    2 Da ma a hamada

    ina da wurin da matafiye za su sauka,

    don in bar mutanena

    in tafi in bar su;

    gama dukansu mazinata ne,

    taron mutane marasa aminci.

    3 “Sun tanƙwasa harshensu

    kamar baka, don su harba ƙarya;

    ba da gaskiya ba ne

    suke nasara a cikin ƙasar.

    Sukan tashi daga wannan zunubi zuwa wancan;

    ba su san ni ba,”

    in ji Ubangiji.

    4 “Ka yi hankali da abokanka;

    kada ka amince da ’yan’uwanka.

    Gama kowane ɗan’uwa munafuki ne,

    kowane aboki kuma mai kushe ne.

    5 Aboki kan ruɗi aboki,

    ba mai faɗar gaskiya.

    Sun koya wa harshensu faɗar ƙarya;

    sun gajiyar da kansu da yin zunubi.

    6 Kai kana zama a tsakiyar ruɗu;

    cikin ruɗunsu sun ƙi su san ni,”

    in ji Ubangiji.

    7 Saboda haka ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa,

    “Ga shi zan tace in kuma gwada su,

    gama me kuwa zan yi

    saboda zunubin mutanena?

    8 Harshensu kibiya ce mai dafi;

    yana magana da ruɗu.

    Da bakinsa kowa yana maganar alheri da maƙwabcinsa,

    amma a zuciyarsa ya sa masa tarko.

    9 Bai kamata in hukunta su saboda wannan ba?”

    In ji Ubangiji.

    “Bai kamata in ɗau fansa

    a kan irin al’umma kamar wannan ba?”

  22. 8 In muka ce ba mu da zunubi, muna ruɗin kanmu ne, gaskiya kuwa ba ta cikinmu. 9 In muka furta zunubanmu, shi mai aminci ne, mai adalci kuma, zai gafarta mana zunubanmu, yă kuma tsarkake mu daga dukan rashin adalci. 10 In muka ce ba mu yi zunubi ba, mun mai da shi maƙaryaci ke nan, maganarsa kuwa ba ta da wuri a cikinmu.

  23. 19 Allah ba mutum ba ne, da zai yi ƙarya,

    shi ba ɗan mutum ba ne, da zai canja tunaninsa.

    Yana maganar abin da ba zai iya aikata ba ne?

    Yakan kuma yi alkawarin da ba zai iya cikawa ba?

  24. 1 Tabbatacce hannun Ubangiji bai kāsa yin ceto ba,

    kunnensa kuma bai kurmance da zai kāsa ji ba.

    2 Amma laifofinku sun raba

    ku da Allahnku;

    zunubanku sun ɓoye fuskarsa daga gare ku,

    saboda kada yă ji.

    3 Gama hannuwanku sun ƙazantu da jini,

    yatsotsinku kuma da alhaki.

    Leɓunanku suna faɗin ƙarairayi,

    harshenku kuma yana raɗar mugayen abubuwa.

    4 Babu wani mai ce a yi adalci;

    babu wani mai nema a dubi al’amarinsa da mutunci.

    Sun dogara a gardandamin banza suna ƙarairayi;

    suna ɗaukar cikin ɓarna, su haifi mugunta.

  25. 19 Leɓunan gaskiya kan dawwama har abada,

    amma harshen ƙarya yakan dawwama na ɗan lokaci ne kawai.

    20 Akwai ruɗu a zukatan waɗanda suke ƙulla mugunta,

    amma waɗanda suke aikata alheri za su yi farin ciki.

  26. 5 Adali yana ƙin abin da yake ƙarya,

    amma mugu kan jawo kunya da ƙasƙanci.

  27. 5 “Kowace maganar Allah ba ta da kuskure;

    shi ne garkuwa ga waɗanda suke neman mafaka daga gare shi.

    6 Kada ka ƙara ga maganarsa,

    in ba haka ba zai tsawata maka ya kuma nuna kai maƙaryaci ne.

  28. 21 Saboda haka Gehazi ya bi Na’aman a guje. Da Na’aman ya hango shi yana zuwa a guje, sai ya sauka daga keken yaƙinsa ya tarye shi ya ce, “Lafiya?”

    22 Gehazi ya amsa ya ce, “Lafiya ƙalau. Maigidana ne ya aiko ni cewa, ‘Samari biyu daga ƙungiyar annabawa sun ziyarce ni daga ƙasa mai duwatsu na yankin Efraim. Ina roƙonka ka ba su talenti na azurfa da tufafi kashi biyu.’ ”

    23 Na’aman ya ce, “Ba damuwa, karɓi talenti biyu.” Ya roƙi Gehazi yă karɓa, sa’an nan ya ƙunsa masa talentin biyu na azurfa ya sa masa a kan jakankuna biyu, ya haɗa da tufafi kashi biyu, ya ba bayinsa biyu suka ɗauka, ya ce su sha gaban Gehazi. 24 Da Gehazi ya isa wani tudu, sai ya karɓi kayan daga wurin bayin ya shiga da su a ɓoye a cikin gida. Sa’an nan ya sallami mutanen suka tafi. 25 Sa’an nan ya shiga ya tsaya a gaban maigidansa Elisha.

    Sai Elisha ya tambaye shi ya ce, “Ina ka je, Gehazi?”

    Sai Gehazi ya amsa ya ce, “Bawanka bai je ko’ina ba.”

    26 Amma Elisha ya ce masa, “Ashe, ba ina tare da kai a ruhu ba sa’ad da mutumin ya sauko daga keken yaƙinsa ya tarye ka. Kana gani wannan lokaci ne da za a karɓi kuɗi, da riguna, da gonar inabi, da tumaki, da bijimai, da bayi maza da mata? 27 Kuturtar Na’aman zai manne maka da zuriyarka har abada.” Sai Gehazi ya fita daga gaban Elisha a kuturce, fari fat kamar dusar ƙanƙara.

  29. 11 Ku zo, ’ya’yana, ku saurare ni;

    zan koya muku tsoron Ubangiji.

    12 Duk waninku da yake ƙaunar rayuwa

    yana kuma so yă ga kwanaki masu kyau,

    13 ka kiyaye harshenka daga mugunta

    da kuma leɓunanku daga faɗar ƙarairayi.

    14 Juyo daga mugunta ku yi alheri;

    nemi salama ku kuma yi ƙoƙarin samunta.

    15 Idanun Ubangiji suna a kan masu adalci

    kuma kunnuwansa suna sauraran kukansu;

  30. 10 Gama,

    “Duk wanda yake so yă ji daɗin rayuwa,

    yă kuma ga kwanaki masu kyau

    dole yă ƙame harshensa daga mugunta

    leɓunansa kuma daga maganar yaudara.

    11 Dole yă juye daga mugunta, ya aikata nagarta;

    dole yă nemi salama yă kuma bi ta.

    12 Gama idanun Ubangiji suna a kan masu adalci

    kunnuwansa kuma suna jin addu’arsu,

    amma fuskar Ubangiji tana gāba da masu mugunta.”

  31. 5 Mashaidi na gaskiya ba ya ruɗu,

    amma mashaidin ƙarya kan baza ƙarairayi.

  32. 1 Ku ji maganar Ubangiji, ku Isra’ilawa,

    gama Ubangiji yana da tuhumar da zai kawo

    a kan ku waɗanda suke zama a ƙasar.

    “Babu aminci, babu ƙauna,

    babu yarda da Allah a cikin ƙasar.

    2 Akwai la’ana ce kawai, yin ƙarya da kisa,

    yin sata da zina;

    sun wuce gona da iri,

    kisankai a kan kisankai.

    3 Saboda wannan ƙasar tana makoki,

    kuma dukan waɗanda suke zama a cikinta sun lalace;

    namun jeji da tsuntsayen sararin sama

    da kuma kifin teku suna mutuwa.

  33. 11 Yayinda yana gab da shiga Masar, sai ya ce wa matarsa Saira, “Na sani ke kyakkyawar mace ce. 12 Sa’ad da Masarawa suka ganki, za su ce, ‘Wannan matarsa ce.’ Za su kuwa kashe ni, su bar ki da rai. 13 Saboda haka ki ce ke ’yar’uwata ce, domin ta dalilinki a mutunta ni, a kuma bar ni da rai.”

  34. 20 Kada ka ba da shaidar ƙarya a kan maƙwabcinka.

  35. 19 Mikahiya ya ci gaba, “Saboda haka ka ji maganar Ubangiji. I, na ga Ubangiji zaune a kursiyinsa tare da dukan rundunar sama tsaye kewaye da shi a dama da hagunsa. 20 Kuma Ubangiji ya ce, ‘Wa zai ruɗi Ahab zuwa yaƙi da Ramot Gileyad, yă kuma kai shi mutuwarsa a can?’

    “Wani ya ce wannan, wani ya ce wancan. 21 A ƙarshe, wani ruhu ya zo gaba, ya tsaya a gaban Ubangiji ya ce, ‘Zan ruɗe shi.’

    22 “Ubangiji ya yi tambaya ‘Ta wace hanya?’ Ya ce,

    “ ‘Zan tafi in zama ruhun ƙarya a bakunan dukan annabawansa.’

    “Ubangiji ya ce, ‘Za ka yi nasara a ruɗinsa. Ka tafi, ka yi haka.’

    23 “Saboda haka yanzu Ubangiji ya sa ruhun ƙarya a bakunan dukan annabawanka. Ubangiji ya zartar maka da masifa.”

  36. 3 Kai, tun haihuwa mugaye sukan kauce;

    daga cikin ciki, su lalatattu ne maƙaryata.

  37. 18 Amma abubuwan da suke fitowa ta baki suna fitowa ne daga zuciya, su ne kuma suke ƙazantar da mutum. 19 Gama daga zuciya ne mugayen tunani, kisankai, zina, fasikanci, sata, shaidar ƙarya, ɓatan suna, suka fitowa. 20 Waɗannan su ne suke ƙazantar da mutum; amma cin abinci ba tare da wanke hannuwa ba, ba ya ƙazantar da mutum.”

  38. 9 Zuwan mai tawayen nan zai zama ta wurin aikin Shaiɗan da aka bayyana cikin kowane irin ayyukan banmamaki, alamu da abubuwan banmamaki na ƙarya, 10 da kuma cikin kowace irin muguntar da take ruɗin waɗanda suke hallaka. Sun hallaka ne domin sun ƙi su ƙaunaci gaskiya don su sami ceto. 11 Saboda haka Allah zai aiko musu da babban ruɗu don su gaskata ƙarya 12 don kuma a hukunta dukan waɗanda ba su gaskata gaskiyar ba sai dai suke jin daɗin mugunta.

  39. 5 Mai ba da shaidar ƙarya ba zai tafi babu hukunci ba,

    kuma duk wanda ya baza ƙarairayi ba zai kuɓuta ba.

  40. 9 Sai Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Ina ɗan’uwanka Habila?”

    Sai Kayinu ya ce, “Ban sani ba, ni mai gadin ɗan’uwana ne?”

  41. 18 Shi kuwa ya tafi wurin mahaifinsa ya ce, “Babana.”

    Shi kuma ya amsa “I, ɗana, wane ne?”

    19 Yaƙub ya ce wa mahaifinsa, “Ni ne Isuwa ɗan farinka. Na yi yadda ka faɗa mini. Ina roƙonka tashi ka zauna ka ci naman, domin ka sa mini albarkarka.”

  42. 3 Amma a ce waɗansu ba su da bangaskiya fa? Rashin bangaskiyarsu nan zai shafe amincin Allah? 4 Ko kaɗan! Bari Allah yă zama mai gaskiya, kowane mutum kuma yă zama maƙaryaci. Kamar yadda yake a rubuce cewa,

    “Gama a tabbatar kana da gaskiya, sa’ad da ka yi magana,

    ka kuma yi nasara sa’ad da ka yi shari’a.”

  43. 16 In mutane za su yi rantsuwa sukan yi haka da wanda ya fi su ne, rantsuwar kuwa takan tabbatar da abin da aka faɗa ta kuma kawo ƙarshen dukan gardama. 17 Saboda haka da Allah ya so yă bayyana nufinsa marar canjawa a sarari ga magādan abin da aka yi alkawari, sai ya tabbatar da shi da rantsuwa. 18 Allah ba ya karya! Haka ma alkawuransa da rantsuwarsa abubuwa biyu ne da ba a iya canjawa. Mun gudu zuwa wurin Allah domin kāriya. Ya kamata alkawuransa su ƙarfafawa sosai mu riƙe begen nan da yake gabanmu.

  44. 6 Dukiyar da aka samu ta wurin harshe mai yin ƙarya

    tarin tururi ne da kuma mugun tarko.

  45. 9 Zuciya ta fi kome ruɗu

    ta fi ƙarfin warkewa.

    Wa zai iya gane ta?

    10 “Ni Ubangiji nakan bincike zuciya

    in gwada tunani,

    don in sāka wa kowane mutum bisa ga halinsa,

    bisa ga ayyukansa.”

  46. 1 Kaiton birni mai zub da jini,

    wadda take cike da ƙarairayi,

    cike da ganima,

    wadda ba a rasa masu fāɗawa cikin wahala!

  47. 6 Yesu ya amsa ya ce, “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai dai ta wurina.

  48. 6 Sai Ishaku ya zauna a Gerar.

    7 Sa’ad da mutanen wurin suka tambaye shi game da matarsa, sai ya ce, “’Yar’uwata ce,” gama yana tsoro yă ce, “Ita matata ce.” Ya yi tunani, “Mutane wannan wuri za su kashe ni ta dalili Rebeka, domin kyakkyawa ce.”

    8 Sa’ad da Ishaku ya daɗe a can, sai Abimelek sarkin Filistiyawa ya duba daga taga ya ga Ishaku yana rungumar matarsa Rebeka. 9 Saboda haka Abimelek ya aika Ishaku yă je, sa’an nan ya ce, “Tabbatacce ita matarka ce! Me ya sa ka ce, ‘Ita ’yar’uwata ce?’ ”

    Ishaku ya amsa masa ya ce, “Don na yi tsammani zan rasa raina saboda ita.”

    10 Sa’an nan Abimelek ya ce, “Me ke nan ka yi mana? Da a ce wani daga mazanmu ya kwana da matarka, ai, da ka jawo laifi a kanmu.”

    11 Saboda haka Abimelek ya yi umarni ga dukan mutane. “Duk wanda ya fitine wannan mutum ko matarsa, tabbatacce za a kashe shi.”

  49. 2 Harshenka kan shirya hallaka;

    yana nan kamar reza mai ci,

    kana ta ruɗu.

    3 Kana ƙaunar mugunta fiye da alheri,

    ƙarya a maimakon faɗin gaskiya. Sela

    4 Kana ƙaunar kowace kalmar cutarwa,

    Ya kai harshe mai ruɗu!

    5 Tabbatacce Allah zai kai ka ga madawwamiyar hallaka.

    Zai fizge ka yă yayyage ka daga tentinka;

    zai tumɓuke ka daga ƙasar masu rai. Sela

  50. 163 Na ƙi ina kuma ƙyamar ƙarya

    amma ina ƙaunar dokarka.

  51. 4 Mugun mutum kan mai da hankali ga mugayen leɓuna;

    maƙaryaci yakan kasa kunne ga harshen ƙarairayi.

  52. 7 Leɓunan basira ba su dace da wawa ba,

    ya ma fi muni a ce mai mulki yana da leɓunan ƙarya!

  53. 22 Abin da mutum yake sha’awa shi ne ƙauna marar ƙarewa;

    gara ka zama matalauci da ka zama maƙaryaci.

  54. 20 Duk mai aikata mugunta yana ƙin haske, ba zai kuwa zo cikin haske ba don yana tsoro kada ayyukansa su tonu. 21 Amma duk mai rayuwa bisa ga gaskiya yakan zo cikin haske, domin a gani a sarari cewa ayyukan da ya yi an yi su ne ta wurin Allah.

  55. 8 To, Istifanus, mutum cike da alheri da ikon Allah, ya aikata manyan ayyukan da alamu masu banmamaki a cikin mutane. 9 Sai hamayya ta taso daga ’yan ƙungiyar Majami’a na ’Yantattu (kamar yadda ake kiransu), Yahudawan Sairin da Alekzandariya da kuma lardunan Silisiya da Asiya. Mutanen nan suka fara muhawwara da Istifanus, 10 amma ba su iya cin nasara kan hikimarsa ko kuma a kan Ruhu wanda ta wurinsa ne ya magana ba.

    11 Sa’an nan a asirce suka zuga waɗansu mutane su ce, “Mun ji Istifanus ya faɗa kalmomin saɓo game da Musa da kuma Allah.”

    12 Ta haka suka tā da hankalin mutane da dattawa da kuma malaman dokoki. Suka kama Istifanus suka kawo shi a gaban Majalisa. 13 Suka kawo masu ba da shaidar ƙarya, waɗanda suka ba da shaida cewa, “Wannan mutum ba ya rabuwa da maganar banza a kan wurin nan mai tsarki da kuma doka.

  56. 13 Gama irin waɗannan mutane manzannin ƙarya ne, ma’aikata ne masu ruɗi, sun ɓad da kamanni kamar su manzannin Kiristi ne. 14 Ba abin mamaki ba ne, gama Shaiɗan kansa ma yana ɓad da kamanni kamar shi mala’ikan haske ne. 15 Don haka, ba abin mamaki ba ne, in bayin Shaiɗan sun ɓad da kamanni kamar su bayin adalci ne. A ƙarshe, za a sāka musu gwargwadon ayyukansu.

  57. 31 Sai suka ɗauki rigar Yusuf, suka yanka akuya suka tsoma rigar a cikin jinin. 32 Suka ɗauki rigan nan mai gwanin kyau, suka kawo wa mahaifinsu suka ce, “Mun sami wannan. Ka bincika shi ka gani ko rigar ɗanka ne.”

    33 Ya gane shi, sai ya ce, “Rigar ɗana ne! Waɗansu mugayen namun jeji sun cinye shi. Tabbatacce an yayyaga Yusuf.”

    34 Sa’an nan Yaƙub ya kyakkece tufafinsa, ya sa tufafin makoki, ya kuma yi makoki domin ɗansa kwanaki masu yawa. 35 Dukan ’ya’yansa maza da mata, suka zo don su ta’azantar da shi, amma ya ƙi yă ta’azantu. Ya ce, “A’a, cikin makoki zan gangara zuwa kabari wurin ɗana.” Saboda haka, mahaifin Yusuf ya yi kuka saboda shi.

  58. 15 Sai Sarkin Masar ya gaya wa ungozomomin matan Ibraniyawa, wato, su Shofra da Fuwa ya ce, 16 “Sa’ad da kuke taimakon matan Ibraniyawa lokacin haihuwa, in jaririn namiji ne ku kashe shi, amma in ta mace ce, ku bar ta da rai.” 17 Amma ungozomomin nan masu tsoron Allah ne, ba su kuwa aikata abin da sarkin Masar ya gaya musu ba; suka bar jarirai maza su rayu. 18 Sai sarkin Masar ya kira ungozomomin, ya tambaye su ya ce, “Don me kuka yi haka? Don me kuka bar jarirai maza su rayu?”

    19 Ungozoman suka amsa wa Fir’auna suka ce, “Ai, matan Ibraniyawa ba kamar matan Masarawa ba ne, gwarzaye ne, sukan haihu kafin ungozomomin su kai wurinsu.”

    20 Saboda haka Allah ya nuna alheri wa ungozomomin, Isra’ilawa kuwa suka yi yawa fiye da dā. 21 Saboda ungozomomin suna tsoron Allah, sai Allah ya ba su iyalan kansu.

  59. 1 “Kada ku baza rahoton ƙarya. Kada kuma ku haɗa baki da mugayen mutane har da ku zama munafukai ta wurin ba da shaidar ƙarya.

    2 “Kada ku yi abin da ba daidai ba, don galibin mutane suna yin haka. Sa’ad da kuke ba da shaida a gaban shari’a, kada ku ba da shaidar ƙarya a kauce wa gaskiya don ku faranta wa taron jama’a rai.

  60. 15 Shaidar mutum guda ba tă isa a tabbatar cewa mutum yana da laifi game da laifin da ake tuhumarsa ba, ko kuwa a kan wani laifin da ake zaginsa da aikata ba. Dole a tabbata da batun ta bakin shaidu biyu, ko uku.

    16 In wani ɗan sharri ya tashi ya yi wa wani sharri, don a sami wani da laifi, 17 dole mutanen nan biyu da suke rikici su tsaya a gaban Ubangiji, a gaban firistoci da alƙalai waɗanda suke aiki a lokacin. 18 Dole alƙalan su yi bincike sosai, in kuma aka tabbatar mai ba da shaida maƙaryaci ne, yana ba da shaidar zur a kan ɗan’uwansa ne, 19 to, sai a yi da shi yadda ya yi niyya yă yi da ɗan’uwansa. Dole ku fid da mugu daga cikinku. 20 Sauran mutane za su ji wannan su kuma ji tsoro, ba kuwa za a ƙara yin irin wannan mugun abu a cikinku ba. 21 Kada ku ji tausayi, rai yă zama a maimakon rai, ido a maimakon ido, haƙori a maimakon haƙori, hannu a maimakon hannu, ƙafa a maimakon ƙafa.

  61. 32 Tabbatacce, ina gāba da waɗannan da suke annabci mafarkan karya,” in ji Ubangiji. “Suna faɗarsu suna ɓad da mutanena da ƙarairayinsu na rashin hankali, duk da haka ban aike su ba, ban kuwa umarce su ba. Ba su amfani wannan mutane ba ko kaɗan,” in ji Ubangiji.

  62. 16 Abubuwan da za ku yi ke nan. Ku gaya wa juna gaskiya, ku kuma dinga yin shari’ar gaskiya a ɗakunanku na shari’arku; 17 kada ku ƙulla wa maƙwabtanku mugunta, kuma kada ku so yin rantsuwa ta ƙarya. Ina ƙyamar waɗannan duka,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.

  63. 13 Wane ne mai hikima da fahimta a cikinku? Bari yă nuna ta ta wurin rayuwarsa mai kyau, ta wurin ayyukan da aka yi cikin tawali’un da suke fitowa daga hikima. 14 Amma in kuna cike da mugun kishi da kuma sonkai a cikin zukatanku, kada ku yi taƙama game da wannan, ko ku danne gaskiya. 15 Irin wannan “hikima” ba daga sama ta sauko ba, ta duniya ce, ta rashin ruhaniya, ta Iblis kuma. 16 Gama inda akwai kishi da sonkai, a can za a tarar da hargitsi da kowane irin mugun aiki.

    17 Amma hikimar da ta zo daga sama da fari tana da tsabta gaba ɗaya; sa’an nan mai ƙaunar salama ce, mai sanin ya kamata, mai biyayya, cike da jinƙai da aiki mai kyau, marar nuna bambanci, sahihiya kuma. 18 Masu salama da suke shuki cikin salama sukan girbe adalci.

  64. 18 Duk wanda ya ɓoye ƙiyayyarsa yana da ƙarya a leɓunansa,

    duk kuma wanda yake baza ƙarairayi wawa ne.

  65. 14 Sai Ubangiji ya ce mini, “Annabawa suna ta annabcin ƙarya da sunana. Ban aike su ba, ban kuma naɗa su ba, ban yi musu magana ba. Suna muku annabci wahayin ƙarya, suna muku duba marar amfani, suna bautar gumaka suna kuma bayyana tunanin kansu ne. 15 Saboda haka, ga abin da Ubangiji ya ce game da annabawan da suke annabci da sunana. Ban aike su ba, duk da haka suna cewa, ‘Babu takobi ko yunwar da zai taɓa wannan ƙasa.’ Waɗannan annabawa takobi da yunwa za su hallaka su.

  66. 20 Ya ci gaba, “Abin da yake fitowa daga mutum ne yake ƙazantar da shi. 21 Gama daga ciki, daga zuciyar mutane, mugayen tunani suke fitowa, fasikanci, sata, kisankai, zina, 22 kwaɗayi, ƙeta, ruɗu, ƙazantaccen sha’awa, kishi, ɓata suna, girman kai da kuma wauta. 23 Duk waɗannan mugayen abubuwa daga cikin suke fitowa, suna kuma ƙazantar da mutum.”

  67. 31 Sai Yesu ya ce wa Yahudawan da suka gaskata da shi, “In dai kun riƙe koyarwata, ku almajiraina ne da gaske. 32 Sa’an nan za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za tă ’yantar da ku.”

  68. 10 A ƙarshe, bari ƙarfin ikon Ubangiji yă ba ku ƙarfi. 11 Ku yafa dukan kayan yaƙin da Allah yake bayarwa, don ku iya kāre kanku daga dabarun Shaiɗan. 12 Gama ba da mutane da suke nama da jini ne muke yaƙi ba. Muna yaƙi ne da ikoki, da hukumomi, da masu mulkin duhu, da kuma a ikokin da suke cikin a sararin sama. 13 Saboda haka sai ku yafa dukan kayan yaƙi na Allah, domin sa’ad da ranar mugun nan ta zo, ku iya yin tsayin daka, bayan kuma kuka gama kome, ku dāge. 14 Saboda haka fa ku dāge, ku sa gaskiya tă zama ɗamararku, adalci yă zama sulkenku, 15 shirin kai bisharar salama yă zama kamar takalmi a ƙafafunku. 16 Ban da waɗannan kuma, ku ɗauki garkuwar bangaskiya, wadda za ku iya kashe dukan kibiyoyin wutar Mugun nan da ita. 17 Ku kuma ɗauki hular kwano na ceto, da takobin Ruhu, wato, Maganar Allah.

  69. 12 Saboda haka Saratu ta yi dariya da ta yi tunani a zuci tana cewa, “Bayan ƙarfina ya ƙare, maigidana kuma ya tsufa, yanzu zan sami wannan jin daɗi?”

    13 Sai Ubangiji ya ce wa Ibrahim, “Me ya ba Saratu dariya har da ta ce, ‘Har zan iya haifi ɗa duk ta tsufata yanzu?’ 14 Akwai abin zai gagari Ubangiji? Zan komo wurinka a ƙayyadadden lokacin nan shekara mai zuwa kuma Saratu za tă haifi ɗa.”

    15 Saratu ta ji tsoro, don haka sai ta yi ƙarya ta ce, “Ban yi dariya ba.”

    Ya ce, “A’a, kin yi dariya.”

  70. 29 Shi wanda yake Ɗaukakar Isra’ila ba ya ƙarya ko yă canja zuciyarsa, gama shi ba mutum ba ne da zai canja zuciyarsa.”

  71. 2 Har yaushe, ya ku mutane za ku mai da ɗaukakata abin kunya?

    Har yaushe za ku ƙaunaci ruɗu ku nemi allolin ƙarya? Sela

  72. 29 Ka kiyaye ni daga hanyoyin ruɗu;

    ka yi mini alheri ta wurin dokokinka.

    30 Na zaɓi hanyar gaskiya;

    na sa zuciyata a kan dokokinka.

  73. 25 Mashaidin gaskiya kan ceci rayuka,

    amma mashaidin ƙarya mai ruɗu ne.

  74. 13 Raguwar Isra’ila ba za su ƙara aikata abin da ba daidai ba,

    ba za su faɗa ƙarya ba,

    ba kuwa za a sami ruɗu a bakunansu ba.

    Za su ci su kuma kwanta

    kuma babu wanda zai ba su tsoro.”

  75. 29 Kada wata ƙazamar magana ta fita daga bakunanku, sai dai abin da yake da amfani don gina waɗansu bisa ga bukatunsu. Ta haka maganarku za tă zama da amfani ga masu jinta. 30 Kada kuma ku ɓata wa Ruhu Mai Tsarki na Allah rai, wanda da shi aka hatimce ku da shi don ranar fansa. 31 Ku rabu da kowane irin ɗacin rai, haushi da hasala, faɗa da ɓata suna, ku rabu da kowace irin ƙeta. 32 Ku yi alheri, ku kuma ji tausayin juna, kuna gafarta wa juna, kamar yadda a cikin Kiristi, Allah ya gafarta muku.

  76. 2 Na san ayyukanka, faman aikinka da daurewarka. Na san cewa ba ka iya haƙuri da mugayen mutane, ka gwada waɗanda suke cewa su manzanni ne, alhali kuwa ba haka ba ne, ka kuwa tarar cewa su na ƙarya ne.

  77. Zabura ta Dawuda.

    1 Ubangiji, wa zai zauna cikin wuri mai tsarkinka?

    Wa zai zauna a kan tudunka mai tsarki?

    2 Sai wanda ba shi da laifi

    kuma yana yin abin da yake daidai,

    wanda yake faɗin gaskiya daga zuciyarsa

    3 ba ya kuwa ɓata sunan wani da harshensa,

    wanda ba ya yi wa maƙwabcinsa mugunta

    ba ya kuwa baza jita-jita a kan ɗan’uwansa,

    4 wanda yake ƙin mugun mutum

    amma yakan girmama masu tsoron Ubangiji,

    yakan cika alkawarinsa

    ko da ma ya zafe shi,

    5 wanda yake ba da rance ba tare da ruwa ba

    kuma ba ya karɓan cin hanci don yă kā da marar laifi.

    Shi wanda yake yin waɗannan abubuwa

    ba zai taɓa jijjiguwa ba.

  78. 11 Kuma cikin rikicewana na ce,

    “Dukan mutane maƙaryata ne.”

  79. 2 Ka cece ni, ya Ubangiji,

    daga leɓuna masu ƙarya

    da kuma daga harsuna masu yaudara.

  80. 7 Matakan mazambaci mugaye ne,

    yana ƙulla mugayen shirye-shirye

    don yă hallaka talakawa da ƙarairayi,

    ko sa’ad da roƙon mai bukata da gaskiya ne.

  81. 22 Ko da yake sun ɗauka su masu hikima ne, sai suka zama wawaye, 23 suka kuma yi musayar ɗaukakar Allah marar mutuwa da siffofin da aka ƙera su yi kama da mutum mai mutuwa da tsuntsaye da dabbobi da kuma halittu masu ja da ciki.

    24 Saboda haka Allah ya yashe su ga mugayen sha’awace-sha’awacen zukatansu ga fasikanci don a ƙasƙantar da jikunansu ga yin abin kunya. 25 Sun sauya gaskiyar Allah da ƙarya, suka kuma yi wa abubuwan da aka halitta sujada suna bauta musu a maimakon Mahalicci, wanda ake yabo har abada. Amin.

  82. 12 Labudda, duk masu niyyar zaman tsarkaka, suna na Kiristi Yesu, za su sha tsanani. 13 Mugayen mutane da masu ruɗi kuwa, ƙara muni za su riƙa yi, suna yaudara, ana kuma yaudararsu. 14 Amma kai kam, ka ci gaba da abin da ka koya ka kuma tabbatar, gama ka san waɗanda ka koye su daga gare su, 15 da kuma yadda tun kana ɗan jinjiri ka san Nassosi masu tsarki, waɗanda suke iya sa ka zama mai hikima zuwa ceto ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu. 16 Dukan Nassi numfashin Allah ne yana kuma da amfani don koyarwa, tsawatarwa, gyara da kuma horarwa cikin adalci, 17 domin mutumin Allah yă zama shiryayye sosai saboda kowane kyakkyawan aiki.

  83. 1 Amma a dā akwai annabawan ƙarya a cikin mutane, kamar yadda za a sami malaman ƙarya a cikinku. A ɓoye za su shigar da karkataccen koyarwa mai hallaka, har ma su yi mūsun Ubangiji mai iko duka wanda ya saye su suna kawo wa kansu hallaka farat ɗaya. 2 Da yawa za su bi hanyoyinsu na rashin kunya su kuma sa a rena hanyar gaskiya. 3 Cikin kwaɗayinsu waɗannan malaman ƙarya za su cuce ku da tatsuniyoyin da suka ƙaga. Hukuncinsu yana a rataye a kansu tun da daɗewa, hallakarsu kuma ba ta barci.

  84. 23 Amma kai, ya Allah, za ka kawar da mugaye

    zuwa cikin ramin lalacewa;

    masu kisa da mutane masu ruɗu

    ba za su kai rabin kwanakin rayuwarsu ba.

    Amma ni dai, na dogara gare ka.

  85. 28 Kada ka ba da shaida a kan maƙwabcinka ba tare da isashen dalili ba,

    ko ka yi amfani da leɓunanka ka yi ruɗu.

  86. 18 Kamar sanda ko takobi ko kibiya mai tsini

    haka yake da mutumin da yake ba da shaidar ƙarya a kan maƙwabcinsa.

  87. 11 “Masu albarka ne ku, sa’ad da mutane suke zaginku, suna tsananta muku, suna kuma faɗin kowace irin muguwar magana a kanku saboda ni. 12 Ku yi murna ku kuma yi farin ciki, domin ladarku mai yawa ne a sama, gama haka suka tsananta wa annabawan da suka riga ku.

  88. 59 Sai manyan firistoci da ’yan majalisa duka suka yi ta neman shaidar ƙarya a kan Yesu, don su sami dama su kashe shi. 60 Amma ba su sami ko ɗaya ba, ko da yake masu shaidar ƙarya da yawa sun firfito.

    A ƙarshe, biyu suka zo gaba, 61 suka furta cewa, “Wannan mutum ya ce, ‘Ina iya rushe haikalin Allah, in sāke gina shi cikin kwana uku.’ ”

  89. 55 Ko da yake ba ku san shi ba, ni dai na san shi. In kuwa na ce ban san shi ba, na zama maƙaryaci kamar ku ke nan, amma na san shi, kuma ina kiyaye maganarsa.

  90. 8 In haka ne, “Ba sai mu yi ta yin mugunta don yă zama hanyar samun nagarta ba”? Kamar yadda masu baƙar magana game da mu suna cewa wai haka muke faɗa. Tabbatacce za a hukunta irin waɗannan da hukuncin da ya dace da su.

  91. 20 Duk wanda ya ce, “Ina ƙaunar Allah,” amma yana ƙin ɗan’uwansa, maƙaryaci ne. Gama duk wanda ba ya ƙaunar ɗan’uwansa da yake gani, ba zai iya ƙaunar Allah wanda ba ya gani ba.

  92. 7 Sa’ad da shekaru dubun nan suka cika, za a saki Shaiɗan daga kurkukun da yake, 8 zai kuma fito don yă ruɗi al’ummai da suke a kursuyoyi huɗu na duniya, Gog da Magog, yă tattara su don yaƙi. Yawansu kuwa ya yi kamar yashi a bakin teku. 9 Suka mamaye duk fāɗin duniya suka kuma kewaye sansanin mutanen Allah, birnin da yake ƙauna. Amma wuta ta fito daga sama ta cinye su. 10 Aka jefa Iblis da ya ruɗe su cikin tafkin farar wuta, inda aka jefa dabban nan da annabin ƙaryan nan. Za a ba su azaba dare da rana har abada abadin.

  93. 1 Ubangiji ya ce wa Musa, 2 “In wani ya yi zunubi bai kuma yi aminci ga Ubangiji ba, wato, ta wurin yin wa abokin zamansa karya game da ajiyar da abokin ya ba shi amana, ko a kan wani alkawarin da suka yi wa juna, ko kuwa a kan yă cuci abokin, 3 ko kuma idan ya sami abin da ya ɓace amma ya yi ƙarya cewa bai samu ba. Ko ya yi rantsuwar ƙarya a kan duk irin abubuwan da akan aikata na laifi, 4 sa’ad da mutum ya yi irin laifin nan, ya kuwa tabbata mai laifi ne, to, sai yă komar da abin da ya ƙwace, ko abin da ya samu ta hanyar zalunci, ko abin da aka ba shi ajiya, ko abin da ya tsinta. 5 Zai mai da abin da ya yi rantsuwar ƙarya a kai. Zai mayar wa mai abin da abinsa a yadda yake, har yă ƙara kashi ashirin bisa ɗari na abin. A ranar da zai yi hadaya don laifinsa, a ranar ce zai mayar wa mai abin da abinsa.

  94. 2 “Na rantse da Allah mai rai, wanda ya danne mini gaskiyata,

    Maɗaukaki, wanda ya sa nake cikin ɗacin rai.

    3 Muddin ina da rai a cikina

    kuma numfashin Allah yana cikin hancina,

    4 bakina ba zai faɗi mugun abu ba,

    harshena kuma ba zai yi ƙarya ba.

    5 Ba zan taɓa yarda cewa kuna da gaskiya ba;

    har in mutu, ba zan daina kāre mutuncina ba.

  95. 3 Wa zai iya hawan tudun Ubangiji?

    Wa zai iya tsaya a wurinsa mai tsarki?

    4 Sai wanda yake da hannu mai tsabta da kuma tsabtar zuciya,

    wanda ba ya ba da ransa ga bautar gunki

    ko ya rantse bisa abin da yake ƙarya.

    5 Zai sami albarka daga Ubangiji

    da fiffitawa daga Allah Mai cetonsa.

  96. 4 Mai albarka ne mutumin

    da ya mai da Ubangiji abin dogararsa,

    wanda ba ya kula da masu girman kai,

    waɗanda suka juya ga allolin ƙarya.

  97. 14 A cikin annabawan Urushalima kuma

    na ga wani abin bantsoro.

    Suna zina suna kuma rayuwar ƙarya.

    Sun ƙarfafa hannuwa masu aikata mugunta,

    domin kada wani ya juya daga muguntarsa.

    Dukansu sun yi kama da Sodom a gare ni;

    mutanen Urushalima sun yi kama da Gomorra.”

  98. 21 Gama a lokacin za a yi wata matsananciyar wahala, wadda ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har ya zuwa yanzu ba kuwa za a ƙara yi ba.

    22 “Da ba don an taƙaita kwanakin nan ba, da babu wani da zai tsira, amma saboda zaɓaɓɓun nan, za a taƙaita kwanakin. 23 A lokacin in wani ya ce muku, ‘Duba, ga Kiristi nan!’ Ko, ‘Ga shi can!’ Kada ku gaskata. 24 Gama Kiristi masu yawa na ƙarya, da annabawan ƙarya za su firfito, su kuma aikata manyan alamu da ayyukan banmamaki don su ruɗi har da zaɓaɓɓu ma in zai yiwu. 25 Ga shi, na faɗa muku tun da wuri.

    26 “Saboda haka in wani ya ce muku, ‘Ga shi can a hamada,’ kada ku fita; ko, ‘Ga shi nan a ɗakunan ciki,’ kada ku gaskata. 27 Gama kamar yadda walƙiya take wulgawa walai daga gabas zuwa yamma, haka dawowar Ɗan Mutum zai kasance.

  99. 17 Ka tsarkake su ta wurin gaskiya; maganarka ce gaskiya.

  100. 17 Ina roƙonku, ’yan’uwa, ku yi hankali fa da masu raba tsakani, saɓanin koyarwar da kuka koya, suna sa tuntuɓe. Ku yi nesa da su. 18 Gama irin waɗannan mutane ba sa bautar Ubangijinmu Kiristi, sai dai cikinsu. Ta wurin yaudara da kuma daɗin baki, suna ruɗin marasa wayo.

  101. 24 Ya tambaya, “Tabbatacce kai ne ɗana Isuwa?”

    Ya amsa ya ce “Ni ne.”

  102. 18 Bari a rufe leɓunan ƙarairayinsu,

    gama da fariya da reni

    suna magana da girman kai a kan adalai.

  103. 5 Shirye-shiryen masu adalci daidai ne,

    amma shawarar mugaye ruɗu ne.

  104. 28 Mai ba da shaidar ƙarya zai hallaka,

    kuma duk wanda ya saurare shi zai hallaka har abada.

  105. 18 Kamar yadda mahaukaci yake harbin

    cukwimai ko kibiyoyi masu dafi

    19 haka yake da mutumin da ya ruɗe maƙwabci

    sa’an nan ya ce, “Wasa ne kawai nake yi!”

  106. 16 To, fa, sai ga wani ya zo wurin Yesu ya tambaye shi ya ce, “Malam, wane abu mai kyau ne ya zama mini dole in yi don in sami rai madawwami?”

    17 Yesu ya amsa ya ce, “Don me kake tambayata game da abin da yake mai kyau? Akwai Mai kyau Ɗaya kaɗai. In kana so ka sami rai madawwami, ka kiyaye dokokin nan.”

    18 Mutumin ya yi tambaya ya ce, “Waɗanne?”

    Yesu ya amsa ya ce, “ ‘Kada ka yi kisankai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka yi shaidar ƙarya, 19 ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,’ ka kuma ‘ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’”

    20 Saurayin ya ce, “Duk waɗannan na kiyaye. Me kuma ya rage mini?”

    21 Yesu ya amsa ya ce, “In kana so ka zama cikakke, ka je, ka sayar da dukan dukiyarka ka kuma ba matalauta, za ka kuwa sami dukiya a sama. Sa’an nan ka zo, ka bi ni.”

    22 Da saurayin ya ji haka, sai ya tafi rai a ɓace, don yana da arziki sosai.

  107. 13 Amma sa’ad da shi, Ruhun gaskiya ya zo, zai bi da ku zuwa ga dukan gaskiya. Ba zai yi magana don kansa ba; zai faɗi abin da ya ji ne kaɗai, zai kuma faɗa muku abin da bai faru ba tukuna.