46 Bible Verses About Honesty
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
17 Mashaidin gaskiya kan ba da shaidar gaskiya,
amma mashaidin ƙarya yana baza ƙarairayi ne.
18 Maganganun rashin tunani sukan soki mutum kamar takobi,
amma harshen mai hikima kan kawo warkarwa.
19 Leɓunan gaskiya kan dawwama har abada,
amma harshen ƙarya yakan dawwama na ɗan lokaci ne kawai.
20 Akwai ruɗu a zukatan waɗanda suke ƙulla mugunta,
amma waɗanda suke aikata alheri za su yi farin ciki.
21 Ba wani lahanin da zai sami masu adalci,
amma mugaye suna da nasu cike da wahala.
22 Ubangiji yana ƙyamar leɓunan masu ƙarya,
amma yana jin daɗin mutanen da suke masu gaskiya.
-
8 A ƙarshe, ’yan’uwa, duk abin da yake na gaskiya, duk abin da yake na girmamawa, duk abin da yake daidai, duk abin da yake da tsarki, duk abin da yake kyakkyawa, duk abin da yake na sha’awa, in ma wani abu mafifici ne, ko ya cancanci yabo, ku yi tunani a kan irin abubuwan nan. 9 Duk abin da kuka koya ko kuka karɓa ko kuka ji daga wurina, ko kuka gani a cikina, ku yi aiki da shi. Allah na salama kuma zai kasance tare da ku.
-
10 Leɓunan sarki kan yi magana kamar ta wurin ikon Allah,
kuma bai kamata bakinsa ya yi kuskure a yanke shari’a ba.
11 Ma’aunai da magwajin gaskiya daga Ubangiji ne;
dukan ma’aunai da suke cikin jaka yinsa ne.
12 Sarakuna suna ƙyamar abin da ba shi da kyau,
gama an kafa kujerar sarauta ta wurin adalci ne.
13 Sarakuna sukan ji daɗi leɓuna masu yin gaskiya;
sukan darjanta mutumin da yake faɗin gaskiya.
-
19 Ba kuwa haka kaɗai ba, har ma ikkilisiyoyi sun zaɓe shi yă riƙa tafiya tare da mu kan wannan aikin alheri da muke yi saboda ɗaukakar Ubangiji, da kuma nuna kyakkyawar niyyarmu. 20 Muna gudu kada wani yă zarge mu, a kan yadda muke gudanar da wannan kyautar da aka bayar hannu sake. 21 Gama muna iya ƙoƙari mu yi abin da yake daidai, ba a gaban Ubangiji kaɗai ba, amma a gaban mutane ma.
-
9 Kada ku yi wa juna ƙarya, da yake kun tuɓe tsohon halinku tare da ayyukansa 10 kun ɗauki sabon halin nan da ake sabuntawa ga sani, bisa ga kamannin Mahaliccinsa. 11 A wannan sabuwar rayuwa babu bambanci ko kai mutumin Al’ummai ne ko mutumin Yahuda, mai kaciya ne ko marar kaciya, baƙo, baƙauye, bawa ne ko ’yantacce, gama Kiristi shi ne kome, kuma yana cikin kome.
-
16 Ba za ka ba da shaidar ƙarya a kan maƙwabcinka ba.
-
22 sai ku tuɓe tsohon mutumin nan naku da kuma rayuwarku ta dā, wadda take lalacewa saboda sha’awace-sha’awacen da suke ruɗe ku. 23 A maimakon haka, bari Ruhu yă sabunta tunaninku da kuma halayenku. 24 Ku sanya sabon halin nan da aka halitta bisa ga kamannin Allah, halin nan kuwa, yă bayyana cikin adalci, da zaman tsarki.
25 Saboda haka dole kowannenku yă bar yin ƙarya, yă kuma riƙa faɗa wa maƙwabcinsa gaskiya, gama dukanmu gaɓoɓi jiki ɗaya ne.
-
10 Gama,
“Duk wanda yake so yă ji daɗin rayuwa,
yă kuma ga kwanaki masu kyau
dole yă ƙame harshensa daga mugunta
leɓunansa kuma daga maganar yaudara.
11 Dole yă juye daga mugunta, ya aikata nagarta;
dole yă nemi salama yă kuma bi ta.
12 Gama idanun Ubangiji suna a kan masu adalci
kunnuwansa kuma suna jin addu’arsu,
amma fuskar Ubangiji tana gāba da masu mugunta.”
-
44 Ku na ubanku ne, Iblis, kuna kuwa so ku aikata abin da ubanku yake so. Shi mai kisankai ne tun farko. Ba ruwansa da gaskiya, gama gaskiya ba ta cikinsa. Yayinda yake ƙarya, yana yin halinsa ne, gama shi maƙaryaci ne, uban ƙarairayi kuma.
-
17 Idan kowa ya yi muku mugunta, kada ku sāka masa da mugunta. Ku lura don ku aikata abin da kowa zai iya gani cewa daidai ne.
-
35 “ ‘Kada ku yi amfani da mudun ƙarya sa’ad da kuke awon tsawo, nauyi, ko yawan abu. 36 Ku yi amfani da ma’auni na gaskiya da mudu na gaskiya, da kuma magwaji na gaskiya. Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar.
-
13 Kada ku kasance da ma’auni iri biyu a jakarku, ɗaya babba, ɗaya ƙarami. 14 Kada ku kasance da mudu iri biyu a jakarku, ɗaya babba, ɗaya ƙarami. 15 Dole ku kasance da ma’aunin da kuma mudun da yake daidai, kuma na gaskiya, saboda ku yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku. 16 Gama Ubangiji Allahnku yana ƙyamar duk mai yi waɗannan abubuwa, da kuma mai rashin gaskiya.
-
Zabura ta Dawuda.
1 Ubangiji, wa zai zauna cikin wuri mai tsarkinka?
Wa zai zauna a kan tudunka mai tsarki?
2 Sai wanda ba shi da laifi
kuma yana yin abin da yake daidai,
wanda yake faɗin gaskiya daga zuciyarsa
3 ba ya kuwa ɓata sunan wani da harshensa,
wanda ba ya yi wa maƙwabcinsa mugunta
ba ya kuwa baza jita-jita a kan ɗan’uwansa,
-
1 Ubangiji yana ƙyamar ma’aunan zamba,
amma ma’aunin da suke daidai ne abin farin cikinsa.
-
3 Mutuncin masu aikata gaskiya takan bi da su,
amma marasa aminci sukan hallaka ta wurin cin amanar da suke yi.
-
2 Ba ruwanmu da ɓoye-ɓoye na munafuncin da suke abubuwan kunya. Ba ruwanmu da ruɗu, ko yin ƙarya da kalmar Allah. Sai dai muna faɗin gaskiya a fili. Ta haka ne kowa zai yi shaidar gaskiyarmu a gaban Allah cikin zuciyarsa.
-
7 Mai adalci kan yi rayuwa marar abin zargi;
masu albarka ne ’ya’yan da za su biyo bayansa.
-
6 Yesu ya amsa ya ce, “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai dai ta wurina.
-
3 Yin abin da yake daidai da kuma nagari
Ubangiji ya fi yarda da shi fiye da hadaya.
-
18 Kamar sanda ko takobi ko kibiya mai tsini
haka yake da mutumin da yake ba da shaidar ƙarya a kan maƙwabcinsa.
-
14 Saboda haka aka kau da yin gaskiya
adalci kuma ya tsaya can da nesa;
gaskiya ta yi tuntuɓe a tituna,
sahihanci ba zai shiga ba.
15 Gaskiya ta ɓace gaba ɗaya,
kuma duk wanda ya guji mugunta zai zama ganima.
Ubangiji ya duba bai kuwa ji daɗi
cewa babu adalci ba.
-
16 Abubuwan da za ku yi ke nan. Ku gaya wa juna gaskiya, ku kuma dinga yin shari’ar gaskiya a ɗakunanku na shari’arku; 17 kada ku ƙulla wa maƙwabtanku mugunta, kuma kada ku so yin rantsuwa ta ƙarya. Ina ƙyamar waɗannan duka,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
-
33 “Har wa yau dai kun ji an faɗa wa mutane a dā, ‘Kada ka karya alkawarinka, sai dai ka cika alkawaran da ka yi wa Ubangiji.’ 34 Amma ina gaya muku, Kada ku yi rantsuwa sam, ko da sama, domin kursiyin Allah ne; 35 ko da ƙasa, domin matashin ƙafafunsa ne; ko kuma da Urushalima, domin birnin Babban Sarki ne. 36 Kada kuma ka rantse da kanka, domin ba za ka iya mai da ko gashi ɗaya yă zama fari ko baƙi ba. 37 Abin da ya kamata ku ce kawai, shi ne, I, ko A’a. Abin da ya wuce haka kuwa daga wurin Mugun nan yake.
-
5 Wannan shi ne saƙon da muka ji daga wurinsa, muna kuma sanar da ku cewa Allah haske ne; a cikinsa kuwa babu duhu ko kaɗan. 6 In muka ce muna zumunci da shi amma muna tafiya cikin duhu, ƙarya muke yi, kuma ba ma rayuwa bisa ga gaskiya. 7 Amma in muna tafiya cikin haske, yadda yake cikin haske, muna da zumunci da juna ke nan, kuma jinin Yesu, Ɗansa, yana tsarkake mu daga dukan zunubi.
8 In muka ce ba mu da zunubi, muna ruɗin kanmu ne, gaskiya kuwa ba ta cikinmu. 9 In muka furta zunubanmu, shi mai aminci ne, mai adalci kuma, zai gafarta mana zunubanmu, yă kuma tsarkake mu daga dukan rashin adalci.
-
4 “Kai kuwa, in ka yi tafiya a gabana da mutunci a zuci da kuma gaskiya, kamar yadda Dawuda mahaifinka ya yi, ka yi dukan abin da na umarta, ka kuma yi biyayya da ƙa’idodina da kuma dokokina, 5 zan kafa kujerar sarautarka a bisa Isra’ila har abada, kamar yadda na alkawarta wa Dawuda mahaifinka sa’ad da na ce, ‘Ba za ka taɓa rasa wani a kan kujerar sarautar Isra’ila ba.’
-
15 Ba su bukaci wani bayani daga waɗanda aka ba wa kuɗin don su biya ma’aikatan ba, domin sun yi aikinsu da aminci.
-
16 Akwai abubuwa shida da Ubangiji ya ƙi,
abubuwa bakwai da suke abin ƙyama gare shi,
17 duban reni,
harshe mai ƙarya,
hannuwa masu zub da jinin marar laifi,
18 zuciyar da take ƙulla mugayen dabaru,
ƙafafun da suke sauri zuwa aikata mugunta,
19 mai shaidar ƙarya wanda yake zuba ƙarairayi,
da kuma mutumin da yake tā-da-na-zaune-tsaye a cikin ’yan’uwa.
20 Ɗana, ka kiyaye umarnan mahaifinka
kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.
-
16 Suka aiki almajiransu tare da mutanen Hiridus wurinsa. Suka ce, “Malam, mun san kai mutum ne mai mutunci, kuma kana koyar da maganar Allah bisa gaskiya. Mutane ba sa ɗaukan hankalinka, domin ba ka kula ko su wane ne ba.
-
26 Amsa da take ta gaskiya
tana kamar sumba a leɓuna.
-
10 “Duk wanda ana amincewa da shi cikin ƙaramin abu, ana kuma amincewa da shi cikin babba. Kuma duk marar gaskiya cikin ƙaramin abu, zai zama marar gaskiya cikin babba. 11 In fa ku ba amintattu ne cikin tafiyar da dukiya ta wannan duniya ba, wa zai amince muku da dukiya ta gaskiya? 12 In fa ku ba amintattu ne cikin tafiyar da dukiyar wani ba, wa zai ba ku dukiya naku, na kanku?
-
9 Mai mutunci yana tafiya lafiya,
amma shi da yake tafiya a karkatattun hanyoyi za a kama shi.
-
1 Gara matalauci wanda yake marar laifi
da wawa wanda leɓunansa masu ƙarya ne.
-
7 Cikin kowane abu ka zama musu misali mai kyau ta wurin aikata abin da yake nagari. A cikin koyarwarka ka nuna mutunci da ƙwazo 8 da kuma sahihanci cikin maganar da ba za a iya kushewa ba, domin masu gāba da kai su ji kunya, su kuma rasa wani mugun abin da za su faɗa game da mu.
-
24 Ka kau da muguwar magana daga bakinka;
ka yi nesa da magana marar kyau daga leɓunanka.
25 Bari idanunka su dubi gaba sosai,
ka kafa idanunka kai tsaye a gabanka.
26 Ka san inda ƙafafunka suke takawa
ka bi hanyoyin da suke daram kawai.
27 Kada ka kauce dama ko hagu;
ka kiyaye ƙafarka daga mugunta.
-
3 Wa zai iya hawan tudun Ubangiji?
Wa zai iya tsaya a wurinsa mai tsarki?
4 Sai wanda yake da hannu mai tsabta da kuma tsabtar zuciya,
wanda ba ya ba da ransa ga bautar gunki
ko ya rantse bisa abin da yake ƙarya.
5 Zai sami albarka daga Ubangiji
da fiffitawa daga Allah Mai cetonsa.
-
13 Mugun mutum kan fāɗa a tarkon maganarsa ta zunubi,
amma adali kan kuɓuta daga wahala.
14 Daga abubuwan da suke fitowa daga leɓunansa mutum kan cika da abubuwa masu kyau
tabbatacce yadda aikin hannuwansa suke ba shi lada.
-
17 Abincin da aka samu ta hanyar zamba yakan zama da daɗi,
amma mutum zai ƙarasa da baki cike da yashi.
-
6 Dukiyar da aka samu ta wurin harshe mai yin ƙarya
tarin tururi ne da kuma mugun tarko.
-
10 Ku yi amfani da garwan da yake daidai, efa da yake daidai da kuma garwa da yake daidai.
-
37 Sai Bilatus ya ce, “To, wato, kai sarki ne!”
Yesu ya amsa ya ce, “Haka yake, ni sarki ne yadda ka faɗa. Tabbatacce, saboda wannan dalili ne aka haife ni, kuma don wannan ne na zo duniya, domin in shaidi gaskiya. Duk wanda yake gefen gaskiya yakan saurare ni.”
38 Bilatus ya tambaye shi ya ce, “Mece ce gaskiya?”
Da ya faɗi haka, sai ya sāke fitowa wurin Yahudawa ya ce, “Ni fa ban sami wani abin zargi game da shi ba.
-
4 Ko kaɗan! Bari Allah yă zama mai gaskiya, kowane mutum kuma yă zama maƙaryaci. Kamar yadda yake a rubuce cewa,
“Gama a tabbatar kana da gaskiya, sa’ad da ka yi magana,
ka kuma yi nasara sa’ad da ka yi shari’a.”
-
7 Muna addu’a ga Allah kada ku aikata wani laifi. Ba don mutane su gani cewa mun ci gwajin ba ne, a’a, sai dai don ku yi abin da yake daidai, ko da yake zai zama kamar mun fāɗi gwajin ne.
-
3 Gama roƙon da muke yi bai fito daga kuskure ko munafunci ba, ba kuwa ƙoƙari muke yi mu yaudare ku ba.
-
7 Da yake an danƙa wa mai kula da ikkilisiya riƙon amana saboda Allah, dole yă zama marar aibi ba mai girman kai ba, ba mai saurin fushi ba, ba mai buguwa ba, ba mai rikici ba, ba kuma mai son ƙazamar riba ba. 8 A maimakon haka dole yă zama mai karɓan baƙi, mai son abu nagari, mai kamunkai, mai adalci, mai tsarki da kuma natsattse. 9 Dole yă riƙe tabbataccen saƙon nan kam-kam yadda aka koyar, don yă iya ƙarfafa waɗansu da sahihiyar koyarwa yă kuma ƙaryata waɗanda suke gāba da shi.
-
22 “Bai taɓa yin laifi ba sam,
ba a kuma sami ƙarya a bakinsa ba.”
-
17 In wani yana da arziki, ya kuma ga ɗan’uwansa cikin rashi, bai kuwa taimake shi ba, anya, ƙaunar Allah tana a cikinsa kuwa? 18 ’Ya’yana ƙaunatattu, kada mu yi ƙauna da fatar baki kawai, sai dai mu nuna ta ta wurin aikatawa da kuma gaskiya.
Shows Read in context, Share and Copy.