38 Bible Verses About Keeping Your Word
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
33 “Har wa yau dai kun ji an faɗa wa mutane a dā, ‘Kada ka karya alkawarinka, sai dai ka cika alkawaran da ka yi wa Ubangiji.’ 34 Amma ina gaya muku, Kada ku yi rantsuwa sam, ko da sama, domin kursiyin Allah ne; 35 ko da ƙasa, domin matashin ƙafafunsa ne; ko kuma da Urushalima, domin birnin Babban Sarki ne. 36 Kada kuma ka rantse da kanka, domin ba za ka iya mai da ko gashi ɗaya yă zama fari ko baƙi ba. 37 Abin da ya kamata ku ce kawai, shi ne, I, ko A’a. Abin da ya wuce haka kuwa daga wurin Mugun nan yake.
-
1 Musa ya ce wa shugabannin kabilan Isra’ila, “Ga abin da Ubangiji ya umarta. 2 Sa’ad da mutum ya yi wa Ubangiji alkawari, ko kuwa ya rantse zai yi wani abu, kada yă ƙi cika maganarsa, amma yă cika kome da ya faɗa.
3 “Sa’ad da yarinya, wadda har yanzu tana a gidan mahaifinta ta yi wa Ubangiji alkawari, ko ta rantse za tă yi wani abu, 4 mahaifinta kuwa ya ji alkawarin da ta yi, bai kuma ce mata kome ba, to, sai alkawarin da ta yi da wa’adinta su tabbata. 5 Amma in mahaifinta ya hana ta, sa’ad da ya ji game da shi, to, ba wani daga cikin alkawari ko rantsuwar da ta yi zai tabbata; Ubangiji kuwa zai gafarta mata domin maihaifinta ya hana ta.
6 “In ta yi aure, sai daga baya ta yi alkawari ko kuwa leɓunanta sun furta alkawari da garaje, cewa za tă yi wani abu, 7 mijinta kuwa ya ji game da wannan, amma bai ce mata kome ba, to, alkawarin da ta yi da kuma rantsuwar da ta yi, su tabbata. 8 Amma in mijin ya hana ta sa’ad da ya ji, zai warware alkawari da kuma rantsuwar da ta yi da garaje, Ubangiji kuwa zai gafarce ta.
-
4 Sa’ad da ka yi alkawari ga Allah, kada ka ɓata lokaci wajen cika shi. Ba ya jin daɗin wawaye; ka cika alkawarinka. 5 Gara kada ka yi alkawari, da ka yi amma ba ka cika ba. 6 Kada ka bar bakinka ya kai ga yin zunubi. Kada kuma ka kai ƙara wurin ɗan saƙon haikali cewa, “Alkawarin da na yi kuskure ne.” Me ya sa Allah yake fushi a kan abin da ka faɗa har yă lalatar da aikin hannuwanka? 7 Yawan buri da yawan magana ba su da amfani. Saboda haka, ka ji tsoron Allah.
-
21 In fa kuka yi alkawari ga Ubangiji Allahnku, to, kada ku yi jinkirin cikawa, gama tabbatacce Ubangiji Allahnku zai neme shi daga gare ku, za ku kuma zama masu laifin zunubi. 22 Amma in ba ku yi alkawari ba, ba kuwa zai zama muku zunubi ba. 23 Duk abin da ya fita daga bakinku, sai ku lura ku cika shi, kamar yadda kuka yarda da kanku, kuka yi alkawarin ga Ubangiji Allahnku da bakinku.
-
Zabura ta Dawuda.
1 Ubangiji, wa zai zauna cikin wuri mai tsarkinka?
Wa zai zauna a kan tudunka mai tsarki?
2 Sai wanda ba shi da laifi
kuma yana yin abin da yake daidai,
wanda yake faɗin gaskiya daga zuciyarsa
3 ba ya kuwa ɓata sunan wani da harshensa,
wanda ba ya yi wa maƙwabcinsa mugunta
ba ya kuwa baza jita-jita a kan ɗan’uwansa,
4 wanda yake ƙin mugun mutum
amma yakan girmama masu tsoron Ubangiji,
yakan cika alkawarinsa
ko da ma ya zafe shi,
5 wanda yake ba da rance ba tare da ruwa ba
kuma ba ya karɓan cin hanci don yă kā da marar laifi.
Shi wanda yake yin waɗannan abubuwa
ba zai taɓa jijjiguwa ba.
-
11 “ ‘Kada ku yi sata.
“ ‘Kada ku yi ƙarya.
“ ‘Kada ku ruɗe juna.
-
44 Ku na ubanku ne, Iblis, kuna kuwa so ku aikata abin da ubanku yake so. Shi mai kisankai ne tun farko. Ba ruwansa da gaskiya, gama gaskiya ba ta cikinsa. Yayinda yake ƙarya, yana yin halinsa ne, gama shi maƙaryaci ne, uban ƙarairayi kuma.
-
12 ’Yan’uwana, fiye da kome, kada ku yi rantsuwa ko da sama, ko da ƙasa ko da wani abu dabam. Bari “I” naku yă zama “I”. “A’a” naku kuma yă zama “A’a”, don kada a hukunta ku.
-
28 Yaƙub ya yi zama a Masar shekaru goma sha bakwai, yawan shekarunsa duka sun zama ɗari da arba’in da bakwai. 29 Sa’ad da lokaci ya gabato da Isra’ila zai mutu, sai ya kira ɗansa Yusuf, ya ce masa, “Ka yi mini wannan alheri, ka sa hannunka ƙarƙashin cinyar ƙafata, ka yi mini alkawari saboda ina roƙonka kaɗa ka bizne ni a Masar, 30 amma sa’ad da na huta da kakannina, ka ɗauke ni, ka fid da ni daga Masar, ka binne ni a inda aka binne su.”
Yusuf ya ce, “Zan yi yadda ka faɗa.”
31 Yaƙub ya ce, “Ka rantse mini.” Sai Yusuf ya rantse masa, Isra’ila kuwa ya yi godiya ga Allah yayinda ya jingina a kan sandansa.
-
4 Kai ba Allahn da yake jin daɗin mugu ba ne;
gama kana gāba da dukan masu aikata mugunta.
5 Masu fariya ba za su iya tsaya
a gabanka ba.
Kana ƙin duk masu aikata abin da ba daidai ba.
6 Kakan hallaka masu yin ƙarya.
Masu kisankai da mutane masu ruɗu
Ubangiji yana ƙyama.
-
22 Ubangiji yana ƙyamar leɓunan masu ƙarya,
amma yana jin daɗin mutanen da suke masu gaskiya.
-
25 Tarko ne ga mutum ya keɓe wani abu da ba tunani
daga baya kuma ya yi la’akari da alkawarinsa.
-
19 Allah ba mutum ba ne, da zai yi ƙarya,
shi ba ɗan mutum ba ne, da zai canja tunaninsa.
Yana maganar abin da ba zai iya aikata ba ne?
Yakan kuma yi alkawarin da ba zai iya cikawa ba?
-
7 Ba za ka yi amfani da sunan Ubangiji Allahnka a banza ba, gama Ubangiji zai hukunta duk wanda ya mai da sunansa banza.
-
14 “Yanzu na kusa barin fuskar duniyan nan. Kun sani da dukan zuciyarku, da dukan ranku cewa, Ba ko ɗaya daga cikin alkawuran da Ubangiji Allahnku ya yi, da bai cika ba. Kowane alkawari ya cika; ba ko ɗaya da bai cika ba.
-
9 Zuciya ta fi kome ruɗu
ta fi ƙarfin warkewa.
Wa zai iya gane ta?
10 “Ni Ubangiji nakan bincike zuciya
in gwada tunani,
don in sāka wa kowane mutum bisa ga halinsa,
bisa ga ayyukansa.”
-
8 Amma matsorata, da marasa bangaskiya, masu ƙazanta, masu kisankai, masu fasikanci, masu sihiri, masu bautar gumaka da dukan maƙaryata, wurinsu zai kasance a cikin tafkin wutar da yake farar wuta mai ci. Wannan fa ita ce mutuwa ta biyu.”
-
22 A lokacin nan Abimelek da Fikol, komandan rundunoninsa suka zo suka ce wa Ibrahim, “Allah yana tare da kai a ko mene ne kake yi. 23 Yanzu ka rantse mini a nan a gaban Allah cewa, ba za ka yaudare ni ko ’ya’yana ko kuma zuriyata ba. Ka nuna mini alheri, kai da ƙasar da kake zama baƙunci kamar yadda na nuna maka.”
24 Ibrahim ya ce, “Na rantse.”
-
20 Sa’an nan Yaƙub ya yi alkawari cewa, “In Allah zai kasance tare da ni yă kuma lura da ni a wannan tafiya, yă kuma ba ni abinci in ci da tufafi in sa, 21 har in dawo lafiya zuwa gidan mahaifina, to, Ubangiji zai zama Allahna 22 kuma wannan dutsen da na kafa al’amudi, zai zama gidan Allah, kuma dukan abin da ka ba ni zan ba ka kashi ɗaya bisa goma.”
-
13 Ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku bauta masa shi kaɗai, ku kuma yi alkawaranku da sunansa.
-
11 Ta yi ta cewa, “Ya Ubangiji Maɗaukaki. In har ka dubi baƙin cikin baiwarka, ka tuna da ni, ba ka kuma manta da baiwarka ba, amma ka ba ta ɗa, ni ma zan miƙa shi ga Ubangiji dukan rayuwarsa, aska kuwa ba za tă taɓa kansa ba.”
-
7 A ƙarshen shekara huɗu, Absalom ya ce wa sarki, “Bari in tafi Hebron in cika alkawarin da na yi wa Ubangiji. 8 Yayinda bawanka yake zama a Geshur, a Aram, na yi wannan alkawari, na ce, ‘In Ubangiji ya komo da ni Urushalima, zan yi wa Ubangiji sujada a Hebron.’ ”
9 Sarki ya ce, “Ka sauka lafiya.” Sai ya tafi Hebron.
10 Sai Absalom ya aiki manzanni a asirce cikin dukan kabilan Isra’ila, ya ce musu su ce, “Da zarar kuka ji an busa ƙaho, sai ku ce, ‘Absalom sarki ne a Hebron.’ ” 11 Mutum ɗari biyu daga Urushalima suka raka Absalom. An gayyace su a matsayin baƙi, suka kuwa tafi cikin rashin sani, ba su san wani abu game da al’amarin ba. 12 Yayinda Absalom yake miƙa hadaya, ya aika a kira Ahitofel mutumin Gilo, mai ba wa Dawuda shawara, yă zo daga Gilo garinsa. Ta haka makircin ya ƙara ƙarfi, masu bin Absalom kuma suka yi ta ƙaruwa.
-
28 “Sauran mutane, wato, firistoci, Lawiyawa, matsaran ƙofofi, mawaƙa, ma’aikatan haikali da dukan waɗanda suka ware kansu daga maƙwabta saboda Dokar Allah, tare da matansu da dukan ’ya’yansu maza da mata waɗanda za su iya fahimta, 29 dukan waɗannan yanzu suka sadu da manyan gari ’yan’uwansu, suka rantse, cewa la’ana ta same su idan ba su kiyaye Dokar Allah da aka bayar ta wurin Musa bawan Allah su kuma mai da hankali ga yin biyayya da dukan umarnai, ƙa’idodi da farillan Ubangiji shugabanmu ba.
-
16 Akwai abubuwa shida da Ubangiji ya ƙi,
abubuwa bakwai da suke abin ƙyama gare shi,
17 duban reni,
harshe mai ƙarya,
hannuwa masu zub da jinin marar laifi,
18 zuciyar da take ƙulla mugayen dabaru,
ƙafafun da suke sauri zuwa aikata mugunta,
19 mai shaidar ƙarya wanda yake zuba ƙarairayi,
da kuma mutumin da yake tā-da-na-zaune-tsaye a cikin ’yan’uwa.
-
9 Mai shaidar ƙarya ba zai tafi babu hukunci ba,
kuma duk mai baza ƙarairayi zai hallaka.
-
4 “Ka yi hankali da abokanka;
kada ka amince da ’yan’uwanka.
Gama kowane ɗan’uwa munafuki ne,
kowane aboki kuma mai kushe ne.
5 Aboki kan ruɗi aboki,
ba mai faɗar gaskiya.
Sun koya wa harshensu faɗar ƙarya;
sun gajiyar da kansu da yin zunubi.
6 Kai kana zama a tsakiyar ruɗu;
cikin ruɗunsu sun ƙi su san ni,”
in ji Ubangiji.
7 Saboda haka ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa,
“Ga shi zan tace in kuma gwada su,
gama me kuwa zan yi
saboda zunubin mutanena?
8 Harshensu kibiya ce mai dafi;
yana magana da ruɗu.
Da bakinsa kowa yana maganar alheri da maƙwabcinsa,
amma a zuciyarsa ya sa masa tarko.
9 Bai kamata in hukunta su saboda wannan ba?”
In ji Ubangiji.
“Bai kamata in ɗau fansa
a kan irin al’umma kamar wannan ba?”
-
9 Amma ni, da waƙar godiya,
zan miƙa tawa hadaya gare ka.
Abin da na yi alkawari, shi ne zan yi.
Ceto yakan zo ne kawai daga wurin Ubangiji.”
-
1 Kaiton birni mai zub da jini,
wadda take cike da ƙarairayi,
cike da ganima,
wadda ba a rasa masu fāɗawa cikin wahala!
-
71 Sa’an nan ya fito zuwa hanyar shiga, inda wata yarinya kuma ta gan shi, ta ce wa mutanen da suke can, “Wannan mutum ma yana tare da Yesu Banazare.”
72 Ya sāke mūsu har da rantsuwa, yana cewa, “Ban ma san mutumin nan ba!”
73 Bayan ɗan lokaci, sai na tsattsaye a wurin, suka hauro wurin Bitrus, suka ce, “Tabbatacce, kai ɗayansu ne, don harshen maganarka, ya tone ka.”
74 Sai ya fara la’antar kansa, yana ta rantsuwa yana ce musu, “Ban ma san mutumin nan ba!”
Nan da take, sai zakara ya yi cara. 75 Sai Bitrus ya tuna da maganar da Yesu ya yi cewa, “Kafin zakara yă yi cara, za ka yi mūsun sani na sau uku.” Sai ya fita waje, ya yi ta kuka.
-
1 Amma a dā akwai annabawan ƙarya a cikin mutane, kamar yadda za a sami malaman ƙarya a cikinku. A ɓoye za su shigar da karkataccen koyarwa mai hallaka, har ma su yi mūsun Ubangiji mai iko duka wanda ya saye su suna kawo wa kansu hallaka farat ɗaya. 2 Da yawa za su bi hanyoyinsu na rashin kunya su kuma sa a rena hanyar gaskiya. 3 Cikin kwaɗayinsu waɗannan malaman ƙarya za su cuce ku da tatsuniyoyin da suka ƙaga. Hukuncinsu yana a rataye a kansu tun da daɗewa, hallakarsu kuma ba ta barci.
-
34 Ba zan take alkawarina ba
ko in canja abin da leɓunana suka ambata.
-
2 Kada ka yi subul da bakinka,
kada zuciyarka tă yi garajen
furta wani abu a gaban Allah.
Allah yana sama
kai kuma kana duniya,
saboda haka, kada kalmominka su zama da yawa.
-
11 Ba za ka yi amfani da sunan Ubangiji Allahnka a banza ba, gama Ubangiji zai ba wa duk mai yin amfani da sunansa a banza laifi.
-
1 Ɗana, in ka shirya tsaya wa maƙwabcinka don yă karɓi bashi,
in ka sa hannunka don ɗaukar lamunin wani,
2 in maganarka ta taɓa kama ka,
ko kalmomin bakinka sun zama maka tarko,
3 to, sai ka yi haka, ɗana don ka ’yantar da kanka;
da yake ka shiga hannuwan maƙwabcinka,
ka tafi ka ƙasƙantar da kanka;
ka roƙi maƙwabcinka!
-
25 Saboda haka dole kowannenku yă bar yin ƙarya, yă kuma riƙa faɗa wa maƙwabcinsa gaskiya, gama dukanmu gaɓoɓi jiki ɗaya ne.
-
3 Ta haka za mu tabbata cewa mun san shi in muna yin biyayya da umarnansa. 4 Mutumin da ya ce, “Na san shi,” amma ba ya yin abin da ya umarta, maƙaryaci ne, gaskiya kuwa ba ta cikinsa. 5 Amma in wani ya yi biyayya da maganarsa, ƙaunar Allah ta zama cikakkiya ke nan a cikinsa. Ta haka muka san cewa muna cikinsa.
-
17 Zan yi hadayar godiya gare ka
in kuma kira bisa sunan Ubangiji.
18 Zan cika alkawurana ga Ubangiji
a gaban dukan mutanensa,
-
18 Bulus kuwa ya ci gaba da zama a Korint na ’yan kwanaki. Sa’an nan ya bar ’yan’uwa ya shiga jirgin ruwa zuwa Suriya tare da Firiskila da Akwila. Kafin ya tashi, ya aske kansa a Kenkireya saboda alkawarin da ya yi.
Shows Read in context, Share and Copy.