65 Bible Verses About Adultery

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Adultery
  1. 27 “Kun dai ji an faɗa, ‘Kada ka yi zina.’ 28 Amma ina gaya muku, duk wanda ya dubi mace, sa’an nan ya yi sha’awarta a zuci, ya riga ya yi zina ke nan da ita a zuciyarsa. 29 In idonka na dama yana sa ka yin zunubi, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta. 30 In kuma hannunka na dama yana sa ka yin zunubi, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta.

    31 “An kuma faɗa, ‘Duk wanda ya saki matarsa, dole yă ba ta takardar saki.’ 32 Amma ina gaya muku, duk wanda ya saki matarsa in ba a kan laifin zina ba, ya sa ta zama mazinaciya ke nan, kuma duk wanda ya auri macen da mijinta ya sake, shi ma yana zina ne.

  2. 14 Ba za ka yi zina ba.

    15 Ba za ka yi sata ba.

    16 Ba za ka ba da shaidar ƙarya a kan maƙwabcinka ba.

    17 Ba za ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka ba. Ba za ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka ba, ko bawansa, ko baiwarsa, ko sansa, ko jakinsa, ko duk abin da yake na maƙwabcinka ba.”

    18 Da mutane suka ga tsawa da walƙiya, suka ji karar ƙaho, suka kuma ga dutsen yana hayaƙi, sai suka yi rawar jiki don tsoro. Suka tsaya da nisa 19 suka ce wa Musa, “Ka yi magana da mu da kanka, za mu kasa kunne. Amma kada Allah ya yi mana magana, don kada mu mutu.”

  3. 23 Gama waɗannan umarnai fitila ne,

    wannan koyarwa haske ne,

    kuma gyare-gyaren horo

    hanyar rayuwa ce,

    24 suna kiyaye ka daga mace marar ɗa’a

    daga sulɓin harshen mace marar aminci.

    25 Kada ka yi sha’awarta a cikin zuciyarka

    kada ka bar ta tă ɗauki hankalinka da idanunta.

    26 Gama karuwa takan mai da kai kamar burodin kyauta,

    mazinaciya kuma takan farauci ranka.

    27 Mutum zai iya ɗiba wuta ya zuba a cinyarsa

    ba tare da rigunansa sun ƙone ba?

    28 Mutum zai iya yin tafi a garwashi wuta mai zafi

    ba tare da ƙafafunsa sun ƙone ba?

    29 Haka yake da wanda ya kwana da matar wani;

    babu wanda ya taɓa ta da zai tafi babu hukunci.

    30 Mutane ba sa ƙyale ɓarawo in ya yi sata

    don yă ƙosar da yunwarsa sa’ad da yake jin yunwa.

    31 Duk da haka in aka kama shi, dole yă biya sau bakwai

    ko da yake abin zai ci dukan arzikin gidansa.

    32 Amma mutumin da ya yi zina ba shi da hankali;

    duk wanda ya yi haka yana hallaka kansa ne.

    33 Dūka da kunya ne za su zama rabonsa,

    kuma kunyarsa za tă dawwama.

    34 Gama kishi kan tā da hasalar miji,

    kuma ba zai ji tausayi ba sa’ad da yake ramawa.

    35 Ba zai karɓi duk wata biya ba;

    zai ƙi cin hanci, kome yawansu.

  4. 9 Ba ku sani ba cewa mugaye ba za su gāji mulkin Allah ba? Kada fa a ruɗe ku. Ba masu fasikanci ko masu bautar gumaka ko masu zina ko karuwan maza, ko ’yan daudu, 10 ko ɓarayi ko masu kwaɗayi ko mashaya ko masu ɓata suna ko masu zamba da za su gāji mulkin Allah. 11 Haka waɗansu a cikinku ma suke a dā. Amma an wanke ku, an tsarkake ku, aka kuma sa kuka zama marasa laifi cikin sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma ta wurin Ruhun Allahnmu.

  5. 4 Aure yă zama abin girmamawa ga kowa, a kuma kiyaye gadon aure da tsabta, gama Allah zai hukunta masu zina da kuma dukan masu fasikanci.

  6. 6 A zamanin Sarki Yosiya, Ubangiji ya ce mini, “Ka ga abin da marar amincin nan, Isra’ila ta yi? Ta haura kan kowane tudu mai tsayi da kowane gindin itace mai duhuwa ta yi zina a can. 7 Na yi zaton bayan ta yi wannan duka, za tă komo wurina amma ba tă yi haka ba, ’yar’uwarta marar aminci nan Yahuda ta gani. 8 Na ba wa Isra’ila marar bangaskiya takardar saki na kuwa kore ta saboda duk zinanta. Duk da haka na ga cewa ’yar’uwarta marar amincin nan Yahuda ba ta da tsoro; ita ma ta fita ta yi zina. 9 Domin fasikancin Isra’ila bai yi tasiri gare ta ba, sai ta ƙazantar da ƙasar ta kuma yi zina da dutse da kuma itace. 10 Duk da wannan duka, Yahuda ’yar’uwarta rashin amincin ba tă komo gare ni da dukan zuciyarta ba, sai a munafunce,” in ji Ubangiji.

  7. 3 Gama leɓunan mazinaciya na ɗigan zuma,

    maganarta tana da sulɓi fiye da mai;

    4 amma a ƙarshe tana da ɗaci kamar tafashiya,

    mai ci kamar takobi mai kaifi biyu.

    5 Ƙafafunta na kaiwa ga mutuwa;

    sawunta na jagora kai tsaye zuwa kabari.

    6 Ba ta wani tunanin rayuwa;

    hanyoyinta karkatacce ne, amma ba tă sani ba.

    7 Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni;

    kada ku juye daga abin da nake faɗa.

    8 Ku yi nesa da hanyarta,

    kana ku je kusa da ƙofar gidanta,

    9 don kada ku ba da ƙarfi mafi kyau ga waɗansu

    da kuma shekarunku ga wani marar imani,

    10 don kada baƙi su yi biki a kan dukiyarku

    wahalarku ta azurta gidan wani mutum dabam.

    11 A ƙarshen rayuwarku za ku yi ta nishi,

    sa’ad da namanku da jikinku suka zagwanye.

    12 Za ku ce, “Me ya sa na ƙi horo!

    Me ya sa zuciyata ta ƙi gyara!

    13 Ban yi biyayya da malamaina ba

    ko in saurari masu koyar da ni.

    14 Na zo gab da hallaka gaba ɗaya

    a tsakiyar dukan taron.”

    15 Ku sha ruwa daga tankinku,

    ruwa mai gudu daga rijiyarku.

    16 In maɓulɓulanku suka cika suna malala har waje,

    rafuffukan ruwanku a dandalin jama’a?

    17 Bari su zama naka kaɗai,

    don kada ka raba da baƙi.

    18 Bari maɓulɓulanka ya zama mai albarka,

    bari kuma ka yi farin ciki da matar ƙuruciyarka.

    19 Ƙaunatacciyar mariri, barewa mai kyan gani,

    bari mamanta su ishe ka kullum,

    bari ƙaunarta ta ɗauke hankalinka kullum.

    20 Ɗana, me ya sa za ka bari mazinaciya ta ɗauke maka hankali?

    Don me za ka rungume matar wani?

    21 Gama hanyar mutum a bayyane take a gaban Ubangiji,

    yana kuma lura da dukan hanyoyinsa.

    22 Ayyukan mugunta na mugun mutum tarko ne gare shi;

    igiyoyin zunubinsa za su daure shi kankan.

    23 Zai mutu saboda rashin ɗa’a

    yawan wawancinsa zai sa yă kauce.

  8. 10 “ ‘In mutum ya yi zina da matar wani, da matar maƙwabcinsa, dole a kashe su biyu da suka yi zinan.

    11 “ ‘In mutum ya kwana da matar mahaifinsa, ya ƙasƙantar da mahaifinsa. Dole a kashe shi da macen, alhakin jininsu zai zauna a kansu.

    12 “ ‘In mutum ya kwana da matar ɗansa, dole a kashe su biyun. Abin da suka yi haram ne; alhakin jininsu zai zauna a kansu.

  9. 8 Yesu ya amsa ya ce, “Musa ya ba ku izini ku saki matanku saboda taurin zuciyarku ne. Amma ba haka yake ba daga farko. 9 Ina faɗa muku cewa duk wanda ya saki matarsa, sai dai a kan rashin aminci a cikin aure, ya kuwa auri wata, ya yi zina ke nan.”

  10. 20 Duk da haka, ina da wannan game da kai. Kana haƙuri da matan nan Yezebel, wadda take kira kanta annabiya. Ta wurin koyarwarta tana ɓad da bayina ga yin fasikanci suka kuma ci abincin da aka miƙa wa gumaka. 21 Na ba ta lokaci tă tuba daga fasikancinta, amma ba ta da niyya. 22 Don haka zan jefa ta a kan gadon wahala, zan kuma sa waɗanda suke zina da ita, su sha azaba ƙwarai, sai dai in sun tuba daga hanyoyinta. 23 Zan kashe ’ya’yanta. Sa’an nan dukan ikkilisiyoyi za su san cewa ni ne mai bincika zukata da tunani, zan kuwa sāka wa kowannenku gwargwadon ayyukansa.

    24 Yanzu, ina ce wa sauranku da kuke a Tiyatira, ku da ba ku riƙe da koyarwarta ba kuma ba ku koyi abin da suke kira zurfafan asiran Shaiɗan, ‘Ba zan ƙara muku wani nauyi ba. 25 Sai dai ku riƙe abin da kuke da shi har sai na zo.’

  11. 10 “Za su ci amma ba za su ƙoshi ba;

    za su shiga karuwanci amma ba za su ƙaru ba,

    gama sun rabu da Ubangiji

    don su ba da kansu 11 ga karuwanci,

    ga tsoho da kuma sabon ruwan inabi,

    waɗanda suka ɗauke ganewar mutanena.

    12 Sun nemi shawarar gunkin da aka yi da itace

    suka kuwa sami amsa daga sanda.

    Halin karuwanci yakan ɓad da su;

    sun yi rashin aminci ga Allahnsu.

    13 Suna miƙa hadaya a kan ƙwanƙolin duwatsu

    suna kuma ƙone hadayu a kan tuddai,

    a ƙarƙashin itatuwa oak, aduruku da katambiri,

    inda inuwa take da daɗi.

    Saboda haka ’ya’yanku mata suka juya wa karuwanci

    surukanku mata kuma suka shiga yin zina.

    14 “Ba zan hukunta ’ya’yanku mata

    sa’ad da suka juya ga yin karuwanci ba,

    balle surukanku mata,

    sa’ad da suka yi zina,

    gama mazan da kansu suna ma’amala da karuwai

    suna kuma miƙa hadaya tare da karuwai na masujada,

    mutane marasa ganewa za su lalace!

  12. 11 Ya amsa ya ce, “Duk wanda ya saki matarsa, ya auri wata, yana da laifin aikata zina a kan matar da ya saki. 12 In kuma ta saki mijinta ta auri wani, ta yi zina ke nan.”

  13. 3 Sai malaman dokoki da Farisiyawa suka kawo wata macen da aka kama a zina. Suka sa ta tsaya a gaban taron 4 suka kuma ce wa Yesu, “Malam, an kama wannan mace tana zina. 5 A cikin Doka Musa ya umarce mu, mu jajjefe irin waɗannan mata. To, me ka ce?” 6 Sun yi wannan tambaya ce don su sa masa tarko, don su sami hanyar zarge shi.

    Amma Yesu ya sunkuya ya fara rubutu a ƙasa da yatsarsa. 7 Da suka ci gaba da yin masa tambayoyi, sai ya miƙe tsaye ya ce musu, “In da wani a cikinku da ba shi da zunubi, sai yă fara jifanta da dutse.” 8 Sai ya sāke sunkuyawa ya kuma yi rubutu a ƙasa.

    9 Da jin haka, waɗanda suka ji sai suka fara tashi daga wurin ɗaya-ɗaya, tun daga babbansu har ya zuwa ƙaraminsu, sai da aka bar Yesu kaɗai, tare da macen tsaye a wurin. 10 Sai Yesu ya miƙe tsaye ya tambaye ta ya ce, “Mace, ina suke? Ba wanda ya hukunta ki?”

    11 Ta ce, “Ba kowa, ranka yă daɗe.”

    Sai Yesu ya ce, “Haka ni ma ban hukunta ki ba. Ki tafi, ki daina rayuwar zunubi.”

  14. 6 To, waɗannan abubuwa misalai ne a gare mu, kada mu yi marmarin mugayen abubuwa, kamar yadda suka yi. 7 Kada ku zama masu bautar gumaka, yadda waɗansunsu suka zama; kamar yadda yake a rubuce cewa, “Mutanen suka zauna don su ci su kuma sha, suka kuma tashi suka shiga rawa ta rashin kunya.” 8 Kada fa mu yi fasikanci yadda waɗansunsu suka yi, har a rana guda mutane dubu ashirin da uku a cikinsu suka mutu. 9 Kada mu gwada Kiristi yadda waɗansunsu suka yi, har macizai suka kakkashe su. 10 Kada kuma ku yi gunaguni yadda waɗansunsu suka yi, har mala’ika mai hallakarwa ya hallaka su. 11 Waɗannnan abubuwa sun same su ne, domin su zama abubuwan koyi, aka kuma rubuta su domin a gargaɗe mu, mu da ƙarshen zamani ya zo mana. 12 Saboda haka in kana tsammani kana tsaye ne, to, ka yi hankali kada ka fāɗi! 13 Ba jarrabar da ta taɓa samunku, wadda ba a saba yi wa mutum ba. Allah mai aminci ne; ba zai bari a jarrabce ku fiye da ƙarfinku ba. Amma in aka jarrabce ku, zai nuna muku mafita, domin ku iya cin nasara.

    14 Saboda haka abokaina ƙaunatattu, ku guje wa bautar gumaka.

  15. 14 Ta wurin ikonsa, Allah ya tashe Ubangiji daga matattu, haka zai tashe mu mu ma. 15 Ba ku sani ba cewa jikunanku gaɓoɓin Kiristi ne kansa? Zai kyautu in ɗauki gaɓoɓin Kiristi in haɗa da jikin karuwa? Sam! 16 Ba ku san cewa shi wanda ya haɗa jikinsa da karuwa sun zama ɗaya a cikin jiki ke nan ba? Gama an ce, “Biyun za su zama jiki ɗaya.” 17 Wanda kuwa ya haɗa jikinsa da Ubangiji ya zama ɗaya da shi ke nan a ruhu.

    18 Ku guji fasikanci. Duk sauran zunubai da mutum yakan aikata suna waje da jikinsa, amma mai yin fasikanci, yana ɗaukar alhalin jikinsa ne. 19 Ba ku san cewa jikin nan naku haikalin Ruhu Mai Tsarki ba ne wanda yake cikinku yake kuma daga Allah? Ku ba na kanku ba ne; 20 saye ku fa aka yi da tsada, saboda haka, sai ku girmama Allah da jikinku.

  16. 22 In aka kama wani yana kwance da matar wani, dole a kashe dukansu biyu, wato, mutumin da ya kwana da matar da kuma matar. Dole a fid da mugu daga Isra’ila.

    23 In mutum ya sadu da budurwa a gari wadda aka yi alkawarin aure, ya kuma kwana da ita 24 sai ku ɗauki su biyu zuwa ƙofar wannan gari, ku jajjefe su da dutse har su mutum, za a kashe yarinyar domin tana a cikin gari ba ta kuwa yi ihu neman taimako ba, za a kashe mutumin domin ya yi lalata da matar wani. Dole ku fi da mugu daga cikinku.

    25 Amma in a bayan gari ne mutumin ya sadu da yarinyar da aka yi alkawari aure, ya kuma yi mata fyaɗe, mutumin da ya yi wannan ne kaɗai zai mutu.

  17. 1 To, game da zancen da kuka rubuto. Yana da kyau mutum yă zauna ba aure. 2 Amma da yake fasikanci ya yi yawa, ya kamata kowane mutum yă kasance da matarsa, kowace mace kuma da mijinta. 3 Ya kamata miji yă cika hakkinsa na aure ga matarsa. Haka kuma matar ta yi ga mijinta. 4 Jikin matar ba nata ne kaɗai ba, amma na mijinta ne ma. Haka ma jikin mijin, ba na shi ne kaɗai ba, amma na matarsa ne ma. 5 Kada ku ƙi kwana da juna sai ko kun yarda a junanku kuma na ɗan lokaci, don ku himmantu ga addu’a. Sa’an nan ku sāke haɗuwa don kada Shaiɗan yă jarrabce ku saboda rashin ƙamewarku.

  18. 4 Ku mazinata, ba ku san cewa abokantaka da duniya gāba ce da Allah ba? Duk wanda ya zaɓa yă zama abokin duniya ya zama abokin gāban Allah ke nan. 5 Ko kuna tsammani a banza ne Nassi ya ce ruhun da ya sa yă zauna a cikinmu yana kishi sosai? 6 Amma yakan ba mu alheri a yalwace. Shi ya sa Nassi ya ce,

    “Allah yana gāba da masu girman kai

    amma yakan ba da alheri ga masu tawali’u.”

    7 Saboda haka, ku miƙa kanku ga Allah. Ku yi tsayayya da Iblis, zai kuwa guje ku.

  19. 9 “In sha’awar mace ya shiga mini zuciya,

    ko kuma na laɓe a ƙofar maƙwabcina,

    10 sai matata ta niƙa hatsin wani

    kuma waɗansu maza su kwana da ita.

    11 Gama wannan zai zama abin kunya,

    zunubin da za a yi shari’a a kai.

    12 Wuta ce take ƙuna har ta hallakar;

    za tă cinye saiwar abin da na shuka ƙurmus.

  20. 9 Me ya sa ka rena maganar Ubangiji ta wurin yin mugunta haka a idonsa? Ka kashe Uriya mutumin Hitti da takobi, ka kuma ɗauki matarsa tă zama matarka. Ka kashe shi da takobin Ammonawa. 10 To, fa, takobi ba zai taɓa rabu da gidanka ba, domin ka rena ni, ka kuma ƙwace matar Uriya mutumin Hitti ta zama matarka.’

    11 “Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Daga cikin iyalinka zan kawo masifa a kanka. A idanunka zan ɗauki matanka in ba wa wani da yake kusa da kai, zai kuwa kwana da su da rana tsaka. 12 Ka aikata wannan a ɓoye, amma zan aikata wannan da rana tsaka, a gaban dukan Isra’ila.’ ”

    13 Sai Dawuda ya ce wa Natan, “Na yi wa Ubangiji zunubi.”

    Natan ya ce, “Ubangiji ya yafe maka zunubin. Ba za ka mutu ba. 14 Amma saboda ka yi haka ka sa abokan gāba suka rena Ubangiji, yaron da aka haifa maka zai mutu.”

  21. 17 Ba ku gane cewa duk abin da ya shiga baki yakan wuce ciki ne daga nan kuma yă fita daga jiki ba? 18 Amma abubuwan da suke fitowa ta baki suna fitowa ne daga zuciya, su ne kuma suke ƙazantar da mutum. 19 Gama daga zuciya ne mugayen tunani, kisankai, zina, fasikanci, sata, shaidar ƙarya, ɓatan suna, suka fitowa. 20 Waɗannan su ne suke ƙazantar da mutum; amma cin abinci ba tare da wanke hannuwa ba, ba ya ƙazantar da mutum.”

  22. 1 Maganar Ubangiji da ta zo wa Hosiya ɗan Beyeri a zamanin mulkin Uzziya, Yotam, Ahaz da Hezekiya, sarakunan Yahuda, da zamanin mulkin Yerobowam ɗan Yowash sarkin Isra’ila.

    2 Sa’ad da Ubangiji ya fara magana ta wurin Hosiya, Ubangiji ya ce masa, “Ka tafi, ka auro wa kanka mazinaciya da ’ya’yan da aka haifa ta hanyar rashin aminci, domin ƙasar tana da laifin mummunan zina ta wurin rabuwa da Ubangiji.” 3 Saboda haka sai ya auri Gomer ’yar Dibilayim, ta kuwa yi ciki ta haifi ɗa namiji.

  23. 18 “Duk wanda ya saki matarsa ya auri wata mace, zina ne yake yi. Kuma mutumin da ya auri macen da aka sake, zina ne yake yi.

  24. 2 Misali, bisa ga doka mace mai aure tana daure ga mijinta muddin mijin yana da rai, amma in mijinta ya mutu, an sake ta ke nan daga dokar aure. 3 Saboda haka fa, in ta auri wani yayinda mijinta yana raye, za a ce da ita mazinaciya. Amma in mijinta ya mutu, an sake ta ke nan daga wannan doka, ita kuwa ba mazinaciya ba ce, ko da yake ta auri wani.

  25. 19 Ayyukan mutuntaka kuwa a fili suke. Wato, fasikanci, ƙazanta da kuma lalata; 20 bautar gumaka da sihiri; ƙiyayya, faɗa, kishi, fushi mai zafi, sonkai, tsattsaguwa, hamayya, 21 da ƙyashi; buguwa, shashanci, da ire-irensu. Na gargaɗe ku, yadda na yi a dā, cewa masu irin wannan rayuwa ba za su gāji mulkin Allah ba.

  26. 3 Nufin Allah ne a tsarkake ku, cewa ku guje wa fasikanci; 4 don kowannenku yă koya yadda zai ƙame kansa a hanyar da take mai tsarki, mai mutunci kuma, 5 ba cikin muguwar sha’awa kamar ta marasa bangaskiya, waɗanda ba su san Allah ba; 6 cikin wannan al’amari kuwa kada wani yă yi wa ɗan’uwansa laifi ko yă cuce shi. Ubangiji zai hukunta mutane saboda dukan irin waɗannan zunubai, kamar yadda muka riga muka gaya muku, muka kuma yi muku gargaɗi. 7 Gama Allah bai kira mu ga zaman marasa tsarki ba, sai dai ga zaman tsarki.

  27. 18 Kada ka yi zina.

  28. 37 gama sun yi zina kuma jinin yana a hannuwansu. Sun yi zina da gumakansu; har suka miƙa ’ya’yansu da suka haifa mini, su zama musu abinci.

  29. 18 Wani mai mulki ya tambayi Yesu ya ce, “Malam managarci, me zan yi don in gāji rai madawwami?”

    19 Yesu ya amsa ya ce, “Don me kake kira na managarci? Ai, ba wani nagari, sai Allah kaɗai. 20 Ka san dokokin da suka ce, ‘Kada ka yi zina, kada ka yi kisankai, kada ka yi sata, kada ka ba da shaida ta ƙarya, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’ ”

  30. 7 “Me zai sa in gafarta muku?

    ’Ya’yanku sun yashe ni

    sun yi rantsuwa da allolin da ba alloli ba ne.

    Na biya musu dukan bukatunsu,

    duk da haka suka yi zina

    suka tattaru a gidajen karuwai.

    8 An ciyar da su sosai, kamar ƙosassun ingarmu,

    masu jaraba,

    kowanne yana haniniya, yana neman matar maƙwabcinsa.

  31. 2 “Ka tsawata wa mahaifiyarka, ka tsawata mata,

    gama ita ba matata ba ce,

    ni kuma ba mijinta ba ne.

    Ku roƙe ta tă daina karuwancinta

    da kuma rashin aminci a tsakanin nononta.

    3 In ba haka ba zai tuɓe ta tsirara

    in bar ta kamar yadda take a ranar da aka haife ta;

    zan sa ta zama kamar hamada,

    in mayar da ita busasshiyar ƙasar,

    in kashe ta da ƙishirwa.

    4 Ba zan nuna wa ’ya’yanta ƙaunata ba,

    domin su ’ya’yan zina ne.

    5 Mahaifiyarsu ta yi rashin aminci

    ta kuma ɗauki cikinsu ta wurin yi abin kunya.

    Ta ce, ‘Zan bi kwartayena,

    waɗanda suke ba ni abinci da ruwa,

    ulu nawa da lilina, mai nawa da kuma abin sha na.’

    6 Saboda haka zai tare hanyarta da ƙaya;

    zan yi mata katanga don kada tă sami hanya.

    7 Za tă bi kwartayenta amma ba za tă kama su ba;

    za tă neme su amma ba za tă same su ba.

    Sa’an nan za tă ce,

    ‘Zan koma ga mijina na fari,

    gama dā ya fi mini yadda nake a yanzu.’

  32. 20 Ya ci gaba, “Abin da yake fitowa daga mutum ne yake ƙazantar da shi. 21 Gama daga ciki, daga zuciyar mutane, mugayen tunani suke fitowa, fasikanci, sata, kisankai, zina, 22 kwaɗayi, ƙeta, ruɗu, ƙazantaccen sha’awa, kishi, ɓata suna, girman kai da kuma wauta. 23 Duk waɗannan mugayen abubuwa daga cikin suke fitowa, suna kuma ƙazantar da mutum.”

  33. 38 Sa’an nan waɗansu Farisiyawa da malaman dokoki suka ce masa, “Malam, muna so mu ga wata alama mai banmamaki daga gare ka.”

    39 Sai ya amsa ya ce, “Mugaye da masu zinan zamanin nan suna neman wata alama mai banmamaki! Amma babu wadda za a nuna musu, sai dai alama ta annabi Yunana.

  34. 18 Mutumin ya yi tambaya ya ce, “Waɗanne?”

    Yesu ya amsa ya ce, “ ‘Kada ka yi kisankai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka yi shaidar ƙarya,

  35. 22 Nan take, ya bi ta

    kamar saniyar da za a kai mayanka,

    kamar wawa zuwa wurin da za a ba shi horo

    23 sai da kibiya ta soki hantarsa,

    kamar tsuntsun da ya ruga cikin tarko,

    ba tare da sani zai zama sanadin ransa ba.

    24 Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni;

    ku kasa kunne ga abin da nake faɗa.

    25 Kada ku bar zuciyarku ta juya zuwa hanyoyinta

    ko ku kauce zuwa hanyoyinta.

    26 Ta zama sanadin fāɗuwar yawanci;

    kisan da ta yi ba ta ƙidayuwa.

    27 Gidanta babbar hanya ce zuwa kabari

    mai yin jagora zuwa ɗakunan lahira.

  36. 13 “A cikin annabawan Samariya

    na ga wannan abin banƙyama.

    Suna annabci ta wurin Ba’al

    suna ɓad da mutanena Isra’ila.

    14 A cikin annabawan Urushalima kuma

    na ga wani abin bantsoro.

    Suna zina suna kuma rayuwar ƙarya.

    Sun ƙarfafa hannuwa masu aikata mugunta,

    domin kada wani ya juya daga muguntarsa.

    Dukansu sun yi kama da Sodom a gare ni;

    mutanen Urushalima sun yi kama da Gomorra.”

  37. 19 Ka san dokokin da suka ce, ‘Kada ka yi kisankai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka ba da shaida ta ƙarya, kada ka cuci wani, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’”

  38. 10 Ga waɗanda suke da aure kuwa ina ba da wannan umarni (ba ni ba, amma Ubangiji) cewa kada mace ta rabu da mijinta. 11 In kuwa ta rabu da shi, sai ta kasance ba aure, ko kuma ta sāke shiryawa da mijinta. Kada miji kuma yă saki matarsa.

  39. 10 Gama duk wanda ya kiyaye dukan doka amma ya yi tuntuɓe a kan abu ɗaya kaɗai, ya zama mai laifin karya dukansu ke nan. 11 Gama shi da ya ce, “Kada ka yi zina,” shi ne kuma ya ce, “Kada ka yi kisankai.” In kuwa ba ka zina amma kana kisankai, ka zama mai karya doka ke nan.

  40. 13 Za a yi musu sakamako da muguntar da suka yi. A ra’ayinsu jin daɗi shi ne a yi annashuwa da rana tsaka. Su ƙazamai ne marasa kunya, suna cike da jin daɗin sha’awace-sha’awacensu yayinda suke cin biki tare da ku. 14 Idanunsu sun cike da zina, ba sa ƙoshi da yin zunubi; suna jarrabtar waɗanda ba tsayayyu ba; gwanaye ne a kan kwaɗayi, la’anannun iri! 15 Sun bar miƙaƙƙiyar hanya suka bauɗe suna bin hanyar Bala’am ɗan Beyor, wanda ya yi ƙaunar hakkin mugunta.

  41. 20 “ ‘Kada ka yi jima’i da matar maƙwabcinka ka ƙazantar da kanka tare da ita.

  42. 14 Bakin mazinaciya rami ne mai zurfi;

    duk wanda yake a ƙarƙashin fushin Ubangiji zai fāɗa a ciki.

  43. 22 Saboda su, dukan masu zaman bauta daga Yahuda waɗanda suke a Babilon za su yi amfani da wannan la’ana cewa, ‘Ubangiji ka yi da mu kamar Zedekiya da Ahab waɗanda sarkin Babilon ya ƙone da wuta.’ 23 Gama sun aikata munanan abubuwa a Isra’ila; sun yi zina da matan maƙwabtansu kuma da sunana suka yi ƙarya, waɗanda ban faɗa musu su yi ba. Na san wannan kuma ni shaida ne ga haka,” in ji Ubangiji.

  44. 32 “ ‘Ke mazinaciyar mace! Kin gwammace baƙi a maimakon mijinki!

  45. 1 Ku ji maganar Ubangiji, ku Isra’ilawa,

    gama Ubangiji yana da tuhumar da zai kawo

    a kan ku waɗanda suke zama a ƙasar.

    “Babu aminci, babu ƙauna,

    babu yarda da Allah a cikin ƙasar.

    2 Akwai la’ana ce kawai, yin ƙarya da kisa,

    yin sata da zina;

    sun wuce gona da iri,

    kisankai a kan kisankai.

  46. 13 Ga kuma wani abin da kuke yi. Kukan cika bagaden Ubangiji da hawaye. Kukan yi kuka kuna ihu gama Ubangiji ba ya mai da hankali ga hadayunku ko yă karɓe su da farin ciki. 14 Kukan ce, “Don me ba ya karɓan hadayunmu?” Ai, domin Ubangiji ya zama shaida tsakaninka da matar ƙuruciyarka, gama ka keta amanar da ka yi mata, ko da yake ita abokiyar zamanka ce, matar aurenka ta alkawari.

    15 Ashe, Ubangiji bai maishe su ɗaya ba? Cikin jiki da ruhu, su nasa ne. Me ya sa suke ɗaya? Domin yana neman ’ya’ya masu tsoron Allah. Saboda haka sai ka lura da kanka, kada kuma ka ci amanar matar ƙuruciyarka.

    16 “Na ƙi kisan aure,” in ji Ubangiji, Allah na Isra’ila. “Na kuma ƙi mutumin da ya rufe kansa da tashin hankali kamar riga,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.

    Saboda haka sai ka lura da kanka, kada kuma ka ci amana.

  47. 22 Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mace daga haƙarƙarin da ya ɗauko daga mutumin, ya kuwa kawo ta wurin mutumin.

    23 Sai mutumin ya ce,

    “Yanzu kam wannan ƙashi ne na ƙasusuwana

    nama kuma na namana.

    Za a ce da ita ‘mace,’

    gama an ciro ta daga namiji.”

    24 Wannan ne ya sa mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa, su kuma zama jiki ɗaya.

  48. 7 bayan an ɗan jima sai matar maigidansa ta fara sha’awar Yusuf, sai ta ce, “Zo ka kwana da ni!”

    8 Amma ya ƙi. Ya ce mata, “Ga shi kome yana a ƙarƙashina, don haka ne ma maigidana bai dami kansa da wani abu a cikin gidan nan ba; kome da ya mallaka, ya danƙa ga kulawata. 9 Babu wani da ya fi ni a wannan gida. Maigidana bai hana ni kome ba sai ke, saboda ke matarsa ce. Yaya fa, zan yi irin wannan mugun abu, in yi zunubi wa Allah?” 10 Ko da yake ta yi ta yin wa Yusuf maganar kowace rana, amma ya ƙi yă kwana da ita, ko ma yă zauna da ita.

    11 Wata rana, ya shiga cikin gida don yă yi ayyukansa, ba wani daga cikin bayin gidan da yake ciki. 12 Sai ta cafke shi a riga, ta ce, “Zo ka kwana da ni!” Amma ya bar rigarsa a hannunta, ya gudu ya fita daga gidan.

  49. 1 Da bazara, a lokacin da sarakuna sukan fita zuwa yaƙi, sai Dawuda ya aiki Yowab tare da mutanen sarki, da dukan Isra’ila. Suka je suka hallaka Ammonawa, suka kuma yi wa Rabba kwanton ɓauna. Amma Dawuda ya yi zamansa a Urushalima.

    2 Wata rana da yamma, Dawuda ya tashi daga gadonsa, ya zaga kewaye a rufin fadansa. Daga rufin ya ga wata mace tana wanka. Matar kyakkyawa ce ƙwarai. 3 Sai Dawuda ya aiki wani yă bincika ko wace ce ita, sai mutumin ya dawo ya ce, “Wannan ba Batsheba ba ce, ’yar Eliyam matar Uriya, mutumin Hitti?” 4 Sa’an nan Dawuda ya aiki manzanni su kawo masa ita. Ta zo wurinsa shi kuma ya kwana da ita (A lokacin kuwa ta gama tsarkake kanta ke nan daga jinin haila.) Sa’an nan ta tafi gida. 5 Matar ta yi ciki, ta kuwa aika wa Dawuda, tana cewa, “Ina da ciki.”

  50. 15 Idanun mazinaci suna jiran yamma ta yi sosai;

    yana tunani cewa, ‘Ba wanda zai gan ni,’

    sai kuma yă ɓoye fuskarsa.

    16 Cikin duhu mutane suna fasa gidaje,

    amma da rana sukan kulle kansu;

    ba sa so wani abu yă haɗa su da haske.

    17 Gama dukansu, duhu mai yawa shi ne safiyarsu;

    suna abokantaka da razanar duhu.

    18 “Duk da haka kamar abu marar nauyi suke a kan ruwa;

    gefen ƙasar da suke, an la’anta ta,

    yadda ba wanda yake zuwa gonar inabinsu.

  51. 1 Ruhun Ubangiji Mai Iko Duka yana a kaina,

    domin Ubangiji ya shafe ni

    domin in yi wa’azi labari mai daɗi ga matalauta.

    Ya aiko ni in warkar da waɗanda suka karai a zuci,

    don in yi shelar ’yanci don ɗaurarru

    in kuma kunce ’yan kurkuku daga duhu

    2 don in yi shelar shekarar tagomashin Ubangiji

    da kuma ranar ɗaukan fansar Allahnmu,

    don in ta’azantar da dukan waɗanda suke makoki,

    3 in tanada wa waɗanda suke baƙin ciki a Sihiyona,

    in maido musu rawani mai kyau

    a maimako na toka,

    man murna

    a maimako na makoki,

    da kuma rigar yabo

    a maimako na ruhun fid da zuciya.

    Za a ce da su itatuwan oak na adalci,

    shukin Ubangiji

    don bayyana darajarsa.

  52. 9 “ ‘Za ku yi sata da kisa, ku yi zina da rantsuwar ƙarya, kuna ƙone turare wa Ba’al kuna kuma bin waɗansu allolin da ba ku sani ba, 10 sa’an nan ku zo ku tsaya a gabana a wannan gida, wanda ake kira da Sunana, kuna cewa, “An cece mu,” mun dace mu aikata waɗannan abubuwa banƙyama?

  53. 27 zinace zinacenku da haniniya kamar dawakai,

    karuwancinku na bankunya!

    Na ga ayyukanku na banƙyama

    a kan tuddai da kuma a filaye.

    Kaitonki, ya Urushalima!

    Har yaushe za ki ci gaba da rashin tsarki?”

  54. 3 Waɗansu Farisiyawa suka zo wurinsa don su gwada shi. Suka yi tambaya suka ce, “Daidai ne mutum yă saki matarsa saboda wani dalili da kuma a kan kowane dalili?”

    4 Ya amsa ya ce, “Ba ku taɓa karantawa ba ne cewa, a farkon halitta, Mahalicci ‘ya yi su namiji da ta mace,’ 5 ya kuma ce, ‘Saboda wannan dalili, namiji zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa yă manne wa matarsa, biyun kuwa su zama jiki guda’? 6 Ta haka, ba sa ƙara zama biyu, sai dai ɗaya. Saboda haka abin da Allah ya haɗa fa, kada mutum yă raba.”

  55. 15 Amma in marar bi ɗin ya raba auren, a ƙyale shi. A irin wannan hali, babu tilas a kan wani, ko wata mai bi. Allah ya kira mu ga zaman lafiya ne.

  56. 17 Kada mutumin Isra’ila ko mutuniyar Isra’ila yă zama karuwar haikali. 18 Kada ku kawo kuɗin a cikin gida Ubangiji Allahnku da aka samu ta wurin karuwanci wanda mace ko namiji ya yi don biyan wani alkawari, domin Ubangiji Allahnku yana ƙyamar su duka.

  57. 18 “Akwai abubuwa uku da suke ba ni mamaki,

    abubuwa huɗu da ba na iya fahimtarsu,

    19 yadda gaggafa take firiya a sararin sama,

    yadda maciji yake tafiya a kan dutse,

    yadda jirgin ruwa yake tafiya a teku,

    da kuma sha’ani tsakanin namiji da ’ya mace.

    20 “Ga yadda mazinaciya take yi.

    Takan ci ta share bakinta

    ta ce, ‘Ban yi wani abu marar kyau ba.’

  58. 1 a duka sa’ad da zan warkar da Isra’ila,

    zunuban Efraim za su tonu

    za a kuma bayyana laifofin Samariya.

    Suna ruɗu,

    ɓarayi sukan fasa su shiga gidaje,

    ’yan fashi sukan yi fashi a tituna;

    2 amma ba su gane

    cewa na tuna da dukan ayyukan muguntarsu ba.

    Zunubansu sun kewaye su;

    kullum suna a gabana.

    3 “Suna faranta wa sarki zuciya da muguntarsu,

    shugabanni kuma da ƙarairayinsu.

    4 Dukansu mazinata ne

    suna ƙuna kamar matoya

    wadda mai gashin burodi ba ya bukata yă tura mata wuta

    daga cuɗe kullu har kumburinsa.

  59. 5 “Ta haka zan zo kusa da ku don in yi hukunci. Zan hanzarta ba da shaida a kan masu yin sihiri, da mazinata da masu shaidar zur. Zan ba da shaida a kan waɗanda suke zaluntar ma’aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye da marayu, suna kuma hana baƙi samun adalci, ba sa ma tsorona,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.

  60. 22 Kai da kake cewa wa mutane kada su yi zina, kana yin zina? Kai da kake ƙyamar gumaka, kana wa haikali fashi?

  61. 9 Umarnan nan, “Kada ka yi zina.” “Kada ka yi kisankai.” “Kada ka yi sata.” “Kada kuma ka yi ƙyashi.” Da dai duk sauran umarnai an ƙunshe su ne a wannan kalma “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”

  62. 16 Ke mace, kin sani ne, ko ke ce za ki ceci mijinki? Kai miji, ka sani ne, ko kai ne za ka ceci matarka?

  63. 17 To, ina dai faɗa muku, ina kuma nace faɗa muku a cikin Ubangiji, cewa kada ku ci gaba da yin rayuwa kamar yadda Al’ummai suke yi, masu banzan tunani. 18 Suna a cikin duhu a fahimtarsu, kuma a rabe suke daga ran Allah saboda jahilcin da yake cikinsu ta dalilin taurarewar zukatansu. 19 Ba sa damu da wani abu ko mai kyau ko marar kyau. Rayukansu sun cika da kowace irin ƙazanta da haɗama.

    20 Amma ba abin da aka koya muku ke nan ba sa’ad da kuka zo ga sanin Kiristi.

  64. 15 Kada ku ƙaunaci duniya, ko wani abin da yake cikinta. In wani yana ƙaunar duniya, ƙaunar Uba ba ta cikinsa. 16 Gama duk abin da yake na duniya, kamar sha’awace-sha’awacen mutuntaka, sha’awar idanunsa, da kuma taƙama da abin da yake da shi, yake kuma yi, ba daga wurin Uba suke fitowa ba sai dai daga duniya. 17 Duniya da sha’awace-sha’awacenta suna shuɗewa, amma mutumin da yake aikata nufin Allah, zai rayu har abada.

  65. 8 Amma matsorata, da marasa bangaskiya, masu ƙazanta, masu kisankai, masu fasikanci, masu sihiri, masu bautar gumaka da dukan maƙaryata, wurinsu zai kasance a cikin tafkin wutar da yake farar wuta mai ci. Wannan fa ita ce mutuwa ta biyu.”