42 Bible Verses About Prostitution
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
9 Ba ku sani ba cewa mugaye ba za su gāji mulkin Allah ba? Kada fa a ruɗe ku. Ba masu fasikanci ko masu bautar gumaka ko masu zina ko karuwan maza, ko ’yan daudu, 10 ko ɓarayi ko masu kwaɗayi ko mashaya ko masu ɓata suna ko masu zamba da za su gāji mulkin Allah. 11 Haka waɗansu a cikinku ma suke a dā. Amma an wanke ku, an tsarkake ku, aka kuma sa kuka zama marasa laifi cikin sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma ta wurin Ruhun Allahnmu.
-
15 Ba ku sani ba cewa jikunanku gaɓoɓin Kiristi ne kansa? Zai kyautu in ɗauki gaɓoɓin Kiristi in haɗa da jikin karuwa? Sam! 16 Ba ku san cewa shi wanda ya haɗa jikinsa da karuwa sun zama ɗaya a cikin jiki ke nan ba? Gama an ce, “Biyun za su zama jiki ɗaya.” 17 Wanda kuwa ya haɗa jikinsa da Ubangiji ya zama ɗaya da shi ke nan a ruhu.
18 Ku guji fasikanci. Duk sauran zunubai da mutum yakan aikata suna waje da jikinsa, amma mai yin fasikanci, yana ɗaukar alhalin jikinsa ne. 19 Ba ku san cewa jikin nan naku haikalin Ruhu Mai Tsarki ba ne wanda yake cikinku yake kuma daga Allah? Ku ba na kanku ba ne; 20 saye ku fa aka yi da tsada, saboda haka, sai ku girmama Allah da jikinku.
-
23 Gama waɗannan umarnai fitila ne,
wannan koyarwa haske ne,
kuma gyare-gyaren horo
hanyar rayuwa ce,
24 suna kiyaye ka daga mace marar ɗa’a
daga sulɓin harshen mace marar aminci.
25 Kada ka yi sha’awarta a cikin zuciyarka
kada ka bar ta tă ɗauki hankalinka da idanunta.
26 Gama karuwa takan mai da kai kamar burodin kyauta,
mazinaciya kuma takan farauci ranka.
27 Mutum zai iya ɗiba wuta ya zuba a cinyarsa
ba tare da rigunansa sun ƙone ba?
28 Mutum zai iya yin tafi a garwashi wuta mai zafi
ba tare da ƙafafunsa sun ƙone ba?
29 Haka yake da wanda ya kwana da matar wani;
babu wanda ya taɓa ta da zai tafi babu hukunci.
-
19 Ayyukan mutuntaka kuwa a fili suke. Wato, fasikanci, ƙazanta da kuma lalata; 20 bautar gumaka da sihiri; ƙiyayya, faɗa, kishi, fushi mai zafi, sonkai, tsattsaguwa, hamayya, 21 da ƙyashi; buguwa, shashanci, da ire-irensu. Na gargaɗe ku, yadda na yi a dā, cewa masu irin wannan rayuwa ba za su gāji mulkin Allah ba.
-
3 Sai malaman dokoki da Farisiyawa suka kawo wata macen da aka kama a zina. Suka sa ta tsaya a gaban taron 4 suka kuma ce wa Yesu, “Malam, an kama wannan mace tana zina. 5 A cikin Doka Musa ya umarce mu, mu jajjefe irin waɗannan mata. To, me ka ce?” 6 Sun yi wannan tambaya ce don su sa masa tarko, don su sami hanyar zarge shi.
Amma Yesu ya sunkuya ya fara rubutu a ƙasa da yatsarsa. 7 Da suka ci gaba da yin masa tambayoyi, sai ya miƙe tsaye ya ce musu, “In da wani a cikinku da ba shi da zunubi, sai yă fara jifanta da dutse.” 8 Sai ya sāke sunkuyawa ya kuma yi rubutu a ƙasa.
9 Da jin haka, waɗanda suka ji sai suka fara tashi daga wurin ɗaya-ɗaya, tun daga babbansu har ya zuwa ƙaraminsu, sai da aka bar Yesu kaɗai, tare da macen tsaye a wurin. 10 Sai Yesu ya miƙe tsaye ya tambaye ta ya ce, “Mace, ina suke? Ba wanda ya hukunta ki?”
11 Ta ce, “Ba kowa, ranka yă daɗe.”
Sai Yesu ya ce, “Haka ni ma ban hukunta ki ba. Ki tafi, ki daina rayuwar zunubi.”
-
17 Kada mutumin Isra’ila ko mutuniyar Isra’ila yă zama karuwar haikali. 18 Kada ku kawo kuɗin a cikin gida Ubangiji Allahnku da aka samu ta wurin karuwanci wanda mace ko namiji ya yi don biyan wani alkawari, domin Ubangiji Allahnku yana ƙyamar su duka.
-
28 “Me kuka gani? An yi wani mutum wanda yake da ’ya’ya biyu maza. Sai ya je wajen ɗan farin ya ce, ‘Ɗana, yau tafi gonar inabi ka yi aiki.’
29 “Ya amsa ya ce, ‘Ba zan tafi ba,’ amma daga baya ya sāke tunani, ya tafi.
30 “Sai mahaifin ya tafi waje na biyun ya faɗa masa iri magana guda. Sai ya amsa ya ce, ‘Zan tafi, ranka yă daɗe,’ amma bai tafi ba.
31 “Wanne cikin yaran nan biyu ya yi abin da mahaifinsa yake so?”
Suka amsa, “Na farin.”
Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, masu karɓar haraji da karuwai suna riga ku shiga mulkin Allah. 32 Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo wurinku don yă nuna muku hanyar adalci, ba ku gaskata shi ba, amma masu karɓar haraji da karuwai sun gaskata. Har ma bayan kun ga wannan, ba ku tuba kun gaskata shi ba.”
-
29 “ ‘Kada ka ƙasƙantar da ’yarka ta wurin mai da ita karuwa, in ba haka ba ƙasar za tă juya ga karuwanci tă kuma cika da mugunta.
-
10 “Za su ci amma ba za su ƙoshi ba;
za su shiga karuwanci amma ba za su ƙaru ba,
gama sun rabu da Ubangiji
don su ba da kansu 11 ga karuwanci,
ga tsoho da kuma sabon ruwan inabi,
waɗanda suka ɗauke ganewar mutanena.
12 Sun nemi shawarar gunkin da aka yi da itace
suka kuwa sami amsa daga sanda.
Halin karuwanci yakan ɓad da su;
sun yi rashin aminci ga Allahnsu.
13 Suna miƙa hadaya a kan ƙwanƙolin duwatsu
suna kuma ƙone hadayu a kan tuddai,
a ƙarƙashin itatuwa oak, aduruku da katambiri,
inda inuwa take da daɗi.
Saboda haka ’ya’yanku mata suka juya wa karuwanci
surukanku mata kuma suka shiga yin zina.
14 “Ba zan hukunta ’ya’yanku mata
sa’ad da suka juya ga yin karuwanci ba,
balle surukanku mata,
sa’ad da suka yi zina,
gama mazan da kansu suna ma’amala da karuwai
suna kuma miƙa hadaya tare da karuwai na masujada,
mutane marasa ganewa za su lalace!
-
25 Ta haka kuma ashe, Rahab karuwan nan ba a ɗauke ta mai adalci ce saboda abin da ta yi ba ne sa’ad da ta ba wa ’yan leƙen asirin nan masauƙi ta kuma sallame su suka tafi ta wata hanya dabam? 26 Kamar yadda jikin da babu ruhu matacce ne, haka ma bangaskiyar da babu ayyuka matacciya ce.
-
1 Ɗaya daga cikin mala’iku bakwai masu ɗauke da kwanoni bakwai nan, ya zo ya ce mini, “Zo, zan nuna maka hukuncin babbar karuwan nan da take zaune a bisan ruwaye masu yawa. 2 Da ita ce sarakunan duniya suka yi zina mazaunan duniya kuma suka bugu da ruwan inabin zinace zinacenta.”
3 Sa’an nan mala’ikan ya ɗauke ni cikin Ruhu zuwa hamada. A can na ga mace zaune a kan wata jan dabbar da aka rufe da sunayen saɓo tana kuma da kawuna bakwai da ƙahoni goma. 4 Macen tana saye da tufafi masu ruwan ja da shunayya, tana ƙyalli da zinariya, duwatsu masu daraja da kuma lu’ulu’ai. Tana riƙe da kwaf na zinariya a hannunta, cike da abubuwa masu banƙyama da kuma ƙazantar zinace zinacenta. 5 Sunan da aka rubuta a goshinta asiri ne,
Babilon mai girma
mahaifiyar karuwai
da kuma na abubuwa masu banƙyama na duniya.
6 Na ga cewa macen ta bugu da jinin tsarkaka, jinin waɗanda suka shaida Yesu.
Da na gan ta, sai na yi mamaki ƙwarai.
-
15 “Ku kula, kada ku yi yarjejjeniya da mazaunan wannan ƙasa, don kada sa’ad da suke yi wa allolinsu sujada, suna miƙa musu hadaya, su gayyace ku, ku ci hadayar da suka miƙa wa allolinsu. 16 Kada ku auro wa ’ya’yanku maza ’yan matansu, waɗanda suke yi wa alloli sujada, har su sa ’ya’yanku su bi allolinsu.
-
1 Wata rana Samson ya tafi Gaza, inda ya ga wata karuwa. Ya shiga wurinta ya kwana. 2 Aka gaya wa mutanen Gaza, “Ai, Samson yana a nan!” Saboda haka suka zo suka kewaye wurin suka yi kwanto dukan dare a bakin ƙofar birni. A daren nan ba su motsa nan da can ba, suna cewa, “Gari yana wayewa za mu kashe shi.”
-
26 Ɗana, ka ba ni zuciyarka
bari kuma idanunka su kiyaye hanyoyina,
27 gama karuwa rami ne mai zurfi
mace marar aminci matsattsiyar rijiya ce.
28 Kamar ’yan fashi, takan kwanta tana jira
tana kuma ninka rashin aminci a cikin maza.
-
3 Duk mai ƙaunar hikima kan kawo wa mahaifinsa farin ciki,
amma wanda yake ma’amala da karuwai kan lalatar da dukiyarsa.
-
9 “ ‘In ’yar firist ta ɓata kanta ta wurin zama karuwa, ta kunyatar da mahaifinta ke nan; dole a ƙone ta da wuta.
-
14 “Ina da hadaya ta salama a gida;
yau zan cika alkawarina.
15 Saboda haka na fito don in sadu da kai;
na neme ka na kuma same ka!
16 Na lulluɓe gadona
da lili masu launi dabam-dabam daga Masar.
17 Na yayyafa turare a gadona
da mur, aloyes da kuma kirfa.
-
13 Wawancin mace a bayyane yake;
ba ta da ɗa’a kuma ba ta da sani.
14 Takan zauna a ƙofar gidanta,
a wurin zama a wurin mafi tsayi na birni,
15 tana kira ga masu wucewa,
waɗanda suke tafiya kai tsaye a hanyarsu.
16 “Bari dukan waɗanda suke marasa azanci su zo cikin nan!”
Tana ce wa marasa hankali.
17 “Ruwan da aka sata ya fi daɗi;
abincin da aka ci a ɓoye ya fi daɗi!”
18 Amma ba su san cewa matattu suna a can ba,
cewa baƙinta suna a can cikin zurfin kabari ba.
-
21 Dubi yadda amintacciyar birni
ta zama karuwa!
Dā ta cika da yin gaskiya;
dā masu adalci a can suke zama,
amma yanzu sai masu kisankai kaɗai!
-
25 “Yayinda ake haka, babban ɗan yana gona. Da ya zo kusa da gida, sai ya ji ana kiɗi ana rawa. 26 Sai ya kira ɗaya daga cikin bayin, ya tambaye shi abin da yake faruwa. 27 Bawan ya ce, ‘Ai, ɗan’uwanka ne ya dawo, shi ne mahaifinka ya yanka ɗan saniya mai ƙiba, gama ya yi murna ya karɓi ɗansa da ya dawo gida lafiyayye, ba abin da ya same shi.’
28 “Sai yayan ya yi fushi, ya ƙi shiga gida. Sai mahaifinsa ya fita ya roƙe shi. 29 Amma ya amsa wa mahaifinsa ya ce, ‘Duba! Duk waɗannan shekaru, ina yin maka aiki kamar bawa, ban taɓa maka rashin biyayya ba. Duk da haka, ba ka taɓa ba ni ko ɗan akuya domin in yi shagali da abokaina ba. 30 Amma da wannan ɗan naka, wanda ya ɓatar da dukiyarka a kan karuwai ya dawo, ka yanka masa ɗan saniya mai ƙiba!’
31 “Sai mahaifin ya ce masa, ‘Ɗana, kullum kana nan tare da ni, kuma duk abin da nake da shi, naka ne. 32 Amma ya zama mana dole, mu yi shagali, mu yi murna, domin ɗan’uwan nan naka, da ya mutu, yanzu kuwa yana da rai, da ya ɓata, amma yanzu an same shi.’ ”
-
16 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Za ka huta tare da kakanninka, waɗannan mutane kuwa ba da daɗewa ba za su yi karuwanci ga baƙin alloli na ƙasar da za su shiga. Za su yashe ni su kuma karya alkawarin da na yi da su.
-
16 Sa’an nan Ubangiji ya naɗa mahukunta, waɗanda suka cece su daga hannun waɗannan musu hari. 17 Duk da haka ba su saurari mahukuntansu ba amma sai suka shiga ha’inci da waɗansu alloli suka kuma bauta musu. Ba kamar kakanninsu ba, nan da nan suka kauce daga hanyar da kakanninsu suka bi, hanyar biyayya ga umarnan Ubangiji.
-
1 A ƙarshe, ’yan’uwa, mun umarce ku yadda za ku yi rayuwa domin ku gamshi Allah, kamar yadda kuke yi. Yanzu muna roƙonku muna kuma gargaɗe ku a cikin Ubangiji Yesu ku yi haka sau da sau. 2 Gama kun san umarnan da muka ba ku ta wurin ikon Ubangiji Yesu.
3 Nufin Allah ne a tsarkake ku, cewa ku guje wa fasikanci; 4 don kowannenku yă koya yadda zai ƙame kansa a hanyar da take mai tsarki, mai mutunci kuma, 5 ba cikin muguwar sha’awa kamar ta marasa bangaskiya, waɗanda ba su san Allah ba; 6 cikin wannan al’amari kuwa kada wani yă yi wa ɗan’uwansa laifi ko yă cuce shi. Ubangiji zai hukunta mutane saboda dukan irin waɗannan zunubai, kamar yadda muka riga muka gaya muku, muka kuma yi muku gargaɗi. 7 Gama Allah bai kira mu ga zaman marasa tsarki ba, sai dai ga zaman tsarki. 8 Saboda haka, duk wanda ya ƙi wannan umarni ba mutum ne ya ƙi ba sai ko Allah, wanda ya ba ku Ruhunsa Mai Tsarki.
-
5 zan yi gāba da wannan mutum da iyalinsa, zan raba shi da kuma duk waɗanda suka bi shi cikin karuwanci ga Molek daga mutanensu.
-
27 Gideyon ya efod da zinariyar, wanda ya ajiye a Ofra, garinsa. Dukan Isra’ila suka shiga yin karuwanci ta wurin yin sujada a can, ya kuwa zama wa Gideyon da dukan iyalinsa tarko.
-
25 Amma ba su yi aminci da Allahn kakanninsu ba, suka kuma yi karuwanci ga waɗansu allolin mutanen ƙasar, waɗanda Allah ya hallaka a gabansu.
-
7 “Me zai sa in gafarta muku?
’Ya’yanku sun yashe ni
sun yi rantsuwa da allolin da ba alloli ba ne.
Na biya musu dukan bukatunsu,
duk da haka suka yi zina
suka tattaru a gidajen karuwai.
8 An ciyar da su sosai, kamar ƙosassun ingarmu,
masu jaraba,
kowanne yana haniniya, yana neman matar maƙwabcinsa.
9 Ba zan hukunta su saboda wannan ba?” In ji Ubangiji.
“Bai kamata in yi ramuwa
a kan irin al’ummar nan ba?
-
8 Amma matsorata, da marasa bangaskiya, masu ƙazanta, masu kisankai, masu fasikanci, masu sihiri, masu bautar gumaka da dukan maƙaryata, wurinsu zai kasance a cikin tafkin wutar da yake farar wuta mai ci. Wannan fa ita ce mutuwa ta biyu.”
-
1 “In mutum ya saki matarsa
ta kuwa bar shi ta auri wani mutum,
zai iya komo da ita kuma?
Ƙasar ba za tă ƙazantu gaba ɗaya ba?
Amma kun yi rayuwa kamar karuwa da masoya masu yawa
yanzu za ki komo wurina?”
In ji Ubangiji.
2 “Ta da idanu ki duba tsaunuka ki gani.
Akwai wani wurin da ba a kwana da ke ba?
A gefen hanya kin zauna kina jiran masoyanki,
kin zauna kamar makiyayi a hamada.
Kin ƙazantar da ƙasar
da karuwancinki da muguntarki.
3 Saboda haka an hana yayyafi,
kuma babu ruwan bazara da ya sauka.
Duk da haka kina da irin kallon da karuwa takan yi;
kin ƙi ki ji kunya.
-
2 Sa’ad da Ubangiji ya fara magana ta wurin Hosiya, Ubangiji ya ce masa, “Ka tafi, ka auro wa kanka mazinaciya da ’ya’yan da aka haifa ta hanyar rashin aminci, domin ƙasar tana da laifin mummunan zina ta wurin rabuwa da Ubangiji.” 3 Saboda haka sai ya auri Gomer ’yar Dibilayim, ta kuwa yi ciki ta haifi ɗa namiji.
-
27 “Kun dai ji an faɗa, ‘Kada ka yi zina.’ 28 Amma ina gaya muku, duk wanda ya dubi mace, sa’an nan ya yi sha’awarta a zuci, ya riga ya yi zina ke nan da ita a zuciyarsa.
-
12 Bayan an daɗe sai matar Yahuda, ’yar Shuwa ta rasu. Sa’ad da Yahuda ya gama makoki, sai ya haura zuwa Timna, zuwa wurin mutanen da suke askin tumakinsa, abokinsa Hira mutumin Adullam kuwa ya tafi tare da shi.
13 Sa’ad da aka faɗa wa Tamar cewa, “Surukinki yana kan hanyarsa zuwa Timna don askin tumakinsa,” 14 sai ta tuɓe rigunan gwaurancinta ta rufe kanta da lulluɓi don ta ɓad da kamanninta, sa’an nan ta je ta zauna a ƙofar shigar Enayim, wadda take a hanyar zuwa Timna. Gama ta lura cewa ko da yake Shela yanzu ya yi girma, ba a ba da ita gare shi ta zama matarsa ba.
15 Sa’ad da Yahuda ya gan ta, ya yi tsammani karuwa ce, gama ta lulluɓe fuskarta. 16 Bai san cewa ita surukarsa ce ba, sai ya ratse zuwa wurinta a gefen hanya ya ce, “Zo mana, in kwana da ke.”
Sai ta ce, “Me za ka ba ni in na kwana da kai?”
17 Ya ce, “Zan aika miki da ɗan akuya daga garkena.”
Sai ta ce, “Za ka ba ni wani abu jingina, kafin ka aika da shi?”
18 Ya ce, “Wace jingina zan ba ki?”
Sai ta amsa, “Hatiminka da ka rataye a wuya da kuma sandan da yake a hannunka.” Ya ba da su gare ta, ya kuma kwana da ita, sai ta yi ciki. 19 Bayan ta tafi, sai ta tuɓe lulluɓin, ta sāke sa tufafin gwaurancinta.
20 Ana cikin haka sai Yahuda ya aika da ɗan akuya ta hannun abokinsa mutumin Adullam don yă karɓo masa jinginar daga wurin macen, amma bai same ta a can ba. 21 Ya tambayi mutanen da suke zama a can ya ce, “Ina karuwar haikalin da take a bakin hanya a Enayim?”
Sai suka ce, “Ba a taɓa kasance da karuwar haikali a nan ba.”
22 Saboda haka sai ya koma zuwa wurin Yahuda ya ce, “Ban same ta ba. Ban da haka ma, mutanen da suke zama a can, sun ce, ‘Ba a taɓa kasance da wata karuwar haikali a nan ba.’ ”
23 Sa’an nan Yahuda ya ce, “Bari tă riƙe kayan kiɗa garin nema mu zama abin dariya. Ni kam, na aika da tunkiyar amma ba a same ta ba.”
24 Bayan misalin wata uku sai aka faɗa wa Yahuda cewa, “Tamar, surukarka ta yi laifin karuwanci, a sakamakon haka yanzu ta yi ciki.”
Yahuda ya ce, “A fid da ita, a ƙone!”
25 Yayinda ake fitar da ita, sai ta aika saƙo zuwa wurin surukinta, ta ce, “Mutumin da yake da waɗannan kayan ne ya yi mini ciki.” Ta kuma ƙara da cewa, “Duba ko za ka gane da hatimin nan, da abin ɗamaran nan, da kuma sandan nan, ko na wane ne?”
26 Yahuda ya gane su, sai ya ce, “Ai, ta fi ni gaskiya, da yake ban ba da ita ga ɗana Shela ba.” Bai kuwa ƙara kwana da ita ba.
-
22 Yoshuwa ya ce wa mutanen nan biyu waɗanda suka je leƙen asirin ƙasar, “Ku shiga gidan karuwan nan ku fitar da ita da duk waɗanda suke nata bisa ga alkawarin da kuka yi mata.” 23 Sai samarin waɗanda suka je leƙen asirin suka shiga suka fitar da Rahab, mahaifinta da mahaifiyarta, da ’yan’uwanta da duk abin da yake nata. Suka fitar da iyalinta gaba ɗaya suka sa su a wani wuri, ba a cikin masauƙin Isra’ilawa ba.
24 Sa’an nan suka ƙona birnin tare da dukan abin da yake ciki tatas, amma suka sa azurfa da zinariya da kayan tagulla da na ƙarfe a cikin ma’aji na haikalin Ubangiji. 25 Amma Yoshuwa ya bar Rahab karuwan nan bai kashe ta ba, ita da iyalinta da duk abin da yake nata, domin ita ta ɓoye mutanen da Yoshuwa ya aika Yeriko don su leƙo asirin ƙasar kuma ta zauna tare da Isra’ilawa har wa yau.
-
33 Ba a daɗe da rasuwar Gideyon ba, sai Isra’ila ta sāke shiga karuwanci suna bauta wa Ba’al. Suka kafa Ba’al-Berit yă zama musu allahnsu ba kuma
-
39 Suka ƙazantar da kansu ta wurin abin da suka yi;
ta wurin ayyukansu suka yi karuwanci.
-
4 “Ayyukansu ba su ba su dama
su koma ga Allahnsu ba.
Halin karuwanci yana cikin zuciyarsu;
ba su yarda da Ubangiji ba.
-
10 Na ga wani abu mai bantsoro
a gidan Isra’ila.
A can Efraim ya miƙa wuya ga karuwanci
Isra’ila kuma ta ƙazantu.
-
1 Taku ta ƙare, ku da kuke shirya makirci,
ku da kuke ƙulle-ƙullen mugunta a kan gadonku!
Da gari ya waye sai ku fita ku aikata mugunta
domin ikon aikatawa yana hannunku.
2 Kukan yi ƙyashin gonaki ku kuma ƙwace su,
ku yi ƙyashin gidaje ku kuma ƙwace.
Kukan zalunci mutum, ku ƙwace masa gidansa,
har ku ƙwace masa gādonsa.
3 Saboda haka, Ubangiji ya ce,
“Ina shirya wa waɗannan mutane bala’i,
yadda ba za ku iya ceton kanku ba.
Ba za ku ƙara tafiya kuna taƙama ba,
gama zai zama lokacin bala’i ne.
-
15 Sa’an nan mala’ikan ya ce mini, “Ruwayen da ka gani, inda karuwan take zama, jama’a ce, taro masu yawa, al’ummai da kuma harsuna. 16 Dabbar da kuma ƙahoni goma da ka gani za su ƙi jinin karuwar. Za su kai ta ga hallaka su kuma bar ta tsirara; za su ci namanta su kuma ƙone ta da wuta.
-
15 “ ‘Amma kika dogara ga kyanki kika kuma yi amfani da sunan da kika yi don ki zama karuwa. Kin yi ta jibga alherai a kan kowa da ya wuce, sai kyanki ya zama naki. 16 Kin ɗauki waɗansu tufafinki don ki yi wa kanki masujadai masu ado, inda kike karuwancinki. Irin waɗannan abubuwa bai kamata su faru ba, bai kuma kamata su taɓa faruwa ba. 17 Kika kuma ɗauki kayan ado masu kyau da na ba ki, kayan adon da aka yi da zinariya da azurfa, kika yi wa kanki gumakan maza kika kuma yi ta yin karuwanci da su. 18 Kika ɗauki rigunanki masu ado don ki sa a kansu, kika kuma miƙa maina da turarena a gabansu. 19 Haka ma abincin da na tanada miki, lallausan gari, man zaitun, da zuman da na ba ki ki ci, kin miƙa su kamar turare mai ƙanshi a gabansu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
20 “ ‘Kika kuma kwashe ’ya’yanki maza da mata waɗanda kin haifa mini kika miƙa su kamar abinci ga gumakanki. Karuwancinki bai isa ba ne? 21 Kin kashe ’ya’yana kika kuma miƙa su ga gumaka. 22 Cikin dukan ayyukan banƙyamarki da karuwancinki ba ki tuna da kwanakin ƙuruciyarki ba, sa’ad da kike tsirara tik, kina birgima cikin jininki.
-
30 “ ‘Kina da rashin ƙarfi a zuci, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, sa’ad da kika yi duk waɗannan abubuwa, kina yi kamar karuwar da aka watsa! 31 Sa’ad da kika gina ɗakunan samanki a kowane gefen titi kika kuma gina ɗakunan tsafinki a kowane dandali, ba kamar karuwa kike ba, domin kin karɓi kuɗi.
32 “ ‘Ke mazinaciyar mace! Kin gwammace baƙi a maimakon mijinki! 33 Kowace karuwa kan karɓi kuɗi, amma kina ba da kyautai ga dukan kwartayenki, kina ba su cin hanci don su zo wurinki daga ko’ina don alherai marasa ƙa’ida. 34 Saboda haka cikin karuwancinki kin sha bamban da saura; babu wanda yake binki saboda alheranki. Ke dai dabam ce, gama kikan biya kuma ba mai biyanki.
-
35 “ ‘Saboda haka, ke karuwa, ki ji maganar Ubangiji! 36 Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa domin kin zubar da dukiyarki kika bayyana tsiraicinki cikin fasikancinki da kwartayenki, kuma saboda dukan gumakan banƙyamarki, kuma saboda kin ba su jinin ’ya’yansu, 37 saboda haka zan tattara dukan kwartayenki, waɗanda kike jin daɗinsu, waɗanda kike ƙauna da waɗanda kike ƙi. Zan tattara su gāba da ke daga dukan kewaye zan kuma tuɓe ki a gabansu, za su kuwa ga dukan tsiraicinki. 38 Zan hukunta ki da hukuncin matan da suke zina da kuma waɗanda suke zub da jini; zan kawo hakkin jini na fushina da kuma fushin kishina. 39 Sa’an nan zan miƙa ki ga kwartayenki, za su kuwa rurrushe ɗakunan samanki su kuma farfashe ɗakunan tsafinki. Za su tuɓe miki tufafinki su kuma kwashe kayan adonki masu kyau su bar ki tsirara tik. 40 Za su kawo taron jama’a a kanki, waɗanda za su jajjefe ki da dutse su sassare ki gunduwa-gunduwa da takubansu. 41 Za su ƙone gidajenki su kuma hukunta ki a idon mata masu yawa. Zan kawo ƙarshen karuwancinki, ba za ki kuma ƙara biyan kwartayenki ba. 42 Sa’an nan fushina a kanki zai huce fushin kishina kuma ya kwanta; zan huce ba kuwa zan ƙara yin fushi ba.
43 “ ‘Domin ba ki tuna da kwanakin ƙuruciyarki ba amma kika husatar da ni da waɗannan abubuwa, tabbatacce zan sāka miki alhakin ayyukanki, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ba kin ƙara lalata ga dukan waɗansu ayyuka masu banƙyamarki ba?
Shows Read in context, Share and Copy.