90 Bible Verses About Wisdom
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
18 Gama saƙon gicciye wauta ne ga waɗanda suke hallaka, amma a gare mu, mu da ake ceto, ikon Allah ne. 19 Gama a rubuce yake cewa,
“Zan rushe hikimar mai hikima,
basirar mai azanci kuma zan rikita shi.”
20 Ina mai hikima? Ina mai zurfin bincike? Ina masana na wannan zamani? Ashe, Allah bai wofinta hikimar duniya ba? 21 Gama tun da a cikin hikimar Allah, duniya a cikin hikimarta ba tă san shi ba, Allah ya ji daɗin ceton waɗanda suka ba da gaskiya ta wurin wautar wa’azin bishara. 22 Yahudawa suna so su ga alama, Hellenawa kuma suna neman hikima, 23 amma mu, muna wa’azin Kiristi wanda aka gicciye ne, wanda ya zama dutsen tuntuɓe ga Yahudawa, wauta kuma ga Al’ummai, 24 amma ga su waɗanda Allah ya kira, Yahudawa da Hellenawa, Kiristi ikon Allah ne, da kuma hikimar Allah. 25 Gama wautar Allah ta fi hikimar mutum, kuma rashin ƙarfin Allah ya fi ƙarfin mutum.
26 ’Yan’uwa, ku tuna yadda kuke sa’ad da aka kira ku. Babu masu hikima da yawa a cikinku, bisa ga ganin mutum; babu masu iko da yawa, babu masu martaba da yawa bisa ga haihuwa. 27 Amma Allah ya zaɓi abubuwa masu wautata duniya, don yă kunyata masu hikima. Allah ya zaɓi abubuwa marasa ƙarfi na duniya, domin ya ba wa masu ƙarfi kunya.
-
2 Ku ɗauki wannan da farin ciki mai tsabta, ’yan’uwana, duk sa’ad da gwaje-gwaje na kowane iri suka zo muku, 3 domin kun san cewa gwajin bangaskiyarku yakan haifi daurewa. 4 Dole daurewa ta kammala aikinta don ku zama balagaggu da kuma cikakku, ba ku kuma rasa kome ba. 5 In waninku ya rasa hikima, ya kamata yă roƙi Allah, mai bayarwa hannu sake ga kowa ba tare da gori ba, za a kuwa ba shi. 6 Amma sa’ad da ya roƙa, dole yă gaskata, ba tare da shakka ba, domin shi mai shakka, yana kama da raƙumar ruwan tekun da iska take kori tana kuma ɓuɓɓugowa. 7 Kada irin wannan mutum yă yi tsammani zai sami wani abu daga Ubangiji; 8 shi mai zuciya biyu ne, marar tsai da zuciyarsa wuri ɗaya a cikin duk abin da yake yi.
-
13 Wane ne mai hikima da fahimta a cikinku? Bari yă nuna ta ta wurin rayuwarsa mai kyau, ta wurin ayyukan da aka yi cikin tawali’un da suke fitowa daga hikima. 14 Amma in kuna cike da mugun kishi da kuma sonkai a cikin zukatanku, kada ku yi taƙama game da wannan, ko ku danne gaskiya. 15 Irin wannan “hikima” ba daga sama ta sauko ba, ta duniya ce, ta rashin ruhaniya, ta Iblis kuma. 16 Gama inda akwai kishi da sonkai, a can za a tarar da hargitsi da kowane irin mugun aiki.
17 Amma hikimar da ta zo daga sama da fari tana da tsabta gaba ɗaya; sa’an nan mai ƙaunar salama ce, mai sanin ya kamata, mai biyayya, cike da jinƙai da aiki mai kyau, marar nuna bambanci, sahihiya kuma. 18 Masu salama da suke shuki cikin salama sukan girbe adalci.
-
1 Ɗana, in ka yarda da kalmomina
ka kuma ajiye umarnaina a cikinka,
2 kana kasa kunne ga abin da yake na hikima,
kana kuma yin ƙoƙari ka fahimce shi,
3 in kuma ka kira ga tsinkaya
ka kuma kira da ƙarfi don ganewa,
4 in ka neme shi yadda ake neman azurfa
ka kuma neme shi kamar yadda ake neman ɓoyayyiyar dukiya,
5 to, za ka gane tsoron Ubangiji
ka kuma sami sanin Allah.
6 Gama Ubangiji yana ba da hikima,
daga bakinsa kuma, sani da ganewa sukan fito.
7 Yana riƙe da nasara a ma’aji don masu yin gaskiya,
shi ne mafaka ga waɗanda tafiyarsu ba ta da laifi,
8 gama yana tsare abin da masu adalci suke bukata
yana kuma tsare hanyar amintattunsa.
9 Sa’an nan za ku fahimci abin da yake daidai da abin da yake na adalci
da abin da yake gaskiya, da kowace hanya mai kyau.
10 Gama hikima za tă shiga cikin zuciyarka,
sani kuma zai faranta maka rai.
-
7 “Yanzu, ya Ubangiji Allahna, ka sa bawanka a wurin mahaifina Dawuda. Amma ni ɗan yaro ne kawai, ban kuma san yadda zan yi ayyukana ba. 8 Bawanka yana nan a cikin mutanen da ka zaɓa, mutane masu girma, waɗanda suka wuce ƙirge, ko a lissafta. 9 Saboda haka ka ba bawanka zuciyar ganewa, don yă shugabanci mutanenka, yă kuma iya rarrabe tsakanin abin da yake daidai da abin da ba daidai ba. Gama wa zai iya shugabance wannan mutanenka masu girma haka?”
10 Sai Ubangiji ya ji daɗi cewa Solomon ya roƙa wannan. 11 Saboda haka Allah ya ce masa, “Da yake ka nemi wannan ne, ba ka kuwa nemi tsawon rai ko arziki wa kanka ba, ba ka kuma nemi mutuwar abokan gābanka ba, amma ka nemi ganewa a aikata gaskiya, 12 zan yi abin da ka roƙa. Zan ba ka zuciya mai hikima da ta ganewa, har yă zama ba a taɓa samun wani kamar ka ba, ba kuwa za a taɓa samunsa ba. 13 Ban da haka ma, zan ba ka abin da ba ka nema ba; arziki da girma, don a rayuwarka ba za ka kasance da wani kamar ka ba a cikin sarakuna. 14 In kuma ka yi tafiya a hanyoyina, ka kuma yi biyayya da farillaina da umarnaina kamar yadda Dawuda mahaifinka ya yi, zan ba ka tsawon rai.”
-
2 Ga karin magana da za su taimake ka don samun hikima da horo;
don ganewa kalmomi masu zurfi;
3 don neman rayuwa ta horo da kuma ta hankali,
kana yin abin da yake daidai, mai adalci da kuma wanda ya dace;
4 don sa marar azanci yă yi hankali,
yă sa matasa su sani, su kuma iya rarrabewa,
5 bari masu hikima su saurara, su kuma ƙara ga saninsu,
bari masu tunani kuma su sami jagora,
6 don su fahimci karin magana da kuma misalai,
kalmomi da kuma kacici-kacici masu hikima.
7 Tsoron Ubangiji shi ne masomin ilimi,
amma wawaye sun rena hikima da horo.
-
1 Da na zo wurinku ’yan’uwa, ban zo da iya magana ko wani mafificin hikima yayinda na yi muku shelar shaida game da Allah ba. 2 Don na ƙudura a raina sa’ad da nake tare da ku cewa ba zan mai da hankali ga kome ba sai dai Yesu Kiristi wanda aka gicciye. 3 Na zo wurinku cikin rashin ƙarfi da tsoro, da rawan jiki ƙwarai. 4 Saƙona da wa’azina ba su zo cikin hikima da kalmomin lallashi ba, sai dai da nuna ikon Ruhu, 5 domin kada bangaskiyarku ta dogara a kan hikimar mutane, sai dai a kan ikon Allah.
6 Duk da haka, muna sanar da saƙon hikima cikin waɗanda suka balaga, amma ba hikima irin ta wannan zamani ba ne, ko kuwa irin ta masu mulkin zamanin nan, waɗanda za su shuɗe ba. 7 A’a, muna magana ne a kan asirin hikimar Allah, hikimar da tun dā, take a ɓoye, wadda Allah ya ƙaddara domin ɗaukakarmu, tun kafin farkon zamanai. 8 Ba ko ɗaya daga cikin masu mulkin wannan zamani da ya fahimce ta, gama da a ce sun fahimce ta, da ba su gicciye Ubangiji mai ɗaukaka ba. 9 Duk da haka, kamar yadda yake a rubuce cewa,
“Ba idon da ya taɓa gani,
ba kunnen da ya taɓa ji,
ba kuma zuciyar da ta taɓa tunanin
abin da Allah ya shirya wa masu ƙaunarsa.”
10 Amma Allah ya bayyana mana shi ta wurin Ruhunsa.
Ruhu yana bincika dukan abubuwa, har ma da abubuwa masu zurfi na Allah. 11 Wane ne a cikin mutane ya san tunanin mutum, in ba ruhun mutumin da yake cikinsa ba? Haka kuma ba wanda ya san tunanin Allah, sai dai Ruhun Allah. 12 Ba mu karɓi ruhun duniya ba, sai dai Ruhun da yake daga Allah, domin mu fahimci abin da Allah ya ba mu hannu sake. 13 Wannan shi ne abin da muke sanarwa, ba da kalmomin da muka koya ta wurin hikimar mutum ba, amma da kalmomin da Ruhu yake koyarwa, muna faɗin gaskiya ta ruhaniya da kalmomin ruhaniya. 14 Mutumin da ba shi da Ruhu, ba ya yarda da abubuwan da suka fita daga Ruhun Allah, domin wauta ce a gare shi. Ba kuwa zai fahimce su ba, domin ta Ruhu ne ake fahimtarsu. 15 Mutumin ruhaniya yakan gwada dukan abubuwa, amma shi kansa ba ya ƙarƙashin shari’ar mutum.
-
10 Ku zaɓi umarnina a maimakon azurfa,
sani a maimakon zinariya zalla,
11 gama hikima ta fi lu’ulu’ai daraja,
kuma ba abin da kake sha’awa da za a kwatanta da ita.
12 “Ni, hikima, ina zama tare da hankali;
ina da sani da iya rarrabewa.
13 Jin tsoron Ubangiji shi ne ƙin mugunta;
ina ƙin girman kai da fariya,
halin mugunta da kuma muguwar magana.
14 Shawara da yin tunani mai kyau nawa ne;
ina da fahimi da kuma iko.
15 Ta wurina sarakuna suke mulki
masu mulki kuma suke yin dokokin da suke da adalci;
16 ta wurina sarakuna suke mulki,
da kuma dukan manyan mutanen da suke mulkin duniya.
17 Ina ƙaunar waɗanda suke ƙaunata,
kuma waɗanda suke nemana sukan same ni.
18 Tare da ni akwai wadata da girmamawa,
dukiya da wadata masu dawwama.
19 ’Ya’yan itacena sun fi zinariya zalla;
amfanin gonar da nake bayar ya fi azurfa mafi kyau.
20 Ina tafiya a hanyar adalci,
a kan hanyoyin gaskiya,
21 ina ba da wadata ga waɗanda suke ƙaunata
ina sa wuraren ajiyarsu su cika.
22 “Ubangiji ya kawo ni a matsayi na farko na ayyukansa,
kafin ayyukansa na tuntuni;
23 an naɗa ni tun fil azal,
daga farko, kafin duniya ta kasance.
-
8 Kada ka tsawata wa masu ba’a gama za su ƙi ka;
ka tsawata wa mai hikima zai kuwa ƙaunace ka.
9 Ka koya wa mai hikima zai kuwa ƙara hikima;
ka koya wa mai adalci zai kuwa ƙara koyonsa.
10 “Tsoron Ubangiji shi ne mafarin hikima,
sanin Mai Tsarki kuwa fahimi ne.
11 Gama ta wurina kwanakinka za su yi yawa,
za a kuwa ƙara wa ranka shekaru.
12 In kana da hikima, hikimarka za tă ba ka lada;
in kai mai ba’a ne, kai kaɗai za ka sha wahala.”
-
13 Mai albarka ne mutumin da ya sami hikima,
mutumin da ya sami fahimi,
14 gama ta fi azurfa riba
tana kuma da amfani fiye da zinariya.
15 Ta fi lu’ulu’u daraja;
ba a kwatanta abin da ka fi sha’awa da ita.
16 Tsawon rai yana a cikin hannunta na dama;
a hannunta na hagu kuwa akwai arziki da bangirma.
17 Hanyoyinta hanyoyi ne masu daɗi,
dukan hanyoyinta kuma salama ne.
18 Ita itacen rai ne ga waɗanda suka rungume ta;
waɗanda suke riƙe da ta za su zama masu albarka.
19 Ta wurin hikima Ubangiji ya kafa harsashin duniya,
ta wurin fahimi ya shirya sammai inda suke;
20 ta wurin sani aka rarraba zurfafa,
gizagizai kuma suka zubo raɓa.
21 Ɗana, ka riƙe sahihiyar shari’a da kuma basira,
kada ka bar su su rabu da kai;
22 za su zama rai a gare ka,
abin adon da zai gyara wuyanka.
23 Sa’an nan za ka bi hanyarka lafiya,
ƙafarka kuwa ba zai yi tuntuɓe ba;
-
29 Allah ya ba Solomon hikima da hangen nesa mai girma, da kuma fāɗin fahimta marar iyaka, kamar yashi a bakin teku. 30 Hikimar Solomon ta fi hikimar mutanen Gabas, ta kuma fi dukan hikimar Masar girma. 31 Ya fi kowane mutum hikima, har da Etan dangin Ezra ma. Yana da hikima fiye da Heman, Kalkol da Darda, ’ya’yan Mahol maza. Sunansa ya bazu ko’ina a ƙasashen da suke kewaye. 32 Ya yi karin magana dubu uku. Waƙoƙinsa kuwa sun kai dubu ɗaya da biyar. 33 Ya yi magana a kan rayuwar itatuwa, daga al’ul na Lebanon zuwa hizzob da yake girma a bangaye. Ya kuma yi koyarwa game da dabbobi, da tsuntsaye, da abubuwa masu rarrafe, da kuma kifi. 34 Mutane suka yi ta zuwa daga ƙasashe dabam-dabam don su ji hikimar Solomon. Sarakuna daga ko’ina a duniya, sun ji labarin hikimarsa, suka kuma aika da mutane don su ji shi.
-
9 Shi ya sa tun daga ranar da muka sami labarin, ba mu fasa yin addu’a dominku ba. Kullum muna roƙon Allah yă sa ku san kome da yake so ku yi, domin ku sami hikima ta Ruhu, ku kuma sami ganewar kome duka. 10 Ta haka za ku yi rayuwa wadda ta dace da Ubangiji, ku kuma gamshe shi a ta kowace hanya, kuna yin aiki mai kyau ta kowace hanya, kuna kuma yin girma cikin sanin Allah.
-
20 Hikima tana kira da ƙarfi a kan titi,
tana ɗaga muryarta a dandalin taron jama’a;
21 tana kira da ƙarfi a kan tituna masu surutu,
tana yin jawabinta a hanyoyin shiga gari.
22 “Har yaushe ku da kuke marasa azanci za ku ci gaba a hanyoyinku marasa azanci?
Har yaushe ku masu ba’a za ku yi ta murna cikin ba’arku
wawaye kuma ku ƙi ilimi?
23 Da a ce kun saurari tsawatata,
da na faɗa muku dukan abin da yake zuciyata
in kuma sanar da ku tunanina.
24 Amma da yake kun ƙi ni sa’ad da na yi kira
ba kuma wanda ya saurara sa’ad da na miƙa hannuna,
25 da yake kun ƙi dukan shawarata
ba ku kuma yarda da tsawatata ba,
26 Zan yi muku dariya sa’ad da masifa ta same ku,
zan yi muku ba’a sa’ad da bala’i ya same ku,
-
5 Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka
kada kuma ka dangana ga ganewarka;
6 cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi,
zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.
7 Kada ka zama mai hikima a ganinka;
ka ji tsoron Ubangiji ka kuma guji mugunta.
8 Wannan zai ba wa jikinka lafiya
yă kuma adana ƙasusuwanka.
-
19 A wannan dare sai aka bayyana wa Daniyel mafarkin cikin wahayi. Daniyel kuwa ya ɗaukaka Allah na sama. 20 Ya ce,
“Yabo ya tabbata ga sunan Allah har abada abadin;
hikima da iko nasa ne.
21 Yana sāke lokuta,
yana tuɓe sarakuna yana kuma naɗa waɗansu.
Yana ba da hikima ga masu hikima
kuma ilimi ga masu basira.
22 Yakan bayyana zurfafa da ɓoyayyun abubuwa;
ya san abin da yake cikin dare,
haske kuwa yana zaune tare da shi.
23 Na gode maka ina yabonka, Allah na kakannina.
Kai ka san hikima da iko,
ka sanar da ni abin da muka tambaye ka, ka kuma sanar da mu mafarkin sarki.”
-
30 Saboda Allah ne kuke cikin Kiristi Yesu, shi wanda ya zama hikima a gare mu daga Allah. Kiristi shi ne adalcinmu, da tsarkinmu, da kuma fansarmu. 31 Saboda haka, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Duk wanda yake taƙama, ya yi taƙama a cikin Ubangiji.”
-
16 ban fasa yin godiya saboda ku ba, ina tuna da ku cikin addu’o’ina. 17 Ina ta roƙo cewa Allah na Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba Maɗaukaki, yă ba ku Ruhun hikima da na ganewa, domin ku san shi da kyau. 18 Ina kuma addu’a cewa zuciyarku tă waye don ku gane ko mene ne sa zuciyan nan da ya kira ku a kansa, ku kuma san darajar dukiyan nan wadda take ta mutanen Allah, wato, albarkunsa. 19 Ina addu’a ku san girman ikon Allah wanda ya wuce misali, wanda yake namu. Ikon da yake aiki a cikinmu, ɗaya ne da ikon nan
-
1 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, 2 “Duba, na zaɓi Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, na kabilar Yahuda, 3 na kuma cika shi da Ruhun Allah, fasaha, azanci, da kuma sani cikin kowace irin sana’a, 4 don yin zāne-zāne na aikin zinariya, azurfa da tagulla, 5 don yanka da shirya duwatsu, yin aikin katako, da kuma yin kowane irin aikin sana’ar hannu.
-
1 Toho zai fito daga kututturen Yesse;
daga saiwarsa Reshe zai ba da ’ya’ya.
2 Ruhun Ubangiji zai kasance a kansa,
Ruhun hikima da na fahimta,
Ruhun shawara da na iko,
Ruhun sani da na tsoron Ubangiji,
3 zai kuwa ji daɗin tsoron Ubangiji.
Ba zai yi hukunci ta wurin abin da ya gani da idanunsa ba,
ba zai kuwa yanke shawara ta wurin abin da ya ji da kunnuwansa ba;
-
10 Tsoron Ubangiji ne mafarin hikima;
dukan waɗanda suke bin farillansa suna da ganewa mai kyau.
Gare shi ne madawwamin yabo.
-
28 Ya kuma ce wa mutum,
‘Tsoron Ubangiji shi ne hikima,
kuma guje wa mugunta shi ne fahimi.’ ”
-
1 Hikima ta gina gidanta;
ta yi ginshiƙansa bakwai.
2 Ta shirya abincinta gauraye da ruwan inabinta;
ta kuma shirya teburinta.
3 Ta aiki bayinta mata, tana kuma kira
daga wurare masu tsayi na birnin.
4 “Bari dukan waɗanda suke marasa azanci su zo nan ciki!”
Tana faɗa wa marasa hankali.
5 “Ku zo, ku ci abincina
da ruwan inabin da na gauraye.
6 Ku bar hanyoyinku marasa hankali za ku kuwa rayu;
yi tafiya a hanyar fahimi.
-
6 Mai ba’a kan nemi hikima amma ba ya samun kome,
amma sani kan zo a sawwaƙe ga mai basira.
7 Ka guji wawa,
gama ba za ka sami sani a leɓunansa ba.
8 Hikima masu la’akari shi ne su yi tunani a kan hanyoyinsu,
amma wautar wawaye ruɗu ne.
-
18 Kada ku ruɗi kanku. In waninku yana tsammani cewa yana da hikima, yadda duniya ta ɗauki hikima, to, sai ya mai da kansa “wawa” don yă zama mai hikima. 19 Gama hikimar duniyan nan, wauta ce a gaban Allah, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yakan kama masu hikima a cikin makircinsu”; 20 kuma a rubuce yake cewa, “Ubangiji ya san dukan tunanin masu hikima banza ne.”
-
12 Ka koya mana yawan kwanakinmu daidai,
don mu sami zuciyar hikima.
-
מ Mem
97 Kash, ga yadda nake ƙaunar dokarka!
Ina tunani a kanta dukan yini.
98 Umarnanka suna sa in zama mai hikima fiye da abokan gābana,
gama kullum suna tare da ni.
99 Ina da ganewa sosai fiye da dukan malamaina,
gama ina tunani a kan farillanka.
100 Ina da ganewa fiye da dattawa,
gama ina biyayya da farillanka.
-
5 Ka nemi hikima, ka nemi fahimi;
kada ka manta da kalmomina ko ka kauce daga gare su.
6 Kada ka ƙyale hikima, za tă kuwa tsare ka;
ka ƙaunace ta, za tă kuwa lura da kai.
7 Hikima ce mafi girma duka; saboda haka ka nemi hikima.
Ko da za tă ci duk abin da kake da shi, ka dai nemi fahimi.
-
33 Kai, zurfin yalwar hikima da kuma sanin Allah yana nan a yalwace!
Hukunce-hukuncensa kuma su fi gaban bincike,
hanyoyinsa kuwa sun wuce gaban ganewa!
34 “Wa ya taɓa sanin zuciyar Ubangiji?
Ko kuwa yă ba shi shawara?”
35 “Wa ya taɓa ba wa Allah wani abu,
da Allah zai sāka masa?”
36 Gama daga gare shi, ta wurinsa, da kuma saboda shi ne dukan abubuwa suka kasance.
Ɗaukaka ta tabbata a gare shi har abada! Amin.
-
12 Ko ba a wurin tsofaffi ake samun hikima ba?
Ba tsawon rai yana kawo ganewa ba?
13 “Allah ne mai iko da kuma hikima,
shawara da ganewa nasa ne.
-
16 Ya ma fi kyau ka sami hikima fiye da zinariya,
ka zaɓi fahimi a maimakon azurfa!
-
16 Ku bar maganar Kiristi ta zauna a cikinku a yalwace yayinda kuke koya, kuna kuma yi wa juna gargaɗi da dukan hikima, da kuma yayinda kuke waƙoƙin zabura, waƙoƙi da waƙoƙin ruhaniya tare da godiya a zukatanku ga Allah.
-
1 Hikima ba ta yin kira ne?
Fahimi ba ya tā da muryarsa ne?
2 A ƙwanƙoli a kan hanya,
inda hanyoyi suka haɗu, ta ɗauki matsayinta;
3 kusa da ƙofofin shiga cikin birni,
a mashigai, ta tā da murya,
4 “Gare ku, ya mutane, nake kira;
na tā da muryata ga dukan ’yan adam.
5 Ku da kuke marasa azanci, ku yi hankali;
ku da kuke wawaye, ku nemi fahimi.
6 Ku saurara, gama ina da abubuwa masu darajan da zan faɗa;
na buɗe leɓunana don in faɗa abin da yake daidai.
-
1 Kada ka yi ƙyashin mugaye,
kada ka yi sha’awar ƙungiyarsu;
2 gama leɓunansu suna maganar tā-da-na-zaune-tsaye ne.
3 Ta wurin hikima ce ake gina gida,
kuma ta wurin fahimi ake kafa ta;
4 ta wurin sani ɗakunanta sukan cika
da kyawawan kayayyaki masu daraja.
5 Mutum mai hikima yana da iko sosai,
kuma mutum mai sani yakan ƙaru da ƙarfi;
6 don yin yaƙi kana bukatar bishewa,
kuma don ka yi nasara kana bukatar mashawarta masu yawa.
7 Hikima ta yi wa wawa nisa ƙwarai
a cikin taro a ƙofar gari ba shi da ta cewa.
-
12 Amma a ina ne za a iya samun hikima?
Ina fahimta take zama?
13 Mutum bai gane muhimmancinta ba,
ba a samunta a ƙasar masu rai.
14 Zurfi ya ce, “Ba ta wurina”;
teku ya ce, “Ba ta wurina.”
15 Ba irin zinariyar da za tă iya sayenta,
ko kuma a iya auna nauyinta da azurfa.
16 Ba za a iya sayenta da zinariyar Ofir,
ko sauran duwatsu masu daraja ba.
17 Zinariya da madubi ba za su iya gwada kansu da ita ba,
ba kuwa za a iya musayarta da abubuwan da aka yi da zinariya ba.
-
2 Sa’ad da girman kai ya zo, sai shan kunya ta zo,
amma hikima kan zo tare da ƙasƙantar da kai.
-
24 “Saboda haka duk wanda yake jin kalmomin nan nawa yake kuma aikata su, yana kama da mutum mai hikima wanda ya gina gidansa a kan dutse. 25 Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuma ta hura ta bugi gidan; duk da haka bai fāɗi ba, gama yana da harsashinsa a kan dutse. 26 Amma duk wanda yake jin kalmomin nan nawa bai kuwa aikata su ba, yana kama da wani wawa wanda ya gina gidansa a kan yashi. 27 Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuwa ta hura ta bugi gidan, sai ya fāɗi da mummunar ragargajewa kuwa.”
-
30 Bakin mutum mai adalci yakan yi magana da hikima,
harshensa kuwa yakan yi maganar abin da yake daidai.
-
24 Ina misalin yawan aikinka, ya Ubangiji!
Cikin hikima ka yi su duka;
duniya ta cika da halittunka.
-
20 Duk wanda ya mai da hankali ga umarni yakan yi nasara,
kuma mai albarka ne wanda yake dogara ga Ubangiji.
21 Akan ce da masu hikima a zuciya hazikai,
kuma kalmomi masu daɗi kan inganta umarni.
22 Fahimi shi ne maɓulɓular rai ga waɗanda suke da shi,
amma wauta kan kawo hukunci ga wawaye.
23 Zuciyar mai hikima kan bi da bakinsa,
kuma leɓunansa kan inganta umarni.
24 Kalmomi masu daɗi suna kama da kakin zuma,
mai zaƙi ga rai da kuma warkarwa ga ƙasusuwa.
-
12 Sai na juya ga tunanina don in lura da hikima,
da kuma hauka da wauta.
Me ya rage wa magājin sarki yă yi
fiye da abin da aka riga aka yi?
13 Na ga cewa hikima ta fi wauta,
kamar yadda haske ya fi duhu.
14 Mai hikima ya san inda ya nufa,
wawa kuwa yana tafiya a cikin duhu;
amma sai na gane
cewa ƙaddara ɗaya ce take samunsu.
15 Sai na yi tunani a zuciyata,
“Ƙaddarar wawa za tă same ni ni ma.
Wace riba ce hikimata za tă jawo mini?”
Na ce a zuciyata,
“Wannan ma ba shi da amfani.”
16 Gama ba za a ƙara tunawa da mai hikima ko wawa ba;
nan gaba za a manta da su.
Yadda wawa zai mutu, haka ma mai hikima!
-
26 Ga wanda ya gamshe shi, Allah yakan ba da hikima da sani da farin ciki, amma ga mai zunubi yakan ba shi aikin tarawa da ajiyar dukiya domin yă miƙa wa wanda ya gamshi Allah. Wannan ma ba shi da amfani, naushin iska ne kawai.
-
1 Wa yake kama da mai hikima?
Wa ya san bayanin abubuwa?
Hikima takan haskaka fuskar mutum,
ta kuma kawo sakin fuska.
-
13 Na kuma ga wani misali game da hikima a duniya wanda ya burge ni sosai. 14 An yi wani ɗan ƙaramin birni mai mutane kaɗan a ciki. Sai wani babban sarki ya kawo masa yaƙi, ya kafa masa babban sansani. 15 A cikin birnin nan kuwa akwai wani mutum matalauci amma mai hikima, ya kuma ceci birnin ta wurin hikimarsa. Amma ba wanda ya tuna da matalaucin nan. 16 Sai na ce, “Hikima ta fi ƙarfe ƙarfi.” Amma aka rena hikimar matalaucin, ba a ma jin maganarsa.
17 Raɗar mai hikima da aka saurara cikin natsuwa
ta fi ihun mai mulkin wawaye.
18 Hikima ta fi kayan yaƙi,
amma mai zunubi ɗaya yakan rushe alheri mai yawa.
-
18 Ana bayyana fushin Allah daga sama a kan dukan rashin sanin Allah da kuma muguntar mutanen da suke danne gaskiya ta wurin muguntarsu, 19 gama abin da ana iya sani game da Allah a bayyane yake a gare su, domin Allah ya bayyana musu shi. 20 Gama tun halittar duniya halayen Allah marar ganuwa, madawwamin ikonsa da kuma allahntakarsa, ana iya ganinsu sarai, ana fahimtarsu ta wurin abubuwan da Allah ya halitta, domin kada mutane su sami wata hujja.
21 Gama ko da yake sun san Allah, ba su ɗaukaka shi a matsayin Allah ko su gode masa ba, sai dai tunaninsu ya zama banza, zukatansu masu wauta kuma suka duhunta. 22 Ko da yake sun ɗauka su masu hikima ne, sai suka zama wawaye, 23 suka kuma yi musayar ɗaukakar Allah marar mutuwa da siffofin da aka ƙera su yi kama da mutum mai mutuwa da tsuntsaye da dabbobi da kuma halittu masu ja da ciki.
-
15 Sai ku yi hankali sosai da yadda kuke rayuwa, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai kamar masu hikima. 16 Ku kuma yi matuƙar amfani da kowane zarafi, don kwanakin nan mugaye ne. 17 Saboda haka kada ku zama wawaye, sai dai ku fahimci ko mene ne nufin Ubangiji.
-
33 Tsoron Ubangiji yakan koya wa mutum hikima,
kuma sauƙinkai kan zo kafin girmamawa.
-
8 Duk wanda ya sami hikima yana ƙaunar ransa;
duka wanda yake jin daɗi fahimi kan ci gaba.
-
26 Duk mai dogara ga kansa wawa ne,
amma duk wanda yake tafiya da hikima zai zauna lafiya.
-
16 Da na mai da hankalina don in sami hikima in kuma lura da wahalar mutum a duniya, ko da a ce idanunsa ba sa barci dare da rana, 17 sam, ba zai taɓa fahimci abin da Allah yake yi ba. Iyakar ƙoƙarin da ka yi duk ba za ka iya ganewa ba. Masu hikima suna iya cewa sun sani, amma kuwa ba su sani ba.
-
4 Akwai baye-baye iri dabam-dabam, amma Ruhu ɗaya ne. 5 Akwai hidimomi iri-iri, amma Ubangiji ɗaya ne. 6 Akwai aiki iri-iri, amma duk Allah ɗaya ne yake aikata su a cikin dukan mutane.
7 An ba wa kowane mutum bayyanuwar Ruhu don amfanin kowa. 8 Ga wani, an ba shi saƙon hikima ta wurin Ruhu, ga wani baiwar saƙon sani ta wurin wannan Ruhu guda. 9 Ga wani bangaskiya ta wurin wannan Ruhu, ga wani kuma baiwar warkarwa ta wurin wannan Ruhu guda. 10 Ga wani yin ayyukan banmamaki, ga wani annabci, ga wani baiwar rarrabe ruhohi, ga wani baiwar magana da harsuna dabam-dabam, ga wani har wa yau iya fassarar harsuna. 11 Duk waɗannan aiki ne na wannan Ruhu guda, yana kuma ba da su ga kowane mutum, yadda yake so.
-
12 Yana dagula shirye-shiryen masu wayo
don kada su yi nasara cikin abubuwan da suke shirin yi.
13 Yana kama masu wayo cikin wayonsu,
yana kawar da shirye-shiryensu ba za su yi nasara ba.
-
8 Mai hikima a zuciya yakan yarda da umarni
amma surutun wawa kan kai ga lalaci.
9 Mai mutunci yana tafiya lafiya,
amma shi da yake tafiya a karkatattun hanyoyi za a kama shi.
-
13 Ka sha zuma, ɗana, ka sha zuma gama tana da kyau;
zuma daga kaki yana da zaƙi a harshenka.
14 Ka kuma san cewa hikima tana da zaƙi ga rai;
in ka same ta, akwai sa zuciya ta nan gaba dominka,
kuma sa zuciyarka ba za tă zama a banza ba.
-
10 Kada ka ce, “Me ya sa kwanakin dā sun fi waɗannan?”
Gama ba daidai ba ne a yi irin waɗannan tambayoyi.
11 Hikima, kamar gādo, abu mai kyau ne
tana kuma da amfani ga waɗanda suka ga rana.
12 Hikima mafaka ce
takan kāre mutum kamar yadda kuɗi suke yi.
Kiyayewar da hikima takan yi wa mai ita
ita ce amfanin ilimi.
13 Ku lura da abin da Allah ya yi.
Wa zai iya miƙe
abin da ya tanƙware?
14 Sa’ad da al’amura suke tafiya daidai, ka yi farin ciki,
amma sa’ad da suka lalace, ka tuna,
Allah ne ya yi wancan
shi ne kuma ya yi wannan.
Saboda haka, mutum ba zai san
wani abu game da nan gabansa ba.
-
21 Kaiton waɗanda suke tsammani suna da hikima
da kuma wayo a idonsu.
-
13 Ubangiji ya ce,
“Waɗannan mutane sun zo kusa da ni da bakinsu
suka kuma girmama ni da leɓunansu,
amma zukatansu suna nesa daga gare ni.
Sujadar da suke mini
cike take da dokokin da mutane suka koyar.
14 Saboda haka zan firgita waɗannan mutane sau ɗaya
da abubuwan banmamaki a kan abubuwan banmamaki;
hikimar masu hikima za tă lalace,
azancin masu azanci zai ɓace.”
-
23 Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“Kada mai hikima ya yi fariya da hikimarsa
ko mai ƙarfi ya yi fariya da ƙarfinsa
ko mai arziki ya yi fariya da arzikinsa,
24 amma bari shi wanda yake taƙama ya yi taƙama da wannan,
cewa ya fahimci ya kuma san ni,
cewa ni ne Ubangiji, wanda yake yin alheri,
gaskiya da kuma adalci a duniya,
gama a waɗannan ne nake jin daɗi,”
in ji Ubangiji.
-
9 Wane ne yake da hikima? Zai gane waɗannan abubuwa.
Hanyoyin Ubangiji daidai ne;
masu adalci sukan yi tafiya a kansu,
amma ’yan tawaye sukan yi tuntuɓe a kansu.
-
54 Yana isowa garinsa, sai ya fara koya wa mutane a cikin majami’arsu, suka kuwa yi mamaki. Suka yi ta tambaya suna cewa, “Ina wannan mutum ya sami irin wannan hikima da kuma ayyukan banmamaki haka?
-
14 Amma ku yi ƙuduri, wato, ku shirya zuciyarku, a kan ba za ku damu ba kafin lokacin, game da yadda za ku kāre kanku. 15 Gama zan ba ku kalmomi, da hikima waɗanda ba ko ɗaya daga cikin maƙiyanku, za su iya tsayayya da ku, ko su ƙaryata.
-
4 Da sarauniya Sheba ta ga dukan hikimar Solomon da fadan da ya gina. 5 Da irin abincin da yake kan teburinsa, da irin zaman fadawansa, da irin rigunan masu hidimarsa, da irin masu shayarwarsa, da kuma hadayun ƙonawar da yake yi a haikalin Ubangiji, sai ta yi mamaki ƙwarai.
6 Ta ce wa sarki, “Labarin da na ji a ƙasata game da abin da ka yi da kuma hikimarka gaskiya ne. 7 Amma ban gaskata waɗannan abubuwa ba sai da na zo na gani da idanuna. Tabbatacce, ba a ma faɗa mini ko rabi ba. Gama cikin hikima da arziki, ka wuce labarin da na ji nesa ba kusa ba. 8 Abin farin ciki ne ga mutanenka! Abin farin ciki ne ga fadawanka, waɗanda suke cin gaba da tsayawa a gabanka suna kuma jin hikimarka!
-
36 Wane ne yake cika zuciya da hikima
ko kuma yake ba zuciya ganewa?
37 Wane ne yake da hikimar iya ƙirga gizagizai?
Wane ne zai iya karkato bakunan tulunan sammai
-
ה He
33 Ka koya mini Ya Ubangiji, don in bi ƙa’idodinka;
sa’an nan zan kiyaye su har ƙarshe.
34 Ka ba ni ganewa, zan kuwa kiyaye dokarka
in kuma yi biyayya da ita da dukan zuciyata.
35 Ka bi da ni a hanyar umarnanka,
gama a can zan sami farin ciki.
-
1 Ɗana, ka mai da hankali ga hikimata
ka saurara da kyau ga kalmomin basirata,
2 don ka ci gaba da yin kome daidai
leɓunanka za su adana sani.
-
10 Girmankai kan jawo faɗa ne kawai,
amma hikima tana samuwa a waɗanda suke jin shawara.
-
20 A gidan mai hikima akwai wuraren ajiya na abinci da mai masu kyau,
amma wawa kan cinye duk abin da yake da shi.
21 Duk wanda ya nemi adalci da ƙauna
kan sami rai, wadata da girmamawa.
-
30 Babu hikima, babu tunani, babu shirin
da zai yi nasara a kan Ubangiji.
-
16 Na yi tunani a raina na ce, “Duba, na yi girma, na kuma ƙaru da hikima fiye da duk wanda ya taɓa mulki a bisa Urushalima kafin ni; na ɗanɗana hikima mai yawa da kuma ilimi.” 17 Sa’an nan na ɗaura aniyata ga fahimtar hikima, in kuma san bambanci tsakanin hauka da wauta, amma na koyi cewa wannan ma, naushin iska ne kawai.
18 Gama yawan hikima yakan kawo yawan baƙin ciki;
yawan sani, yawan ɓacin rai.
-
5 Duk wanda ya yi biyayya da umarninsa ba zai sami lahani ba,
zuciya mai hikima kuma zai san lokacin da ya dace da kuma hanyoyin da suka fi.
-
52 Yesu kuwa ya yi girma, ya kuma ƙaru cikin hikima, ya kuma sami tagomashi a wurin Allah da mutane.
-
2 Ku nace da yin addu’a, kuna zaman tsaro da kuma godiya. 3 Ku kuma yi mana addu’a, mu ma, don Allah yă buɗe ƙofa saboda saƙonmu, don mu iya yin shelar asirin Kiristi, wanda saboda shi nake cikin sarƙoƙi. 4 Ku yi addu’a yadda zan yi shelarsa, yadda ya kamata. 5 Ku zama masu hikima a yadda kuke ma’amala da waɗanda suke ba masu bi ba; ku kuma yi amfani da kowane zarafi. 6 Bari maganarku kullum ta zama da ladabi da kuma daɗin ji, domin ku san amsar da ta dace ku ba wa kowa.
-
6 Tabbatacce kana son gaskiya a sassan ciki;
ka koya mini hikima a wuri can ciki.
-
43 Duk mai hikima, bari yă ji waɗannan abubuwa
yă kuma lura da ƙauna mai girma ta Ubangiji.
-
32 “Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni;
masu albarka ne waɗanda suke kiyaye hanyoyina.
33 Ku saurari umarnina ku kuma zama masu hikima;
kada ku ƙyale ta.
34 Mai albarka ne wanda ya saurare ni;
yana tsaro kullum a ƙofofina,
yana jira a ƙofar shigata.
35 Gama duk wanda ya same ni ya sami rai
zai kuma sami tagomashi daga Ubangiji.
36 Amma duk wanda ya kāsa samuna ya cuci kansa;
dukan waɗanda suke ƙina suna ƙaunar mutuwa ke nan.”
-
30 ’Ya’yan itacen adali itacen rai ne,
kuma duk mai samun rayuka mai hikima ne.
-
33 Hikima tana a zuciyar mai azanci,
kuma ko a cikin wawaye takan sa a santa.
-
3 Duk mai ƙaunar hikima kan kawo wa mahaifinsa farin ciki,
amma wanda yake ma’amala da karuwai kan lalatar da dukiyarsa.
-
15 Sandar gyara kan ba da hikima,
amma yaron da aka bari ba horo kan jawo kunya ga mahaifiyarsa.
-
11 Kalmomin masu hikima kamar tsinken tsokanar dabba ne, tarin maganganunsu kuma kamar ƙusoshi ne da aka kafa daram, da aka ba wa Makiyayi guda.
-
8 “Gama tunanina ba tunaninku ba ne,
yadda kuke yin abubuwa ba yadda nake yin abubuwa ba ne,”
in ji Ubangiji.
9 “Kamar yadda sammai suke can nesa da ƙasa,
haka yadda nake yin abubuwa suke dabam da yadda kuke yin abubuwa
tunanina kuma dabam da naku.
-
7 Ko shamuwa ta sararin sama ma
takan san lokutan da aka tsara mata,
kurciya, mashirare da kuma zalɓe
sukan lura da lokacin ƙauransu.
Amma mutanena ba su san
abubuwan da Ubangiji yake bukata ba.
8 “ ‘Yaya za ku ce, “Muna da hikima,
gama muna da dokar Ubangiji,”
alhali alƙalamin ƙarya na magatakarda
ya yi ƙarya?
9 Za a kunyatar da masu hikima;
za su yi fargaba a kuma kama su.
Da yake sun ƙi maganar Ubangiji,
wace irin hikima kuka ce kuke da ita?
-
20 A dukan al’amuran hikima da na fahimta wanda sarki ya tambaye su, ya tarar sun fi dukan masu sihiri da bokaye waɗanda suke cikin mulkinsa sau goma.
-
11 Akwai wani mutum a masarautarka wanda yake da ruhun alloli masu tsarki a cikinsa. A zamanin mahaifinka an gane cewa yana da basira da hazaka da hikima kamar na alloli. Sarki Nebukadnezzar mahaifinka, mahaifinka sarki, na ce, ya naɗa shugaban masu dabo, da masu sihiri, masanan taurari da kuma masu duba. 12 Wannan mutum Daniyel, wanda sarki ya kira Belteshazar, an gane yana da ruhu nagari, da ilimi, da ganewa don yin fassarar mafarkai, da bayyana ma’anar kacici-kacici, da warware al’amura masu wuya. Ka kira Daniyel shi kuwa zai faɗa maka abin da rubutun nan yake nufi.”
-
3 Waɗanda suke da hikima za su haskaka kamar hasken samaniya, waɗanda kuma suka jagoranci waɗansu da yawa zuwa adalci, za su zama kamar taurari har abada abadin. 4 Amma kai, Daniyel, ka rufe zancen nan ka kuma liƙe kalmomin littafin nan har sai ƙarshe. Mutane da yawa za su yi ta kai komo don neman sani.”
-
25 A wannan lokaci sai Yesu ya ce, “Ina yabonka, Uba, Ubangijin sama da ƙasa, gama ka ɓoye waɗannan abubuwa ga masu hikima da masu ilimi, ka kuma bayyana su ga ƙananan yara. 26 I, Uba, gama wannan shi ne abin da ka ji daɗin yi.
27 “Dukan kome Ubana ya danƙa mini. Ba wanda ya san Ɗan sai dai Uban, ba kuma wanda ya san Uban, sai dai Ɗan da kuma waɗanda Ɗan ya so yă bayyana musu shi.
-
21 A wannan lokaci, Yesu, cike da murna ta wurin Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Na yabe ka, ya Uba, Ubangijin sama da ƙasa, domin ka ɓoye waɗannan abubuwa ga masu hikima, da masu ilimi, ka kuma bayyana su ga ƙananan yara. I, ya Uba, gama wannan shi ne nufinka mai kyau.
-
23 Sarki Solomon ya yi suna a wadata fiye da dukan sarakunan duniya. 24 Dukan duniya ta nemi su zo wurin Solomon don su ji hikimar da Allah ya sa a zuciyarsa.
-
13 Ana samun hikima a leɓunan masu fahimi,
amma bulala domin bayan marasa azanci ne.
14 Mai hikima kan yi ajiyar sani,
amma bakin wawa kan gayyaci lalaci.
-
Maganganu Masu Hikima
17 Ka kasa kunne ka kuma saurara ga maganganu masu hikima;
ka yi amfani da abin da nake koyarwa,
18 gama yana da daɗi sa’ad da ka kiyaye su a zuciyarka
ka kuma kasance da su a shirye a leɓunanka.
19 Domin dogarawarka ta kasance ga Ubangiji,
ina koya maka yau, har kai ma.
20 Ban rubuta maka maganganu talatin ba,
maganganun shawara da sani,
21 ina koya maka gaskiya da kalmomin da za ka dogara a kai,
saboda ka iya ba da amsa daidai
ga duk wanda ya aike ka?
-
12 Amma Allah ya yi duniya ta wurin ikonsa;
ya kafa duniya ta wurin hikimarsa
ya shimfiɗa sammai ta wurin fahiminsa.
Shows Read in context, Share and Copy.