58 Bible Verses About Understanding

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Understanding
  1. 5 Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka

    kada kuma ka dangana ga ganewarka;

    6 cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi,

    zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.

    7 Kada ka zama mai hikima a ganinka;

    ka ji tsoron Ubangiji ka kuma guji mugunta.

  2. 9 Shi ya sa tun daga ranar da muka sami labarin, ba mu fasa yin addu’a dominku ba. Kullum muna roƙon Allah yă sa ku san kome da yake so ku yi, domin ku sami hikima ta Ruhu, ku kuma sami ganewar kome duka. 10 Ta haka za ku yi rayuwa wadda ta dace da Ubangiji, ku kuma gamshe shi a ta kowace hanya, kuna yin aiki mai kyau ta kowace hanya, kuna kuma yin girma cikin sanin Allah. 11 Allah yă ƙarfafa ku da dukan iko bisa ga ɗaukakar ƙarfinsa domin ku kasance da jimrewa sosai da kuma haƙuri, cikin farin ciki 12 kuna gode wa Uba, wanda ya sa kuka cancanci ku sami rabo a gādon tsarkaka a cikin mulkin haske.

  3. 7 Ka yi tunani a kan abin da nake faɗi, gama Ubangiji zai ba ka ganewa cikin dukan wannan.

  4. 28 Al’ummai ne marasa azanci,

    babu ganewa a cikinsu.

    29 A ce su masu hikima ne har su gane wannan

    su gane abin da ƙarshensu zai zama!

  5. 13 Abin da ya sa nake musu magana da misalai ke nan.

    “Ko da yake suna kallo, ba sa gani;

    ko da yake suna saurara, ba sa ji ko su gane.

    14 A kansu ne aka cika annabcin Ishaya cewa,

    “ ‘Za ku yi ta ji amma ba za ku taɓa ganewa ba;

    za ku yi ta kallo amma ba za ku taɓa gani ba.

    15 Gama zuciyar mutanen nan ta taurare;

    da ƙyar suke ji da kunnuwansu,

    sun kuma rufe idanunsu.

    Da ba haka ba, mai yiwuwa su gani da idanunsu,

    su kuma ji da kunnuwansu,

    su gane a zuciyarsu,

    su kuwa juya, in kuma warkar da su.’

  6. 17 Saboda haka kada ku zama wawaye, sai dai ku fahimci ko mene ne nufin Ubangiji.

  7. 5 Ga shi, na koya muku ƙa’idodi da dokoki, yadda Ubangiji Allahna ya umarce ni, don ku bi su a ƙasar da za ku shiga ku mallaki. 6 Ku kiyaye su, ku aikata su, gama yin haka zai tabbatar wa sauran al’ummai, kuna da hikima da ganewa. Sa’ad da al’ummai za su ji waɗannan dokoki, za su ce, “Ba shakka, wannan babbar al’umma tana da hikima da ganewa.”

  8. 29 Allah ya ba Solomon hikima da hangen nesa mai girma, da kuma fāɗin fahimta marar iyaka, kamar yashi a bakin teku.

  9. 12 Bari Ubangiji ya ba ka basira da fahimi sa’ad da ya sa ka shugaba a bisa Isra’ila, saboda ka kiyaye dokar Ubangiji Allahnka.

  10. 104 Na sami ganewa daga farillanka;

    saboda haka ina ƙin kowace hanyar da ba daidai ba.

  11. 11 Sai ya ce musu, “An ba ku sanin asirin mulkin Allah. Amma ga waɗanda suke waje kuwa, kome sai da misalai. 12 Saboda,

    “ ‘ko sun dinga duba, ba za su taɓa gane ba,

    kuma ko su dinga ji, ba za su taɓa fahimta ba,

    in ba haka ba, mai yiwuwa, su tuba, a gafarta musu!’ ”

  12. 25 Suka kāsa yarda da juna suka fara watsewa bayan Bulus ya yi wannan magana guda cewa, “Ruhu Mai Tsarki ya faɗa wa kakannin-kakanninku gaskiya sa’ad da ya ce ta bakin annabi Ishaya cewa,

    26 “ ‘Je ka wurin mutanen nan ka ce,

    “Za ku yi ta ji amma ba za ku fahimta ba;

    za ku yi ta dubawa, amma ba za ku gani ba.”

    27 Gama zuciyar mutanen nan ta yi tauri;

    da ƙyar suke ji da kunnuwansu,

    sun kuma rufe idanunsu.

    In ba haka ba za su iya gani da idanunsu,

    su ji da kunnuwansu,

    su fahimta a zukatansu,

    su kuma juyo, in kuwa warkar da su.’

  13. 17 To, ina dai faɗa muku, ina kuma nace faɗa muku a cikin Ubangiji, cewa kada ku ci gaba da yin rayuwa kamar yadda Al’ummai suke yi, masu banzan tunani. 18 Suna a cikin duhu a fahimtarsu, kuma a rabe suke daga ran Allah saboda jahilcin da yake cikinsu ta dalilin taurarewar zukatansu. 19 Ba sa damu da wani abu ko mai kyau ko marar kyau. Rayukansu sun cika da kowace irin ƙazanta da haɗama.

    20 Amma ba abin da aka koya muku ke nan ba sa’ad da kuka zo ga sanin Kiristi. 21 Da yake kun ji duka game da shi, kuka kuma koyi gaskiyar da take cikin Yesu, 22 sai ku tuɓe tsohon mutumin nan naku da kuma rayuwarku ta dā, wadda take lalacewa saboda sha’awace-sha’awacen da suke ruɗe ku. 23 A maimakon haka, bari Ruhu yă sabunta tunaninku da kuma halayenku. 24 Ku sanya sabon halin nan da aka halitta bisa ga kamannin Allah, halin nan kuwa, yă bayyana cikin adalci, da zaman tsarki.

  14. 20 Mun san cewa Ɗan Allah ya zo duniya, ya kuma ba mu ganewa domin mu san shi wanda yake na gaskiya. Mu kuwa muna cikinsa, shi da yake Allah na gaskiya wato, cikin Ɗansa Yesu Kiristi. Shi ne Allah na gaskiya da kuma rai na har abada.

  15. 8 “Tambayi na gaba da kai

    ka ji abin da iyayenka suka koya

    9 gama jiya kaɗai aka haife mu ba mu san kome ba,

    kuma kwanakinmu a duniya masu wucewa ne.

    10 Ba za su bishe ka su kuma gaya maka abin da za ka yi ba?

    Ba za su yi magana daga cikin hikimar da suke da ita ba?

  16. 28 Ya kuma ce wa mutum,

    ‘Tsoron Ubangiji shi ne hikima,

    kuma guje wa mugunta shi ne fahimi.’ ”

  17. 9 Kada ka zama kamar doki ko doki,

    wanda ba su da azanci

    wanda dole sai an bi da su da linzami da ragama

    in ba haka ba, ba za su zo wurinka ba.

  18. 6 Gama Ubangiji yana ba da hikima,

    daga bakinsa kuma, sani da ganewa sukan fito.

  19. 14 Shawara da yin tunani mai kyau nawa ne;

    ina da fahimi da kuma iko.

  20. 10 “Tsoron Ubangiji shi ne mafarin hikima,

    sanin Mai Tsarki kuwa fahimi ne.

  21. 12 Mutum da ba shi da azanci kan ki maƙwabci,

    amma mutum mai fahimi kan ƙame harshensa.

  22. 11 Duk wanda ya nome gonarsa zai sami abinci a yalwace,

    amma shi da yake naushin iska marar azanci ne.

  23. 15 Fahimta mai kyau kan sami tagomashi,

    amma hanyar marar aminci tana da wuya.

  24. 27 Mutum mai sani yakan yi la’akari da amfani da kalmomi,

    mutum mai basira kuma natsattse ne.

  25. 1 Mutumin da ba ya abokantaka yakan nema ya cika burinsa ne kaɗai;

    yakan ƙi yarda da kowace maganar da take daidai.

    2 Wawa ba ya sha’awa ya sami fahimta

    amma abin da yake so ya yi kaɗai, shi ne ya ba da ra’ayinsa.

  26. 30 Na wuce cikin gonar rago,

    na wuce cikin gonar inabin mutumin da ba shi da azanci;

    31 ƙayayyuwa sun yi girma ko’ina,

    ciyayi sun rufe ƙasar,

    katangar duwatsu duk ta rushe.

  27. 22 “Mutanena wawaye ne;

    ba su san ni ba.

    Su ’ya’ya ne marasa azanci;

    ba su da fahimi.

    Suna da dabarar aikata mugunta;

    ba su san yadda za su aikata alheri ba.”

  28. 10 Sai ya ce, “Ku ne aka ba sanin asirin mulkin Allah, amma ga sauran mutane kam, ina magana da misalai, saboda,

    “ ‘ko da yake suna kallo, ba za su gani ba,

    ko da yake suna ji, ba za su gane ba.’

  29. 45 Sai ya wayar da tunaninsu don su fahimci Nassi.

  30. 18 Wannan yana bukata hikima. Duk mai hankali, sai yă lissafta lambar dabbar, gama lamban nan ta mutum ne. Lambarta kuwa ita ce 666.

  31. 4 Ka rufe zuciyarsu yadda ba za su iya ganewa ba,

    saboda haka ba za ka bari su yi nasara ba.

  32. 8 Amma ruhun da yake cikin mutum,

    numfashin Maɗaukaki shi ne yake ba shi ganewa.

  33. 10 “Saboda haka ku saurare ni, ku masu ganewa.

    Ko kaɗan Allah ba ya mugunta,

    Maɗaukaki ba ya kuskure.

    11 Yana biyan mutum bisa ga abin da ya yi;

    yana kawo masa abin da ayyukansa suka jawo.

  34. 36 Wane ne yake cika zuciya da hikima

    ko kuma yake ba zuciya ganewa?

  35. 34 Ka ba ni ganewa, zan kuwa kiyaye dokarka

    in kuma yi biyayya da ita da dukan zuciyata.

  36. 130 Fassarar maganganunka sukan ba da haske;

    sukan ba da ganewa ga marar ilimi.

  37. 5 Shugabanmu mai girma ne mai iko duka;

    ganewarsa ba shi da iyaka.

  38. 1 Ku saurara ’ya’yana ga koyarwar mahaifinku;

    ku mai da hankali, ku sami fahimi.

  39. 2 Ruhun Ubangiji zai kasance a kansa,

    Ruhun hikima da na fahimta,

    Ruhun shawara da na iko,

    Ruhun sani da na tsoron Ubangiji,

  40. 28 Ba ku sani ba?

    Ba ku ji ba?

    Ubangiji madawwamin Allah ne,

    Mahaliccin iyakokin duniya.

    Ba zai taɓa gaji ko yă kasala ba,

    kuma fahimtarsa ya wuce gaban ganewar mutum.

  41. 10 “Ku ne shaiduna,” in ji Ubangiji,

    “bawana kuma wanda na zaɓa,

    saboda ka sani ka kuma gaskata ni

    ka kuma fahimci cewa ni ne shi.

    Kafin ni babu allahn da aka siffanta,

    ba kuwa za a yi wani a bayana ba.

  42. 24 amma bari shi wanda yake taƙama ya yi taƙama da wannan,

    cewa ya fahimci ya kuma san ni,

    cewa ni ne Ubangiji, wanda yake yin alheri,

    gaskiya da kuma adalci a duniya,

    gama a waɗannan ne nake jin daɗi,”

    in ji Ubangiji.

  43. 21 Yana sāke lokuta,

    yana tuɓe sarakuna yana kuma naɗa waɗansu.

    Yana ba da hikima ga masu hikima

    kuma ilimi ga masu basira.

  44. 23 Amma wanda ya karɓi irin da ya fāɗi a ƙasa mai kyau, shi ne mutumin da yakan ji maganar yă kuwa fahimce ta. Yakan ba da amfani wani riɓi ɗari, sittin, ko talatin na abin da aka shuka.”

  45. 18 Ya ce, “Ashe, ba ku da saurin ganewa? Ba ku gane cewa ba abin da yake shiga mutum daga waje ba ne yake ƙazantar da shi. 19 Gama ba ya shiga cikin zuciyarsa, sai dai cikin tumbinsa, sa’an nan kuma yă fita daga jikinsa.” (Da faɗin haka, Yesu ya nuna tsabtar kowane irin abinci.)

    20 Ya ci gaba, “Abin da yake fitowa daga mutum ne yake ƙazantar da shi. 21 Gama daga ciki, daga zuciyar mutane, mugayen tunani suke fitowa, fasikanci, sata, kisankai, zina, 22 kwaɗayi, ƙeta, ruɗu, ƙazantaccen sha’awa, kishi, ɓata suna, girman kai da kuma wauta. 23 Duk waɗannan mugayen abubuwa daga cikin suke fitowa, suna kuma ƙazantar da mutum.”

  46. 30 Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan hankalinka, da kuma dukan ƙarfinka.’ 31 Na biyun ita ce, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’ Ba wata doka da ta fi waɗannan.”

    32 Mutumin ya ce, “Malam, ka faɗi daidai. Daidai ne da ka ce, Allah ɗaya ne, babu kuma wani sai shi. 33 Nuna ƙauna ga Allah da dukan zuciyarka, da dukan ganewarka, da dukan ƙarfinka, da kuma nuna ƙauna ga maƙwabcinka kamar kanka, ya fi dukan hadayun ƙonawa da sadakoki.”

    34 Da Yesu ya ga ya amsa da hikima, sai ya ce masa, “Ba ka da nisa da mulkin Allah.” Daga lokacin, ba wanda ya yi karambani yin masa wata tambaya.

  47. 32 Amma ya ce musu, “Ina da abincin da ba ku san kome a kai ba.”

    33 Sai almajiran suka ce wa juna, “Shin, ko wani ya kawo masa abinci ne?”

  48. 43 Me ya sa ba kwa gane da maganata? Don ba kwa iya jin abin da nake faɗi. 44 Ku na ubanku ne, Iblis, kuna kuwa so ku aikata abin da ubanku yake so. Shi mai kisankai ne tun farko. Ba ruwansa da gaskiya, gama gaskiya ba ta cikinsa. Yayinda yake ƙarya, yana yin halinsa ne, gama shi maƙaryaci ne, uban ƙarairayi kuma. 45 Amma domin ina faɗin gaskiya, ba kwa gaskata!

  49. 40 “Ya makantar da idanunsu

    ya kuma taurare zukatansu,

    don kada su gani da idanunsu,

    ko su fahimta a zukatansu,

    ko kuwa su juyo, har in warkar da su.”

  50. 30 Sai Filibus ya ruga zuwa wajen keken yaƙin ya kuma ji mutumin yana karatun littafin annabin Ishaya. Filibus ya yi tambaya ya ce, “Ka fahimci abin da kake karantawa?”

    31 Sai ya ce, “Ina fa zan iya, in ba dai wani ya fassara mini ba?” Saboda haka sai ya gayyaci Filibus yă hau yă zauna tare da shi.

  51. 18 Ana bayyana fushin Allah daga sama a kan dukan rashin sanin Allah da kuma muguntar mutanen da suke danne gaskiya ta wurin muguntarsu, 19 gama abin da ana iya sani game da Allah a bayyane yake a gare su, domin Allah ya bayyana musu shi. 20 Gama tun halittar duniya halayen Allah marar ganuwa, madawwamin ikonsa da kuma allahntakarsa, ana iya ganinsu sarai, ana fahimtarsu ta wurin abubuwan da Allah ya halitta, domin kada mutane su sami wata hujja.

    21 Gama ko da yake sun san Allah, ba su ɗaukaka shi a matsayin Allah ko su gode masa ba, sai dai tunaninsu ya zama banza, zukatansu masu wauta kuma suka duhunta.

  52. 21 Sai dai kamar yadda yake a rubuce,

    “Waɗanda ba a faɗa musu labarinsa ba za su gani,

    waɗanda kuma ba su ji ba za su fahimta.”

  53. 16 ban fasa yin godiya saboda ku ba, ina tuna da ku cikin addu’o’ina. 17 Ina ta roƙo cewa Allah na Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba Maɗaukaki, yă ba ku Ruhun hikima da na ganewa, domin ku san shi da kyau. 18 Ina kuma addu’a cewa zuciyarku tă waye don ku gane ko mene ne sa zuciyan nan da ya kira ku a kansa, ku kuma san darajar dukiyan nan wadda take ta mutanen Allah, wato, albarkunsa. 19 Ina addu’a ku san girman ikon Allah wanda ya wuce misali, wanda yake namu. Ikon da yake aiki a cikinmu, ɗaya ne da ikon nan 20 da ya tā da Kiristi daga matattu, ya kuma sa ya zauna a hannun damansa a cikin mulkin samaniya. 21 Yanzu yana mulki a kan dukan masu sarauta, da masu iko, da masu ƙarfi, da kuma masu mulki. Yana mulkin kome a wannan duniya, zai kuma yi mulkin duniya mai zuwa. 22 Allah ya sa kome a ƙarƙashin ikonsa, ya kuma ba shi iko a kan kome don amfanin ikkilisiya. 23 Kuma ikkilisiya ce jikinsa; ta kuma cika da Kiristi, wanda ya cika kome ta kowace hanya.

  54. 14 Saboda wannan ne nake a durƙushe a gaban Uba, 15 wanda ya ba wa kowane iyali a sama da ƙasa suna. 16 Ina addu’a cewa daga yalwar ɗaukakarsa zai ƙarfafa ku da iko daga ciki ta wurin Ruhunsa. 17 Ina addu’a domin Kiristi yă zauna a cikin zukatanku ta wurin bangaskiya. Ina kuma addu’a saboda ku da kuka kahu sosai cikin ƙauna, 18 don ku sami iko, tare da dukan tsarkaka, ku fahimci fāɗi, tsawo, da kuma zurfin ƙaunar Kiristi take. 19 Ku kuma san wannan ƙauna wadda ta fi gaban sani, domin a cika ku da dukan cikar Allah.

  55. 9 Addu’ata ita ce ƙaunarku tă yi ta cin gaba da ƙaruwa cikin sani da kuma zurfin ganewa, 10 don ku iya rarrabe abin da yake mafi kyau, ku kuma zama da tsarki, marasa aibi har yă zuwa ranar Kiristi,

  56. 7 Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za tă tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.

  57. 3 Ta wurin bangaskiya ne muka fahimci cewa an halicci duniya bisa ga umarnin Allah, saboda an halicce abin da ake gani daga abin da ba a gani.

  58. 13 Wane ne mai hikima da fahimta a cikinku? Bari yă nuna ta ta wurin rayuwarsa mai kyau, ta wurin ayyukan da aka yi cikin tawali’un da suke fitowa daga hikima.