37 Bible Verses About God's Beautiful Creation
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
1 A farko-farko, Allah ya halicci sama da ƙasa. 2 To, ƙasa dai ba ta da siffa, babu kuma kome a cikinta, duhu ne kawai ya rufe ko’ina, Ruhun Allah kuwa yana yawo a kan ruwan.
3 Sai Allah ya ce, “Bari haske yă kasance,” sai kuwa ga haske. 4 Allah ya ga hasken yana da kyau, sai ya raba tsakanin hasken da duhu. 5 Allah ya kira hasken “yini,” ya kuma kira duhun “dare.” Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta fari ke nan.
6 Allah ya ce, “Bari sarari yă kasance tsakanin ruwaye domin yă raba ruwa da ruwa.” 7 Saboda haka Allah ya yi sarari ya raba ruwan da yake ƙarƙashin sararin da ruwan da yake bisansa. Haka kuwa ya kasance. 8 Allah ya kira sararin “sama.” Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta biyu ke nan.
9 Allah ya ce, “Bari ruwan da yake ƙarƙashin sama yă tattaru wuri ɗaya, bari kuma busasshiyar ƙasa tă bayyana.” Haka kuwa ya kasance. 10 Allah ya kira busasshiyar ƙasar “doron ƙasa,” ruwan da ya taru kuma, ya kira “tekuna.” Allah ya ga yana da kyau.
11 Sa’an nan Allah ya ce, “Bari ƙasa tă fid da tsire-tsire, da shuke-shuke, da itatuwa a bisa ƙasa masu ba da amfani da ’ya’ya a cikinsu, bisa ga irinsu.” Haka kuwa ya kasance. 12 Ƙasar ta fid da tsire-tsire, da shuke-shuke masu ba da ’ya’ya bisa ga irinsu, ta fid kuma da itatuwa masu ba da ’ya’ya da iri a cikinsu bisa ga irinsu. Allah ya ga yana da kyau. 13 Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta uku ke nan.
14 Allah kuma ya ce, “Bari haskoki su kasance a sararin sama domin su raba yini da dare, bari su zama alamu domin su nuna yanayi, da ranaku, da kuma shekaru, 15 bari kuma haskokin su kasance a sararin sama domin su ba da haske a duniya.” Haka kuwa ya kasance. 16 Allah ya yi manyan haskoki biyu, babban hasken yă mallaki yini, ƙaramin kuma yă mallaki dare. Ya kuma yi taurari. 17 Allah ya sa su a sararin sama domin su ba da haske a duniya, 18 su mallaki yini da kuma dare, su kuma raba haske da duhu. Allah kuwa ya ga yana da kyau. 19 Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta huɗu ke nan.
20 Allah ya ce, “Bari ruwa yă cika da halittu masu rai, bari tsuntsaye kuma su tashi sama a bisa duniya a sararin sama.” 21 Allah ya halicci manyan halittun teku, da kowane mai rai da abin da yake motsi a ruwa, bisa ga irinsu, da kuma kowane tsuntsu mai fiffike bisa ga irinsa. Allah kuwa ya ga yana da kyau. 22 Allah ya albarkace su ya ce, “Ku yi ta haihuwa ku kuma ƙaru da yawa, ku cika ruwan tekuna, bari kuma tsuntsaye su yi yawa a bisa duniya.” 23 Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta biyar ke nan.
24 Allah kuwa ya ce, “Bari ƙasa tă ba da halittu masu rai bisa ga irinsu; dabbobi da halittu masu rarrafe, da kuma namun jeji, kowane bisa ga irinsa.” Haka kuwa ya kasance. 25 Allah ya halicci namun jeji bisa ga irinsu, dabbobi bisa ga irinsu, da kuma dukan halittu masu rarrafe a ƙasa bisa ga irinsu. Allah kuwa ya ga yana da kyau.
26 Sa’an nan Allah ya ce, “Bari mu yi mutum cikin siffarmu, cikin kamanninmu, bari kuma su yi mulki a bisa kifin teku, tsuntsayen sama, da kuma dabbobi, su yi mulki a bisa dukan duniya, da kuma a bisa dukan halittu, da masu rarrafe a ƙasa.”
27 Saboda haka Allah ya halicci mutum cikin siffarsa.
Cikin kamannin Allah, Allah ya halicci mutum.
Miji da mace ya halicce su.
28 Allah ya albarkace su, ya kuma ce musu, “Ku yi ta haihuwa ku ƙaru da yawa, ku mamaye duniya, ku mallake ta. Ku yi mulki a bisa kifin teku, da tsuntsayen sararin sama, da kuma bisa kowace halitta mai rai wadda take rarrafe a ƙasa.”
29 Sa’an nan Allah ya ce, “Ga shi, na ba ku kowane tsiro mai ba da ’ya’ya masu kwaya da suke a fāɗin duniya, da dukan itatuwa masu ba da ’ya’ya, don su zama abinci a gare ku. 30 Na kuma ba da dukan dabbobin ƙasa, da dukan tsuntsayen sama, da dukan abin da yake rarrafe a ƙasa, da dai iyakar abin da yake numfashi; haka kuma na ba da ganyaye su zama abinci.” Haka kuwa ya kasance.
31 Allah ya ga dukan abin da ya yi, yana da kyau ƙwarai. Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta shida ke nan.
-
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit. Zabura ta Dawuda.
1 Ya Ubangiji, shugabanmu,
sunanka da girma take a cikin dukan duniya!
Ka kafa ɗaukakarka
bisa sammai.
2 Daga leɓunan yara da jarirai
ka kafa yabo domin su sa abokan gābanka
da masu ɗaukan fansa su yi shiru.
3 Sa’ad da na dubi sammai,
aikin yatsotsinka,
wata da taurari
waɗanda ka ajiye a wurarensu,
4 wane ne mutum da kake tunawa da shi,
ɗan mutum da kake lura da shi?
5 Ka yi shi ƙasa kaɗan da Allah
ka yi masa rawani da ɗaukaka da girma.
6 Ka mai da shi mai mulki bisa ayyukan hannuwanka;
ka sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa,
7 dukan shanu da tumaki,
da kuma namun jeji,
8 tsuntsayen sararin sama
da kifin teku,
da dukan abin da yake yawo a ƙarƙashin ruwan teku.
9 Ya Ubangiji, shugabanmu,
sunanka da girma take a cikin dukan duniya!
-
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda.
1 Sammai suna shelar ɗaukakar Allah;
sararin sama suna furta aikin hannuwansa.
2 Kowace rana tana yin jawabi;
kowane dare yana nuna sani.
3 Ba magana, ba kalmar da aka hurta,
ba wani amon da aka ji daga gare su.
4 Duk da haka muryarsu tana kaiwa ga dukan duniya,
kalmominsu zuwa iyakokin duniya.
A sammai Allah ya kafa tenti domin rana,
5 wanda yake kamar ango mai fitowa daga rumfarsa,
kamar gwani ɗan wasan da yake farin ciki yă yi tsere.
6 Takan taso daga ƙarshen sammai
ta kewaye zuwa wancan;
babu abin da yake ɓuya wa zafinta.
-
18 Ana bayyana fushin Allah daga sama a kan dukan rashin sanin Allah da kuma muguntar mutanen da suke danne gaskiya ta wurin muguntarsu, 19 gama abin da ana iya sani game da Allah a bayyane yake a gare su, domin Allah ya bayyana musu shi. 20 Gama tun halittar duniya halayen Allah marar ganuwa, madawwamin ikonsa da kuma allahntakarsa, ana iya ganinsu sarai, ana fahimtarsu ta wurin abubuwan da Allah ya halitta, domin kada mutane su sami wata hujja.
21 Gama ko da yake sun san Allah, ba su ɗaukaka shi a matsayin Allah ko su gode masa ba, sai dai tunaninsu ya zama banza, zukatansu masu wauta kuma suka duhunta. 22 Ko da yake sun ɗauka su masu hikima ne, sai suka zama wawaye, 23 suka kuma yi musayar ɗaukakar Allah marar mutuwa da siffofin da aka ƙera su yi kama da mutum mai mutuwa da tsuntsaye da dabbobi da kuma halittu masu ja da ciki.
-
Zabura ta Dawuda.
1 Duniya ta Ubangiji ce da kome da yake cikinta,
duniya, da dukan waɗanda suke zama a cikinta;
2 gama ya gina ta a kan tekuna
ya kafa ta a kan ruwaye.
-
1 Yabi Ubangiji, ya raina.
Ya Ubangiji Allahna, kana da girma ƙwarai;
kana saye da daraja da ɗaukaka.
2 Ubangiji ya naɗe kansa da haske kamar riga
ya shimfiɗa sammai kamar tenti
3 ya kafa ginshiƙan ɗakin samansa a kan ruwaye.
Ya maido da gizagizai suka zama keken yaƙinsa
yana hawa a kan fikafikan iska.
4 Ya mai da iska suka zama ’yan saƙonsa
harsunan wuta kuma bayinsa.
5 Ya kafa duniya a kan tussanta;
ba za a iya matsar da ita ba.
6 Ka rufe ta da zurfi kamar da riga
ruwaye sun tsaya a bisa duwatsu.
7 Amma a tsawatawarka ruwaye suka gudu
da jin ƙarar tsawanka suka ruga da gudu;
8 suka gudu a bisa duwatsu,
suka gangara zuwa cikin kwaruruka,
zuwa wurin da ka shirya musu.
9 Ka kafa iyakar da ba a iya tsallakawa;
ba za su ƙara rufe duniya ba.
10 Ya sa maɓulɓulai suka zuba ruwa cikin kwaruruka;
yana gudu tsakanin duwatsu.
11 Suna ba da ruwa ga dukan namun jeji;
jakunan jeji suna kashe ƙishirwansu.
12 Tsuntsaye sarari suna sheƙunansu kusa da ruwan;
suna rera cikin rassa.
13 Yana wa duwatsu banruwa daga ɗakinsa na sama;
ƙasa tana ƙoshiya da amfanin aikinsa.
14 Yana sa ciyawa tă yi girma saboda shanu,
tsire-tsire domin mutum ya nome,
suna fid da abinci daga ƙasa,
15 ruwan inabi yakan sa zuciyar mutum tă yi murna,
mai kuwa yakan sa fuska tă yi haske,
abinci kuma da yake riƙe zuciyarsa.
16 Ana yi wa itatuwan Ubangiji banruwa sosai,
al’ul na Lebanon da ya shuka.
17 A can tsuntsaye suke sheƙunnansu;
shamuwa tana da gidanta a itatuwan fir.
18 Manyan duwatsu na awakin jeji ne;
tsagaggun duwatsun mafaka ne ga rema.
19 Wata ne ke ƙididdigar lokuta,
rana kuma ta san sa’ad da za tă fāɗi.
20 Ka yi duhu, sai ya zama dare,
sai dukan namun jeji a kurmi suka fito a maƙe.
21 Zakoki sun yi ruri sa’ad da suke farauta
suna kuma neman abincinsu daga Allah.
22 Rana ta fito, sai suka koma shiru;
suka koma suka kwanta a kogwanninsu.
23 Mutum yakan tafi aikinsa,
zuwa wurin aikinsa har yamma.
24 Ina misalin yawan aikinka, ya Ubangiji!
Cikin hikima ka yi su duka;
duniya ta cika da halittunka.
25 Akwai teku, babba da kuma fāɗi,
cike da halittun da suka wuce ƙirga,
abubuwa masu rai babba da ƙarami.
26 A can jiragen ruwa suna kai komo,
kuma dodon ruwan da ka yi, yă yi wasa a can.
27 Waɗannan duka suna dogara gare ka
don ka ba su abincinsu a daidai lokaci.
28 Sa’ad da ba su da shi,
sai su tattara shi;
sa’ad da ka buɗe hannunka,
sukan ƙoshi da abubuwa masu kyau.
29 Sa’ad da ka ɓoye fuskarka,
sai su razana;
sa’ad da ka ɗauke numfashinsu,
sai su mutu su kuma koma ga ƙura.
30 Sa’ad da ka aika da Ruhunka,
sai su halittu,
su kuma sabunta fuskar duniya.
31 Bari ɗaukakar Ubangiji ta dawwama har abada;
bari Ubangiji yă yi farin ciki cikin aikinsa,
32 shi wanda ya dubi duniya, sai ta razana,
wanda ya taɓa duwatsu, sai suka yi hayaƙi.
33 Zan rera ga Ubangiji dukan raina;
zan rera yabo ga Allahna muddin ina raye.
34 Bari tunanina yă gamshe shi,
yayinda nake farin ciki a cikin Ubangiji.
35 Amma bari masu zunubi su ɓace daga duniya
mugaye kuma kada a ƙara ganinsu.
Yabi Ubangiji, ya raina.
Yabi Ubangiji.
-
24 “Allahn da ya halicci duniya da kome da yake cikinta shi ne Ubangijin sama da ƙasa, ba ya kuma zama a haikalin da aka gina da hannuwa. 25 Ba a kuma yin masa hidima da hannun mutum, sai ka ce mai bukatan wani abu, domin shi kansa ne ke ba wa dukan mutane rai da numfashi da kuma kome. 26 Daga mutum ɗaya, ya halicci kowace al’ummar mutane, don su zauna a duk duniya; shi ne kuma ya ƙaddara lokuta bisa ga tsarinsu da kuma inda za su kasance. 27 Allah ya yi wannan domin mutane su neme shi mai yiwuwa kuma su lalluba su same shi, ko da yake ba shi da nisa daga kowannenmu. 28 ‘Gama a cikinsa ne muke rayuwa muke motsi muka kuma kasance.’ Yadda waɗansu mawaƙanku suka ce, ‘Mu zuriyarsa ce.’
29 “Saboda haka da yake mu zuriyar Allah ce, kada mu yi tsammani cewa kamannin Allah yana kama da zinariya ko azurfa ko dutse, siffar da mutum ya ƙago ta wurin dabararsa.
-
7 “Amma ka tambayi dabbobi, za su kuma koya maka,
ko kuma tsuntsayen sararin sama kuma za su gaya maka.
8 Ko ka yi magana da duniya, za tă kuma koya maka,
ko kuma ka bar kifin teku su sanar da kai.
9 Wane ne cikin waɗannan bai san
cewa hannun Ubangiji ne ya yi wannan ba?
10 Ran kowace halitta yana a hannunsa,
haka kuma numfashin dukan ’yan adam.
-
1 Tun farar farawa akwai Kalma, Kalman kuwa yana nan tare da Allah, Kalman kuwa Allah ne. 2 Yana nan tare da Allah tun farar farawa. 3 Ta wurin Kalman ne aka halicci dukan abubuwa. In ba tare da shi ba, babu abin da aka yi wanda aka yi.
-
4 Wannan shi ne asalin tarihin sammai da duniya sa’ad da aka halicce su.
Sa’ad da Ubangiji Allah ya yi duniya da sammai, 5 babu tsiro a duniya kuma ganyaye ba su tsira a busasshiyar ƙasa ko ba, gama Ubangiji Allah bai aiko da ruwan sama a kan duniya ba tukuna, babu kuma wani mutumin da zai nome ƙasar, 6 amma dai rafuffuka suna ɓullo da ruwa daga ƙasa suna jiƙe ko’ina a fāɗin ƙasa. 7 Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mutum daga turɓayar ƙasa, ya kuma hura numfashin rai cikin hancinsa, mutumin kuwa ya zama rayayyen taliki.
8 To, fa, Ubangiji Allah ya yi lambu a gabas, a Eden, a can kuwa ya sa mutumin da ya yi. 9 Ubangiji Allah ya kuma sa kowane irin itace ya tsira daga ƙasa, itace mai kyan gani, mai amfani kuma don abinci. A tsakiyar lambun kuwa akwai itacen rai da kuma itacen sanin abin da yake da kyau da abin da yake mugu.
-
12 Ai, ni ne wanda ya yi duniya
na kuma halicci mutum a kanta.
Hannuwana ne sun miƙe sammai;
na umarci rundunar sararin sama.
-
11 “Ya Ubangijinmu da Allahnmu,
ka cancanci ɗaukaka da girma da iko,
domin ka halicci dukan abubuwa,
kuma ta wurin nufinka aka halicce su
suka kuma kasance.”
-
5 Ubangiji yana ƙaunar adalci
duniya ta cika da ƙaunarsa marar ƙarewa.
6 Ta wurin maganar Ubangiji aka yi sammai,
rundunar taurarinsu kuwa da numfashin bakinsa.
7 Ya tattara ruwan teku cikin tuluna;
ya sa zurfafa cikin gidajen ajiya.
8 Bari dukan duniya ta ji tsoron Ubangiji;
bari dukan mutanen duniya su girmama shi.
9 Gama ya yi magana, abu ya kuwa kasance;
ya umarta, ya kuwa tsaya daram.
-
3 Gama Ubangiji Allah mai girma ne,
babban Sarki a bisa dukan alloli.
4 A hannunsa ne zurfafan duniya suke,
ƙwanƙolin dutse kuma nasa ne.
5 Teku nasa ne, gama shi ne ya yi shi,
da hannuwansa kuma ya yi busasshiyar ƙasa.
-
13 Gama ka halicci ciki-cikina;
ka gina ni gaba ɗaya a cikin mahaifar mahaifiyata.
14 Ina yabonka domin yadda ka yi ni abin tsoro ne da kuma abin mamaki;
ayyukanka suna da banmamaki,
na san da haka sosai.
15 Ƙasusuwana ba a ɓoye suke a gare ka ba
sa’ad da aka yi ni asirce.
Sa’ad da saƙa ni gaba ɗaya a zurfafan duniya.
16 Idanunka sun ga jikina marar fasali;
dukan kwanakin da aka tsara mini a rubuce suke a littafinka
kafin ɗayansu yă kasance.
-
19 Halitta tana jira da marmari ta ƙosa ta ga bayyanuwar ’ya’yan Allah. 20 Gama an sa halitta a cikin wulaƙanci, ba da son ta ba, sai dai ta wurin nufin wannan da ya mai da ita haka, da bege 21 cewa za a ’yantar da halitta kanta daga bautarta ga ruɓewa a kuma kawo ta cikin ’yancin ɗaukakar ’ya’yan Allah.
22 Mun san cewa dukan halitta tana nishi sai ka ce mace mai naƙuda har yă zuwa wannan lokaci.
-
10 Ai, mu aikinsa ne, an sāke halittarmu a cikin Kiristi Yesu musamman domin mu yi kyawawan ayyuka, waɗanda Allah ya tanadar mana tun da fari, mu yi.
-
Zabura ta Asaf.
1 Maɗaukaki, Allah, Ubangiji,
ya yi magana ya kuma kira duniya
daga fitowar rana zuwa inda take fāɗuwa.
2 Daga Sihiyona, cikakkiya a kyau,
Allah na haskakawa.
3 Allahnmu yana zuwa
ba kuwa zai yi shiru ba;
wuta mai cinyewa a gabansa,
babban hadari kuma ya kewaye shi.
4 Ya kira sammai da suke bisa,
da duniya, don yă shari’anta mutanensa.
5 “Ku tattara mini shafaffuna,
waɗanda suka yi alkawari da ni ta wurin hadaya.”
6 Sammai kuwa sun yi shelar adalcinsa
gama Allah kansa alƙali ne. Sela
-
1 Yabi Ubangiji.
Yabi Ubangiji daga sammai,
yabe shi a bisa sammai.
2 Yabe shi, dukanku mala’ikunsa,
yabe shi, dukanku rundunarsa na sama.
3 Yabe shi, rana da wata,
yabe shi, dukanku taurari masu haskakawa.
4 Yabe shi, ku bisa sammai
da kuma ku ruwan bisa sarari.
5 Bari su yabi sunan Ubangiji,
gama ya umarta aka kuwa halicce su.
6 Ya sa su a wurarensu har abada abadin;
ya ba da umarnin da ba zai taɓa shuɗe ba.
7 Yabi Ubangiji daga duniya,
ku manyan halittun teku da kuma dukan zurfafan teku,
8 walƙiya da ƙanƙara, dusar ƙanƙara da gizagizai,
hadirin iskar da suke biyayya da umarnansa,
9 ku duwatsu da dukan tuddai,
itatuwa masu ’ya’ya da dukan al’ul,
10 namun jeji da dukan dabbobin gida,
ƙanana halittu da tsuntsaye masu firiya,
11 sarakunan duniya da dukan al’ummai,
ku sarakuna da dukan masu mulkin duniya,
12 samari da ’yan mata,
tsofaffi da yara.
13 Bari su yabi sunan Ubangiji,
gama sunansa ne kaɗai mafi ɗaukaka;
darajarsa ta fi ƙarfin duniya da sammai.
14 Ya tayar wa mutanensa ƙaho,
yabon dukan tsarkakansa,
na Isra’ila, mutanen da suke kurkusa da zuciyarsa.
Yabi Ubangiji.
-
11 Ya yi kowane abu da kyau a lokacinsa. Ya kuma sa matuƙa a zukatan mutane, duk da haka sun kāsa gane abin da Allah ya yi daga farko zuwa ƙarshe.
-
5 Da ikon mai ƙarfi da kuma hannuna da na miƙa na yi duniya da mutanenta da kuma dabbobin da suke ciki, na ba da ita ga duk wanda na ga dama.
-
28 “Me ya sa kuke damuwa a kan riguna? Ku dubi yadda furannin jeji suke girma mana. Ba sa aiki ko saƙa. 29 Duk da haka ina gaya muku ko Solomon cikin dukan darajarsa bai sa kayan adon da ya kai na ko ɗaya a cikinsu ba. 30 In haka Allah yake yi wa ciyawar jeji sutura, wadda yau tana nan, gobe kuwa a jefa a cikin wuta, ba zai ma fi yi muku sutura ba, ya ku masu ƙarancin bangaskiya? 31 Don haka, kada ku damu, kuna cewa, ‘Me za mu ci?’ Ko, ‘Me za mu sha?’ Ko kuma, ‘Me za mu sa?’ 32 Gama marasa sanin Allah suna fama neman dukan waɗannan abubuwa, Ubanku na sama kuwa ya san kuna bukatarsu.
-
29 Ba akan sayar da kanari biyu kobo ɗaya ba? Duk da haka ba ɗayansu da zai fāɗi ƙasa ba da yardar Ubanku. 30 Kai, ko gashin kanku ma duk an ƙidaya su. 31 Saboda haka kada ku ji tsoro; kun fi kanari masu yawa, daraja nesa.
-
7 Ya shimfiɗa arewancin sararin sama a sarari;
ya rataye duniya ba a jikin wani abu ba.
8 Ya naɗe ruwaye a cikin gizagizansa,
duk da haka girgijen bai yage saboda nauyi ba.
9 Ya rufe fuskar wata,
ya shimfiɗa gizagizai a kan shi,
10 ya zāna iyakar fuskar ruwa
a kan iyakar da take tsakanin duhu da haske.
11 Madogaran sama sun girgiza,
saboda tsawatawarsa.
12 Da ikonsa ya kwantar da teku;
da hikimarsa ya hallaka dodon ruwan nan Rahab.
13 Da numfashinsa ya sa sararin sama ya yi kyau
da hannunsa ya soke macijin nan mai gudu.
14 Waɗannan kaɗan ke nan daga cikin ayyukansa masu yawa.
Kaɗan kawai muke ji game da shi!
Wane ne kuwa yake iya gane tsawar ikonsa?”
-
11 Yana cika gizagizai da lema;
yana baza walƙiyarsa ta cikinsu.
12 Bisa ga bishewarsa suke juyawa
a kan fuskar duniya,
suna yin dukan abin da ya
umarce su su yi.
13 Yana aiko da ruwa domin horon mutane,
ko kuma don yă jiƙa duniya yă kuma nuna ƙaunarsa.
14 “Ka saurari wannan Ayuba;
ka tsaya ka dubi abubuwan al’ajabi na Allah.
15 Ko ka san yadda Allah yake iko da gizagizai
ya kuma sa walƙiyarsa ta haskaka?
16 Ko ka san yadda gizagizai suke tsayawa cik a sararin sama,
waɗannan abubuwa al’ajabi na mai cikakken sani.
-
11 Sammai naka ne, haka kuma duniya;
ka kafa duniya da dukan abin da yake cikinta.
-
15 Ubangiji Allah ya ɗauko mutumin ya sa shi cikin Lambun Eden domin yă nome shi, yă kuma lura da shi.
-
11 Bari sammai su yi farin ciki, bari duniya tă yi murna;
bari teku tă yi ruri, da kuma dukan abin da yake cikinsa;
12 bari gonaki su yi tsalle da murna, da kuma kome da yake cikinsu.
Ta haka dukan itatuwan kurmi za su rera don farin ciki;
13 za su rera a gaban Ubangiji, gama yana zuwa,
yana zuwa don yă hukunta duniya.
Zai hukunta duniya cikin adalci
mutane kuma cikin amincinsa.
-
13 Sa’ad da ya yi tsawa, ruwaye a cikin sammai sukan yi ƙugi;
yakan sa gizagizai su taso daga iyakokin duniya.
Yakan aiki walƙiya da ruwan sama
ya fitar da iska daga gidajen ajiyarsa.
-
8 (Shi wanda ya yi Taurarin nan da ake ce Kaza da ’Ya’yanta da kuma Mai Farauta da Kare,
wanda ya mai da duhu ya zama haske
ya kuma baƙanta rana ta zama dare,
yakan kwashe ruwan teku
ya zubar a ƙasa,
Ubangiji ne sunansa,
9 yakan kawo hallaka a mafaka mai ƙarfi
yakan kuma mai da birnin mai katanga ya zama kufai).
-
27 “Ku dubi yadda furanni suke girma. Ba sukan yi aiki, ko saƙa ba, duk da haka, ina faɗa muku cewa, ko Solomon cikin kyakkyawan darajarsa duka, bai yafa kayan ado da ya kai kamar na ko ɗaya a cikinsu ba.
-
6 Kai kaɗai ne Ubangiji. Kai ka yi sammai, har ma da sama sammai, da dukan rundunar taurari, da duniya da kuma dukan abin da yake cikinta, da tekuna da dukan abubuwan da suke cikinsu. Ka ba da rai ga kome, kuma rundunonin sama suna maka sujada.
-
1 Duba, Ubangiji zai wofinta duniya
ya kuma yi kaca-kaca da ita;
zai ɓata fuskarta
ya watsar da mazaunanta,
2 zai zama abu ɗaya
ga firist kamar yadda yake ga mutane,
ga maigida kamar yadda yake ga bawa,
ga uwargijiya kamar yadda yake ga baiwa,
ga mai sayarwa kamar yadda yake ga mai saya,
ga mai karɓan rance kamar yadda yake ga mai ba da rance,
ga mai karɓan bashi kamar yadda yake ga mai ba da bashi.
3 Za a wofinta duniya ƙaƙaf
a kuma washe ta sarai.
Ubangiji ne ya faɗa haka.
4 Duniya ta bushe ta kuma yanƙwane,
duniya tana shan azaba ta kuma raunana,
masu daraja na duniya suna shan azaba.
5 Duniya ta ƙazantu ta wurin mutanenta
sun ƙi yin biyayya da dokoki,
sun keta farillai
suka kuma karya madawwamin alkawari.
6 Saboda haka la’ana za tă auko wa duniya;
dole mutanenta su ɗauki hakkin laifinsu.
Saboda haka aka ƙone mazaunan duniya,
kuma kaɗan ne kurum suka rage.
-
28 Ba ku sani ba?
Ba ku ji ba?
Ubangiji madawwamin Allah ne,
Mahaliccin iyakokin duniya.
Ba zai taɓa gaji ko yă kasala ba,
kuma fahimtarsa ya wuce gaban ganewar mutum.
-
17 “Ga shi, na halicci
sabuwar sama da kuma sabuwar duniya.
Abubuwa na dā za a manta da su,
ba kuwa za a ƙara tuna da su ba.
18 Amma ku yi murna ku kuma yi farin ciki har abada
a abin da na halitta,
gama zan halicci Urushalima ta zama abin murna
mutanenta kuwa abin farin ciki.
-
6 Sai Ubangiji Allah ya sa wata ’yar kuringa ta tsiro, ta yi girma a inda Yunana yake, don ta inuwantar da shi, yă ji daɗi. Yunana kuwa ya yi murna matuƙa da wannan kuringa. 7 Amma kashegari da safe sai Allah ya sa tsutsa ta cinye ’yar kuringar har ta mutu. 8 Sa’ad da rana ta yi sama, sai Allah ya sa iskar gabas mai zafi ta huro, zafin ranar kuma ya buga kan Yunana, har ya ji sai ka ce zai suma. Ya so a ce ya mutu ma, sai ya ce, “Gara in mutu da a ce ina zaune da rai.”
9 Amma Allah ya ce wa Yunana, “Daidai ne ka yi fushi saboda wannan kuringa?”
Sai Yunana ya ce, “I, daidai ne, ina fushi matuƙa, har ina so da na mutu ma.”
10 Sai Ubangiji ya ce, “Ai, wannan kuringa ta tsira dare ɗaya ta kuma ɓace kafin dare na biyu, ba ka yi wata wahala dominta ba, ba kai ne ka sa ta yi girma ba, duk da haka ranka ya ɓace saboda ita. 11 Ashe, ba dole ne in ji tausayin babban birnin nan Ninebe mai mutum sama da dubu ɗari da ashirin (120,000) marasa alhaki, da kuma dabbobi masu yawa ba?”
-
6 Ba ana sayar da kanari biyar a kan kobo biyu ba? Duk da haka, Allah bai manta da ko ɗayansu ba.
Shows Read in context, Share and Copy.