12 Bible Verses About Pets

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Pets
  1. 20 Allah ya ce, “Bari ruwa yă cika da halittu masu rai, bari tsuntsaye kuma su tashi sama a bisa duniya a sararin sama.” 21 Allah ya halicci manyan halittun teku, da kowane mai rai da abin da yake motsi a ruwa, bisa ga irinsu, da kuma kowane tsuntsu mai fiffike bisa ga irinsa. Allah kuwa ya ga yana da kyau. 22 Allah ya albarkace su ya ce, “Ku yi ta haihuwa ku kuma ƙaru da yawa, ku cika ruwan tekuna, bari kuma tsuntsaye su yi yawa a bisa duniya.” 23 Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta biyar ke nan.

    24 Allah kuwa ya ce, “Bari ƙasa tă ba da halittu masu rai bisa ga irinsu; dabbobi da halittu masu rarrafe, da kuma namun jeji, kowane bisa ga irinsa.” Haka kuwa ya kasance. 25 Allah ya halicci namun jeji bisa ga irinsu, dabbobi bisa ga irinsu, da kuma dukan halittu masu rarrafe a ƙasa bisa ga irinsu. Allah kuwa ya ga yana da kyau.

  2. 6 Kyarkeci zai zauna tare da ɗan rago

    damisa za tă kwanta tare da akuya,

    ɗan maraƙi da zaki da ɗan saniya za su yi kiwo tare;

    ɗan yaro ne zai lura da su.

    7 Saniya da beyar za su yi kiwo tare,

    ƙananansu za su kwanta tare,

    zaki kuma zai ci ciyawa kamar saniya.

    8 Jariri zai yi wasa kurkusa da ramin gamsheƙa,

    ɗan yaro kuma zai sa hannunsa a ramin maciji mai mugun dafi.

    9 Ba za su yi lahani ko su hallaka

    wani a dutsena mai tsarki ba,

    gama duniya za tă cika da sanin Ubangiji

    kamar yadda ruwaye suka rufe teku.

    10 A wannan rana Saiwar Yesse zai miƙe kamar tuta don mutanenta; al’ummai za su tattaru wurinsa, wurin hutunsa kuma zai zama mai daraja.

  3. 9 “Yanzu na kafa alkawarina da ku da zuriyarku a bayanku, 10 da kowace halitta mai rai wadda ta kasance tare da kai; wato, tsuntsaye da dabbobin gida da kuma dukan namun jeji, duk dai iyakar abin da ya fita daga jirgin; wato, kowane mai rai na duniya. 11 Na kafa alkawarina da ku, ba za a ƙara hallaka dukan rayuka da ambaliyar ruwa ba; ba za a ƙara yin ambaliya don a hallaka duniya ba.”

  4. 4 Kada ku yi wa saniya takunkumi sa’ad da take tattaka hatsi.

  5. 1 Ubangiji ya aiki Natan wurin Dawuda. Da ya tafi wajensa, sai ya ce, “An yi waɗansu mutum biyu a wani gari, ɗaya mai arziki, ɗayan kuma matalauci. 2 Mai arzikin yana da babban garken tumaki, da kuma shanu, 3 amma matalauci ba shi da kome sai ’yar tunkiyar da ya sayo. Ya yi kiwonta, ta kuwa yi girma tare shi da yaransa. Takan ci tare da shi ta sha ruwa a kwaf nasa, har ma ta kwanta a ƙirjinsa. Ta ma zama kamar ’ya a gare shi.

    4 “To, sai ga wani baƙo ya zo wurin mai arzikin nan, amma mai arzikin ya ƙi yă kama tunkiyarsa, ko saniyarsa yă yanka don yă shirya wa baƙon da ya zo abinci. A maimako, sai ya je ya kama ’yar tunkiyan nan ta matalaucin ya yanka ya shirya wa mutumin da ya zo masa.”

    5 Dawuda ya husata ƙwarai da mutumin, ya ce wa Natan, “Muddin Ubangiji yana a raye, mutumin da ya yi wannan ya cancanci yă mutu! 6 Dole yă biya diyyar tunkiyan nan sau huɗu, domin ya aikata haka ba tausayi.”

  6. 7 “Amma ka tambayi dabbobi, za su kuma koya maka,

    ko kuma tsuntsayen sararin sama kuma za su gaya maka.

    8 Ko ka yi magana da duniya, za tă kuma koya maka,

    ko kuma ka bar kifin teku su sanar da kai.

    9 Wane ne cikin waɗannan bai san

    cewa hannun Ubangiji ne ya yi wannan ba?

    10 Ran kowace halitta yana a hannunsa,

    haka kuma numfashin dukan ’yan adam.

  7. 10 Mai adalci kan kula da bukatun dabbobinsa,

    amma halaye mafi kyau na mugaye su ne ƙeta.

  8. 18 Na sāke yin tunani, “Game da mutane kam, Allah kan gwada su don su san cewa ba su fi dabba ba. 19 Ƙaddarar mutum ɗaya take da ta dabba; ƙaddara ɗaya ce take jiransu biyu. Yadda ɗayan yake mutuwa, haka ma ɗayan. Dukansu numfashinsu iri ɗaya ne; mutum bai fi dabba ba. Kowane abu ba shi da amfani. 20 Duka wuri ɗaya za su tafi; gama duka daga turɓaya suka fito, kuma ga turɓaya duka za su koma. 21 Wa ya tabbatar cewa ruhun mutum yakan tashi sama sa’an nan na dabba yă sauka ƙasa?”

  9. 9 Ku zo, dukanku namun jeji,

    ku zo ku ci, dukanku namun jeji!

    10 Matsaran Isra’ila makafi ne,

    dukansu jahilai ne;

    dukansu bebayen karnuka ne

    ba za su iya haushi ba;

    suna kwance ne kawai suna mafarki,

    suna son barci ba dama.

    11 Su karnuka ne masu kwaɗayi;

    ba su taɓa ƙoshi.

    Su makiyaya ne marasa ganewa;

    duk sun nufi inda suka ga dama,

    kowa yana nemar wa kansa riba.

    12 Kowanne yakan ce, “Zo, bari in samo ruwan inabi!

    Bari mu cika cikinmu da barasa!

    Gobe ma zai zama kamar yau,

    ko ma fiye da haka.”

  10. 6 “Kada ku ba karnuka abin da yake mai tsarki; kada kuma ku jefa wa aladu lu’ulu’anku. In kuka yi haka za su tattake su, sa’an nan su juyo su jijji muku ciwo.

  11. 6 Ba ana sayar da kanari biyar a kan kobo biyu ba? Duk da haka, Allah bai manta da ko ɗayansu ba.

  12. 11 Sai na ga sama a buɗe can kuwa a gabana ga farin doki, sunan mahayinsa Mai Aminci da Mai Gaskiya ne. Da adalci yake shari’a yake kuma yaƙi. 12 Idanunsa sun yi kamar harshen wuta, a kansa kuwa akwai rawani masu yawa. Yana da suna rubuce a kansa da babu wanda ya sani sai dai shi. 13 Yana saye da rigar da aka tsoma a jini, sunansa kuwa Kalman Allah ne. 14 Mayaƙan sama suna biye da shi, suna hawan fararen dawakai, saye da fararen tufafi masu tsabta na lallausan lilin.