105 Bible Verses About Poverty

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Poverty
  1. 2 A ce wani ya shigo cikin taronku saye da zoben zinariya da riguna masu tsada, wani matalauci kuma saye da tsummoki shi ma ya shigo, 3 in kuka mai da hankali na musamman ga mutumin da yake da riguna masu tsadan nan kuka kuma ce, “Ga wurin zama mai kyau dominka,” amma kuka ce wa matalaucin nan, “Kai tsaya daga can,” ko kuwa, “Ka zauna a ƙasa kusa da ƙafafuna,” 4 ashe, ba ku nuna bambanci a tsakaninku ke nan ba, kuka kuma zama alƙalai masu mugayen tunani?

    5 Ku saurara, ’yan’uwana ƙaunatattu. Ashe, Allah bai zaɓi waɗanda suke matalauta a idon duniya don su zama masu wadata cikin bangaskiya, su kuma gāji mulkin da ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari ba? 6 Ga shi kun wulaƙanta matalauta. Ashe, ba masu arziki ne suke cutarku ba? Ba su ba ne suke jan ku zuwa kotu? 7 Ba su ba ne suke ɓata sunan nan mai martaba wanda aka san ku da shi ba?

    8 In fa kun kiyaye dokan nan ta mulki wadda take cikin Nassi mai cewa, “Ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka,” kun yi daidai. 9 Amma in kuka nuna bambanci, kun yi zunubi ke nan shari’a kuma ta same ku da laifi a matsayin masu karya doka.

  2. 3 “Masu albarka ne waɗanda suke matalauta a ruhu,

    gama mulkin sama nasu ne.

  3. 18 “Ruhun Ubangiji yana kaina,

    domin ya shafe ni,

    in yi wa matalauta wa’azin bishara.

    Ya aiko ni in yi shelar ’yanci ga ’yan kurkuku,

    in kuma buɗe idanun makafi,

    in ba da ’yanci ga waɗanda aka danne.

    19 In yi shelar shekarar tagomashin Ubangiji.”

  4. 21 Yesu ya amsa ya ce, “In kana so ka zama cikakke, ka je, ka sayar da dukan dukiyarka ka kuma ba matalauta, za ka kuwa sami dukiya a sama. Sa’an nan ka zo, ka bi ni.”

    22 Da saurayin ya ji haka, sai ya tafi rai a ɓace, don yana da arziki sosai.

    23 Sa’an nan Yesu ya ce wa almajiransa, “Gaskiya nake gaya muku, yana da wuya mai arziki yă shiga mulkin sama. 24 Har wa yau ina gaya muku, zai fi sauƙi raƙumi yă shiga ta kafar allura, da mai arziki yă shiga mulkin Allah.”

  5. 6 Ku tuna fa, duk wanda ya yi shuki kaɗan zai girbe kaɗan, kuma duk wanda ya yi shuki da yawa, zai girbe a yalwace. 7 Ya kamata kowa yă bayar bisa ga abin da ya yi shawara a zuciyarsa, ba tare da jin nauyi ko don dole ba, gama Allah yana son mai bayarwa da daɗin rai. 8 Allah kuwa yana da iko yă ba ku fiye da bukatarku, domin kullum ku wadata da kome ta kowace hanya, kuna ta bayarwa hannu sake, kowane irin kyakkyawan aiki. 9 Kamar yadda yake a rubuce cewa,

    “Ya ba gajiyayyu hannu sake,

    ayyukansa na alheri madawwama ne.”

    10 To, shi da yake ba mai shuka iri, yake kuma ba da abinci a ci, shi ne zai ba ku irin shukawa, yă riɓanya shi, yă kuma albarkaci ayyukanku na alheri da yawa. 11 Za a wadatar da ku ta kowace hanya, domin ku riƙa bayarwa hannu sake a kowane lokaci. Ta wurinmu kuma bayarwarku hannu sake za tă zama sanadin godiya ga Allah.

  6. 25 Yanzu kam, ina hanyata zuwa Urushalima don in kai gudummawa ga tsarkaka a can. 26 Gama Makidoniya da Akayya sun ji daɗin yin gudummawa domin matalautan da suke cikin tsarkakan da suke a Urushalima. 27 Sun kuwa ji daɗin yin haka, gama ya zama kamar bashi ne a gare su. Da yake Al’ummai sun sami rabo cikin albarkun ruhaniyar Yahudawa, ya zama musu kamar bashi su ma su taimaki Yahudawa da albarkunsu na kayan duniya.

  7. 7 Masu adalci sun damu game da adalci don talakawa,

    amma mugaye ba su da wannan damuwa.

  8. 41 Yesu ya zauna ɗaura da inda ake bayarwa, ya kuma dubi yadda taron suke sa kuɗinsu a cikin ɗakunan ajiya haikali. Masu arziki da yawa suka zuba kuɗaɗe masu yawa. 42 Amma wata matalauciya gwauruwa, ta zo ta saka anini biyu, da suka yi daidai da rabin kobo.

    43 Yesu ya kira almajiransa wurinsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, abin da matalauciya gwauruwan nan ta zuba cikin ɗakunan ajiya nan ya fi na sauran dukan. 44 Dukansu sun bayar ne daga cikin arzikinsu; ita kuwa, daga cikin talaucinta, ta ba da kome, duk abin da take da shi na rayuwa.”

  9. 7 Gama ku kanku kun san yadda ya kamata ku bi gurbinmu. Ba mu yi zaman banza sa’ad da muke tare da ku ba, 8 ba mu kuwa ci abincin kowa ba tare da ba mu biya ba. A maimakon haka, mun yi aiki dare da rana, muna fama muna wahala kuma don kada mu nawaita wa waninku. 9 Mun yi wannan, ba don ba mu da ’yancin karɓar irin taimakon nan ba ne, sai dai domin mu zama gurbin da za ku bi. 10 Ko ma a sa’ad da muke tare da ku, mun ba ku wannan umarni cewa, “In mutum ya ƙi yin aiki, kada a ba shi abinci.”

    11 Mun ji cewa waɗansunku suna zaman banza. Ba sa aikin kome; sai shisshigi kurum. 12 Irin waɗannan mutane muna ba da umarni muna kuma gargaɗe su cikin Ubangiji Yesu Kiristi su natsu su kuma nemi abincin da suke ci.

  10. 17 Ka umarci waɗanda suke da arziki a wannan duniya kada su ɗaga kai ko su sa begensu a kan dukiyar da ba ta da tabbaci, sai dai su sa begensu ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don jin daɗinmu. 18 Ka umarce su su yi nagarta, su wadatu cikin ayyuka nagari, su kuma zama masu bayarwa hannu sake da kuma masu niyyar yin taimako. 19 Ta haka za su ajiye wa kansu dukiya a matsayin tushen mai ƙarfi don tsara mai zuwa, don su riƙi rai wanda yake na tabbatacce.

  11. 27 Addinin da Allah Ubanmu ya yarda da shi a matsayin mai tsabta da kuma marar aibi shi ne, a kula da marayu da gwauraye cikin damuwoyinsu, a kuma kiyaye kai daga lalacin da duniya take sa wa.

  12. 19 “An yi wani mutum mai arziki wanda yakan sa tufafi masu ruwan shunayya, da kuma na lallausan lilin, yana kuma cikin rayuwar jin daɗi kullum. 20 A ƙofar gidansa kuma akan ajiye wani mai bara, mai suna Lazarus, wanda jikinsa duk gyambuna ne. 21 Shi kuwa yakan yi marmarin cin abin da yakan fāɗi daga tebur na mai arzikin nan. Har karnuka ma sukan zo su lashe gyambunansa.

    22 “Ana nan, sai mai baran ya mutu, kuma mala’iku suka ɗauke shi zuwa gefen Ibrahim. Mai arzikin ma ya mutu, aka kuma binne shi. 23 A cikin jahannama ta wuta, inda yana shan azaba, ya ɗaga kai ya hangi Ibrahim can nesa, da kuma Lazarus a gefensa. 24 Sai ya yi masa kira ya ce, ‘Baba, Ibrahim, ka ji tausayina, ka aiki Lazarus ya sa ɗan yatsarsa a ruwa, ya ɗiga mini a harshe saboda in ji sanyi, domin ina shan azaba cikin wannan wuta.’

    25 “Amma Ibrahim ya ce, ‘Ka tuna fa ɗana, a lokacin da kake duniya, ka sami abubuwa masu kyau naka, Lazarus kuwa ya sami munanan abubuwa. Amma yanzu ya sami ta’aziyya a nan, kai kuwa kana shan azaba. 26 Ban da wannan duka ma, tsakaninmu da kai, akwai wani babban rami da aka yi, yadda waɗanda suke son ƙetarewa daga nan zuwa wurinku, ba za su iya ba, kuma ba mai iya ƙetarewa daga wurinku zuwa wurinmu.’

  13. 3 Ka girmama gwauraye waɗanda suke cikin bukata ta ainihi. 4 Amma in gwauruwa tana da ’ya’ya ko jikoki, to, sai su fara koyon yin ayyukan addininsu ga danginsu, ta haka za su sāka wa iyayensu da kakanninsu, gama wannan yakan gamshi Allah.

  14. 12 Sai Yesu ya ce wa wanda ya gayyace shi, “Lokacin da ka shirya biki ko liyafa, kada ka gayyaci abokanka, ko ’yan’uwanka, ko danginka, ko kuma maƙwabtanka masu arziki, gama in ka yi haka, suna iya gayyatarka, su biya maka alherin da ka yi musu. 13 Amma lokacin da ka kira biki, ka gayyaci matalauta, da guragu, da shanyayyu, da makafi. 14 Ta haka, za ka sami albarka. Ko da yake ba za su iya biyan ka ba, za a biya ka a ranar tashin masu adalci daga matattu.”

  15. 10 “Shekara shida za ku nome gonakinku ku girbe amfanin gonar, 11 amma a shekara ta bakwai za ku bar ƙasa tă huta. Sa’an nan matalautan da suke cikinku za su sami abinci daga cikinta, namun jeji kuma za su ci abin da aka bari. Ku yi haka da gonakinku na inabi, da na itatuwan zaitun.

  16. 20 Da ya dubi almajiransa, sai ya ce,

    “Masu albarka ne ku da kuke matalauta,

    gama mulkin Allah naku ne.

    21 Masu albarka ne ku da kuke jin yunwa yanzu,

    gama za ku ƙoshi.

    Masu albarka ne ku da kuke kuka yanzu,

    gama za ku yi dariya.

  17. 9 Gama kun san alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi cewa ko da yake shi mawadaci ne, duk da haka, ya zama matalauci saboda ku, domin ta wurin talaucinsa, ku zama mawadata.

  18. 13 Kada ka so barci in ba haka ba za ka talauce;

    ka zauna a faɗake za ka kuwa kasance da sauran abinci.

  19. 19 Duk wanda ya nome gonarsa zai sami amfani a yalwace,

    amma duk wanda yake zaman banza zai zama matalauci a koyaushe.

  20. 1 Ruhun Ubangiji Mai Iko Duka yana a kaina,

    domin Ubangiji ya shafe ni

    domin in yi wa’azi labari mai daɗi ga matalauta.

    Ya aiko ni in warkar da waɗanda suka karai a zuci,

    don in yi shelar ’yanci don ɗaurarru

    in kuma kunce ’yan kurkuku daga duhu

    2 don in yi shelar shekarar tagomashin Ubangiji

    da kuma ranar ɗaukan fansar Allahnmu,

    don in ta’azantar da dukan waɗanda suke makoki,

    3 in tanada wa waɗanda suke baƙin ciki a Sihiyona,

    in maido musu rawani mai kyau

    a maimako na toka,

    man murna

    a maimako na makoki,

    da kuma rigar yabo

    a maimako na ruhun fid da zuciya.

    Za a ce da su itatuwan oak na adalci,

    shukin Ubangiji

    don bayyana darajarsa.

  21. 17 In wani yana da arziki, ya kuma ga ɗan’uwansa cikin rashi, bai kuwa taimake shi ba, anya, ƙaunar Allah tana a cikinsa kuwa? 18 ’Ya’yana ƙaunatattu, kada mu yi ƙauna da fatar baki kawai, sai dai mu nuna ta ta wurin aikatawa da kuma gaskiya.

  22. 6 Ku masu mugunta kuna sa ƙoƙarin matalauta yă zama banza,

    amma Ubangiji ne mafakansu.

  23. 10 Dukan raina zai ce,

    “Wane ne kamar ka, ya Ubangiji?

    Ka kuɓutar da matalauta daga waɗanda suka fi ƙarfinsu,

    matalauta da masu bukata daga waɗanda suke musu fashi.”

  24. 14 Wanda amfani ne, ’yan’uwana, a ce wani yă ce yana da bangaskiya, amma ba shi da ayyuka? Anya, wannan bangaskiya za tă iya cetonsa kuwa? 15 A ce wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa ba shi da riguna ko abincin yini, 16 sai waninku yă ce masa, “Sauka lafiya, Allah ya ba da ci da sha da kuma sutura,” amma bai yi wani abu game da bukatunsa na jiki ba, ina amfani? 17 Haka ma bangaskiya ita kaɗai, in ba tare da ayyuka ba, matacciya ce.

  25. 3 Ku tsare mutuncin marasa ƙarfi da marayu;

    ku kāre hakkin matalauta da waɗanda ake danniya.

    4 Ku ceci marasa ƙarfi da masu bukata;

    ku kuɓutar da su daga hannun mugaye.

  26. 12 Na san cewa Ubangiji ya shirya wa matalauta adalci

    yana kuma yi wa mabukata adalci.

  27. 22 Kada ka zalunci matalauta a kan suna matalauta

    kada kuma ka ƙwari wanda ba shi da mai taimako a gaban shari’a,

    23 gama Ubangiji zai yi magana dominsu

    zai kuwa washe waɗanda suka washe su.

  28. 1 Kaiton waɗanda suke kafa dokokin rashin gaskiya,

    waɗanda suke ba da ƙa’idodin danniya,

    2 don su hana matalauta hakkinsu

    su kuma ƙi yin shari’ar gaskiya a kan waɗanda suke zaluntar mutanena,

    suna ƙwace wa gwauraye dukiyarsu

    suna kuma yi wa marayu ƙwace.

    3 Me za ku yi a ranan nan ta hukunci,

    sa’ad da masifa ta zo daga nesa?

    Ga wa za ku tafi don neman taimako?

    Ina za ku bar dukiyarku?

  29. 21 “Kada a wulaƙanta, ko a zalunci baƙo, domin dā ku baƙi ne a ƙasar Masar.

    22 “Kada ku ci zalin gwauruwa, ko maraya. 23 In kuka yi haka, idan kuma suka yi kuka gare ni, zan ji kukansu. 24 Zan husata, in kuma kashe ku da takobi; matanku kuma, su ma su zama gwauraye, ’ya’yanku kuwa su zama marayu.

    25 “In kun ba wa jama’ata matalauta da suke tsakaninku bashin kuɗi, kada ku zama kamar masu ba da rance; kada ku sa yă biya da ruwa. 26 In kun ɗauki mayafi maƙwabcinku a matsayin jingina, ku mayar masa kafin fāɗuwar rana, 27 domin mayafin ne abin da yake da shi na rufe jikinsa. To, da me zai rufu yă yi barci? Sa’ad da ya yi mini kuka, zan ji, gama ni mai tausayi ne.

  30. 6 “Kada ku kāsa yin adalci ga matalauci a wurin shari’a.

  31. 9 Ya rarraba kyautansa ga matalauta,

    adalcinsa zai dawwama har abada;

    za a ɗaga ƙahonsa sama da bangirma.

  32. 1 Gara matalauci wanda yake marar laifi

    da wawa wanda leɓunansa masu ƙarya ne.

  33. 1 An fi son suna mai kyau fiye da wadata mai yawa;

    tagomashi kuma ya fi azurfa ko zinariya.

    2 Mawadaci da matalauci suna da abu guda.

    Ubangiji ne Mahaliccinsu duka.

  34. 6 Ga abin da Ubangiji ya ce,

    “Saboda zunubai uku na Isra’ila,

    har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba.

    Don sun sayar da adalai waɗanda

    suka kāsa biyan bashinsu.

    Sun kuma sayar da matalauta

    waɗanda bashinsu bai ma kai ko kuɗin bi-labi ba.

    7 Sun tattake kawunan matalauta

    kamar yadda suke taka laka

    suka kuma danne wa marasa galihu gaskiya.

    Uba da ɗa su na kwana da yarinya guda,

    suna kuma ɓata sunana mai tsarki.

  35. 10 cikin baƙin ciki, duk da haka kullum cikin murna muke. Cikin matalauta, duk da haka muna azurtar da mutane da yawa. Ba mu da kome, alhali kuwa kome namu ne.

  36. 7 In akwai matalauci a cikin ’yan’uwanku, a duk wani daga cikin biranen da Ubangiji Allahnku yake ba ku, kada ku taurara zuciya, ko ku ƙi saki hannu ga ɗan’uwanku matalauci. 8 A maimakon haka ku bayar hannu sake, ku kuma ba shi bashi gwargwadon abin da yake bukata a sauƙaƙe. 9 Ku yi hankali kada ku riƙe wannan mugun tunani cewa, “Shekara ta bakwai, shekarar yafewar basusuwa, ta yi kusa,” har ku nuna mugun nufi ga ɗan’uwa mabukaci, ku ƙi ba shi wani abu. Zai yi kuka ga Ubangiji a kanku, abin kuwa zai zama laifi a kanku. 10 Ku bayar hannu sake gare shi, ku kuma yi haka ba tare da gunaguni ba; saboda wannan fa Ubangiji Allahnku zai albarkace ku a cikin dukan aikinku, da kuma kome da kuka sa hannunku a kai. 11 Kullum za ku kasance da matalauta a ƙasar. Saboda haka na umarce ku ku bayar hannu sake ga ’yan’uwa da kuma matalauta, da masu bukata a ƙasarku.

  37. 18 Duk wanda ya ƙyale horo yakan kai ga talauci da kuma kunya,

    amma duk wanda ya karɓi gyara yakan sami girma.

  38. 20 Maƙwabta sukan gudu daga matalauta,

    amma masu arziki suna da abokai da yawa.

    21 Duk wanda ya rena maƙwabci ya yi zunubi,

    amma mai albarka ne wanda yake alheri ga mabukata.

  39. 27 Duk wanda yake bayarwa ga matalauta ba zai rasa kome ba,

    amma duk wanda bai kula da su ba yana samu la’ana masu yawa.

  40. 10 Abin da dai suka roƙa shi ne ya kamata mu riƙa tuna da matalauta, abin nan da nake marmarin yi.

  41. 1 Yanzu fa sai ku saurara, ku masu arziki, ku yi kuka da ihu, saboda azabar da take zuwa a kanku. 2 Arzikinku ya ruɓa, asu kuma sun cinye tufafinku. 3 Zinariyarku da azurfarku sun yi tsatsa. Tsatsarsu kuwa za tă zama shaida a kanku, ta kuma ci namar jikinku kamar wuta. Kun ɓoye dukiya a kwanakin ƙarshe. 4 Ga shi! Zaluncin da kuka yi na hakkin ma’aikatan gonakinku yana ta ƙara. Kukan masu girbi ya kai kunnuwan Ubangiji Maɗaukaki. 5 Kun yi rayuwar jin daɗi a duniya kuna ci kuna sha na ganin dama. Kun ciyar da kanku kun yi ƙiba don ranar yanka. 6 Kun hukunta kun kuma kashe mutane marasa laifi, waɗanda ba su yi gāba da ku ba.

  42. 5 Mai albarka ne wanda Allah na Yaƙub ne taimakonsa,

    wanda sa zuciyarsa yana a kan Ubangiji Allahnsa.

    6 Mahaliccin sama da ƙasa,

    teku, da kome da yake cikinsu,

    Ubangiji, wanda yake mai aminci har abada.

    7 Yakan biya bukatun mutanen da aka danne

    ya kuma ba da abinci ga mayunwata.

    Ubangiji yakan ’yantar da ’yan kurkuku,

    8 Ubangiji yakan ba wa makafi ido,

    Ubangiji yakan ɗaga waɗanda aka rusunar da su ƙasa,

    Ubangiji yana ƙaunar masu adalci.

    9 Ubangiji yana tsaron baƙi

    yana kuma lura da marayu da kuma gwauruwa,

    amma yakan lalatar da hanyoyin mugaye.

  43. 10 Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi,

    ɗan naɗin hannuwa don a huta,

    11 talauci kuwa zai zo kamar ’yan hari

    rashi kuma kamar ɗan fashi.

  44. 20 Kada ka haɗa kai da waɗanda suke shan ruwan inabi da yawa

    ko masu haɗama kansu da abinci,

    21 gama bugaggu da ruwan inabi da masu yawan ci sukan zama matalauta,

    gama jiri yakan yi musu sutura da tsummoki.

  45. 8 Sai maganar Ubangiji ta sāke zuwa wa Zakariya cewa, 9 “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ku yi shari’ar gaskiya; ku nuna jinƙai da tausayi ga juna. 10 Kada ku danne gwauruwa ko maraya, baƙo ko talaka. A cikin zuciyarku kada ku yi mugun tunani game da juna.’

  46. 20 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Yanyawa suna da ramummuka, tsuntsayen sararin sama suna da sheƙuna, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin da zai sa kansa.”

  47. 11 Ya amsa ya ce, “Ya kamata, mutumin da yake da riguna biyu, yă raba da wanda ba shi da riga, mai abinci kuma yă yi haka.”

  48. 16 In mace mai bi tana da gwauraye a iyalinta, ya kamata tă taimake su, kada tă bar wa ikkilisiya wannan nauyi, domin ikkilisiya ta sami zarafin taimakon gwaurayen da suke da bukata ta ainihi.

  49. 9 Na san wahalarka da kuma talaucinka, duk da haka kai mai arziki ne! Na san ɓata suna da waɗannan suke yi maka waɗannan da suke cewa su Yahudawa ne alhali kuwa ba haka ba ne, su dai majami’ar Shaiɗan ne.

  50. 9 Ka kori gwauraye hannu wofi,

    ka kuma karya ƙarfin marayu.

    10 Shi ya sa kake kewaye da tarkuna,

    shi ya sa ka cika da tsoron mugun abin da zai auko maka.

    11 An yi duhu ƙwarai, har ba ka iya gani,

    shi ya sa ambaliyar ruwa ta rufe ka.

  51. 24 Wani mutum kan bayar hannu sake, duk da haka yakan sami fiye;

    wani yakan riƙe abin da ba nasa ba, amma sai ya ƙarasa cikin talauci.

    25 Mutum mai kyauta zai azurta;

    shi da yakan taimake waɗansu, za a taimake shi.

  52. 23 Duk aiki tuƙuru yakan kawo riba,

    amma zama kana surutu kan kai ga talauci kawai.

  53. 5 Duk wanda yake wa matalauta ba’a yana zagin Mahaliccinsu ne;

    duk wanda ya yi murna akan masifar da ta sami wani za a hukunta shi.

  54. 17 Duk wanda yake kirki ga matalauta yana ba wa Ubangiji bashi ne,

    zai kuwa sami lada game da abin da ya yi.

  55. 22 Abin da mutum yake sha’awa shi ne ƙauna marar ƙarewa;

    gara ka zama matalauci da ka zama maƙaryaci.

  56. 17 Duk mai son jin daɗi zai zama matalauci;

    duk mai son ruwan inabi da mai ba zai taɓa zama mai arziki ba.

  57. 8 “Yi magana domin bebaye,

    domin hakkin dukan waɗanda suke naƙasassu.

    9 Yi magana a kuma yi shari’ar adalci;

    a tsare hakkin talakawa da masu bukata.”

  58. 8 (Shi wanda ya yi Taurarin nan da ake ce Kaza da ’Ya’yanta da kuma Mai Farauta da Kare,

    wanda ya mai da duhu ya zama haske

    ya kuma baƙanta rana ta zama dare,

    yakan kwashe ruwan teku

    ya zubar a ƙasa,

    Ubangiji ne sunansa,

    9 yakan kawo hallaka a mafaka mai ƙarfi

    yakan kuma mai da birnin mai katanga ya zama kufai).

    10 Ba ku son mai yin gaskiya a ɗakin shari’a

    kuna ƙin mai faɗar gaskiya.

    11 Kuna matsa wa matalauta

    kuna sa su dole su ba ku hatsi.

    Saboda haka, ko da yake kun gina gidajen duwatsu,

    ba za ku zauna a cikinsu ba;

    ko da yake kun nome gonaki masu kyau,

    ba za ku sha ruwan inabinsu ba.

    12 Gama na san yawan laifofinku

    da kuma girman zunubanku.

    Kuna danne masu adalci kuna kuma cin hanci

    kuna kuma hana a yi wa matalauta shari’ar adalci a majalisa.

    13 Saboda haka mai hankali yakan yi shiru a lokuta kamar haka,

    gama lokutan mugaye ne.

  59. 21 “Bawansa ya dawo ya gaya wa maigidansa wannan. Sai maigidan ya yi fushi, ya ba da umarni ga bawansa ya ce, ‘Ka fita da sauri, ka bi titi-titi da lungu-lungu na garin, ka kawo matalauta, da guragu, da makafi, da shanyayyu.’

  60. 8 Amma Zakka ya tashi a tsaye, ya ce wa Ubangiji, “Duba, Ubangiji! Nan take, rabin dukiyar da nake da shi, na ba wa matalauta. In kuma na taɓa cutan wani, a kan wani abu, zan mayar da shi ninki huɗu.”

  61. 1 A waɗannan kwanaki, sa’ad da yawan almajirai suke ƙaruwa, sai Yahudawan masu jin Hellenanci a cikinsu suka yi gunaguni a kan Yahudawan da suke Ibraniyawa domin ba a kula da gwaurayensu a wajen raba abinci na yau da kullum.

  62. 35 Cikin kowane abin da na yi, na nuna muku cewa da irin wannan aiki tuƙuru don mu taimaki marasa ƙarfi, muna tunawa da kalmomin da Ubangiji Yesu kansa ya ce, ‘Bayarwa ta fi karɓa albarka.’ ”

  63. 9 Kada a lasafta gwauruwa cikin jerin gwauraye sai ta wuce shekara sittin, ta kuma yi zaman aminci ga mijinta, 10 aka kuma santa sosai saboda ayyuka masu kyau, kamar renon ’ya’ya, da karɓan baƙi, tana yi wa tsarkaka hidima, tana taimakon waɗanda suke cikin wahala tana kuma ba da kanta ga yin kowane aikin mai kyau.

  64. 15 Na san ayyukanka, ba ka da sanyi ba ka kuma da zafi. Na so da kai ɗaya ne daga ciki, ko sanyi, ko zafi! 16 Amma domin kana tsaka-tsaka ba zafi ba, ba kuma sanyi ba, ina dab da tofar da kai daga bakina. 17 Ka ce, ‘Ina da arziki; na sami dukiya ba na kuma bukatar kome.’ Amma ba ka gane ba cewa kai matsiyaci ne, abin tausayi, matalauci, makaho kana kuma tsirara. 18 Na shawarce ka ka sayi zinariyar da aka tace cikin wuta daga gare ni, don ka yi arziki; da fararen tufafi ka sa, don ka rufe kunyar tsirancinka; da kuma maganin ido ka sa a idanunka, don ka gani.

    19 Waɗanda nake ƙauna su nake tsawata wa, nake kuma horo. Saboda haka ka yi himma ka tuba. 20 Ga ni! Ina tsaye a bakin ƙofa, ina ƙwanƙwasawa. Duk wanda ya ji muryata ya kuma buɗe ƙofar, zan shiga in kuma ci tare da shi, shi kuma tare da ni.

    21 Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ikon zama tare da ni a kursiyina, kamar yadda na ci nasara, kuma ina zaune tare da Ubana a kursiyinsa. 22 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi.”

  65. 17 Mugaye za su koma kabari,

    dukan al’umman da suka manta da Allah.

    18 Amma har abada ba za a manta da mai bukata ba,

    ba kuwa sa zuciyar mai wahala zai taɓa hallaka.

  66. 5 “Saboda danniyar marasa ƙarfi da kuma nishin masu bukata,

    zan tashi yanzu,” in ji Ubangiji.

    “Zan kāre su daga masu yin musu sharri.”

  67. 10 Mutanenka suka zauna a cikinsa,

    kuma daga yalwarka, ya Allah, ka tanada wa matalauta.

  68. 12 Gama zai ceci masu bukatan da suka yi kuka,

    marasa ƙarfin da ba su da mai taimako.

    13 Zai ji tausayin gajiyayyu da masu bukata

    yă ceci masu bukata daga mutuwa.

    14 Zai kuɓutar da su daga danniya da rikici,

    gama jininsu yake a gabansa.

    15 Bari yă yi doguwar rayuwa!

    Bari a ba shi zinariya daga Sheba.

    Bari mutane su riƙa yin addu’a dominsa

    su kuma albarkace shi dukan yini.

  69. 31 Duk wanda ya zalunci matalauci ya zagi Mahaliccinsu ke nan,

    amma duk wanda ya yi alheri ga mabukata yana girmama Allah ne.

  70. 6 Gara matalauci wanda yake tafiya babu abin zargi

    da mai arziki wanda hanyoyinsa mugaye ne.

  71. 16 Ya kāre muradin matalauta da mabukata,

    ta haka kome ya tafi masa daidai.

    Ba abin da ake nufi da ba san ni ke nan ba?”

    In ji Ubangiji.

  72. 4 Ku ji wannan, ku da kuke tattake masu bukata

    kuka kori matalautan ƙasar.

    5 Kuna cewa,

    “Yaushe Sabon Wata zai wuce

    don mu sayar da hatsi,

    Asabbaci ta wuce,

    don mu sayar da alkama?”

    Mu yi awo da ma’aunin zalunci

    mu ƙara kuɗin kaya

    mu kuma cutar da mai saya,

    6 mu sayi matalauta da azurfa

    masu bukata kuma da takalmi,

    mu sayar da alkamar haɗe da yayi.

  73. 1 To, ’yan’uwa, muna so ku san abin da alherin Allah ya ba wa ikkilisiyoyin Makidoniya. 2 Gama sun sha wuya sosai saboda tsananin wahalar da suka shiga, har yawan farin cikinsu ya kai su ga yin alheri ta bayarwa ga waɗansu, ko da yake suna cikin tsananin talauci. 3 Gama ina shaida cewa sun bayar daidai gwargwadon iyawarsu, har ma fiye da ƙarfinsu. Su kansu, 4 sun roƙe mu sosai don su sami damar yin bayarwa a wannan hidima ga tsarkaka. 5 Ba su yi yadda muka za tă ba, sai ma suka fara ba da kansu ga Ubangiji, sa’an nan sai suka ba da kansu gare mu bisa ga nufin Allah.

  74. 28 Duk wanda yake sata, sai yă daina sata, dole kuma yă yi aiki, yă yi wani abu mai amfani da hannuwansa, don yă sami abin da zai iya raba da masu bukata.

  75. 1 Ubangiji ya aiki Natan wurin Dawuda. Da ya tafi wajensa, sai ya ce, “An yi waɗansu mutum biyu a wani gari, ɗaya mai arziki, ɗayan kuma matalauci. 2 Mai arzikin yana da babban garken tumaki, da kuma shanu, 3 amma matalauci ba shi da kome sai ’yar tunkiyar da ya sayo. Ya yi kiwonta, ta kuwa yi girma tare shi da yaransa. Takan ci tare da shi ta sha ruwa a kwaf nasa, har ma ta kwanta a ƙirjinsa. Ta ma zama kamar ’ya a gare shi.

    4 “To, sai ga wani baƙo ya zo wurin mai arzikin nan, amma mai arzikin ya ƙi yă kama tunkiyarsa, ko saniyarsa yă yanka don yă shirya wa baƙon da ya zo abinci. A maimako, sai ya je ya kama ’yar tunkiyan nan ta matalaucin ya yanka ya shirya wa mutumin da ya zo masa.”

    5 Dawuda ya husata ƙwarai da mutumin, ya ce wa Natan, “Muddin Ubangiji yana a raye, mutumin da ya yi wannan ya cancanci yă mutu! 6 Dole yă biya diyyar tunkiyan nan sau huɗu, domin ya aikata haka ba tausayi.”

  76. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda.

    1 Mai albarka ne wanda yake jin tausayin marasa ƙarfi;

    Ubangiji yakan kuɓutar da shi a lokutan wahala.

    2 Ubangiji zai kāre shi yă kuma kiyaye ransa;

    zai albarkace shi a cikin ƙasar

    ba kuwa zai miƙa shi ga hannun maƙiyansa ba.

    3 Ubangiji zai ba shi ƙarfi a gadon rashin lafiyarsa

    ya mayar masa da lafiya daga ciwon da ya kwantar da shi.

  77. 16 Duk wanda yake danne matalauta don yă azurta

    kuma duk wanda yake kyauta ga mawadata, dukansu kan talauta.

  78. 7 “Abu biyu ina roƙonka, ya Ubangiji;

    kada ka hana ni kafin in mutu.

    8 Ka kawar da ƙarya da kuma ƙarairayi nesa da ni;

    kada ka ba ni talauci ko arziki,

    amma ka ba ni abincina na yini kaɗai.

    9 In ba haka ba, zan wadace in ƙi ka

    har in ce, ‘Wane ne Ubangiji?’

    Ko kuwa in zama matalauci in yi sata

    ta haka in kunyata sunan Allahna.

  79. 13 Ubangiji ya ɗauki mazauninsa a cikin ɗakin shari’a;

    ya tashi don yă shari’anta mutane.

    14 Ubangiji yana shari’a

    da dattawa da kuma shugabannin mutanensa,

    “Ku ne kuka lalace gonar inabina;

    ganimar talakawa suna a gidajenku.

    15 Ina dalilin da kuke marmatsa mutanena

    kuna gurgurje fuskokin talakawa?”

    Ni Ubangiji Maɗaukaki na faɗa.

  80. 32 Dukan masu bi kuwa zuciyarsu ɗaya ne, nufinsu kuwa ɗaya. Babu wani da ya ce abin da ya mallaka nasa ne, amma sun raba kome da suke da shi. 33 Da iko mai ƙarfi manzanni suka ci gaba da shaidar tashin matattu na Ubangiji Yesu, alheri mai yawa kuwa yana bisansu duka. 34 Babu mabukata a cikinsu. Lokaci-lokaci waɗanda suke da gonaki ko gidaje sukan sayar da su, su kawo kuɗi daga abin da suka sayar, 35 su ajiye a sawun manzannin, a kuma raba wa kowa gwargwadon bukatarsa.

  81. 14 “ ‘Kada ku zagi kurma, ko ku sa abin tuntuɓe a gaban makaho, amma ku ji tsoron Allahnku. Ni ne Ubangiji.

    15 “ ‘Kada ku yi rashin adalci cikin shari’a; kada ku nuna sonkai ga matalauci, ko ku goyi bayan mai arziki, amma ku shari’anta maƙwabci cikin gaskiya.

    16 “ ‘Kada ku yi ta yawo kuna yaɗa ƙarya a cikin mutanenku.

    “ ‘Kada ku yi wani abin da zai sa ran maƙwabcinku cikin hatsari. Ni ne Ubangiji.

  82. 14 Amma kai, ya Allah, kana gani wahala da baƙin ciki;

    kana lura da yadda suke ɗaukansu a hannu.

    Marar taimako kan danƙa kansa gare ka;

    kai ne mai taimakon marayu

  83. 15 Dukiyar masu arziki yakan zama mafakar birninsu,

    amma talauci shi ne lalacin matalauci.

  84. 30 Na wuce cikin gonar rago,

    na wuce cikin gonar inabin mutumin da ba shi da azanci;

    31 ƙayayyuwa sun yi girma ko’ina,

    ciyayi sun rufe ƙasar,

    katangar duwatsu duk ta rushe.

    32 Na yi tunani a zuciyata

    na kuwa koyi darasi daga abin da na gani.

    33 Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi,

    ɗan naɗin hannuwa don a huta,

    34 sai talauci ya shigo maka kamar ’yan fashi

    rashi kuma ya zo maka kamar mai hari.

  85. 17 Da Yesu ya kama hanya, sai wani mutum ya ruga da gudu ya zo wajensa, ya durƙusa a gabansa ya ce, “Malam nagari, me zan yi domin in gāji rai madawwami?”

    18 Yesu ya amsa ya ce, “Don me kake ce da ni mai nagarta? Ai, ba wani nagari, sai Allah kaɗai. 19 Ka san dokokin da suka ce, ‘Kada ka yi kisankai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka ba da shaida ta ƙarya, kada ka cuci wani, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’”

    20 Mutumin ya ce, “Malam, ai, tun ina yaro na kiyaye duk waɗannan.”

    21 Yesu ya kalle shi da ƙauna ya ce, “Abu ɗaya ka rasa, ka tafi ka sayar da duk abin da kake da shi, ka ba wa matalauta, za ka kuwa sami dukiya a sama. Sa’an nan ka zo ka bi ni.”

    22 Da jin wannan, sai mutumin ya ɓata fuskarsa, ya tafi da baƙin ciki, gama yana da arziki sosai.

  86. 22 Sai ya amsa wa almajiran Yohanna ya ce, “Ku koma ku faɗa wa Yohanna abin da kuka ji, da abin da kuka gani. Makafi suna ganin gari, guragu suna tafiya, ana warkar da waɗanda suke da kuturta, kurame suna ji, ana tā da matattu, ana kuma yi wa matalauta wa’azin bishara.

  87. 9 Bari ɗan’uwan da yake cikin halin ƙasƙanci yă yi taƙama a matsayinsa na ɗaukaka. 10 Amma wanda yake mai arziki, ya kamata yă yi taƙama a matsayinsa na ƙasƙanci, gama ba zai daɗe ba kamar furen jeji. 11 Gama in rana ta fito ta yi zafi mai tsanani sai ta sa tsiro yă yanƙwane tsiro; furensa yă kakkaɓe, kyansa kuma yă lalace. Haka ma mai arziki zai shuɗe yayinda yake cikin harkarsa.

  88. 1 Matar wani daga ƙungiyar annabawa ta yi wa Elisha kuka ta ce, “Mijina, bawanka, ya mutu, ka kuma san yadda ya girmama Ubangiji. Amma ga shi yanzu mai binsa bashi ya zo yă kwashe ’ya’yana maza biyu su zama bayinsa.”

    2 Elisha ya amsa mata ya ce, “Me kike so in yi miki? Ki faɗa mini, me kike da shi a gidanki?”

    Sai ta ce, “Baiwarka ba ta da kome a can, sai ɗan tulun man zaitun.”

    3 Elisha ya ce, “Ki je wurin dukan maƙwabtanki, ki nemi tulunan da babu kome a ciki. Kada ki nemo kaɗan kawai. 4 Sa’an nan ki shiga ciki, ki kulle ƙofar da ke da ’ya’yanki kuke ciki. Ku ɗuɗɗura man a dukan tulunan, sa’ad da kowanne ya cika, sai ki ajiye a gefe.”

    5 Ta tashi ta shiga tare da ’ya’yanta maza, suka kulle ƙofa. ’Ya’yanta suka kawo mata tuluna, ita kuma tana ɗurawa. 6 Da dukan tulunan suka cika, sai ta ce wa ɗanta, “Kawo mini wani tulu.”

    Amma ya amsa ya ce, “Ai, ba saura.” Sa’an nan man ya daina zuba.

    7 Sai ta tafi ta faɗa wa mutumin Allah. Shi kuwa ya ce mata, “Tafi, ki sayar da man, ki biya bashinki. Ki biya bukatanki da na ’ya’yanki da sauran da ya rage.”

  89. 6 Ka sa ɗan’uwanka yă biya ka bashin da kake binsa ba dalili;

    ka ƙwace wa mutanen rigunansu ka bar su tsirara.

    7 Ba ka ba masu jin ƙishirwa su sha ba

    kuma ka hana wa masu jin yunwa abinci su ci.

  90. 5 Waɗanda suke dubansa sukan haskaka;

    fuskokinsu ba sa rufuwa da kunya.

    6 Wannan matalauci ya yi kira, Ubangiji kuwa ya ji shi;

    ya cece shi daga dukan wahalarsa.

  91. 4 Ragwanci kan sa mutum yă zama matalauci,

    amma aiki tuƙuru kan ba da dukiya.

  92. 5 Shirye-shiryen mai aiki tuƙuru kan kai ga riba

    in kuwa ka cika gaggawa zai kai ga talauci.

  93. 4 Kai ka zama mafakar matalauta, mafaka don mabukata cikin damuwa,

    wurin ɓuya daga hadari, inuwa kuma daga zafin rana.

    Gama numfashin mugaye yana kamar da hadari mai bugun bango

  94. 41 “Sa’an nan zai ce wa waɗanda suke a hagunsa, ‘Ku rabu da ni, la’anannu, zuwa cikin madawwamiyar wutar da aka shirya don Iblis da mala’ikunsa. 42 Gama da nake jin yunwa, ba ku ba ni abinci ba, da nake jin ƙishirwa, ba ku ba ni abin sha ba, 43 da na yi baƙunci, ba ku karɓe ni ba, da nake bukatar tufafi, ba ku yi mini sutura ba, da na yi rashin lafiya kuma ina a kurkuku, ba ku lura da ni ba.’

    44 “Su ma za su amsa, su ce, ‘Ubangiji, yaushe muka gan ka cikin yunwa ko ƙishirwa ko baƙo ko cikin bukatar tufafi ko cikin rashin lafiya ko cikin kurkuku, ba mu taimake ka ba?’

    45 “Zai amsa, yă ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, duk abin da ba ku yi wa ɗaya daga cikin waɗannan mafi ƙanƙanta ba, ba ku yi mini ba ke nan.’

    46 “Sa’an nan za su tafi cikin madawwamiyar hukunci, amma masu adalci kuwa za su shiga rai madawwami.”

  95. 10 Saboda haka, in da hali, bari mu aikata nagarta ga dukan mutane, musamman ga waɗanda suke na iyalin masu bi.

  96. 9 Yanzu kuwa game da ƙaunar ’yan’uwa, ba ma bukata mu rubuta muku, gama ku kanku Allah ya riga ya koya muku ku ƙaunaci juna. 10 Gaskiyar kuwa ita ce, kuna ƙaunar dukan ’yan’uwa ko’ina a Makidoniya. Duk da haka muna ƙara gargaɗe ku, ’yan’uwa, ku yi haka sau da sau. 11 Ku mai da wannan burinku na yi natsattsiyar rayuwa, kuna mai da hankali ga sha’anin da yake gabanku, kuna kuma yin aiki da hannuwanku, kamar dai yadda muka gaya muku, 12 don rayuwanku ta kullum ta zama da mutunci ga waɗanda suke na waje don kuma kada ku dogara a kan kowa.

  97. 9 Mai bayarwa hannu sake shi kansa zai sami albarka,

    gama yakan raba abincinsa da matalauta.

  98. 3 In na ba wa matalauta dukan abin da nake da shi, na kuma miƙa jikina a ƙone, amma ba ni da ƙauna, ban yi riban kome ba.

  99. 9 Yanzu sai ku gaggauta zuwa wurin mahaifina ku faɗa masa, ‘Abin da ɗanka Yusuf ya ce; Allah ya mai da ni shugaban dukan Masar. Gangaro wurina; kada ka jinkirta. 10 Za ka yi zama a yankin Goshen, ka kasance kusa da ni. Kai, ’ya’yanka da kuma jikokinka, garkunanka da shanunka, da kuma dukan abin da kake da shi. 11 Zan tanada maka a nan, domin akwai saura shekaru biyar na yunwa masu zuwa. In ba haka ba, kai da gidanka da dukan mallakarka za ku zama gajiyayyu.’

  100. 9 “ ‘Sa’ad da kuka yi girbin amfanin gonarku, kada ku girbe har zuwa gefen gonar, ko ku yi kalan girbinku. 10 Kada ku koma gonar inabinku kuna kala, ko ku tattara ’ya’yan inabin da suka fāffāɗi. Ku bar su domin matalauta da kuma baƙi. Ni ne Ubangiji Allahnku.

  101. 25 “ ‘In ɗaya daga cikin mutanen ƙasarku ya talauta, ya kuma sayar da mallakarsa, sai danginsa na kusa yă je yă fanshi abin da mutumin ƙasarsa ya sayar. 26 In mutumin ba shi da wanda zai fansa masa ita, shi kansa kuwa ya wadace, ya kuma sami isashen halin fansarta, 27 sai yă lasafta yawan shekarun da aka yi tun da an sayar da filin. Kuɗin filin zai dangana ga yawan shekarun da suka rage kafin shekara hamsin ta murna da za tă zo; sa’an nan zai iya koma ga mallakarsa. 28 Amma in bai sami halin sāke biyansa ba, abin nan da ya sayar zai ci gaba da zama mallakar mai sayan, sai Shekara ta Murna. Za a maido masa da ita a Shekara ta Murna, sa’an nan zai iya koma ga mallakarsa.

    29 “ ‘In mutum ya sayar da gida a birni mai katanga, yana da izini yă fanshe shi a ƙarshen shekara guda, bayan ya sayar da shi. 30 In ba a fanshe shi a ƙarshen shekara ba, gidan da yake a birni mai katanga, zai zama mallakar na ɗinɗinɗin na mai sayan da kuma zuriyarsa. Ba za a mai da shi a Shekara ta Murna ba.

  102. 28 A ƙarshen kowace shekara uku, ku kawo dukan zakkarku na amfanin gona na wannan shekara, ku ajiye su a cikin birane, 29 saboda Lawiyawa (waɗanda ba su da rabo ko gādo na kansu) da baƙo, da marayu, da kuma gwauraye, waɗanda suke zama a biranenku, su zo su ci su ƙoshi, ta haka Ubangiji Allahnku zai albarkace ku cikin dukan ayyukan hannuwanku.

  103. 10 Sa’ad da kuka ba da rance na kowane iri ga maƙwabcinku, kada ku shiga gidansa don karɓar wani abu a matsayin jingina. 11 Ku tsaya a waje ku bar mutumin da yake karɓan rancen yă kawo muku abin da zai bayar a matsayin jingina. 12 In matalauci ne, kada ku kwana da abin da zai bayar a matsayin jingina a wurinku. 13 Ku mayar da rigarsa a fāɗuwar rana saboda yă sami abin rufuwa. Yin haka zai sa yă gode muku, za a kuma ɗauka wannan a matsayin aikin adalci da kuka yi a gaban Ubangiji Allahnku.

    14 Kada ku zalunci ɗan ƙodago matalauci da mabukaci, ko da shi ɗan’uwanku ne mutumin Isra’ila, ko baƙon da yake zama a cikin garuruwanku. 15 Ku biya kuɗin aikinsa kowace rana kafin fāɗuwar rana, domin shi matalauci ne, yana kuma sa rai a kan wannan hakkin ne, don kada ya yi wa Ubangiji kuka a kanku, har yă zama laifi a gare ku.

  104. 7 Ubangiji ne yakan aika da talauci da kuma dukiya;

    yakan ƙasƙantar yă kuma ɗaukaka.

    8 Yakan tā da matalauci daga ƙura,

    yă kuma ɗaga mai bukata daga tarin toka;

    yă zaunar da su tare da ’ya’yan sarki;

    yă kuma sa su gāji mulki na ɗaukaka.

    “Harsashin duniya na Ubangiji ne;

    a bisansu ne ya kafa duniya.

  105. 10 “A ce yana da ɗa wanda yana kisa ko yana yin ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa 11 (ko da yake mahaifin bai yi ko ɗaya daga cikinsu ba).

    “Yakan ci abinci a duwatsun tsafi.

    Yakan ƙazantar da matar maƙwabci.

    12 Yakan ci zalin matalauta da mabukata.

    Yakan yi fashi.

    Ba ya mayar da abin da aka jinginar masa.

    Ya dogara ga gumaka.

    Yana aikata ayyukan banƙyama.

    13 Yakan ba da bashi da ruwa ya kuma karɓi riba mai yawa.

    Irin wannan mutum zai rayu? Ba zai rayu ba! Domin ya aikata dukan waɗannan abubuwa masu banƙyama, tabbatacce za a kashe shi, kuma hakkin jininsa zai zauna a kansa.