29 Bible Verses About Sleep

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Sleep
  1. 8 Zan kwanta in kuma yi barci lafiya,

    gama kai kaɗai, ya Ubangiji,

    kake sa mazaunina yă kasance lafiya lau.

  2. Waƙar haurawa. Ta Solomon.

    1 In ba Ubangiji ne ya gina gida ba,

    masu gininta suna wahala a banza ne.

    In ba Ubangiji ne yake tsaron birni ba,

    masu tsaro suna yin tsaro a banza.

    2 Banza ne ka farka da wuri

    ka koma da latti,

    kana fama don abincin da za ka ci,

    gama yakan ba da barci ga waɗanda yake ƙauna.

  3. 2 Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji,

    wanda ya kafa sama da ƙasa.

    3 Ba zai bari ƙafarka tă yi santsi ba,

    shi da yake tsaronka ba zai yi gyangyaɗi ba;

    4 tabbatacce, shi da yake tsaron Isra’ila

    ba ya gyangyaɗi ko barci.

    5 Ubangiji yana tsaronka,

    Ubangiji ne inuwa a hannun damanka;

    6 rana ba za tă buge ka cikin yini ba

    balle wata da dare.

  4. 11 Ku yi wannan domin kun san irin zamanin da kuke ciki. Lokaci ya yi da za ku farka daga barcinku, don cetonmu ya yi kusa yanzu fiye da lokacin da muka fara ba da gaskiya. 12 Dare fa ya kusan ƙarewa; gari kuma yana gab da wayewa. Saboda haka bari mu kawar da ayyukan duhu mu kuma yafa kayan yaƙi na haske. 13 Bari mu tafiyar da al’amuranmu yadda ya dace a yi da rana, ba a cikin shashanci da buguwa ba, ba cikin fasikanci da rashin kunya ba, ba kuma cikin faɗa da kishi ba. 14 A maimakon haka, ku ɗauki halin Ubangiji Yesu Kiristi, kada kuma ku yi tunani game da yadda za ku gamsar da sha’awace-sha’awacen mutuntaka.

  5. 11 Bayan ya faɗa haka, sai ya ƙara ce musu, “Abokinmu Lazarus ya yi barci, amma za ni in tashe shi.”

    12 Almajiransa suka ce, “Ubangiji, in barci ne yake, to, ai, zai sami sauƙi.” 13 Yesu kuwa yana magana mutuwarsa ce, amma almajiransa suka ɗauka yana nufin barcin gaskiya ne.

    14 Saboda haka sai ya gaya musu a fili cewa, “Lazarus ya mutu,

  6. 21 Ɗana, ka riƙe sahihiyar shari’a da kuma basira,

    kada ka bar su su rabu da kai;

    22 za su zama rai a gare ka,

    abin adon da zai gyara wuyanka.

    23 Sa’an nan za ka bi hanyarka lafiya,

    ƙafarka kuwa ba zai yi tuntuɓe ba;

    24 sa’ad da ka kwanta, ba za ka ji tsoro ba;

    sa’ad da ka kwanta, barci zai yi maka daɗi.

    25 Kada ka ji tsoron masifar da za tă faru farat ɗaya

    ko lalacin da yakan auka wa mugaye,

  7. 1 To, ’yan’uwa, game da lokuta da ranaku, ba ma bukata mu rubuta muku, 2 gama kun sani sarai cewa ranar Ubangiji za tă zo kamar ɓarawo da dare. 3 Yayinda mutane suke cewa, “Akwai salama da zaman lafiya,” hallaka za tă auko musu farat ɗaya, kamar yadda naƙuda take kama mace mai ciki, ba za su kuwa tsira ba.

    4 Amma ku, ’yan’uwa, ba kwa cikin duhu da wannan rana za tă zo muku ba zato kamar ɓarawo. 5 Dukanku ’ya’yan haske ne da kuma ’ya’yan rana. Mu ba mutanen dare ko na duhu ba ne. 6 Saboda haka fa, kada mu zama kamar saura, waɗanda suke barci, sai dai mu zama masu tsaro da masu kamunkai. 7 Gama masu barci, da dad dare suke barci, masu sha su bugu kuwa, da dad dare suke buguwa. 8 Amma da yake mu na rana ne, bari mu zama masu kamunkai, sanye da bangaskiya da ƙauna kamar sulke, begen cetonmu kuma kamar hular kwano. 9 Gama Allah bai naɗa mu don mu sha fushi ba, sai dai mu sami ceto ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi. 10 Ya mutu saboda mu domin, ko muna a faɗake ko muna barci, mu kasance tare da shi. 11 Saboda haka ku ƙarfafa juna ku kuma gina juna, kamar dai yadda kuke yi.

  8. 3 Amma kai ne garkuwa kewaye da ni, ya Ubangiji;

    ka ba ni ɗaukaka ka kuma ɗaga kaina.

    4 Ga Ubangiji na yi kuka mai ƙarfi,

    ya kuwa amsa mini daga tudunsa mai tsarki. Sela

    5 Na kwanta na yi barci;

    na kuma farka, gama Ubangiji yana kiyaye ni.

    6 Ba zan ji tsoro ko dubu goma

    suka ja dāgā gāba da ni a kowane gefe ba.

  9. 7 A ranar farko ta mako muka taru wuri ɗaya don gutsuttsura burodi. Bulus ya yi wa mutane magana, don yana niyyar tashi kashegari, sai ya yi ta yin magana har tsakar dare. 8 Akwai fitilu da yawa a ɗakin gidan saman da muka taru. 9 Akwai wani saurayi zaune a taga mai suna Yitikus, wanda barci mai nauyi ya ɗauke shi yayinda Bulus yake ta tsawaita magana. Sa’ad da yake barci, sai ya fāɗi daga gidan sama a hawa ta uku aka kuma ɗauke shi matacce. 10 Sai Bulus ya sauka, ya miƙe a kan saurayin ya rungume shi ya ce, “Kada ku damu, yana da rai!” 11 Sai ya koma ɗakin da yake a gidan sama, ya gutsuttsura burodi ya kuma ci. Bayan ya yi magana har gari ya waye, sai ya tafi. 12 Mutanen suka ɗauki saurayin da rai zuwa gida suka kuma ta’azantu ƙwarai da gaske.

  10. 28 “Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji kuke kuma fama da kaya, zan kuwa ba ku hutu. 29 Ku ɗauki karkiyata a kanku, ku kuma yi koyi da ni, gama ni mai tawali’u ne marar girman kai, za ku kuwa sami hutu don rayukanku. 30 Gama karkiyata mai sauƙi ce, kayana kuma marasa nauyi ne.”

  11. 9 Har yaushe za ku kwanta a can, ku ragwaye?

    Yaushe za ku farka daga barcinku?

    10 Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi,

    ɗan naɗin hannuwa don a huta,

    11 talauci kuwa zai zo kamar ’yan hari

    rashi kuma kamar ɗan fashi.

  12. 5 Dukan matuƙan jirgin suka tsorata, kowannensu kuma ya yi kuka ga allahnsa, suka kuma jefar da kayan jirgi a cikin teku domin su rage nauyin jirgin.

    Ana cikin haka, ashe, Yunana ya sauka can ƙarƙashin jirgi ya je ya kwanta, yana ta sharar barcinsa. 6 Sai kyaftin ɗin ya je wajensa ya ce masa, “Don me kake barci? Tashi ka kira bisa ga allahnka! Mai yiwuwa yă ji mu, yă cece mu don kada mu hallaka.”

  13. 35 “Saboda haka, sai ku zauna a shirye, domin ba ku san lokacin da maigidan zai dawo ba, ko da yamma ne, ko da tsakar dare ne, ko lokacin da zakara na cara ne, ko kuma da safe ne. 36 In ya zo kwaram, kada ka bari yă tarar da kai kana barci. 37 Abin da na faɗa muku, na faɗa wa kowa. ‘Ku yi tsaro!’ ”

  14. 6 Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya. 7 Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za tă tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.

  15. 20 Saboda haka mutumin ya sa wa dukan dabbobi, da tsuntsayen sama da dukan namun jeji sunaye.

    Amma ba a sami mataimakin da ya dace da Adamu ba. 21 Saboda haka Ubangiji Allah ya sa mutumin ya yi barci mai nauyi; yayinda yake barci sai ya ɗauko ɗaya daga cikin haƙarƙarin mutumin, ya kuma rufe wurin da nama. 22 Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mace daga haƙarƙarin da ya ɗauko daga mutumin, ya kuwa kawo ta wurin mutumin.

  16. 14 Gama Allah yana magana,

    yanzu ga wannan hanya, yanzu kuma ga wata hanya

    ko da yake ba lalle mutum yă lura ba.

    15 A cikin mafarki, cikin wahayi da dare,

    sa’ad da barci mai zurfi ya fāɗo a kan mutane

    lokacin da suke cikin barci kan gadajensu,

    16 mai yiwuwa yă yi musu magana a cikin kunnuwansu

    yă razana su da gargaɗinsa,

    17 don a juyar da su daga abin da yake yi da ba daidai ba

    a kuma hana su daga girman kai,

    18 don a kāre su daga fāɗuwa cikin rami,

    a kāre su daga hallaka ta wurin takobi.

  17. 14 Shi ya sa aka ce,

    “Ka farka, ya kai mai barci,

    ka tashi daga matattu,

    Kiristi kuwa zai haskaka ka.”

    15 Sai ku yi hankali sosai da yadda kuke rayuwa, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai kamar masu hikima. 16 Ku kuma yi matuƙar amfani da kowane zarafi, don kwanakin nan mugaye ne.

  18. 13 Kada ka so barci in ba haka ba za ka talauce;

    ka zauna a faɗake za ka kuwa kasance da sauran abinci.

  19. 22 Wata rana Yesu ya ce wa almajiransa, “Mu haye zuwa wancan gefen tafkin.” Sai suka shiga jirgin ruwa suka fara tafiya. 23 Da suna cikin tafiya, sai barci ya kwashe shi. Sai wata babban iska ta taso kan tafkin, har ruwa ya fara shiga cikin jirgin. Suka shiga babban hatsari.

    24 Almajiran suka je suka tashe shi daga barci, suka ce, “Ubangiji, Ubangiji, za mu nutse!”

    Ya tashi ya kwaɓe iskar da kuma haukar ruwan. Sai ruwan da iskar suka natsu. Kome ya yi tsit. 25 Sai ya tambayi almajiransa, “Ina bangaskiyarku?”

    A cikin tsoro da mamaki, suka ce wa junansu, “Wane ne wannan? Yana ba da umarni ga iska da ruwa ma, kuma suna biyayya da shi?”

  20. 6 A daren da in gari ya waye da Hiridus yake niyyar kawo shi domin a yi masa shari’a, Bitrus yana barci tsakanin sojoji biyu, daure da sarƙoƙi biyu, masu gadi kuma suna bakin ƙofa. 7 Ba zato ba tsammani sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana haske kuma ya haskaka a ɗakin. Ya bugi Bitrus a gefe ya kuma tashe shi ya ce, “Maza, ka tashi!” Sarƙoƙin kuwa suka zube daga hannuwansa.

  21. 15 Ragwanci kan jawo zurfin barci,

    mutum mai sanyin jiki kuma yana tare da yunwa.

  22. 5 Ango ya yi jinkirin zuwa, sai duk suka shiga gyangyaɗi har barci ya kwashe su.

  23. 36 Sa’an nan Yesu ya tafi da almajiransa zuwa wani wurin da ake kira Getsemane, ya ce musu, “Ku zauna nan, in je can in yi addu’a.” 37 Ya ɗauki Bitrus da ’ya’ya biyun nan na Zebedi tare da shi, sai ya fara baƙin ciki, ya kuma damu. 38 Sai ya ce musu, “Raina yana cike da baƙin ciki har kamar zan mutu. Ku dakata a nan, ku kuma yi tsaro tare da ni.”

    39 Da ya yi gaba kaɗan, sai ya fāɗi a ƙasa, ya yi addu’a ya ce, “Ubana, in mai yiwuwa ne, a ɗauke mini wannan kwaf. Amma ba nufina ba, sai naka.”

    40 Sa’an nan ya komo wurin almajiransa, ya tarar suna barci. Ya tambayi Bitrus ya ce, “Ashe, ba za ku iya yin tsaro tare da ni ko na sa’a guda ba? 41 Ku yi tsaro, ku kuma yi addu’a, don kada ku fāɗi cikin jarraba. Ruhu yana so, sai dai jiki raunana ne.”

  24. 1 Shi wanda yake zama a wurin Mafi Ɗaukaka

    zai huta a cikin inuwar Maɗaukaki.

    2 Zan ce game da Ubangiji, “Shi ne mafakata da kagarata,

    Allahna, wanda nake dogara.”

    3 Tabbatacce zai cece ka

    daga tarkon mai farauta

    da kuma daga cututtuka masu kisa.

    4 Zai rufe ka da fikafikansa,

    a ƙarƙashin fikafikansa kuwa za ka sami mafaka;

    amincinsa zai zama maka garkuwa da katanga.

    5 Ba za ka ji tsoron razanar dare,

    ko kibiyoyi da suke firiya da rana ba,

    6 ko bala’in da yake aukowa cikin duhu,

    ko annobar da take hallakarwa da tsakar rana.

    7 Dubu za su iya fāɗuwa a gefenka,

    dubu goma a hannun damanka,

    amma ba abin da zai zo kusa da kai.

    8 Za ka dai gan da idanunka

    yadda ake hukunta mugaye.

    9 In ka mai da Mafi Ɗaukaka wurin zamanka,

    har ma Ubangiji wanda yake mafakata,

    10 to, babu wani mugun abin da zai same ka,

    ba masifar da za tă zo kusa da tentinka.

  25. 12 Barcin ma’aikaci daɗi gare shi,

    ko yă ci kaɗan ko da yawa,

    amma yalwar mai arziki

    ba ta barinsa yă iya yin barci.

  26. 33 Da farko dai, ku nemi mulkin Allah da kuma adalcinsa, za a kuwa ba ku dukan waɗannan abubuwa. 34 Saboda haka kada ku damu game da gobe, gama gobe zai damu da kansa. Damuwar yau ma ta isa wahala.

  27. 3 Za ka kiyaye shi da cikakken salama

    shi wanda ya kafa zuciyarsa gare ka,

    domin ya dogara a gare ka.

    4 Ku dogara ga Ubangiji,

    gama shi Ubangiji, ne madawwamin Dutse.

  28. 25 Zan wartsake waɗanda suka gaji in kuma ƙosar da waɗanda ransu ya yi yaushi.”

    26 A kan wannan na farka na duba kewaye. Barcina ya yi mini daɗi.

  29. 16 Da irin wannan fitina ta tsokane shi kwana da kwanaki har sai da ya gaji kamar zai mutu.

    17 Saboda haka sai ya faɗa mata kome ya ce, “Ba a taɓa sa reza a kaina ba, domin ni Naziri ne keɓaɓɓe ga Allah tun haihuwa. In kuwa an aske kaina, ƙarfina zai rabu da ni, sai in zama kamar kowa.”

    18 Da Delila ta gane ya gaya mata kome yanzu, sai ta aika saƙo zuwa ga shugabannin Filistiyawa ta ce, “Ku ƙara zuwa sau ɗayan nan, ai, ya gaya mini kome.” Saboda haka shugabannin Filistiyawa suka dawo tare da azurfa a hannuwansu. 19 Bayan ta sa shi ya yi barci a cinyarta, sai ta kira wani ya zo ya aske kitso guda bakwai nan a kansa, aka fara rinjayensa. Ƙarfinsa kuwa ya rabu da shi.

    20 Sa’an nan ta yi ihu ta ce, “Samson ga Filistiyawa sun zo su kama ka!”

    Sai ya farka daga barci yana tsammani cewa, “Zan fita kamar dā in miƙe jikina.” Amma bai san cewa Ubangiji ya rabu da shi ba.

    21 Sa’an nan Filistiyawa suka fizge shi, suka ƙwaƙule idanunsa suka gangara da shi zuwa Gaza. Da suka daure shi da sarƙoƙin tagulla, sai aka sa shi yana niƙa a kurkuku.