108 Bible Verses About Protection
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
1 Shi wanda yake zama a wurin Mafi Ɗaukaka
zai huta a cikin inuwar Maɗaukaki.
2 Zan ce game da Ubangiji, “Shi ne mafakata da kagarata,
Allahna, wanda nake dogara.”
3 Tabbatacce zai cece ka
daga tarkon mai farauta
da kuma daga cututtuka masu kisa.
4 Zai rufe ka da fikafikansa,
a ƙarƙashin fikafikansa kuwa za ka sami mafaka;
amincinsa zai zama maka garkuwa da katanga.
5 Ba za ka ji tsoron razanar dare,
ko kibiyoyi da suke firiya da rana ba,
6 ko bala’in da yake aukowa cikin duhu,
ko annobar da take hallakarwa da tsakar rana.
7 Dubu za su iya fāɗuwa a gefenka,
dubu goma a hannun damanka,
amma ba abin da zai zo kusa da kai.
8 Za ka dai gan da idanunka
yadda ake hukunta mugaye.
9 In ka mai da Mafi Ɗaukaka wurin zamanka,
har ma Ubangiji wanda yake mafakata,
10 to, babu wani mugun abin da zai same ka,
ba masifar da za tă zo kusa da tentinka.
11 Gama zai umarci mala’ikunsa game da kai
don su tsare ka a dukan hanyoyinka;
12 za su tallafe ka da hannuwansu,
don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.
-
Zabura ta Dawuda.
1 Ubangiji ne yake kiwona, ba zan rasa kome ba,
2 Yakan sa in kwanta a makiyaya mai ɗanyar ciyawa,
yakan bi da ni kusa da ruwaye marar hayaniya,
3 yakan maido da raina.
Yakan bi da ni a hanyoyin adalci
saboda sunansa.
4 Ko da na yi tafiya
ta kwari na inuwar mutuwa,
ba zan ji tsoron mugu ba,
gama kana tare da ni;
bulalarka na dūka da kuma sandanka na tafiya,
za su yi mini ta’aziyya.
-
Waƙar haurawa.
1 Na tā da idanuna zuwa wajen tuddai,
ta ina ne taimakona zai zo?
2 Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji,
wanda ya kafa sama da ƙasa.
3 Ba zai bari ƙafarka tă yi santsi ba,
shi da yake tsaronka ba zai yi gyangyaɗi ba;
4 tabbatacce, shi da yake tsaron Isra’ila
ba ya gyangyaɗi ko barci.
5 Ubangiji yana tsaronka,
Ubangiji ne inuwa a hannun damanka;
6 rana ba za tă buge ka cikin yini ba
balle wata da dare.
7 Ubangiji zai kiyaye ka daga dukan masifa,
zai tsare ranka;
8 Ubangiji zai kiyaye shigarka da fitarka
yanzu da har abada kuma.
-
10 A ƙarshe, bari ƙarfin ikon Ubangiji yă ba ku ƙarfi. 11 Ku yafa dukan kayan yaƙin da Allah yake bayarwa, don ku iya kāre kanku daga dabarun Shaiɗan. 12 Gama ba da mutane da suke nama da jini ne muke yaƙi ba. Muna yaƙi ne da ikoki, da hukumomi, da masu mulkin duhu, da kuma a ikokin da suke cikin a sararin sama. 13 Saboda haka sai ku yafa dukan kayan yaƙi na Allah, domin sa’ad da ranar mugun nan ta zo, ku iya yin tsayin daka, bayan kuma kuka gama kome, ku dāge. 14 Saboda haka fa ku dāge, ku sa gaskiya tă zama ɗamararku, adalci yă zama sulkenku, 15 shirin kai bisharar salama yă zama kamar takalmi a ƙafafunku. 16 Ban da waɗannan kuma, ku ɗauki garkuwar bangaskiya, wadda za ku iya kashe dukan kibiyoyin wutar Mugun nan da ita. 17 Ku kuma ɗauki hular kwano na ceto, da takobin Ruhu, wato, Maganar Allah.
-
3 Ubangiji mai aminci ne, zai ƙarfafa ku, yă kuma tsare ku daga mugun nan. 4 Muna da tabbaci cikin Ubangiji cewa kuna bin umarnai da muka yi muku, za ku kuma ci gaba da yin abubuwan da muka umarta. 5 Bari Ubangiji yă bi da zukatanku ga ƙaunan nan ta Allah da kuma jimirin nan na Kiristi.
-
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta ’Ya’yan Kora maza. Bisa ga alamot Waƙa ce.
1 Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu,
kullum yana a shirye yă taimaka a lokacin wahala.
2 Saboda haka ba za mu ji tsoro ba, ko da ƙasa ta girgiza
duwatsu kuma suka fāɗi cikin zurfin teku,
-
3 Amma kai ne garkuwa kewaye da ni, ya Ubangiji;
ka ba ni ɗaukaka ka kuma ɗaga kaina.
4 Ga Ubangiji na yi kuka mai ƙarfi,
ya kuwa amsa mini daga tudunsa mai tsarki. Sela
5 Na kwanta na yi barci;
na kuma farka, gama Ubangiji yana kiyaye ni.
-
10 Saboda haka kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai;
kada ka karai, gama ni ne Allahnka.
Zan ƙarfafa ka in kuma taimake ka;
zan riƙe ka da hannun damana mai adalci.
11 “Duk wanda ya yi fushi da kai
tabbatacce zai sha kunya da ƙasƙanci;
waɗanda suka yi hamayya da kai
za su zama kamar ba kome ba su kuma hallaka.
12 Ko ka nemi abokan gābanka,
ba za ka same su ba.
Waɗanda suke yaƙi da kai
za su zama kamar ba kome ba.
-
11 Amma bari dukan waɗanda suke neman mafaka gare ka su yi murna;
bari kullum su yi ta rerawa saboda farin ciki.
Ka buɗe kāriyarka a bisansu,
domin waɗanda suke ƙaunar sunanka su yi farin ciki a cikinka.
-
7 Kai ne wurin ɓuyata;
za ka tsare ni daga wahala
ka kewaye ni da waƙoƙin ceto. Sela
-
10 Sunan Ubangiji hasumiya ce mai ƙarfi;
masu adalci kan gudu zuwa wurinta don su zauna lafiya.
11 Dukiyar masu arziki ita ce birninsu mai katanga;
suna gani cewa ba za a iya huda katangar ba.
12 Kafin fāɗuwarsa zuciyar mutum takan yi girman kai,
amma sauƙinkai kan zo kafin girmamawa.
-
17 ba makamin da aka ƙera don yă cuce ki da zai yi nasara,
za ki kuma mayar da magana ga duk wanda ya zarge ki.
Wannan ne gādon bayin Ubangiji,
kuma wannan ita ce nasararsu daga gare ni,”
in ji Ubangiji.
-
28 Ina ba su rai madawwami, ba za su taɓa hallaka ba; ba kuma mai ƙwace su daga hannuna. 29 Ubana, wanda ya ba ni su, ya fi duka girma, ba mai ƙwace su daga hannun Ubana. 30 Da ni da Uba ɗaya ne.”
-
16 A lokacin da na kāre kaina da farko, ba wanda ya goyi bayana, sai ma kowa ya yashe ni. Ina fata ba za a lasafta wannan laifi a kansu ba. 17 Amma Ubangiji ya tsaya tare da ni, ya kuma ba ni ƙarfi, don ta wurina a yi cikakkiyar shelar saƙon har Al’ummai duka su ji. Aka kuma cece ni daga bakin zaki. 18 Ubangiji zai cece ni daga kowane mugun hari yă kuma kai ni mulkinsa na sama lafiya. A gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada abadin. Amin.
-
13 Ba jarrabar da ta taɓa samunku, wadda ba a saba yi wa mutum ba. Allah mai aminci ne; ba zai bari a jarrabce ku fiye da ƙarfinku ba. Amma in aka jarrabce ku, zai nuna muku mafita, domin ku iya cin nasara.
-
6 Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tafe tare da ku, ba zai taɓa barinku ko yă yashe ku ba.”
-
7 Mala’ikan Ubangiji ya kafa sansani kewaye da waɗanda suke tsoronsa,
ya kuwa cece su.
8 Ku gwada ku gani cewa Ubangiji yana da kyau;
mai albarka ne mutumin da yake neman mafaka a gare shi.
9 Ku ji tsoron Ubangiji, ku tsarkakansa,
gama masu tsoronsa ba sa rasa kome.
-
23 Bari Allah da kansa, Allah na salama, yă tsarkake ku sarai. Bari dukan ruhunku, ranku, da kuma jikinku su zama marar aibi a dawowar Ubangijinmu Yesu Kiristi. 24 Wannan wanda ya kira ku mai aminci ne zai kuwa aikata.
-
13 Musa ya amsa wa mutane ya ce, “Kada ku ji tsoro. Ku tsaya dai ku ga ceton da Ubangiji zai kawo muku yau. Masarawan da kuke gani yau, ba za ku ƙara ganinsu ba. 14 Ubangiji zai yi yaƙi dominku, ku dai tsaya kurum.”
-
1 To, fa, ga abin da Ubangiji yana cewa,
shi da ya halicce ka, ya Yaƙub,
shi da ya siffanta ka, ya Isra’ila,
“Kada ka ji tsoro, gama na fanshe ka;
na kira ka da suna; kai nawa ne.
2 Sa’ad da kuka bi ta ruwaye,
zan kasance tare da ku;
sa’ad da kuka bi ta koguna,
ba za su kwashe ku ba.
Sa’ad da kuke tafiyata cikin wuta,
ba za tă ƙone ku ba;
harsunan wutar ba za su ƙone ku ba.
3 Gama ni ne Ubangiji, Allahnku,
Mai Tsarkin nan na Isra’ila, Mai Cetonku;
na bayar da Masar don fansa,
Kush da Seba a maimakonku.
-
6 Ubangiji yana tare da ni; ba zan ji tsoro ba.
Me mutum zai yi mini?
7 Ubangiji yana tare da ni; shi ne mai taimakona.
Zan yi nasara a kan abokan gābana.
8 Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji
da in dogara ga mutum.
9 Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji
da in dogara ga sarakuna.
-
7 Ka nuna mini girmar ƙaunarka mai banmamaki,
kai da kake ceton waɗanda suke neman mafaka daga abokan gābansu
da hannunka na dama.
8 Ka kiyaye ni yadda ake kiyaye ido;
ka ɓoye ni cikin inuwar fikafikanka
9 daga mugaye waɗanda suke kai mini hari,
daga abokan gāba masu mutuwa waɗanda suka kewaye ni.
10 Sun rufe zukatansu marar tausayi,
da bakunansu suna magana da fariya.
-
17 Adalai kan yi kuka, Ubangiji kuwa yakan ji su;
yakan cece su daga dukan wahalarsu.
18 Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai
ya kuma cece waɗanda aka ragargaza a ruhu.
19 Adali zai iya kasance da wahala da yawa,
amma Ubangiji yakan cece shi daga dukansu;
20 yakan tsare dukan ƙasusuwansa,
ba ko ɗayansu da zai karye.
-
7 Ko da na yi tafiya a tsakiyar wahala,
kana kiyaye raina;
ka miƙa hannunka a kan fushin maƙiyana,
da hannunka na dama ka cece ni.
-
3 Allahna shi ne dutsena. A gare shi nake samun kāriya
shi ne garkuwata da kuma ƙahon cetona.
Shi ne mafakata, maɓuyata, da mai cetona.
Daga mutane masu fitina, ka cece ni.
4 “Na kira ga Ubangiji, wanda ya cancanci yabo,
na kuwa tsira daga abokan gābana.
-
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Kada Ka Hallaka.” Ta Dawuda. Wani miktam. Sa’ad da ya gudu daga Shawulu zuwa cikin kogo.
1 Ka yi mini jinƙai, ya Allah, ka yi mini jinƙai,
gama a gare ka raina yake samun mafaka.
Zan sami mafaka a inuwar fikafikanka
sai masifar ta wuce.
-
114 Kai ne mafakata da garkuwata;
na sa zuciyata a maganarka.
-
1 A ƙarshe, ’yan’uwana, ku yi farin ciki a cikin Ubangiji! Ba abin damuwa ba ne a gare ni in sāke rubuta muku irin waɗannan abubuwa, domin lafiyarku ne. 2 Ku yi hankali da waɗancan karnuka, waɗancan mutane masu aikata mugunta, waɗancan masu yankan jiki. 3 Gama mu ne masu kaciya, mu da muke yi sujada ta wurin Ruhun Allah, mu da muke taƙama a cikin Kiristi Yesu, mu da ba mu dogara da ayyukan da ake gani ba,
-
14 Ubangiji ya ce, “Domin ya ƙaunace ni, zan kuɓutar da shi;
zan kiyaye shi, gama ya yarda da sunana.
15 Zai kira bisa sunana, zan kuma amsa masa;
zan kasance tare da shi a lokacin wahala,
zan kuɓutar da shi in kuma girmama shi.
16 Da tsawon rai zan ƙosar da shi
in kuma nuna masa cetona.”
-
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda bawan Ubangiji. Ya rera ta ga Ubangiji kalmomin wannan waƙa sa’ad da Ubangiji ya cece shi daga hannun dukan abokan gābansa da kuma daga hannun Shawulu, ya ce,
1 Ina ƙaunarka, ya Ubangiji, ƙarfina.
2 Ubangiji shi ne dutsena, kagarata da kuma mai cetona;
Allahna shi ne dutsena, a gare shi nake neman mafaka.
Shi ne garkuwata da ƙahon cetona, mafakata.
-
16 Amma zan rera game da ƙarfinka,
da safe zan rera game da ƙaunarka;
gama kai ne mafakata,
kagarata a lokacin wahala.
-
4 Har lokacin da kuka tsufa kuka yi furfura
ni ne shi, ni ne shi wanda zai lura da ku.
Na yi ku zan kuma riƙe ku;
zan lura da ku
in kuma kuɓutar da ku.
-
31 Me za mu ce ke nan game da wannan abu? In Allah yana goyon bayanmu, wa kuwa zai iya gāba da mu? 32 Shi da bai hana Ɗansa ba, sai ma ya ba da shi saboda mu duka, ashe, ba zai kuma ba mu, tare da shi, dukan abubuwa cikin alherinsa ba? 33 Wa zai kawo wani zargi a kan waɗanda Allah ya zaɓa? Allah ne mai kuɓutarwa.
-
6 Saboda haka muna iya fitowa gabagadi, mu ce,
“Ubangiji ne mai taimakona; ba zan ji tsoro ba.
Me mutum zai iya yi mini?”
-
7 Saboda haka, ku miƙa kanku ga Allah. Ku yi tsayayya da Iblis, zai kuwa guje ku. 8 Ku matso kusa da Allah shi kuwa zai matso kusa da ku. Ku wanke hannuwanku, ku masu zunubi, ku kuma tsarkake zukatanku, ku masu zuciya biyu.
-
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Kada Ka Hallaka.” Ta Dawuda. Wani miktam. Sa’ad da Shawulu ya aiki mutane su yi tsaron gidan Dawuda don yă kashe shi.
1 Ka cece ni daga abokan gābana, ya Allah;
ka tsare ni daga waɗanda suka tayar mini.
-
7 Ubangiji nagari ne,
mafaka kuma a lokacin wahala.
Yana kula da waɗanda suka dogara gare shi,
-
15 Ba addu’ata ba ce ka ɗauke su daga duniya ba, sai dai ka kāre su daga mugun nan.
-
Miktam ne na Dawuda.
1 Ka kiyaye ni, ya Allah,
gama a cikinka nake samun mafaka.
2 Na ce wa Ubangiji, “Kai ne shugabana;
in ba tare da kai ba, ba ni da wani abu mai kyau.”
-
30 Game da Allah kuwa, hanyarsa cikakkiya ce;
maganar Ubangiji marar kuskure ne.
Shi garkuwa ne ga dukan waɗanda suke neman mafaka a gare shi.
31 Gama wane ne Allah in ba Ubangiji ba?
Wane ne kuwa Dutse in ba Allahnmu ba?
32 Allah ne ya ƙarfafa ni da ƙarfi
ya kuma sa hanyarta ta zama cikakkiya.
-
22 Ubangiji yakan cece bayinsa;
ba wanda yake neman mafaka a wurinsa da za a hukunta.
-
7 Don kada in cika da girman kai saboda waɗannan mafifitan manyan wahayoyi, sai aka sa mini wata ƙaya a jikina wadda ta zama ɗan saƙon Shaiɗan, don ta wahalshe ni. 8 Sau uku na roƙi Ubangiji yă raba ni da wannan abu. 9 Amma ya ce mini, “Alherina ya ishe ka, domin a cikin rashin ƙarfi ne ake ganin cikar ikona.” Saboda haka, zan ƙara yin taƙama da farin ciki game da rashin ƙarfina, domin ikon Yesu Kiristi yă zauna tare da ni. 10 Shi ya sa nake murna cikin rashin ƙarfi, da zagi, da shan wahaloli, da tsanantawa, da matsaloli, saboda Kiristi. Don a sa’ad da nake marar ƙarfi a nan ne nake da ƙarfi.
-
5 Ku kiyaye kanku daga yawan son kuɗi, ku kuma gamsu da abin da kuke da shi, gama Allah ya ce,
“Ba zan taɓa bar ka ba;
ba zan taɓa yashe ka ba.”
-
5 Sai Iblis ya kai shi birni mai tsarki, ya kai shi can wuri mafi tsayi duka na haikali. 6 Ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, yi tsalle ka sauka ƙasa. Gama a rubuce yake,
“ ‘Zai umarci mala’ikunsa game da kai,
za su tallafe ka da hannuwansu,
don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.’”
7 Yesu ya amsa masa ya ce, “A rubuce yake kuma cewa, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’”
-
42 Bafilistin ya dubi Dawuda daga sama har ƙasa, ya gan dai ɗan yaro ne kawai, kyakkyawa kuma mai ƙoshin lafiya, sai ya rena shi. 43 Ya ce masa, “Kana tsammani ni kare ne da za ka zo mini da sanda?” Sai ya la’anci Dawuda da sunayen allolin Filistiyawa. 44 Ya ce, “Zo nan, ni kuwa zan ba da naman jikinka ga tsuntsayen sama da namun jeji su ci.”
45 Dawuda ya ce wa Bafilistin, “Kana zuwa ka yaƙe ni da māshi da takobi da kere, amma ni ina zuwa in yaƙe ka a cikin sunan Ubangiji Maɗaukaki, Allah na rundunar Isra’ila, wanda ka rena. 46 Yau nan, Ubangiji zai bashe ka a hannuna, zan kuwa kashe ka, in datse kanka. Yau, zan ba da gawawwakin rundunar Filistiyawa ga tsuntsayen sama da namun jeji, da haka duniya za tă sani lalle akwai Allah a cikin Isra’ila. 47 Duk waɗanda suka taru a nan za su san cewa ba da māshi ko takobi ne Ubangiji yake ceto ba, gama yaƙin nan na Ubangiji ne, shi kuwa zai bashe ku duka a hannuwanmu.”
48 Yayinda Bafilistin yana matsowa kusa domin yă fāɗa wa Dawuda, sai Dawuda ya ruga a guje zuwa bakin dāgā don yă same shi. 49 Ya sa hannu a jakarsa ya ɗauki dutse, ya sa cikin majajjawa ya wurga, dutsen kuwa ya bugi Bafilistin a goshi, dutsen ya shiga cikin goshinsa, sai Bafilistin ya fāɗi rubda ciki.
-
9 Gama gaban Ubangiji yana ko’ina a duniya don yă ƙarfafa waɗanda zukatansu suke binsa cikin aminci. Ka yi wauta, daga yanzu nan gaba za ka yi ta yaƙi.”
-
5 “Saboda danniyar marasa ƙarfi da kuma nishin masu bukata,
zan tashi yanzu,” in ji Ubangiji.
“Zan kāre su daga masu yin musu sharri.”
-
35 Ka ba ni garkuwar nasara,
kuma hannunka na dama yana riƙe ni;
ya sunkuya don ka mai da ni mai girma.
36 Ka fadada hanyar da yake a ƙarƙashina,
don kada ɗiɗɗigena yă juya.
-
7 Domin kai ne mai taimakona,
ina rera a cikin inuwar fikafikanka.
8 Raina ya manne maka;
hannunka na dama yana riƙe da ni.
9 Su da suke neman raina za su hallaka;
za su gangara zuwa zurfafan duniya.
-
4 Ka kiyaye ni, ya Ubangiji, daga hannuwan mugaye;
ka tsare ni daga mutane masu rikici
waɗanda suke shirin kwashe ni a ƙafafu.
-
3 “Ku shirya garkuwoyinku, manya da ƙanana,
ku kuma fito don yaƙi!
4 Ku shirya dawakai,
ku sa musu sirdi!
Ku tsaya a wurarenku
saye da hulunan kwano a kai!
Ku wasa māsunku,
ku yafa kayan yaƙinku!
-
28 Mun kuma san cewa a cikin dukan abubuwa Allah yana aikata alheri ga waɗanda suke ƙaunarsa, yana waɗanda aka kira bisa ga nufinsa.
-
4 Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji kullum. Ina sāke gaya muku ku yi farin ciki! 5 Bari kowa yă kasance da sauƙinkai. Ubangiji ya yi kusan zuwa. 6 Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya. 7 Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za tă tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.
-
4 Ku, ’ya’yana ƙaunatattu, ku daga Allah ne, kun kuma yi nasara a kan magabtan Kiristi, domin wanda yake a cikinku ya fi wanda yake a duniya girma.
-
10 Da yake ka kiyaye umarnina ta wurin jimrewa, ni ma zan tsare ka daga lokacin nan na gwaji wanda zai zo bisan dukan duniya don a gwada waɗanda suke zama a duniya.
-
1 Sa’ad da kuka tafi yaƙi da abokan gābanku, kuka ga dawakai da kekunan yaƙi da kuma mayaƙan da suka fi ku yawa, kada ku ji tsoronsu, domin Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar zai kasance tare da ku. 2 Sa’ad da kuke gab da kama yaƙi, sai firist yă zo gaba yă yi wa mayaƙan jawabi. 3 Zai ce, “Ku ji, ya Isra’ila, yau kuna gab da kama da abokan gābanku. Kada ku karai, ko ku ji tsoro; kada ku firgita, ko ku yi rawar jiki a gabansu. 4 Gama Ubangiji Allahnku, yana tafe tare da ku, zai yaƙi abokan gābanku dominku, yă ba ku nasara.”
-
5 Ba wanda zai yi tsayayya da kai dukan kwanakin ranka. Yadda na kasance tare da Musa, haka zan kasance tare da kai; ba zan taɓa rabuwa da kai ba; ba zan yashe ka ba.
-
9 Ba ni na umarce ka ba? Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro. Kada ka ji tsoro; kada ka karaya, gama Ubangiji Allahnka zai kasance tare da kai duk inda za ka je.”
-
8 Kullum nakan sa Ubangiji a gabana.
Gama yana a hannun damana, ba zan jijjigu ba.
-
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda.
1 Mai albarka ne wanda yake jin tausayin marasa ƙarfi;
Ubangiji yakan kuɓutar da shi a lokutan wahala.
2 Ubangiji zai kāre shi yă kuma kiyaye ransa;
zai albarkace shi a cikin ƙasar
ba kuwa zai miƙa shi ga hannun maƙiyansa ba.
-
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Ta Dawuda.
1 Ka ji kukata, ya Allah;
ka saurari addu’ata.
2 Daga iyakar duniya na yi kira gare ka,
na yi kira yayinda zuciyata ta karai;
ka bishe ni zuwa dutsen da ya fi ni tsayi.
3 Gama kai ne mafakata,
hasumiya mai ƙarfi gāba da maƙiyi.
4 Ina marmari in zauna a tentinka har abada
in sami mafaka a cikin inuwar fikafikanka. Sela
-
2 Shi kaɗai ne dutsena da cetona;
shi ne kagarata, ba zan jijjigu ba.
-
25 Kada ka ji tsoron masifar da za tă faru farat ɗaya
ko lalacin da yakan auka wa mugaye,
26 gama Ubangiji zai zama ƙarfin halinka
zai kuwa kiyaye ƙafarka daga fāɗawa a tarko.
-
5 Ka nemi hikima, ka nemi fahimi;
kada ka manta da kalmomina ko ka kauce daga gare su.
6 Kada ka ƙyale hikima, za tă kuwa tsare ka;
ka ƙaunace ta, za tă kuwa lura da kai.
7 Hikima ce mafi girma duka; saboda haka ka nemi hikima.
Ko da za tă ci duk abin da kake da shi, ka dai nemi fahimi.
8 Ka ƙaunace ta, za tă ɗaukaka ka;
ka rungume ta, za tă kuwa girmama ka.
9 Za tă zama kayan ado da za su inganta kanka
tă kuma zamar maka rawanin ɗaukaka.”
-
23 Tsoron Ubangiji yakan kai ga rai.
Sa’an nan mutum ya sami biyan bukata, ba abin da zai cuce shi.
-
5 “Kowace maganar Allah ba ta da kuskure;
shi ne garkuwa ga waɗanda suke neman mafaka daga gare shi.
-
17 Ku koyi yin nagarta; ku nemi adalci.
Ku ƙarfafa waɗanda aka zalunta.
Ku ba wa marayu hakkinsu,
ku taimaki gwauruwa.
-
17 Ubangiji Allahnki yana tare da ke,
mai iko ne don ceto.
Zai yi matuƙar farin ciki da ke,
zai rufe ki da ƙaunarsa,
zai yi farin ciki da ke ta wurin rerawa.”
-
19 Na ba ku iko da za ku tattaka macizai, da kunamai, ku kuma shawo kan dukan ikon abokin gāba, kuma ba wani lahani da zai same ku.
-
16 Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami. 17 Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yă yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin yă ceci duniya ta wurinsa.
-
24 To, yabo yă tabbata a gare shi, shi wanda yake da iko yă tsare ku daga fāɗuwa, yă kuma miƙa ku marasa laifi a gaban ɗaukakarsa da matuƙar farin ciki. 25 Gare shi kuma, shi da yake kaɗai Allah Mai Cetonmu, ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu, bari ɗaukaka, daraja, iko da mulki, su tabbata a gare shi, tun farkon zamanai, yanzu, da har abada abadin! Amin.
-
Waƙar haurawa. Ta Solomon.
1 In ba Ubangiji ne ya gina gida ba,
masu gininta suna wahala a banza ne.
In ba Ubangiji ne yake tsaron birni ba,
masu tsaro suna yin tsaro a banza.
-
15 Ina tare da kai, zan lura da kai duk inda ka tafi, zan kuma dawo da kai zuwa wannan ƙasa. Ba zan rabu da kai ba sai na cika abin da na yi maka alkawari.”
-
37 Zai ce, “To, ina allolinsu,
dutsen da suka yi mafaka a ciki,
38 allolin da suka ci kitsen hadayunsu
suka kuma sha ruwan inabin hadayunsu?
Ku sa su tashi su taimake ku mana!
Bari su ba ku mafaka!
39 “Ku duba yanzu cewa ni ne Shi!
Ba wani allah in ban da ni.
Nakan kashe in kuma rayar,
nakan sa rauni in kuma warkar,
ba wanda yake da iko yă cece wani daga hannuna.
-
38 Sai Shawulu ya kawo kayan yaƙinsa ya sa wa Dawuda. Ya sa masa hular kwanon da aka yi da tagulla a kansa, ya kuma sa masa rigar ƙarfensa.
-
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda.
1 Ubangiji ya amsa maka sa’ad da ka yi kira cikin wahala;
bari sunan Allah na Yaƙub yă kiyaye ka.
-
15 Idanun Ubangiji suna a kan masu adalci
kuma kunnuwansa suna sauraran kukansu;
-
3 Sa’ad da nake tsoro, zan dogara gare ka.
4 Ga Allah wanda maganarsa nake yabo
ga Allah na dogara; ba zan ji tsoro ba.
Me mutum mai mutuwa zai yi mini?
-
Waƙar haurawa.
1 Waɗanda suke dogara ga Ubangiji suna kama da Dutsen Sihiyona,
wanda ba ya jijjiguwa amma dawwammame ne har abada.
2 Kamar duwatsun da sun kewaye Urushalima,
haka Ubangiji ya kewaye mutanensa
yanzu da har abada kuma.
-
19 Yakan cika sha’awar waɗanda suke tsoronsa;
yakan ji kukansu yă kuma cece su.
-
33 amma duk wanda ya saurare ni, zai zauna lafiya
yă kuma kasance da rai kwance, ba tare da tsoron lahani ba.”
-
21 Ba wani lahanin da zai sami masu adalci,
amma mugaye suna da nasu cike da wahala.
-
26 Duk mai tsoron Ubangiji yana da zaunannen mafaka,
kuma ga ’ya’yansa zai zama mafaka.
-
12 Mai basira kan hango hatsari ya kuma kauce,
marar azanci zai yi ta kutsa kai ciki, daga baya ya yi da na sani.
-
1 A wannan rana za a rera wannan waƙa a ƙasar Yahuda.
Muna da birni mai ƙarfi;
Allah yake ceton
katanga da kuma kagarunta.
2 A buɗe ƙofofi
saboda al’umma mai adalci ta shiga,
al’ummar da mai aminci.
3 Za ka kiyaye shi da cikakken salama
shi wanda ya kafa zuciyarsa gare ka,
domin ya dogara a gare ka.
4 Ku dogara ga Ubangiji,
gama shi Ubangiji, ne madawwamin Dutse.
5 Yakan ƙasƙantar da waɗanda suke zama a bisa
ya kawar da birni mai alfarma ƙasa;
ya rusa ta har ƙasa
ya jefar da ita cikin ƙura.
6 Ƙafafu sukan tattake ta,
ƙafafu waɗanda aka zalunta,
wato, sawun matalauta.
-
16 Har iyayenku, da ’yan’uwanku maza, da danginku, da abokanku ma, duk za su bashe ku, su kuma kashe waɗansunku. 17 Duk mutane za su ƙi ku saboda ni. 18 Amma ko gashi ɗaya na kanku, ba zai hallaka ba. 19 Ta wurin tsayawa da ƙarfi, za ku sami rai.
-
33 “Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin a cikina ku sami salama. A duniyan nan za ku sha wahala. Amma ku yi ƙarfin hali! Na yi nasara a kan duniya.”
-
11 Ba sauran zamana a duniya, amma waɗannan a duniya suke, ni kuwa ina zuwa wurinka. Ya Uba Mai Tsarki, ka kiyaye su ta wurin ikon sunanka, sunan da ka ba ni, don su zama ɗaya kamar yadda muke ɗaya. 12 Yayinda nake tare da su, na kāre su na kuma kiyaye su ta wurin sunan nan da ka ba ni. Ba ko ɗayan da ya ɓace, sai dai wannan da aka ƙaddara zuwa ga hallaka don Nassi yă cika.
-
19 Kada ku yi ramuwa, abokaina, sai dai ku bar wa Allah. Gama a rubuce yake cewa, “Ramuwa tawa ce; zan kuwa sāka,” in ji Ubangiji.
-
13 Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi.
-
8 In wani bai kula da danginsa ba, musamman iyalinsa na kurkusa, ya mūsunta bangaskiya ke nan, ya kuma fi marar ba da gaskiya muni.
-
19 Mun san cewa mu ’ya’yan Allah ne, duniya duka kuwa tana hannun Mugun.
-
32 Gama wane ne Allah, in ba Ubangiji ba?
Wane ne dutse kuma in ba Allahnmu ba?
-
Wani shiggayiyon ta Dawuda, wanda Ya Rera wa Ubangiji game da Kush mutumin Benyamin.
1 Ya Ubangiji Allahna, na zo neman mafaka a wurinka;
ka cece ni ka kuɓutar da ni daga dukan waɗanda suke bi na,
-
9 Ya Allah mai adalci,
wanda yake binciken tunani da zukata,
ka kawo ƙarshen rikicin mugaye
ka kuma sa adalai su zauna lafiya.
-
9 Ubangiji shi ne mafakan waɗanda ake danniya,
mafaka a lokutan wahala.
10 Waɗanda suka san sunanka za su dogara da kai,
gama kai, Ubangiji, ba ka taɓa yashe waɗanda suke nemanka ba.
-
Ta Dawuda.
1 Ubangiji ne haskena da cetona,
wa zan ji tsoro?
Ubangiji ne mafakar raina,
wane ne zan ji tsoro?
-
19 Alherinka da girma yake,
wanda ka ajiye domin waɗanda suke tsoronka,
wanda ka mayar a gaban mutane
a kan waɗanda suke neman mafaka daga gare ka.
-
11 Kada ka hana mini jinƙanka, ya Ubangiji;
bari ƙaunarka da gaskiyarka kullum su kāre ni.
12 Gama damuwoyin da suka wuce misali sun kewaye ni;
zunubaina sun mamaye ni, kuma ba na iya gani.
Sun fi gashin kaina yawa,
har ma na fid da zuciya.
13 Ka ji daɗin cetona, ya Ubangiji;
Ya Ubangiji, ka zo da sauri ka taimake ni.
-
7 Cetona da girmata sun dangana ga Allah ne,
shi ne dutsena mai ƙarfi, mafakata.
8 Ku dogara a gare shi a duk lokuta, ya mutane;
ku faɗi albarkaci bakin zukatanku a gare shi,
gama Allah ne mafakarmu. Sela
-
12 Gama zai ceci masu bukatan da suka yi kuka,
marasa ƙarfin da ba su da mai taimako.
13 Zai ji tausayin gajiyayyu da masu bukata
yă ceci masu bukata daga mutuwa.
14 Zai kuɓutar da su daga danniya da rikici,
gama jininsu yake a gabansa.
-
10 Bari masu ƙaunar Ubangiji su ƙi mugunta,
gama yana tsaron rayukan amintattunsa
yana kuma kuɓutar da su daga hannun mugaye.
-
Waƙar haurawa. Ta Dawuda.
1 Da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu ba,
bari Isra’ila yă ce,
2 da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu ba
sa’ad da aka auka mana,
3 sa’ad da fushinsu ya ƙuna a kanmu,
ai, da sun haɗiye mu da rai;
4 da rigyawa ta kwashe mu,
da ambaliya ta rufe mu.
5 Da ruwa mai hauka
ya share mu ƙaf.
-
7 Yana riƙe da nasara a ma’aji don masu yin gaskiya,
shi ne mafaka ga waɗanda tafiyarsu ba ta da laifi,
8 gama yana tsare abin da masu adalci suke bukata
yana kuma tsare hanyar amintattunsa.
-
5 Yanzu zan faɗa muku
abin da zan yi da gonar inabina.
Zan cire katangar da ta kewaye ta,
za tă kuwa lalace;
zan rushe bangonta,
za a kuwa tattake ta.
6 Zan mai da ita kango,
ba zan aske ta ba, ba kuwa zan nome ta ba,
sarƙaƙƙiya da ƙayayyuwa kuwa za su yi girma a can
Zan umarci gizagizai
kada su yi ruwan sama a kanta.”
7 Gonar inabin Ubangiji Maɗaukaki
ita ce gidan Isra’ila,
mutanen Yahuda kuma
su ne lambun farin cikinsa.
Yana kuma nema ganin gaskiya, amma sai ga zub da jini;
yana neman adalci, amma sai ga shi kukan azaba yake ji.
-
1 “A wannan lokaci Mika’ilu, babban mai mulki wanda yake kāre mutanenka, zai tashi. Za a yi lokacin matsananciyar wahala wanda ba a taɓa yi tun farkon ƙasashe har zuwa yanzu. Amma a lokacin da mutanenka, kowane mutum wanda aka sami sunansa a rubuce a cikin littafin, za a cece shi.
-
13 Kada ka bari a kai mu cikin jarraba,
amma ka cece mu daga mugun nan. ’
-
28 Kada ku ji tsoron masu kashe jiki amma ba sa iya kashe rai. A maimakon haka, ku ji tsoron Wannan wanda yake da iko yă hallaka rai duk da jiki a jahannama ta wuta. 29 Ba akan sayar da kanari biyu kobo ɗaya ba? Duk da haka ba ɗayansu da zai fāɗi ƙasa ba da yardar Ubanku. 30 Kai, ko gashin kanku ma duk an ƙidaya su. 31 Saboda haka kada ku ji tsoro; kun fi kanari masu yawa, daraja nesa.
Shows Read in context, Share and Copy.