101 Bible Verses About Hatred

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Hatred
  1. 18 “In duniya ta ƙi ku, ku san cewa ta fara ƙin na ne. 19 Da ku na duniya ne, da ta ƙaunaci abinta. Kamar yadda yake, ku ba na duniya ba ne, na zaɓe ku daga duniya, shi ya sa duniya take ƙinku. 20 Ku tuna da kalmomin da na yi muku cewa, ‘Ba bawan da ya fi maigidansa,’ In sun tsananta mini, ku ma za su tsananta muku. Da sun yi biyayya da koyarwata, da za su yi biyayya da taku ma. 21 Za su yi muku haka saboda sunana, gama ba su san Wannan da ya aiko ni ba. 22 Da a ce ban zo na yi musu magana ba, da ba su da zunubi. Yanzu kam, ba su da wata hujja a kan zunubinsu. 23 Wanda ya ƙi ni ya ƙi ya ƙi Ubana ma. 24 Da a ce ban yi ayyuka a cikinsu waɗanda babu wani da ya taɓa yi ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu sun ga waɗannan ayyukan banmamaki, duk da haka sun ƙi ni sun kuma ƙi Ubana. 25 Amma wannan ya faru ne domin a cika abin da yake a rubuce cikin Dokarsu cewa, ‘Sun ƙi ni ba dalili.’

  2. 43 “Kun dai ji an faɗa, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka, ka kuma ƙi abokin gābanka.’ 44 Amma ina gaya muku, ku ƙaunaci abokan gābanku kuma ku yi wa waɗanda suke tsananta muku addu’a, 45 don ku zama ’ya’yan Ubanku na sama. Shi yakan sa ranarsa ta haskaka a kan mugaye da masu kirki; yakan kuma sako ruwan sama a bisa masu adalci da marasa adalci. 46 In masoyarku kawai kuke ƙauna, wace lada ce gare ku? Ko masu karɓar haraji ma ba haka suke yi ba? 47 In kuwa kuna gai da ’yan’uwanku ne kaɗai, me kuke yi fiye da waɗansu? Marasa bin Allah ma ba haka suke yi ba? 48 Saboda haka sai ku zama cikakku, yadda Ubanku na sama yake cikakke.

  3. 27 “Amma ina faɗa muku, ku da kuke ji na, ku ƙaunaci abokan gābanku, ku yi wa masu ƙinku alheri. 28 Ku albarkaci waɗanda suke la’anta ku, ku kuma yi wa waɗanda suke wulaƙanta ku addu’a. 29 In wani ya mare ka a wannan kumatu, juya masa ɗayan ma, in wani ya ƙwace maka babban riga, kada ma ka hana masa ’yar cikin ma. 30 Duk wanda ya roƙe ka abu, ka ba shi. In kuma wani ya yi maka ƙwace, kada ka nema yă mayar maka.

  4. 8 Duk mai aikata abin da yake zunubi shi na Iblis ne, domin Iblis mai aikata zunubi ne tun farko. Dalilin da ya sa Ɗan Allah ya bayyana kuwa shi ne don yă rushe aikin Iblis. 9 Babu haifaffe na Allah da zai ci gaba da yin zunubi, domin iri na Allah yana a cikinsa; ba zai iya ci gaba da yin zunubi ba, domin haifaffe ne na Allah. 10 Ta haka muka san waɗanda suke ’ya’yan Allah da kuma waɗanda suke ’ya’yan Iblis. Duk wanda ba ya yin abin da yake daidai, ba ɗan Allah ba ne; haka ma wanda ba ya ƙaunar ɗan’uwansa.

    11 Wannan shi ne saƙon da kuka ji tun farko. Ya kamata mu ƙaunaci juna. 12 Kada ku zama kamar Kayinu, wanda ya zama na mugun nan, ya kuma kashe ɗan’uwansa. Me ya sa ya kashe shi? Domin ayyukansa mugaye ne, na ɗan’uwansa kuma na adalci ne. 13 Kada ku yi mamaki ’yan’uwana, in duniya ta ƙi ku. 14 Mun san cewa mun riga mun ratsa daga mutuwa zuwa rai, domin muna ƙaunar ’yan’uwanmu. Duk wanda ba ya ƙauna matacce ne har yanzu. 15 Duk mai ƙin ɗan’uwansa mai kisankai ne, kun kuma san cewa ba mai kisankan da yake da rai madawwami a cikinsa.

    16 Yadda muka san ƙauna ke nan, wato, Yesu Kiristi ya ba da ransa dominmu. Ya kamata mu ma mu ba da rayukanmu domin ’yan’uwanmu. 17 In wani yana da arziki, ya kuma ga ɗan’uwansa cikin rashi, bai kuwa taimake shi ba, anya, ƙaunar Allah tana a cikinsa kuwa? 18 ’Ya’yana ƙaunatattu, kada mu yi ƙauna da fatar baki kawai, sai dai mu nuna ta ta wurin aikatawa da kuma gaskiya.

  5. 7 Abokaina ƙaunatattu, ba sabon umarni nake rubuta muku ba, a’a, daɗaɗɗen umarnin nan ne, wanda kuke da shi tun farko. Wannan tsohon umarni shi ne saƙon da kuka riga kuka ji. 8 Duk da haka ina rubuta muku sabon umarni; ana ganin gaskiyar umarnin a cikinsa da kuma cikinku, gama duhu yana shuɗewa, haske na gaskiya kuwa yana haskakawa.

    9 Duk wanda ya ce yana cikin haske yana kuma ƙin ɗan’uwansa, ashe a duhu yake har yanzu. 10 Duk wanda yake ƙaunar ɗan’uwansa, a cikin hasken yake rayuwa ke nan, kuma babu wani abin da yake cikinsa da zai sa yă yi tuntuɓe. 11 Amma duk wanda yake ƙin ɗan’uwansa, cikin duhu yake, yana kuma tafiya cikin duhu ke nan; bai ma san inda za shi ba, domin duhun ya makanta shi.

  6. 19 Ayyukan mutuntaka kuwa a fili suke. Wato, fasikanci, ƙazanta da kuma lalata; 20 bautar gumaka da sihiri; ƙiyayya, faɗa, kishi, fushi mai zafi, sonkai, tsattsaguwa, hamayya, 21 da ƙyashi; buguwa, shashanci, da ire-irensu. Na gargaɗe ku, yadda na yi a dā, cewa masu irin wannan rayuwa ba za su gāji mulkin Allah ba.

    22 Amma amfanin da Ruhu yake bayar shi ne ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci, 23 sauƙinkai, da kuma kamunkai. Ai, ba ruwan Doka da waɗannan abubuwa.

  7. 10 Bari masu ƙaunar Ubangiji su ƙi mugunta,

    gama yana tsaron rayukan amintattunsa

    yana kuma kuɓutar da su daga hannun mugaye.

  8. 12 Ƙiyayya kan haddasa wahala,

    amma ƙauna kan rufe dukan laifofi.

  9. 17 Tunaninka suna da daraja gare ni, ya Allah!

    Yawansu ba su da iyaka!

    18 A ce zan iya ƙirgansu,

    za su fi yashin teku yawa.

    Sa’ad da na farka, ina nan tare da kai har yanzu.

    19 Da kawai za ka kashe mugaye, ya Allah!

    Ku rabu da ni, ku masu kisankai!

    20 Suna magana game da kai da mugun nufi;

    maƙiyanka suna ɗaukan sunanka a banza.

    21 Ba ina ƙin masu ƙinka ba, ya Ubangiji,

    ina kuma ƙyamar waɗanda suke tayar maka ba?

    22 Ba ni da wani abu da nake musu sai kiyaye kawai;

    na ɗauke su abokan gābana.

    23 Ka bincike ni, ya Allah ka kuma san zuciyata;

    ka gwada ni ka kuma san damuwata.

    24 Duba ko akwai wani laifi a cikina,

    ka bishe ni a madawwamiyar hanya.

  10. 19 Muna ƙauna, domin ya ƙaunace mu da farko. 20 Duk wanda ya ce, “Ina ƙaunar Allah,” amma yana ƙin ɗan’uwansa, maƙaryaci ne. Gama duk wanda ba ya ƙaunar ɗan’uwansa da yake gani, ba zai iya ƙaunar Allah wanda ba ya gani ba. 21 Ya kuma ba mu wannan umarni cewa duk wanda yake ƙaunar Allah, dole yă ƙaunaci ɗan’uwansa.

  11. 13 Jin tsoron Ubangiji shi ne ƙin mugunta;

    ina ƙin girman kai da fariya,

    halin mugunta da kuma muguwar magana.

  12. 22 Dukan mutane za su ƙi ku saboda ni, amma wanda ya jure har ƙarshe zai sami ceto.

  13. 4 Kai ba Allahn da yake jin daɗin mugu ba ne;

    gama kana gāba da dukan masu aikata mugunta.

    5 Masu fariya ba za su iya tsaya

    a gabanka ba.

    Kana ƙin duk masu aikata abin da ba daidai ba.

    6 Kakan hallaka masu yin ƙarya.

    Masu kisankai da mutane masu ruɗu

    Ubangiji yana ƙyama.

  14. 24 Mai yin ƙiyayya yakan ɓoye kansa da maganar bakinsa,

    amma a cikin zuciyarsa yana cike da munafunci

    25 Ko da jawabinsa ya ɗauki hankali, kada ka gaskata shi,

    gama abubuwa ƙyama guda bakwai sun cika zuciyarsa.

    26 Wataƙila ya ɓoye ƙiyayyarsa da ƙarya,

    duk da haka za a tone muguntarsa a cikin taro.

  15. 16 Akwai abubuwa shida da Ubangiji ya ƙi,

    abubuwa bakwai da suke abin ƙyama gare shi,

    17 duban reni,

    harshe mai ƙarya,

    hannuwa masu zub da jinin marar laifi,

    18 zuciyar da take ƙulla mugayen dabaru,

    ƙafafun da suke sauri zuwa aikata mugunta,

    19 mai shaidar ƙarya wanda yake zuba ƙarairayi,

    da kuma mutumin da yake tā-da-na-zaune-tsaye a cikin ’yan’uwa.

  16. 9 “Sa’an nan za a bashe ku don a tsananta muku a kuma kashe ku, dukan al’ummai za su ƙi ku saboda ni. 10 A wannan lokaci, da yawa za su juya daga bangaskiya, su ci amana su kuma ƙi juna, 11 annabawan ƙarya da yawa za su firfito su kuma ruɗi mutane da yawa. 12 Saboda ƙaruwar mugunta, ƙaunar yawanci za tă yi sanyi, 13 amma duk wanda ya tsaya da ƙarfi har ƙarshe, zai sami ceto.

  17. 26 “Duk wanda yakan zo wurina, amma bai ƙi mahaifinsa da mahaifiyarsa, da matarsa da ’ya’yansa, da ’yan’uwansa mata da maza, kai, har ma ransa ba, ba zai iya zama almajirina ba. 27 Kuma duk wanda ba yakan ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, ba zai iya zama almajirina ba.

  18. 17 “ ‘Kada ka yi ƙiyayyar ɗan’uwanka a zuciya. Ka tsawata wa maƙwabcinka da gaske don kada ka sami rabo cikin laifinsa.

    18 “ ‘Kada ka nemi yin ramuwa, ko ka riƙe wani cikin mutanenka a zuciya, amma ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka. Ni ne Ubangiji.

  19. 3 Ba zan kafa a gaban idanuna 1

    wani abu marar kyau ba.

    Na ƙi jinin ayyukan mutane marasa aminci;

    ba za su manne mini ba.

  20. 104 Na sami ganewa daga farillanka;

    saboda haka ina ƙin kowace hanyar da ba daidai ba.

  21. 19 Dubi yadda abokan gābana sun ƙaru

    da kuma yadda suka ƙara ƙina!

  22. 163 Na ƙi ina kuma ƙyamar ƙarya

    amma ina ƙaunar dokarka.

  23. 17 Gara a ci abincin kayan ganye inda akwai ƙauna

    da a ci kiwotaccen saniya inda ƙiyayya take.

  24. 14 Ku yi nagarta, ba mugunta ba;

    don ku rayu

    sa’an nan Ubangiji Allah Maɗaukaki zai kasance da ku,

    kamar yadda kuka ce zai yi.

    15 Ku ƙi mugunta, ku ƙaunaci nagarta;

    ku dinga yin shari’ar gaskiya a ɗakunan shari’a.

    Mai yiwuwa Ubangiji Allah Maɗaukaki zai ji tausayin

    raguwar Yusuf.

  25. 6 Ba cewa maganar Allah ta kāsa ba ne. Gama ba duk waɗanda suke zuriyar Isra’ila ne suke Isra’ila na gaske ba. 7 Ba kuwa don su zuriyarsa ne dukansu suka zama ’ya’yan Ibrahim ba. A maimako, “Ta wurin Ishaku ne za a lissafta zuriyarka.” 8 Ana iya cewa zaman zuriyar Ibrahim, ba shi ne zama ’ya’yan Allah ba, a’a, zuriya ta alkawarin nan su ne ake lasaftawa zuriyar Ibrahim. 9 Ga yadda aka yi alkawarin nan, “A ƙayyadadden lokaci zan dawo, Saratu kuma za tă haifi ɗa.”

    10 Ba ma haka kaɗai ba, ’ya’yan Rifkatu suna da mahaifi guda ne, wato, mahaifinmu Ishaku. 11 Duk da haka, tun ba a haifi tagwayen nan ba, balle su yi wani abu mai kyau ko marar kyau don nufin Allah bisa ga zaɓensa ya tabbata, ba ga aikin lada ba, sai dai ga kiransa, 12 ba ta wurin ayyuka ba sai dai ta wurin shi wanda ya kira, aka faɗa mata cewa, “Babban zai bauta wa ƙaramin.” 13 Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yaƙub ne na so, amma Isuwa ne na ƙi.”

    14 Me za mu ce ke nan? Allah marar adalci ne? Sam, ko kaɗan! 15 Gama ya ce wa Musa,

    “Zan nuna jinƙai ga wanda zan nuna jinƙai,

    zan kuma ji tausayin wanda zan ji tausayi.”

  26. 3 A wani lokaci can baya mu ma wawaye ne, marasa biyayya, aka ruɗe mu, sha’awace-sha’awace da kwaɗayi iri-iri suka daure mu, muka yi zaman ƙiyayya da kishi, aka ƙi mu, mu kuma muka ƙi juna.

  27. 7 Duniya ba za tă iya ƙinku ba, amma ni take ƙi domin ina shaida cewa ayyukanta mugaye ne.

  28. 6 Sai dai kana da wannan abu mai kyau. Ka ƙi ayyukan Nikolaitawa da ni ma nake ƙi.

  29. 3 Isra’ila dai ya fi ƙaunar Yusuf fiye da kowanne a cikin sauran ’ya’yansa maza, gama an haifa masa shi a cikin tsufansa. Sai ya yi masa riga mai gwanin kyau. 4 Sa’ad da ’yan’uwansa suka ga cewa mahaifinsu ya fi ƙaunarsa fiye da kowanne daga cikinsu, sai suka ƙi jininsa, ba sa kuma maganar alheri da shi.

    5 Sai Yusuf ya yi mafarki, sa’ad da ya faɗa wa ’yan’uwansa, suka ƙara ƙin jininsa. 6 Ya ce musu, “Ku saurari wannan mafarkin da na yi. 7 Muna daurin dammunan hatsi a gona, sai nan da nan damina ya tashi ya tsaya, yayinda dammunanku suka taru kewaye da nawa suka rusuna masa.”

    8 Sai ’yan’uwansa suka ce masa, “Kana nufin za ka yi mulki a kanmu ke nan? Ko kuwa za ka zama sarki, a bisanmu?” Suka ƙara ƙin jininsa saboda mafarkinsa da kuma abin da ya faɗa.

  30. 19 Kada ka bar maƙaryatan nan,

    su yi farin ciki a kaina;

    kada ka bar waɗanda suke ƙina ba dalili,

    su ji daɗin baƙin cikina.

  31. 18 Duk wanda ya ɓoye ƙiyayyarsa yana da ƙarya a leɓunansa,

    duk kuma wanda yake baza ƙarairayi wawa ne.

  32. 28 Da yake ba su yi tunani cewa ya dace su riƙe sanin Allah da suke da shi ba, sai ya yashe su ga tunanin banza da wofi, su aikata abin da bai kamata a yi ba. 29 Sun cika da kowace irin ƙeta, mugunta, kwaɗayi, da tunanin banza da wofi. Suka kuma cika da kishi, kisankai, faɗa, ruɗu, da kuma riƙo a zuci. Su masu gulma ne, 30 da masu ɓata suna, masu ƙin Allah, masu rashin kunya, masu girman kai, masu rigima; sukan ƙaga hanyoyin yin mugunta; suna rashin biyayya ga iyayensu; 31 su marasa hankali ne, marasa bangaskiya, marasa ƙauna, marasa tausayi. 32 Ko da yake sun san dokar adalcin Allah cewa masu aikata irin waɗannan abubuwa sun cancanci mutuwa, duk da haka ba cin gaba da aikata waɗannan abubuwa kaɗai suke yi ba, har ma suna goyon bayan masu yinsu.

  33. 9 Dole ƙauna tă zama ta gaskiya. Ku ƙi duk abin da yake mugu; ku manne wa abin da yake nagari.

  34. 3 Da kalmomin ƙiyayya sun kewaye ni;

    sun tasar mini ba dalili.

    4 A maimakon ƙauna sun sāka mini da zargi,

    amma ni mutum ne mai addu’a.

    5 Sun sāka mini alheri da mugunta,

    ƙauna kuma da ƙiyayya.

  35. 16 “Na ƙi kisan aure,” in ji Ubangiji, Allah na Isra’ila. “Na kuma ƙi mutumin da ya rufe kansa da tashin hankali kamar riga,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.

    Saboda haka sai ka lura da kanka, kada kuma ka ci amana.

  36. 14 Na gaya musu maganarka duniya kuwa ta ƙi su, don su ba na duniya ba ne yadda ni ma ba na duniya ba ne.

  37. 7 Kana ƙaunar abin da yake daidai kana kuma ƙin mugunta;

    saboda haka Allah, Allahnka, ya sa ka a bisa abokanka

    ta wurin shafe ka da man farin ciki.

  38. 128 saboda kuma ina lura da dukan farillanka da kyau,

    na ƙi kowace hanyar da ba daidai ba.

  39. 16 Ku yi zaman lafiya da juna. Kada ku nuna girman kai, sai ma ku riƙa cuɗanya da talakawa. Kada ku zama masu ɗaga kai.

    17 Idan kowa ya yi muku mugunta, kada ku sāka masa da mugunta. Ku lura don ku aikata abin da kowa zai iya gani cewa daidai ne. 18 Ku yi iya ƙoƙarinku, in zai yiwu, ku yi zaman lafiya da kowa. 19 Kada ku yi ramuwa, abokaina, sai dai ku bar wa Allah. Gama a rubuce yake cewa, “Ramuwa tawa ce; zan kuwa sāka,” in ji Ubangiji. 20 A maimakon haka,

    “In abokin gābanka yana jin yunwa, ka ciyar da shi;

    in yana jin ƙishirwa, ka ba shi ruwan sha.

    Ta yin haka, za ka tara garwashin wuta a kansa.”

    21 Kada ku bar mugunta ta sha kanku, sai dai ku sha kan mugunta ta wurin aikata nagarta.

  40. 2 “Na ƙaunace ku, in ji Ubangiji.

    “Amma sai kuka ce, ‘Yaya ka ƙaunace mu?’

    “Isuwa ba ɗan’uwan Yaƙub ba ne?” In ji Ubangiji. “Duk da haka na ƙaunaci Yaƙub, 3 amma na ƙi Isuwa, na kuma mai da ƙasarsa da take kan duwatsu kango, na ba da gādonsa ga dilolin hamada.”

    4 Edom zai iya cewa, “Ko da yake an ragargaza mu, ai, za mu sāke gina kufanmu.”

    Amma ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Za su iya gini, amma zan rushe. Za a ce da su Muguwar Ƙasa, mutane da kullum suke a ƙarƙashi fushin Ubangiji. 5 Za ku ga wannan da idanunku ku kuma ce, ‘Ubangiji da girma yake, har gaba da iyakokin Isra’ila ma!’

  41. 5 Ba za ka durƙusa gare su, ko ka yi musu sujada ba. Gama ni, Ubangiji Allahnka mai kishi ne, nakan hukunta ’ya’ya har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suke ƙina,

  42. 4 Ubangiji yana cikin haikalinsa mai tsarki;

    Ubangiji yana a kursiyinsa a sama.

    Yana kallon ’ya’yan mutane;

    idanunsa suna bincike su.

    5 Ubangiji yana bincike adalai,

    amma ransa yana ƙi mugaye

    da masu son rikici.

    6 A kan mugaye zai zuba

    garwashin wuta mai zafi da kuma kibiritu;

    iska mai zafi zai zama rabonsu.

    7 Gama Ubangiji mai adalci ne,

    yana ƙaunar gaskiya

    masu adalci za su ga fuskarsa.

  43. 10 Masu kisankai sukan ƙi mutum mai mutunci

    su kuma nema su kashe mai aikata gaskiya.

  44. 16 Abubuwan da za ku yi ke nan. Ku gaya wa juna gaskiya, ku kuma dinga yin shari’ar gaskiya a ɗakunanku na shari’arku; 17 kada ku ƙulla wa maƙwabtanku mugunta, kuma kada ku so yin rantsuwa ta ƙarya. Ina ƙyamar waɗannan duka,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.

  45. 19 Hukuncin shi ne, Haske ya zo cikin duniya, amma mutane suka so duhu a maimakon haske domin ayyukansu mugaye ne. 20 Duk mai aikata mugunta yana ƙin haske, ba zai kuwa zo cikin haske ba don yana tsoro kada ayyukansa su tonu. 21 Amma duk mai rayuwa bisa ga gaskiya yakan zo cikin haske, domin a gani a sarari cewa ayyukan da ya yi an yi su ne ta wurin Allah.

  46. 9 Ka ƙaunaci abin da yake daidai, ka kuma ƙi mugunta;

    saboda haka Allah, Allahnka, ya ɗora ka a bisan abokan zamanka,

    ta wurin shafan da ya yi maka da man farin ciki.”

  47. 41 Isuwa ya riƙe Yaƙub a zuciya saboda albarkar da mahaifinsa ya sa masa. Ya ce wa kansa, “Kwanakin mutuwar mahaifina sun yi kusa; sa’an nan zan kashe ɗan’uwana Yaƙub.”

    42 Sa’ad da aka faɗa wa Rebeka abin da babban ɗanta Isuwa ya faɗa, sai ta kira ɗanta Yaƙub ta ce masa, “Ɗan’uwanka Isuwa yana ta’azantar da kansa da tunanin kashe ka. 43 To, fa, ɗana, yi abin da na ce; gudu nan take zuwa wurin ɗan’uwana Laban a Haran. 44 Zauna tare da shi na ɗan lokaci sai ɗan’uwanka ya huce. 45 Sa’ad da ɗan’uwanka ya daina fushi da kai, ya kuma manta da abin da ka yi masa, zan aika don ka dawo daga can. Don me zan rasa ku biyu a rana guda?”

  48. 8 Sarkin Isra’ila ya amsa wa Yehoshafat, ya ce, “Akwai mutum guda har yanzu wanda ta wurinsa za mu iya nemi nufin Ubangiji, amma na ƙi jininsa domin bai taɓa yin annabci wani abu mai kyau game da ni ba, sai dai mummuna kullum. Shi ne Mikahiya ɗan Imla.”

    Yehoshafat ya ce, “Kada sarki ya ce haka.”

  49. 6 Na ƙi waɗanda suke manne wa gumakan banza;

    na dogara ga Ubangiji.

  50. 1 Akwai lokaci domin kowane abu,

    da kuma lokaci domin kowane aiki a duniya.

    2 Lokacin haihuwa da lokacin mutuwa,

    lokacin shuki da lokacin tumɓukewa.

    3 Lokacin kisa da lokacin warkarwa,

    lokacin rushewa da lokacin ginawa.

    4 Lokacin kuka da lokacin dariya,

    lokacin makoki da lokacin rawa.

    5 Lokacin warwatsa duwatsu da lokacin tara su,

    lokacin runguma da lokacin dainawa.

    6 Lokacin nema, da lokacin fid da zuciya,

    lokacin ajiyewa da lokacin zubarwa.

    7 Lokacin yagewa da lokacin ɗinkewa,

    lokacin yin shiru da lokacin magana.

    8 Lokacin ƙauna da lokacin ƙiyayya,

    lokacin yaƙi da lokacin salama.

  51. 4 Ba na zama tare da masu ruɗu,

    ko in yi tarayya da masu riya;

    5 na ƙi jinin taron masu aikata mugunta

    na ƙi in zauna tare da mugaye.

  52. 21 “Na ƙi, ina kuma ƙyamar bukukkuwanku na addini;

    ba na son ganin tarurrukanku.

    22 Ko da kun kawo mini hadayu na ƙonawa da kuma hadayu na hatsi,

    ba zan karɓa ba.

    Ko da kun kawo zaɓaɓɓun hadayu na zumunta,

    ba zan ɗauke su a bakin kome ba.

    23 Ku tashi daga nan da surutan waƙoƙinku!

    Ba zan saurari kaɗe-kaɗe da bushe bushenku ba.

    24 Amma bari gaskiya ta kwararo kamar kogi,

    adalci kuma kamar rafin da ba ya taɓa bushewa!

    25 “Kun kawo mini hadayu da sadakoki

    shekaru arba’in a cikin jeji, ya ku gidan Isra’ila?

    26 Kun ɗaga masujadar sarkinku,

    siffofin gumakanku,

    tauraron allahnku,

    wanda kuka yi wa kanku.

    27 Saboda haka zan tura ku zaman bauta gaba da Damaskus,”

    in ji Ubangiji, wanda sunansa ne Allah Mai Iko.

  53. 68 “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila,

    domin ya zo ya kuma fanshe mutanensa.

    69 Ya tā mana ƙahon ceto

    a gidan bawansa Dawuda

    70 (yadda ya yi magana tun tuni ta wurin annabawansa masu tsarki),

    71 cewa zai cece mu daga abokan gābanmu

    daga kuma hannun dukan waɗanda suke ƙinmu

  54. 7 Yefta ya ce musu, “Ba kun ƙi ni kuka kuma kore ni daga gidan mahaifina ba? Me ya sa kuke zuwa wurina yanzu sa’ad da kuke cikin wahala?”

  55. 2 Yehu mai duba, ɗan Hanani, ya fita don yă tarye shi, ya kuma ce wa sarki, “Ya yi kyau ke nan da ka taimaki mugu ka kuma ƙaunaci waɗanda suke ƙin Ubangiji? Da yake ka yi haka fushin Ubangiji yana a kanka 3 Duk da haka an sami wani abin kirki a wurinka, gama ka kawar da ginshiƙan Ashera a ƙasar, ka kuma sa zuciyarka a kan neman Allah.”

  56. 21 Mugunta zai kashe mugu;

    za a hukunta abokan gāban adalai.

  57. 21 “Kun dai ji an faɗa wa mutanen dā cewa, ‘Kada ka yi kisankai; kuma duk wanda ya yi kisankai za a hukunta shi.’ 22 Amma ina gaya muku, duk wanda ya yi fushi da ɗan’uwansa, za a hukunta shi. Kuma duk wanda ya ce wa ɗan’uwansa ‘Raka,’ za a kai shi gaban Majalisa. Amma duk wanda ya ce, ‘Kai wawa!’ Zai kasance a hatsarin shiga jahannama ta wuta.

    23 “Saboda haka, in kana cikin ba da baikonka a kan bagade, a can kuwa ka tuna cewa ɗan’uwanka yana riƙe da kai a zuci, 24 sai ka bar baikonka a can gaban bagade. Ka je ka shirya tukuna da ɗan’uwanka; sa’an nan ka zo ka ba da baikonka.

    25 “Ka yi hanzari ka shirya al’amura da maƙiyinka wanda yake ƙararka a kotu. Ka yi haka, tun kana tare da shi a kan hanya, in ba haka ba, zai miƙa ka ga alƙali, alƙali kuma yă miƙa ka ga ɗan sanda, mai yiwuwa kuwa a jefa ka a kurkuku. 26 Gaskiya nake gaya maka, ba za ka fita ba, sai ka biya kobo na ƙarshe.

  58. 12 Kashegari, Yahudawa suka ƙulla makirci suka kuma yi rantsuwa cewa ba za su ci ko sha ba sai sun kashe Bulus. 13 Fiye da mutane arba’in ne suka ƙulla wannan makirci. 14 Suka je wajen manyan firistoci da dattawa suka ce, “Mun yi babbar rantsuwa cewa ba za mu ci kome ba sai mun kashe Bulus. 15 Saboda haka, sai ku da Majalisa sai ku roƙi shugaban ƙungiyar sojan yă kawo shi a gabanku kamar kuna so ku ƙara samun cikakken bayani game da zancensa. Mu kuwa muna a shirye mu kashe shi kafin yă iso nan.”

  59. 41 sa’ad da na wasa takobi mai walƙiya

    hannuna kuwa ya cafke shi don yin hukunci,

    zan ɗau fansa a kan abokan gābana

    in sāka wa waɗanda suke ƙina.

  60. 22 Absalom kuwa bai yi wa Amnon wata magana ta alheri ko ta mugunta ba; ya ƙi jinin Amnon domin ya ci mutuncin ƙanuwarsa Tamar.

  61. 5 Adali yana ƙin abin da yake ƙarya,

    amma mugu kan jawo kunya da ƙasƙanci.

  62. 13 Ku daina kawo hadayu marasa amfani!

    Turarenku abin ƙyama ne gare ni.

    Ina ƙin bukukkuwanku na Sabon Wata, da na ranakun Asabbaci, da taronku na addini,

    ba zan iya jure wa mugun taronku ba.

    14 Bukukkuwanku na Sabon Wata da na tsarkakan ranaku

    na ƙi su.

    Sun zama mini kaya;

    na gaji da ɗaukansu.

  63. 8 “Gama ni, Ubangiji, ina ƙaunar adalci;

    na ƙi fashi da aikata laifi.

    Cikin adalcina zan sāka musu

    in kuma yi madawwamin alkawari da su.

  64. 24 “Ba mai iya bauta wa iyayengiji biyu. Ko dai yă ƙi ɗaya, yă ƙaunaci ɗaya, ko kuwa yă yi aminci ga ɗaya, sa’an nan yă rena ɗayan. Ba dama ku bauta wa Allah, ku kuma bauta wa kuɗi gaba ɗaya.”

  65. 3 Sai manyan firistoci da dattawan mutane, suka taru a fadan babban firist, mai suna Kayifas, 4 suka ƙulla shawara su kama Yesu da makirci, su kuma kashe shi.

  66. 13 Dukan mutane za su ƙi ku saboda ni, amma wanda ya tsaya da ƙarfi har ƙarshe, zai sami ceto.

  67. 16 Har iyayenku, da ’yan’uwanku maza, da danginku, da abokanku ma, duk za su bashe ku, su kuma kashe waɗansunku. 17 Duk mutane za su ƙi ku saboda ni. 18 Amma ko gashi ɗaya na kanku, ba zai hallaka ba. 19 Ta wurin tsayawa da ƙarfi, za ku sami rai.

  68. 6 Kun ga, a daidai lokaci, yayinda muke marasa ƙarfi, Kiristi ya mutu saboda waɗanda ba su san Allah ba. 7 Da ƙyar wani yă mutu saboda mai adalci, ko da yake saboda mutumin kirki wani zai iya ƙarfin hali yă mutu. 8 Amma Allah ya nuna mana ƙaunarsa a wannan. Tun muna masu zunubi tukuna, Kiristi ya mutu dominmu.

    9 Da yake yanzu mun sami zama marasa laifi ta wurin jininsa, ashe kuwa za a cece mu daga fushin Allah ta wurinsa! 10 Gama in kuwa, sa’ad da muke abokan gāban Allah, aka sulhunta mu da shi ta wurin mutuwar Ɗansa, ashe, da yake an sulhunta mu, za mu sami ceto ta wurin ransa!

  69. 5 Saboda haka, sai ku fid da duk wani abin da yake kawo sha’awa a zukatanku, fasikanci, ƙazanta, sha’awa, muguwar sha’awa, da kuma kwaɗayi wanda shi ma bautar gumaka ne. 6 Gama fushin Allah zai sauko a kan masu aikata waɗannan. 7 Dā kun yi waɗannan abubuwa, sa’ad da rayuwar tana cikin duniya mai wannan hali. 8 Amma yanzu dole ku raba kanku da dukan ire-iren abubuwan nan. Ku daina fushi, ku daina ƙiyayya da ƙeta. Ku bar ɓatan suna da kuma ƙazamar magana daga leɓunanku. 9 Kada ku yi wa juna ƙarya, da yake kun tuɓe tsohon halinku tare da ayyukansa 10 kun ɗauki sabon halin nan da ake sabuntawa ga sani, bisa ga kamannin Mahaliccinsa. 11 A wannan sabuwar rayuwa babu bambanci ko kai mutumin Al’ummai ne ko mutumin Yahuda, mai kaciya ne ko marar kaciya, baƙo, baƙauye, bawa ne ko ’yantacce, gama Kiristi shi ne kome, kuma yana cikin kome.

  70. 21 Amma ka zaɓi mutane masu iyawa daga dukan mutane, maza masu tsoron Allah, amintattu, masu ƙin rashawa, ka sanya su shugabanni na dubbai, ɗari-ɗari, hamsin-hamsin da goma-goma.

  71. 9 Saboda haka, ku sani cewa Ubangiji Allahnku, shi ne Allah; shi Allah ne mai aminci, yana kiyaye alkawarinsa na ƙauna ga tsararraki dubu na waɗanda suke ƙaunarsa suke kuma kiyaye umarnansa. 10 Amma

    waɗanda suke ƙinsa, a fili yakan sāka musu da hallaka;

    ba zai yi jinkiri yin ramuwa a kan maƙiyinsa ba, zai yi ramuwar a fili.

  72. 31 Ba za ku yi wa Ubangiji Allahnku sujada a hanyar da suke yi ba, gama a cikin yin sujada wa allolinsu, sun yi dukan abubuwan banƙyaman da Ubangiji yake ƙi. Har ma sukan ƙone ’ya’yansu maza da mata a wuta a matsayin hadayu.

  73. 16 Amma ga mugaye, Allah ya ce,

    “Wace dama ce kuke da ita na haddace dokokina

    ko na yin maganar alkawarina a leɓunanku?

    17 Kun ƙi umarnina

    kuka kuma zubar da kalmomina a bayanku

    18 Sa’ad da kuka ga ɓarawo, kukan haɗa kai da shi;

    kukan haɗa kai da mazinata.

    19 Kuna amfani da bakunanku don mugunta

    kuna kuma gyara harshenku don ruɗu.

    20 Kuna ci gaba da magana a kan ɗan’uwanku

    ku kuma yi maganar ƙarya a kan ɗan mahaifinku.

  74. 15 Waɗanda suke ƙin Ubangiji za su fāɗi a gabansa da rawar jiki,

    hukuncinsu kuma zai dawwama har abada.

  75. 28 Harshe mai faɗin ƙarya yana ƙin waɗanda yake ɓata musu rai,

    daɗin baki kuma yakan aikata ɓarna.

  76. 3 Mutane suka rena shi suka ƙi shi,

    mutum ne cike da baƙin ciki, ya kuma saba da wahala.

    Kamar wanda mutane suna ɓuya fuskokinsu daga gare shi

    aka rena shi aka yi banza da shi.

  77. 5 Ku ji maganar Ubangiji,

    ku da kuke rawar jiki ga maganarsa,

    “’Yan’uwanku da suke ƙinku,

    suna kuma ware ku saboda sunana, sun ce,

    ‘Bari a ɗaukaka Ubangiji,

    don mu ga farin cikinku!’

    Duk da haka za su sha kunya.

  78. 15 “Saboda dukan muguntarsu a Gilgal,

    na ƙi su a can.

    Saboda ayyukansu na zunubi,

    zan kore su daga gidana.

    Ba zan ƙara ƙaunace su ba;

    dukan shugabanninsu ’yan tawaye ne.

  79. 31 Ku rabu da kowane irin ɗacin rai, haushi da hasala, faɗa da ɓata suna, ku rabu da kowace irin ƙeta. 32 Ku yi alheri, ku kuma ji tausayin juna, kuna gafarta wa juna, kamar yadda a cikin Kiristi, Allah ya gafarta muku.

  80. 4 Ku mazinata, ba ku san cewa abokantaka da duniya gāba ce da Allah ba? Duk wanda ya zaɓa yă zama abokin duniya ya zama abokin gāban Allah ke nan.

  81. 30 Yaƙub ya kwana da Rahila ita ma, ya kuwa ƙaunaci Rahila fiye da Liyatu. Ya kuma yi wa Laban aiki na ƙarin waɗansu shekaru bakwai.

    31 Sa’ad da Ubangiji ya ga ba a ƙaunar Liyatu, sai ya buɗe mahaifarta, amma Rahila ta zama bakararriya.

  82. 5 In ka ga jakin wani maƙiyinka ya fāɗi a ƙarƙashin kayan da ya ɗauka, kada ka bar shi can, ka yi ƙoƙari ka taimake shi.

  83. 15 Ubangiji zai kiyaye ku daga kowace cuta. Ba zai wahalshe ku da mugayen cututtukan da kuka sani a Masar ba, amma zai aukar wa dukan maƙiyanku.

  84. 19 Da yawa ne masu gāba da ni da ƙarfi;

    waɗanda suke kina ba dalili sun yi yawa.

  85. 7 amma kana ba mu nasara a kan abokan gābanmu,

    ka sa abokan gābanmu suka sha kunya.

  86. 4 Waɗanda suke ƙina ba dalili

    sun fi gashin kaina yawa;

    da yawa ne abokan gābana babu dalili,

    su da suke nema su hallaka ni.

    An tilasta mini in

    mayar da abin da ban sata ba.

  87. 23 Zan murƙushe maƙiyansa a gabansa

    in kashe dukan abokan gābansa.

  88. 29 Da yake sun ƙi sani

    ba su kuwa zaɓi tsoron Ubangiji ba,

    30 da yake ba su karɓi shawarata ba

    suka kuwa yi kunnen ƙashi ga tsawatata,

    31 za su sami sakayyar abubuwan da suka yi

    su kuma ƙoshi da sakayyar makircinsu.

  89. 8 Ubangiji yana ƙyamar hadayar mugaye,

    amma addu’ar masu aikata gaskiya kan sa ya ji daɗi.

    9 Ubangiji yana ƙin hanyar mugaye

    amma yana ƙaunar waɗanda suke neman adalci.

  90. 17 Kada ka cika ziyarar gidan maƙwabcinka

    yawan ganinka zai sa ya ƙi ka.

  91. 9 “ ‘Za ku yi sata da kisa, ku yi zina da rantsuwar ƙarya, kuna ƙone turare wa Ba’al kuna kuma bin waɗansu allolin da ba ku sani ba, 10 sa’an nan ku zo ku tsaya a gabana a wannan gida, wanda ake kira da Sunana, kuna cewa, “An cece mu,” mun dace mu aikata waɗannan abubuwa banƙyama?

  92. 8 Gādona ya zama mini

    kamar zaki a kurmi.

    Yana mini ruri;

    saboda haka na ƙi shi.

  93. 10 Ba ku son mai yin gaskiya a ɗakin shari’a

    kuna ƙin mai faɗar gaskiya.

  94. 14 Gama in kuna yafe wa mutane sa’ad da suka yi muku laifi, Ubanku da yake cikin sama ma zai gafarta muku. 15 Amma in ba kwa yafe wa mutane laifofinsu, Ubanku ma ba zai gafarta muku zunubanku ba.

  95. 22 Ku ji tausayin waɗanda suke shakka; 23 ku cece waɗansu ta wurin fizge su daga wuta. Ga waɗansu kuma ku ji tausayinsu, amma tare da tsoro, har ma ku yi ƙyamar tufafin da suka ɓata da ayyukansu na jiki.

  96. ס Samek

    113 Na ƙi mutane masu baki biyu,

    amma ina ƙauna dokarka.

  97. 14 Mun san cewa doka aba ce ta ruhu; amma ni ba na ruhu ba ne, an sayar da ni a matsayin bawa ga zunubi. 15 Ban gane abin da nake yi ba. Don abin da nakan so yi, ba shi nakan yi ba, sai dai abin da nake ƙi, shi nake yi. 16 In kuma na yi abin da ba na son yi, na yarda da cewa dokar aba ce mai kyau. 17 Kamar dai yadda yake, ba ni kaina nake yinsa ba, sai dai zunubin da yake zaune a cikina ne. 18 Gama na san cewa babu wani abin kirkin da yake zaune a cikina, wato, a mutuntakata. Gama sha’awar yin abu mai kyau kam ina da ita, sai dai ikon yin ne fa babu. 19 Gama abin da nake yi ba shi ne abu mai kyau da nake so in yi ba; a’a, mugun da ba na so in yi, shi ne nake ci gaba da yi.

  98. 22 Ubangiji yana ƙyamar leɓunan masu ƙarya,

    amma yana jin daɗin mutanen da suke masu gaskiya.

  99. 34 Da jin Yesu ya ƙure Sadukiyawa, sai Farisiyawa suka tattaru. 35 Ɗaya daga cikinsu, wani masanin Doka, ya gwada shi da wannan tambaya. 36 “Malam, wace doka ce mafi girma a cikin dokoki?”

    37 Yesu ya amsa ya ce, “ ‘Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka da dukan ranka da kuma dukan hankalinka.’ 38 Wannan, ita ce doka ta fari da kuma mafi girma. 39 Ta biye kuma kamar ta farkon take. ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’ 40 Dukan Doka da Annabawa suna rataya ne a kan waɗannan dokoki biyu.”

  100. 2 Ku sa hankulanku a kan abubuwan sama, ba kan abubuwan duniya ba.

  101. 3 Duk mai wannan bege a cikinsa yakan tsarkake kansa, kamar yadda shi Kiristi yake da tsabta.