41 Bible Verses About Bad Friends
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
33 Kada fa a ruɗe ku, “Ajiyar mugayen abokai yana ɓata hali mai kyau.”
-
12 Umarnina shi ne, Ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku. 13 Babu ƙaunar da ta fi wannan, a ce mutum ya ba da ransa saboda abokansa. 14 Ku abokaina ne, in kun yi abin da na umarta. 15 Ba zan ƙara ce da ku bayi ba, don bawa bai san abin da maigidansa yake yi ba. A maimako in ce da ku abokai, domin na sanar da ku duk abin da na ji daga wurin Ubana. 16 Ba ku kuka zaɓe ni ba, a’a, ni ne na zaɓe ku na kuma naɗa ku ku je ku ba da ’ya’ya-’ya’yan da za su dawwama. Uba kuwa zai ba ku duk abin da kuka roƙa cikin sunana.
-
17 Aboki yakan yi ƙauna a koyaushe,
ɗan’uwa kuma, ai, don ɗaukar nawayar juna ne aka haife shi.
-
24 Kada ka yi abokantaka da mai zafin rai,
kada ka haɗa kai da wanda ba shi da wuya ya yi fushi,
25 in ba haka ba za ka koyi hanyoyinsa
ka kuma sa kanka a tarko.
26 Kada ka zama mai ɗaukar lamuni
ko ka ba da jingina saboda bashi;
27 gama in ka kāsa biya
za a ƙwace gadon da kake kwanciya a kai ma.
-
19 Marmarin da aka cika yana da daɗi ga rai,
amma wawa yana ƙyamar juyewa daga mugunta.
20 Shi da yake tafiya tare da masu hikima yakan ƙaru da hikima,
amma abokin wawaye zai yi fama da lahani.
21 Rashin sa’a kan fafare mai zunubi,
amma wadata ce ladar adali.
-
5 Gara tsawatawar da ake yi a fili
da ƙaunar da ake yi a ɓoye.
6 Za a iya amince da rauni daga aboki,
amma abokin gāba ko da ya sumbace ka kada ka sake da shi!
-
24 Mutum mai abokai masu yawa kan lalace,
amma akwai abokin da yakan manne kurkusa fiye da ɗan’uwa.
-
26 Adali yakan yi hankali a abokantaka,
amma hanyar mugaye kan kai su ga kaucewa.
-
28 Fitinannen mutum yakan zuga tashin hankali,
mai gulma kuma yakan raba abokai na kusa.
29 Mutum mai tā-da-na-zaune-tsaye yakan ruɗi maƙwabcinsa
ya kai shi a hanyar da ba ta da kyau.
-
9 Man shafawa mai ƙanshi da kuma turare kan faranta zuciya,
gaisuwar amini kuma takan fito daga shawarar kirki.
10 Kada ka manta da abokinka da kuma abokin mahaifinka,
kuma kada ka tafi gidan ɗan’uwanka sa’ad da masifa ta same ka,
gara ka je wurin maƙwabci na kusa da ka je wurin ɗan’uwan da yake da nisa.
-
17 Kamar yadda ƙarfe kan wasa ƙarfe
haka mutum kan koyi daga mutum.
-
9 Biyu sun fi ɗaya,
gama suna samun riba mai kyau na aikinsu.
10 In ɗaya ya fāɗi,
abokinsa zai taimake shi yă tashi.
Amma abin tausayi ne ga mutumin da ya fāɗi
ba shi kuma da wanda zai taimake shi yă tashi!
11 In mutum biyu sun kwanta tare, za su ji ɗumin juna.
Amma yaya mutum ɗaya zai ji ɗumi yana shi kaɗai?
12 Ana iya shan ƙarfin mutum ɗaya,
mutum biyu za su iya kāre kansu.
Igiya riɓi uku tana da wuya tsinkawa.
-
9 Duk wanda ya rufe laifi yana inganta ƙauna ne,
amma duk wanda ya yi ta maimaita batu yakan raba abokai na kusa.
-
4 Ku mazinata, ba ku san cewa abokantaka da duniya gāba ce da Allah ba? Duk wanda ya zaɓa yă zama abokin duniya ya zama abokin gāban Allah ke nan.
-
12 Da a ce abokin gāba ne ke zagina,
da na jure da shi;
da a ce maƙiyi yana tā da kansa a kaina,
da na ɓoye daga gare shi.
13 Amma kai ne, mutum kamar ni,
abokina, abokina na kurkusa,
14 wanda na taɓa jin daɗin zumunci da shi sosai
yayinda muke tafiya tare
a taron jama’a a gidan Allah.
-
6 Mai ba’a kan nemi hikima amma ba ya samun kome,
amma sani kan zo a sawwaƙe ga mai basira.
7 Ka guji wawa,
gama ba za ka sami sani a leɓunansa ba.
-
5 Abokan gābana suna muguwar magana a kaina cewa,
“Yaushe zai mutu sunansa yă ɓace ne?”
6 Duk sa’ad da wani ya zo ganina,
yakan yi maganar ƙarya, yayinda zuciyarsa tana tattare da cin zarafi;
sa’an nan yă fita yă yi ta bazawa ko’ina.
7 Dukan abokan gābana suna raɗa tare a kaina;
suna fata mugun abu ya same ni, suna cewa,
8 “Mugun ciwo ya kama shi;
ba zai taɓa tashi daga inda yake kwanciya ba.”
9 Har abokina na kurkusa,
wanda na amince da shi,
wanda muke cin abinci tare,
ya juya yana gāba da ni.
-
20 Abokina ya kai wa abokansa hari;
ya tā da alkawarinsa.
21 Maganarsa tana da laushi kamar man zaitun,
duk da haka yaƙi yana a cikin zuciyarsa;
kalmominsa sun fi mai sulɓi,
duk da haka takuba ne zārarru.
-
16 A lokacin da na kāre kaina da farko, ba wanda ya goyi bayana, sai ma kowa ya yashe ni. Ina fata ba za a lasafta wannan laifi a kansu ba.
-
5 Kada ka yarda da maƙwabci;
kada ka sa begenka ga abokai.
Ko ma wadda take kwance a ƙirjinka,
ka yi hankali da kalmominka.
6 Gama ɗa yakan ce wannan ba mahaifinsa ba ne,
diya kuma takan tayar wa mahaifiyarta,
matar ɗa takan yi gāba da uwar mijinta,
abokan gāban mutum su ne iyalin cikin gidansa.
-
16 Yanzu na zama abokin gābanku don na faɗa muku gaskiya ke nan?
17 Waɗancan mutane suna neman su rinjaye ku da ƙwazo, amma ba da kyakkyawar aniya ba. Abin da suke so shi ne su raba ku da mu, saboda ƙwazonku yă koma gare su. 18 Yana da kyau ku kasance da irin wannan niyya idan da nufi mai kyau ne, ku kuma kasance a haka koyaushe ba sai ina tare da ku ba. 19 Ya ku ’ya’yana ƙaunatattu, ina sāke shan wahalar naƙudarku, har sai Kiristi ya kahu a cikinku. 20 Da ma a ce ina tare da ku yanzu in canja muryata mana! Gama na damu ƙwarai saboda ku!
-
10 gama Demas, saboda ƙaunar wannan duniya, ya yashe ni ya tafi Tessalonika. Kirssens ya tafi Galatiya, Titus kuwa ya tafi Dalmatiya.
-
16 Yadda muka san ƙauna ke nan, wato, Yesu Kiristi ya ba da ransa dominmu. Ya kamata mu ma mu ba da rayukanmu domin ’yan’uwanmu. 17 In wani yana da arziki, ya kuma ga ɗan’uwansa cikin rashi, bai kuwa taimake shi ba, anya, ƙaunar Allah tana a cikinsa kuwa? 18 ’Ya’yana ƙaunatattu, kada mu yi ƙauna da fatar baki kawai, sai dai mu nuna ta ta wurin aikatawa da kuma gaskiya.
-
6 In ɗan’uwanka, ko ɗanka, ko ’yarka, ko matar da kake ƙauna, ko abokinka na kusa, a ɓoye ya ruɗe ka, yana cewa, “Mu je mu yi wa waɗansu alloli sujada” (allolin da ko kai, ko kakanninka ba su sani ba, 7 allolin mutanen kewayenku, ko na kusa, ko na nisa, daga wannan ƙarshen ƙasar zuwa wancan), 8 kada ka yarda da shi, kada ma ka saurare shi. Kada ka ji tausayinsa. Kada ka haƙura da shi, ko ka tsare shi. 9 Dole ka kashe shi. Dole hannunka yă zama na farko a kisansa, sa’an nan hannuwan sauran dukan mutane. 10 Ku jajjefe shi da duwatsu har sai ya mutu, domin ya yi ƙoƙari yă juye ku daga Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar, daga ƙasar bauta kuma. 11 Sa’an nan dukan Isra’ila za su ji su kuma tsorata, babu kuma wani a cikinku da zai ƙara yin irin wannan mugun abu.
-
11 Lokacin da abokan Ayuba su uku wato, Elifaz mutumin Teman, Bildad mutumin Shuwa, da Zofar mutumin Na’ama suka ji wahalar da ta auka wa Ayuba, sai suka shirya suka bar gidajensu suka je don su ta’azantar da shi. 12 Sa’ad da suka gan shi daga nesa, da ƙyar suka gane shi; sai suka fara kuka da ƙarfi, suka yayyaga tufafinsu suka zuba toka a kawunansu, 13 sai suka zauna da shi a ƙasa har kwana bakwai. Ba wanda ya ce masa kome, don sun ga tsananin wahalar da yake ciki.
-
29 In idonka na dama yana sa ka yin zunubi, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta. 30 In kuma hannunka na dama yana sa ka yin zunubi, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta.
-
14 “Duk wanda ya ƙi yă yi alheri ga aboki
ya rabu ta tsoron Maɗaukaki.
15 Amma ’yan’uwana sun nuna ba zan iya dogara gare su ba,
kamar rafin da yakan bushe da rani,
16 kamar rafin da yakan cika a lokacin ƙanƙara,
yă kuma kumbura kamar ƙanƙarar da ta narke,
17 amma da rani sai yă bushe,
lokacin zafi ba a samun ruwa yana gudu a wurin.
-
19 Duk abokaina sun yashe ni;
waɗanda nake ƙauna sun zama ba sa ƙaunata.
-
Gargaɗi don a rungumi hikima
8 Ɗana, ka saurari umarnin mahaifinka
kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.
9 Za su zama kayan ado don su inganta ka
da kuma sarƙar wuya don su yi wa wuyanka ado.
10 Ɗana, in masu zunubi sun jarabce ka,
kada ka yarda.
11 In suka ce, “Zo mu tafi;
mu yi kwanton ɓauna, mu nemi wani mu kashe,
mu fāɗa wa marasa laifi;
12 mu haɗiye su da rai gaba ɗaya kamar kabari,
kamar waɗanda suke gangarawa zuwa rami;
13 za mu sami dukiya masu daraja iri-iri,
mu kuma cika gidajenmu da ganima;
14 ka haɗa kai da mu,
za mu kuwa raba abin da muka sato”
-
1 Da ma kaina maɓulɓulan ruwa ne
idanuna kuma maɓulɓulan hawaye!
Da sai in yi kuka dare da rana
saboda mutanena da aka kashe.
2 Da ma a hamada
ina da wurin da matafiye za su sauka,
don in bar mutanena
in tafi in bar su;
gama dukansu mazinata ne,
taron mutane marasa aminci.
3 “Sun tanƙwasa harshensu
kamar baka, don su harba ƙarya;
ba da gaskiya ba ne
suke nasara a cikin ƙasar.
Sukan tashi daga wannan zunubi zuwa wancan;
ba su san ni ba,”
in ji Ubangiji.
4 “Ka yi hankali da abokanka;
kada ka amince da ’yan’uwanka.
Gama kowane ɗan’uwa munafuki ne,
kowane aboki kuma mai kushe ne.
5 Aboki kan ruɗi aboki,
ba mai faɗar gaskiya.
Sun koya wa harshensu faɗar ƙarya;
sun gajiyar da kansu da yin zunubi.
-
14 Sai ɗaya daga cikin Sha Biyun nan, wanda ake kira Yahuda Iskariyot, ya je wurin manyan firistoci 15 ya ce, “Me za ku ba ni, in na bashe shi gare ku?” Sai suka ƙirga masa kuɗi azurfa talatin. 16 Daga wannan lokaci, Yahuda ya yi ta neman zarafin da zai miƙa shi.
-
11 Yanzu dai ina rubuta muku cewa kada ku haɗa kai da duk mai kiran kansa ɗan’uwa, amma yana fasikanci, ko kwaɗayi, ko bautar gumaka, ko ɓata suna, ko mashayi, ko mazambaci. Kada ku ko ci abinci da irin wannan mutum. 12 Me zai kai yin hukunci ga waɗanda ba ’yan ikkilisiya ba. Ai, waɗanda suke ’yan ikkilisiya ne za ku hukunta.
-
29 Kada wata ƙazamar magana ta fita daga bakunanku, sai dai abin da yake da amfani don gina waɗansu bisa ga bukatunsu. Ta haka maganarku za tă zama da amfani ga masu jinta. 30 Kada kuma ku ɓata wa Ruhu Mai Tsarki na Allah rai, wanda da shi aka hatimce ku da shi don ranar fansa. 31 Ku rabu da kowane irin ɗacin rai, haushi da hasala, faɗa da ɓata suna, ku rabu da kowace irin ƙeta. 32 Ku yi alheri, ku kuma ji tausayin juna, kuna gafarta wa juna, kamar yadda a cikin Kiristi, Allah ya gafarta muku.
-
LITTAFI NA ƊAYA
1 Mai farin ciki ne mutumin
da ba ya aiki da shawarar mugaye
ko yă yi abin da masu zunubi suke yi
ko yă zauna tare da masu yin ba’a.
2 Amma yana jin daɗin bin dokar Ubangiji,
kuma yana ta nazarinta dare da rana.
3 Yana kama da itacen da aka shuka kusa da maɓulɓulan ruwa,
wanda yake ba da amfani a daidai lokaci
wanda kuma ganyensa ba sa bushewa.
Duk abin da yake yi, yakan yi nasara.
4 Ba haka yake da mugaye ba!
Su kamar yayi ne
da iska take kwashewa.
-
11 Abokaina da maƙwabtana sun guje ni saboda miyakuna;
maƙwabtana ba sa zuwa kusa.
-
6 Ku bar hanyoyinku marasa hankali za ku kuwa rayu;
yi tafiya a hanyar fahimi.
-
4 Wadata kan kawo abokai da yawa,
amma abokin matalauci kan bar shi.
-
16 Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami. 17 Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yă yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin yă ceci duniya ta wurinsa.
-
13 Ba jarrabar da ta taɓa samunku, wadda ba a saba yi wa mutum ba. Allah mai aminci ne; ba zai bari a jarrabce ku fiye da ƙarfinku ba. Amma in aka jarrabce ku, zai nuna muku mafita, domin ku iya cin nasara.
-
7 Kada a ruɗe ku. Ba a yi wa Allah ba’a. Mutum yakan girbe abin da ya shuka ne.
-
6 Kada wani yă ruɗe ku da kalmomin wofi, gama saboda waɗannan abubuwa ne fushin Allah yake zuwa a kan marasa biyayya.
Shows Read in context, Share and Copy.