23 Bible Verses About Summer

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Summer
  1. 22 “Muddin duniya tana nan,

    lokacin shuki da na girbi,

    lokacin sanyi da na zafi,

    lokacin damina da na rani,

    dare da rana

    ba za su daina ba.”

  2. 5 Shi da ya tattara hatsi da rani ɗa ne mai hikima,

    amma shi da yakan yi barci a lokacin girbi ɗa ne wanda ya zama abin kunya.

  3. 12 Amma kai, ya Allah, kai ne sarki tun da daɗewa;

    ka kawo ceto a kan duniya.

    13 Kai ne ka raba teku ta wurin ikonka;

    ka farfashe kawunan dodo a cikin ruwaye.

    14 Kai ne ka murƙushe kawunan dodon ruwa

    ka kuma ba da shi yă zama abinci ga halittun hamada.

    15 Kai ne ka bubbuɗe maɓulɓulai da rafuffuka;

    ka busar da koguna masu ruwa.

    16 Yini naka ne, dare kuma naka ne;

    ka kafa rana da wata.

    17 Kai ne ka kafa dukan iyakokin duniya;

    ka yi rani da damina.

  4. 6 Ku tafi wurin kyashi, ku ragwaye;

    ku lura da hanyoyinsa ku zama masu hikima!

    7 Ba shi da jagora

    ba shugaba ko mai mulki,

    8 duk da haka yakan yi tanade-tanadensa da rani

    ya kuma tattara abincinsa a lokacin girbi.

  5. 32 “Yanzu fa, sai ku koyi wannan darasi daga itacen ɓaure. Da zarar rassansa suka yi taushi ganyayensa kuma suka toho, kun san damina ta kusa. 33 Haka kuma, sa’ad da kun ga dukan waɗannan abubuwa, ku sani ya yi kusan zuwa, yana ma dab da bakin ƙofa.

  6. 18 Ya mai ta’aziyyata a cikin baƙin ciki,

    zuciyata ta ɓaci ƙwarai.

    19 Ka saurari kukan mutanena

    daga ƙasa mai nisa suna cewa,

    “Ubangiji ba ya a Sihiyona ne?

    Sarkinta ba ya can ne kuma?”

    “Me ya sa suka tsokane ni da gumakansu har na yi fushi,

    da baƙin gumakansu marasa amfani?”

    20 “Girbi ya wuce,

    damuna ta ƙare,

    ba a kuwa cece mu ba.”

    21 Da yake an ragargazar da mutanena, an ragargaza ni ke nan;

    na yi kuka, tsoro ya kama ni.

    22 Ba magani ne a Gileyad?

    Ba likita ne a can?

    To, me ya sa ba warkarwa

    wa raunin mutanena?

  7. 25 Kyashi halittu ne da ba su da ƙarfi sosai,

    duk da haka suna ajiyar abincinsu da rani;

  8. 29 Sai ya gaya musu wannan misali ya ce, “Ku dubi itacen ɓaure da dukan itatuwa. 30 A duk lokacin da sun fara fitar da ganye, za ku gani da kanku, ku san cewa, damina ta yi kusa. 31 Haka ma, in kuka ga waɗannan abubuwa suna faruwa, ku sani mulkin Allah ya yi kusa.

  9. 1 Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya nuna mini. Ubangiji ya nuna mini kwandon nunannun ’ya’yan itace. 2 Ya yi tambaya ya ce, “Me ka gani Amos?”

    Sai na amsa na ce, “Kwandon nunannun ’ya’yan itace.”

    Sai Ubangiji ya ce mini, “Lokaci ya yi wa mutanena Isra’ila da ba zan ƙara barinsu ba.

    3 “A ranan nan,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka, “Waƙoƙin a haikali za su koma makoki. Za a ga gawawwaki a ko’ina! Shiru!”

    4 Ku ji wannan, ku da kuke tattake masu bukata

    kuka kori matalautan ƙasar.

    5 Kuna cewa,

    “Yaushe Sabon Wata zai wuce

    don mu sayar da hatsi,

    Asabbaci ta wuce,

    don mu sayar da alkama?”

    Mu yi awo da ma’aunin zalunci

    mu ƙara kuɗin kaya

    mu kuma cutar da mai saya,

    6 mu sayi matalauta da azurfa

    masu bukata kuma da takalmi,

    mu sayar da alkamar haɗe da yayi.

  10. 1 Tawa ta ƙare!

    Ina kama da wanda yake tattara ’ya’yan itatuwa

    a lokacin kalar ’ya’yan inabi;

    babu sauran nonon inabin da za a tsinka a ci,

    babu kuma ’ya’yan ɓaure na farko-farkon da raina yake marmari.

  11. 1 Kamar ƙanƙara a rani ko ruwan sama a lokacin girbi,

    haka girmamawa bai dace da wawa ba.

  12. 15 Zan rushe gidan rani

    da na damina;

    gidajen da aka yi musu ado da hauren giwa za a rushe su

    haka ma duk za a rurrushe manyan gidaje,”

    in ji Ubangiji.

  13. 28 “To, sai ku yi koyi da itacen ɓaure. Da zarar rassansa suka yi taushi, ganyayensa kuma suka toho, kun san cewa damina ta yi kusa ke nan. 29 Haka ma, in kuka ga waɗannan abubuwa suna faruwa, ku san cewa ya yi kusan zuwa, yana ma dab da bakin ƙofa.

  14. 35 Sai ƙarfen da yambun da tagulla da azurfan da kuma zinariyan suka ragargaje a lokaci ɗaya ya zama kamar ƙaiƙayi a masussuka a lokacin kaka. Sai iska ta kwashe su ta tafi, har ba a iya ganin ko alamarsu. Amma dutsen da ya fāɗo a siffar ya girke ya zama tsauni ya kuma cika dukan duniya.

  15. 4 Wannan fure mai yanƙwanewa, darajarar kyansa,

    da aka sa a kan kwari mai ba da amfani,

    zai zama kamar ’ya’yan ɓaure, nunan fari,

    da zarar wani ya gani ya kuma tsinka,

    zai haɗiye shi.

  16. 8 Za su zama kamar itacen da aka dasa kusa da ruwa

    wanda ya miƙa saiwoyinsa zuwa cikin rafi.

    Ba ya jin tsoro sa’ad da zafi ya zo;

    ganyayensa kullum kore suke.

    Ba shi da damuwa a shekarar fări

    ba ya taɓa fasa ba da ’ya’ya.”

  17. 6 Duk za a bar su wa tsuntsayen dutse su ci

    da kuma namun jeji;

    tsuntsaye kuma za su ci rani a kansu,

    namun jeji kuma za su yi damina a kansu.

  18. 14 “Duk wanda ya ƙi yă yi alheri ga aboki

    ya rabu ta tsoron Maɗaukaki.

    15 Amma ’yan’uwana sun nuna ba zan iya dogara gare su ba,

    kamar rafin da yakan bushe da rani,

    16 kamar rafin da yakan cika a lokacin ƙanƙara,

    yă kuma kumbura kamar ƙanƙarar da ta narke,

    17 amma da rani sai yă bushe,

    lokacin zafi ba a samun ruwa yana gudu a wurin.

  19. 4 Gama dare da rana

    hannunka yana da nauyi a kaina;

    an shanye ƙarfina ƙaf

    sai ka ce a zafin bazara. Sela

  20. 4 Ga abin da Ubangiji ya faɗa mini,

    “Zan yi shiru in kuma duba a hankali daga mazaunina,

    kamar ƙuna mai zafi a hasken rana,

    kamar girgijen raba a lokacin girbi.”

  21. 17 Kowane abu mai kyau da kuma kowace cikakkiyar kyauta daga sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.

  22. 10 Ni kaina zan zauna a Mizfa in zama wakilinku a gaban Babiloniyawa waɗanda za su zo wurinmu, amma ku girbe ruwan inabi, ’ya’yan itatuwa na kaka, da mai, ku zuba su a tulunan ajiyarku, ku kuma zauna a garuruwan da kuka ci.”

    11 Sa’ad da dukan Yahudawan da suke a Mowab, Ammon, Edom da sauran ƙasashe suka ji cewa sarkin Babilon ya bar raguwa a Yahuda ya kuma naɗa Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan gwamna a kansu, 12 sai suka dawo ƙasar Yahuda, wurin Gedaliya a Mizfa, daga dukan ƙasashen da suke a warwatse. Suka girbe ruwan inabi a yalwace da ’ya’yan itatuwan kaka.

  23. 8 A ranan nan ruwan rai zai kwararo daga Urushalima, rabi zai gangara gabas zuwa teku rabi kuma zai gangara yamma zuwa Bahar Rum, a damina da rani.