82 Bible Verses About Light

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Light
  1. 1 Tun farar farawa akwai Kalma, Kalman kuwa yana nan tare da Allah, Kalman kuwa Allah ne. 2 Yana nan tare da Allah tun farar farawa. 3 Ta wurin Kalman ne aka halicci dukan abubuwa. In ba tare da shi ba, babu abin da aka yi wanda aka yi. 4 A cikinsa rai ya kasance, wannan rai kuwa shi ne hasken mutane. 5 Hasken yana haskakawa cikin duhu, amma duhun bai rinjaye shi ba.

    6 Akwai wani mutumin da aka aiko daga Allah; mai suna Yohanna. 7 Ya zo a matsayin mai shaida domin yă ba da shaida game da wannan haske, don ta wurinsa dukan mutane su ba da gaskiya. 8 Shi kansa ba shi ne hasken ba; sai dai ya zo a matsayin shaida ne kaɗai ga hasken.

    9 Haske na gaskiya da yake ba da haske ga kowane mutum mai shigowa duniya. 10 Yana a duniya, kuma ko da yake an yi duniya ta wurinsa ne, duniya ba tă gane shi ba. 11 Ya zo wurin abin da yake nasa, amma nasa ɗin ba su karɓe shi ba. 12 Duk da haka dukan waɗanda suka karɓe shi, ga waɗanda suka gaskata a sunansa, ya ba su iko su zama ’ya’yan Allah 13 ’ya’yan da aka haifa ba bisa hanyar ’yan adam, ko shawarar mutum ko nufin namiji ba, sai dai haifaffu bisa ga nufin Allah.

    14 Kalman ya zama mutum, ya kuwa zauna a cikinmu. Muka ga ɗaukakarsa, ɗaukaka ta wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaici, wanda ya zo daga wurin Uba, cike da alheri da gaskiya.

  2. 13 “Ku ne gishirin duniya, amma in gishiri ya rabu da daɗin ɗanɗanonsa, yaya za a sāke mai da daɗin ɗanɗanonsa? Ba shi da sauran amfani, sai dai a zubar da shi mutane kuma su tattaka.

    14 “Ku ne hasken duniya. Birnin da yake a bisan tudu ba ya ɓoyuwa. 15 Mutane ba sa ƙuna fitila su rufe ta da murfi. A maimako, sukan ajiye ta a kan wurin ajiye fitila, takan kuma ba da haske ga kowa a cikin gida. 16 Haka ma, bari haskenku yă haskaka a gaban mutane, domin su ga ayyukanku masu kyau, su kuwa yabi Ubanku da yake cikin sama.

  3. 8 Gama a dā zukatanku sun cika da duhu, amma yanzu ku haske ne a cikin Ubangiji. Ku yi rayuwa kamar ’ya’yan haske 9 (domin amfanin haske ya ƙunshi nagarta, adalci, da kuma gaskiya) 10 ku nemi abin da zai gamshi Ubangiji. 11 Ku yi nesa da ayyukan duhun da mutane suke yi, a maimakon haka, ku tona su. 12 Gama abin kunya ne a ma faɗi abubuwan da marasa biyayya suke yi a ɓoye. 13 Duk abin da aka kawo a gaban haske ana iya ganinsa, kuma duk abin da aka haskaka yakan zama haske. 14 Shi ya sa aka ce,

    “Ka farka, ya kai mai barci,

    ka tashi daga matattu,

    Kiristi kuwa zai haskaka ka.”

  4. 5 Wannan shi ne saƙon da muka ji daga wurinsa, muna kuma sanar da ku cewa Allah haske ne; a cikinsa kuwa babu duhu ko kaɗan. 6 In muka ce muna zumunci da shi amma muna tafiya cikin duhu, ƙarya muke yi, kuma ba ma rayuwa bisa ga gaskiya. 7 Amma in muna tafiya cikin haske, yadda yake cikin haske, muna da zumunci da juna ke nan, kuma jinin Yesu, Ɗansa, yana tsarkake mu daga dukan zunubi.

    8 In muka ce ba mu da zunubi, muna ruɗin kanmu ne, gaskiya kuwa ba ta cikinmu. 9 In muka furta zunubanmu, shi mai aminci ne, mai adalci kuma, zai gafarta mana zunubanmu, yă kuma tsarkake mu daga dukan rashin adalci. 10 In muka ce ba mu yi zunubi ba, mun mai da shi maƙaryaci ke nan, maganarsa kuwa ba ta da wuri a cikinmu.

  5. 12 Sa’ad da Yesu ya sāke magana da mutanen, sai ya ce, “Ni ne hasken duniya. Duk wanda ya bi ni ba zai yi tafiya cikin duhu ba, sai dai yă sami hasken rayuwa.”

  6. 1 A farko-farko, Allah ya halicci sama da ƙasa. 2 To, ƙasa dai ba ta da siffa, babu kuma kome a cikinta, duhu ne kawai ya rufe ko’ina, Ruhun Allah kuwa yana yawo a kan ruwan.

    3 Sai Allah ya ce, “Bari haske yă kasance,” sai kuwa ga haske. 4 Allah ya ga hasken yana da kyau, sai ya raba tsakanin hasken da duhu. 5 Allah ya kira hasken “yini,” ya kuma kira duhun “dare.” Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta fari ke nan.

  7. 16 Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami. 17 Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yă yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin yă ceci duniya ta wurinsa. 18 Duk wanda ya gaskata da shi ba za a yi masa hukunci ba, amma duk wanda bai gaskata ba an riga an yi masa hukunci domin bai gaskata da sunan wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗan Allah ba. 19 Hukuncin shi ne, Haske ya zo cikin duniya, amma mutane suka so duhu a maimakon haske domin ayyukansu mugaye ne. 20 Duk mai aikata mugunta yana ƙin haske, ba zai kuwa zo cikin haske ba don yana tsoro kada ayyukansa su tonu. 21 Amma duk mai rayuwa bisa ga gaskiya yakan zo cikin haske, domin a gani a sarari cewa ayyukan da ya yi an yi su ne ta wurin Allah.

  8. נ Nun

    105 Maganarka fitila ce ga ƙafafuna

    haske kuma a kan hanyata.

  9. 3 Ko da bishararmu a rufe take, tana a rufe ne ga waɗanda suke hallaka. 4 Allahn zamanin nan ya makanta hankulan marasa ba da gaskiya, yadda har ba za su iya ganin hasken bishara ta ɗaukakar Kiristi ba, wanda yake kamannin Allah. 5 Gama ba wa’azin kanmu muke yi ba, sai dai na Yesu Kiristi, a kan shi ne Ubangiji, mu kuma bayinku saboda Yesu. 6 Domin shi Allah wanda ya ce, “Bari haske yă haskaka daga duhu,” ya sa haskensa ya haskaka a cikin zukatanmu, don yă ba mu hasken sanin ɗaukakar Allah a fuskar Kiristi.

    7 Amma muna da wannan dukiya a cikin tulunan yumɓu, don a nuna wannan mafificin ikon nan daga Allah ne, ba daga gare mu ba.

  10. 14 Ku yi kome ba tare da gunaguni ko gardama ba, 15 don ku zama marasa abin zargi, sahihai ’ya’yan Allah, waɗanda ba su da laifi, a zamanin mutane karkatattu, kangararru, waɗanda kuke haskakawa a cikinsu kamar fitilu a duniya 16 kuna kuwa cin gaba da riƙe maganar rai domin in yi taƙama a ranar Kiristi cewa ban yi gudu ko fama a banza ba.

  11. 9 Amma ku zaɓaɓɓu ne, ƙungiyar firistocin babban Sarki, al’umma mai tsarki, jama’a mallakar Allah, domin ku shaida yabon shi wanda ya kira ku daga cikin duhu zuwa haskensa mai banmamaki.

  12. Ta Dawuda.

    1 Ubangiji ne haskena da cetona,

    wa zan ji tsoro?

    Ubangiji ne mafakar raina,

    wane ne zan ji tsoro?

    2 Sa’ad da mugaye suka tasar mini

    don su cinye ni,

    sa’ad da abokan gābana da maƙiyina suka kawo mini hari,

    sun yi tuntuɓe suka fāɗi.

  13. 35 Sai Yesu ya ce musu, “Haske zai kasance da ku na ɗan lokaci. Ku yi tafiya yayinda hasken yana nan tare da ku, kada duhu yă cim muku. Mai tafiya a cikin duhu bai san inda za shi ba. 36 Ku dogara ga hasken yayinda kuke da shi, don ku zama ’ya’yan haske.” Da Yesu ya gama magana, sai ya tafi ya ɓuya daga gare su.

    37 Ko bayan Yesu ya yi dukan waɗannan abubuwan banmamaki a gabansu, duk da haka ba su gaskata da shi ba.

  14. 19 Rana ba za tă ƙara zama haskenki a yini ba,

    balle hasken wata ya haskaka a kanki,

    gama Ubangiji zai zama madawwamin haskenki,

    Allahnki kuma zai zama ɗaukakarki.

    20 Ranarki ba za tă ƙara fāɗuwa ba

    watanki kuma ba zai ƙara shuɗewa ba;

    Ubangiji zai zama madawwamin haskenki,

    kwanakin baƙin cikinki za su ƙare.

  15. 1 “Ki tashi, ki haskaka, gama haskenki ya zo,

    ɗaukakar Ubangiji ya taso a kanki.

    2 Duba, duhu ya rufe duniya

    duhu mai kauri kuma yana bisa mutane,

    amma Ubangiji ya taso a kanki

    ɗaukakarsa kuma ya bayyana a bisanki.

    3 Al’ummai za su zo wurin haskenki,

    sarakuna kuma zuwa asubahin sabon yininki.

    4 “Ki ɗaga idanunki ki duba kewaye da ke.

    Duka sun tattaru suka kuma zo wurinki;

    ’ya’yanki maza daga nesa,

    ana kuma ɗaukan ’ya’yanki mata a hannu.

    5 Sa’an nan za ki duba ki kuma haskaka

    zuciyarki zai motsa ya kuma cika da farin ciki;

    za a kawo miki wadata daga tekuna,

    za a kawo miki arzikin al’ummai.

  16. 11 Ku yi wannan domin kun san irin zamanin da kuke ciki. Lokaci ya yi da za ku farka daga barcinku, don cetonmu ya yi kusa yanzu fiye da lokacin da muka fara ba da gaskiya. 12 Dare fa ya kusan ƙarewa; gari kuma yana gab da wayewa. Saboda haka bari mu kawar da ayyukan duhu mu kuma yafa kayan yaƙi na haske. 13 Bari mu tafiyar da al’amuranmu yadda ya dace a yi da rana, ba a cikin shashanci da buguwa ba, ba cikin fasikanci da rashin kunya ba, ba kuma cikin faɗa da kishi ba. 14 A maimakon haka, ku ɗauki halin Ubangiji Yesu Kiristi, kada kuma ku yi tunani game da yadda za ku gamsar da sha’awace-sha’awacen mutuntaka.

  17. 17 Kowane abu mai kyau da kuma kowace cikakkiyar kyauta daga sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.

  18. 1 To, ’yan’uwa, game da lokuta da ranaku, ba ma bukata mu rubuta muku, 2 gama kun sani sarai cewa ranar Ubangiji za tă zo kamar ɓarawo da dare. 3 Yayinda mutane suke cewa, “Akwai salama da zaman lafiya,” hallaka za tă auko musu farat ɗaya, kamar yadda naƙuda take kama mace mai ciki, ba za su kuwa tsira ba.

    4 Amma ku, ’yan’uwa, ba kwa cikin duhu da wannan rana za tă zo muku ba zato kamar ɓarawo. 5 Dukanku ’ya’yan haske ne da kuma ’ya’yan rana. Mu ba mutanen dare ko na duhu ba ne. 6 Saboda haka fa, kada mu zama kamar saura, waɗanda suke barci, sai dai mu zama masu tsaro da masu kamunkai.

  19. 44 Sa’an nan Yesu ya ɗaga murya ya ce, “Duk wanda ya gaskata da ni, ba ni yake gaskatawa ba, amma ga wanda ya aiko ni ne. 45 Duk mai dubana, yana duban wanda ya aiko ni ne. 46 Na zo cikin duniya a kan ni haske ne, don duk wanda ya gaskata da ni, kada yă zauna a cikin duhu.

  20. 126 Lokaci ya yi da za ka yi wani abu, ya Ubangiji;

    ana karya dokarka.

    127 Saboda ina ƙaunar umarnanka

    fiye da zinariya, kai, fiye da zinariya zalla,

    128 saboda kuma ina lura da dukan farillanka da kyau,

    na ƙi kowace hanyar da ba daidai ba.

    פ Fe

    129 Farillanka masu banmamaki ne;

    saboda haka nake yin biyayya da su.

    130 Fassarar maganganunka sukan ba da haske;

    sukan ba da ganewa ga marar ilimi.

  21. 15 “Ƙasar Zebulun da ƙasar Naftali,

    da kuke a hanyar zuwa tekun Galili, a ƙetaren Urdun,

    wannan yankin Galili ta Al’ummai,

    16 mutanen da suke zama cikin duhu

    sun ga babban haske;

    haske kuma ya haskaka

    a kan waɗanda suke zama a inuwar mutuwa.”

  22. 2 A can aka sāke kamanninsa a gabansu. Fuskarsa ta haskaka kamar rana, tufafinsa kuwa suka zama fari fat suna walƙiya.

  23. 23 Birnin ba ya bukatar rana ko wata su haskaka shi, gama ɗaukakar Allah tana ba shi haske, Ɗan Ragon kuwa shi ne fitilar birnin. 24 Al’ummai za su yi tafiya cikin hasken birnin, sarakunan duniya kuma za su kawo darajarsu cikin birnin. 25 Ba za a taɓa rufe ƙofofin birnin da rana ba, gama ba za a yi dare a can ba.

  24. 28 sai Siman ya karɓi yaron a hannuwansa ya yabi Allah, yana cewa,

    29 “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kamar yadda ka yi alkawari,

    yanzu ka sallami bawanka lafiya.

    30 Gama idanuna sun ga cetonka,

    31 wanda ka shirya a gaban dukan mutane,

    32 haske don bayyanawa ga Al’ummai

    da kuma ɗaukaka ga mutanenka Isra’ila.”

  25. 12 kuna gode wa Uba, wanda ya sa kuka cancanci ku sami rabo a gādon tsarkaka a cikin mulkin haske. 13 Gama ya riga ya cece mu daga mulkin duhu ya kuma kawo mu cikin mulkin Ɗan da yake ƙauna, 14 wanda ta wurinsa muka sami fansa da kuma gafarar zunubai.

  26. 7 Ina misalin ƙaunarka marar ƙarewa!

    Mutane manya da ƙanana kan sami mafaka cikin inuwar fikafikanka.

    8 Suna biki a yalwar gidanka;

    kakan ba su sha daga rafin farin cikinka.

    9 Gama a gare ka akwai maɓulɓular rai

    cikin haskenka mukan ga haske.

  27. 8 Sa’an nan haskenku zai keto kamar ketowar alfijir,

    warkarwarku kuma zai bayyana nan da nan;

    sa’an nan adalcinku zai tafi a gabanku,

    ɗaukakar Ubangiji kuma zai tsare ku daga baya.

    9 Sa’an nan za ku yi kira, Ubangiji kuma zai amsa;

    za ku yi kuka don neman taimako, zai kuwa ce ga ni nan.

    “In kuka kawar da karkiyar zalunci,

    kuka daina nuna wa juna yatsa da kuma faɗar mugayen maganganu,

    10 in kuma kuka ɗauki lokaci kuka ƙosar da mayunwata

    kuka kuma biya bukatun waɗanda suke shan tsanani,

    sa’an nan ne haskenku zai haskaka cikin duhu

    darenku kuma zai zama kamar tsakar rana.

  28. 35 Yohanna fitila ne da ya ci ya kuma ba da haske, kun kuwa zaɓa ku ji daɗin haskensa na ɗan lokaci.

  29. 47 Gama abin da Allah ya umarce mu ke nan cewa,

    “ ‘Na sa ka zama haske ga Al’ummai,

    don ka kawo cetona zuwa iyakokin duniya.’”

  30. 9 Duk wanda ya ce yana cikin haske yana kuma ƙin ɗan’uwansa, ashe a duhu yake har yanzu. 10 Duk wanda yake ƙaunar ɗan’uwansa, a cikin hasken yake rayuwa ke nan, kuma babu wani abin da yake cikinsa da zai sa yă yi tuntuɓe.

  31. 14 Allah kuma ya ce, “Bari haskoki su kasance a sararin sama domin su raba yini da dare, bari su zama alamu domin su nuna yanayi, da ranaku, da kuma shekaru, 15 bari kuma haskokin su kasance a sararin sama domin su ba da haske a duniya.” Haka kuwa ya kasance. 16 Allah ya yi manyan haskoki biyu, babban hasken yă mallaki yini, ƙaramin kuma yă mallaki dare. Ya kuma yi taurari. 17 Allah ya sa su a sararin sama domin su ba da haske a duniya, 18 su mallaki yini da kuma dare, su kuma raba haske da duhu. Allah kuwa ya ga yana da kyau. 19 Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta huɗu ke nan.

  32. 11 An haskaka haske a kan masu adalci

    da kuma farin ciki a kan masu gaskiya a zuciya.

  33. 13 Na umarce ka, a gaban Allah mai ba da rai ga kome, da kuma Kiristi Yesu wanda yayinda yake ba da shaida a gaban Buntus Bilatus ya yi kyakkyawar shaida, 14 ka kiyaye wannan umarni ba tare da wani aibi ko abin zargi ba har yă bayyanuwar Ubangijinmu Yesu Kiristi, 15 wanda Allah zai kawo a daidai lokaci, Allah, mai albarka wanda yake kaɗai Mai Mulki, Sarkin sarakuna da Ubangijin iyayengiji, 16 wanda shi kaɗai ne marar mutuwa wanda kuma yake zaune cikin hasken da ba ya kusatuwa, wanda babu wanda ya taɓa gani ko zai iya gani. A gare shi girma da iko su tabbata har abada. Amin.

  34. 18 Hanyar adali kamar fitowar rana ce,

    sai ƙara haske take yi, har ta kai tsaka.

    19 Amma hanyar mugaye kamar zurfin duhu ne;

    ba sa sanin abin da ya sa suke tuntuɓe.

  35. 3 Da ya yi kusa da Damaskus a kan hanyarsa, ba zato ba tsammani sai wani haske daga sama ya haskaka kewaye da shi. 4 Sai ya fāɗi a ƙasa ya kuma ji wata murya ta ce masa, “Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mini?”

    5 Shawulu ya yi tambaya ya ce, “Wane ne kai, ya Ubangiji?”

    Ya amsa ya ce, “Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa.

  36. 3 Ba za a ƙara samun la’ana ba. Kursiyin Allah da na Ɗan Ragon zai kasance a cikin birnin, bayinsa kuma za su yi masa hidima. 4 Za su ga fuskarsa, sunansa kuma zai kasance a goshinsu. 5 Ba za a ƙara yin dare ba. Ba za su bukaci hasken fitila ko hasken rana ba, domin Ubangiji Allah zai haskaka su. Za su kuwa yi mulki har abada abadin.

  37. 5 Yayinda ina a cikin duniya, ni ne hasken duniya.”

  38. 6 “Ni Ubangiji, na kira ka cikin adalci;

    zan riƙe hannunka.

    Zan kiyaye ka in kuma sa ka

    zama alkawari ga mutane

    haske kuma ga Al’ummai,

    7 don ka buɗe idanun makafi

    ka ’yantar da kamammu daga kurkuku

    kuma kunce ɗaurarrun kurkuku masu zama cikin duhu.

  39. 33 “Babu wanda yakan ƙuna fitila sa’an nan ya ɓoye ta, ko ya rufe ta da murfi ba. A maimako, yakan ajiye ta a kan wurin ajiye fitila, don masu shiga su ga haske. 34 Idonka shi ne fitilar jikinka. Sa’ad da idanunka suna da lafiya, dukan jikinka ma na cike da haske, amma sa’ad da idanunka suna da lahani, dukan jikinka ma na cike da duhu. 35 Ka lura fa, kada hasken da yake cikinka ya zamana duhu ne. 36 Saboda haka, in dukan jikinka yana cike da haske, ba inda ke da duhu, jikinka kuwa zai kasance da haske gaba ɗaya, kamar yadda hasken fitila yake haskaka ka.”

  40. 8 “Maigidan kuwa ya yabi manajan nan marar gaskiya saboda wayonsa. Gama ’yan duniyan nan suna da wayon yin hulɗa da junansu fiye da ’yan haske.

  41. 23 Gama waɗannan umarnai fitila ne,

    wannan koyarwa haske ne,

    kuma gyare-gyaren horo

    hanyar rayuwa ce,

  42. 22 “Ido shi ne fitilar jiki. In idanunka suna da kyau, dukan jikinka zai cika da haske. 23 Amma in idanunka suna da lahani, dukan jikinka ma zai cika da duhu. To, in hasken da yake a cikinka duhu ne, duhun ya wuce misali ke nan!

    24 “Ba mai iya bauta wa iyayengiji biyu. Ko dai yă ƙi ɗaya, yă ƙaunaci ɗaya, ko kuwa yă yi aminci ga ɗaya, sa’an nan yă rena ɗayan. Ba dama ku bauta wa Allah, ku kuma bauta wa kuɗi gaba ɗaya.”

  43. 4 Ko a cikin duhu haske kan haskaka wa mai aikata gaskiya,

    mai alheri mai tausayi da kuma mai adalci.

  44. 19 Muna kuwa da maganar annabawa da aka ƙara tabbatar mana, zai fi kyau in kuka lura da ita, kamar hasken da yake haskakawa a wuri mai duhu, har yă zuwa wayewar gari da kuma haskakawar tauraron asubahi a zukatanku.

  45. 13 “Akwai waɗanda suke yi wa haske tawaye,

    waɗanda ba su san hanyoyinsa ba

    ko kuma ba su taɓa bin hanyoyinsa ba.

    14 Sa’ad da hasken yini ya tafi, mai kisankai yakan tashi;

    yă je yă kashe matalauta da masu bukata;

    a cikin dare yake shigowa kamar ɓarawo.

    15 Idanun mazinaci suna jiran yamma ta yi sosai;

    yana tunani cewa, ‘Ba wanda zai gan ni,’

    sai kuma yă ɓoye fuskarsa.

    16 Cikin duhu mutane suna fasa gidaje,

    amma da rana sukan kulle kansu;

    ba sa so wani abu yă haɗa su da haske.

    17 Gama dukansu, duhu mai yawa shi ne safiyarsu;

    suna abokantaka da razanar duhu.

  46. 16 Yanzu ka tashi, ka tsaya da ƙafafunka. Na bayyana a gare ka don in naɗa ka bawa da kuma mai shaidar abin da ka gani game da ni da kuma abin da zan nuna maka. 17 Zan tsirar da kai daga mutanenka da kuma daga Al’ummai. Ina aikan ka zuwa gare su domin 18 ka buɗe idanunsu su kuwa juyo daga duhu zuwa haske, daga mulkin Shaiɗan kuma zuwa wurin Allah, domin su sami gafarar zunubai da kuma matsayi a cikin waɗanda aka tsarkake ta wurin bangaskiya a cikina.’

  47. 3 Allah na Isra’ila ya yi magana,

    Dutsen Isra’ila ya ce mini,

    ‘Sa’ad da wani ya yi mulkin mutane da adalci,

    sa’ad da ya yi mulki da tsoron Allah,

    4 yana kama da hasken safiya

    a safiya marar girgije,

    kamar haske bayan ruwan sama

    da yakan sa ciyawa ta tsiro daga ƙasa.’

  48. 2 Ubangiji ya naɗe kansa da haske kamar riga

    ya shimfiɗa sammai kamar tenti

  49. 14 Kada ku haɗa kai da marasa bi. Gama me ya haɗa adalci da mugunta? Ko kuwa me ya haɗa haske da duhu? 15 Wace daidaituwa ce tsakanin Kiristi da Iblis? Me ya haɗa mai bi da marar bi?

  50. 6 Yawanci suna cewa, “Wa zai yi mana alheri?”

    Bari hasken fuskarka yă haskaka a kanmu, ya Ubangiji.

  51. 6 ya ce,

    “Ɗan ƙaramin abu ne ka zama bawana

    don ka maido da kabilar Yaƙub

    ka kuma dawo da waɗannan na Isra’ilawan da na kiyaye.

    Zan kuma mai da kai haske ga Al’ummai,

    don ka kawo cetona zuwa iyakokin duniya.”

  52. 23 Ba wanda ya iya gani wani ko yă bar wurinsa na kwana uku. Amma dukan Isra’ilawa sun kasance da haske a inda suke zama.

  53. 14 Ya bishe su da girgije da rana

    da kuma haske daga wuta dukan dare.

  54. 30 Dubi yadda ya baza walƙiyarsa kewaye da shi,

    tana haskaka zurfin teku.

    31 Haka yake mulkin al’ummai

    yana kuma tanada abinci a wadace.

    32 Yana cika hannuwansa da walƙiya

    kuma yana ba ta umarni tă fāɗi a inda ya yi nufi.

  55. 28 Kai Ya Ubangiji, ka sa fitilata ta yi ta ci;

    Allahna ya mai da duhu ya zama haske.

  56. 7 Haske da yana da kyau,

    abu mai kyau ne kuma idanu su dubi rana.

  57. 1 Saboda Sihiyona ba zan yi shiru ba,

    saboda Urushalima ba zan huta ba,

    sai adalcinta ya haskaka kamar hasken safiya,

    cetonta kuma ya haskaka kamar fitila mai haske.

  58. 4 Darajarsa ta yi kamar fitowar rana;

    ƙyalƙyali ya wulga daga hannunsa,

    inda ikonsa yake a ɓoye.

  59. 2 Amma ku da kuke girmama sunana, ranar adalci za tă fito tare da warkarwa a fikafikanta. Za ku kuwa fita kuna tsalle kamar ’yan maruƙan da aka sake daga garke.

  60. 14 Ba abin mamaki ba ne, gama Shaiɗan kansa ma yana ɓad da kamanni kamar shi mala’ikan haske ne. 15 Don haka, ba abin mamaki ba ne, in bayin Shaiɗan sun ɓad da kamanni kamar su bayin adalci ne. A ƙarshe, za a sāka musu gwargwadon ayyukansu.

  61. 20 ya dawo tsakanin sojojin Masar da na Isra’ila. Duk dare, girgijen ya jawo duhu ga gefe ɗaya, haske kuma ga ɗaya gefen; saboda haka ba wanda ya kusaci wani duk dare.

  62. 7 Dokar Ubangiji cikakkiya ce,

    takan wartsakar da rai.

    Farillan Ubangiji abin dogara ne,

    suna mai da hikima da sauƙi.

    8 Ƙa’idodin Ubangiji daidai ne,

    suna ba da farin ciki ga zuciya.

    Umarnan Ubangiji haske ne

    suna ba da haske ga idanu.

    9 Tsoron Ubangiji yakan kawo tsabtar zuciya,

    zai kasance har abada.

    Farillan Ubangiji tabbatattu ne,

    kuma gaba ɗaya masu adalci ne.

    10 Sun fi zinariya daraja,

    fiye da zalla zinariya nesa;

    sun fi zuma zaƙi

    fiye da zuma daga kaki.

  63. 11 Gama Ubangiji Allah rana ne da kuma garkuwa;

    Ubangiji yakan yi alheri da kuma daraja;

    ba ya hana kowane abu mai kyau

    wa waɗanda suke aikata abin da yake daidai.

  64. 9 Hasken masu adalci kan haskaka ƙwarai,

    amma fitilar mugaye mutuwa take.

  65. 13 Na ga cewa hikima ta fi wauta,

    kamar yadda haske ya fi duhu.

  66. 20 Kaiton waɗanda suke ce da mugunta nagarta

    nagarta kuma mugunta,

    waɗanda suke mai da duhu haske

    haske kuma duhu,

    waɗanda suke mai da ɗaci zaƙi

    zaƙi kuma ɗaci.

  67. 3 Waɗanda suke da hikima za su haskaka kamar hasken samaniya, waɗanda kuma suka jagoranci waɗansu da yawa zuwa adalci, za su zama kamar taurari har abada abadin.

  68. 15 Dukan waɗanda suke zaune a Majalisar suka kafa wa Istifanus ido, suka kuma ga fuskarsa ta yi kama da ta mala’ika.

  69. 21 Da rana Ubangiji yakan ja gabansu a cikin al’amudin girgije domin yă bishe su a kan hanyarsu, da dare kuma a cikin al’amudin wuta domin yă ba su haske, domin su iya tafiya dare da rana. 22 Al’amudan nan biyu, na girgije da na wuta, ba su daina yi wa jama’a jagora ba.

  70. 18 Numfashinta yana fitar da wuta;

    idanunta kamar hasken zuwan safe.

    19 Wuta tana fitowa daga bakinta;

    tartsatsin wuta suna fitowa,

    20 Hayaƙi yana fitowa daga hancinta

    kamar daga tukunya mai tafasa a kan wutar itace.

    21 Numfashinta yana sa garwashi yă kama wuta,

    harshen wuta yana fita daga bakinta.

  71. 10 Zan kawar da muryoyin farin ciki da murna daga gare su, muryoyin amarya da na ango, ƙarar dutsen niƙa da hasken fitila.

  72. 3 Kamanninsa yana kama da walƙiya, tufafinsa kuma fari fat kamar dusan ƙanƙara.

  73. 4 Muddin da sauran rana, dole mu yi aikin wanda ya aiko ni. Dare yana zuwa, sa’ad da ba wanda zai iya yin aiki.

  74. 9 Yesu ya amsa ya ce, “Ba sa’a goma sha biyu ce yini guda ba? Mutumin da yake tafiya da rana ba zai yi tuntuɓe ba gama yana ganin hasken duniyan nan. 10 Sai a sa’ad da yake tafiya da dare ne zai yi tuntuɓe, don ba shi da haske.”

  75. 7 Ba zato ba tsammani sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana haske kuma ya haskaka a ɗakin. Ya bugi Bitrus a gefe ya kuma tashe shi ya ce, “Maza, ka tashi!” Sarƙoƙin kuwa suka zube daga hannuwansa.

  76. 3 Ɗan shi ne hasken ɗaukakar Allah, shi ne kuma ainihin kamanninsa, yana riƙe da dukan abubuwa ta wurin kalmarsa mai iko. Bayan ya yi tsarkakewa don zunubai, sai ya zauna a hannun daman Maɗaukaki a sama. 4 Ta haka yake da fifiko a kan mala’iku kamar yadda sunan da ya gāda ya fi nasu fifiko.

  77. 16 A hannunsa na dama ya riƙe taurari bakwai, daga bakinsa kuwa takobi mai kaifi biyu ya fito. Fuskarsa ta yi kamar rana mai haskakawa da dukan haskenta.

  78. 29 Sa’ad da Musa ya sauko daga kan Dutsen Sinai tare da alluna biyu na Alkawari a hannuwansa, bai san cewa fuskarsa tana ƙyalli ba saboda zaman da ya yi a gaban Ubangiji. 30 Da Haruna da dukan Isra’ila suka ga Musa, fuskarsa kuma tana ƙyalli, sai suka ji tsoron zuwa kusa da shi.

  79. 26 Duk da haka sa’ad da nake begen abu mai kyau,

    mugun abu ne ya zo;

    Sa’ad da nake neman haske, sai duhu ya zo.

  80. 5 Waɗanda suke dubansa sukan haskaka;

    fuskokinsu ba sa rufuwa da kunya.

  81. 17 Hasken Isra’ila zai zo kamar wuta,

    Mai Tsarkinsu zai zama kamar wuta;

    a rana guda zai ƙone yă kuma cinye

    ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiyarsa.

  82. 5 Saboda haka, kada ku shari’anta kome tun lokaci bai yi ba. Ku jira sai Ubangiji ya zo. Zai bayyana abin da yake a ɓoye a cikin duhu a sarari, zai kuma tone nufin zukatan mutane. A lokacin ne fa kowa zai karɓi yabo daga wurin Allah daidai gwargwado.