73 Bible Verses About Cancer
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
13 Akwai waninku da yake shan wahala? Ya kamata yă yi addu’a. Akwai wani mai murna? Sai yă rera waƙoƙin yabo. 14 Akwai waninku da yake ciwo? Ya kamata yă kira dattawan ikkilisiya su yi masa addu’a, su kuma shafa masa mai cikin sunan Ubangiji. 15 Addu’ar da aka yi cikin bangaskiya, za tă warkar da marar lafiya, Ubangiji zai tashe shi. In ya yi zunubi kuwa za a gafarta masa. 16 Saboda haka, ku furta wa juna zunubanku, ku yi addu’a saboda juna, domin ku sami warkarwa. Addu’ar mai adalci tana da iko da kuma amfani.
17 Iliya mutum ne kamar mu. Ya yi addu’a da gaske don kada a yi ruwan sama, ba a kuma yi ruwan sama a ƙasar ba har shekaru uku da rabi. 18 Ya sāke yin addu’a, sai sammai suka ba da ruwan sama, ƙasa kuma ta ba da amfaninta.
-
4 Tabbatacce ya ɗauki cututtukanmu
ya kuma daure da baƙin cikinmu
duk da haka muka ɗauka Allah ya hukunta shi ne,
ya buge shi ya kuma sa ya sha azaba.
5 Amma aka yi masa rauni saboda laifofinmu,
aka ƙuje shi saboda kurakuranmu;
hukuncin da ya kawo mana salama ya kasance a kansa,
kuma ta wurin mikinsa ya sa muka warke.
6 Dukanmu, muna kama da tumakin da suka ɓata,
kowannenmu ya kama hanyarsa;
Ubangiji kuwa ya sa hukunci ya auko a kansa
hukuncin da ya wajaba a kanmu.
-
24 Kalmomi masu daɗi suna kama da kakin zuma,
mai zaƙi ga rai da kuma warkarwa ga ƙasusuwa.
-
14 Da Yesu ya zo cikin gidan Bitrus, sai ya ga surukar Bitrus tana kwance a gado tana da zazzaɓi. 15 Ya taɓa hannunta sai zazzaɓin ya sake ta, ta kuwa tashi ta fara yin masa hidima.
16 Da yamma ta yi, aka kawo masa masu aljanu da yawa, ya kuwa fitar da ruhohin ta wurin magana, ya kuma warkar da dukan marasa lafiya. 17 Wannan ya faru ne domin a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya cewa,
“Ya ɗebi rashin lafiyarmu,
ya kuma ɗauki cututtukanmu.”
-
35 Yesu ya zazzaga dukan garuruwa da ƙauyuka, yana koyarwa a majami’unsu, yana wa’azin labari mai daɗi na mulkin yana kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.
-
23 Yesu ya zazzaga dukan Galili, yana koyarwa a cikin majami’unsu, yana wa’azin labari mai daɗi na mulkin sama, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiyar mutane. 24 Labarinsa ya bazu ko’ina a Suriya, mutane kuwa suka kawo masa dukan waɗanda suke fama da cututtuka iri-iri, da waɗanda suke da zafin ciwo, da masu aljanu, da waɗanda suke masu farfaɗiya, da shanyayyu, ya kuwa warkar da su.
-
34 “Sa’an nan Sarki zai ce wa waɗanda suke damansa, ‘Ku zo, ku da Ubana ya yi wa albarka; ku karɓi gādonku, mulkin da aka shirya muku tun halittar duniya. 35 Gama da nake jin yunwa, kun ciyar da ni, da nake jin ƙishirwa, kun ba ni abin sha, da nake baƙunci, kun karɓe ni, 36 da nake bukatar tufafi, kun yi mini sutura, da na yi rashin lafiya, kun lura da ni, da nake kurkuku, kun ziyarce ni.’
37 “Sa’an nan masu adalci za su amsa masa, su ce, ‘Ubangiji, yaushe muka gan ka da yunwa muka ciyar da kai, ko da ƙishirwa muka ba ka abin sha? 38 Yaushe kuma muka gan ka baƙo muka karɓe ka, ko cikin bukatar tufafi muka yi maka sutura? 39 Yaushe kuma muka gan ka cikin rashin lafiya ko a kurkuku muka ziyarce ka?’
40 “Sarkin zai amsa ya ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, duk abin da kuka yi wa ɗaya daga cikin waɗannan ’yan’uwana mafi ƙanƙanta, ni kuka yi wa.’
-
26 Ya ce, “In kun kasa kunne ga muryar Ubangiji Allahnku kuka yi abin da yake daidai a idanunsa, in kun mai da hankali ga umarnansa, kuka kiyaye dukan farillansa, ba zan kawo muku wani ciwon da na kawo a kan Masarawa ba, gama ni ne Ubangiji da nake warkar da ku.”
-
Ta Dawuda.
1 Yabi Ubangiji, ya raina;
dukan abin da yake cikin cikina, yabi sunansa mai tsarki.
2 Yabi Ubangiji, ya raina,
kada kuma ka manta dukan alheransa,
3 wanda yake gafarta dukan zunubai
yake kuma warkar da dukan cututtuka,
4 wanda ya fanshi ranka daga rami
ya naɗa maka rawani da ƙauna da kuma tausayi,
5 Wanda ya ƙosar da kai da abubuwa masu kyau
domin a sabunta ƙuruciyarka kamar na gaggafa.
-
3 Na kuma ji wata babbar murya daga kursiyin tana cewa, “Yanzu mazaunin Allah yana tare da mutane, zai kuma zauna tare da su. Za su zama mutanensa, Allah kansa kuwa zai kasance tare da su yă kuma zama Allahnsu. 4 Zai share dukan hawaye daga idanunsu. Ba sauran mutuwa ko makoki ko kuka ko azaba, gama tsofaffin al’amura sun shuɗe.”
-
29 Yakan ba da ƙarfi ga waɗanda suka gaji
yă kuma ƙara ƙarfi ga marasa ƙarfi.
30 Ko matasa ma kan gaji su kuma kasala,
samari kuma kan yi tuntuɓe su fāɗi;
31 amma waɗanda suka dogara ga Ubangiji
za su sabunta ƙarfinsu.
Za su yi firiya da fikafikai kamar gaggafa;
za su kuma yi gudu ba kuwa za su gaji ba,
za su yi tafiya ba kuwa za su kasala ba.
-
1 Sai ya kira almajiransa goma sha biyu wurinsa ya kuma ba su iko su fitar aljanu, su kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.
2 Ga sunayen manzannin nan goma sha biyu,
da fari, Siman (wanda ake kira Bitrus) da ɗan’uwansa Andarawus;
Yaƙub ɗan Zebedi da ɗan’uwansa Yohanna;
3 Filibus da Bartolomeyu;
Toma da Mattiyu mai karɓar haraji;
Yaƙub ɗan Alfayus da Taddayus;
4 Siman Zilot da kuma Yahuda Iskariyot wanda ya bashe Yesu.
5 Waɗannan sha biyun ne Yesu ya aika da umarni cewa, “Kada ku je cikin Al’ummai, ko kuwa ku shiga wani garin Samariyawa. 6 A maimakon haka ku je wajen ɓatattun tumakin Isra’ila. 7 Sa’ad da kuke tafiya, ku yi wa’azi, kuna cewa, ‘Mulkin sama ya kusato.’ 8 Ku warkar da marasa lafiya, ku tā da matattu, ku tsabtacce kutare, ku kuma fitar da aljanu. A kyauta kuka samu, ku kuma bayar a kyauta.
-
25 Ku bauta wa Ubangiji Allahnku, albarkansa kuwa za tă kasance a kan abincinku da ruwan shanku. Zan ɗauke cuta daga cikinku. 26 A ƙasarku, mace ba za tă yi ɓari ba, ba kuma za a sami marar haihuwa ba. Zan ba ku tsawon rai.
-
14 Ka warkar da ni, ya Ubangiji, zan kuwa warke;
ka cece ni zan kuwa cetu,
gama kai ne nake yabo.
-
28 “Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji kuke kuma fama da kaya, zan kuwa ba ku hutu. 29 Ku ɗauki karkiyata a kanku, ku kuma yi koyi da ni, gama ni mai tawali’u ne marar girman kai, za ku kuwa sami hutu don rayukanku. 30 Gama karkiyata mai sauƙi ce, kayana kuma marasa nauyi ne.”
-
10 Saboda haka kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai;
kada ka karai, gama ni ne Allahnka.
Zan ƙarfafa ka in kuma taimake ka;
zan riƙe ka da hannun damana mai adalci.
-
17 Amma zan mayar muku da lafiya
in kuma warkar da mikinku,’ in ji Ubangiji,
‘domin ana ce da ku yasassu,
Sihiyona wadda ba wanda ya kula da ita.’
-
7 Don kada in cika da girman kai saboda waɗannan mafifitan manyan wahayoyi, sai aka sa mini wata ƙaya a jikina wadda ta zama ɗan saƙon Shaiɗan, don ta wahalshe ni. 8 Sau uku na roƙi Ubangiji yă raba ni da wannan abu. 9 Amma ya ce mini, “Alherina ya ishe ka, domin a cikin rashin ƙarfi ne ake ganin cikar ikona.” Saboda haka, zan ƙara yin taƙama da farin ciki game da rashin ƙarfina, domin ikon Yesu Kiristi yă zauna tare da ni. 10 Shi ya sa nake murna cikin rashin ƙarfi, da zagi, da shan wahaloli, da tsanantawa, da matsaloli, saboda Kiristi. Don a sa’ad da nake marar ƙarfi a nan ne nake da ƙarfi.
-
1 A kwanakin nan sai Hezekiya ya kamu da rashin lafiya har ya kusa mutuwa. Sai annabi Ishaya ɗan Amoz ya zo wurinsa ya ce, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ka kintsa gidanka domin za ka mutu, ba za ka warke ba.”
2 Hezekiya ya juya fuskarsa wajen bango ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, 3 “Ya Ubangiji, ka tuna yadda na yi tafiya a gabanka da aminci da zuciya ɗaya, na kuma aikata abin da yake daidai a gabanka.” Sai Hezekiya ya yi kuka mai zafi.
4 Kafin Ishaya yă bar tsakiyar filin gida, sai maganar Ubangiji ta zo masa cewa, 5 “Ka koma ka ce wa Hezekiya, shugaban mutanena, ‘Ga abin da Ubangiji Allah na mahaifinka Dawuda ya ce, na ji addu’arka na kuma ga hawayenka; zan warkar da kai. A rana ta uku daga yau za ka haura zuwa haikalin Ubangiji. 6 Zan ƙara maka shekara goma sha biyar. Zan kuma cece ka daga hannun sarkin Assuriya. Zan kāre birnin nan saboda kaina da kuma bawana Dawuda.’ ”
7 Sai Ishaya ya ce, “A kwaɓa ɓaure.” Sai aka yi haka, aka shafa wa marurun, ya kuma warke.
-
2 Ya Ubangiji Allahna, na yi kira gare ka don taimako
ka kuwa warkar da ni.
3 Ya Ubangiji, ka dawo da ni daga kabari;
ka kiyaye ni daga gangarawa zuwa cikin rami.
-
3 Ya warkar da masu raunanar zuciya
ya ɗaɗɗaura miyakunsu.
-
24 Shi kansa ya ɗauki zunubanmu a jikinsa a kan itace, domin mu mutu ga zunubai mu kuma rayu ga adalci; ta wurin raunukansa ne kuka sami warkarwa.
-
2 Ubangiji zai kāre shi yă kuma kiyaye ransa;
zai albarkace shi a cikin ƙasar
ba kuwa zai miƙa shi ga hannun maƙiyansa ba.
3 Ubangiji zai ba shi ƙarfi a gadon rashin lafiyarsa
ya mayar masa da lafiya daga ciwon da ya kwantar da shi.
-
14 Kamar dai yadda Musa ya ɗaga maciji a hamada, haka dole ne a ɗaga Ɗan Mutum, 15 don duk mai gaskata da shi ya sami rai madawwami.”
16 Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami. 17 Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yă yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin yă ceci duniya ta wurinsa.
-
29 Da suka bar majami’ar, sai suka tafi gidan su Siman da Andarawus, tare da Yaƙub da Yohanna. 30 Surukar Siman tana kwance da zazzaɓi, sai suka gaya wa Yesu game da ita. 31 Sai ya je wajenta, ya kama hannunta, ya ɗaga ta. Zazzaɓin kuwa ya sāke ta, ta kuma yi musu hidima.
32 A wannan yamma, bayan fāɗuwar rana, mutane suka kawo wa Yesu dukan marasa lafiya, da masu aljanu. 33 Duk garin ya taru a ƙofar gidan. 34 Yesu kuwa ya warkar da marasa lafiya da yawa da suke da cututtuka iri-iri. Ya kuma fitar da aljanu da yawa, amma bai yarda aljanun suka yi magana ba, don sun san wane ne shi.
-
27 Salama na bari tare da ku; salamata nake ba ku. Ba kamar yadda duniya take bayarwa nake ba ku ba. Kada zuciyarku ta ɓaci kada kuma ku ji tsoro.
-
28 Mun kuma san cewa a cikin dukan abubuwa Allah yana aikata alheri ga waɗanda suke ƙaunarsa, yana waɗanda aka kira bisa ga nufinsa.
-
2 Ka yi mini jinƙai, Ubangiji, gama na suma;
Ya Ubangiji, ka warkar da ni, gama ƙasusuwana suna zafin ciwo.
-
22 Zuciya mai farin ciki magani ne mai kyau,
amma bakin rai kan busar da ƙasusuwa.
-
4 Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji kullum. Ina sāke gaya muku ku yi farin ciki! 5 Bari kowa yă kasance da sauƙinkai. Ubangiji ya yi kusan zuwa. 6 Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya. 7 Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za tă tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.
-
34 Sai ya ce mata, “Diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya, kin kuma rabu da dukan wahalarki.”
-
1 Saboda haka, da yake an same mu marasa laifi ta wurin bangaskiya, muna da salama tare da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi, 2 ta wurinsa ne muka sami shiga wannan alherin da muke tsaye yanzu, ta wurin bangaskiya. Muna kuma farin ciki a begen ɗaukakar Allah. 3 Ba haka kawai ba, amma muna kuma da farin ciki cikin shan wuyanmu, gama mun san cewa shan wuyan nan takan haifi jimiri; 4 jimiri kuma yakan kawo hali mai kyau; hali mai kyau kuma yakan sa bege. 5 Bege kuwa ba ya ba mu kunya, domin Allah ya zuba ƙaunarsa a zukatanmu ta wurin Ruhu Mai Tsarkin da ya ba mu.
-
1 Da ya sauko daga dutsen, sai taron mutane mai yawan gaske suka bi shi. 2 Wani mutum mai kuturta ya zo ya durƙusa a gabansa ya ce, “Ubangiji, in kana so, kana iya tsabtacce ni.”
3 Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin. Ya ce, “Ina so, ka tsabtacce!” Nan da nan aka warkar da shi daga kuturtarsa.
-
14 Da Yesu ya sauka ya kuma ga taro mai yawa, sai ya ji tausayinsu ya kuma warkar da marasa lafiyarsu.
-
17 Waɗannan alamu za su kasance tare da waɗanda suka gaskata. A cikin sunana za su fitar da aljanu, za su yi magana da sababbin harsuna. 18 Za su ɗauki macizai da hannuwansu. In kuwa suka sha mugun dafi, ba zai cuce su ba ko kaɗan. Za su ɗibiya hannuwansu a kan marasa lafiya, su kuwa warke.”
-
1 Da Yesu yana tafiya, sai ya ga wani mutum wanda aka haifa makaho. 2 Sai almajiransa suka tambaye shi suka ce, “Rabbi, wane ne ya yi zunubi, mutumin ne, ko iyayensa, da ya sa aka haife shi makaho?”
3 Sai Yesu ya ce, “Ba don mutumin ko iyayensa sun yi zunubi ne ba, sai dai don a bayyana aikin Allah ne a rayuwarsa. 4 Muddin da sauran rana, dole mu yi aikin wanda ya aiko ni. Dare yana zuwa, sa’ad da ba wanda zai iya yin aiki. 5 Yayinda ina a cikin duniya, ni ne hasken duniya.”
6 Bayan ya faɗi haka, sai ya tofa miyau a ƙasa, ya kwaɓa laka da miyau ɗin, ya kuma shafa a idanun mutumin. 7 Ya ce masa, “Je ka, ka wanke a Tafkin Silowam” (kalman nan tana nufin “Aikakke”). Saboda haka mutumin ya tafi ya wanke, ya kuma dawo gida yana gani.
-
23 Ba haka kaɗai ba ma, mu kanmu da muke da nunan fari na Ruhu, muna nishi a ciki-cikinmu yayinda muke jira da marmari a maishe mu ’ya’yan riƙo na Allah, fansar jikunanmu. 24 Gama a wannan begen ne muka sami ceto. Amma begen da ake gani ba bege ba ne sam. Wa yake begen abin da ya riga ya samu? 25 Amma in muna begen abin da ba mu riga mun samu tukuna ba, mukan jira da haƙuri.
26 Haka nan ma, Ruhu yana taimakonmu cikin rashin ƙarfinmu. Ba mu san abin da ya kamata mu roƙa cikin addu’a ba, amma Ruhu kansa yana roƙo a madadinmu da nishe-nishen da kalmomi ba sa iya bayyanawa. 27 Shi kuma wanda yake binciken zukatanmu ya san halin Ruhu, domin Ruhu yana roƙo a madadin tsarkaka bisa ga nufin Allah.
-
35 Wane ne zai raba mu da ƙaunar Kiristi? Masifa ce ko wahala ko tsanani ko yunwa ko tsiraici ko hatsari ko takobi? 36 Kamar yadda yake a rubuce cewa,
“Saboda kai ne muke fuskantar mutuwa dukan yini;
an ɗauke mu kamar tumakin da za a yanka.”
37 A’a, cikin dukan waɗannan abubuwa mun ma fi masu nasara ta wurin shi wanda ya ƙaunace mu. 38 Gama na tabbata cewa ko mutuwa ko rai, ko mala’iku ko aljanu, ko abubuwa na yanzu ko abubuwa masu zuwa nan gaba, ko ikoki, 39 ko tsayi ko zurfi, ko wani abu dabam cikin dukan halitta da zai iya raba mu da ƙaunar Allah wadda take cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.
-
1 Wata rana kuma mala’iku suka sāke kawo kansu gaban Ubangiji, sai Shaiɗan shi ma ya zo tare da su yă nuna kansa a gabansa. 2 Sai Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Daga ina ka fito?”
Shaiɗan ya amsa wa Ubangiji ya ce, “Daga yawo a duniya ina kai da kawowa a cikinta.”
3 Sai Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Ko ka ga bawana Ayuba? A cikin duniya babu wani kamar sa; shi marar laifi ne, adali kuma, mutum ne mai tsoron Allah ba ruwansa da mugunta. Kuma har yanzu bai fasa zama mai aminci ba duk da wahalar da ka sa na bari ka ba shi ba tare da wani dalili ba.”
4 Shaiɗan ya amsa ya ce, “Fata don fata! Mutum zai iya rabuwa da duk abin da yake da shi domin ransa. 5 Ka ɗan taɓa lafiyar jikinsa ka gani ba shakka zai la’anta ka kana ji kana gani.”
6 Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “To, shi ke nan, duk abin da yake da shi yana hannunka, amma kada ka taɓa shi, shi kansa.”
7 Sai Shaiɗan ya bar Ubangiji, ya je ya sa wa Ayuba ƙuraje masu zafi a jikinsa daga tafin ƙafafunsa har zuwa kansa. 8 Sai Ayuba ya ɗauki kaskon tukunya yana ta sosa ƙurajen da shi, yayinda yake zaune cikin toka.
9 Matarsa ta ce masa, “Har yanzu kana nan da amincinka? Ka la’anta Allah ka mutu!”
10 Ya amsa ya ce, “Kina magana kamar wawiya. Alheri kaɗai za mu dinga samu daga Allah ban da wahala?”
A cikin wannan duka Ayuba bai yi zunubi ba cikin maganarsa.
-
Zabura ta Dawuda.
1 Ubangiji ne yake kiwona, ba zan rasa kome ba,
2 Yakan sa in kwanta a makiyaya mai ɗanyar ciyawa,
yakan bi da ni kusa da ruwaye marar hayaniya,
3 yakan maido da raina.
Yakan bi da ni a hanyoyin adalci
saboda sunansa.
4 Ko da na yi tafiya
ta kwari na inuwar mutuwa,
ba zan ji tsoron mugu ba,
gama kana tare da ni;
bulalarka na dūka da kuma sandanka na tafiya,
za su yi mini ta’aziyya.
-
5 Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka
kada kuma ka dangana ga ganewarka;
6 cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi,
zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.
7 Kada ka zama mai hikima a ganinka;
ka ji tsoron Ubangiji ka kuma guji mugunta.
8 Wannan zai ba wa jikinka lafiya
yă kuma adana ƙasusuwanka.
-
1 Akwai lokaci domin kowane abu,
da kuma lokaci domin kowane aiki a duniya.
2 Lokacin haihuwa da lokacin mutuwa,
lokacin shuki da lokacin tumɓukewa.
3 Lokacin kisa da lokacin warkarwa,
lokacin rushewa da lokacin ginawa.
4 Lokacin kuka da lokacin dariya,
lokacin makoki da lokacin rawa.
5 Lokacin warwatsa duwatsu da lokacin tara su,
lokacin runguma da lokacin dainawa.
6 Lokacin nema, da lokacin fid da zuciya,
lokacin ajiyewa da lokacin zubarwa.
7 Lokacin yagewa da lokacin ɗinkewa,
lokacin yin shiru da lokacin magana.
8 Lokacin ƙauna da lokacin ƙiyayya,
lokacin yaƙi da lokacin salama.
-
6 Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tafe tare da ku, ba zai taɓa barinku ko yă yashe ku ba.”
-
17 Adalai kan yi kuka, Ubangiji kuwa yakan ji su;
yakan cece su daga dukan wahalarsu.
18 Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai
ya kuma cece waɗanda aka ragargaza a ruhu.
19 Adali zai iya kasance da wahala da yawa,
amma Ubangiji yakan cece shi daga dukansu;
20 yakan tsare dukan ƙasusuwansa,
ba ko ɗayansu da zai karye.
21 Mugunta zai kashe mugu;
za a hukunta abokan gāban adalai.
22 Ubangiji yakan cece bayinsa;
ba wanda yake neman mafaka a wurinsa da za a hukunta.
-
1 A kwanakin nan sai Hezekiya ya kamu da ciwo ya kuma kusa ya mutu. Annabi Ishaya ɗan Amoz ya tafi wurinsa ya kuma ce, “Ga abin da Ubangiji ya ce ka shirya gidanka, domin za ka mutu; ba za ka warke ba.”
2 Hezekiya ya juye fuskarsa wajen bango ya kuma yi addu’a ga Ubangiji, 3 “Ka tuna, ya Ubangiji, yadda na yi tafiya a gabanka da aminci da dukan zuciya na kuma yi abin da yake nagari a idanunka.” Sai Hezekiya ya yi kuka mai zafi.
4 Sai maganar Ubangiji ta zo wa Ishaya cewa, 5 “Ka tafi ka faɗa wa Hezekiya, ‘Ga abin da Ubangiji Allah na kakanka Dawuda, ya ce na ji addu’arka na kuma ga hawayenka; zan ƙara maka shekaru goma sha biyar ga rayuwarka. 6 Zan kuwa cece ka da wannan birni daga hannun sarkin Assuriya. Zan kiyaye wannan birni.
-
40 Rana tana fāɗuwa, sai mutane suka yi ta kawo wa Yesu dukan waɗanda suke da cuta iri-iri, sai ya ɗibiya wa kowannensu hannuwansa, ya warkar da su.
-
16 Saboda haka, ba mu fid da zuciya ba. Ko da yake a waje, jikinmu mai mutuwa yana lalacewa, amma can ciki, ana sabunta mu kowace rana. 17 Don wannan ’yar wahalar tamu mai saurin wucewa, ita take tanadar mana madawwamiyar ɗaukaka mai yawa, fiye da kwatanci. 18 Domin ba abubuwan da ido yake gani ne muke dubawa ba, sai dai marasa ganuwa. Gama abubuwan da ake gani masu saurin wucewa ne, marasa ganuwa kuwa, madawwama ne.
-
19 Allahna kuma zai biya dukan bukatunku bisa ga ɗaukakar wadatarsa cikin Kiristi Yesu.
-
15 Ubangiji zai kiyaye ku daga kowace cuta. Ba zai wahalshe ku da mugayen cututtukan da kuka sani a Masar ba, amma zai aukar wa dukan maƙiyanku.
-
11 Gama na san shirye-shiryen da na yi muku,” in ji Ubangiji, “shirye-shiryen cin gaba ba na cutarwa ba, shirye-shiryen ba ku sa zuciya da kuma na nan gaba.
-
10 Wata ranar Asabbaci, Yesu yana koyarwa a wata majami’a, 11 a wurin kuwa, akwai wata mace wadda aljani ya gurgunta, har na shekaru goma sha takwas. Duk ta tanƙware, ba ta ma iya miƙewa ko kaɗan. 12 Da Yesu ya gan ta, sai ya kirata gaba, ya ce mata, “Mace, an ’yantar da ke daga rashin lafiyarki.” 13 Sai ya ɗibiya hannuwansa a kanta, nan da nan sai ta miƙe, ta yabi Allah.
-
29 Gama duk wanda ya ci ya kuma sha ba tare da fahimtar jikin Ubangiji ba, ya ci ya kuma sha wa kansa hukunci ne. 30 Shi ya sa da yawa a cikinku ba su da ƙarfi, suna kuma da rashin lafiya, waɗansunku kuma sun riga sun yi barci. 31 Amma in da za mu auna kanmu sosai, da ba za mu shiga irin hukuncin nan ba. 32 Duk da haka sa’ad da Ubangiji ya hukunta mu, ana yin mana horo ne don kada a ƙarshe a hallaka mu tare da duniya.
-
26 Jikina da zuciyata za su iya raunana,
amma Allah ne ƙarfin zuciyata
da kuma rabona har abada.
-
15 Zai kira bisa sunana, zan kuma amsa masa;
zan kasance tare da shi a lokacin wahala,
zan kuɓutar da shi in kuma girmama shi.
16 Da tsawon rai zan ƙosar da shi
in kuma nuna masa cetona.”
-
2 Amma ku da kuke girmama sunana, ranar adalci za tă fito tare da warkarwa a fikafikanta. Za ku kuwa fita kuna tsalle kamar ’yan maruƙan da aka sake daga garke.
-
19 Kuma dukan mutane suka yi ƙoƙari su taɓa shi, domin iko yana fitowa daga gare shi, ya kuwa warkar da su duka.
-
49 Yayinda Yesu na cikin magana har yanzu, sai ga wani daga gidan Yayirus, mai mulkin majami’ar ya ce, “Kada ka ƙara damun malam, diyarka ta rasu.”
50 Da Yesu ya ji wannan, sai ya ce wa Yayirus, “Kada ka ji tsoro, ka gaskata, za a kuma warkar da ita.”
51 Da ya iso gidan Yayirus, sai ya hana kowa yă bi shi cikin ɗakin, sai dai Bitrus, da Yohanna, da Yaƙub, da kuma mahaifin da mahaifiyar. 52 Ana cikin haka, dukan mutanen kuma sai kuka da makoki suke ta yi, domin yarinyar. Sai Yesu ya ce, “Ka daina yin kuka, ba tă mutu ba, tana barci ne.”
53 Sai suka yi masa dariya, da yake sun san cewa, ta mutu. 54 Amma Yesu ya kama ta a hannu ya ce, “Diyata, tashi.” 55 Ruhunta ya dawo, kuma ta tashi, nan take. Yesu ya ce musu, su ba ta wani abu tă ci. 56 Iyayenta suka yi mamaki, amma ya ba su umarni kada su faɗa wa kowa abin da ya faru.
-
9 Ku warkar da marasa lafiya da suke wurin. Ku kuma faɗa musu cewa, ‘Mulkin Allah yana kusa da ku.’
-
10 Ɓarawo yakan zo don yă yi sata ne kawai da kisa da kuma ɓarna. Ni kuwa na zo ne don su sami rai, su kuma same shi a yalwace.
-
8 Mahaifinsa kuwa yana kwanciya a gado yana fama da zazzaɓi da atuni. Bulus ya shiga ciki don yă gan shi, bayan ya yi masa addu’a, sai ya ɗibiya masa hannuwa ya warkar da shi. 9 Sa’ad da wannan ya faru, sauran marasa lafiya a tsibirin suka zo aka kuma warkar da su.
-
6 Saboda haka, ku ƙasƙantar da kanku a ƙarƙashin hannun Allah mai ƙarfi, don yă ɗaukaka ku a lokacin da ya ga dama. 7 Ku danƙa masa dukan damuwarku, domin shi ne yake lura da ku.
-
3 Saboda hasalarka babu lafiya a jikina;
ƙasusuwana ba lafiya saboda zunubina.
-
1 Shi wanda yake zama a wurin Mafi Ɗaukaka
zai huta a cikin inuwar Maɗaukaki.
2 Zan ce game da Ubangiji, “Shi ne mafakata da kagarata,
Allahna, wanda nake dogara.”
3 Tabbatacce zai cece ka
daga tarkon mai farauta
da kuma daga cututtuka masu kisa.
4 Zai rufe ka da fikafikansa,
a ƙarƙashin fikafikansa kuwa za ka sami mafaka;
amincinsa zai zama maka garkuwa da katanga.
5 Ba za ka ji tsoron razanar dare,
ko kibiyoyi da suke firiya da rana ba,
6 ko bala’in da yake aukowa cikin duhu,
ko annobar da take hallakarwa da tsakar rana.
7 Dubu za su iya fāɗuwa a gefenka,
dubu goma a hannun damanka,
amma ba abin da zai zo kusa da kai.
8 Za ka dai gan da idanunka
yadda ake hukunta mugaye.
-
2 Ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai;
muna marmarinka.
Ka zama ƙarfinmu kowace safiya,
cetonmu a lokacin damuwa.
-
13 Sa’an nan Yesu ya ce wa jarumin, “Je ka! Za a yi bisa ga bangaskiyarka.” A daidai wannan lokaci bawansa kuwa ya warke.
-
12 Da jin wannan, Yesu ya ce, “Ai, ba masu lafiya ba ne su bukatar likita, sai dai marasa lafiya. 13 Amma ku je ku koyi abin da wannan yake nufi, ‘Jinƙai nake bukata, ba hadaya ba.’ Gama ban zo domin in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi.”
-
35 Da mutanen wurin suka gane da Yesu, sai suka kai labari a ko’ina a ƙauyukan da suke kewaye. Mutane suka kawo masa dukan marasa lafiyarsu 36 suka kuwa roƙe shi yă bar marasa lafiya su taɓa ko da gefen rigarsa kawai, duk waɗanda suka taɓa shi kuwa suka warke.
-
2 Ya kuma aike su, su yi wa’azin mulkin Allah, su kuma warkar da marasa lafiya.
-
6 Akwai aiki iri-iri, amma duk Allah ɗaya ne yake aikata su a cikin dukan mutane.
7 An ba wa kowane mutum bayyanuwar Ruhu don amfanin kowa. 8 Ga wani, an ba shi saƙon hikima ta wurin Ruhu, ga wani baiwar saƙon sani ta wurin wannan Ruhu guda. 9 Ga wani bangaskiya ta wurin wannan Ruhu, ga wani kuma baiwar warkarwa ta wurin wannan Ruhu guda. 10 Ga wani yin ayyukan banmamaki, ga wani annabci, ga wani baiwar rarrabe ruhohi, ga wani baiwar magana da harsuna dabam-dabam, ga wani har wa yau iya fassarar harsuna.
-
3 Yabo ya tabbata ga Allah, da Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba mai tausayi, da kuma Allah na dukan ta’aziyya, 4 wanda yakan yi mana ta’aziyya a cikin dukan wahalolinmu, domin mu kuma mu iya ta’azantar da waɗanda suke cikin kowace irin wahala, da ta’aziyyar da mu kanmu muka samu daga Allah. 5 Gama kamar yadda wahalar Kiristi ta cika har tana zuba a cikin rayuwarmu, haka nan kuma ta wurin Kiristi ta’aziyyarmu ta cika har tana zuba. 6 In muna shan wahala, ai, muna shanta domin ta’aziyyarku, da cetonku ne, in mun sami ta’aziyya, ai, mun same ta domin ta’aziyyarku ce, wadda take sa ku jure wa irin wahalan nan, da muke sha. 7 Begen da muke da shi dominku kuwa, tabbatacce ne, domin mun san cewa kamar yadda kuke tarayya da mu a cikin wahalolinmu, haka kuma kuke tarayya da mu a cikin ta’aziyyarmu.
-
12 Na san mene ne zaman rashi, na kuma san mene ne zaman samu. Zan iya zama cikin kowane hali, ko cikin ƙoshi ko cikin yunwa, ko cikin yalwa ko kuma cikin fatara. 13 Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi.
-
15 Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka gabatar da kanka a gaban Allah a matsayin wanda aka amince da shi, ma’aikaci wanda ba shi da dalilin jin kunya wanda kuma yake fassara kalmar gaskiya daidai. 16 Ka yi nesa da maganganun banza na rashin tsoron Allah, gama waɗanda suka mai da hankali ga yin waɗannan za su ƙara zama marasa tsoron Allah. 17 Koyarwarsu za tă bazu kamar ruɓaɓɓen gyambo. A cikinsu akwai Himenayus da Filetus,
-
1 Bangaskiya ita ce kasance tabbacin abin da muke bege a kai da kuma tabbatar da abin da ba mu gani ba.
Shows Read in context, Share and Copy.