44 Bible Verses About Cursing
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
5 Haka ma harshe yake, ga shi ɗan ƙanƙanin gaɓar jiki ne, amma sai manyan fariya. Ku dubi yadda ɗan ƙaramin ƙyastu yake ƙuna wa babban jeji wuta mana. 6 Harshe ma wuta ne! A cikin duk gaɓoɓinmu, harshe shi ne tushen kowace irin mugunta, mai ɓata mutum gaba ɗaya, mai zuga zuciyar mutum ta tafasa, shi kuwa jahannama ce take zuga shi.
7 Kowace irin dabba, tsuntsu, masu ja da ciki da kuma halittun da suke cikin teku an sarrafa su kuma mutum ne ya sarrafa, 8 amma ba mutumin da zai iya ya sarrafa harshe. Mugu ne marar hutu, cike da dafi mai kisa.
9 Da harshe mukan yabi Ubangijinmu da kuma Ubanmu, da shi kuma muke la’antar mutane, waɗanda aka halitta a kamannin Allah. 10 Daga wannan baki guda yabo da la’ana suke fitowa. ’Yan’uwana, wannan bai kamata yă zama haka ba. 11 Ruwa mai kyau da kuma ruwan gishiri zai iya fito daga maɓulɓula ɗaya? 12 ’Yan’uwana, itacen ɓaure yana iya haifar ’ya’yan zaitun, ko kuma itacen inabi yă haifi ’ya’yan ɓaure? Haka ma, maɓulɓular ruwan gishiri ba zai iya ba da ruwa mai kyau ba.
13 Wane ne mai hikima da fahimta a cikinku? Bari yă nuna ta ta wurin rayuwarsa mai kyau, ta wurin ayyukan da aka yi cikin tawali’un da suke fitowa daga hikima.
-
27 “Amma ina faɗa muku, ku da kuke ji na, ku ƙaunaci abokan gābanku, ku yi wa masu ƙinku alheri. 28 Ku albarkaci waɗanda suke la’anta ku, ku kuma yi wa waɗanda suke wulaƙanta ku addu’a. 29 In wani ya mare ka a wannan kumatu, juya masa ɗayan ma, in wani ya ƙwace maka babban riga, kada ma ka hana masa ’yar cikin ma. 30 Duk wanda ya roƙe ka abu, ka ba shi. In kuma wani ya yi maka ƙwace, kada ka nema yă mayar maka.
-
29 Kada wata ƙazamar magana ta fita daga bakunanku, sai dai abin da yake da amfani don gina waɗansu bisa ga bukatunsu. Ta haka maganarku za tă zama da amfani ga masu jinta. 30 Kada kuma ku ɓata wa Ruhu Mai Tsarki na Allah rai, wanda da shi aka hatimce ku da shi don ranar fansa. 31 Ku rabu da kowane irin ɗacin rai, haushi da hasala, faɗa da ɓata suna, ku rabu da kowace irin ƙeta.
-
10 Sai Yesu ya kira taron wurinsa ya ce, “Ku saurara ku kuma gane. 11 Abin da yake shiga bakin mutum ba ya ƙazantar da shi, sai dai abin da yake fitowa daga bakinsa, shi ne yake ƙazantar da shi.”
-
14 Ku sa wa masu tsananta muku albarka; ku sa albarka kada fa ku la’anta.
-
10 Dukan waɗanda suka dogara ga kiyaye Doka la’anannu ne, gama a rubuce yake cewa, “La’ananne ne duk wanda bai ci gaba da yi dukan abubuwan da aka rubuta a Littafin Doka ba.” 11 A fili yake ba wanda zai kuɓuta a gaban Allah ta wurin Doka, domin “Mai adalci zai rayu ta wurin bangaskiya.” 12 Doka ba tă dangana ga bangaskiya ba; a maimakon haka, “Mutumin da ya aikata waɗannan abubuwa zai rayu ta wurinsu.” 13 Kiristi ya fanshe mu daga la’anar Doka ta wurin zama la’ana saboda mu, gama a rubuce yake cewa, “La’ananne ne duk wanda aka rataye a kan itace.” 14 Ya fanshe mu domin albarkar da aka yi wa Ibrahim yă zo ga Al’ummai, ta wurin Kiristi Yesu, domin ta wurin bangaskiya mu karɓi alkawarin Ruhu.
-
14 Saboda haka Ubangiji Allah ya ce wa macijin, “Saboda ka yi haka,
“Na la’anta ka cikin dukan dabbobi da kuma cikin dukan namun jeji!
Daga yanzu rubda ciki za ka yi tafiya
turɓaya kuma za ka ci
dukan kwanakin rayuwarka.
15 Zan kuma sa ƙiyayya
tsakaninka da macen,
tsakanin zuriyarka da zuriyarta.
Zai ragargaje kanka,
kai kuma za ka sari ɗiɗɗigensa.”
16 Sa’an nan ya ce wa macen,
“Zan tsananta naƙudarki ainun,
da azaba kuma za ki haifi ’ya’ya.
Za ki riƙa yin marmarin mijinki
zai kuwa yi mulki a kanki.”
17 Ga Adamu kuwa ya ce, “Saboda ka saurari matarka, ka kuma ci daga itacen da na ce, ‘Kada ka ci,’
“Za a la’anta ƙasa saboda kai.
Da wahala za ka ci daga cikinta dukan kwanakin rayuwarka.
18 Za tă ba ka ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya
za ka kuwa ci ganyayen gona.
19 Da zuffan goshinka za ka ci abincinka har ka koma ga ƙasa,
da yake daga cikinta aka yi ka.
Gama kai turɓaya ne,
kuma ga turɓaya za ka koma.”
-
26 Ga shi, a yau, ina sa a gabanku albarka da kuma la’ana, 27 albarka in kun yi biyayya da umarnan Ubangiji Allahnku, da nake ba ku; 28 la’ana in ba ku yi biyayya da umarnan Ubangiji Allahnku, kuka kuma juya daga hanyar da na umarce ku, ta wurin bin waɗansu alloli, waɗanda ba ku sani ba. 29 Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya kawo ku cikin ƙasar da za ku shiga ku ci gādonta, sai ku yi shelar albarkun nan a dutsen Gerizim, ku kuma yi na la’ana a dutsen Ebal.
-
33 “Har wa yau dai kun ji an faɗa wa mutane a dā, ‘Kada ka karya alkawarinka, sai dai ka cika alkawaran da ka yi wa Ubangiji.’ 34 Amma ina gaya muku, Kada ku yi rantsuwa sam, ko da sama, domin kursiyin Allah ne; 35 ko da ƙasa, domin matashin ƙafafunsa ne; ko kuma da Urushalima, domin birnin Babban Sarki ne. 36 Kada kuma ka rantse da kanka, domin ba za ka iya mai da ko gashi ɗaya yă zama fari ko baƙi ba. 37 Abin da ya kamata ku ce kawai, shi ne, I, ko A’a. Abin da ya wuce haka kuwa daga wurin Mugun nan yake.
-
2 “Zan mai da kai al’umma mai girma,
zan kuma albarkace ka;
zan sa sunanka yă zama mai girma,
ka kuma zama sanadin albarka.
3 Zan albarkaci duk wanda ya albarkace ka,
in kuma la’anci duk wanda ya la’anta ka,
dukan mutanen duniya
za su sami albarka ta wurinka.”
-
7 Ba za ka yi amfani da sunan Ubangiji Allahnka a banza ba, gama Ubangiji zai hukunta duk wanda ya mai da sunansa banza.
-
17 “Duk wanda ya la’anta mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole a kashe shi.
-
24 Sa’ad da Nuhu ya farka daga buguwarsa ya kuma gane abin da ƙarami ɗansa ya yi, 25 sai ya ce,
“Kan’ana la’ananne ne,
zai zama bawa mafi ƙanƙanta
ga ’yan’uwansa.”
26 Ya kuma ce,
“Albarka ta tabbata ga Ubangiji Allah na Shem!
Bari Kan’ana yă zama bawan Shem.
27 Allah yă ƙara fāɗin ƙasar Yafet;
bari Yafet yă zauna a tentunan Shem,
bari kuma Kan’ana yă zama bawansa.”
-
17 Yana jin daɗin la’antarwa,
bari yă dawo a kansa;
ba ya son sa albarka,
bari kada kowa yă sa masa albarka.
18 Ya sa la’antarwa kamar rigarsa;
ta shiga cikin jikinsa kamar ruwa,
cikin ƙasusuwansa kamar mai.
-
7 Cikin kowane abu ka zama musu misali mai kyau ta wurin aikata abin da yake nagari. A cikin koyarwarka ka nuna mutunci da ƙwazo 8 da kuma sahihanci cikin maganar da ba za a iya kushewa ba, domin masu gāba da kai su ji kunya, su kuma rasa wani mugun abin da za su faɗa game da mu.
-
34 Ku macizai, ta yaya ku da kuke mugaye za ku iya magana kirki? Gama daga baki, mutum yakan faɗi abin da yake cikin zuciya. 35 Mutumin kirki yakan fito da abubuwa masu kyau daga ajiyar da aka a yi cikinsa, mugun mutum kuwa yakan fito da mugayen abubuwa daga cikin muguntar da aka yi ajiya a cikinsa. 36 Amma ina gaya muku cewa mutane za su ba da lissafi a ranar shari’a a kan kowace kalmar banza da suka faɗa. 37 Gama ta wurin kalmominka za a kuɓutar da kai, kuma ta wurin kalmominka za a hukunta ka.”
-
13 “Maƙogwaronsu kamar buɗaɗɗun kaburbura ne,
harsunansu suna yin ƙarya.”
“Dafin mugun maciji yana a leɓunansu.”
14 “Bakunansu sun cike da la’ana da ɗacin rai.”
15 “Ƙafafunsu suna saurin kai su zuwa ga zub da jini;
16 hallaka da baƙin ciki suna ko’ina a hanyoyinsu,
17 ba su kuma san hanyar salama ba.”
18 “Babu tsoron Allah a idanunsu.”
-
8 Amma yanzu dole ku raba kanku da dukan ire-iren abubuwan nan. Ku daina fushi, ku daina ƙiyayya da ƙeta. Ku bar ɓatan suna da kuma ƙazamar magana daga leɓunanku.
-
14 “ ‘Kada ku zagi kurma, ko ku sa abin tuntuɓe a gaban makaho, amma ku ji tsoron Allahnku. Ni ne Ubangiji.
-
9 “ ‘In wani ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole a kashe shi. Domin ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, alhakin jininsa zai zauna a kansa.
-
3 Kada a ma ambaci fasikanci, da kowane irin aikin lalata, ko kwaɗayi a tsakaninku, domin bai dace da mutane masu tsarki na Allah ba. 4 Haka ma bai kamata a sami datti, ƙazamar magana, ko zancen banza a cikinku ba, domin ba su dace ba, a maimakon haka sai ku yi ta yin godiya.
-
2 Kamar gwara mai yawo ko alallaka mai firiya,
haka yake da la’anar da ba tă dace tă kama ka ba take.
-
21 “Kun dai ji an faɗa wa mutanen dā cewa, ‘Kada ka yi kisankai; kuma duk wanda ya yi kisankai za a hukunta shi.’ 22 Amma ina gaya muku, duk wanda ya yi fushi da ɗan’uwansa, za a hukunta shi. Kuma duk wanda ya ce wa ɗan’uwansa ‘Raka,’ za a kai shi gaban Majalisa. Amma duk wanda ya ce, ‘Kai wawa!’ Zai kasance a hatsarin shiga jahannama ta wuta.
-
26 In wani ya ɗauki kansa mai addini ne duk da haka bai ƙame harshensa ba, ruɗin kansa yake yi addininsa kuwa banza ne.
-
28 “Kada ku yi maganar saɓo ga Allah, ko ku la’anta mai mulkin mutanenku.
-
23 “ ‘Firist zai rubuta waɗannan la’anoni a littafi, sa’an nan yă wanke su cikin ruwa mai ɗaci.
-
1 In kun yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku, kuka kuma lura, kuka bi dukan umarnan da na ba ku a yau, Ubangiji Allahnku zai sa ku bisa dukan al’ummai a duniya. 2 Dukan waɗannan albarku za su sauko muku, su zama naku, in kuka yi biyayya ga Ubangiji Allahnku.
3 Za ku zama masu albarka a cikin birni, za ku kuma zama masu albarka har a ƙauye.
4 ’Ya’yanku za su zama masu albarka, haka ma hatsin gonakinku da kuma ’ya’yan dabbobinku, wato, ’ya’yan shanu da ’yan tumakinku.
5 Za a albarkaci kwandonku da kwanon kwaɓan kullunku.
6 Za ku zama masu albarka sa’ad da kuka shiga, za ku kuma zama masu albarka sa’ad da kuka fita.
-
13 ka kiyaye harshenka daga mugunta
da kuma leɓunanku daga faɗar ƙarairayi.
14 Juyo daga mugunta ku yi alheri;
nemi salama ku kuma yi ƙoƙarin samunta.
-
8 “Mutum zai iya yi wa Allah fashi ne? Duk da haka kun yi mini fashi.
“Amma sai kuka ce, ‘Yaya muka yi maka fashi?’
“A wajen zakka da hadayu. 9 Kuna ƙarƙashin la’ana, dukan al’ummarku, domin kuna yin mini fashi. 10 Ku kawo dukan zakka cikin gidan ajiya, don a kasance da abinci a gidana. Ku gwada ni a wannan ku ga, ko ba zan buɗe taskokin sama in zubo muku albarka mai yawa, wadda har ba za ku rasa wurin sa ta ba, in ji Ubangiji Maɗaukaki. 11 Zan hana ƙwari su cinye hatsinku. Kuringar inabi a gonakinku kuma ba za su zubar da ’ya’yansu kafin su nuna ba,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
-
45 Mutumin nagari yakan nuna abubuwa nagari daga cikin nagarta da yake a ɓoye a zuciyarsa, mugun mutum kuwa yakan nuna mugayen abubuwa daga muguntar da take a ɓoye a zuciyarsa. Gama baki yakan faɗa abin da ya cika zuciya ne.”
-
12 ’Yan’uwana, fiye da kome, kada ku yi rantsuwa ko da sama, ko da ƙasa ko da wani abu dabam. Bari “I” naku yă zama “I”. “A’a” naku kuma yă zama “A’a”, don kada a hukunta ku.
-
11 Yanzu, kai la’ananne ne, an kuma kore ka daga ƙasa wadda ta buɗe bakinta ta shanye jinin ɗan’uwanka daga hannunka. 12 In ka nome ƙasa, ba za tă ƙara ba ka hatsinta ba. Za ka kuma zama mai yawo barkatai a duniya.”
13 Kayinu ya ce wa Ubangiji, “Horon nan ya sha ƙarfina. 14 Ga shi, yau kana kori na daga ƙasar, zan zama a ɓoye daga fuskarka, zan kuma zama mai yawo barkatai, duk wanda ya same ni kuwa zai kashe ni.”
15 Amma Ubangiji ya ce masa, “Ba haka ba ne! Duk wanda ya kashe Kayinu, za a ninƙa hukuncinsa har sau bakwai.” Sa’an nan Ubangiji ya sa wa Kayinu alama don duk wanda ya same shi kada yă kashe shi. 16 Saboda haka Kayinu ya yi tafiyarsa ya rabu da Ubangiji, ya je ya zauna ƙasar Nod a gabashin Eden.
-
21 Da Ubangiji ya ji ƙanshi mai daɗi, sai ya ce a zuciyarsa, “Ba zan ƙara la’anta ƙasa saboda mutum ba, ko da yake dukan tunanin zuciyar mutum mugu ne tun yana ƙarami. Ba kuwa zan ƙara hallaka dukan halittu masu rai, kamar yadda na yi ba.
-
12 A ce baba ya tattaɓa ni fa? Zai zama kamar ina ruɗunsa ne, wannan fa zai jawo mini la’ana a maimakon albarka.”
13 Mahaifiyarsa ta ce masa, “Ɗana, bari la’anar tă fāɗo a kaina. Kai dai yi abin da na faɗa, jeka ka kawo mini su.”
-
12 “ ‘Kada ku rantse bisa ƙarya da sunana, ta haka har ku ƙasƙantar da sunan Allahnku. Ni ne Ubangiji.
-
23 Daga nan sai Elisha ya tafi Betel. Yayinda yake tafiya a hanya, sai waɗansu matasa suka fito daga cikin gari, suka yi masa dariya suna cewa, “Ka haura, ya kai mai kai marar gashi! Ka haura, kai mai kai marar gashi!” 24 Sai ya juya ya dube su, ya la’anta su da sunan Ubangiji. Sai beyar guda biyu suka fito daga jeji suka hallaka matasa arba’in da biyu daga cikinsu.
-
9 Matarsa ta ce masa, “Har yanzu kana nan da amincinka? Ka la’anta Allah ka mutu!”
-
7 Bakinsa ya cika da zage-zage da ƙarairayi da kuma barazana;
wahala da mugunta suna a ƙarƙashin harshensa.
8 Yakan yi kwanto kusa da ƙauyuka;
daga kwanton yakan kashe marar laifi.
Yana kallon waɗanda za su shiga hannunsa a ɓoye.
-
12 Saboda zunuban bakunansu,
saboda maganganun leɓunansu,
bari a kama su cikin fariyarsu.
Saboda zage-zage da ƙarairayin da suke yi,
-
24 Ka kau da muguwar magana daga bakinka;
ka yi nesa da magana marar kyau daga leɓunanka.
-
21 Harshe yana da ikon rai da mutuwa,
kuma waɗanda suke ƙaunarsa za su ci amfaninsa.
-
18 Amma abubuwan da suke fitowa ta baki suna fitowa ne daga zuciya, su ne kuma suke ƙazantar da mutum. 19 Gama daga zuciya ne mugayen tunani, kisankai, zina, fasikanci, sata, shaidar ƙarya, ɓatan suna, suka fitowa. 20 Waɗannan su ne suke ƙazantar da mutum; amma cin abinci ba tare da wanke hannuwa ba, ba ya ƙazantar da mutum.”
-
74 Sai ya fara la’antar kansa, yana ta rantsuwa yana ce musu, “Ban ma san mutumin nan ba!”
Nan da take, sai zakara ya yi cara.
-
6 Bari maganarku kullum ta zama da ladabi da kuma daɗin ji, domin ku san amsar da ta dace ku ba wa kowa.
Shows Read in context, Share and Copy.