68 Bible Verses About Redemption

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Redemption
  1. 13 Saboda haka, ku shirya kanku don aiki; ku zama masu kamunkai; ku kafa begenku duka a kan alherin da za a ba ku sa’ad da aka bayyana Yesu Kiristi. 14 Kamar ’ya’ya masu biyayya, kada ku bi mugayen sha’awace-sha’awacen da dā kuke da su sa’ad da kuke rayuwa a cikin jahilci. 15 Amma kamar yadda wanda ya kira ku yake mai tsarki, haka ku ma sai ku kasance masu tsarki cikin dukan abubuwan da kuke yi; 16 gama a rubuce yake cewa, “Ku zama masu tsarki, domin ni mai tsarki ne.”

    17 Tun da yake kuna kira ga Uba wanda yake yin wa kowane mutum shari’a bisa ga ayyukansa ba bambanci, sai ku yi rayuwarku a nan kamar baƙi cikin tsoro mai bangirma. 18 Gama kun san cewa ba da abubuwa masu lalacewa kamar azurfa ko zinariya ce aka fanshe ku daga rayuwar banza da kuka karɓa daga kakanni-kakanninku ba, 19 sai dai an fanshe ku da jini mai daraja na Kiristi, ɗan rago marar aibi ko lahani. 20 An zaɓe shi kafin halittar duniya, amma an bayyana shi a zamanin ƙarshe saboda ku. 21 Ta gare shi ne kuka gaskata da Allah, wanda ya tā da shi daga matattu, aka kuma ɗaukaka shi, ta haka bari bangaskiyarku da begenku su kasance ga Allah.

  2. 3 Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ya kawo mana kowace albarka ta ruhaniya daga sama. 4 Gama ya zaɓe mu a cikin Kiristi tun dā can, kafin ma a halicci duniya don mu zama masu tsarki da kuma marasa aibi a gabansa. 5 A cikin ƙauna, ya ƙaddara mu zama ’ya’yansa na riƙo ta wurin Kiristi Yesu, bisa ga nufinsa na alheri. 6 Ya yi haka don mu yabi Allah saboda alherin da ya yi mana saboda mu na ƙaunataccen Ɗansa ne. 7 A cikinsa muka sami fansa ta wurin jininsa, wato, yafewar zunubanmu. Kiristi ya yi wannan saboda yawan alherin Allah 8 wanda ya ba mu babu iyaka tare da dukan hikima da fahimta. 9 Allah ya yi abin da ya nufa, ya kuma sanar mana shirin asirin da ya riga ya shirya yă cika ta wurin Kiristi. 10 Nufinsa ke nan, idan lokaci ya cika, yă harhaɗa dukan abubuwa a ƙarƙashin ikon Kiristi, wato, dukan abubuwan da suke sama da abubuwan da suke ƙasa.

  3. 21 Amma yanzu an bayyana wani adalci daga Allah, wannan adalcin bai danganta ga doka ba, Doka da Annabawa suna ba da shaida game da wannan adalci. 22 Wannan adalcin Allah yana zuwa ta wurin bangaskiya a cikin Yesu Kiristi ga dukan waɗanda suka ba da gaskiya ne. Ba bambanci, 23 gama duka sun yi zunubi suka kuma kāsa ga ɗaukakar Allah, 24 an kuma kuɓutar da su kyauta ta wurin alherinsa bisa ga aikin fansar da ya zo ta wurin Yesu Kiristi. 25 Allah ya miƙa Yesu Kiristi a matsayin hadayar kafara, ta wurin bangaskiya cikin jininsa. Ya yi haka domin yă nuna adalcinsa, domin a cikin haƙurinsa bai hukunta zunuban da aka aikata a dā ba 26 ya yi haka domin yă nuna adalcinsa a wannan lokaci, saboda yă zama mai adalci da mai kuɓutar da waɗanda suke ba da gaskiya a cikin Yesu.

    27 To, me za mu yi taƙama a kai? Babu wani abin da zamu yi taƙama a kai. A kan wace ƙa’ida ce za mu yi taƙama? Ta hanyar bin doka ne? A’a, sai dai ta wurin bangaskiya. 28 Gama mun tsaya a kan cewa ta wurin bangaskiya ne ake kuɓutar da mutum, ba ta wurin kiyaye doka ba.

  4. 15 Kiristi shi ne surar da ake gani na Allah wanda ba a iya gani, ɗan fari a kan dukan halitta. 16 Ta wurinsa aka halicci dukan abu, abubuwan da suke cikin sama da abubuwan da suke a duniya, waɗanda ake gani, da waɗanda ba a gani, ko kursiyoyi ko ikoki ko masu mulki ko hukumomi; an halicci dukan abu ta wurinsa da kuma dominsa ne. 17 Ya kasance kafin dukan abu, kuma a cikinsa ne dukan abubuwa suke a harhaɗe. 18 Shi ne kuma kan ikkilisiya, wadda take jikinsa. Shi ne mafari da kuma na farko da ya tashi daga matattu, domin a cikin kowane abu yă zama mafifici. 19 Gama Allah ya ji daɗi yă sa dukan cikarsa ta kasance a cikin Kiristi, 20 ta wurin Kiristi ne ya komar da kome zuwa ga kansa. Ya kawo salama ga abubuwan da suke ƙasa da abubuwan da suke sama, ta wurin jinin Kiristi da ya zubar a kan gicciye.

    21 A dā kuna a ware da Allah, kuka kuma zama abokan gāba a cikin tunaninku saboda mugun halinku. 22 Amma Ɗansa ya zama mutum ya kuma mutu. Saboda haka Allah ya yi sulhu da ku, yanzu kuwa ya bar ku ku tsaya a gabansa da tsarki, marasa aibi, da kuma marasa abin zargi.

  5. 11 Gama alherin Allah mai kawo ceto ya bayyana ga dukan mutane. 12 Yana koya mana mu ce, “A’a” ga rashin tsoron Allah da kuma sha’awace-sha’awacen duniya, mu kuma yi rayuwa ta kamunkai, ta adalci da kuma ta tsoron Allah a cikin wannan zamani, 13 yayinda muke sauraron begenmu mai albarka bayyanuwar ɗaukakar Allahnmu mai girma da kuma Mai Cetonmu, Yesu Kiristi, 14 wanda ya ba da kansa dominmu don yă fanshe mu daga dukan mugunta yă kuma tsarkake wa kansa mutanen da suke nasa, waɗanda suke marmarin yin abin da yake nagari.

  6. 11 Sa’ad da Kiristi ya zo a matsayin babban firist na kyawawan abubuwan da suka riga suka kasance a nan, ya bi ta cikin tabanakul mafi girma da kuma mafi cikakke wanda ba mutum ne ya yi ba, wato, ba na wannan halitta ba. 12 Bai shiga ta wurin jinin awaki da na maruƙa ba; amma ya shiga Wuri Mafi Tsarki sau ɗaya tak ta wurin jininsa, bayan ya samo madawwamiyar fansa. 13 In har akan yayyafa jinin awaki da na bijimai da kuma tokar karsanar a kan waɗanda suke marasa tsabta bisa ga al’ada, a tsarkake su yadda za su zama masu tsabta a waje, 14 balle jinin Kiristi, wanda ta wurin Ruhu madawwami ya miƙa kansa marar aibi ga Allah, ai, zai tsabtacce lamirinmu daga ayyukan da suke kai ga mutuwa, don mu bauta wa Allah mai rai!

    15 Saboda haka Kiristi shi ne matsakancin sabon alkawari, don waɗanda aka kira su sami madawwamin gādon da aka yi alkawari, yanzu da ya mutu a matsayin mai fansa don yă ’yantar da su daga zunuban da aka aikata a ƙarƙashin alkawari na farko.

  7. 1 Abin da nake nufi shi ne, muddin magāji yana ɗan yaro ne tukuna, babu bambanci tsakaninsa da bawa, ko da yake shi ne da mallakar kome. 2 Yana ƙarƙashin iyayen goyonsa da masu riƙon amana har yă zuwa cikar lokacin da mahaifinsa ya sa. 3 Haka yake, sa’ad da muke ’yan yara, mun kasance cikin bauta a ƙarƙashin ƙa’idodin duniya. 4 Amma da lokacin da aka tsara ya yi sosai, sai Allah ya aiki Ɗansa, haifaffe daga mace, haifaffe a ƙarƙashin Doka, 5 domin yă fanshi waɗanda suke a ƙarƙashin doka, saboda mu sami cikakken matsayin zaman ’ya’ya. 6 Da yake ku ’ya’ya ne, sai Allah ya aiko da Ruhun Ɗansa a cikin zukatanmu, Ruhun da yake kira, “Abba, Uba.” 7 Saboda haka kai ba bawa ba ne kuma, kai ɗa ne; da yake kuwa kai ɗa ne, Allah ya mai da kai magāji.

  8. 13 Kiristi ya fanshe mu daga la’anar Doka ta wurin zama la’ana saboda mu, gama a rubuce yake cewa, “La’ananne ne duk wanda aka rataye a kan itace.” 14 Ya fanshe mu domin albarkar da aka yi wa Ibrahim yă zo ga Al’ummai, ta wurin Kiristi Yesu, domin ta wurin bangaskiya mu karɓi alkawarin Ruhu.

  9. 18 A ganina, wuyar da muke sha a wannan lokaci ba su isa a kwatanta da ɗaukakar da za a bayyana a cikinmu ba. 19 Halitta tana jira da marmari ta ƙosa ta ga bayyanuwar ’ya’yan Allah. 20 Gama an sa halitta a cikin wulaƙanci, ba da son ta ba, sai dai ta wurin nufin wannan da ya mai da ita haka, da bege 21 cewa za a ’yantar da halitta kanta daga bautarta ga ruɓewa a kuma kawo ta cikin ’yancin ɗaukakar ’ya’yan Allah.

    22 Mun san cewa dukan halitta tana nishi sai ka ce mace mai naƙuda har yă zuwa wannan lokaci. 23 Ba haka kaɗai ba ma, mu kanmu da muke da nunan fari na Ruhu, muna nishi a ciki-cikinmu yayinda muke jira da marmari a maishe mu ’ya’yan riƙo na Allah, fansar jikunanmu.

  10. 1 To, fa, ga abin da Ubangiji yana cewa,

    shi da ya halicce ka, ya Yaƙub,

    shi da ya siffanta ka, ya Isra’ila,

    “Kada ka ji tsoro, gama na fanshe ka;

    na kira ka da suna; kai nawa ne.

    2 Sa’ad da kuka bi ta ruwaye,

    zan kasance tare da ku;

    sa’ad da kuka bi ta koguna,

    ba za su kwashe ku ba.

    Sa’ad da kuke tafiyata cikin wuta,

    ba za tă ƙone ku ba;

    harsunan wutar ba za su ƙone ku ba.

    3 Gama ni ne Ubangiji, Allahnku,

    Mai Tsarkin nan na Isra’ila, Mai Cetonku;

    na bayar da Masar don fansa,

    Kush da Seba a maimakonku.

    4 Da yake ku masu daraja da kuma girma ne a idona,

    saboda kuma ina ƙaunarku,

    zan ba da mutane a maimakonku,

    al’umma kuma domin ranku.

  11. 8 Bayan ya karɓa, sai halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan nan ashirin da huɗu suka fāɗi ƙasa a gaban Ɗan Ragon. Kowannensu yana da garaya kuma suna riƙe da kaskon zinariya cike da turare, waɗanda suke addu’o’in tsarkaka. 9 Suka rera sabuwar waƙa,

    “Ka cancanci ka karɓi naɗaɗɗen littafin

    ka kuma buɗe hatimansa,

    domin an kashe ka,

    da jininka kuma ka sayi mutane wa Allah,

    daga kowace kabila da harshe da mutane da kuma al’umma.

    10 Ka mai da su masarauta da kuma firistoci, don su yi wa Allahnmu hidima,

    kuma za su yi mulki a duniya.”

    11 Sai na duba na kuma ji muryar mala’iku masu yawa, yawansu kuwa ya kai dubu dubbai, da kuma dubu goma sau dubu goma. Suka kewaye kursiyin da halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan nan. 12 Da babbar murya suka rera,

    “Macancanci ne Ɗan Ragon nan da aka kashe,

    don yă sami iko da wadata da hikima da ƙarfi

    da girma da ɗaukaka da kuma yabo!”

    13 Sa’an nan na ji kowace halitta a sama da ƙasa da ƙarƙashin ƙasa da kuma bisan teku, da kome da yake cikinsu yana rerawa,

    “Gare shi mai zama a kan kursiyin da kuma ga Ɗan Ragon

    yabo da girma da ɗaukaka da iko,

    sun tabbata har abada abadin!”

    14 Sai halittu huɗun nan masu rai suka ce, “Amin”, dattawan kuma suka fāɗi suka yi sujada.

  12. 24 Ko’ina a ƙasar da kuke da mallaka, dole ku tanadar da dama fansar ƙasar.

    25 “ ‘In ɗaya daga cikin mutanen ƙasarku ya talauta, ya kuma sayar da mallakarsa, sai danginsa na kusa yă je yă fanshi abin da mutumin ƙasarsa ya sayar. 26 In mutumin ba shi da wanda zai fansa masa ita, shi kansa kuwa ya wadace, ya kuma sami isashen halin fansarta, 27 sai yă lasafta yawan shekarun da aka yi tun da an sayar da filin. Kuɗin filin zai dangana ga yawan shekarun da suka rage kafin shekara hamsin ta murna da za tă zo; sa’an nan zai iya koma ga mallakarsa. 28 Amma in bai sami halin sāke biyansa ba, abin nan da ya sayar zai ci gaba da zama mallakar mai sayan, sai Shekara ta Murna. Za a maido masa da ita a Shekara ta Murna, sa’an nan zai iya koma ga mallakarsa.

  13. 25 Na san wanda zai fanshe ni yana nan da rai,

    kuma a ƙarshe zai tsaya a kan duniya.

    26 Kuma bayan an hallaka fatata,

    duk da haka a cikin jiki zan ga Allah.

    27 Zan gan shi da kaina

    da idanuna, Ni, ba wani ba ne.

    Zuciyata ta cika da wannan tunani!

  14. 16 Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami. 17 Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yă yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin yă ceci duniya ta wurinsa. 18 Duk wanda ya gaskata da shi ba za a yi masa hukunci ba, amma duk wanda bai gaskata ba an riga an yi masa hukunci domin bai gaskata da sunan wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗan Allah ba.

  15. 7 Ba wani da zai iya ceton ran wani

    ko yă ba wa Allah kuɗin fansa saboda shi,

    8 kuɗin fansa domin rai yana da tsada,

    babu abin da za a biya da ya taɓa isa,

    9 da zai sa yă ci gaba da rayuwa har abada

    yă hana shi shigan kabari yă ruɓa.

  16. 30 Kada kuma ku ɓata wa Ruhu Mai Tsarki na Allah rai, wanda da shi aka hatimce ku da shi don ranar fansa. 31 Ku rabu da kowane irin ɗacin rai, haushi da hasala, faɗa da ɓata suna, ku rabu da kowace irin ƙeta.

  17. 6 “Saboda haka, ka ce wa Isra’ilawa, ‘Ni ne Ubangiji, zan kuma fitar da ku daga bauta ta Masarawa. Zan ’yantar da ku daga zama bayinsu, da ƙarfina zan fanshe ku, in kawo hukunci mai zafi a kansu, don in cece ku. 7 Zan ɗauke ku tamƙar mutanena, in kuma zama Allahnku. Sa’an nan za ku sani Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga wahalar Masarawa. 8 Zan kuwa kawo ku a ƙasar da na rantse da hannun da na ɗaga sama, cewa zan ba wa Ibrahim, wa Ishaku, da kuma wa Yaƙub. Zan ba da ita gare ku gādo. Ni ne Ubangiji.’ ”

  18. 44 Sai Ubangiji ya kuma yi magana da Musa ya ce, 45 “Ka ɗauki Lawiyawa a maimakon dukan ’ya’yan fari na Isra’ila, dabbobin Lawiyawa kuma a maimakon dabbobinsu. Lawiyawa za su zama nawa. Ni ne Ubangiji. 46 Don a fanshi ’ya’yan fari 273 na Isra’ilawa da suka fi Lawiyawa yawa, 47 ka karɓi shekel biyar domin kowannensu, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, wanda yake da nauyin gera ashirin. 48 Ka ba wa Haruna da ’ya’yansa kuɗin fansar da ya haura kai na ’ya’yan farin Isra’ilawa.”

    49 Haka, Musa ya karɓi kuɗin fansar waɗanda suka haura yawan Lawiyawa. 50 Daga ’ya’yan fari na Isra’ilawa, ya karɓi azurfa masu nauyin shekel 1,365, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri. 51 Sa’an nan Musa ya ba da kuɗin fansar ga Haruna da ’ya’yansa, yadda maganar Ubangiji ta umarce shi.

  19. 21 “Tuna da waɗannan abubuwa, ya Yaƙub,

    gama kai bawana ne, ya Isra’ila.

    Na yi ka, kai bawana ne;

    Ya Isra’ila, ba zan manta da kai ba.

    22 Na shafe laifofinka kamar girgije,

    zunubanka kamar hazon safe.

    Ka komo wurina,

    gama na kuɓutar da kai.”

    23 Ku rera don farin ciki, ya sammai, gama Ubangiji ya aikata wannan;

    ku yi sowa, ya duniya a ƙarƙashi.

    Ku ɓarke da waƙoƙi, ku duwatsu,

    ku jeji da dukan itatuwanku,

    gama Ubangiji ya kuɓutar da Yaƙub,

    ya nuna ɗaukakarsa a cikin Isra’ila.

  20. 25 Yesu ya kira su wuri ɗaya ya ce, “Kun san cewa masu mulkin Al’ummai sukan nuna musu iko, hakimansu kuma sukan gasa musu iko. 26 Ba haka zai kasance da ku ba. Maimakon haka, duk mai son zama babba a cikinku, dole yă zama bawanku, 27 kuma duk mai son zama shugaba, dole yă zama bawanku, 28 kamar yadda Ɗan Mutum bai zo don a bauta masa ba, sai dai don yă yi bauta, yă kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.”

  21. 28 Ku lura da kanku da dukan garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu kula da shi. Ku zama masu kiwon ikkilisiyar Allah, wadda ya saya da jininsa.

  22. 1 Sai Hannatu ta yi addu’a ta ce,

    “Zuciyata tana farin ciki a cikin Ubangiji;

    a cikin Ubangiji an sa ina jin daɗi ƙwarai.

    Na buɗe bakina na yi wa abokan gābana dariya.

    Kai! Ina murna domin ka cece ni!

  23. 11 “Bayan Ubangiji ya kawo ku cikin ƙasar Kan’aniyawa, ya kuma ba da ita yadda ya alkawarta muku da rantsuwa, ku da kakanninku, 12 sai ku miƙa kowane ɗan fari ga Ubangiji. Duk ɗan farin dabbobinku na Ubangiji ne. 13 Amma a fanshi kowane ɗan farin jakinku da ɗan rago. In kuwa ba za ku fanshe shi ba, sai ku karye wuyansa. Sai ku fanshe kowane ɗan farin daga cikin ’ya’yanku.

    14 “A kwanaki masu zuwa, in ɗanka ya tambaye ka, ‘Mene ne manufar wannan?’ Ka faɗa masa cewa, ‘Da hannu mai iko Ubangiji ya fito da mu daga Masar, daga ƙasar bauta. 15 Sa’ad da Fir’auna ya taurare zuciyarsa, bai yarda ya sallame mu ba, sai Ubangiji ya kashe dukan ’ya’yan farin ƙasar Masar, na mutum da na dabba, gaba ɗaya. Domin haka nake yin hadaya ga Ubangiji da ’ya’yan fari, maza, da suka fara buɗe mahaifa, amma nakan fanshi dukan ’ya’yan farina maza.’ 16 Za tă kuma zama alama a hannunku da kuma shaida a goshinku cewa Ubangiji ya fito da mu daga Masar da hannunsa mai iko.”

  24. 5 Gama Allah ɗaya ne, matsakanci kuma ɗaya tsakanin Allah da mutane, shi ne kuwa Kiristi Yesu, 6 wanda ya ba da kansa fansa domin dukan mutane, shaidar da aka bayar a daidai lokaci. 7 Don haka ne aka sa ni mai wa’azi, da manzo kuma, gaskiya nake faɗa, ba ƙarya ba, na kuma zama malami mai koya wa al’ummai al’amarin bangaskiya da kuma na gaskiya.

  25. 6 Kun ga, a daidai lokaci, yayinda muke marasa ƙarfi, Kiristi ya mutu saboda waɗanda ba su san Allah ba. 7 Da ƙyar wani yă mutu saboda mai adalci, ko da yake saboda mutumin kirki wani zai iya ƙarfin hali yă mutu. 8 Amma Allah ya nuna mana ƙaunarsa a wannan. Tun muna masu zunubi tukuna, Kiristi ya mutu dominmu.

    9 Da yake yanzu mun sami zama marasa laifi ta wurin jininsa, ashe kuwa za a cece mu daga fushin Allah ta wurinsa! 10 Gama in kuwa, sa’ad da muke abokan gāban Allah, aka sulhunta mu da shi ta wurin mutuwar Ɗansa, ashe, da yake an sulhunta mu, za mu sami ceto ta wurin ransa! 11 Ba ma haka yake kawai ba, har muna farin ciki da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ta wurinsa yanzu muka sami sulhu.

  26. 7 Ya Isra’ila, sa zuciya ga Ubangiji,

    gama tare da Ubangiji akwai ƙauna marar ƙarewa

    kuma tare da shi akwai cikakkiyar fansa.

    8 Shi kansa zai fanshi Isra’ila

    daga dukan zunubansu.

  27. 45 Gama ko Ɗan Mutum ma, bai zo domin a bauta masa ba, amma don yă yi bauta, yă kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.”

  28. 25 “Za a yi alamu a cikin rana, da cikin wata, da cikin taurari. A duniya, al’ummai za su yi baƙin ciki, su kuma rikice don tsoro, saboda ruri da kuma tafasar teku. 26 Mutane za su suma don tsoro, za su kuma yi fargaba, a kan abin da yake zuwa a bisan duniya, gama za a girgiza duniyar taurarin sararin sama. 27 A lokacin ne za su ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin girgije, da iko, da ɗaukaka mai girma. 28 Sa’ad da waɗannan abubuwa sun fara faruwa, ku tashi tsaye, ku ɗaga kawunanku, domin fansarku yana matsowa kusa.”

  29. 68 “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila,

    domin ya zo ya kuma fanshe mutanensa.

    69 Ya tā mana ƙahon ceto

    a gidan bawansa Dawuda

    70 (yadda ya yi magana tun tuni ta wurin annabawansa masu tsarki),

    71 cewa zai cece mu daga abokan gābanmu

    daga kuma hannun dukan waɗanda suke ƙinmu

    72 don yă nuna jinƙai ga kakanninmu,

    yă kuma tuna da alkawarinsa mai tsarki,

    73 rantsuwar da ya yi wa mahaifinmu Ibrahim,

    74 don yă kuɓutar da mu daga hannun abokan gābanmu,

    yă kuma sa mu iya yin masa hidima babu tsoro,

    75 cikin tsarki da adalci a gabansa dukan kwanakinmu.

  30. 22 Gama wanda yake bawa sa’ad da Ubangiji ya kira shi, ’yantacce ne na Ubangiji; haka ma, wanda yake ’yantacce sa’ad da aka kira shi, bawa ne na Kiristi. 23 Da tsada fa aka saye ku, kada ku zama bayin mutane.

  31. 3 Suka kuwa rera sabuwar waƙa a gaban kursiyin da kuma a gaban halittu huɗun nan masu rai, da kuma a gaban dattawa. Ba wanda ya iya koyon waƙar sai mutanen nan 144,000 da aka fansa daga duniya. 4 Waɗannan su ne waɗanda ba su ƙazantar da kansu da mata ba, gama sun kiyaye kansu da tsarki. Suna bin Ɗan Ragon duk inda ya tafi. Su ne aka saya daga cikin mutane aka kuwa miƙa su kamar ’ya’yan fari ga Allah da kuma Ɗan Ragon.

  32. LITTAFI NA BIYAR

    1 Ku yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi;

    ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.

    2 Bari fansassu na Ubangiji su faɗa wannan,

    su da aka fansa daga hannun maƙiyi,

    3 su da ya tattara daga ƙasashe,

    daga gabas da yamma, daga arewa da kudu.

  33. 9 Yana ba da ceto ga mutanensa;

    ya kafa alkawarinsa har abada,

    tsarki da banrazana ne sunansa.

  34. 2 Yabi Ubangiji, ya raina,

    kada kuma ka manta dukan alheransa,

    3 wanda yake gafarta dukan zunubai

    yake kuma warkar da dukan cututtuka,

    4 wanda ya fanshi ranka daga rami

    ya naɗa maka rawani da ƙauna da kuma tausayi,

    5 Wanda ya ƙosar da kai da abubuwa masu kyau

    domin a sabunta ƙuruciyarka kamar na gaggafa.

  35. 15 Me za mu ce ke nan? Za mu ci gaba yin zunubi domin ba ma ƙarƙashin doka sai dai ƙarƙashin alheri? Sam, ko kaɗan! 16 Ba ku sani ba cewa sa’ad da kuka miƙa kanku ga wani don ku yi masa biyayya a matsayin bayi, ko ku bayi ne ga zunubi, wanda yake kai ga mutuwa, ko kuwa ga biyayya, wadda take kai ga adalci, ashe, ba kun zama bayi ga wannan da kuke yi wa biyayya ba ke nan? 17 Amma godiya ga Allah don ko da yake a dā ku bayi ne ga ikon zunubi, da dukan zuciyarku kun yi biyayya ga irin koyarwar da aka danƙa muku. 18 An ’yanta ku daga zunubi, kun kuma zama bayi ga aikin adalci.

  36. 5 Cikin hannuwanka na miƙa ruhuna;

    ka cece ni, ya Ubangiji Allah na gaskiya.

  37. 15 Amma Allah zai ceci raina daga kabari;

    tabbatacce zai ɗauke ni zuwa wurinsa. Sela

  38. 57 Ka zo kusa lokacin da na kira ka,

    kuma ka ce mini, “Kada ka ji tsoro.”

    58 Ya Ubangiji, ka goyi bayana;

    ka fanshi raina.

  39. 3 Dukanmu a dā mun yi irin rayuwan nan a cikinsu, muna bin kwaɗayi da sha’awace-sha’awacen jikunanmu da tunaninmu. Kamar sauran mutane, mun cancanci fushin Allah. 4 Amma saboda yawan ƙaunar da yake mana, Allah, wanda yake mai yawan jinƙai, 5 ya ba mu rai sa’ad da ya tashe Kiristi daga matattu. Ta wurin alherin Allah ne aka cece ku. 6 Allah ya tashe mu tare da Kiristi, ya kuma ba mu wurin zama tare da shi a cikin mulkin samaniya. 7 Allah ya yi haka domin a tsararraki masu zuwa yă nuna yalwar alherinsa da ya wuce misali, an bayyana alheransa da ya yi mana ta wurin Kiristi Yesu. 8 Allah ya cece ku ta wurin alheri sa’ad da kuka ba da gaskiya. Wannan kuwa ba yinku ba ne, kyauta ce daga Allah. 9 Ba kuwa saboda aikin lada ba, don kada wani yă ɗaga kai. 10 Ai, mu aikinsa ne, an sāke halittarmu a cikin Kiristi Yesu musamman domin mu yi kyawawan ayyuka, waɗanda Allah ya tanadar mana tun da fari, mu yi.

  40. 3 Sa’an nan ya ce wa dangin nan mai fansa, “Na’omi, wadda ta dawo daga Mowab, tana so ta sayar da filin da yake na ɗan’uwanmu Elimelek. 4 Na ga ya kamata in jawo hankalinka ga batun in kuma ba da shawara ka saye shi a gaban waɗannan da suke zazzaune a nan da kuma a gaban dattawan jama’a. In kana so ka fanshe shi, to, sai ka yi. Amma in ba za ka yi ba, sai ka faɗa mini, don in sani. Gama babu wani mai izinin yin haka sai kai, ni ne kuwa na biye.”

    Sai ya ce, “Zan fansa.”

    5 Sa’an nan Bowaz ya ce, “A ranar da ka saya filin daga Na’omi da kuma daga Rut mutuniyar Mowab, ka sayi gwauruwar marigayin nan, domin ka riƙe sunan marigayin da kuma kayansa.”

    6 Da jin haka, sai dangin nan mai fansa ya ce, “To, ba zan iya fanshe shi ba don kada in yi wa nawa mallakar rauni. Za ka iya fanshe shi wa kanka. Ni dai ba zan iya ba.”

  41. 14 “Zan fanshe su daga ikon kabari;

    zan cece su daga mutuwa.

    Ina annobanki, ya mutuwa?

    Ina hallakarka, ya kabari?

    “Ba zan ji tausayi ba,

  42. 38 Tana haurawa wurinsu ke nan a wannan lokaci, sai ta yi wa Allah godiya ta kuma yi magana game da yaron nan ga dukan waɗanda suke sauraron fansar Urushalima.

  43. 9 Amma ku zaɓaɓɓu ne, ƙungiyar firistocin babban Sarki, al’umma mai tsarki, jama’a mallakar Allah, domin ku shaida yabon shi wanda ya kira ku daga cikin duhu zuwa haskensa mai banmamaki.

  44. 19 “Ɗan fari na kowane mutum zai zama nawa, har da ɗan farin na dabbobi, ko na garken shanu ko na tumaki. 20 Ku fanshi ɗan farin jaki da na tunkiya, amma in ba ku fanshe shi ba, ku karya wuyansa. Ku fanshi duk ’ya’yan farinku maza.

    “Kada wani yă zo gabana hannu wofi.

  45. 23 Wane ne kuma yake kamar da mutanenka Isra’ila, al’umma guda a duniya wadda Allah ya fita don yă kuɓutar wa kansa, ya kuma yi suna wa kansa, ya kuma aikata manyan abubuwa da kuma al’amuran banmamaki ta wurin korin al’ummai da allolinsu daga gaban mutanenka, waɗanda ka kuɓutar daga Masar? 24 Ka kafa mutanenka Isra’ila kamar naka na kanka har abada, kai kuma, ya Ubangiji, ka zama Allahnsu.

  46. 15 Da hannunka mai ƙarfi ka fanshi mutanenka,

    zuriyar Yaƙub da Yusuf. Sela

  47. 3 Gama ga abin Ubangiji yana cewa,

    “An sayar da ke ba da kuɗi ba,

    kuma ba da kuɗi za a fanshe ki ba.”

  48. 11 Amma na yi rayuwa marar zargi;

    ka cece ni ka kuma yi mini jinƙai.

  49. 9 Ya tsawata wa Jan Teku, ya kuwa bushe;

    ya bi da su ta cikin zurfafa sai ka ce a hamada.

    10 Ya cece su daga hannun maƙiyi;

    daga hannun abokin gāba ya fanshe su.

    11 Ruwaye suka rufe abokan gābansu;

    babu ko ɗaya da ya tsira.

  50. 7 Ga abin da Ubangiji yana cewa,

    Mai Fansa da kuma Mai Tsarkin nan na Isra’ila

    gare shi wanda al’ummai suka rena suka kuma ki,

    ga bawan masu mulki.

    “Sarakuna za su gan ka su kuma miƙe tsaye,

    sarakuna za su gani su kuma rusuna,

    saboda Ubangiji, wanda yake mai aminci,

    Mai Tsarkin nan na Isra’ila, wanda ya zaɓe ka.”

  51. 9 Cikin dukan damuwarsu shi ma ya damu,

    mala’ikan da yake gabansa ya cece su.

    Cikin ƙauna da jinƙai ya fanshe su;

    ya kuma ɗaga su ya riƙe su

    dukan kwanakin dā

  52. 1 ’Ya’yana ƙaunatattu, ina rubuta muku wannan ne don kada ku yi zunubi. Amma in wani ya yi zunubi, muna da wani wanda yake magana da Uba don taimakonmu, wato, Yesu Kiristi, Mai Adalci. 2 Shi ne hadayar kafara saboda zunubanmu, kuma ba don namu kaɗai ba amma har ma da zunuban duniya duka.

  53. 11 Wane ne cikin alloli,

    ya yi kamar ka, ya Ubangiji?

    Wane ne kamar ka,

    mai ɗaukaka cikin tsarki,

    mai banrazana cikin ɗaukaka,

    mai aikata al’ajabai?

    12 “Ka miƙa hannunka na dama,

    ƙasa ta haɗiye abokan gābanka.

    13 A cikin ƙaunarka marar iyaka, za ka bishe

    mutanen da ka fansa.

    A cikin ƙarfinka, za ka bishe su

    zuwa mazauninka mai tsarki.

  54. 7 Ba don kun fi sauran al’ummai yawa ne ya sa Ubangiji ya ƙaunace ku, ya kuma zaɓe ku ba, gama ku ne mafi ƙanƙanta cikin dukan al’ummai. 8 Amma ya zama haka domin Ubangiji ya ƙaunace ku, ya kuma kiyaye rantsuwar da ya yi wa kakanninku da ya fitar da ku da hannu mai ƙarfi, ya kuma cece ku daga ƙasar bauta, daga ikon Fir’auna sarkin Masar.

  55. 22 Ka fanshi Isra’ila, ya Allah,

    daga dukan wahalarsu!

  56. 11 Waɗanda Ubangiji ya fansar za su dawo.

    Za su shiga Sihiyona da waƙoƙi;

    madawwamin farin ciki zai rufe kansu da rawani.

    Murna da farin ciki zai cika su,

    baƙin ciki da nishi zai ɓace.

  57. 21 “Zan cece ka daga hannuwan mugaye

    in ɓamɓare ka daga hannun marasa tausayi.”

  58. 11 Gama Ubangiji zai fanshi Yaƙub

    zai cece su daga hannun waɗanda suka fi su ƙarfi.

  59. 20 An gicciye ni tare da Kiristi. Yanzu ba ni ne nake raye ba, Kiristi ne yake raye a cikina. Rayuwar da nake yi a jiki, ina rayuwa ce ta wurin bangaskiya cikin Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni ya kuma ba da kansa domina.

  60. 9 Sai ya yi tambaya ya ce, “Ke wace ce?”

    Ta amsa ta ce, “Ni ce baranyarka Rut, ka rufe ni ta mayafinka da yake kai dangi, mai fansa ne na kusa.”

  61. 21 Wane ne kuma yake kamar mutanenka Isra’ila, al’umma guda a duniya wadda Allahnta ya fita don yă fanshi mutane wa kansa, ya kuma yi suna wa kansa, ya kuma aikata manyan abubuwa masu banmamaki masu banrazana ta wurin korin al’ummai daga gaban mutanenka, waɗanda ka fansa daga Masar? 22 Ka mai da mutanenka Isra’ila na kanka har abada, kuma kai, ya Ubangiji, ka zama Allahnsu.

  62. 26 Ka tashi ka taimake mu;

    ka cece mu saboda ƙaunarka marar ƙarewa.

  63. 17 Kada ka ɓoye fuskarka daga bawanka;

    ka amsa mini da sauri, gama ina cikin wahala.

    18 Ka zo kusa ka kuɓutar da ni;

    ka fanshe ni saboda maƙiyana.

  64. 23 Leɓunana za su yi sowa don farin ciki

    sa’ad da na rera yabo gare ka,

    ni, wanda ka fansa.

  65. 34 A duk sa’ad da Allah ya kashe su, sai su neme shi;

    sukan juyo a natse gare shi.

    35 Sun tuna cewa Allah ne Dutsensu,

    cewa Allah Mafi Ɗaukaka ne Mai fansarsu.

  66. 5 Gama Mahaliccinki shi ne mijinki,

    Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa,

    Mai Tsarkin nan na Isra’ila ne Mai Fansarki;

    ana ce da shi Allahn dukan duniya.

    6 Ubangiji zai kira

    sai ka ce ke mace ce da aka yashe ta tana kuma damuwa a ranta,

    macen da ta yi aure a ƙuruciya,

    sai kawai aka ƙi ta,” in ji Allahnki.

    7 “Gama a ɗan ƙanƙanen lokaci na rabu da ke,

    amma da ƙauna mai zurfi zan sāke dawo da ke.

    8 Cikin fushi mai zafi

    na ɓoye fuskata daga gare ki na ɗan lokaci,

    amma da madawwamin alheri

    zan ji tausayinki,”

    in ji Ubangiji Mai Fansarki.

  67. 21 Saboda haka na gane wannan ƙa’ida ce take aiki a cikina. Sa’ad da nake so in yi abu mai kyau, sai in ga cewa mugun nan ne nake yi. 22 Gama a ciki-cikina ina farin cikin da dokar Allah; 23 amma ina ganin wata doka tana aiki a gaɓoɓin jikina, tana yaƙi da dokar hankalina, tana kuma sa in zama ɗaurarren dokar zunubin da take aiki a gaɓoɓin jikina. 24 Kaitona! Wane ne zai cece ni daga wannan jiki mai mutuwa? 25 Godiya ga Allah ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu!

    Saboda haka fa, ni kaina a cikin hankalina, ni bawa ne ga dokar Allah, amma a mutuntaka, ni bawa ne ga dokar zunubi.

  68. 1 Sai mala’ikan ya nuna mini kogin ruwan rai, mai ƙyalli kamar madubi, yana gangarawa daga kursiyin Allah da na Ɗan Ragon, 2 yana bin tsakiyar babban titi na birnin. A kowane gefen kogin akwai itacen rai mai ba da ’ya’ya goma sha biyu, yana ba da ’ya’yansa kowane wata. Ganyayen itacen kuwa saboda warkar da al’ummai ne. 3 Ba za a ƙara samun la’ana ba. Kursiyin Allah da na Ɗan Ragon zai kasance a cikin birnin, bayinsa kuma za su yi masa hidima. 4 Za su ga fuskarsa, sunansa kuma zai kasance a goshinsu. 5 Ba za a ƙara yin dare ba. Ba za su bukaci hasken fitila ko hasken rana ba, domin Ubangiji Allah zai haskaka su. Za su kuwa yi mulki har abada abadin.