60 Bible Verses About Mercy

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Mercy
  1. 1 Ku kam, a dā ku matattu ne saboda laifofinku da kuma zunubanku. 2 Kun yi rayuwa kamar yadda sauran mutanen duniya suke yi, cike da zunubi, kuna biyayya ga sarki masu ikon sarari sama, wato, ruhun nan da yanzu yake aiki a cikin masu ƙin biyayya ga Allah. 3 Dukanmu a dā mun yi irin rayuwan nan a cikinsu, muna bin kwaɗayi da sha’awace-sha’awacen jikunanmu da tunaninmu. Kamar sauran mutane, mun cancanci fushin Allah. 4 Amma saboda yawan ƙaunar da yake mana, Allah, wanda yake mai yawan jinƙai, 5 ya ba mu rai sa’ad da ya tashe Kiristi daga matattu. Ta wurin alherin Allah ne aka cece ku.

  2. 7 Masu albarka ne waɗanda suke masu jinƙai,

    gama za a nuna musu jinƙai.

  3. 35 Amma, ku ƙaunaci abokan gābanku, ku kuma yi musu alheri, ku ba su bashi, ba da sa zuciya sai an biya ku ba. Ta yin haka ne kawai, za ku sami lada mai yawa, ku kuma zama ’ya’yan Mafi Ɗaukaka, gama shi mai alheri ne ga marasa godiya da mugaye. 36 Ku zama masu jinƙai, kamar yadda Ubanku mai jinƙai ne.

    37 “Kada ku ɗora wa wani, ku ma ba za a ɗora muku ba. Kada ku yanke wa wani hukunci, ku ma ba za a yanke muku ba. Ku gafarta, ku ma za a gafarta muku.

  4. 14 Saboda haka, da yake muna da babban firist mai girma wanda ya ratsa sama, Yesu Ɗan Allah, bari mu riƙe bangaskiyan nan wadda muke shaidawa da ƙarfi. 15 Gama babban firist da muke da shi ba marar juyayin kāsawarmu ba ne, amma muna da wanda aka gwada ta kowace hanya, kamar dai yadda akan yi mana, duk da haka bai yi zunubi ba. 16 Saboda haka sai mu matso kusa da kursiyin alheri da ƙarfi zuciya, don mu sami jinƙai mu kuma sami alherin da zai taimake mu a lokacin bukata.

  5. 12 Ku yi magana ku kuma yi aiki kamar waɗanda za a yi musu shari’a bisa ga doka mai ba da ’yanci, 13 gama za a yi wa duk wanda bai nuna jinƙai ba hukunci babu jinƙai. Jinƙai yakan yi nasara a kan hukunci!

  6. 19 Na tuna da azabata da kuma sintiri,

    da na yi ta yi da ɗacin rai.

    20 Na tuna su sosai,

    sai kuma na ji ba daɗi a raina.

    21 Duk da haka na tuna da wannan

    na kuma sa bege ga nan gaba.

    22 Domin ƙaunar Ubangiji ba mu hallaka ba;

    gama jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa.

    23 Sababbi ne kowace safiya;

    amincinka kuwa mai girma ne.

    24 Na ce wa kaina, “Ubangiji shi ne nawa;

    saboda haka zan jira shi.”

  7. 15 Gama ya ce wa Musa,

    “Zan nuna jinƙai ga wanda zan nuna jinƙai,

    zan kuma ji tausayin wanda zan ji tausayi.”

    16 Saboda haka, bai danganta ga sha’awar mutum ko ƙoƙarinsa ba, sai dai ga jinƙan Allah. 17 Gama Nassi ya ce wa Fir’auna, “Na ɗaga ka saboda wannan manufa, saboda in nuna ikona a cikinka domin kuma a shaida sunana a duniya duka.” 18 Saboda haka Allah yana nuna jinƙai ga wanda yake so, yana kuma taurara zuciyar wanda yake so.

    19 Waninku zai iya ce mini, “To, don me har yanzu Allah yake ganin laifinmu? Gama wa zai iya tsayayya da nufinsa?” 20 Amma wane ne kai, ya mutum, da za ka mayar wa Allah magana? “Ashe, abin da aka gina zai iya ce wa wanda ya gina shi, ‘Don me ka gina ni haka?’ ” 21 Ashe, mai ginin tukwane ba shi da iko yin amfani da yumɓu guda yă gina tukunya domin ayyuka masu daraja da kuma waɗansu don ayyuka marasa daraja?

    22 Haka ma aikin Allah yake. Ya so yă nuna fushinsa yă kuma sanar da ikonsa, ya yi haka cikin haƙuri ƙwarai ga waɗanda suka cancanci fushinsa, waɗanda aka shirya domin hallaka? 23 Haka kuma ya so yă sanar da wadatar ɗaukakarsa ga waɗanda suka cancanci jinƙansa, waɗanda ya shirya tun kafin lokaci don ɗaukaka 24 har da mu ma, mu da ya kira, ba daga cikin Yahudawa kaɗai ba amma har ma daga cikin Al’ummai?

  8. 17 “Ka yi murfin kafara da zinariya zalla, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kuma kamu ɗaya da rabi. 18 Ka kuma yi kerubobi biyu da zinariyar da aka ƙera, ka sa a gefen nan biyu na murfin. 19 Ka yi kerubobi biyu, ɗaya a wannan gefe, ɗaya kuma a ɗayan gefen; za ka manne su a kan murfin, su zama abu ɗaya. 20 Kerubobin su kasance da fikafikansu a buɗe, domin su inuwantar da murfin, za su fuskanci juna, suna duba murfin. 21 Ka sa murfin a bisa akwatin ka kuma sa allunan dokokin alkawarin da zan ba ka a ciki. 22 Can, a bisa murfin da yake tsakanin kerubobi biyu da suke bisa akwatin alkawari na Shaida, zan sadu da kai, in kuma ba ka dukan umarnai domin Isra’ilawa.

  9. 4 Amma da alheri da kuma ƙaunar Allah Mai Cetonmu suka bayyana, 5 sai ya cece mu, ba saboda abubuwan adalcin da muka aikata ba, sai dai saboda jinƙansa. Ya cece mu ta wurin wankan nan na sāke haihuwa da kuma sabuntawan nan ta Ruhu Mai Tsarki, 6 wanda ya zubo mana a yalwace ta wurin Yesu Kiristi Mai Cetonmu, 7 wannan fa domin an kuɓutar da mu ne ta wurin alherinsa, don mu zama magāda masu begen ga rai madawwami.

  10. 4 Ka nuna mini hanyoyinka, ya Ubangiji,

    ka koya mini hanyoyinka;

    5 ka bi da ni cikin gaskiyarka ka kuma koya mini,

    gama kai ne Allah Mai cetona,

    kuma begena yana a kanka dukan yini.

    6 Ka tuna, ya Ubangiji da jinƙai da kuma ƙaunarka mai girma,

    gama suna nan tun dā.

    7 Kada ka tuna da zunuban ƙuruciyata

    da kuma hanyoyin tawayena;

    bisa ga ƙaunarka ka tuna da ni,

    gama kai nagari ne, ya Ubangiji.

    8 Ubangiji nagari da mai adalci ne;

    saboda haka yakan koyar da masu zunubi a hanyoyinsa.

    9 Yakan bi da masu tawali’u cikin abin da yake daidai

    ya kuma koyar da su hanyoyinsa.

  11. 18 Wane ne Allah kamar ka,

    wanda yake yafe zunubi yă kuma gafarta laifofin mutanensa da suka ragu?

    Ba ka zama mai fushi har abada

    amma kana marmari ka nuna jinƙai.

    19 Za ka sāke jin tausayinmu;

    za ka tattake zunubanmu a ƙarƙashin sawunka

    ka kuma tura dukan kurakuranmu zuwa cikin zurfafan teku.

    20 Za ka yi wa Yaƙub aminci,

    ka kuma nuna jinƙai ga Ibrahim,

    kamar yadda ka yi alkawari da rantsuwa ga kakanninmu

    tun a kwanankin dā.

  12. 1 Saboda haka, ina roƙonku, ’yan’uwa, saboda yawan jinƙan Allah, ku miƙa jikunanku hadaya wadda take mai rai, mai tsarki abin karɓa kuma ga Allah, wannan ita ce hanyar hidimarku ta ruhaniya. 2 Kada ku ci gaba da yin abin da duniya take yi, sai dai ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so yake, abu mai kyau, mai daɗi da kuma cikakke.

  13. 8 Ya nuna maka, ya mutum, abin da yake mai kyau.

    Me Ubangiji yake bukata daga gare ka kuwa

    shi ne ka yi gaskiya ka so aikata jinƙai

    ka kuma yi tafiya da tawali’u a gaban Allah.

  14. 6 Sai Ubangiji ya wuce a gaban Musa, ya yi shela ya ce, “Ni ne Ubangiji Allah mai tausayi, mai alheri, mai jinkirin fushi, cike da ƙauna da aminci, 7 nakan nuna ƙauna wa dubbai, nakan kuma gafarta mugunta, tawaye da zunubi. Amma ba na barin mai laifi, ba tare da na hore shi ba; nakan hukunta ’ya’ya da jikoki har tsara ta uku da ta huɗu saboda laifin iyaye.”

  15. 76 “Kai kuma, ɗana, za a ce da kai annabin Maɗaukaki;

    gama za ka sha gaban Ubangiji don ka shirya masa hanya,

    77 don ka sanar da mutanensa ceto,

    ta wurin gafarar zunubansu,

    78 saboda jinƙai na Allahnmu mai ƙauna,

    hasken nan na ceto zai ɓullo mana daga sama,

    79 don yă haskaka a kan waɗanda suke zama cikin duhu,

    da kuma cikin inuwar mutuwa,

    don yă bi da ƙafafunmu a hanyar salama.”

  16. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Sa’ad da annabi Natan ya zo wurinsa bayan Dawuda ya yi zina da Batsheba.

    1 Ka yi mini jinƙai, ya Allah,

    bisa ga ƙaunarka marar ƙarewa;

    bisa ga tausayinka mai girma

    ka shafe laifofina.

    2 Ka wanke dukan kurakuraina

    ka tsarkake ni daga zunubina.

    3 Gama ina sane da laifofina

    zunubaina kuma kullum suna a gabana.

    4 Kai kaɗai na yi wa zunubi

    na yi abin da yake mugu a idonka,

    ta haka an tabbatar kai mai gaskiya sa’ad da ka yi magana

    aka kuma nuna kai mai adalci ne sa’ad da ka hukunta.

  17. 14 An zubo mini alherin Ubangijinmu a yalwace, tare da bangaskiya da ƙaunar da take cikin Kiristi Yesu.

    15 Ga wata magana tabbatacciya wadda ta cancanci cikakkiyar karɓa. Kiristi Yesu ya zo duniya domin ceton masu zunubi, wanda nake mafi muni a cikinsu. 16 Amma saboda wannan dalilin ne aka nuna mini jinƙai domin ta wurina, mafi zunubi duka, Kiristi Yesu yă iya bayyana matuƙar haƙurinsa a matsayin misali ga waɗanda za su gaskata shi su kuma sami rai madawwami.

  18. 8 Ubangiji mai alheri da kuma tausayi,

    mai jinkirin fushi cike kuma da ƙauna.

    9 Ubangiji nagari ne ga duka;

    yana tausayin dukan abubuwan da ya yi.

  19. 6 Ubangiji zai kira

    sai ka ce ke mace ce da aka yashe ta tana kuma damuwa a ranta,

    macen da ta yi aure a ƙuruciya,

    sai kawai aka ƙi ta,” in ji Allahnki.

    7 “Gama a ɗan ƙanƙanen lokaci na rabu da ke,

    amma da ƙauna mai zurfi zan sāke dawo da ke.

    8 Cikin fushi mai zafi

    na ɓoye fuskata daga gare ki na ɗan lokaci,

    amma da madawwamin alheri

    zan ji tausayinki,”

    in ji Ubangiji Mai Fansarki.

  20. 13 Amma ku je ku koyi abin da wannan yake nufi, ‘Jinƙai nake bukata, ba hadaya ba.’ Gama ban zo domin in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi.”

  21. 21 Sai Bitrus ya zo wurin Yesu ya yi masa tambaya ya ce, “Ubangiji, sau nawa zan yafe wa ɗan’uwana sa’ad da ya yi mini zunubi? Har sau bakwai?”

    22 Yesu amsa ya ce, “Ina gaya maka, ba sau bakwai ba, amma sau saba’in da bakwai.

  22. 12 Da yake Allah ya mai da ku zaɓaɓɓu, tsarkaka, ƙaunatattu, sai ku dinga jin tausayin juna, kuna yin alheri, kuna nuna tawali’u da sauƙinkai da jimrewa. 13 Ku riƙa yin haƙuri da juna kuna kuma gafarta wa juna duk wani laifin da wani ya yi muku. Ku gafarta kamar yadda Ubangiji ya gafarce ku. 14 Fiye da waɗannan duka, ku yi ƙaunar juna, gama ƙauna ce take haɗa kome gaba ɗaya.

  23. 15 Amma kai, ya Ubangiji, kai Allah mai tausayi ne da kuma mai alheri,

    mai jinkirin fushi, mai yawan ƙauna da aminci.

    16 Ka juyo gare ni ka yi mini jinƙai;

    ka ba wa bawanka ƙarfi;

    ka ceci ni gama na bauta maka

    yadda mahaifiyata ta yi.

  24. 1 Yahuda, bawan Yesu Kiristi, ɗan’uwan Yaƙub,

    Zuwa ga waɗanda aka kira, waɗanda Allah Uba yake ƙauna, waɗanda kuma Yesu Kiristi ya kiyaye.

    2 Jinƙai, salama da kuma ƙauna, su kasance tare da ku a yalwace.

  25. 49 gama Mai Iko Duka ya yi mini manyan abubuwa,

    sunansa labudda Mai Tsarki ne.

    50 Jinƙansa ya kai ga masu tsoronsa,

    daga zamani zuwa zamani.

  26. 14 Dawuda ya ce wa Gad, “Na shiga uku. Gara mu fāɗa a hannuwan Ubangiji gama alherinsa da girma yake. Amma fa kada ka bar ni in fāɗa a hannun mutane.”

  27. 12 Ka tafi, ka yi shelar saƙon nan wajen arewa cewa,

    “ ‘Ki komo, Isra’ila marar bangaskiya,’ in ji Ubangiji,

    ‘Ba zan ƙara yin fushi da ke ba,

    gama ni mai jinƙai ne,’ in ji Ubangiji,

    ‘Ba zan yi fushi da ke har abada ba.

  28. 16 Bari Ubangiji yă yi wa iyalin Onesiforus jinƙai, domin sau da dama yakan wartsakar da ni, bai kuma ji kunyar sarƙoƙina ba. 17 A maimakon haka ma, sa’ad da yake a Roma, ya neme ni ido a rufe sai da ya same ni. 18 Bari Ubangiji yă sa yă sami jinƙai daga Ubangiji a wancan ranar! Ka sani sarai yadda ya taimake ni a hanyoyi dabam-dabam a Afisa.

  29. 31 Gama Ubangiji Allahnku, Allah ne mai jinƙai; ba zai yashe ku ko yă hallaka, ko kuma yă manta da alkawarin da ya yi da kakanninku, wanda ya tabbatar da su da rantsuwa ba.

  30. 10 ba ya yin da mu gwargwadon zunubanmu

    ko yă sāka mana bisa ga laifofinmu.

    11 Gama kamar yadda sammai suke can bisa duniya,

    haka girmar ƙaunarsa yake wa masu tsoronsa;

    12 kamar yadda gabas yake daga yamma,

    haka ya cire laifofinmu daga gare mu.

    13 Kamar yadda mahaifi yake jin tausayin ’ya’yansa,

    haka Ubangiji yake jin tausayin waɗanda suke tsoronsa;

    14 gama ya san yadda aka yi mu,

    ya tuna cewa mu ƙura ne.

  31. 13 Duk wanda ya ɓoye zunubansa ba ya taɓa cin nasara,

    amma duk wanda ya furta ya kuma ƙi su yakan sami jinƙai.

    14 Mai albarka ne mutumin da kullum yake jin tsoron Allah,

    amma duk wanda ya taurare zuciyarsa yakan shiga wahala.

  32. 30 Makafi biyu kuwa suna zaune a bakin hanya, da suka ji cewa Yesu yana wucewa, sai suka ɗaga murya suka ce, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayinmu!”

    31 Mutane suka tsawata musu, suka ce musu su yi shiru. Sai suka ƙara ɗaga murya suna cewa, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayinmu!”

    32 Yesu ya tsaya ya kira su. Ya tambaye su, “Me kuke so in yi muku?”

    33 Suka amsa suka ce, “Ubangiji, muna so mu sami ganin gari.”

    34 Sai Yesu ya ji tausayinsu, ya taɓa idanunsu. Nan da nan kuwa suka sami ganin gari, suka kuma bi shi.

  33. 17 Amma hikimar da ta zo daga sama da fari tana da tsabta gaba ɗaya; sa’an nan mai ƙaunar salama ce, mai sanin ya kamata, mai biyayya, cike da jinƙai da aiki mai kyau, marar nuna bambanci, sahihiya kuma.

  34. 23 “Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kukan ba da kashi ɗaya bisa goma na kayan yajinku, na’ana’a, anise, da lafsur. Amma kun ƙyale abubuwan da suka fi girma na dokoki, adalci, jinƙai da aminci. Waɗannan ne ya kamata da kun kiyaye ba tare da kun ƙyale sauran ba.

  35. 3 Yabo ya tabbata ga Allah, da Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba mai tausayi, da kuma Allah na dukan ta’aziyya, 4 wanda yakan yi mana ta’aziyya a cikin dukan wahalolinmu, domin mu kuma mu iya ta’azantar da waɗanda suke cikin kowace irin wahala, da ta’aziyyar da mu kanmu muka samu daga Allah.

  36. 8 Ubangiji mai tausayi ne da kuma alheri,

    mai jinkirin fushi, cike da ƙauna.

  37. 7 Bari mugu ya bar irin halinsa

    mugu kuma ya sāke irin tunaninsa.

    Bari yă juyo ga Ubangiji, zai kuwa ji tausayinsa,

    ya juyo ga Allahnmu kuma, gama shi mai gafartawa ne a sauƙaƙe.

  38. 9 Ubangiji Allahnmu mai jinƙai ne, mai gafartawa ne kuma, ko da yake mun yi masa tawaye;

  39. 17 Amma ku abokaina ƙaunatattu, ku tuna da abin da manzannin Ubangijinmu Yesu Kiristi suka faɗa a dā. 18 Sun ce muku, “A kwanakin ƙarshe za a kasance da masu ba’a waɗanda za su bi sha’awace-sha’awacensu na rashin tsoron Allah.” 19 Waɗannan mutanen ne, suke kawo rabe-rabe, masu bin abin da jiki yake so, marasa Ruhu.

    20 Amma ku, abokaina ƙaunatattu, ku gina kanku cikin bangaskiyarku mafi tsarki, ku kuma yi addu’a cikin Ruhu Mai Tsarki. 21 Ku zauna cikin ƙaunar Allah yayinda kuke jira jinƙan Ubangijinmu Yesu Kiristi don yă kawo ku ga rai madawwami.

    22 Ku ji tausayin waɗanda suke shakka; 23 ku cece waɗansu ta wurin fizge su daga wuta. Ga waɗansu kuma ku ji tausayinsu, amma tare da tsoro, har ma ku yi ƙyamar tufafin da suka ɓata da ayyukansu na jiki.

    24 To, yabo yă tabbata a gare shi, shi wanda yake da iko yă tsare ku daga fāɗuwa, yă kuma miƙa ku marasa laifi a gaban ɗaukakarsa da matuƙar farin ciki. 25 Gare shi kuma, shi da yake kaɗai Allah Mai Cetonmu, ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu, bari ɗaukaka, daraja, iko da mulki, su tabbata a gare shi, tun farkon zamanai, yanzu, da har abada abadin! Amin.

  40. 13 Ku kyakkece zuciyarku

    ba rigunanku ba.

    Ku juyo ga Ubangiji Allahnku,

    gama shi mai alheri ne mai tausayi kuma

    mai jinkirin fushi da yawan ƙauna,

    yakan kuma janye daga aika da bala’i.

  41. 16 Da yana jan jiki, sai mutanen suka kama hannunsa da hannuwan matarsa da na ’ya’yansa biyu mata, suka kai su bayan birni, gama Ubangiji ya nuna musu jinƙai.

  42. 10 Ƙauna da aminci za su sadu;

    adalci da salama za su yi wa juna sumba.

  43. 10 Dā ku ba mutane ba ne, amma yanzu ku mutanen Allah ne; Dā ba ku karɓi jinƙai ba, amma yanzu kun karɓi jinƙai.

  44. 29 Amma domin ya kāre kansa, sai ya tambayi Yesu ya ce, “Shin, wane ne maƙwabcina?”

    30 Yesu ya amsa ya ce, “Wani mutum ya tashi daga Urushalima za shi Yeriko, sai ya fāɗi a hannun mafasa, wato, ’yan fashi. Suka ƙwace tufafinsa, suka yi masa dūka, suka bar shi nan bakin rai da mutuwa. 31 Ya zamana wani firist ya bi kan wannan hanya. Da ya ga mutumin, sai ya bi gefe ya wuce abinsa. 32 Haka ma wani daga kabilar Lawi, mai hidima cikin haikali, da ya zo wurin, ya gan shi, sai shi ma ya bi gefe ɗaya, ya wuce abinsa. 33 Amma wani mutumin Samariya da yake kan tafiya, da ya kai inda mutumin yake, ya gan shi, sai ya ji tausayinsa. 34 Ya je wurinsa, ya daddaure masa raunukansa, sa’an nan ya zuba mai, da ruwan inabi. Ya ɗauki mutumin ya sa a kan jakinsa, ya kai shi wani masauƙi, ya yi jinyarsa. 35 Kashegari, sai ya ɗauki dinari biyu, ya ba wa mai masauƙin ya ce, ‘Ka lura da shi, bayan na dawo, zan biya ka duk abin da ka ƙara kashewa a kansa.’

    36 “A ganinka, a cikin waɗannan mutane uku, wane ne maƙwabcin mutumin da ya fāɗi a hannun mafasa?”

    37 Masanin dokoki ya amsa ya ce, “Wanda ya nuna masa jinƙai.”

    Yesu ya ce masa, “Je ka, ka yi haka nan.”

  45. 18 Zan tashi in koma wurin mahaifina, in ce masa, “Baba, na yi wa sama, na kuma yi maka zunubi. 19 Ni ban isa a ƙara kira na ɗanka ba. Ka mai da ni kamar ɗaya daga cikin bayinka.” ’ 20 Sai ya tashi ya kama hanya ya koma wurin mahaifinsa.

    “Amma tun yana nesa, mahaifinsa ya hange shi. Tausayi kuma ya kama shi, sai ya tashi ya ruga da gudu wurinsa, ya rungume shi, ya yi masa sumba.

  46. 11 Yesu yana kan hanyarsa zuwa Urushalima, sai ya bi takan iyakar Samariya da Galili. 12 Da zai shiga wani ƙauye, sai maza goma da suke da kuturta suka sadu da shi. Suka tsaya da nesa, 13 suka yi kira da babbar murya, suka ce, “Yesu, Ubangiji, ka ji tausayinmu!”

  47. 22 Wannan adalcin Allah yana zuwa ta wurin bangaskiya a cikin Yesu Kiristi ga dukan waɗanda suka ba da gaskiya ne. Ba bambanci, 23 gama duka sun yi zunubi suka kuma kāsa ga ɗaukakar Allah, 24 an kuma kuɓutar da su kyauta ta wurin alherinsa bisa ga aikin fansar da ya zo ta wurin Yesu Kiristi. 25 Allah ya miƙa Yesu Kiristi a matsayin hadayar kafara, ta wurin bangaskiya cikin jininsa. Ya yi haka domin yă nuna adalcinsa, domin a cikin haƙurinsa bai hukunta zunuban da aka aikata a dā ba 26 ya yi haka domin yă nuna adalcinsa a wannan lokaci, saboda yă zama mai adalci da mai kuɓutar da waɗanda suke ba da gaskiya a cikin Yesu.

    27 To, me za mu yi taƙama a kai? Babu wani abin da zamu yi taƙama a kai. A kan wace ƙa’ida ce za mu yi taƙama? Ta hanyar bin doka ne? A’a, sai dai ta wurin bangaskiya.

  48. 28 Game da zancen nan na bishara kuwa, su abokan gāba ne saboda ku; amma game da zaɓen kuwa, su ƙaunatattunsa ne, albarkacin kakannin kakanninsu, 29 gama kyautar Allah da kiransa ba a sokewa. 30 Kamar yadda a dā can ku da kuke marasa biyayya ga Allah kuka sami jinƙai yanzu ta dalilin rashin biyayyarsu, 31 haka su ma suka zama marasa biyayya a yanzu domin su ma su sami jinƙai ta dalilin jinƙan da Allah ya yi muku. 32 Gama Allah ya daure dukan mutane ga rashin biyayya don yă nuna jinƙai ga kowa.

  49. 11 Kamar yadda kuka sani, mukan ce da waɗanda suka jure, masu albarka ne. Kun ji daurewar Ayuba, kuka kuma ga abin da Ubangiji ya yi a ƙarshe. Ubangiji yana cike da tausayi da jinƙai.

  50. 4 Sai na kira ga sunan Ubangiji na ce,

    “Ya Ubangiji, ka cece ni!”

    5 Ubangiji mai alheri ne da kuma mai adalci;

    Allahnmu yana cike da tausayi.

    6 Ubangiji yana tsare masu tawali’u;

    sa’ad da nake cikin tsananin bukata, ya cece ni.

  51. 2 Ka yi mini jinƙai, Ubangiji, gama na suma;

    Ya Ubangiji, ka warkar da ni, gama ƙasusuwana suna zafin ciwo.

  52. 16 Ka amsa mini, ya Ubangiji cikin alherin ƙaunarka;

    cikin jinƙanka mai girma ka juyo gare ni.

    17 Kada ka ɓoye fuskarka daga bawanka;

    ka amsa mini da sauri, gama ina cikin wahala.

    18 Ka zo kusa ka kuɓutar da ni;

    ka fanshe ni saboda maƙiyana.

    19 Ka san yadda ake mini ba’a, ake kunyatar da ni da kuma yadda nake shan kunya;

    dukan abokan gābana suna a gabanka.

    20 Ba’a ta sa zuciyata ta karai

    ta bar ni ba mataimaki;

    Na nemi a ji tausayina, amma ban sami ko ɗaya ba,

    na nemi masu ta’aziyya, amma ban sami ko ɗaya ba.

    21 Sun sa abin ɗaci cikin abincina

    suka kuma ba ni ruwan inabi mai tsami sa’ad da nake jin ƙishi.

  53. 2 Ya Ubangiji, na ji irin shaharar da ka yi;

    na yi al’ajabi game da ayyukanka, ya Ubangiji.

    Ka maimaita su a kwanakinmu,

    ka sanar da su a lokacinmu;

    ka yi jinƙai ko a lokacin da kake fushi.

  54. 13 Sa’ad da Yesu ya ji abin da ya faru, sai ya shiga jirgin ruwa ya janye shi kaɗai zuwa wani wuri inda ba kowa. Da jin haka, taron mutane suka bi shi da ƙafa daga garuruwa. 14 Da Yesu ya sauka ya kuma ga taro mai yawa, sai ya ji tausayinsu ya kuma warkar da marasa lafiyarsu.

  55. 13 A cikin ƙaunarka marar iyaka, za ka bishe

    mutanen da ka fansa.

    A cikin ƙarfinka, za ka bishe su

    zuwa mazauninka mai tsarki.

  56. 1 Ina ƙaunar Ubangiji, gama ya ji muryata;

    ya ji kukata ta neman jinƙai.

    2 Domin ya juye kunnensa gare ni,

    zan kira gare shi muddin ina da rai.

  57. Waƙar haurawa.

    1 Daga cikin zurfafa na yi kuka gare ka, ya Ubangiji;

    2 Ya Ubangiji, ka ji muryata.

    Bari kunnuwanka su saurara

    ga kukata ta neman jinƙai.

    3 In kai, ya Ubangiji, za ka lissafta zunubai,

    Ya Ubangiji, wa zai tsaya?

    4 Amma tare da kai akwai gafartawa,

    saboda haka ake tsoronka.

  58. 10 “Baƙi za su sāke gina katangarki,

    sarakunansu kuma za su yi miki hidima.

    Ko da yake a cikin fushi na buge ki,

    da tagomashi zan yi miki jinƙai.

  59. 13 “Amma mai karɓar harajin ya tsaya daga nesa. Bai ma iya ɗaga kansa sama ba, sai ya buga ƙirjinsa, yana cewa, ‘Allah, ka yi mini jinƙai, ni mai zunubi ne.’

  60. 9 Ubangiji ba mai jinkiri ba ne wajen cika alkawarinsa, yadda waɗansunku suka fahimci jinkiri. Yana haƙuri da ku, ba ya so wani yă hallaka, sai dai kowa yă kai ga tuba.