67 Bible Verses About Forgiveness of Sins

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Forgiveness of Sins
  1. 9 “To, ga yadda ya kamata ku yi addu’a.

    “ ‘Ubanmu wanda yake cikin sama,

    a tsarkake sunanka,

    10 mulkinka yă zo

    a aikata nufinka a duniya

    kamar yadda ake yi a sama.

    11 Ka ba mu yau abincin yininmu.

    12 Ka gafarta mana laifofinmu,

    kamar yadda mu ma muke gafarta wa masu yin mana laifi.

    13 Kada ka bari a kai mu cikin jarraba,

    amma ka cece mu daga mugun nan. ’

    14 Gama in kuna yafe wa mutane sa’ad da suka yi muku laifi, Ubanku da yake cikin sama ma zai gafarta muku. 15 Amma in ba kwa yafe wa mutane laifofinsu, Ubanku ma ba zai gafarta muku zunubanku ba.

  2. 5 Wannan shi ne saƙon da muka ji daga wurinsa, muna kuma sanar da ku cewa Allah haske ne; a cikinsa kuwa babu duhu ko kaɗan. 6 In muka ce muna zumunci da shi amma muna tafiya cikin duhu, ƙarya muke yi, kuma ba ma rayuwa bisa ga gaskiya. 7 Amma in muna tafiya cikin haske, yadda yake cikin haske, muna da zumunci da juna ke nan, kuma jinin Yesu, Ɗansa, yana tsarkake mu daga dukan zunubi.

    8 In muka ce ba mu da zunubi, muna ruɗin kanmu ne, gaskiya kuwa ba ta cikinmu. 9 In muka furta zunubanmu, shi mai aminci ne, mai adalci kuma, zai gafarta mana zunubanmu, yă kuma tsarkake mu daga dukan rashin adalci. 10 In muka ce ba mu yi zunubi ba, mun mai da shi maƙaryaci ke nan, maganarsa kuwa ba ta da wuri a cikinmu.

  3. 37 Sa’ad da mutane suka ji wannan, sai suka soku a zuci sai suka ce wa Bitrus da sauran manzanni, “’Yan’uwa, me za mu yi?”

    38 Bitrus ya amsa, “Ku tuba a kuma yi muku baftisma, kowannenku a cikin sunan Yesu Kiristi domin gafarar zunubanku. Za ku kuwa karɓi kyautar Ruhu Mai Tsarki. 39 Alkawarin dominku ne da ’ya’yanku da kuma dukan waɗanda suke da nesa, domin dukan waɗanda Ubangiji Allahnmu zai kira.”

  4. 25 A duk lokacin da kuke tsaye cikin addu’a, in kuna riƙe da wani mutum a zuciyarku, ku gafarta masa, domin Ubanku da yake sama shi ma yă gafarta muku zunubanku.”

  5. 7 A cikinsa muka sami fansa ta wurin jininsa, wato, yafewar zunubanmu. Kiristi ya yi wannan saboda yawan alherin Allah 8 wanda ya ba mu babu iyaka tare da dukan hikima da fahimta. 9 Allah ya yi abin da ya nufa, ya kuma sanar mana shirin asirin da ya riga ya shirya yă cika ta wurin Kiristi. 10 Nufinsa ke nan, idan lokaci ya cika, yă harhaɗa dukan abubuwa a ƙarƙashin ikon Kiristi, wato, dukan abubuwan da suke sama da abubuwan da suke ƙasa.

  6. 12 Da yake Allah ya mai da ku zaɓaɓɓu, tsarkaka, ƙaunatattu, sai ku dinga jin tausayin juna, kuna yin alheri, kuna nuna tawali’u da sauƙinkai da jimrewa. 13 Ku riƙa yin haƙuri da juna kuna kuma gafarta wa juna duk wani laifin da wani ya yi muku. Ku gafarta kamar yadda Ubangiji ya gafarce ku.

  7. Ta Dawuda. Maskil ne.

    1 Mai farin ciki ne shi

    wanda aka gafarta masa laifofinsa,

    wanda aka shafe zunubansa.

    2 Mai farin ciki ne mutumin

    da Ubangiji ba ya lissafin zunubinsa a kansa

    wanda kuma babu ruɗu a ruhunsa.

    3 Sa’ad da na yi shiru,

    ƙasusuwana sun yi ta mutuwa

    cikin nishina dukan yini.

    4 Gama dare da rana

    hannunka yana da nauyi a kaina;

    an shanye ƙarfina ƙaf

    sai ka ce a zafin bazara. Sela

    5 Sa’an nan na furta zunubina a gare ka

    ban kuwa ɓoye laifina ba.

    Na ce, “Zan furta

    laifofina ga Ubangiji.”

    Ka kuwa gafarta

    laifin zunubina. Sela

  8. 3 Saboda haka, ku lura da kanku.

    “In ɗan’uwanka ya yi zunubi, ka kwaɓe shi. In ya tuba, ka gafarta masa. 4 In ya yi maka laifi sau bakwai a rana ɗaya, ya kuma dawo sau bakwai ɗin a wurinka, yana cewa, ‘Na tuba,’ sai ka gafarta masa.”

    5 Sai manzannin suka ce wa Ubangiji, “Ka ƙara mana bangaskiya!”

  9. 33 Da suka isa wurin da ake kira “Ƙoƙon Kai,” nan suka gicciye shi, tare da masu laifin nan, ɗaya a hannun damansa, ɗayan kuma a hagunsa. 34 Yesu ya ce, “Ya Uba ka yi musu gafara, don ba su san abin da suke yi ba.” Suka rarraba tufafinsa ta wurin jefa ƙuri’a.

  10. 37 “Kada ku ɗora wa wani, ku ma ba za a ɗora muku ba. Kada ku yanke wa wani hukunci, ku ma ba za a yanke muku ba. Ku gafarta, ku ma za a gafarta muku.

  11. 8 Ubangiji mai tausayi ne da kuma alheri,

    mai jinkirin fushi, cike da ƙauna.

    9 Ba zai yi ta zargi ba

    ba kuwa zai yi ta jin fushi har abada ba;

    10 ba ya yin da mu gwargwadon zunubanmu

    ko yă sāka mana bisa ga laifofinmu.

    11 Gama kamar yadda sammai suke can bisa duniya,

    haka girmar ƙaunarsa yake wa masu tsoronsa;

    12 kamar yadda gabas yake daga yamma,

    haka ya cire laifofinmu daga gare mu.

    13 Kamar yadda mahaifi yake jin tausayin ’ya’yansa,

    haka Ubangiji yake jin tausayin waɗanda suke tsoronsa;

    14 gama ya san yadda aka yi mu,

    ya tuna cewa mu ƙura ne.

  12. 21 Amma yanzu an bayyana wani adalci daga Allah, wannan adalcin bai danganta ga doka ba, Doka da Annabawa suna ba da shaida game da wannan adalci. 22 Wannan adalcin Allah yana zuwa ta wurin bangaskiya a cikin Yesu Kiristi ga dukan waɗanda suka ba da gaskiya ne. Ba bambanci, 23 gama duka sun yi zunubi suka kuma kāsa ga ɗaukakar Allah, 24 an kuma kuɓutar da su kyauta ta wurin alherinsa bisa ga aikin fansar da ya zo ta wurin Yesu Kiristi. 25 Allah ya miƙa Yesu Kiristi a matsayin hadayar kafara, ta wurin bangaskiya cikin jininsa. Ya yi haka domin yă nuna adalcinsa, domin a cikin haƙurinsa bai hukunta zunuban da aka aikata a dā ba 26 ya yi haka domin yă nuna adalcinsa a wannan lokaci, saboda yă zama mai adalci da mai kuɓutar da waɗanda suke ba da gaskiya a cikin Yesu.

  13. 16 Ku yi wanka ku kuma tsabtacce kanku.

    Ku kawar da mugayen ayyukanku daga gabana;

    Ku daina aikata mugunta.

    17 Ku koyi yin nagarta; ku nemi adalci.

    Ku ƙarfafa waɗanda aka zalunta.

    Ku ba wa marayu hakkinsu,

    ku taimaki gwauruwa.

    18 Ubangiji ya ce,

    “Yanzu fa ku zo, bari mu dubi batun nan tare,

    Ko da zunubanku sun yi ja kamar garura,

    za su zama fari kamar ƙanƙara;

    ko da sun yi ja kamar mulufi,

    za su zama kamar ulu.

    19 In kuna da niyya kuna kuma yi mini biyayya,

    za ku ci abubuwa masu kyau daga ƙasar;

    20 amma in kuka yi tsayayya kuka kuma yi tayarwa,

    za a kashe ku da takobi.”

    Ni Ubangiji na faɗa.

  14. 18 Wane ne Allah kamar ka,

    wanda yake yafe zunubi yă kuma gafarta laifofin mutanensa da suka ragu?

    Ba ka zama mai fushi har abada

    amma kana marmari ka nuna jinƙai.

    19 Za ka sāke jin tausayinmu;

    za ka tattake zunubanmu a ƙarƙashin sawunka

    ka kuma tura dukan kurakuranmu zuwa cikin zurfafan teku.

    20 Za ka yi wa Yaƙub aminci,

    ka kuma nuna jinƙai ga Ibrahim,

    kamar yadda ka yi alkawari da rantsuwa ga kakanninmu

    tun a kwanankin dā.

  15. 21 Sai Bitrus ya zo wurin Yesu ya yi masa tambaya ya ce, “Ubangiji, sau nawa zan yafe wa ɗan’uwana sa’ad da ya yi mini zunubi? Har sau bakwai?”

    22 Yesu amsa ya ce, “Ina gaya maka, ba sau bakwai ba, amma sau saba’in da bakwai.

    23 “Saboda haka, mulkin sama yana kama da wani sarki wanda ya so yă yi ƙididdigar dukiyarsa da take a hannun bayinsa. 24 Da ya fara ƙididdigar, sai aka kawo masa wani wanda yake bin bashin talenti dubu goma. 25 Da yake bai iya biya ba, sai maigida ya umarta a sayar da shi da matarsa da yaransa da kuma duk abin da yake da shi, a biya bashin.

    26 “Bawan ya durƙusa a gabansa. Ya yi roƙo ya ce, ‘Ka yi mini haƙuri, zan biya ka ƙaf.’ 27 Maigidan bawan ya ji tausayinsa, ya yafe masa bashin, ya kuma sake shi.

    28 “Amma da wannan bawa ya fita, sai ya gamu da wani abokin bautarsa wanda yake binsa bashin dinari ɗari. Sai ya cafke shi, ya shaƙe shi a wuya yana cewa, ‘Biya ni abin da nake binka!’

    29 “Wannan abokin bautarsa ya durƙusa ya roƙe shi, ‘Ka yi mini haƙuri, zan biya ka.’

    30 “Amma ya ƙi. A maimako, sai ya je ya sa aka jefa shi a kurkuku, har yă biya bashin. 31 Sa’ad da sauran bayin suka ga abin da ya faru, abin ya ɓata musu rai ƙwarai, sai suka tafi suka faɗa wa maigidansu dukan abin da ya faru.

    32 “Sai maigidan ya kira wannan bawa. Ya ce, ‘Kai mugun bawa, na yafe duk bashin da nake binka domin ka roƙe ni. 33 Ashe, bai kamata kai ma ka ji tausayin abokin bautarka yadda na yi maka ba?’ 34 Cikin fushi, maigidan ya miƙa shi ga ma’aikatan kurkuku su gwada masa azaba, har yă biya dukan bashin da ake binsa.

    35 “Haka Ubana da yake cikin sama zai yi da kowannenku, in ba ku yafe wa ’yan’uwanku daga zuciyarku ba.”

  16. 25 “Ni kaɗai ne na shafe

    laifofinku, saboda sunana,

    ban kuma ƙara tunawa da zunubanku ba.

    26 Ku tunashe ni abin da ya riga ya wuce,

    bari mu yi muhawwara wannan batu tare;

    ku kawo hujjarku na nuna rashin laifinku.

  17. 6 Ku nemi Ubangiji tun yana samuwa;

    ku yi kira gare shi tun yana kusa.

    7 Bari mugu ya bar irin halinsa

    mugu kuma ya sāke irin tunaninsa.

    Bari yă juyo ga Ubangiji, zai kuwa ji tausayinsa,

    ya juyo ga Allahnmu kuma, gama shi mai gafartawa ne a sauƙaƙe.

    8 “Gama tunanina ba tunaninku ba ne,

    yadda kuke yin abubuwa ba yadda nake yin abubuwa ba ne,”

    in ji Ubangiji.

    9 “Kamar yadda sammai suke can nesa da ƙasa,

    haka yadda nake yin abubuwa suke dabam da yadda kuke yin abubuwa

    tunanina kuma dabam da naku.

  18. 13 Duk wanda ya ɓoye zunubansa ba ya taɓa cin nasara,

    amma duk wanda ya furta ya kuma ƙi su yakan sami jinƙai.

  19. 13 Akwai waninku da yake shan wahala? Ya kamata yă yi addu’a. Akwai wani mai murna? Sai yă rera waƙoƙin yabo. 14 Akwai waninku da yake ciwo? Ya kamata yă kira dattawan ikkilisiya su yi masa addu’a, su kuma shafa masa mai cikin sunan Ubangiji. 15 Addu’ar da aka yi cikin bangaskiya, za tă warkar da marar lafiya, Ubangiji zai tashe shi. In ya yi zunubi kuwa za a gafarta masa. 16 Saboda haka, ku furta wa juna zunubanku, ku yi addu’a saboda juna, domin ku sami warkarwa. Addu’ar mai adalci tana da iko da kuma amfani.

    17 Iliya mutum ne kamar mu. Ya yi addu’a da gaske don kada a yi ruwan sama, ba a kuma yi ruwan sama a ƙasar ba har shekaru uku da rabi.

  20. 19 Saboda haka ku tuba, ku juyo ga Allah, don a shafe zunubanku, don lokutan wartsakewa su zo daga wurin Ubangiji, 20 don kuma ya iya aika da Kiristi, wanda aka naɗa tun dā saboda ku, Yesu ke nan.

  21. 38 “Saboda haka, ’yan’uwana, ina so ku san cewa ta wurin Yesu ana sanar muku da gafarar zunubi. 39 Ta wurinsa kowa da ya gaskata an kuɓutar da shi daga dukan abin da Dokar Musa ba tă iya kuɓutar ba.

  22. 10 Wannan shi ne alkawarin da zan yi da gidan Isra’ila,

    bayan lokacin nan,

    in ji Ubangiji.

    Zan sa dokokina a cikin zukatansu,

    in kuma rubuta su a kan zukatansu.

    Zan zama Allahnsu,

    su kuwa za su zama mutanena.

    11 Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabcinsa ba,

    balle mutum yă ce wa ɗan’uwansa, ‘Ka san Ubangiji,’

    domin dukansu za su san ni,

    daga ƙaraminsu zuwa babba.

    12 Gama zan gafarta muguntarsu

    ba zan kuma ƙara tuna da zunubansu ba.”

  23. 3 In kai, ya Ubangiji, za ka lissafta zunubai,

    Ya Ubangiji, wa zai tsaya?

    4 Amma tare da kai akwai gafartawa,

    saboda haka ake tsoronka.

  24. 9 Duk wanda ya rufe laifi yana inganta ƙauna ne,

    amma duk wanda ya yi ta maimaita batu yakan raba abokai na kusa.

  25. 2 Sai ya ce musu, “Sa’ad da kuke yin addu’a ku ce,

    “ ‘Ya Uba,

    sunanka mai tsarki ne

    mulkinka ya zo.

    3 Ka ba mu kowace rana abincin yini.

    4 Ka gafarta mana zunubanmu,

    kamar yadda mu ma ke gafarta wa duk wanda ya yi mana laifi.

    Kada ka bari a kai mu cikin jarraba.’ ”

  26. 1 ’Ya’yana ƙaunatattu, ina rubuta muku wannan ne don kada ku yi zunubi. Amma in wani ya yi zunubi, muna da wani wanda yake magana da Uba don taimakonmu, wato, Yesu Kiristi, Mai Adalci. 2 Shi ne hadayar kafara saboda zunubanmu, kuma ba don namu kaɗai ba amma har ma da zunuban duniya duka.

  27. 27 Sa’an nan ya ɗauki kwaf, ya yi godiya, ya kuma ba su, yana cewa, “Ku shassha daga cikinsa, dukanku. 28 Wannan jinina ne na sabon alkawari, wanda aka zubar saboda mutane da yawa, don gafarar zunubai.

  28. 16 Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami. 17 Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yă yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin yă ceci duniya ta wurinsa.

  29. 30 A dā Allah ya kawar da Allah ya kawar da kai ga zamanin jahilci, amma yanzu ya umarci dukan mutane a ko’ina su tuba. 31 Gama ya sa ranar da zai yi wa duniya shari’a da adalci ta wurin mutumin da ya naɗa. Ya riga ya ba da tabbacin wannan ga dukan mutane ta wurin tā da shi daga matattu.”

  30. 16 “Wannan shi ne alkawarin da zan yi da su

    bayan wannan lokaci,

    in ji Ubangiji.

    Zan sa dokokina a cikin zukatansu,

    in kuma rubuta su a kan zukatansu.”

    17 Sai ya ƙara da cewa,

    “Zunubansu da kurakuransu

    ba zan ƙara tunawa da su ba.”

    18 In an gafarta zunubai, babu sauran bukatar miƙa hadaya.

  31. 14 in mutanena, waɗanda ake kira da sunana, sun ƙasƙantar da kansu, suka kuma yi addu’a, suka nemi fuskata, suka kuma juye daga mugayen hanyoyinsu, zan ji daga sama in kuma gafarta zunubinsu in kuwa warkar da ƙasarsu.

  32. 9 Ubangiji Allahnmu mai jinƙai ne, mai gafartawa ne kuma, ko da yake mun yi masa tawaye;

  33. 43 Duk annabawa sun yi shaida game da shi cewa duk wanda ya ba da gaskiya gare shi zai sami gafarar zunubai ta wurin sunansa.”

  34. 17 “Yanzu bari Ubangiji yă nuna ikonsa, kamar dai yadda ka furta. 18 ‘Ubangiji mai jinkiri fushi ne, mai yawan ƙauna, mai gafarta zunubi da tawaye. Duk da haka ba ya ƙyale mai laifi, babu horo. Yana horin ’ya’ya saboda zunubin iyayensu har tsara ta uku, da ta huɗu.’ 19 Bisa ga ƙaunarka mai girma, ka gafarta zunubin mutanen nan, kamar dai yadda ka gafarta musu daga lokacin da suka bar Masar har zuwa yanzu.”

    20 Ubangiji ya amsa ya ce, “Na gafarta musu, yadda ka roƙa. 21 Duk da haka, muddin ina raye, kuma muddin ɗaukakar Ubangiji ta cika dukan duniya, 22 ko ɗaya daga cikinsu da suka ga ɗaukakata da mu’ujizai da na yi a Masar, da kuma a cikin hamada, da suka ƙi yin mini biyayya, suka kuma gwada ni har sau goma, 23 ba ko ɗayansu da zai gan ƙasar da na yi alkawari da rantsuwa zan ba wa kakanninsu. Ba ko ɗaya da ya rena ni, da zai taɓa ganinta.

  35. 5 Sa’an nan Ubangiji ya sauko a cikin girgije ya tsaya can tare da shi, ya kuma yi shelar sunansa. 6 Sai Ubangiji ya wuce a gaban Musa, ya yi shela ya ce, “Ni ne Ubangiji Allah mai tausayi, mai alheri, mai jinkirin fushi, cike da ƙauna da aminci, 7 nakan nuna ƙauna wa dubbai, nakan kuma gafarta mugunta, tawaye da zunubi. Amma ba na barin mai laifi, ba tare da na hore shi ba; nakan hukunta ’ya’ya da jikoki har tsara ta uku da ta huɗu saboda laifin iyaye.”

    8 Musa ya yi sauri ya rusuna har ƙasa, ya yi sujada. 9 Ya ce, “Ya Ubangiji, in na sami tagomashi a idanunka, bari Ubangiji yă tafi tare da mu. Ko da yake wannan mutane masu taurinkai ne, ka gafarta muguntanmu da zunubanmu, ka kuma sāke sa mu zama abin gādonka.”

  36. 5 Kai mai gafartawa da kuma mai alheri ne, ya Ubangiji,

    cike da ƙauna ga dukan waɗanda suke kira gare ka.

  37. 4 Ta haka Yohanna ya zo, yana baftisma a yankin hamada, yana kuma wa’azin baftismar tuba don gafarar zunubai. 5 Dukan ƙauyukan Yahudiya da dukan mutanen Urushalima suka fiffito zuwa wurinsa. Suna furta zunubansu, ya kuwa yi musu baftisma a Kogin Urdun.

  38. 59 Yayinda suke cikin jifansa, sai Istifanus ya yi addu’a ya ce, “Ubangiji Yesu, ka karɓi ruhuna.” 60 Sa’an nan ya durƙusa ya ɗaga murya ya ce, “Ubangiji, kada ka riƙe wannan zunubi a kansu.” Da ya faɗi haka, sai ya yi barci.

  39. 20 Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce, “Saurayi, an gafarta maka zunubanka.”

    21 Farisiyawa da malaman dokoki suka fara yin tunani a zukatansu, “Wane ne wannan mutum da yake saɓo haka? Wa zai iya gafarta zunubai, in ba Allah kaɗai ba?”

  40. 11 A cikinsa ne kuma aka yi muku kaciya, ba kuwa yin mutum ba, amma wadda Kiristi ya yi muku, ta wurin tuɓe halinku na mutuntaka. 12 Da yake an binne ku tare da shi cikin baftisma haka kuma aka tashe ku tare da shi ta wurin bangaskiyarku a cikin ikon Allah, wanda ya tashe shi daga matattu.

    13 Kun zama matattu saboda ku masu zunubi ne kuma saboda halin zunubanku aka ware. Sa’an nan Allah ya sa kuka rayu tare da Kiristi. Ya gafarta mana dukan zunubanmu. 14 Ya soke rubutacciyar doka tare da ƙa’idodinta, wadda take gāba da mu, take kuma hamayya da mu; ya kuma kawar da ta, ya kafe ta a kan gicciye. 15 Bayan ya ƙwace makaman ikoki da hukumomi, ya kunyata su a sarari, ya ci nasara a bisansu ta wurin gicciye.

  41. 10 “Ɗan mutum, faɗa wa gidan Isra’ila, ‘Ga abin da kuke cewa, “Laifofinmu da zunubanmu suna nawaita mana, muna kuma lalacewa saboda su. Ta ƙaƙa za mu rayu?” ’ 11 Ka faɗa musu, ‘Muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ba na jin daɗin mutuwar mugu, amma a maimako haka ya fi su juye daga hanyoyinsu su rayu. Ku juye! Ku juye daga mugayen hanyoyinku! Don me za ku mutu, ya gidan Isra’ila?’

    12 “Saboda haka, ɗan mutum, ka faɗa wa mutanen ƙasarka, ‘Adalcin adali ba zai cece shi sa’ad da ya ƙi yin biyayya ba, kuma muguntar mugu ba za tă sa ya fāɗi sa’ad da ya juya daga gare ta ba. Adali, in ya yi zunubi, ba za a bari yă rayu saboda adalcinsa na dā ba.’ 13 In na faɗa wa adali cewa tabbatacce zai rayu, amma sai ya dogara ga adalcinsa ya kuma aikata mugunta, babu ayyukan adalcinsa da za a tuna; zai mutu saboda muguntar da ya aikata. 14 Kuma in na ce wa mugu, ‘Tabbatacce za ka mutu,’ amma sai ya juye daga zunubinsa ya kuma yi abin da yake gaskiya da kuma daidai, 15 in ya mayar da jingina, ya mayar da abin da ya sata, ya kiyaye ƙa’idodin da suke ba da rai, ya daina yin mugunta, tabbatacce zai rayu; ba zai mutu ba. 16 Babu wani zunubin da ya aikata da za a tuna da shi. Ya yi abin da yake gaskiya da kuma daidai; tabbatacce zai rayu.

  42. 17 “Da hankalinsa ya dawo, sai ya ce, ‘Kai, bayin mahaifina guda nawa ne, da suke da abinci fiye da isashe, ni kuma ina nan, zan mutu don yunwa! 18 Zan tashi in koma wurin mahaifina, in ce masa, “Baba, na yi wa sama, na kuma yi maka zunubi. 19 Ni ban isa a ƙara kira na ɗanka ba. Ka mai da ni kamar ɗaya daga cikin bayinka.” ’ 20 Sai ya tashi ya kama hanya ya koma wurin mahaifinsa.

    “Amma tun yana nesa, mahaifinsa ya hange shi. Tausayi kuma ya kama shi, sai ya tashi ya ruga da gudu wurinsa, ya rungume shi, ya yi masa sumba.

    21 “Sai ɗan ya ce masa, ‘Baba, na yi wa sama, na kuma yi maka zunubi. Ni ban isa a ƙara kira na ɗanka ba.’

    22 “Amma mahaifin ya ce wa bayinsa, ‘Maza! Ku kawo riga mafi kyau ku sa masa. Ku sa zobe a yatsarsa, da takalma kuma a ƙafafunsa. 23 Ku kawo ɗan saniya mai ƙiba ku yanka. Bari mu yi biki mu yi shagali. 24 Gama ɗan nan nawa, da ya mutu, amma yanzu yana da rai kuma. Da ya ɓata, amma yanzu an same shi.’ Sai suka fara shagali.

  43. 46 Ya ce musu, “Wannan shi ne abin da aka rubuta, cewa dole Kiristi yă sha wahala, a rana ta uku kuma yă tashi daga matattu. 47 Kuma a cikin sunansa za a yi wa’azin tuba da gafarar zunubai, ga dukan ƙasashe. Za a kuwa fara daga Urushalima. 48 Ku ne shaidun waɗannan abubuwa. 49 Zan aika muku da abin da Ubana ya yi alkawari. Amma ku dakata a birnin tukuna, sai an rufe ku da iko daga sama.”

  44. 15 “Sai na yi tambaya na ce, ‘Wane ne kai, ya Ubangiji?’

    “Ubangiji ya ce, ‘Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa. 16 Yanzu ka tashi, ka tsaya da ƙafafunka. Na bayyana a gare ka don in naɗa ka bawa da kuma mai shaidar abin da ka gani game da ni da kuma abin da zan nuna maka. 17 Zan tsirar da kai daga mutanenka da kuma daga Al’ummai. Ina aikan ka zuwa gare su domin 18 ka buɗe idanunsu su kuwa juyo daga duhu zuwa haske, daga mulkin Shaiɗan kuma zuwa wurin Allah, domin su sami gafarar zunubai da kuma matsayi a cikin waɗanda aka tsarkake ta wurin bangaskiya a cikina.’

  45. 23 Gama sakamakon zunubi mutuwa ne, amma kyautar Allah rai madawwami ne a cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.

  46. 22 Tabbatacce, doka ta bukaci a tsabtacce kusa kowane abu da jini, kuma in ba tare da zub da jini ba babu gafara.

  47. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Sa’ad da annabi Natan ya zo wurinsa bayan Dawuda ya yi zina da Batsheba.

    1 Ka yi mini jinƙai, ya Allah,

    bisa ga ƙaunarka marar ƙarewa;

    bisa ga tausayinka mai girma

    ka shafe laifofina.

    2 Ka wanke dukan kurakuraina

    ka tsarkake ni daga zunubina.

    3 Gama ina sane da laifofina

    zunubaina kuma kullum suna a gabana.

    4 Kai kaɗai na yi wa zunubi

    na yi abin da yake mugu a idonka,

    ta haka an tabbatar kai mai gaskiya sa’ad da ka yi magana

    aka kuma nuna kai mai adalci ne sa’ad da ka hukunta.

    5 Tabbatacce ni mai zunubi ne tun haihuwa

    mai zunubi daga lokacin da mahaifiyata ta yi cikina.

  48. 1 A shekarar da Sarki Uzziya ya mutu, na ga Ubangiji zaune a kan kujerar sarauta a sama cike da ɗaukaka, zatinsa ya cika haikali. 2 A bisansa akwai serafofi, kowanne yana da fikafikai shida. Fikafikai biyu sun rufe fuskokinsu, da biyu suka rufe ƙafafunsu, biyu kuma da su suke tashi. 3 Suna kiran juna,

    “Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki! Ubangiji Maɗaukaki ne;

    duniya ta cika da ɗaukakarsa.”

    4 Da jin ƙarar muryoyinsu madogarai da madogaran ƙofa suka girgiza, haikali kuma ya cika da hayaƙi.

    5 Sai na tā da murya na ce, “Kaitona! Na shiga uku! Gama ni mutum ne mai leɓuna marar tsarki, kuma ina raye a cikin mutane masu leɓuna marasa tsarki, idanuna kuma sun ga Sarki, Ubangiji Maɗaukaki.”

    6 Sai ɗaya daga cikin serafofin ya yi firiya zuwa wurina tare da garwashi mai wuta a hannunsa, wanda ya ɗiba da arautaki daga bagade. 7 Da shi ne ya taɓa bakina ya ce, “Duba, wannan ya taɓa leɓunanka, yanzu fa an kawar da laifofinka, an kuma gafarta maka zunubanka.”

  49. 7 Masu albarka ne waɗanda suke masu jinƙai,

    gama za a nuna musu jinƙai.

  50. 21 “Kun dai ji an faɗa wa mutanen dā cewa, ‘Kada ka yi kisankai; kuma duk wanda ya yi kisankai za a hukunta shi.’ 22 Amma ina gaya muku, duk wanda ya yi fushi da ɗan’uwansa, za a hukunta shi. Kuma duk wanda ya ce wa ɗan’uwansa ‘Raka,’ za a kai shi gaban Majalisa. Amma duk wanda ya ce, ‘Kai wawa!’ Zai kasance a hatsarin shiga jahannama ta wuta.

    23 “Saboda haka, in kana cikin ba da baikonka a kan bagade, a can kuwa ka tuna cewa ɗan’uwanka yana riƙe da kai a zuci, 24 sai ka bar baikonka a can gaban bagade. Ka je ka shirya tukuna da ɗan’uwanka; sa’an nan ka zo ka ba da baikonka.

  51. 2 Waɗansu mutane suka kawo masa wani shanyayye, kwance a tabarma. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, “Kada ka damu saurayi, an gafarta maka zunubanka.”

    3 Da jin wannan, waɗansu malaman dokoki suka ce wa juna, “Wannan mutum yana yin saɓo!”

    4 Sane da tunaninsu, Yesu ya ce, “Me ya sa kuke da mugun tunani a zuciyarku? 5 Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuwa a ce, ‘Tashi ka yi tafiya?’ 6 Amma don ku san cewa Ɗan Mutum yana da iko a duniya yă gafarta zunubai.” Sai ya ce wa shanyayyen, “Tashi, ɗauki tabarmarka ka tafi gida.”

  52. 12 “Me kuka gani? In wani yana da tumaki ɗari, sai ɗaya daga cikinsu ta ɓace, ba sai yă bar tasa’in da taran a kan tuddai yă je neman guda ɗayan da ta ɓace ba? 13 In kuwa ya same ta, ina gaya muku gaskiya, zai yi murna saboda ɗayan fiye da tasa’in da taran da ba su ɓace ba. 14 Haka ma Ubanku da yake cikin sama ba ya so ko ɗaya daga cikin ƙananan nan yă ɓace.

    15 “In ɗan’uwanka ya yi maka laifi, ka je ka nuna masa laifinsa, tsakaninku biyu kaɗai. In ya saurare ka, ka maido da ɗan’uwanka ke nan. 16 Amma in bai saurare ka ba, ka je tare da mutum ɗaya ko biyu, domin ‘a tabbatar da kowace magana a bakin shaidu biyu ko uku.’ 17 In kuwa ya ƙi yă saurare su, sai ka gaya wa ikkilisiya; in kuma ya ƙi yă saurari ikkilisiya ma, ka yi da shi kamar marar sanin Allah ko mai karɓar haraji.

    18 “Gaskiya nake gaya muku, duk abin da kuka daure a duniya, za a daure a sama, duk kuma abin da kuka kunce a duniya, za a kunce shi a sama.

  53. 47 “Saboda haka ina gaya maka, zunubanta masu yawa, an gafarta mata, gama ƙaunarta mai yawa ce. Amma wanda aka gafarta wa kaɗan kuwa, yakan nuna ƙauna kaɗan.”

    48 Sai Yesu ya ce mata, “An gafarta miki zunubanki.”

  54. 29 Kashegari Yohanna ya ga Yesu yana zuwa wajensa sai ya ce, “Ku ga, ga Ɗan Rago na Allah mai ɗauke zunubin duniya!

  55. 1 Saboda haka, yanzu babu hukunci don waɗanda suke cikin Kiristi Yesu, 2 gama ta wurin Kiristi Yesu dokar Ruhu mai ba da rai ta ’yantar da ni daga Dokar Musa. 3 Gama abin da dokar ba tă iya yi saboda kāsawar mutuntaka ba, Allah ya yi shi sa’ad da ya aiko da Ɗansa a kamannin mutum mai zunubi, don yă zama hadaya ta zunubi. Ta haka, ya hukunta zunubi a cikin mutum mai zunubi. 4 Ya yi haka domin yă cika bukatun adalcin doka a cikinmu, mu da ba ma rayuwa bisa ga mutuntaka, sai dai bisa ga Ruhu.

  56. 8 Amma mene ne aka ce? “Maganar tana kusa da kai; tana cikin bakinka da kuma cikin zuciyarka,” wato, maganar bangaskiyan nan da muke shela. 9 Cewa in ka furta da bakinka, “Yesu Ubangiji ne,” ka kuma gaskata a zuciyarka cewa Allah ya tā da shi daga matattu, za ka sami ceto. 10 Gama da zuciyarka ce kakan gaskata a kuma kuɓutar da kai, da bakinka ne kuma kake furta a kuma cece ka.

  57. 9 Ba ku sani ba cewa mugaye ba za su gāji mulkin Allah ba? Kada fa a ruɗe ku. Ba masu fasikanci ko masu bautar gumaka ko masu zina ko karuwan maza, ko ’yan daudu, 10 ko ɓarayi ko masu kwaɗayi ko mashaya ko masu ɓata suna ko masu zamba da za su gāji mulkin Allah. 11 Haka waɗansu a cikinku ma suke a dā. Amma an wanke ku, an tsarkake ku, aka kuma sa kuka zama marasa laifi cikin sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma ta wurin Ruhun Allahnmu.

  58. 16 Yanzu me kake jira? Ka tashi, a yi maka baftisma, a wanke zunubanka, ta wurin kira bisa ga sunansa.’

  59. 8 Fiye da kome, ku ƙaunaci juna sosai, domin ƙauna tana rufe zunubai masu ɗumbun yawa.

  60. 12 Ina rubuta muku, ’ya’yana ƙaunatattu,

    domin an gafarta muku zunubanku saboda sunansa.

  61. 13 Sai Dawuda ya ce wa Natan, “Na yi wa Ubangiji zunubi.”

    Natan ya ce, “Ubangiji ya yafe maka zunubin. Ba za ka mutu ba.

  62. 12 Ka tafi, ka yi shelar saƙon nan wajen arewa cewa,

    “ ‘Ki komo, Isra’ila marar bangaskiya,’ in ji Ubangiji,

    ‘Ba zan ƙara yin fushi da ke ba,

    gama ni mai jinƙai ne,’ in ji Ubangiji,

    ‘Ba zan yi fushi da ke har abada ba.

  63. 21 Sai Yesu ya sāke ce musu, “Salama tă kasance tare da ku! Kamar yadda Uba ya aiko ni, haka ni ma ina aikan ku.” 22 Da wannan sai ya hura musu numfashinsa ya ce, “Ku karɓi Ruhu Mai Tsarki. 23 Duk wanda kuka gafarta wa zunubansa, an gafarta masa ke nan. Duk wanda ba ku gafarta wa ba kuwa, ba a gafarta masa ba ke nan.”

  64. 18 Da yawa cikin waɗanda suka gaskata yanzu suka zo a fili suka furta mugayen ayyukansu.

  65. 6 Irin wannan mutum, horon da yawancin mutane suka yi masa ya isa haka. 7 Yanzu fa, a maimako, gara ku yafe masa, ku kuma ta’azantar da shi, don kada baƙin ciki mai yawa yă sha kansa. 8 Saboda haka, ina roƙonku, ku sāke nuna masa ƙaunarku. 9 Abin da ya sa na rubuta muku shi ne don in ga ko za ku jimre da gwajin nan, kuna kuma yin biyayya ta kowace hanya. 10 In kuka gafarta wa wani, ni ma na gafarta masa. Abin da na gafarta kuwa, in har ma da abin gafartawa, saboda ku ne na gafarta masa, albarkacin Kiristi, 11 don kada Shaiɗan yă rinjaye mu. Da yake muna sane da dabarunsa.

  66. 10 Baƙin ciki irin na tsoron Allah yana kai ga tuban da yake kawo ceto, ba ya kuma kawo baƙin ciki, amma baƙin ciki irin na duniya yakan kawo mutuwa.

  67. 29 Kada wata ƙazamar magana ta fita daga bakunanku, sai dai abin da yake da amfani don gina waɗansu bisa ga bukatunsu. Ta haka maganarku za tă zama da amfani ga masu jinta. 30 Kada kuma ku ɓata wa Ruhu Mai Tsarki na Allah rai, wanda da shi aka hatimce ku da shi don ranar fansa. 31 Ku rabu da kowane irin ɗacin rai, haushi da hasala, faɗa da ɓata suna, ku rabu da kowace irin ƙeta. 32 Ku yi alheri, ku kuma ji tausayin juna, kuna gafarta wa juna, kamar yadda a cikin Kiristi, Allah ya gafarta muku.