45 Bible Verses About Satan's Tricks
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
1 To, maciji dai ya fi kowane a cikin namun jejin da Ubangiji Allah ya yi wayo. Ya ce wa macen, “Tabbatacce ne Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga kowane itace a lambu’?”
2 Macen ta ce wa macijin, “Za mu iya ci daga ’ya’ya itatuwa a lambun, 3 amma Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga ’ya’yan itacen da yake tsakiyar lambu, kada kuma ku taɓa shi, in ba haka ba kuwa za ku mutu.’ ”
4 Maciji ya ce wa macen, “Tabbatacce ba za ku mutu ba. 5 Gama Allah ya san cewa sa’ad da kuka ci daga itacen idanunku za su buɗe, za ku kuma zama kamar Allah, ku san abin da yake mai kyau da abin da yake mugu.”
6 Sa’ad da macen ta ga ’ya’yan itacen suna da kyau don abinci, abin sha’awa ga ido, abin marmari kuma don samun hikima, sai ta tsinka ta ci, ta kuma ba da waɗansu wa mijinta wanda yake tare da ita, shi ma ya ci.
-
10 A ƙarshe, bari ƙarfin ikon Ubangiji yă ba ku ƙarfi. 11 Ku yafa dukan kayan yaƙin da Allah yake bayarwa, don ku iya kāre kanku daga dabarun Shaiɗan. 12 Gama ba da mutane da suke nama da jini ne muke yaƙi ba. Muna yaƙi ne da ikoki, da hukumomi, da masu mulkin duhu, da kuma a ikokin da suke cikin a sararin sama. 13 Saboda haka sai ku yafa dukan kayan yaƙi na Allah, domin sa’ad da ranar mugun nan ta zo, ku iya yin tsayin daka, bayan kuma kuka gama kome, ku dāge. 14 Saboda haka fa ku dāge, ku sa gaskiya tă zama ɗamararku, adalci yă zama sulkenku, 15 shirin kai bisharar salama yă zama kamar takalmi a ƙafafunku. 16 Ban da waɗannan kuma, ku ɗauki garkuwar bangaskiya, wadda za ku iya kashe dukan kibiyoyin wutar Mugun nan da ita. 17 Ku kuma ɗauki hular kwano na ceto, da takobin Ruhu, wato, Maganar Allah.
18 A koyaushe ku kasance kuna addu’a da roƙo ta wurin ikon Ruhu ba fasawa. A kan wannan manufa ku zauna a faɗake da matuƙar naci, kuna yin wa dukan mutanen Ubangiji addu’a. 19 Ku kuma yi addu’a domina, don duk sa’ad da na buɗe bakina, in sami kalmomi babu tsoro, don in sanar da asirin bishara, 20 wadda nake jakadanta cikin sarƙoƙi. Ku yi addu’a don in iya yin shelarta babu tsoro, yadda ya kamata in yi.
-
8 Ku zama masu kamunkai, ku kuma zauna a faɗake. Abokin gābanku, Iblis yana kewayewa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai cinye. 9 Ku yi tsayayya da shi, kuna tsayawa daram cikin bangaskiya, domin kun san cewa ’yan’uwanku ko’ina a duniya suna shan irin wahalolin nan.
-
7 Aka kuwa yi yaƙi a sama. Mika’ilu da mala’ikunsa yaƙi macijin, maciji da mala’ikunsa su ma suka mai da martani. 8 Amma macijin nan ba shi da isashen ƙarfi, har suka rasa matsayinsu a sama. 9 Aka jefar da ƙaton jan macijin ƙasa, tsohon maciji nan da ake kira Iblis, ko Shaiɗan, wanda ya ɓad da dukan duniya. Aka jefar da shi ƙasa, tare da mala’ikunsa a duniya.
10 Sa’an nan na ji babbar murya daga sama tana cewa,
“Yanzu ceto da iko da mulkin Allahnmu,
da kuma ikon Kiristinsa.
Gama mai zargin ’yan’uwanmu,
wanda yake zarginsu a gaban Allahnmu dare da rana,
an jefar da shi ƙasa.
11 Sun ci nasara a kansa
ta wurin jinin Ɗan Ragon
da ta wurin kalmar shaidarsu;
ba su ƙaunaci rayukansu sosai
har da za su ja da baya daga mutuwa.
12 Saboda haka ku yi farin ciki, ku sammai,
da ku da kuke zaune a cikinsu!
Amma kaiton duniya da kuma teku,
gama Iblis ya sauko gare ku!
Ya cika da fushi,
domin ya san cewa lokacinsa ya rage kaɗan.”
-
42 Yesu ya ce musu, “Da Allah ne Ubanku, da kun ƙaunace ni, gama daga Allah na fito yanzu kuma ga ni nan. Ban zo saboda kaina ba, amma shi ne ya aiko ni. 43 Me ya sa ba kwa gane da maganata? Don ba kwa iya jin abin da nake faɗi. 44 Ku na ubanku ne, Iblis, kuna kuwa so ku aikata abin da ubanku yake so. Shi mai kisankai ne tun farko. Ba ruwansa da gaskiya, gama gaskiya ba ta cikinsa. Yayinda yake ƙarya, yana yin halinsa ne, gama shi maƙaryaci ne, uban ƙarairayi kuma. 45 Amma domin ina faɗin gaskiya, ba kwa gaskata! 46 Akwai waninku da zai iya haƙaƙƙewa na taɓa yin zunubi? In kuwa gaskiya na faɗa, me ya sa ba kwa gaskata ni? 47 Wanda yake na Allah, yakan ji abin da Allah yake faɗi. Abin da ya sa ba kwa jin sa kuwa shi ne don ku ba na Allah ba ne.”
-
10 In kuka gafarta wa wani, ni ma na gafarta masa. Abin da na gafarta kuwa, in har ma da abin gafartawa, saboda ku ne na gafarta masa, albarkacin Kiristi, 11 don kada Shaiɗan yă rinjaye mu. Da yake muna sane da dabarunsa.
-
12 Zan kuma ci gaba da yin abin da nake yi, domin in toshe kafar mutanen nan da suke fariya, suna nema mu daidaita da su. 13 Gama irin waɗannan mutane manzannin ƙarya ne, ma’aikata ne masu ruɗi, sun ɓad da kamanni kamar su manzannin Kiristi ne. 14 Ba abin mamaki ba ne, gama Shaiɗan kansa ma yana ɓad da kamanni kamar shi mala’ikan haske ne. 15 Don haka, ba abin mamaki ba ne, in bayin Shaiɗan sun ɓad da kamanni kamar su bayin adalci ne. A ƙarshe, za a sāka musu gwargwadon ayyukansu.
-
6 Wata rana mala’iku suka kawo kansu gaban Ubangiji, Shaiɗan shi ma ya zo tare da su. 7 Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Daga ina ka fito?”
Shaiɗan ya amsa wa Ubangiji ya ce, “Daga yawo a duniya ina kai da kawowa a cikinta.”
8 Sai Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Ko ka ga bawana Ayuba? A cikin duniya babu wani kamar sa; shi marar laifi ne, adali kuma, mutum ne mai tsoron Allah, ba ruwansa da mugunta.”
9 Sai Shaiɗan ya amsa ya ce, “Haka kawai Ayuba yake tsoron Allah? 10 Ba ka kāre shi da iyalinsa gaba ɗaya da duk mallakarsa ba? Ka Albarkaci ayyukan hannunsa yadda dabbobinsa duk sun cika ko’ina. 11 Ka ɗan miƙa hannunka ka raba shi da duk abin da yake da shi, ba shakka zai la’anta ka kana ji, kana gani.”
-
3 Ko da bishararmu a rufe take, tana a rufe ne ga waɗanda suke hallaka. 4 Allahn zamanin nan ya makanta hankulan marasa ba da gaskiya, yadda har ba za su iya ganin hasken bishara ta ɗaukakar Kiristi ba, wanda yake kamannin Allah.
-
7 Saboda haka, ku miƙa kanku ga Allah. Ku yi tsayayya da Iblis, zai kuwa guje ku.
-
1 Ku kam, a dā ku matattu ne saboda laifofinku da kuma zunubanku. 2 Kun yi rayuwa kamar yadda sauran mutanen duniya suke yi, cike da zunubi, kuna biyayya ga sarki masu ikon sarari sama, wato, ruhun nan da yanzu yake aiki a cikin masu ƙin biyayya ga Allah. 3 Dukanmu a dā mun yi irin rayuwan nan a cikinsu, muna bin kwaɗayi da sha’awace-sha’awacen jikunanmu da tunaninmu. Kamar sauran mutane, mun cancanci fushin Allah.
-
1 Na kuma ga wani mala’ika yana saukowa daga sama, yana da mabuɗin Abis yana kuma riƙe da ƙaton sarƙa a hannunsa. 2 Ya kama macijin, wannan tsohon maciji, wanda yake shi ne Iblis, ko kuwa Shaiɗan, aka kuma ɗaura shi har shekara dubu. 3 Ya jefa shi cikin Abis, ya kuma kulle ya sa hatimi a kansa, don a hana kada yă ƙara ruɗin al’ummai, sai shekarun nan dubu sun cika. Bayan wannan, dole a sake shi na ɗan lokaci.
4 Na ga kursiyoyi inda waɗanda aka ba su ikon shari’a suke zama a kai. Sai na ga rayukan waɗanda aka yanke kawunansu saboda shaidarsu don Yesu saboda kuma maganar Allah. Ba su yi wa dabban nan ko siffarta sujada ba, ba su kuma sami alamarta a goshinsu ko a hannuwansu ba. Suka sāke rayuwa daga matattu, suka yi mulki tare da Kiristi shekaru dubu. 5 (Sauran matattu ba su sāke rayuwa ba, sai da shekaru dubun nan suka cika.) Wannan fa shi ne tashin matattu na farko. 6 Masu albarka da kuma tsarki ne waɗanda suke da rabo a tashin matattu na farko. Mutuwa ta biyu ba ta da iko a kansu, sai dai za su zama firistocin Allah da kuma na Kiristi za su kuma yi mulki tare da shi na shekaru dubu.
7 Sa’ad da shekaru dubun nan suka cika, za a saki Shaiɗan daga kurkukun da yake, 8 zai kuma fito don yă ruɗi al’ummai da suke a kursuyoyi huɗu na duniya, Gog da Magog, yă tattara su don yaƙi. Yawansu kuwa ya yi kamar yashi a bakin teku.
-
8 Sa’an nan za a bayyana mai tawayen, Ubangiji Yesu kuwa zai hamɓare shi da numfashin bakinsa yă kuma hallaka shi da darajar dawowarsa. 9 Zuwan mai tawayen nan zai zama ta wurin aikin Shaiɗan da aka bayyana cikin kowane irin ayyukan banmamaki, alamu da abubuwan banmamaki na ƙarya, 10 da kuma cikin kowace irin muguntar da take ruɗin waɗanda suke hallaka. Sun hallaka ne domin sun ƙi su ƙaunaci gaskiya don su sami ceto. 11 Saboda haka Allah zai aiko musu da babban ruɗu don su gaskata ƙarya 12 don kuma a hukunta dukan waɗanda ba su gaskata gaskiyar ba sai dai suke jin daɗin mugunta.
-
8 Duk mai aikata abin da yake zunubi shi na Iblis ne, domin Iblis mai aikata zunubi ne tun farko. Dalilin da ya sa Ɗan Allah ya bayyana kuwa shi ne don yă rushe aikin Iblis.
-
9 Na san wahalarka da kuma talaucinka, duk da haka kai mai arziki ne! Na san ɓata suna da waɗannan suke yi maka waɗannan da suke cewa su Yahudawa ne alhali kuwa ba haka ba ne, su dai majami’ar Shaiɗan ne. 10 Kada ka ji tsoron wahalar da kake gab da sha. Ina gaya maka, Iblis zai sa waɗansunku a kurkuku don yă gwada ku. Za ku sha tsanani na kwana goma. Ka yi aminci ko da za a kashe ka, ni kuwa zan ba ka rawanin rai.
-
1 Sai Shaiɗan ya tashi gāba da Isra’ila, ya zuga Dawuda ya ƙidaya Isra’ila.
-
1 Saboda haka, yanzu babu hukunci don waɗanda suke cikin Kiristi Yesu, 2 gama ta wurin Kiristi Yesu dokar Ruhu mai ba da rai ta ’yantar da ni daga Dokar Musa. 3 Gama abin da dokar ba tă iya yi saboda kāsawar mutuntaka ba, Allah ya yi shi sa’ad da ya aiko da Ɗansa a kamannin mutum mai zunubi, don yă zama hadaya ta zunubi. Ta haka, ya hukunta zunubi a cikin mutum mai zunubi. 4 Ya yi haka domin yă cika bukatun adalcin doka a cikinmu, mu da ba ma rayuwa bisa ga mutuntaka, sai dai bisa ga Ruhu.
5 Waɗanda suke rayuwa bisa ga mutuntaka sun kafa hankulansu a kan sha’awace-shawa’acen jiki; amma waɗanda suke rayuwa bisa ga Ruhu sun kafa hankulansu a kan abubuwan da Ruhu yake so. 6 Ƙwallafa rai ga al’amuran halin mutuntaka ƙarshensa mutuwa ne, ƙwallafa rai ga al’amuran Ruhu kuwa rai ne da salama; 7 hankalin mai zunubi na gāba da Allah. Ba ya biyayya da dokar Allah, ba kuwa zai iya yin haka ba. 8 Waɗanda mutuntaka yake mulkinsu ba za su iya su gamshi Allah ba.
9 Ku kam, ana mulkinku ba ta wurin mutuntaka ba, sai dai ta wurin Ruhu, in Ruhun Allah yana zaune a cikinku. In kuma wani ba shi da Ruhun Kiristi, shi ba na Kiristi ba ne.
-
13 Ina rubuta muku, ubanni,
domin kun san shi wanda yake tun farko.
Ina rubuta muku, samari,
domin kun ci nasara a kan mugun nan.
14 Ina rubuta muku, ’ya’yana ƙaunatattu,
domin kun san Uba.
Ina rubuta muku, ubanni,
domin kun san shi wanda yake tun farko.
Ina rubuta muku, samari,
domin kuna da ƙarfi,
maganar Allah kuwa tana zaune a cikinku,
kun kuma ci nasara a kan mugun nan.
15 Kada ku ƙaunaci duniya, ko wani abin da yake cikinta. In wani yana ƙaunar duniya, ƙaunar Uba ba ta cikinsa. 16 Gama duk abin da yake na duniya, kamar sha’awace-sha’awacen mutuntaka, sha’awar idanunsa, da kuma taƙama da abin da yake da shi, yake kuma yi, ba daga wurin Uba suke fitowa ba sai dai daga duniya.
-
31 “Siman, Siman, Shaiɗan ya nemi izini ya sheƙe ka kamar alkama. 32 Amma na yi maka addu’a, Siman, domin kada bangaskiyarka ta kāsa. Bayan ka juyo, ka ƙarfafa ’yan’uwanka.”
33 Amma ya amsa ya ce, “Ubangiji, ina a shirye in tafi tare da kai har kurkuku, ko mutuwa ma.”
34 Yesu ya ce, “Ina gaya maka Bitrus, kafin zakara ya yi cara yau, za ka yi mūsun sanina sau uku.”
-
3 Sai dai ina tsoro kada yă zama, kamar yadda maciji ya yaudari Hawwa’u da makircinsa, ku ma a bauɗar da hankalinku daga sahihiyar biyayya amintacciya ga Kiristi. 4 Gama in wani ya zo wurinku yana wa’azin wani Yesu dabam da wanda muka yi wa’azinsa, ko kuma in kun karɓi wani ruhu dabam da wanda kuka karɓa, ko wata bishara dabam da wadda kuka karɓa, ya nuna kun yarda da su ke nan cikin sauƙinkai.
-
3 Sai Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Ko ka ga bawana Ayuba? A cikin duniya babu wani kamar sa; shi marar laifi ne, adali kuma, mutum ne mai tsoron Allah ba ruwansa da mugunta. Kuma har yanzu bai fasa zama mai aminci ba duk da wahalar da ka sa na bari ka ba shi ba tare da wani dalili ba.”
4 Shaiɗan ya amsa ya ce, “Fata don fata! Mutum zai iya rabuwa da duk abin da yake da shi domin ransa. 5 Ka ɗan taɓa lafiyar jikinsa ka gani ba shakka zai la’anta ka kana ji kana gani.”
6 Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “To, shi ke nan, duk abin da yake da shi yana hannunka, amma kada ka taɓa shi, shi kansa.”
7 Sai Shaiɗan ya bar Ubangiji, ya je ya sa wa Ayuba ƙuraje masu zafi a jikinsa daga tafin ƙafafunsa har zuwa kansa.
-
36 Sa’an nan ya bar taron ya shiga gida. Almajiransa kuwa suka zo wurinsa suka ce, “Bayyana mana misalin ciyayin nan a gona.”
37 Ya amsa ya ce, “Mai yafa irin mai kyan nan, shi ne Ɗan Mutum. 38 Gonar kuwa ita ce duniya, irin nan mai kyau kuwa suna a matsayin ’ya’yan mulkin. Ciyayin nan kuma su ne ’ya’yan mugun nan, 39 abokin gāban da yake shuka su kuwa, Iblis ne. Lokacin girbi kuma shi ne ƙarshen zamani, masu girbin kuwa su ne mala’iku.
40 “Kamar yadda aka tattara ciyayin aka kuma ƙone a wuta, haka zai zama a ƙarshen zamani. 41 Ɗan Mutum zai aiki mala’ikunsa, su kuwa cire daga mulkinsa kome da yake jawo zunubi da kuma duk masu aikata mugunta. 42 Za su jefa su cikin wuta mai zafi, inda za a yi kuka da cizon haƙora. 43 Sa’an nan masu adalci za su haskaka kamar rana a mulkin Ubansu. Duk mai kunnen ji, yă ji.”
-
3 Ko da yake muna cikin duniya, ba ma yaƙi kamar yadda duniya take yi. 4 Makaman da muke yaƙi da su, ba makamai na duniya ba ne. Sai dai na ikon Allah ne, masu rushe wuraren mafaka masu ƙarfi. 5 Muna ka da masu gardama da kowane tunanin ɗaga kai da yake kafa kansa gāba da sanin Allah, muna kuma jan hankalin kowa ga bautar Kiristi. 6 A shirye muke mu hori kowane rashin biyayya, sa’ad da biyayyarku ta cika.
-
22 Ka yi nesa da mugayen sha’awace-sha’awace na ƙuruciya, ka kuma bi adalci, bangaskiya, ƙauna da kuma salama, tare da waɗanda suke kira ga Ubangiji daga zuciya mai tsabta. 23 Kada wani abu yă haɗa ka da gardandamin banza da wofi, domin ka san yadda suke jawo faɗa. 24 Bai kamata bawan Ubangiji yă zama mai neman faɗa ba; a maimako, dole yă nuna alheri ga kowa, mai iya koyarwa, mai haƙuri kuma. 25 Waɗanda suke gāba da shi kuwa dole yă yi musu gargaɗi cikin hankali, da fata Allah zai sa su tuba su kai ga sanin gaskiya, 26 su kuma dawo cikin hankulansu su kuɓuta daga tarkon Iblis, wanda ya sa suka zama kamammu don su aikata nufinsa.
-
13 Sai Ubangiji Allah ya ce wa matar, “Me ke nan kika yi?”
Matar ta ce, “Macijin ne ya ruɗe ni, na kuwa ci.”
14 Saboda haka Ubangiji Allah ya ce wa macijin, “Saboda ka yi haka,
“Na la’anta ka cikin dukan dabbobi da kuma cikin dukan namun jeji!
Daga yanzu rubda ciki za ka yi tafiya
turɓaya kuma za ka ci
dukan kwanakin rayuwarka.
15 Zan kuma sa ƙiyayya
tsakaninka da macen,
tsakanin zuriyarka da zuriyarta.
Zai ragargaje kanka,
kai kuma za ka sari ɗiɗɗigensa.”
-
24 Amma da Farisiyawa suka ji haka, sai suka ce, “Ahab, da Be’elzebub sarkin aljanu ne kaɗai, wannan mutum yake fitar da aljanu.”
25 Yesu kuwa ya san tunaninsu sai ya ce musu, “Duk mulkin da yake gāba da kansa zai lalace, kuma duk birni ko gidan da yake rabe gāba da kansa ba zai ɗore ba. 26 In Shaiɗan yana fitar da Shaiɗan, ai, ya rabu yana gāba da kansa ke nan. Yaya kuwa mulkinsa zai ɗore?
-
10 Ɓarawo yakan zo don yă yi sata ne kawai da kisa da kuma ɓarna. Ni kuwa na zo ne don su sami rai, su kuma same shi a yalwace.
-
15 “Ku yi hankali da annabawan ƙarya. Sukan zo muku da kamannin tumaki, amma daga ciki mugayen kyarketai ne. 16 Ta wurin aikinsu za ku gane su. Mutane suna iya tsinkan inabi a jikin ƙaya, ko kuwa ɓaure a jikin sarƙaƙƙiya?
-
1 Yesu kuwa cike da Ruhu Mai Tsarki, ya dawo daga Urdun, Ruhu kuma ya kai shi cikin hamada, 2 inda kwana arba’in, Iblis ya gwada shi. Bai ci kome ba a cikin kwanakin nan, a ƙarshensu kuwa ya ji yunwa.
3 Iblis ya ce masa, “In kai Ɗan Allah ne, ka faɗa wa wannan dutse yă zama burodi.”
4 Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake, ‘Ba da abinci kaɗai mutum zai rayu ba.’”
5 Iblis ya kai shi can kan wani wuri mai tsawo, ya nunnuna masa a ƙyiftawar ido dukan mulkokin duniya. 6 Ya ce masa, “Zan ba ka dukan ikonsu da darajarsu, gama ni aka danƙa wa, kuma zan bai wa duk wanda na ga dama. 7 Saboda haka in ka yi mini sujada, dukan wannan zai zama naka.”
8 Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake, ‘Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, kuma shi kaɗai za ka bauta wa.’”
9 Sai Iblis, ya kai shi Urushalima ya sa ya tsaya a kan wuri mafi tsayi na haikali ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, ka yi tsalle daga nan zuwa ƙasa. 10 Gama a rubuce yake,
“ ‘Zai umarci mala’ikunsa game da kai,
su kiyaye ka da kyau;
11 za su tallafe ka da hannuwansu,
don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.’”
12 Yesu ya amsa ya ce, “An ce, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’”
13 Da Iblis ya gama dukan wannan gwajin, ya bar shi sai lokacin da wata dama ta samu.
-
1 Abokaina ƙaunatattu, ba kowane ruhu za ku gaskata ba, sai dai ku gwada ruhohi don ku ga ko daga Allah ne, domin annabawan ƙarya da yawa sun fito duniya. 2 Ga yadda za ku gane Ruhun Allah, duk ruhun da ya yarda cewa Yesu Kiristi ya zo cikin jiki, to, daga Allah yake. 3 Amma duk ruhun da bai yarda da Yesu ba, ba daga Allah ba ne, ruhun magabcin Kiristi ne, wanda kuka ji yana zuwa, har ma ya riga ya shigo duniya.
4 Ku, ’ya’yana ƙaunatattu, ku daga Allah ne, kun kuma yi nasara a kan magabtan Kiristi, domin wanda yake a cikinku ya fi wanda yake a duniya girma. 5 Su daga duniya ne saboda haka suke magana yadda duniya take ganin abubuwa, duniya kuwa tana sauraronsu. 6 Mu daga Allah ne, kuma duk wanda ya san Allah yakan saurare mu. Amma duk wanda ba daga Allah ba, ba ya sauraronmu. Ta haka ne muke gane Ruhun gaskiya, da kuma ruhun ƙarya.
-
1 Sa’an nan Ruhu ya kai Yesu cikin hamada don Iblis yă gwada shi. 2 Bayan ya yi azumi yini arba’in da kuma dare arba’in, sai ya ji yunwa. 3 Sai mai gwajin ya zo wurinsa ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, ka ce wa duwatsun nan su zama burodi.”
4 Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake cewa, ‘Ba da abinci kaɗai mutum yake rayuwa ba, sai dai da kowace kalmar da take fitowa daga bakin Allah.’”
5 Sai Iblis ya kai shi birni mai tsarki, ya kai shi can wuri mafi tsayi duka na haikali. 6 Ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, yi tsalle ka sauka ƙasa. Gama a rubuce yake,
“ ‘Zai umarci mala’ikunsa game da kai,
za su tallafe ka da hannuwansu,
don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.’”
7 Yesu ya amsa masa ya ce, “A rubuce yake kuma cewa, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’”
8 Har wa yau, Iblis ya kai shi bisa wani dutse mai tsawo sosai, ya nunnuna masa dukan mulkokin duniya da darajarsu. 9 Ya ce, “Zan ba ka dukan wannan, in za ka durƙusa ka yi mini sujada.”
10 Sai Yesu ya ce masa, “Rabu da ni, Shaiɗan! Gama a rubuce yake, ‘Yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kaɗai kuma za ka bauta wa.’”
11 Sa’an nan Iblis ya bar shi, mala’iku kuwa suka zo suka yi masa hidima.
-
1 Yanzu fa, Bikin Burodi Marar Yistin da ake kira Bikin Ƙetarewa ya yi kusa, 2 manyan firistoci da malaman dokoki kuma suna neman yadda za su kashe Yesu a ɓoye, don suna tsoron mutane. 3 Shaiɗan kuwa ya shiga Yahuda, wanda ake kira Iskariyot, ɗaya daga cikin Sha Biyun. 4 Sai Yahuda ya je ya tattauna da manyan firistoci, da ma’aikatan ’yan gadin haikali, a kan yadda zai ba da Yesu a gare su. 5 Suka kuwa yi murna, suka yarda su ba shi kuɗi. 6 Ya ko yarda, ya fara neman zarafin da zai ba da Yesu a gare su, sa’ad da taro ba sa nan tare da shi.
-
5 Kada ku ƙi kwana da juna sai ko kun yarda a junanku kuma na ɗan lokaci, don ku himmantu ga addu’a. Sa’an nan ku sāke haɗuwa don kada Shaiɗan yă jarrabce ku saboda rashin ƙamewarku.
-
24 Gama Kiristi masu yawa na ƙarya, da annabawan ƙarya za su firfito, su kuma aikata manyan alamu da ayyukan banmamaki don su ruɗi har da zaɓaɓɓu ma in zai yiwu.
-
12 Nan da nan, sai Ruhu ya kai shi cikin hamada, 13 ya kuma kasance a hamada kwana arba’in, Shaiɗan yana gwada shi. Yana tare da namomin jeji, mala’iku kuma suka yi masa hidima.
-
22 Malaman dokokin da suka zo daga Urushalima suka ce, “Ai, yana da Be’elzebub! Da ikon sarkin aljanu yake fitar da aljanu.”
23 Sai Yesu ya kira su, ya yi musu magana da misalai ya ce, “Yaya Shaiɗan zai fitar da Shaiɗan? 24 In mulki yana gāba da kansa, wannan mulki ba zai tsaya ba. 25 In gida yana gāba da kansa, wannan gida ba zai tsaya ba. 26 In kuwa Shaiɗan yana gāba da kansa, ya kuma rabu biyu, ba zai tsaya ba, ƙarshensa ya zo ke nan.
-
5 Saboda wannan, sa’ad da ban iya jimrewa ba, sai na aika domin in sami labarin bangaskiyarku, da fata kada yă zama mai jarraban nan ya riga ya jarrabce ku, ƙoƙarinmu kuma yă zama banza.
-
7 Dole kuma yă kasance da shaida mai kyau ga waɗanda suke na waje, don kada yă zama abin kunya yă kuma fāɗa cikin tarkon Iblis.
-
7 Don kada in cika da girman kai saboda waɗannan mafifitan manyan wahayoyi, sai aka sa mini wata ƙaya a jikina wadda ta zama ɗan saƙon Shaiɗan, don ta wahalshe ni. 8 Sau uku na roƙi Ubangiji yă raba ni da wannan abu. 9 Amma ya ce mini, “Alherina ya ishe ka, domin a cikin rashin ƙarfi ne ake ganin cikar ikona.” Saboda haka, zan ƙara yin taƙama da farin ciki game da rashin ƙarfina, domin ikon Yesu Kiristi yă zauna tare da ni. 10 Shi ya sa nake murna cikin rashin ƙarfi, da zagi, da shan wahaloli, da tsanantawa, da matsaloli, saboda Kiristi. Don a sa’ad da nake marar ƙarfi a nan ne nake da ƙarfi.
-
13 Sa’ad da aka jarrabci mutum, kada yă ce, “Allah ne yake jarrabtarsa.” Gama ba ya yiwuwa a jarrabci Allah da mugunta, shi kuma ba ya jarrabtar kowa; 14 amma akan jarrabce kowane mutum sa’ad da muguwar sha’awarsa ta janye shi ta kuma rinjaye shi. 15 Sa’an nan, bayan da sha’awar ta yi ciki, takan haifi zunubi; zunubi kuwa, sa’ad da ya balaga yakan haifi mutuwa.
-
6 Suka zaga dukan tsibirin har sai da suka kai Bafos. A can suka sadu da wani mutumin Yahuda mai sihiri, annabin ƙarya, mai suna Bar-Yesu, 7 wanda yake ma’aikacin muƙaddas Sergiyus Bulus ne. Muƙaddas ɗin kuwa mai azanci ne ƙwarai, ya sa aka kira Barnabas da Shawulu don yana so ya ji maganar Allah. 8 Amma Elimas mai sihirin nan (domin ma’anar sunansa ke nan) ya yi hamayya da maganarsu ya kuma yi ƙoƙari ya juyar da muƙaddas ɗin daga bangaskiya. 9 Sai Shawulu, wanda kuma ake kira Bulus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya kafa wa Elimas ido ya ce, 10 “Kai ɗan Iblis ne abokin gāban dukan abin da yake daidai! Kana cike da kowane irin ruɗi da munafunci. Ba za ka daina karkata hanyoyin da suke daidai na Ubangiji ba? 11 Ga shi hannun Ubangiji yana gāba da kai. Za ka makance, kuma ba za ka ga rana ba har na wani lokaci.”
Nan take, hazo da duhu suka sauko a kansa, ya yi ta lallubawa, yana neman wanda zai yi masa jagora.
-
11 Saboda haka Kiristi kansa ya ba wa waɗansu baiwa su zama manzanni, waɗansu su zama annabawa, waɗansu su zama masu wa’azi, waɗansu kuma su zama fastoci, da kuma malamai. 12 Ya yi haka don yă shirya mutanensa saboda ayyukan hidima, don a gina jikin Kiristi. 13 Wannan zai ci gaba har sai mun zama ɗaya a cikin bangaskiya da kuma ta wurin fahimtarmu na Ɗan Allah. Sa’an nan za mu zama balagaggu, kamar yadda Kiristi yake, mu kuma zama gaba ɗaya cikakku kamar sa.
14 An yi wannan kuwa don kada mu koma zama kamar yara, muna ta canja zukatanmu game da abin da muka gaskata don kawai wani ya faɗa mana wani abu dabam, ko domin wani ya yi wayo ya ruɗe mu, ya sa ƙarya ta zama kamar gaskiya. 15 Ya kamata kullum ƙauna tă sa mu faɗa gaskiya. Ta haka za mu yi girma a kowace hanya, mu kuma zama kamar Kiristi, wanda yake kan 16 dukan jiki. Shi ne ya haɗe jiki duka, ya kuma sa dukan gaɓoɓin jiki suna aiki daidai, yayinda kowace gaɓa take aikinta cikin ƙauna.
-
11 Ya kamata mace ta riƙa koyo cikin natsuwa da cikakkiyar biyayya. 12 Ban ba mace izini ta koyar ko tă yi mulki a kan namiji ba; sai dai ta zauna shiru. 13 Gama Adamu ne aka fara halitta, sa’an nan Hawwa’u. 14 Ba kuma Adamu ne aka yaudara ba; macen ce aka yaudara ta kuma zama mai zunubi. 15 Amma mata Za tă sami ceto za su sami ceto ta wurin haihuwa, in suka ci gaba cikin bangaskiya, ƙauna da kuma tsarki tare da halin sanin ya kamata.
-
1 Ruhu a sarari ya faɗa cewa a kwanakin ƙarshe waɗansu za su watsar da bangaskiya su bi ruhohi masu ruɗu da kuma abubuwan da aljanu suke koyarwa. 2 Irin koyarwan nan tana zuwa ne daga waɗansu munafukai maƙaryata, waɗanda aka yi wa lamirinsu kaca-kaca. 3 Suna hana mutane yin aure suna kuma umarce su kada su ci waɗansu irin abinci, waɗanda Allah ya halitta don waɗanda suka gaskata suka kuma san gaskiya, su karɓa da godiya.
-
13 Mugayen mutane da masu ruɗi kuwa, ƙara muni za su riƙa yi, suna yaudara, ana kuma yaudararsu.
Shows Read in context, Share and Copy.