31 Bible Verses About Spiritual Warfare

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Spiritual Warfare
  1. 10 A ƙarshe, bari ƙarfin ikon Ubangiji yă ba ku ƙarfi. 11 Ku yafa dukan kayan yaƙin da Allah yake bayarwa, don ku iya kāre kanku daga dabarun Shaiɗan. 12 Gama ba da mutane da suke nama da jini ne muke yaƙi ba. Muna yaƙi ne da ikoki, da hukumomi, da masu mulkin duhu, da kuma a ikokin da suke cikin a sararin sama. 13 Saboda haka sai ku yafa dukan kayan yaƙi na Allah, domin sa’ad da ranar mugun nan ta zo, ku iya yin tsayin daka, bayan kuma kuka gama kome, ku dāge. 14 Saboda haka fa ku dāge, ku sa gaskiya tă zama ɗamararku, adalci yă zama sulkenku, 15 shirin kai bisharar salama yă zama kamar takalmi a ƙafafunku. 16 Ban da waɗannan kuma, ku ɗauki garkuwar bangaskiya, wadda za ku iya kashe dukan kibiyoyin wutar Mugun nan da ita. 17 Ku kuma ɗauki hular kwano na ceto, da takobin Ruhu, wato, Maganar Allah.

    18 A koyaushe ku kasance kuna addu’a da roƙo ta wurin ikon Ruhu ba fasawa. A kan wannan manufa ku zauna a faɗake da matuƙar naci, kuna yin wa dukan mutanen Ubangiji addu’a.

  2. 3 Ko da yake muna cikin duniya, ba ma yaƙi kamar yadda duniya take yi. 4 Makaman da muke yaƙi da su, ba makamai na duniya ba ne. Sai dai na ikon Allah ne, masu rushe wuraren mafaka masu ƙarfi. 5 Muna ka da masu gardama da kowane tunanin ɗaga kai da yake kafa kansa gāba da sanin Allah, muna kuma jan hankalin kowa ga bautar Kiristi. 6 A shirye muke mu hori kowane rashin biyayya, sa’ad da biyayyarku ta cika.

  3. 6 Wata rana mala’iku suka kawo kansu gaban Ubangiji, Shaiɗan shi ma ya zo tare da su. 7 Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Daga ina ka fito?”

    Shaiɗan ya amsa wa Ubangiji ya ce, “Daga yawo a duniya ina kai da kawowa a cikinta.”

    8 Sai Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Ko ka ga bawana Ayuba? A cikin duniya babu wani kamar sa; shi marar laifi ne, adali kuma, mutum ne mai tsoron Allah, ba ruwansa da mugunta.”

    9 Sai Shaiɗan ya amsa ya ce, “Haka kawai Ayuba yake tsoron Allah? 10 Ba ka kāre shi da iyalinsa gaba ɗaya da duk mallakarsa ba? Ka Albarkaci ayyukan hannunsa yadda dabbobinsa duk sun cika ko’ina. 11 Ka ɗan miƙa hannunka ka raba shi da duk abin da yake da shi, ba shakka zai la’anta ka kana ji, kana gani.”

    12 Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “To, shi ke nan, duk abin da yake da shi yana hannunka, amma kada ka taɓa shi, shi kansa.”

    Sai Shaiɗan ya bar Ubangiji.

  4. 6 Saboda haka, ku ƙasƙantar da kanku a ƙarƙashin hannun Allah mai ƙarfi, don yă ɗaukaka ku a lokacin da ya ga dama. 7 Ku danƙa masa dukan damuwarku, domin shi ne yake lura da ku.

    8 Ku zama masu kamunkai, ku kuma zauna a faɗake. Abokin gābanku, Iblis yana kewayewa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai cinye. 9 Ku yi tsayayya da shi, kuna tsayawa daram cikin bangaskiya, domin kun san cewa ’yan’uwanku ko’ina a duniya suna shan irin wahalolin nan.

    10 Allah mai dukan alheri, wanda ya kira ku ga madawwamiyar ɗaukaka cikin Kiristi, bayan kun sha wahala na ɗan lokaci, shi da kansa zai raya ku, yă kuma sa ku yi ƙarfi, ku kahu, ku kuma tsaya daram.

  5. 1 Sa’an nan Ubangiji ya amsa wa Ayuba. Ya ce,

    2 “Wane ne wannan da yake ɓata mini shawarata

    da surutan wofi?

    3 Ka sha ɗamara kamar namiji;

    zan yi maka tambaya,

    za ka kuwa amsa mini.

  6. 7 Saboda haka, ku miƙa kanku ga Allah. Ku yi tsayayya da Iblis, zai kuwa guje ku.

  7. 7 Aka kuwa yi yaƙi a sama. Mika’ilu da mala’ikunsa yaƙi macijin, maciji da mala’ikunsa su ma suka mai da martani. 8 Amma macijin nan ba shi da isashen ƙarfi, har suka rasa matsayinsu a sama. 9 Aka jefar da ƙaton jan macijin ƙasa, tsohon maciji nan da ake kira Iblis, ko Shaiɗan, wanda ya ɓad da dukan duniya. Aka jefar da shi ƙasa, tare da mala’ikunsa a duniya.

  8. 17 Mutum saba’in da biyun nan suka dawo da murna, suka ce, “Ubangiji, har mun sha ƙarfin aljanu ma a cikin sunanka.”

    18 Sai ya amsa ya ce, “Na ga Shaiɗan ya fāɗi daga sama kamar walƙiya. 19 Na ba ku iko da za ku tattaka macizai, da kunamai, ku kuma shawo kan dukan ikon abokin gāba, kuma ba wani lahani da zai same ku. 20 Duk da haka, kada ku yi farin ciki da cewa, kun sha ƙarfin ruhohi, amma ku yi farin ciki, domin an rubuta sunayenku a sama.”

  9. 35 Wane ne zai raba mu da ƙaunar Kiristi? Masifa ce ko wahala ko tsanani ko yunwa ko tsiraici ko hatsari ko takobi? 36 Kamar yadda yake a rubuce cewa,

    “Saboda kai ne muke fuskantar mutuwa dukan yini;

    an ɗauke mu kamar tumakin da za a yanka.”

    37 A’a, cikin dukan waɗannan abubuwa mun ma fi masu nasara ta wurin shi wanda ya ƙaunace mu. 38 Gama na tabbata cewa ko mutuwa ko rai, ko mala’iku ko aljanu, ko abubuwa na yanzu ko abubuwa masu zuwa nan gaba, ko ikoki, 39 ko tsayi ko zurfi, ko wani abu dabam cikin dukan halitta da zai iya raba mu da ƙaunar Allah wadda take cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.

  10. 44 Ku na ubanku ne, Iblis, kuna kuwa so ku aikata abin da ubanku yake so. Shi mai kisankai ne tun farko. Ba ruwansa da gaskiya, gama gaskiya ba ta cikinsa. Yayinda yake ƙarya, yana yin halinsa ne, gama shi maƙaryaci ne, uban ƙarairayi kuma.

  11. 33 “Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin a cikina ku sami salama. A duniyan nan za ku sha wahala. Amma ku yi ƙarfin hali! Na yi nasara a kan duniya.”

  12. 1 Saboda haka, da yake ta wurin jinƙan Allah ne muke da wannan hidima, ba za mu fid da zuciya ba. 2 Ba ruwanmu da ɓoye-ɓoye na munafuncin da suke abubuwan kunya. Ba ruwanmu da ruɗu, ko yin ƙarya da kalmar Allah. Sai dai muna faɗin gaskiya a fili. Ta haka ne kowa zai yi shaidar gaskiyarmu a gaban Allah cikin zuciyarsa. 3 Ko da bishararmu a rufe take, tana a rufe ne ga waɗanda suke hallaka. 4 Allahn zamanin nan ya makanta hankulan marasa ba da gaskiya, yadda har ba za su iya ganin hasken bishara ta ɗaukakar Kiristi ba, wanda yake kamannin Allah. 5 Gama ba wa’azin kanmu muke yi ba, sai dai na Yesu Kiristi, a kan shi ne Ubangiji, mu kuma bayinku saboda Yesu. 6 Domin shi Allah wanda ya ce, “Bari haske yă haskaka daga duhu,” ya sa haskensa ya haskaka a cikin zukatanmu, don yă ba mu hasken sanin ɗaukakar Allah a fuskar Kiristi.

  13. 17 ba makamin da aka ƙera don yă cuce ki da zai yi nasara,

    za ki kuma mayar da magana ga duk wanda ya zarge ki.

    Wannan ne gādon bayin Ubangiji,

    kuma wannan ita ce nasararsu daga gare ni,”

    in ji Ubangiji.

  14. 22 Kada ku ji tsoronsu, gama Ubangiji Allahnku zai yi yaƙi dominku.”

  15. 18 “Gaskiya nake gaya muku, duk abin da kuka daure a duniya, za a daure a sama, duk kuma abin da kuka kunce a duniya, za a kunce shi a sama.

    19 “Har wa yau, ina gaya muku cewa in mutum biyu a cikinku a duniya suka yarda su roƙi wani abu, Ubana da yake cikin sama zai yi muku. 20 Gama inda mutum biyu ko uku suka taru cikin sunana, a can ma ina tare da su.”

  16. 3 Ubangiji mai aminci ne, zai ƙarfafa ku, yă kuma tsare ku daga mugun nan.

  17. 12 Ka yi fama, kyakkyawar fama ta bangaskiya. Ka riƙi rai madawwamin nan, wanda aka kira saboda shi, sa’ad da ka yi kyakkyawar shaida a gaban shaidu masu yawa.

  18. 12 Abokaina ƙaunatattu, kada ku yi mamakin gwaji mai tsananin da kuke sha, sai ka ce wani baƙon abu ne yake faruwa da ku. 13 Sai dai ku yi murna cewa kuna tarayya cikin shan wahalolin Kiristi, domin ku kai ga farin ciki mai yawa sa’ad da aka bayyana ɗaukakarsa.

  19. 4 Ku, ’ya’yana ƙaunatattu, ku daga Allah ne, kun kuma yi nasara a kan magabtan Kiristi, domin wanda yake a cikinku ya fi wanda yake a duniya girma.

  20. 4 domin duk haifaffe na Allah yana cin nasara a kan duniya. Bangaskiyarmu kuwa ita ce ta ba mu wannan nasara a kan duniya. 5 Wa ya cin nasara a kan duniya? Sai wanda ya gaskata cewa Yesu Ɗan Allah ne.

  21. 57 Amma godiya ga Allah! Shi ne ya ba mu nasara ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi.

  22. 1 Yanzu mun san cewa in an hallaka tentin duniyan nan da muke ciki, muna da wani gini daga Allah, madawwamin gida a sama, wanda ba da hannuwan mutum ne suka gina shi ba. 2 Kafin nan muna nishi, da marmari a yi mana sutura da gidanmu na sama, 3 don sa’ad da aka yi mana sutura, ba za a same mu tsirara ba. 4 Sa’ad da muke zaune a cikin jikin nan na duniya, nishi muke domin matsuwar da muke sha, ba domin muna so mu rabu da jikinmu na wannan duniya ba ne, sai dai don so muke yi a suturta mu da na Sama, domin mai rai ya shafe mai mutuwa. 5 Allah ne ya yi mu domin wannan, ya kuma ba mu Ruhu a matsayin abin ajiya, yana kuma tabbatar da abin da zai zo nan gaba.

    6 Saboda haka, kullum muna da tabbaci mun kuma san cewa, muddin muna a duniya cikin jikin nan, ana raba mu da Ubangiji. 7 Rayuwa bangaskiya muke, ba ta ganin ido ba. 8 Ina cewa muna da tabbaci, za mu fi so mu rabu da jikin nan, mu kuma kasance a sama tare da Ubangiji. 9 Saboda haka, niyyarmu ita ce, mu gamshe shi, ko muna a duniya cikin jikin nan, ko ba mu nan. 10 Gama dole dukanmu mu bayyana a gaban kujerar shari’ar Kiristi, domin kowannenmu yă karɓi ladan aikin da ya yi a wannan jiki, ko mai kyau ne ko marar kyau.

    11 To, da yake mun san ko mene tsoron Ubangiji yake, muna ƙoƙari mu rinjaye mutane. Yadda muke kuwa, yana sane a sarari ga Allah, ina kuma fata yana nan a sarari a lamirinku.

  23. 1 Kai kuma, ɗana, ka yi ƙarfi cikin alherin da yake cikin Kiristi Yesu. 2 Abubuwan da ka ji na faɗa a gaban shaidu masu yawa kuwa ka danƙa wa amintattun mutane waɗanda su ma za su iya koya wa waɗansu. 3 Ka jure wa shan wahala tare da mu kamar soja mai kyau na Kiristi Yesu. 4 Ba wanda yake aikin soja da zai sa kansa a sha’anin mutumin da ba ya aikin soja, domin yakan so yă gamshi wanda ya ɗauke shi soja.

  24. 1 Me yake jawo faɗace-faɗace da gardandami a tsakaninku? Ashe, ba sha’awace-sha’awacenku da suke yaƙi a zukatanku ba ne? 2 Kukan nemi abu ku rasa, sai ku yi kisa da ƙyashi. In kuka rasa abin da kuke nema sai ku shiga yin gardama da faɗa. Kukan rasa ne, domin ba ku roƙi Allah ba. 3 Sa’ad da kuka roƙa, ba kwa samu, don kun roƙa da mugun nufi, don ku kashe abin da kuka samu a kan sha’awace-sha’awacenku.

    4 Ku mazinata, ba ku san cewa abokantaka da duniya gāba ce da Allah ba? Duk wanda ya zaɓa yă zama abokin duniya ya zama abokin gāban Allah ke nan.

  25. 1 Shi wanda yake zama a wurin Mafi Ɗaukaka

    zai huta a cikin inuwar Maɗaukaki.

    2 Zan ce game da Ubangiji, “Shi ne mafakata da kagarata,

    Allahna, wanda nake dogara.”

    3 Tabbatacce zai cece ka

    daga tarkon mai farauta

    da kuma daga cututtuka masu kisa.

    4 Zai rufe ka da fikafikansa,

    a ƙarƙashin fikafikansa kuwa za ka sami mafaka;

    amincinsa zai zama maka garkuwa da katanga.

  26. 31 “Siman, Siman, Shaiɗan ya nemi izini ya sheƙe ka kamar alkama. 32 Amma na yi maka addu’a, Siman, domin kada bangaskiyarka ta kāsa. Bayan ka juyo, ka ƙarfafa ’yan’uwanka.”

  27. 15 Ban gane abin da nake yi ba. Don abin da nakan so yi, ba shi nakan yi ba, sai dai abin da nake ƙi, shi nake yi. 16 In kuma na yi abin da ba na son yi, na yarda da cewa dokar aba ce mai kyau. 17 Kamar dai yadda yake, ba ni kaina nake yinsa ba, sai dai zunubin da yake zaune a cikina ne. 18 Gama na san cewa babu wani abin kirkin da yake zaune a cikina, wato, a mutuntakata. Gama sha’awar yin abu mai kyau kam ina da ita, sai dai ikon yin ne fa babu. 19 Gama abin da nake yi ba shi ne abu mai kyau da nake so in yi ba; a’a, mugun da ba na so in yi, shi ne nake ci gaba da yi. 20 To, in na yi abin da ba na so in yi, ba ni ba ne nake yinsa, sai dai zunubin nan da yake zaune a cikina.

    21 Saboda haka na gane wannan ƙa’ida ce take aiki a cikina. Sa’ad da nake so in yi abu mai kyau, sai in ga cewa mugun nan ne nake yi. 22 Gama a ciki-cikina ina farin cikin da dokar Allah; 23 amma ina ganin wata doka tana aiki a gaɓoɓin jikina, tana yaƙi da dokar hankalina, tana kuma sa in zama ɗaurarren dokar zunubin da take aiki a gaɓoɓin jikina. 24 Kaitona! Wane ne zai cece ni daga wannan jiki mai mutuwa? 25 Godiya ga Allah ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu!

    Saboda haka fa, ni kaina a cikin hankalina, ni bawa ne ga dokar Allah, amma a mutuntaka, ni bawa ne ga dokar zunubi.

  28. 2 Kada ku ci gaba da yin abin da duniya take yi, sai dai ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so yake, abu mai kyau, mai daɗi da kuma cikakke.

  29. 14 Ba abin mamaki ba ne, gama Shaiɗan kansa ma yana ɓad da kamanni kamar shi mala’ikan haske ne. 15 Don haka, ba abin mamaki ba ne, in bayin Shaiɗan sun ɓad da kamanni kamar su bayin adalci ne. A ƙarshe, za a sāka musu gwargwadon ayyukansu.

  30. 16 Saboda haka ina ce muku, ku yi rayuwa ta wurin Ruhu, ba za ku kuwa gamsar da sha’awace-sha’awacen mutuntaka ba. 17 Gama mutuntaka yana son abin da Ruhu yake ƙi, Ruhu kuma yana son abin da mutuntaka yake ƙi. Waɗannan biyu kuwa gāba suke da juna, har ku kāsa yin abin da kuke so.

  31. 18 Timoti, ɗana, na ba ka wannan umarni bisa ga annabce-annabcen da aka yi a dā game da kai, domin ta wurin binsu ka iya yin yaƙi mai kyau, 19 kana riƙe da bangaskiya da kuma lamiri mai kyau. Gama waɗansu mutane, saboda ƙin kasa kunne ga lamirinsu, suka lalatar da bangaskiyarsu. 20 Cikinsu kuwa akwai Himenayus da Alekzanda, waɗanda na miƙa ga Shaiɗan don su horo su bar yin saɓo.