82 Bible Verses About Fear and Worry

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Fear and Worry
  1. 4 Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji kullum. Ina sāke gaya muku ku yi farin ciki! 5 Bari kowa yă kasance da sauƙinkai. Ubangiji ya yi kusan zuwa. 6 Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya. 7 Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za tă tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.

    8 A ƙarshe, ’yan’uwa, duk abin da yake na gaskiya, duk abin da yake na girmamawa, duk abin da yake daidai, duk abin da yake da tsarki, duk abin da yake kyakkyawa, duk abin da yake na sha’awa, in ma wani abu mafifici ne, ko ya cancanci yabo, ku yi tunani a kan irin abubuwan nan. 9 Duk abin da kuka koya ko kuka karɓa ko kuka ji daga wurina, ko kuka gani a cikina, ku yi aiki da shi. Allah na salama kuma zai kasance tare da ku.

  2. 6 Saboda haka, ku ƙasƙantar da kanku a ƙarƙashin hannun Allah mai ƙarfi, don yă ɗaukaka ku a lokacin da ya ga dama. 7 Ku danƙa masa dukan damuwarku, domin shi ne yake lura da ku.

  3. 8 “Amma kai, ya Isra’ila, bawana,

    Yaƙub, wanda na zaɓa,

    zuriyar Ibrahim abokina,

    9 na ɗauke ka daga iyakar duniya,

    daga kusurwoyi masu nesa na kira ka.

    Na ce, ‘Kai bawana ne’;

    na zaɓe ka ban kuwa ƙi ka ba.

    10 Saboda haka kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai;

    kada ka karai, gama ni ne Allahnka.

    Zan ƙarfafa ka in kuma taimake ka;

    zan riƙe ka da hannun damana mai adalci.

    11 “Duk wanda ya yi fushi da kai

    tabbatacce zai sha kunya da ƙasƙanci;

    waɗanda suka yi hamayya da kai

    za su zama kamar ba kome ba su kuma hallaka.

    12 Ko ka nemi abokan gābanka,

    ba za ka same su ba.

    Waɗanda suke yaƙi da kai

    za su zama kamar ba kome ba.

    13 Gama ni ne Ubangiji Allahnka,

    wanda ya riƙe ka da hannun damana

    ya kuma ce maka, Kada ka ji tsoro;

    zan taimake ka.

    14 Kada ka ji tsoro, ya Yaƙub marar ƙarfi,

    ya ƙaramin Isra’ila,

    gama ni kaina zan taimake ka,” in ji Ubangiji,

    Mai Fansarka, Mai Tsarkin nan na Isra’ila.

  4. 4 Na nemi Ubangiji, ya kuwa amsa mini;

    ya cece ni daga dukan tsoro.

    5 Waɗanda suke dubansa sukan haskaka;

    fuskokinsu ba sa rufuwa da kunya.

    6 Wannan matalauci ya yi kira, Ubangiji kuwa ya ji shi;

    ya cece shi daga dukan wahalarsa.

    7 Mala’ikan Ubangiji ya kafa sansani kewaye da waɗanda suke tsoronsa,

    ya kuwa cece su.

    8 Ku gwada ku gani cewa Ubangiji yana da kyau;

    mai albarka ne mutumin da yake neman mafaka a gare shi.

    9 Ku ji tsoron Ubangiji, ku tsarkakansa,

    gama masu tsoronsa ba sa rasa kome.

  5. 26 Amma Mai Taimako, Ruhu Mai Tsarki, wanda Uba zai aiko cikin sunana, zai koya muku kome, zai kuma tuna muku duk abin da na faɗa muku. 27 Salama na bari tare da ku; salamata nake ba ku. Ba kamar yadda duniya take bayarwa nake ba ku ba. Kada zuciyarku ta ɓaci kada kuma ku ji tsoro.

    28 “Kun dai ji na ce, ‘Zan tafi in kuma sāke dawo wurinku.’ In har kuna ƙaunata, za ku yi farin ciki cewa za ni wurin Uba, domin kuwa Uban ya fi ni.

  6. 26 Haka nan ma, Ruhu yana taimakonmu cikin rashin ƙarfinmu. Ba mu san abin da ya kamata mu roƙa cikin addu’a ba, amma Ruhu kansa yana roƙo a madadinmu da nishe-nishen da kalmomi ba sa iya bayyanawa. 27 Shi kuma wanda yake binciken zukatanmu ya san halin Ruhu, domin Ruhu yana roƙo a madadin tsarkaka bisa ga nufin Allah.

    28 Mun kuma san cewa a cikin dukan abubuwa Allah yana aikata alheri ga waɗanda suke ƙaunarsa, yana waɗanda aka kira bisa ga nufinsa.

  7. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da murya “Kurciya a Itatuwan Oak Mai Nisa.” Ta Dawuda. Wani miktam. Sa’ad da Filistiyawa suka kama shi a birnin Gat.

    1 Ka yi mini jinƙai,

    ya Allah, gama mutane sun tasar mini da zafi;

    dukan yini suna matsa harinsu.

    2 Masu ɓata sunana suna bina dukan yini;

    da yawa suna kai mini hari cikin fariyarsu.

    3 Sa’ad da nake tsoro, zan dogara gare ka.

    4 Ga Allah wanda maganarsa nake yabo

    ga Allah na dogara; ba zan ji tsoro ba.

    Me mutum mai mutuwa zai yi mini?

  8. 24 “Ba mai iya bauta wa iyayengiji biyu. Ko dai yă ƙi ɗaya, yă ƙaunaci ɗaya, ko kuwa yă yi aminci ga ɗaya, sa’an nan yă rena ɗayan. Ba dama ku bauta wa Allah, ku kuma bauta wa kuɗi gaba ɗaya.”

    25 “Saboda haka, ina gaya muku, kada ku damu game da rayuwarku, game da abin da za ku ci, ko abin da za ku sha; ko kuma game da jikinku, game da abin da za ku sa. Ashe, rai bai fi abinci ba, jiki kuma bai fi tufafi ba? 26 Ku dubi tsuntsayen sararin sama mana; ba sa shuki ko girbi ko ajiya a rumbuna, duk da haka, Ubanku na sama yana ciyar da su. Ashe, ba ku fi su daraja nesa ba? 27 Wane ne a cikinku ta wurin damuwa zai iya ƙara wa rayuwarsa ko sa’a ɗaya?

    28 “Me ya sa kuke damuwa a kan riguna? Ku dubi yadda furannin jeji suke girma mana. Ba sa aiki ko saƙa. 29 Duk da haka ina gaya muku ko Solomon cikin dukan darajarsa bai sa kayan adon da ya kai na ko ɗaya a cikinsu ba. 30 In haka Allah yake yi wa ciyawar jeji sutura, wadda yau tana nan, gobe kuwa a jefa a cikin wuta, ba zai ma fi yi muku sutura ba, ya ku masu ƙarancin bangaskiya? 31 Don haka, kada ku damu, kuna cewa, ‘Me za mu ci?’ Ko, ‘Me za mu sha?’ Ko kuma, ‘Me za mu sa?’ 32 Gama marasa sanin Allah suna fama neman dukan waɗannan abubuwa, Ubanku na sama kuwa ya san kuna bukatarsu. 33 Da farko dai, ku nemi mulkin Allah da kuma adalcinsa, za a kuwa ba ku dukan waɗannan abubuwa. 34 Saboda haka kada ku damu game da gobe, gama gobe zai damu da kansa. Damuwar yau ma ta isa wahala.

  9. 6 Saboda haka, ina so in faɗakar da kai, ka lura baiwan nan ta Allah, wadda take tare da kai ta wurin ɗibiya maka hannuwana. 7 Gama Allah bai ba mu ruhun tsoro ba, sai dai ruhun iko, na ƙauna da kuma na kamunkai.

  10. 16 Ta haka muka sani, muke kuma dogara ga ƙaunar da Allah yake mana.

    Allah ƙauna ne. Duk wanda yake rayuwa cikin ƙauna, yana rayuwa a cikin Allah ne, Allah kuma a cikinsa. 17 Ta haka, ƙauna ta zama cikakkiya a cikinmu domin mu kasance masu ƙarfin hali a ranar shari’a, domin a wannan duniya muna kama da shi. 18 Babu tsoro cikin ƙauna. Cikakkiyar ƙauna dai takan kawar da tsoro, domin hukunci ne yake kawo tsoro. Mai jin tsoro ba cikakke ba ne a cikin ƙauna.

    19 Muna ƙauna, domin ya ƙaunace mu da farko.

  11. Zabura ta Dawuda.

    1 Ubangiji ne yake kiwona, ba zan rasa kome ba,

    2 Yakan sa in kwanta a makiyaya mai ɗanyar ciyawa,

    yakan bi da ni kusa da ruwaye marar hayaniya,

    3 yakan maido da raina.

    Yakan bi da ni a hanyoyin adalci

    saboda sunansa.

    4 Ko da na yi tafiya

    ta kwari na inuwar mutuwa,

    ba zan ji tsoron mugu ba,

    gama kana tare da ni;

    bulalarka na dūka da kuma sandanka na tafiya,

    za su yi mini ta’aziyya.

  12. 22 Sai Yesu ya ce wa almajiransa, “Saboda haka, ina faɗa muku, kada ku damu game da rayuwarku, abin da za ku ci, ko kuma game da jikinku, abin da za ku yafa. 23 Rai ya fi abinci, jiki kuma ya fi tufafi. 24 Ku dubi hankaki. Ba sa shuki ko girbi, kuma ba su da ɗakin ajiya ko rumbu ba, duk da haka, duk da haka, Allah na ciyar da su. Darajarku ta fi na tsuntsaye sau da yawa! 25 Wane ne a cikinku ta wurin damuwarsa, zai iya ƙara ko sa’a ɗaya ga rayuwarsa? 26 Tun da ba za ku iya yin wannan ƙanƙanin abu ba, me ya sa kuke damuwa a kan sauran?

    27 “Ku dubi yadda furanni suke girma. Ba sukan yi aiki, ko saƙa ba, duk da haka, ina faɗa muku cewa, ko Solomon cikin kyakkyawan darajarsa duka, bai yafa kayan ado da ya kai kamar na ko ɗaya a cikinsu ba. 28 In haka ne Allah yake yi wa ciyayin jeji sutura, wadda yau suna nan, sa’an nan gobe kuma a jefa cikin wuta, Allah ba zai yi muku sutura fiye da ciyayin jeji ba, ya ku masu ƙarancin bangaskiya! 29 Kada ku sa zuciyarku a kan abin da za ku ci, ko abin da za ku sha, kada ku damu a kan su. 30 Gama duniya da ba tă san Allah ba, tana faman neman dukan waɗannan abubuwa, Ubanku na sama kuwa, ya san kuna bukatarsu. 31 Amma ku nemi mulkinsa, za a kuwa ƙara muku waɗannan abubuwa.

    32 “Ya ƙaramin garke, kada ku ji tsoro, gama ya gamshi Ubanku ya ba ku mulkin. 33 Ku sayar da dukiyarku, ku ba wa matalauta. Ku yi wa kanku jakar kuɗin da ba za su lalace ba. Ku yi wa kanku ajiyar dukiyar da ba za tă kare ba a sama, inda ɓarawo ba zai yi kusa ba, asu kuma ba za su iya su lalatar ba. 34 Gama inda dukiyarku take, nan ne zuciyarku ma take.

  13. 5 Ku kiyaye kanku daga yawan son kuɗi, ku kuma gamsu da abin da kuke da shi, gama Allah ya ce,

    “Ba zan taɓa bar ka ba;

    ba zan taɓa yashe ka ba.”

    6 Saboda haka muna iya fitowa gabagadi, mu ce,

    “Ubangiji ne mai taimakona; ba zan ji tsoro ba.

    Me mutum zai iya yi mini?”

  14. 1 To, fa, ga abin da Ubangiji yana cewa,

    shi da ya halicce ka, ya Yaƙub,

    shi da ya siffanta ka, ya Isra’ila,

    “Kada ka ji tsoro, gama na fanshe ka;

    na kira ka da suna; kai nawa ne.

    2 Sa’ad da kuka bi ta ruwaye,

    zan kasance tare da ku;

    sa’ad da kuka bi ta koguna,

    ba za su kwashe ku ba.

    Sa’ad da kuke tafiyata cikin wuta,

    ba za tă ƙone ku ba;

    harsunan wutar ba za su ƙone ku ba.

    3 Gama ni ne Ubangiji, Allahnku,

    Mai Tsarkin nan na Isra’ila, Mai Cetonku;

    na bayar da Masar don fansa,

    Kush da Seba a maimakonku.

    4 Da yake ku masu daraja da kuma girma ne a idona,

    saboda kuma ina ƙaunarku,

    zan ba da mutane a maimakonku,

    al’umma kuma domin ranku.

    5 Kada ku ji tsoro, gama ina tare da ku;

    zan kawo yaranku daga gabas

    in kuma tattara ku daga yamma.

  15. Ta Dawuda.

    1 Ubangiji ne haskena da cetona,

    wa zan ji tsoro?

    Ubangiji ne mafakar raina,

    wane ne zan ji tsoro?

    2 Sa’ad da mugaye suka tasar mini

    don su cinye ni,

    sa’ad da abokan gābana da maƙiyina suka kawo mini hari,

    sun yi tuntuɓe suka fāɗi.

    3 Ko da yake mayaƙa sun kewaye ni,

    zuciyata ba za tă ji tsoro ba;

    ko da yake ya ɓarke a kaina,

    duk da haka zan ƙarfafa.

  16. 17 Da ba don Ubangiji ya yi mini taimako ba,

    da tuni na zauna shiru a wurin mutuwa.

    18 Sa’ad da na ce, “Ƙafata na santsi,”

    ƙaunarka, ya Ubangiji, ta riƙe ni.

    19 Sa’ad da alhini ya yi yawa a cikina,

    ta’aziyyarka ta kawo farin ciki wa raina.

    20 Zai yiwu kursiyin da ya cika da lalaci yă haɗa kai da kai,

    wanda yake kawo azaba ta wurin abin da ya zartar?

  17. 5 Ba wanda zai yi tsayayya da kai dukan kwanakin ranka. Yadda na kasance tare da Musa, haka zan kasance tare da kai; ba zan taɓa rabuwa da kai ba; ba zan yashe ka ba.

    6 “Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro, gama kai za ka bi da mutanen nan har su karɓi ƙasar da na yi wa kakanninsu alkawari zan ba su. 7 Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro, ka yi lura fa, ka yi biyayya da dokokin da bawana Musa ya ba ka; kada ka kauce ga bin dokokin ko hagu ko dama, domin ka yi nasara a duk, inda za ka je. 8 Kada ka bar Littafin Dokokin nan yă rabu da bakinka, sai dai ka yi ta tunani game da shi dare da rana, don ka lura, ka yi duk abin da aka rubuta a ciki, ta haka ne za ka yi nasara cikin duk abin da za ka yi. 9 Ba ni na umarce ka ba? Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro. Kada ka ji tsoro; kada ka karaya, gama Ubangiji Allahnka zai kasance tare da kai duk inda za ka je.”

  18. 22 Ku kawo damuwoyinku ga Ubangiji

    zai kuwa riƙe ku;

    ba zai taɓa barin

    mai adalci yă fāɗi ba.

    23 Amma kai, ya Allah, za ka kawar da mugaye

    zuwa cikin ramin lalacewa;

    masu kisa da mutane masu ruɗu

    ba za su kai rabin kwanakin rayuwarsu ba.

    Amma ni dai, na dogara gare ka.

  19. 28 “Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji kuke kuma fama da kaya, zan kuwa ba ku hutu. 29 Ku ɗauki karkiyata a kanku, ku kuma yi koyi da ni, gama ni mai tawali’u ne marar girman kai, za ku kuwa sami hutu don rayukanku. 30 Gama karkiyata mai sauƙi ce, kayana kuma marasa nauyi ne.”

  20. 5 Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka

    kada kuma ka dangana ga ganewarka;

    6 cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi,

    zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.

    7 Kada ka zama mai hikima a ganinka;

    ka ji tsoron Ubangiji ka kuma guji mugunta.

    8 Wannan zai ba wa jikinka lafiya

    yă kuma adana ƙasusuwanka.

  21. 35 Wane ne zai raba mu da ƙaunar Kiristi? Masifa ce ko wahala ko tsanani ko yunwa ko tsiraici ko hatsari ko takobi? 36 Kamar yadda yake a rubuce cewa,

    “Saboda kai ne muke fuskantar mutuwa dukan yini;

    an ɗauke mu kamar tumakin da za a yanka.”

    37 A’a, cikin dukan waɗannan abubuwa mun ma fi masu nasara ta wurin shi wanda ya ƙaunace mu. 38 Gama na tabbata cewa ko mutuwa ko rai, ko mala’iku ko aljanu, ko abubuwa na yanzu ko abubuwa masu zuwa nan gaba, ko ikoki, 39 ko tsayi ko zurfi, ko wani abu dabam cikin dukan halitta da zai iya raba mu da ƙaunar Allah wadda take cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.

  22. 25 Zuciya mai damuwa takan naƙasar da mutum,

    amma maganar alheri kan faranta masa rai.

  23. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta ’Ya’yan Kora maza. Bisa ga alamot Waƙa ce.

    1 Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu,

    kullum yana a shirye yă taimaka a lokacin wahala.

    2 Saboda haka ba za mu ji tsoro ba, ko da ƙasa ta girgiza

    duwatsu kuma suka fāɗi cikin zurfin teku,

    3 ko da ruwansa suna ruri suna kumfa

    duwatsu kuma suna girgiza da tumbatsansu. Sela

  24. 12 Gama idanun Ubangiji suna a kan masu adalci

    kunnuwansa kuma suna jin addu’arsu,

    amma fuskar Ubangiji tana gāba da masu mugunta.”

    13 Wa zai yi muku lahani in kun himmantu ga yin nagarta? 14 Amma ko da za ku sha wahala saboda abin da yake daidai, ku masu albarka ne. “Kada ku ji tsoron abin da suke tsoro; kada kuma ku firgita.” 15 Sai dai a cikin zukatanku ku keɓe Kiristi a matsayin Ubangiji. A kullum, ku kasance a shirye ku ba da amsa ga duk wanda yake neman ku ba da dalilin wannan begen da kuke da shi. Amma ku yi wannan cikin tawali’u da ladabi, 16 tare da lamiri mai kyau, saboda waɗanda suke maganganun banza a kan kyawawan ayyukanku cikin Kiristi su ji kunya da irin ɓata suna da suke yi. 17 Ya fi kyau, in nufin Allah ne, a sha wahala don yin nagarta fiye da yin mugunta.

  25. 26 “Saboda haka kada ku ji tsoronsu. Ba abin da yake a rufe da ba za a tone ba, ko kuwa a ɓoye da ba za a bayyana ba. 27 Abin da na faɗa muku a asirce, ku faɗe shi a sarari; abin da aka faɗa muku a kunne, ku yi shelarsa daga kan rufin ɗaki. 28 Kada ku ji tsoron masu kashe jiki amma ba sa iya kashe rai. A maimakon haka, ku ji tsoron Wannan wanda yake da iko yă hallaka rai duk da jiki a jahannama ta wuta. 29 Ba akan sayar da kanari biyu kobo ɗaya ba? Duk da haka ba ɗayansu da zai fāɗi ƙasa ba da yardar Ubanku. 30 Kai, ko gashin kanku ma duk an ƙidaya su. 31 Saboda haka kada ku ji tsoro; kun fi kanari masu yawa, daraja nesa.

  26. Ta Dawuda.

    1 Kada ka tsorata saboda mugayen mutane

    ko ka yi kishin waɗanda suka aikata mugunta;

    2 gama kamar ciyawa za su bushe,

    kamar ɗanyun ganyaye za su mutu.

    3 Ka dogara ga Ubangiji ka kuma aikata alheri;

    yi zama cikin ƙasar ka kuma more makiyaya mai lafiya.

    4 Ka ji daɗinka a cikin Ubangiji

    zai kuwa biya bukatun zuciyarka.

    5 Ka sa kanka a hanyar Ubangiji;

    ka kuma dogara gare shi zai kuwa yi wannan.

    6 Zai sa adalcinka yă haskaka kamar hasken safiya,

    gaskiyarka kuma kamar rana a tsaka.

    7 Ka natsu a gaban Ubangiji

    ka kuma jira da haƙuri gare shi;

    kada ka tsorata sa’ad da mutane ke nasara a hanyoyinsu,

    sa’ad da suke aikata mugayen shirye-shiryensu.

    8 Kada ka yi fushi kada kuma ka yi hasala;

    kada ka tsorata, wannan yakan kai ga mugunta ne kawai.

    9 Gama za a datse mugayen mutane,

    amma waɗanda suke sa zuciya ga Ubangiji za su gāji ƙasar.

  27. 3 Ku ƙarfafa hannuwa marasa ƙarfi,

    ku ƙarfafa gwiwoyin da suka gaji;

    4 ku faɗa wa waɗanda suka karai a zukata,

    “Ku yi ƙarfin hali, kada ku ji tsoro;

    Allahnku zai zo,

    zai zo domin ya ɗau fansa;

    da ramuwar Allah

    zai zo don yă cece ku.”

  28. 5 Cikin azabata na yi kuka ga Ubangiji,

    ya kuwa amsa ta wurin ’yantar da ni.

    6 Ubangiji yana tare da ni; ba zan ji tsoro ba.

    Me mutum zai yi mini?

    7 Ubangiji yana tare da ni; shi ne mai taimakona.

    Zan yi nasara a kan abokan gābana.

    8 Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji

    da in dogara ga mutum.

  29. 11 Gama na san shirye-shiryen da na yi muku,” in ji Ubangiji, “shirye-shiryen cin gaba ba na cutarwa ba, shirye-shiryen ba ku sa zuciya da kuma na nan gaba. 12 Sa’an nan za ku kira gare ni ku zo ku kuma yi addu’a gare ni, zan kuwa ji ku. 13 Za ku neme ni ku kuwa same ni sa’ad da kuka neme ni da dukan zuciyarku. 14 Za ku same ni,” in ji Ubangiji, “zan kuma komo da ku daga bauta. Zan tattaro ku daga dukan al’ummai in sa ku inda na kore ku,” in ji Ubangiji, “zan kuma komo da ku zuwa wurin da na kwashe ku zuwa zaman bauta.”

  30. 1 “Kada zuciyarku ta ɓaci. Ku gaskata da Allah, ku kuma gaskata da ni. 2 A cikin gidan Ubana akwai wurin zama da yawa; da a ce ba haka ba ne, da na gaya muku. Za ni can don in shirya muku wuri. 3 In kuwa na tafi na shirya muku wuri, sai in dawo in ɗauke ku ku kasance tare da ni don ku kasance inda nake. 4 Ai, kun san hanyar zuwa inda za ni.”

  31. 6 Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tafe tare da ku, ba zai taɓa barinku ko yă yashe ku ba.”

  32. 5 Ga abin da Ubangiji yana cewa,

    “La’ananne ne mutumin da yake dogara ga mutum,

    wanda ya dogara ga jiki don ƙarfi

    wanda kuma zuciyarsa ta juya wa Ubangiji baya.

    6 Zai zama kamar ɗan kurmi a ƙasar da take kango;

    ba za su ga arziki sa’ad da ya zo ba.

    Za su zauna a busassun wuraren hamada,

    a cikin ƙasar gishiri inda ba kowa.

    7 “Amma mai albarka ne mutumin da yake dogara ga Ubangiji,

    wanda ƙarfin halinsa yana daga Ubangiji.

    8 Za su zama kamar itacen da aka dasa kusa da ruwa

    wanda ya miƙa saiwoyinsa zuwa cikin rafi.

    Ba ya jin tsoro sa’ad da zafi ya zo;

    ganyayensa kullum kore suke.

    Ba shi da damuwa a shekarar fări

    ba ya taɓa fasa ba da ’ya’ya.”

  33. 11 Ba na faɗin haka domin ina cikin bukata, gama na koya yadda zan gamsu a cikin kowane hali. 12 Na san mene ne zaman rashi, na kuma san mene ne zaman samu. Zan iya zama cikin kowane hali, ko cikin ƙoshi ko cikin yunwa, ko cikin yalwa ko kuma cikin fatara. 13 Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi.

  34. 23 Sai ya shiga jirgin ruwa, almajiransa kuwa suka bi shi. 24 Ba zato ba tsammani, sai wani babban hadari ya taso a tafkin, har raƙuman ruwan suka sha kan jirgin. Amma Yesu yana barci. 25 Almajiran suka je suka tashe shi, suna cewa, “Ubangiji, ka cece mu! Za mu nutse!”

    26 Ya amsa ya ce, “Ku masu ƙarancin bangaskiya, me ya sa kuke tsoro haka?” Sa’an nan ya tashi ya tsawata wa iskar da kuma raƙuman ruwan, sai wuri ya yi tsit gaba ɗaya.

    27 Mutanen suka yi mamaki suka ce, “Wane irin mutum ne wannan? Har iska da raƙuman ruwa suna masa biyayya!”

  35. 14 Domin waɗanda Ruhun Allah yake bi da su ne ’ya’yan Allah. 15 Gama ba ku karɓi ruhun da ya mai da ku bayi da za ku sāke jin tsoro ba ne, sai dai kun karɓi Ruhun zaman ɗa. Ta wurinsa kuwa muke kira, “Abba, Uba.” 16 Ruhu kansa yana ba da shaida tare da ruhunmu cewa mu ’ya’yan Allah ne. 17 In kuwa mu ’ya’ya ne, to, mu magāda ne, magādan Allah da kuma abokan gādo tare da Kiristi, in kuwa muna tarayya a cikin shan wuyarsa to, za mu yi tarayya a cikin ɗaukakarsa.

    18 A ganina, wuyar da muke sha a wannan lokaci ba su isa a kwatanta da ɗaukakar da za a bayyana a cikinmu ba. 19 Halitta tana jira da marmari ta ƙosa ta ga bayyanuwar ’ya’yan Allah.

  36. 4 “Ina dai gaya muku abokaina, kada ku ji tsoron masu kashe jiki, amma bayan haka, ba sauran abin da za su iya yi. 5 Amma zan nuna muku wanda za ku ji tsoronsa. Ku ji tsoron wanda, bayan da ya kashe jikin, yana da iko ya jefa ku cikin jahannama ta wuta. I, ina gaya muku, ku ji tsoronsa. 6 Ba ana sayar da kanari biyar a kan kobo biyu ba? Duk da haka, Allah bai manta da ko ɗayansu ba. 7 Tabbatacce, gashin kanku ɗin nan ma, an ƙidaya su duka. Kada ku ji tsoro. Darajarku ta fi na kanari masu yawa girma.

    8 “Ina gaya muku, duk wanda ya shaida ni a gaban mutane, Ɗan Mutum ma zai shaida shi a gaban mala’ikun Allah. 9 Amma wanda ya yi mūsun sanina a gaban mutane, shi ma za a yi mūsunsa a gaban mala’ikun Allah.

  37. 7 Ba zai ji tsoron labari marar daɗi ba;

    zuciyarsa tsayayyiya ce, tana dogara ga Ubangiji.

    8 Zuciyarsa tana da kāriya, ba zai ji tsoro ba;

    a ƙarshe zai zama mai nasara a kan maƙiyansa.

  38. 18 Da mutane suka ga tsawa da walƙiya, suka ji karar ƙaho, suka kuma ga dutsen yana hayaƙi, sai suka yi rawar jiki don tsoro. Suka tsaya da nisa 19 suka ce wa Musa, “Ka yi magana da mu da kanka, za mu kasa kunne. Amma kada Allah ya yi mana magana, don kada mu mutu.”

    20 Musa ya ce wa mutane, “Kada ku ji tsoro, gama Allah ya zo don yă gwada ku, don ku riƙa girmama shi, don kuma kada ku yi zunubi.”

  39. 10 “Ku natsu ku kuma san cewa ni ne Allah;

    za a ɗaukaka ni a cikin al’ummai,

    za a ɗaukaka ni cikin duniya.”

    11 Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu;

    Allah na Yaƙub ne kagararmu. Sela

  40. Waƙar haurawa.

    1 Na tā da idanuna zuwa wajen tuddai,

    ta ina ne taimakona zai zo?

    2 Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji,

    wanda ya kafa sama da ƙasa.

  41. 30 Ko matasa ma kan gaji su kuma kasala,

    samari kuma kan yi tuntuɓe su fāɗi;

    31 amma waɗanda suka dogara ga Ubangiji

    za su sabunta ƙarfinsu.

    Za su yi firiya da fikafikai kamar gaggafa;

    za su kuma yi gudu ba kuwa za su gaji ba,

    za su yi tafiya ba kuwa za su kasala ba.

  42. 22 Wanda ya karɓi irin da ya fāɗi cikin ƙaya kuwa, shi ne mutumin da yakan ji maganar, sai dai damuwoyin rayuwan nan da jarrabar arzikin duniya sukan shaƙe shi, yă sa maganar ta kāsa amfani.

  43. 7 Sai Musa ya kira Yoshuwa, ya ce masa a gaban dukan Isra’ila, “Ka ƙarfafa, ka kuma yi ƙarfin hali, gama dole ka tafi tare da mutanen nan zuwa cikin ƙasar da Ubangiji ya rantse cewa za ba wa kakanninku, dole kuma ka raba ta gare su ta zama gādonsu. 8 Ubangiji kansa yana tafe a gabanka, zai kuma kasance tare da kai, ba zai taɓa barinka ko yă yashe ka ba. Kada ka ji tsoro; kada kuma ka karai.”

  44. 1 Shi wanda yake zama a wurin Mafi Ɗaukaka

    zai huta a cikin inuwar Maɗaukaki.

    2 Zan ce game da Ubangiji, “Shi ne mafakata da kagarata,

    Allahna, wanda nake dogara.”

    3 Tabbatacce zai cece ka

    daga tarkon mai farauta

    da kuma daga cututtuka masu kisa.

    4 Zai rufe ka da fikafikansa,

    a ƙarƙashin fikafikansa kuwa za ka sami mafaka;

    amincinsa zai zama maka garkuwa da katanga.

    5 Ba za ka ji tsoron razanar dare,

    ko kibiyoyi da suke firiya da rana ba,

    6 ko bala’in da yake aukowa cikin duhu,

    ko annobar da take hallakarwa da tsakar rana.

  45. 16 Yanzu, bari Ubangiji mai salama kansa yă ba ku salama a kowane lokaci da kuma a ta kowace hanya. Ubangiji yă kasance tare da ku duka.

  46. 13 Ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku bauta masa shi kaɗai, ku kuma yi alkawaranku da sunansa. 14 Kada ku bi waɗansu alloli, allolin mutanen da suke kewaye da ku; 15 gama Ubangiji Allahnku, wanda yake cikinku, Allah ne mai kishi, fushinsa kuma zai yi ƙuna gāba da ku, zai kuma hallaka ku daga fuskar ƙasar.

  47. 39 Sai ya farka ya tsawata wa iskar, ya ce wa raƙuman ruwan, “Shiru! Ku natsu!” Sai iskar ta kwanta, kome kuma ya yi tsit.

    40 Sai ya ce wa almajiransa, “Don me kuke tsoro haka? Har yanzu ba ku da bangaskiya ne?”

    41 Suka tsorata, suka ce wa juna, “Wane ne wannan? Har iska da raƙuman ruwa ma suna masa biyayya!”

  48. 32 Amma lokaci na zuwa, har ma ya yi, da za a warwatsa ku, kowa yă koma gidansa. Za ku bar ni ni kaɗai. Duk da haka ba ni kaɗai ba ne, gama Ubana yana tare da ni.

    33 “Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin a cikina ku sami salama. A duniyan nan za ku sha wahala. Amma ku yi ƙarfin hali! Na yi nasara a kan duniya.”

  49. 17 Sa’ad da na gan shi, sai na fāɗi a gabansa sai ka ce matacce. Sai ya ɗibiya hannunsa na dama a kaina ya ce, “Kada ka ji tsoro. Ni ne Farko da kuma Ƙarshe. 18 Ni ne Rayayye, dā na mutu, ga shi kuwa ina a raye har abada abadin! Ina kuma riƙe da mabuɗan mutuwa da na Hades.

  50. 40 Marta kuwa, aikin hidima da ya kamata a yi, ya ɗauke mata hankali, sai ta zo wurin Yesu, ta ce, “Ubangiji, ba ka damu da yadda ’yar’uwata ta bar mini aiki ni kaɗai ba? Gaya mata ta taimake ni!”

    41 Amma Ubangiji ya amsa ya ce, “Marta, Marta, hankalinki ya tashi, kuma kina damuwa a kan abubuwa da yawa. 42 Amma abu ɗaya tak ake bukata, Maryamu ta zaɓi abin da ya fi kyau, kuma ba za a raba ta da shi ba.”

  51. 32 Zan so ku ’yantu daga damuwa. Mutum marar aure ya damu ne da al’amuran Ubangiji, yadda zai gamshi Ubangiji. 33 Amma mutumin da yake da aure yakan damu ne da al’amuran wannan duniya, yadda zai gamshi matarsa 34 hankalinsa a rabe yake. Mace marar aure ko kuwa budurwa ta damu ne da al’amuran Ubangiji. Nufinta shi ne ta ba da kanta ga Ubangiji cikin jiki da ruhu. Amma mace da take da aure ta damu ne da al’amuran wannan duniya, yadda za tă gamshi mijinta.

  52. 12 To wane ne mai tsoron Ubangiji?

    Zai koyar da shi a hanyar da ya zaɓa masa.

    13 Zai ci kwanakinsa a wadace,

    kuma zuriyarsa za su gāji ƙasar.

    14 Ubangiji yakan amince da waɗanda suke tsoronsa;

    yakan sa su san alkawarinsa.

  53. 10 Tsoron Ubangiji ne mafarin hikima;

    dukan waɗanda suke bin farillansa suna da ganewa mai kyau.

    Gare shi ne madawwamin yabo.

  54. 26 Duk mai tsoron Ubangiji yana da zaunannen mafaka,

    kuma ga ’ya’yansa zai zama mafaka.

    27 Tsoron Ubangiji shi ne maɓulɓular rai

    yakan juye mutum daga tarkon mutuwa.

  55. 15 Ubangiji ya ɗauke hukuncinki,

    ya mai da abokan gābanki baya.

    Ubangiji, Sarkin Isra’ila, yana tare da ke;

    ba kuma za ki ƙara jin tsoron wani lahani ba.

    16 A wannan rana za su cewa Urushalima,

    “Kada ki ji tsoro, ya Sihiyona;

    kada ki bar hannuwanki su raunana.

    17 Ubangiji Allahnki yana tare da ke,

    mai iko ne don ceto.

    Zai yi matuƙar farin ciki da ke,

    zai rufe ki da ƙaunarsa,

    zai yi farin ciki da ke ta wurin rerawa.”

  56. 36 Yesu bai kula da abin da suka faɗa ba, sai ya ce wa mai mulkin majami’ar, “Kada ka ji tsoro, ka gaskata kawai.”

  57. 48 Ya ga almajiran suna fama da tuƙi saboda iska tana gāba da su. Wajen tsara ta huɗu na dare, sai ya tafi wurinsu, yana takawa a kan tafkin. Ya yi kamar zai wuce su, 49 amma da suka gan shi yana takawa a kan tafkin, sai suka yi tsammani fatalwa ce. Sai suka yi ihu, 50 domin dukansu sun gan shi, suka kuma tsorata.

    Nan da nan ya yi magana da su ya ce, “Ku yi ƙarfin hali! Ni ne. Kada ku ji tsoro.” 51 Sai ya shiga jirgin ruwan tare da su, iskar kuma ta kwanta. Dukansu suka yi mamaki,

  58. 22 Kada ku ji tsoronsu, gama Ubangiji Allahnku zai yi yaƙi dominku.”

  59. 1 Yabi Ubangiji.

    Mai albarka ne mutumin da yake tsoron Ubangiji,

    wanda yakan sami farin ciki mai girma a umarnansa.

  60. 10 “Tsoron Ubangiji shi ne mafarin hikima,

    sanin Mai Tsarki kuwa fahimi ne.

  61. 11 “Sa’ad da an kai ku a gaban majami’u, da gaban masu mulki, da kuma gaban masu iko, kada ku damu da yadda za ku kāre kanku, ko kuma abin da za ku faɗa, 12 gama Ruhu Mai Tsarki zai koya muku abin da ya dace ku faɗa a lokacin.”

  62. 22 Me mutum zai samu daga aikin da ya yi duka, da irin ɗawainiyar da ya sha a kan yin aikin a duniya? 23 Dukan kwanakinsa aikinsa damuwa ce da ɓacin zuciya; ko da dare ma hankalinsa ba a kwance yake ba. Wannan ma ba shi da amfani.

  63. 12 Saboda haka, ya abokaina ƙaunatattu, kamar yadda kullum kuke biyayya ba kawai sa’ad da ina nan ba, amma yanzu da ba na nan tare da ku, ku ci gaba da yin ayyukan cetonku da tsoro da kuma rawan jiki,

  64. 26 Ba wata hadayar da za a yi don mutanen da suka yanke shawara su yi ci gaba da yin zunubi da gangan bayan sun sami sanin gaskiya. 27 A maimakon haka za su kasance da babban fargabar hukunci da kuma ta ƙunar wuta wadda za tă cinye abokan gāban Allah.

  65. 15 Sa’ad da bawan mutumin Allah ya farka ya kuma fita kashegari da sassafe, sai ga mayaƙa tare da dawakai da kekunan yaƙi sun kewaye birni. Sai bawan ya ce, “Ranka yă daɗe! Me za mu yi?”

    16 Sai annabin ya ce, “Kada ka ji tsoro, waɗanda suke tare da mu sun fi waɗanda suke tare da su.”

    17 Sa’an nan Elisha ya yi addu’a ya ce, “Ya Ubangiji, ka buɗe idanunsa yă gani!” Sai Ubangiji ya buɗe idanun bawan, ya duba, ya ga tuddai cike da dawakai da keken yaƙin wuta kewaye da Elisha.

  66. 26 Sa’ad da almajiran suka gan shi yana takawa a kan tafkin, sai tsoro ya kama su. Suka yi ihu don tsoro suka ce, “Fatalwa ce.”

    27 Amma nan da nan Yesu ya ce musu, “Ku yi ƙarfin hali! Ni ne. Kada ku ji tsoro.”

  67. 3 Amma kai ne garkuwa kewaye da ni, ya Ubangiji;

    ka ba ni ɗaukaka ka kuma ɗaga kaina.

    4 Ga Ubangiji na yi kuka mai ƙarfi,

    ya kuwa amsa mini daga tudunsa mai tsarki. Sela

    5 Na kwanta na yi barci;

    na kuma farka, gama Ubangiji yana kiyaye ni.

    6 Ba zan ji tsoro ko dubu goma

    suka ja dāgā gāba da ni a kowane gefe ba.

  68. 13 Kamar yadda mahaifi yake jin tausayin ’ya’yansa,

    haka Ubangiji yake jin tausayin waɗanda suke tsoronsa;

  69. 13 Yanzu an ji kome;

    ga ƙarshen magana.

    Ka ji tsoron Allah ka kuma kiyaye umarnansa,

    gama wannan shi ne dukan hakkin mutum.

    14 Gama Allah zai shari’anta kowane irin aiki,

    har da waɗanda aka yi a ɓoye,

    ko nagari ne, ko mugu.

  70. 14 Amma ku yi ƙuduri, wato, ku shirya zuciyarku, a kan ba za ku damu ba kafin lokacin, game da yadda za ku kāre kanku. 15 Gama zan ba ku kalmomi, da hikima waɗanda ba ko ɗaya daga cikin maƙiyanku, za su iya tsayayya da ku, ko su ƙaryata.

  71. 19 Allahna kuma zai biya dukan bukatunku bisa ga ɗaukakar wadatarsa cikin Kiristi Yesu.

  72. 1 Bayan wannan, maganar Ubangiji ta zo wa Abram cikin mafarki cewa,

    “Kada ka ji tsoro, Abram.

    Ni ne garkuwarka,

    kuma ladanka zai zama mai girma.”

  73. 12 Da Zakariya ya gan shi sai ya firgita, tsoro kuma ya kama shi. 13 Amma mala’ikan ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, Zakariya; an ji addu’arka. Matarka Elizabet za tă haifa maka ɗa, za ka kuma ba shi suna Yohanna.

  74. 28 Ban da waɗannan abubuwa, kowace rana ina ɗauke da nauyin kula da dukan ikkilisiyoyi.

  75. 10 A ƙarshe, bari ƙarfin ikon Ubangiji yă ba ku ƙarfi. 11 Ku yafa dukan kayan yaƙin da Allah yake bayarwa, don ku iya kāre kanku daga dabarun Shaiɗan. 12 Gama ba da mutane da suke nama da jini ne muke yaƙi ba. Muna yaƙi ne da ikoki, da hukumomi, da masu mulkin duhu, da kuma a ikokin da suke cikin a sararin sama. 13 Saboda haka sai ku yafa dukan kayan yaƙi na Allah, domin sa’ad da ranar mugun nan ta zo, ku iya yin tsayin daka, bayan kuma kuka gama kome, ku dāge.

  76. 11 Ku bauta wa Ubangiji da tsoro

    ku kuma yi farin ciki kuna rawar jiki.

  77. 4 Masu gadin kabarin kuma suka ji tsoro ƙwarai, suka yi rawan jiki, suka zama kamar matattu.

  78. 23 Tsoron Ubangiji yakan kai ga rai.

    Sa’an nan mutum ya sami biyan bukata, ba abin da zai cuce shi.

  79. 57 Ka zo kusa lokacin da na kira ka,

    kuma ka ce mini, “Kada ka ji tsoro.”

    58 Ya Ubangiji, ka goyi bayana;

    ka fanshi raina.

  80. 20 Amma yana cikin wannan tunani, sai wani mala’ikan Ubangiji ya bayyana masa cikin mafarki ya ce, “Yusuf ɗan Dawuda, kada ka ji tsoron ɗaukan Maryamu zuwa gidanka a matsayin matarka, gama cikin nan nata, daga wurin Ruhu Mai Tsarki ne.

  81. 5 Tsibirai sun gan shi suka kuma ji tsoro;

    iyakokin duniya sun yi rawar jiki.

    Suka kusato suka kuma zo gaba;

  82. 25 “Za a yi alamu a cikin rana, da cikin wata, da cikin taurari. A duniya, al’ummai za su yi baƙin ciki, su kuma rikice don tsoro, saboda ruri da kuma tafasar teku. 26 Mutane za su suma don tsoro, za su kuma yi fargaba, a kan abin da yake zuwa a bisan duniya, gama za a girgiza duniyar taurarin sararin sama. 27 A lokacin ne za su ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin girgije, da iko, da ɗaukaka mai girma. 28 Sa’ad da waɗannan abubuwa sun fara faruwa, ku tashi tsaye, ku ɗaga kawunanku, domin fansarku yana matsowa kusa.”