39 Bible Verses About Obedience
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
19 ’Yan’uwana ƙaunatattu, ku lura da wannan. Ya kamata kowa yă kasance mai saurin saurara, ba mai saurin magana ba, ba kuma mai saurin fushi ba, 20 gama fushin mutum ba ya kawo rayuwar adalcin da Allah yake so. 21 Saboda haka, ku rabu da ƙazamin hali da kuma kowace irin mugunta ku kuma yi na’am da maganar da aka shuka a cikinku da tawali’u, wadda za tă iya cetonku.
22 Kada ku zama masu ji kawai, ku ruɗi kanku. A maimakon haka ku zama masu yin abin da ta ce. 23 Duk wanda yake ji magana ne kawai, bai kuwa aikata abin da ta ce ba, yana kama da mutumin da ya kalli fuskarsa a madubi 24 bayan ya kalli kansa, sa’ad da ya tashi daga wurin, nan da nan sai yă manta da kamanninsa. 25 Amma duk mai duba cikakkiyar ƙa’idan nan ta ’yanci, ya kuma nace a kanta, ya zama ba mai ji ne kawai yă mance ba, sai dai mai yi ne yă zartar, to wannan shi za a yi wa albarka a cikin abin da yake yi.
-
15 “In kuna ƙaunata za ku yi biyayya da umarnina.
-
17 Gama in, ta wurin laifin mutum ɗaya, mutuwa ta yi mulki ta wurin mutum ɗayan nan, ashe, waɗanda suka sami kyautar alherin Allah a yalwace da kuma kyautar adalci za su yi mulki a wannan rayuwa ta wurin mutum ɗayan nan, Yesu Kiristi.
18 Saboda haka, kamar yadda sakamakon laifin mutum guda ya jawo hallaka ga dukan mutane, haka ma sakamakon aikin adalci guda ya sa Allah ya same mu marasa laifi, wannan kuwa kawo rai ga dukan mutane. 19 Gama kamar yadda ta wurin rashin biyayyar mutum guda, mutane masu yawa suka zama masu zunubi, haka kuma ta wurin biyayyar mutum guda, mutane da yawa za su zama masu adalci.
-
16 Ba ku sani ba cewa sa’ad da kuka miƙa kanku ga wani don ku yi masa biyayya a matsayin bayi, ko ku bayi ne ga zunubi, wanda yake kai ga mutuwa, ko kuwa ga biyayya, wadda take kai ga adalci, ashe, ba kun zama bayi ga wannan da kuke yi wa biyayya ba ke nan? 17 Amma godiya ga Allah don ko da yake a dā ku bayi ne ga ikon zunubi, da dukan zuciyarku kun yi biyayya ga irin koyarwar da aka danƙa muku. 18 An ’yanta ku daga zunubi, kun kuma zama bayi ga aikin adalci.
-
22 Sai Yahuda (ba Yahuda Iskariyot ba) ya ce, “Ubangiji, me ya sa za ka bayyana kanka gare mu amma ba ga duniya ba?”
23 Yesu ya amsa ya ce, “Duk mai ƙaunata, zai yi biyayya da koyarwata. Ubana zai ƙaunace shi, za mu kuwa zo wurinsa mu zauna tare da shi. 24 Wanda ba ya ƙaunata ba zai yi biyayya da koyarwata ba. Waɗannan kalmomin da kuke ji ba nawa ba ne; na Uba ne da ya aiko ni.
-
18 Ubangiji ya ce,
“Yanzu fa ku zo, bari mu dubi batun nan tare,
Ko da zunubanku sun yi ja kamar garura,
za su zama fari kamar ƙanƙara;
ko da sun yi ja kamar mulufi,
za su zama kamar ulu.
19 In kuna da niyya kuna kuma yi mini biyayya,
za ku ci abubuwa masu kyau daga ƙasar;
20 amma in kuka yi tsayayya kuka kuma yi tayarwa,
za a kashe ku da takobi.”
Ni Ubangiji na faɗa.
-
21 “Ba duk mai ce mini, ‘Ubangiji, Ubangiji,’ ne zai shiga mulkin sama ba, sai dai wanda yake aikata nufin Ubana da yake sama. 22 Da yawa za su ce mini a wannan rana, ‘Ubangiji, Ubangiji, ashe, ba mu yi annabci a cikin sunanka ba, ba kuma a cikin sunanka ne muka fitar da aljanu, muka yi abubuwan banmamaki da yawa ba?’ 23 Sa’an nan zan ce musu a fili, ‘Ban taɓa saninku ba. Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta!’
24 “Saboda haka duk wanda yake jin kalmomin nan nawa yake kuma aikata su, yana kama da mutum mai hikima wanda ya gina gidansa a kan dutse. 25 Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuma ta hura ta bugi gidan; duk da haka bai fāɗi ba, gama yana da harsashinsa a kan dutse. 26 Amma duk wanda yake jin kalmomin nan nawa bai kuwa aikata su ba, yana kama da wani wawa wanda ya gina gidansa a kan yashi. 27 Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuwa ta hura ta bugi gidan, sai ya fāɗi da mummunar ragargajewa kuwa.”
-
22 Amma Sama’ila ya ce,
“Ubangiji yana murna da sadaka da hadaya
fiye da biyayya ga maganar Ubangiji?
Yin biyayya ta fi hadaya
a kula kuma ta fi ƙibabbun raguna.
23 Gama tawaye yana kama da zunubi na duba,
girman kai kuma yana kama da bautar gumaka.
Saboda ka ƙi maganar Ubangiji,
shi ma ya ƙi ka da zaman sarki.”
-
21 Duk wanda yake da umarnaina yana kuma yin biyayya da su, shi ne wanda yake ƙaunata. Wanda yake ƙaunata kuwa Ubana zai ƙaunace shi, ni ma zan ƙaunace shi, in kuma bayyana kaina gare shi.”
-
10 In kuka yi biyayya da umarnaina, za ku kasance a cikin ƙaunata, kamar dai yadda na yi biyayya da umarnan Ubana na kuma kasance a cikin ƙaunarsa. 11 Na gaya muku wannan domin murnata ta kasance a cikinku, murnanku kuma ta zama cikakkiya. 12 Umarnina shi ne, Ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku. 13 Babu ƙaunar da ta fi wannan, a ce mutum ya ba da ransa saboda abokansa. 14 Ku abokaina ne, in kun yi abin da na umarta.
-
5 A cikin dangantakarku da juna, ya kamata halayenku su zama kamar na Kiristi Yesu.
6 Wanda, ko da yake cikin ainihin surar Allah yake,
bai mai da daidaitakansa nan da Allah wani abin riƙewa kam-kam ba,
7 amma ya mai da kansa ba kome ba,
yana ɗaukan ainihin surar bawa,
aka yi shi cikin siffar mutum.
8 Aka kuma same shi a kamannin mutum,
ya ƙasƙantar da kansa
ya kuma zama mai biyayya wadda ta kai shi har mutuwa,
mutuwar ma ta gicciye!
-
13 Saboda haka, ku shirya kanku don aiki; ku zama masu kamunkai; ku kafa begenku duka a kan alherin da za a ba ku sa’ad da aka bayyana Yesu Kiristi. 14 Kamar ’ya’ya masu biyayya, kada ku bi mugayen sha’awace-sha’awacen da dā kuke da su sa’ad da kuke rayuwa a cikin jahilci. 15 Amma kamar yadda wanda ya kira ku yake mai tsarki, haka ku ma sai ku kasance masu tsarki cikin dukan abubuwan da kuke yi; 16 gama a rubuce yake cewa, “Ku zama masu tsarki, domin ni mai tsarki ne.”
17 Tun da yake kuna kira ga Uba wanda yake yin wa kowane mutum shari’a bisa ga ayyukansa ba bambanci, sai ku yi rayuwarku a nan kamar baƙi cikin tsoro mai bangirma.
-
2 Ga yadda muka san cewa muna ƙaunar ’ya’yan Allah. Muna yin haka ta wurin ƙaunar Allah da kuma aikata umarnansa. 3 Ƙaunar Allah ita ce, a yi biyayya da umarnansa. Umarnansa kuwa ba masu nauyi ba ne;
-
27 Da Yesu yake cikin faɗin waɗannan abubuwa, sai wata mace daga cikin taron ta ɗaga murya ta ce masa, “Mai albarka ce uwar da ta haife ka, wadda ka sha mamanta.”
28 Yesu ya amsa ya ce, “A maimakon, masu albarka ne waɗanda suke jin maganar Allah, suna kuma biyayya da ita.”
-
14 Wanda amfani ne, ’yan’uwana, a ce wani yă ce yana da bangaskiya, amma ba shi da ayyuka? Anya, wannan bangaskiya za tă iya cetonsa kuwa? 15 A ce wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa ba shi da riguna ko abincin yini, 16 sai waninku yă ce masa, “Sauka lafiya, Allah ya ba da ci da sha da kuma sutura,” amma bai yi wani abu game da bukatunsa na jiki ba, ina amfani? 17 Haka ma bangaskiya ita kaɗai, in ba tare da ayyuka ba, matacciya ce.
18 Amma wani zai ce, “Kai kana da bangaskiya; ni kuma ina da ayyuka.”
Ka nuna mini bangaskiyarka ba tare da ayyuka ba, ni kuma zan nuna maka bangaskiyata ta wurin abin da nake yi. 19 Ka gaskata cewa Allah ɗaya ne. To, da kyau! Ai, ko aljanu ma sun gaskata wannan, har da rawan jiki.
20 Kai wawa, kana son tabbaci cewa bangaskiya marar ayyuka banza ce? 21 Ashe, ba a mai da kakanmu Ibrahim mai adalci saboda abin da ya yi ba ne sa’ad da ya miƙa ɗansa Ishaku a bisa bagade? 22 Ai, ka gani cewa bangaskiyarsa da ayyukansa sun yi aiki tare, bangaskiyarsa kuma ta zama cikakkiya ta wurin abin da ya yi. 23 Aka kuma cika nassin nan da ya ce, “Ibrahim ya gaskata Allah, aka kuma lissafta wannan adalci ne gare shi,” aka kuma ce da shi abokin Allah. 24 Kun ga cewa ashe mutum zai sami kuɓuta ta wurin abin da ya yi ne ba ta wurin bangaskiya kaɗai ba.
25 Ta haka kuma ashe, Rahab karuwan nan ba a ɗauke ta mai adalci ce saboda abin da ta yi ba ne sa’ad da ta ba wa ’yan leƙen asirin nan masauƙi ta kuma sallame su suka tafi ta wata hanya dabam? 26 Kamar yadda jikin da babu ruhu matacce ne, haka ma bangaskiyar da babu ayyuka matacciya ce.
-
15 Mala’ikan Ubangiji ya kira Ibrahim daga sama sau na biyu 16 ya ce, “Na rantse da kaina, in ji Ubangiji, domin ka yi wannan, ba ka kuwa hana ni ɗanka, makaɗaicin ɗanka ba, 17 tabbatacce zan albarkace ka, zan kuma sa zuriyarka su yi yawa kamar taurari a sararin sama, kamar kuma yashi a bakin teku. Zuriyarka za su mallaki biranen abokan gābansu, 18 ta wurin zuriyarka kuma dukan al’umman duniya za su sami albarka, domin ka yi mini biyayya.”
-
7 Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro, ka yi lura fa, ka yi biyayya da dokokin da bawana Musa ya ba ka; kada ka kauce ga bin dokokin ko hagu ko dama, domin ka yi nasara a duk, inda za ka je. 8 Kada ka bar Littafin Dokokin nan yă rabu da bakinka, sai dai ka yi ta tunani game da shi dare da rana, don ka lura, ka yi duk abin da aka rubuta a ciki, ta haka ne za ka yi nasara cikin duk abin da za ka yi.
-
1 ’Ya’yana ƙaunatattu, ina rubuta muku wannan ne don kada ku yi zunubi. Amma in wani ya yi zunubi, muna da wani wanda yake magana da Uba don taimakonmu, wato, Yesu Kiristi, Mai Adalci. 2 Shi ne hadayar kafara saboda zunubanmu, kuma ba don namu kaɗai ba amma har ma da zunuban duniya duka.
3 Ta haka za mu tabbata cewa mun san shi in muna yin biyayya da umarnansa. 4 Mutumin da ya ce, “Na san shi,” amma ba ya yin abin da ya umarta, maƙaryaci ne, gaskiya kuwa ba ta cikinsa. 5 Amma in wani ya yi biyayya da maganarsa, ƙaunar Allah ta zama cikakkiya ke nan a cikinsa. Ta haka muka san cewa muna cikinsa. 6 Duk wanda ya ce yana rayuwa a cikinsa dole yă yi tafiya kamar yadda Yesu ya yi.
-
21 Abokaina ƙaunatattu, in zukatanmu ba su ba mu laifi ba, muna da ƙarfin halin tsayawa a gaban Allah ke nan. 22 Muna kuma samun dukan abin da muka roƙa daga gare shi, domin muna biyayya da umarnansa, muna kuma yin abin da ya gamshe shi. 23 Umarninsa kuwa shi ne, mu gaskata da sunan Ɗansa, Yesu Kiristi, mu kuma ƙaunaci juna kamar yadda ya umarce mu. 24 Waɗanda suke biyayya da umarnansa kuwa suna rayuwa a cikinsa, shi kuma a cikinsu. Ta haka muka san cewa yana raye a cikinmu. Mun san haka ta wurin Ruhun da ya ba mu.
-
1 Dole kowa yă yi biyayya ga masu mulki, gama babu wani iko sai ko in Allah ya yarda. Duk hukumomin da muke su, naɗin Allah ne. 2 Saboda haka, duk wanda ya yi tawaye ga hukuma yana yin tawaye da abin da Allah ya naɗa ne, waɗanda kuwa suke aikata haka, za su jawo wa kansu hukunci.
-
46 “Don me kuke ce da ni, ‘Ubangiji, Ubangiji,’ amma ba kwa yin abin da na faɗa? 47 Zan nuna muku kwatancin mutumin da yakan zo wurina, yă ji kalmomina, yă kuma aikata. 48 Yana kama da mutumin da ya gina gida, wanda ya haƙa ƙasa da zurfi, sa’an nan ya kafa tushen ginin a kan dutse. Da ambaliyar ruwa ta taso, ƙarfin ruwa kuwa ya buga gidan, wannan bai jijjiga shi ba, domin an yi masa tushen gini na ainihi.
-
1 Ku ’ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku, gama ku na Ubangiji, abin da ya dace ku yi ke nan. 2 Doka ta farko wadda aka haɗa da alkawari ita ce, “Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, 3 don ka zauna lafiya, ka kuma yi tsawon rai a duniya.”
-
א Alef
1 Albarka ta tabbata ga waɗanda rayuwarsu ba ta da abin zargi,
waɗanda suke tafiya bisa ga dokar Ubangiji.
2 Albarka ta tabbata ga waɗanda suke kiyaye ƙa’idodinsa
suke kuma nemansa da dukan zuciyarsu.
3 Ba sa yin wani abin da ba daidai ba;
suna tafiya a hanyoyinsa.
4 Ka shimfiɗa farillan
da dole a yi biyayya da su.
5 Kash, da a ce hanyoyina tsayayyu ne
a yin biyayya da ƙa’idodinka mana!
6 Da ba zan sha kunya ba
sa’ad da na lura da dukan umarnanka.
7 Zan yabe ka da zuciya ta gaskiya
yayinda nake koyon dokokinka masu adalci.
8 Zan yi biyayya da ƙa’idodinka;
kada ka yashe ni ɗungum.
ב Bet
9 Yaya matashi zai kiyaye hanyarsa da tsabta?
Sai ta yin rayuwa bisa ga maganarka.
10 Na neme ka da dukan zuciyata;
kada ka bar ni in kauce daga umarnanka.
11 Na ɓoye maganarka a cikin zuciyata
don kada in yi maka zunubi.
-
12 Saboda haka, ya abokaina ƙaunatattu, kamar yadda kullum kuke biyayya ba kawai sa’ad da ina nan ba, amma yanzu da ba na nan tare da ku, ku ci gaba da yin ayyukan cetonku da tsoro da kuma rawan jiki, 13 gama Allah ne yake aiki a cikinku, don ku nufa ku kuma aikata bisa ga nufinsa mai kyau.
-
18 Mata, ku yi biyayya ga mazanku, yadda ya dace cikin Ubangiji.
19 Maza, ku ƙaunaci matanku kada ku nuna musu hali marar tausayi.
20 ’Ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku cikin kome, gama wannan yakan gamshi Ubangiji.
21 Ubanni, kada ku matsa wa yaranku lamba, don kada su fid da zuciya.
22 Bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya cikin kome; kada ku yi aikin ganin ido kamar masu neman yabon mutane, sai dai ku yi aiki tsakaninku da Allah, kamar masu tsoron Ubangiji. 23 Kome kuke yi, ku yi shi da dukan zuciyarku, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba ga mutum ba. 24 Kun san cewa zai ba ku gādo a matsayin ladanku. Ubangiji Kiristi ne fa kuke bauta wa. 25 Duk wanda ya yi laifi, za a sāka masa don laifinsa, babu sonkai.
-
4 Ku ji, ya Isra’ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne. 5 Ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku da dukan zuciyarku, da dukan ranku, da kuma dukan ƙarfinku. 6 Waɗannan umarnai da nake ba ku a yau, za su kasance a zukatanku. 7 Ku koya wa ’ya’yanku su da himma. Yi musu magana game da su sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya a hanya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi. 8 Ku ɗaura su su zama alamu a hannuwanku, ku kuma ɗaura su a goshinku. 9 Ku rubuta su a dogaran ƙofofin gidajenku, da ƙofofinku.
-
59 Na lura da hanyoyina
na kuma mayar da matakaina ga farillanka.
60 Zan gaggauta ba zan ɓata lokaci ba
in yi biyayya da umarnanka.
61 Ko da yake mugaye sun ɗaura ni da igiyoyi,
ba zan manta da dokokinka ba.
62 Da tsakar dare nakan tashi in gode maka
saboda dokokinka masu adalci.
-
13 Yanzu an ji kome;
ga ƙarshen magana.
Ka ji tsoron Allah ka kuma kiyaye umarnansa,
gama wannan shi ne dukan hakkin mutum.
14 Gama Allah zai shari’anta kowane irin aiki,
har da waɗanda aka yi a ɓoye,
ko nagari ne, ko mugu.
-
1 Ka tuna wa mutane su zama masu biyayya ga masu mulki da kuma hukumomi, su zama masu biyayya suna kuma a shirye su yi kowane abin da yake mai kyau,
-
16 Yau Ubangiji Allahnku ya umarce ku ku bi waɗannan ƙa’idodi da kuma dokoki, cikin natsuwa ku kiyaye su da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku. 17 Kun furta a wannan rana cewa Ubangiji shi ne Allahnku, cewa za ku kuma yi tafiya a hanyoyinsa, cewa za ku kiyaye ƙa’idodinsa, umarnansa da kuma dokokinsa, kuka kuma ce za ku yi masa biyayya. 18 Ubangiji kuwa ya furta a wannan rana cewa ku mutanensa ne, mallakarsa kamar yadda ya yi alkawari, da kuma cewa za ku kiyaye dukan umarnansa.
-
50 Ai, duk wanda yake aikata nufin Ubana wanda yake cikin sama, shi ne ɗan’uwana da ’yar’uwata da kuma mahaifiyata.”
-
3 Sai ya shiga ɗaya jirgin ruwan da yake na Siman, ya kuma roƙe shi yă tura shi kaɗan daga gaci. Sai ya zauna a jirgin ruwan, ya koyar da mutane daga ciki.
4 Da ya gama magana, sai ya ce wa Siman, “Ka tuƙa jirgin zuwa inda akwai zurfi, ka saukar da abin kamun kifinka ka kama kifi.”
5 Siman ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, duk dare mun yi ta fama ba mu kama kome ba, amma tun da ka ce haka, zan saki abin kamun kifin.”
-
6 Allah, “Zai sāka wa kowane mutum gwargwadon aikin da ya yi.” 7 Ga waɗanda ta wurin naciya suna yin nagarta suna neman ɗaukaka, girma da rashin mutuwa, su za a ba su rai madawwami. 8 Amma ga waɗanda suke sonkai waɗanda suke ƙin gaskiya suke kuma bin mugunta, akwai fushi da haushi dominsu. 9 Akwai wahala da baƙin ciki ga duk mutumin da yake aikata mugunta, da farko Yahudawa, sa’an nan Al’ummai, 10 amma akwai ɗaukaka, girma da salama ga duk mutumin da yake aikata alheri, da farko Yahudawa, sa’an nan Al’ummai. 11 Gama Allah ba ya nuna bambanci.
-
22 Ka kasa kunne ga mahaifinka, wanda ya ba ka rai,
kada kuwa ka rena mahaifiyarka sa’ad da ta tsufa.
-
16 To, fa, sai ga wani ya zo wurin Yesu ya tambaye shi ya ce, “Malam, wane abu mai kyau ne ya zama mini dole in yi don in sami rai madawwami?”
17 Yesu ya amsa ya ce, “Don me kake tambayata game da abin da yake mai kyau? Akwai Mai kyau Ɗaya kaɗai. In kana so ka sami rai madawwami, ka kiyaye dokokin nan.”
-
2 Ku ɗauki nawayar juna, a haka kuwa za ku cika dokar Kiristi.
-
13 Ni ne Alfa da kuma Omega, na Fari da kuma na Baya, Farko da kuma Ƙarshe.
14 “Masu albarka ne waɗanda suka wanke tufafinsu, don su sami izinin ci daga itacen rai su kuma shiga birnin ta ƙofofi.
-
29 Kash, da a ce zukatansu za su zama masu tsorona, su kuma kiyaye dukan dokokina kullum mana, saboda kome yă zama da lafiya gare su, da kuma ’ya’yansu har abada!
-
18 Sai Yesu ya zo wurinsu ya ce, “An ba ni dukan iko a sama da kuma ƙasa. 19 Saboda haka ku tafi, ku mai da dukan al’umman duniya su zama almajiraina, kuna yi musu baftisma a cikin sunan Uba, da na Ɗa, da na Ruhu Mai Tsarki, 20 kuna kuma koya musu, su yi biyayya da duk abin da na umarce ku, kuma tabbatacce, ina tare da ku kullum, har ƙarshen zamani.”
Shows Read in context, Share and Copy.