40 Bible Verses About God's Goodness

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About God's Goodness
  1. 5 Za su yi zancen ɗaukakarka mai daraja,

    zan kuma yi tunani a kan ayyukanka masu banmamaki.

    6 Za su yi magana game da ikon ayyukanka masu bantsoro,

    zan kuma yi shelar manyan ayyukanka.

    7 Za su yi bikin yalwar alherinka

    suka kuma rera adalcinka da farin ciki.

    8 Ubangiji mai alheri da kuma tausayi,

    mai jinkirin fushi cike kuma da ƙauna.

    9 Ubangiji nagari ne ga duka;

    yana tausayin dukan abubuwan da ya yi.

  2. 1 Saboda haka, kai da kake ba wa wani laifi, ba ka da wata hujja, gama a duk lokacin da kake ba wa wani laifi, kana hukunta kanka ne, domin kai da kake ba wa wani laifi kai ma kana aikata waɗannan abubuwa. 2 Yanzu mun san cewa hukuncin Allah a kan masu aikata waɗannan abubuwa daidai ne. 3 Saboda haka sa’ad da kai mutum kurum, kana ba su laifi, duk da haka kana aikata abubuwan nan, kana tsammani za ka tsere wa hukuncin Allah ne? 4 Ko kuma kana rena wadatar alherinsa, haƙurinsa, da kuma jimrewarsa ne ba tare da sanin cewa alherin Allah yana kai ka ga tuba ba ne?

    5 Amma saboda taurinkanka da zuciyarka marar tuba, kana tara wa kanka fushi a ranar fushin Allah, sa’ad da za a bayyana hukuncinsa mai adalci. 6 Allah, “Zai sāka wa kowane mutum gwargwadon aikin da ya yi.” 7 Ga waɗanda ta wurin naciya suna yin nagarta suna neman ɗaukaka, girma da rashin mutuwa, su za a ba su rai madawwami. 8 Amma ga waɗanda suke sonkai waɗanda suke ƙin gaskiya suke kuma bin mugunta, akwai fushi da haushi dominsu. 9 Akwai wahala da baƙin ciki ga duk mutumin da yake aikata mugunta, da farko Yahudawa, sa’an nan Al’ummai, 10 amma akwai ɗaukaka, girma da salama ga duk mutumin da yake aikata alheri, da farko Yahudawa, sa’an nan Al’ummai. 11 Gama Allah ba ya nuna bambanci.

  3. 19 Alherinka da girma yake,

    wanda ka ajiye domin waɗanda suke tsoronka,

    wanda ka mayar a gaban mutane

    a kan waɗanda suke neman mafaka daga gare ka.

    20 Cikin inuwar kasancewarka ka ɓoye su

    daga makircin mutane;

    a wurin zamanka ka kiyaye su lafiya

    daga harsuna masu zagi.

  4. 28 Mun kuma san cewa a cikin dukan abubuwa Allah yana aikata alheri ga waɗanda suke ƙaunarsa, yana waɗanda aka kira bisa ga nufinsa. 29 Gama waɗanda Allah ya rigyasani ya kuma ƙaddara su dace da kamannin Ɗansa, don yă zama ɗan fari cikin ’yan’uwa masu yawa. 30 Waɗanda kuwa ya ƙaddara, su ne ya kira; waɗanda ya kira kuwa, su ne ya kuɓutar; waɗanda ya kuɓutar kuwa, su ne ya ɗaukaka.

  5. 4 Na nemi Ubangiji, ya kuwa amsa mini;

    ya cece ni daga dukan tsoro.

    5 Waɗanda suke dubansa sukan haskaka;

    fuskokinsu ba sa rufuwa da kunya.

    6 Wannan matalauci ya yi kira, Ubangiji kuwa ya ji shi;

    ya cece shi daga dukan wahalarsa.

    7 Mala’ikan Ubangiji ya kafa sansani kewaye da waɗanda suke tsoronsa,

    ya kuwa cece su.

    8 Ku gwada ku gani cewa Ubangiji yana da kyau;

    mai albarka ne mutumin da yake neman mafaka a gare shi.

  6. 5 Sa’an nan Ubangiji ya sauko a cikin girgije ya tsaya can tare da shi, ya kuma yi shelar sunansa. 6 Sai Ubangiji ya wuce a gaban Musa, ya yi shela ya ce, “Ni ne Ubangiji Allah mai tausayi, mai alheri, mai jinkirin fushi, cike da ƙauna da aminci, 7 nakan nuna ƙauna wa dubbai, nakan kuma gafarta mugunta, tawaye da zunubi. Amma ba na barin mai laifi, ba tare da na hore shi ba; nakan hukunta ’ya’ya da jikoki har tsara ta uku da ta huɗu saboda laifin iyaye.”

  7. 17 Da Yesu ya kama hanya, sai wani mutum ya ruga da gudu ya zo wajensa, ya durƙusa a gabansa ya ce, “Malam nagari, me zan yi domin in gāji rai madawwami?”

    18 Yesu ya amsa ya ce, “Don me kake ce da ni mai nagarta? Ai, ba wani nagari, sai Allah kaɗai. 19 Ka san dokokin da suka ce, ‘Kada ka yi kisankai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka ba da shaida ta ƙarya, kada ka cuci wani, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’”

    20 Mutumin ya ce, “Malam, ai, tun ina yaro na kiyaye duk waɗannan.”

    21 Yesu ya kalle shi da ƙauna ya ce, “Abu ɗaya ka rasa, ka tafi ka sayar da duk abin da kake da shi, ka ba wa matalauta, za ka kuwa sami dukiya a sama. Sa’an nan ka zo ka bi ni.”

    22 Da jin wannan, sai mutumin ya ɓata fuskarsa, ya tafi da baƙin ciki, gama yana da arziki sosai.

  8. 22 Amma amfanin da Ruhu yake bayar shi ne ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci, 23 sauƙinkai, da kuma kamunkai. Ai, ba ruwan Doka da waɗannan abubuwa.

  9. 68 Kai nagari ne, kuma abin da kake yi yana da kyau;

    ka koya mini ƙa’idodinka.

  10. 18 Musa kuwa ya ce, “To, ka nuna mini ɗaukakarka.”

    19 Sai Ubangiji ya ce, “Zan wuce a gabanka, Ni Ubangiji zan yi shelar sunana a gabanka. Zan yi alheri ga duk wanda na so in yi masa alheri, zan nuna jinƙai ga duk wanda na so in yi masa jinƙai. 20 Amma ya ce, ba za ka ga fuskata ba, don ba mutumin da zai gan ni yă rayu.”

    21 Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Ga wani wuri kusa da ni inda za ka tsaya bisa dutsen. 22 A sa’ad da ɗaukakata tana wucewa, zan sa ka a cikin tsaguwar dutsen, in rufe ka da hannuna har sai na wuce. 23 Sa’an nan zan ɗauke hannuna, ka kuwa ga bayana; amma fuskata, ba za ka gani ba.”

  11. 13 Sa’ad da aka jarrabci mutum, kada yă ce, “Allah ne yake jarrabtarsa.” Gama ba ya yiwuwa a jarrabci Allah da mugunta, shi kuma ba ya jarrabtar kowa; 14 amma akan jarrabce kowane mutum sa’ad da muguwar sha’awarsa ta janye shi ta kuma rinjaye shi. 15 Sa’an nan, bayan da sha’awar ta yi ciki, takan haifi zunubi; zunubi kuwa, sa’ad da ya balaga yakan haifi mutuwa.

    16 Kada a ruɗe ku, ’yan’uwana ƙaunatattu. 17 Kowane abu mai kyau da kuma kowace cikakkiyar kyauta daga sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau. 18 Ya zaɓa yă haife mu ta wurin kalmar gaskiya, domin mu zama ’ya’yan fari na dukan abin da ya halitta.

  12. 7 Ubangiji nagari ne,

    mafaka kuma a lokacin wahala.

    Yana kula da waɗanda suka dogara gare shi,

  13. 5 Kai mai gafartawa da kuma mai alheri ne, ya Ubangiji,

    cike da ƙauna ga dukan waɗanda suke kira gare ka.

  14. 34 Ku yi godiya ga Ubangiji, gama shi nagari ne;

    ƙaunarsa madawwamiya ce.

  15. 6 Ka tuna, ya Ubangiji da jinƙai da kuma ƙaunarka mai girma,

    gama suna nan tun dā.

    7 Kada ka tuna da zunuban ƙuruciyata

    da kuma hanyoyin tawayena;

    bisa ga ƙaunarka ka tuna da ni,

    gama kai nagari ne, ya Ubangiji.

    8 Ubangiji nagari da mai adalci ne;

    saboda haka yakan koyar da masu zunubi a hanyoyinsa.

  16. 13 Har yanzu ina da ƙarfin gwiwa a wannan cewa

    zan ga alherin Ubangiji;

    a ƙasar masu rai.

  17. 11 Gama Ubangiji Allah rana ne da kuma garkuwa;

    Ubangiji yakan yi alheri da kuma daraja;

    ba ya hana kowane abu mai kyau

    wa waɗanda suke aikata abin da yake daidai.

  18. 43 “Kun dai ji an faɗa, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka, ka kuma ƙi abokin gābanka.’ 44 Amma ina gaya muku, ku ƙaunaci abokan gābanku kuma ku yi wa waɗanda suke tsananta muku addu’a, 45 don ku zama ’ya’yan Ubanku na sama. Shi yakan sa ranarsa ta haskaka a kan mugaye da masu kirki; yakan kuma sako ruwan sama a bisa masu adalci da marasa adalci. 46 In masoyarku kawai kuke ƙauna, wace lada ce gare ku? Ko masu karɓar haraji ma ba haka suke yi ba? 47 In kuwa kuna gai da ’yan’uwanku ne kaɗai, me kuke yi fiye da waɗansu? Marasa bin Allah ma ba haka suke yi ba? 48 Saboda haka sai ku zama cikakku, yadda Ubanku na sama yake cikakke.

  19. 7 “Ku roƙa za a ba ku; ku nema za ku samu; ku ƙwanƙwasa za a kuwa buɗe muku ƙofa. 8 Gama duk wanda ya roƙa, akan ba shi; wanda ya nema kuwa, yakan samu, wanda kuma ya ƙwanƙwasa, za a buɗe masa ƙofa.

    9 “Wane ne a cikinku in ɗansa ya roƙe shi burodi, sai yă ba shi dutse? 10 Ko kuwa in ya roƙe shi kifi, sai yă ba shi maciji? 11 In ku da kuke mugaye kun san yadda za ku ba da kyautai masu kyau ga ’ya’yanku, balle Ubanku na sama, ba zai fi ku iya ba da abubuwa masu kyau, ga su waɗanda suka roƙe shi ba!

  20. 16 To, fa, sai ga wani ya zo wurin Yesu ya tambaye shi ya ce, “Malam, wane abu mai kyau ne ya zama mini dole in yi don in sami rai madawwami?”

    17 Yesu ya amsa ya ce, “Don me kake tambayata game da abin da yake mai kyau? Akwai Mai kyau Ɗaya kaɗai. In kana so ka sami rai madawwami, ka kiyaye dokokin nan.”

  21. LITTAFI NA BIYAR

    1 Ku yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi;

    ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.

  22. 31 Allah ya ga dukan abin da ya yi, yana da kyau ƙwarai. Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta shida ke nan.

  23. 4 Ku shiga ƙofofinsa da godiya

    filayen gidansa kuma da yabo;

    ku gode masa ku kuma yabi sunansa.

    5 Gama Ubangiji yana da kyau kuma ƙaunarsa madawwamiya ce har abada;

    amincinsa na cin gaba a dukan zamanai.

  24. 22 Domin ƙaunar Ubangiji ba mu hallaka ba;

    gama jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa.

    23 Sababbi ne kowace safiya;

    amincinka kuwa mai girma ne.

    24 Na ce wa kaina, “Ubangiji shi ne nawa;

    saboda haka zan jira shi.”

    25 Ubangiji mai alheri ne ga waɗanda suke da bege a cikinsa,

    ga kuma wanda yake neman shi;

    26 yana da kyau ka jira shiru

    domin samun ceton Ubangiji.

  25. 22 Ka lura fa da alheri da kuma tsananin Allah, tsanani ga waɗanda suka fāɗi, amma alheri a gare ka, da fata za ka ci gaba cikin alherinsa. In ba haka ba, kai ma za a sare ka.

  26. 2 Kada ku ci gaba da yin abin da duniya take yi, sai dai ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so yake, abu mai kyau, mai daɗi da kuma cikakke.

  27. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Wani maskil ta Dawuda. Sa’ad da Doyeg mutumin Edom ya tafi wurin Shawulu ya ce masa, “Dawuda ya tafi gidan Ahimelek.”

    1 Me ya sa kake fariya game da mugunta, kai babban mutum?

    Me ya sa kake fariya dukan yini,

    kai da kake abin kunya a idanun Allah?

  28. 18 Wani mai mulki ya tambayi Yesu ya ce, “Malam managarci, me zan yi don in gāji rai madawwami?”

    19 Yesu ya amsa ya ce, “Don me kake kira na managarci? Ai, ba wani nagari, sai Allah kaɗai.

  29. 9 Ni ne ƙofar; duk wanda ya shiga ta wurina zai sami ceto. Zai riƙa shiga yă fita yă kuwa sami wurin kiwo. 10 Ɓarawo yakan zo don yă yi sata ne kawai da kisa da kuma ɓarna. Ni kuwa na zo ne don su sami rai, su kuma same shi a yalwace.

    11 “Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau yakan ba da ransa domin tumakin.

  30. 6 Kun ga, a daidai lokaci, yayinda muke marasa ƙarfi, Kiristi ya mutu saboda waɗanda ba su san Allah ba. 7 Da ƙyar wani yă mutu saboda mai adalci, ko da yake saboda mutumin kirki wani zai iya ƙarfin hali yă mutu. 8 Amma Allah ya nuna mana ƙaunarsa a wannan. Tun muna masu zunubi tukuna, Kiristi ya mutu dominmu.

  31. 4 Gama duk abin da Allah ya halitta yana da kyau, kada kuma a ƙi kome in dai an karɓe shi da godiya, 5 domin an tsarkake shi ta wurin maganar Allah da kuma addu’a.

  32. 2 Na ce wa Ubangiji, “Kai ne shugabana;

    in ba tare da kai ba, ba ni da wani abu mai kyau.”

  33. 8 Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa

    da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane,

    9 gama yana shayar da masu ƙishirwa

    yana kuma ƙosar da mayunwata da abubuwa masu kyau.

  34. 1 Ku yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi.

    Ƙaunarsa madawwamiya ce.

    2 Ku yi godiya ga Allahn alloli.

    Ƙaunarsa madawwamiya ce.

    3 Ku yi godiya ga Ubangijin iyayengiji.

    Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  35. 14 Zan ƙosar da firistoci da yalwa,

    mutanena kuma za su cika da yalwa,”

    in ji Ubangiji.

  36. 9 Yetro ya yi murna da jin duk abubuwa masu kyau da Ubangiji ya yi wa Isra’ila, wajen cetonsu daga hannun Masarawa.

  37. 14 Ni kaina na tabbata, ’yan’uwana, cewa ku kanku kuna cike da kirki, cikakku cikin sani da kuma ƙwararru don yin wa juna gargaɗi.

  38. 9 In muka furta zunubanmu, shi mai aminci ne, mai adalci kuma, zai gafarta mana zunubanmu, yă kuma tsarkake mu daga dukan rashin adalci.

  39. 35 Amma, ku ƙaunaci abokan gābanku, ku kuma yi musu alheri, ku ba su bashi, ba da sa zuciya sai an biya ku ba. Ta yin haka ne kawai, za ku sami lada mai yawa, ku kuma zama ’ya’yan Mafi Ɗaukaka, gama shi mai alheri ne ga marasa godiya da mugaye.

  40. 9 Ubangiji ba mai jinkiri ba ne wajen cika alkawarinsa, yadda waɗansunku suka fahimci jinkiri. Yana haƙuri da ku, ba ya so wani yă hallaka, sai dai kowa yă kai ga tuba.